Author : Bilyn Abdull Category : Romance
da yanayin nuna tausayawa a gareshi da kuma ɓoyayyar fargaba. Shi ko kallonta yake kamar yana karanta rubutu a cikin idanun nata.
Murmushi ya mata mai nauyi da isar da saƙo kakkaifa, ita ma sai ta maida masa murtani a karo na farko. Ya lumshe idanu ya sake buɗewa saboda murmushin nata ya shigesa, cike da iya sarrafa harshe da wayo cikin siririyar murya ya furta, “Na fahimci idanunki suna cike da tambayoyi. Bari na amsa su da yanayin da kika fi buƙata a maimakon magana. Ki ce da ni kawai (Kana tare da ni Besty?). Niko nayi alƙawarin zance da ke, (Har abada)”.
Murmushi ta sake sakar masa a hankali, zuciyarta na ɗan sakewa, gangar jikinta na rage tsoron, haka ma bugun zuciyarta na saisaita a cikin ƙirjinta. Kanta ta kauda gefe a cike da kunya, ciki-ciki ta furta, “Kana da wayo sosai”.
Murmushin yayi shima, sai kuma ya rungumeta a hankali. Babu matsawa. Babu gaggawa. Sai nutsuwa da shauƙi mai sanyi, a cikin kunnenta ya ce, “Duk wayona na kaiki ne, keda kika ɗauka buhunnan alƙawurra gashi kina neman ɓigewa da zame-zame.”
Ƙoƙarin janye jikinta tayi, sai ya hanata yin hakan ta hanyar sake rungumeta da ƙyau. “Ina kike ƙoƙarin guduwa? Bayan naji wani abu mai sanyi yana ratsani, kamar numfashinki. Rungumarki ce kuma tamkar addu’ar da ta yi karo da cikar amsar da nake nema. Ina so ki cigaba da zama a haka a kirjina, ba dan yau kawai ba, sai dan in cigaba da tuna cewa kece sassanyan lambun da zuciyata take so ta huta daga yau har zuwa ƘARSHEN RAYUWA. Na miki alƙawarin in sha ALLAHU zaki cigaba da kasancewa anan. A duk lokacin da duniya ta rikice, zan ajiyeki a wannan mafakar ta jikina babu mai damunki koda da harara”.
Hawaye ne suka gangaro mata a hankali, tsigar jikinta na ƙara tashi saboda salon da yake mata a cikin gashi mai nauyi ne. Muryarta a ƙurya sosai ta ce, “Kafin wata rana ina kallonka ne a matsayin garkuwa ta, amma a yanzu sai na ji kamar zuciyata na rawa da zama cikin ƙaulanin ƙila wa ƙala musamman a gaɓar tuna rana mai girma da tarihi ya ajiye mana”.
Fuskarsa ya cusa cikin wuyanta, cikin dunƙullen amo ya furta, “Ki bar ni na lallaɓa maki tunanin da ke yawo cikin gangar jikinki, na shafe miki wancan tarihin dake a zuciyarki, na ajiye miki sabon tarihin da zan tabbatarma duniya ke ɗin SARAUNIYAR mata ce. Tanadina mai girma ne a kanki, mai kuma muhimmancin da zai fitar da saƙon daya daɗe AJIYE A DUHU ne Maanal. Ki yarda da ni, duk wata fargaba da ta zo da tsoro ko rashin tabbas, zan shafe ta a yau cikin wannan daren. Ina taɓa gangar jikinki ne tamkar yadda ake taɓa ZINARE a tsakiyar talalaɓuwar ƙasa. Saboda a cikinki akwai daraja da tsarki da bai kamata a yi gaggawa da shi ba.”
Ajiyar zuciya ta sake saukewa, fargabarta da tsoro na sake daidaituwa a cikin gangar jikinta. Ɗagowa tai a hankali ta zuba masa ido, shima kallon nata yake a cikin ɗan hasken ɗakin mara ƙarfi. Lips ta motsa a hankali zatai magana ya ɗaura yatsarsa a kansu yana wani lumshe mata idanun da buɗewa. “Ba sai kince komai ba. Idanunki suna gaya min abubuwan da baki ba zai iya furtawa ba ma. Na ga fargaba, tsoro, juyayi, tausayi, rauni, karaya, amma na fi ganin ƙauna da sha’awa mai tsarki.”
Idanu ta zaro sosai. Ya kashe mata ido ɗaya. “Yes! Na ga wata murya a cikinsu da ke cewa, (KA KULA DA NI! KA BANI GARKUWA!) kuma na rantse, zan kula Besty, zan baki garkuwa daga ɓangaren kowanne abun hari kina barci ko ido biyu..”
Sosai ta wani kalar lumshe idanu tana ɗan murmushi, dan yanda bakinsa ya buɗe yake zuba zance sai take jin shauƙin hakan. Shima murmushin yake, sai kuma ya kai yatsarsa a saman idanunta yay kamar yana sosawa, hakan ya sata ta ɗan lumshe ta sake buɗewa a cikin nashi. Shima lumshe nasan yayi ya sake buɗewa a cikin nata. “Idanunki sunyi shiru, amma tawa zuciyar nata amsa dukkan abinda suke son isarwa. Bari mu kalli juna har duniya ta manta da lokaci. Saboda ni da ke mun ishi juna a wannan ƙyaƙyƙyawan dare har zuwa sassanyar safiya. Kice kin amince ni kuma zan baki tabbaci”.
Cikin wani irin tausayinsa da kasalliyar murya ta ce, “Na amince” ta faɗa tana ɗan sumbatar lips ɗinsa, sai kuma tai yunƙurin ƙwace jikinta zata juya dan kunya. Sai kawai ya wani riƙota da saura ya ɗaura tausasan lips ɗinsa akan nata.
Alhmdllh kamar yanda yay fata batayi musu ba, sai ma ajiyar zuciya da take saukewa a jajjere. Sannu a hankali ta miƙa wuya tare da sake shigewa jikinsa harma da maida murtani, hakan sai ya ƙara masa ƙaimi da armashi, gaba ɗaya yaji duniyar tai wani irin zama shirun da su kaɗai yake zaton sun rage a raye a cikinta.....
(Ikon ALLAH AA mu duk mun mutu kenan, kai dai AA ka dinga tsoron ALLAH ☹️🥱😏)...
_____★
A lokacin da can AA kema tunanin duk mun mutu sai shi da Manaluwa gyatumarsa ta haihuwa Mamy ce a yanayi irin na matattu, dan duk yanda taso zuwa sashen nasa da alama jiri bazai barta ba. Cike da zuga Maman Saheeba ta ce, “Yaya kiyi kwanciyarki kawai bara ni naje na kira miki shi kawai. Dan wannan juwar zata iya kadaki a hanya”.
Cike da gamsuwa Mamy ta amince, Maman Saheeba ta miƙe ta ɗauka hijjab ta zura ta ɗauka wayarta, “Ki ajiye wayarki a kusa idan yay gaddama zan kiraki”.
Kai Mamy ta jinjina mata kawai. fitowa daga sashen Maman Saheeba tai, ta nufi sashen AA. Tana zuwa kofar kitchen ɗin sashen ta baya Saheeba da Nuratu da'a daren nan tazo gidan duk ta rame tai duhu na tsaye na jiranta. Murmushi suka sakarma juna, ƙasa-ƙasa tace ku muje. Sai da suka gama bin gidan da kallo suka tabbatar ko'ina tsitt hatta masu gadi sun kwanta sannan sukai wuff ta suka shige ciki. Cikin sa'a kuwa ƙofar a buɗe take. Cak Mamman Saheeba ta tsaya tana bin kitchen ɗin da kallo saboda ta cikinsa suka shigo, itam Nuratu sai ta tsaya tana kallon komai, dan kuwa dai komai yaji, daka gani kuma kasa na ƴar gata ne. Maimakon su wuce abinsu sai Saheeba catai, “Eh lallai wannan daka gani kasan kuɗin Ajwaad ne da aka wawura bara muga store ɗin shi kuma uwar mi suka ajiye mata tunda anje an tile kayan gara sashen haɗamatu (Wai Oum). Nuratu batai niyyar shiga ba, sai ta ja kujerar work table ta zauna, ga ƙasan zuciyarta na cigaba da bata shawarar ta koma karta biye ma su Mamanata. Amma gefen sheɗaniyar na angizata akan bawani nan taje taga ƙwal uwar daka... A haka Saheeba da mamansu suka fito suka sameta, sai faman taɓe baki suke dan sun rasa abin kushewa acan ɗin ma. Miƙewa kawai Nuratu tai suka shige ciki, Mammansu na ayyana a ranta ai wlhy ko tsinke bazasu sayama Nuratu ba suma shine zai yi komai kamar wannan dan sun san shine yayi. Sun sami falon komai a kashe, Mamman Saheeba ta haska fitilar wayarta ta kunna ta falon. Sai ta shiga leƙe-leƙen bedrooms ɗin ƙasan tana faɗin, “Kuyi maza ku sassaka mu haura saman kafin suji motsin mu”.
Da to Nuratu da Saheeba suka amsa suna buɗe wasu ƙullikan tsuma suka shiga cusawa a cikin kujeru, sai rubutu a gora shima suka yayyarfa, sai da suka gama komai tsaf suka haura sama harda maman tasu......
ALLAH ka rabamu da mugun ji da mugun gani dai to🥱😜😂🏃.
_______★
Sannu a hankali salon wasan ya fara canjawa, jikin Maanal ya fara rawa, tsoronta na dawowa fresh a zuciya. Ƙoƙarin janye jikinta take amma babu dama, ga baki ma ya rufe mata ruf da nashi ba damar magana. Dai-dai yana gama ɓalle illahirin botiran rigarta ya finciketa yay wurgi da ita Maanal data fara shiga gigita dan Alaramma AA ya fara zuwa inda ake masa rowa ta sake ƙoƙarin fincike jikinta ya sake nuna mata ina ai ta riga ta shiga tarko kuma, ba kuma yaji baya gani sam. Siffofin komawarsa kurma, kuma makaho suka fara tattara kansu. A dai-dai gaɓar ya gama rabasu da garkuwarsu daga ita har shi, ALLAH ya bama Maanal sa'ar fincike lips ɗinta da jikinta tana ƙoƙarin matsawa ya riƙota, ta fashe masa da kuka. Cikin matuƙar gigitar roƙo da magiya ta ce, “Wlhy bazan iya ba! Ka tausaya min na tuba Yaya Ajwaad na tuba.”
Ƙasa-ƙasa muryarsa a dasushe kamar tata shima a raɗa ya ce, “Idan na barki mutuwa zanyi Maanal”.
“Wlhy nima mutuwa zanyi Ajwaad”.
“I'm sorry”.
“Ka riƙe Sorryn ni ka bani salama”.
“Idan na baki ni taya zan samu tawa salamar. Ki zama mai adalci da tausayi”.
“Na shiga uku, da gaske ka zama kurma da makahon da kai alƙawarin komawa? Kafa min alƙawarin barina na har abada”.
“Maybe a lokacin dana faɗa aljanuna ne, amma Maanal wake alƙawari zana rubutu akan ruwa mai gudana! Bayan yasan in ma yayi kamar abu ne bamai yiwuwa ba”.
“Ka tuna kai fa Bestyna ne”.
“Hakan ne zai sake bamu damar zama AMINAI na musamman na kuma har abada”.
“Bazaka haƙura ba kenan”.
“Idan na haƙura ni wazai bani haƙurin”.
“Besty!”.
“Na'ama Bestyn Bestynsa”.
Baki ta sake buɗewa zatai magana ƙarfin kukanta na ƙaruwa ya ce, “Shiiiii!!!” ya sake maida lips ɗinsa akan nata. Yayinda yake wani kalar bata saƙonsa mai nauyi da karya garkuwar jiki, cikin gushewar tunani ya sake himmatuwar isa inda ya daɗe a cikin mafarki da hasashen zuciya kawai..
A dai-dai lokacin su Maman Saheeba ke ƙarasa hawawo upstairs ɗin, a kuma dai-dai nan Maanal ta fisge lips ɗinta a karo na biyu ta fashe da kuka mai ƙarfi na azaba da ƙwala kiran sunan Oum da Ammie a tare cikin matsamnaciyar gigita.........✍️
Subahannallah, Jamila tayi ɓari, aranar jajibiri😆😛. A ririya-ririya Kamila💃 ƴar sarƙar wuya... Iya nan na iya🤣😜🏃
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖7️⃣4️⃣
______________
.........Ai wani irin cak Maman Saheeba da Saheeba da Nuratu suka tsaya kamar waɗan da aka dakama tsawa, sai kuma suka kalla juna, mizai faru sautin disa-sashshiyar muryar AA ce ta daki cikin kunnuwansu. Tare da fitar kukan Maanal dake magiya da roƙo da neman ɗauki harda sunan Mamy kanta amma tabbas AA ya zama kurma, kuma makawo dan yau dai sai addu'a kawai.....
Rikica, Mama da Saheeba sukaji a ƙasa, da sauri suka kalli wajen suma nasu jikunan na rawa. Al'amari mai matuƙar nauyi da girma na cigaba da shiga cikin kunnuwansu. “Na shiga uku! Nuratu! Nuratu!”. Suka shiga faɗa suna kamo Nuratu datai wanwanr a ƙasa, cike suke da tashin hankali da ƙunci da baƙin ciki ƙololuwa dan duk wani mai shekarun girma irin Maman Saheeba dama Saheeba ɗin yaji wannan kukan da Maanal keyi har tana yin kamar zata shiɗe yasan ina.....
Sosai jikin Maman Saheeba ke sake rawar mazari, wlhy da tasa abin kunnayensu zasu zo suji musu kenan da bata yarda sunzo ɗin ba. Gashi nan basu gama saka maganin ba sunji abinda zai yi maganinsu. Amma shegen bokan nan fa ya tabbatar mata da yayi aiki babu abinda Ajwaad zai ma yarinyar nan a wannan daren, acewarsu ma barci zai sakar musu har suzo suyi abinda zasu yi su fita wani bai sani ba, dan ita kanta Mamyn abu ta zuba mata a shayin data sha kuma bokan ne ya bata.
______★
Duk rakin Maanal a zuwan farko tamkar wasa farin girki ne ga Ajwaad, dan ta riga ta firgita matuƙa taƙi bashi damar samunta yanda yake so. A nashi ɓangaren shima yanayin halin daya daɗe a ciki ya sashi samun nutsuwa bada wani nisa ba. Koda ya matsa daga jikinta yanda ta cigaba da masa kuka kansa kawai ya girgiza, dan shi yasan ba'ai komai ba. Kai bama a fara wasan ba na gaskiya dan sharar hanya kawai akayi. Komai baice da ita ba, sai ma miƙewa da yay yana tafiya a dudduƙe saboda cikinsa dake wani irin sabon ƙullewa. Bayi ya shiga ya haɗa ruwa masu zafi, koda ya dawo cike da dauriya ya ɗagata cak. Kuka ta sake sakar masa, cike da tsiwa tana faɗin ita ya sauketa ya daina taɓata zata iya. Bata so ya barta. Bai kulata ba, sai da ya direba a jacuzzi ɗin tana ƙoƙarin miƙewa tare da sakin kuka ya riƙeta da ƙyau.
Kuka ta sakar masa sosai wai zafi. Cikin shaƙaƙƙiyar muryarsa ya raɗa mata, “Faɗan da ba'a fara ba har kike tunanin maida duka, dama kin hutar da kanki dan komai ba'a fara ba yarinya. Yaushe ma aka kai maƙura balle kiji zafin, daga tonon farko kawai”
Da sauri Maanal ta kallesa hawaye shaɓe-shaɓe a fuska duk da ba komai ta fahimta ba a kalaman nasa ta gane wasu sarsi. Gira ya ɗage mata yana sake ƙanƙance rinannun idanunsa dake cike da fitina. Sai kuma ya ɗan cije baki saboda cikinsa sake ƙullewa yake yi. Ita kanta ta fahimci akwai abinda ke damunsa. Amma haushin abinda yay mata da ƙin saurarenta da yayi da rashin tausayi yasa taƙi magana. A ƙasan zuciyarta kuwa mamaki take ashe ma ba wata wahala sosai da ake wani sha, dan zafin da take ji ba wani ƙololuwa bane matuƙa kamar yanda take ji ana faɗa, amma dai tana jin zafin tabbas. Haka ya gama kimtsata cikin dauriya ya sata tai wanka shima yayi sannan ya sake ɗakkota suka fito. Saman kujera ya ajiyeta ya kwashe zanin gadon, duk da yasan bazai kasance da damuwa sosai a tare da shi ba amma dai zasu fi samun nutsuwa idan ya canja ɗin. Sai da ya maida mata kayanta tana faman masa ciccika bai kulata ba ya maidata a gadon ya rufa mata duvet. Sai faman sauke ajiyar zuciya take na uban kukan da taci wanda raki yafi yawa. Shi dai yama kasa kwanciyar saboda cikinsa da yay masifar ɗaurewa. Takai yama kasa zaman kujerar ya koma ƙasan lallausan carpet ɗin gaban gadon kawai. Tun yana ɗaukar al'amarin zai iya lafawa harya fara fin ƙarfinsa. Dan wani sabon yanayi jikinsa ke ƙara ɗauka tamkar ma baiyi komai ba. Ga wani irin rawa da jikin nasa ke ƙoƙarin fara yi. Numfashinsa kansa wani irin fisga yake fita a cikin ƙirjinsa, amma kasancewarsa jarumi gwanin dakewa a nutsensa yake a zahirance. Jin abin na neman fin ƙarfinsa dole ya juya ya ɗauka wayarsa daya aje saman side drawer, ko a lokacin bai wani lura da tarin miss call ɗin Mamy ba ya shiga ƙoƙarin fara bincike akan minene ya kawo masa hakan, ko dan ya samu ya rage damuwarsa ne yake jin ciwon?. Da ƙyar ma yake iya gane bayanin saboda ciwo dake cigaba da cin ƙarfinsa. Sakamakon da binciken ya bashi ne ya sashi ji a ransa akwai matsala. Saboda ya tabbatar Maanal ta riga ta firgita, idan yace zai sake zuwa mata to wlhy zata iya sume masa ma shi kuma yayi imanin a karo na biyu bazai iya mata sassaunci ba mai gaba ɗaya zai yi ba kamar a farko ba, mai gaba ɗayan ma irin na babu ragi babu ragowar nan. Wayar ya ajiye ya sake kifewa na tsawon lokaci, wlhy ji yake kamar bazai ga wayewar garin gobe ba idan bai samu mafita ba. Dole ya sake ɗaukar wayar saboda shawarar da zuciyarsa ke basa akan kiran RK ko zai bashi wata mafitar bayan wannan.
Sai da wayar ta kusa tsinkewa RK ya ɗauka, cikin yanayin barci ya ce, “Waye?”.
Ɗan jimmm AA yayi, kafin acan cikin maƙoshi a kuma dakensa ya furta, “Ajwaad”.
Tsai RK yayi shima, sai kuma a hankali ya janye Nuwaira dake jikinsa dan wayo ya mata suka tafi masaukinsa bayan sun ma AA rakkiya. A nutse shima ya furta, “Are you okay?”.
Da ƙyar AA ya ce, “No!”.
Gaban RK ya ɗan faɗi, Daga gadon ya sauka gaba ɗaya ya nufi ƙofar fita, sai da ya buɗe ya juya ya ɗan kalla Nuwaira, ganin barci take sosai ya fice. Sai da ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun falon ya kunna lamp dake gefen kujerar sannan yay ɗan gyaran murya, dan yana jiyo saukar numfashin AA a wahale duk da yana ƙoƙarin dakewa. Cikin serious sosai RK ya ce, “Ajwaad akwai matsala ne?”.
Shiru AA ya masa na tsawon sakanni kamar bazai ce komai ba sai zuwa can ya ce, “Cikina ke ciwo, ina jin kamar zan mutu. Ka faɗa min me zanyi da zan samu sassauci?”.
Zama RK ya gyara, babu wasa a tare da shi sam ya ce, “Ajwaad! Ga matarka a kusa da kai mi kake jira? Kaima kasan minene ma'anar wannan ciwon cikin, dan duk da baka kasance likita ba kanada ƙoƙarin bincike akan abubuwa”.
“Rafeeq a tsorace take matuƙa,