AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   175 / 213

522K to 525K   out of 636.6K words

har sai da Abah yay mata magana. Yayinda Mabera da shi sarai ya santa ya wani ɗauke kai kawai gefe yay fuska. Haka suka fice Haule na waiwayensa har abin ya bama Abah mamaki. Kamar zai yi magana sai kuma yay shiru kawai.
       Babu wani kunya babu baƙunta Mabera ya buɗe ciki yaci abinci yay nak. Sai da ya kammala kafin ya kalla Abah ya ce, “Darma ya bayan rabuwa?”.
         “Kai ya kamata na tambaya bayan rabuwa Mabera. Daga kammala hidimar ƙasa shike nan kawai ka ɓace.”
     Murmushi sosai Baban Nazeefa yayi, sai kuma ya kalla Abah, “Ɓacewata ta farko kasan dalilinta Darma, kawai dai kana nan da halinka bazaka canja ba. Mutum ya maka laifi ka sharesa kamar baka san mima yayi ba”.
        Murmushi shima Aban yayi a kwaro na barkatai, ya kalla Mabera da ƙyau. “Abinda ya faru ai ya riga ya faru ya kuma wuce. Amma ban taɓa tunanin a dalilin hakan zaka gujeni ba Junaid. A tunani na ni da kai ai mun zama jini ɗaya. Kuma dama zo mu zauna ai zo mu saɓa ne. Kayi kuskure na kuma gaya maka kuskurenka a lokacin. Na kuma sameka har gida na nuna maka komai ya wuce ina buƙatar mu koma yanda muke. Saboda kaine aboki dana fara yi a duniya kuka amini bayan ƴar uwata Fateema dana tashi da ita. Bazan so kuɗi ya zama sanadin yankewar alaƙarmu ba. Amma abin mamaki na jika shiru bayan na dawo sake nemanka akace min ai bama asan inda kake ba, a dawowa ta biyu suma su Abbah na samu basa nan wai sun bar Kano. Na shiga mamaki da ruɗani sosai, na kuma cigaba da nemanka amma ko labarin wanda yasan inda kake bamma samu ba. Daga ƙarshe dole na haƙura duk da ina jin kewarka, yanda ka zauna a zuciyata yasa bana rabo da yin mafarkinka. Sannan a komai na ban san miyasa ba ban taɓa mantawa da kai ba”.
      “ALLAH sarki Darma lallai kai amini ne na ƙwarai kuma na gaskiya. Ni kaina kana a zuciyata, dan ban taɓa na manta da kai ba a dukkan al'amurana. Amma kafin na baka dukkan labarin bayan rabuwa bari na fara gaisawa da Fateema, dan nasan idan muka fara lokaci zai iya riƙemu da yawa”.
     Ɗan jimmm Abah yayi, sai Mabera yay murmushi. “Darma wannan ba Maberan da bane, in dai akan Fateema ne ka ɗauka a yanzu babu komai a wannan zuciyar sai alkairi wlhy. Kuma ko a baya kaima kasan da hakan, hasalima randa naci duka a wajenka kuskure aka samu da rashin fahimta”
      Sai da Abah ya sauke ajiyar numfashi, kafin ya kalla Mabera cikin ido sosai. “Nasan babu koman ai Mabera, kai koda akwai koman ma a yanzu babu abinda komai zatayi.”
          “Darma nawa, kana nan a yanda na sanka dai”.
    Ƴar dariya Abah yayi, ya ce, “Kai kuma kana nan da saka idonka ba”. Shima Mabera sai ya dara. Abah ya ɗauki waya yay kiran Oum yace dukansu suzo har yaran......

________★

       Wani irin azababben mari Hajiya Basariyya ta ɗauke fuskar Huznah da shi. Cikin matuƙar kaushin harshe ta ce, “Na rantse miki da ALLAH idan kinga ba'ai miki wannan allurar ba mutuwa nayi. Amma babu fashi wannan shegen cikin sai na zubar da shi. Kuma aurenki da Sageer ya ƙare, idan bai sakeki ta arziƙi ba zai sakeki ta tsiya-tsiya. Madam yi aikin ki”.
       Doctor dake zaune tana kallon su ta gama haɗa allura ta taso kai tsaye ta iso inda Huznah take. Babu tausayinta ko na sisin kwabo a zuciyarta duk da yanda take kuka tace ta tashi suje ciki. Wani ɗaki dake anan cikin falon suka shiga. Daga gani ɗakin yara ne, Huznah ta ɗan bi ɗakin da kallo, sai kuma ta kalla Doctor tana share hawaye tace zatai fitsari. Karaf Hajiya Basariyya dake bayansu tace, “Baki isa ba, doctor yimata alluran inma fitsarin zatai”. Ai ko sai Huznah ta sake fashewa da kuka. Ko'a jikin Hajiya Basariyya balle Doctor dake aikin kuɗinta, haka ta danna mata allurai har biyu masu ƙarfi, sannan tace taje tai fitsarin. Kuka Huznah take yi na fitar hankali. Tana shiga bayi ta ciro ƙaramar wayarta da take ɓoyewa suna waya da Sageer dan Hajiya Basariyya ta kwace waccan shine Basira ta bata wannan ƙaramar sai take ɓoyewa shiyyasa Hajiya Basariyyan bata san da ita ba har yanzu. Shiru tai tana tunanin wa zata kira. Zuwa can kawai ta yanke shawarar kiran Sageer, sai dai harta yanke bai ɗaga ba, ta sake kira har sau uku ya zama huɗu amma ba'a ɗaga ba. Sauri-sauri ta tafa saƙo ta tura masa. Jin cikinta ya fara mata ciwo tai kiran number Daddy. Shima harta tsinke bai ɗaga ba, ga Hajiya Basariyya ta fara ƙwala mata kira da faɗin ubammi take a bayin da taƙi fitowa. Kuka ta sake fashewa da shi tace gata nan zata fito. Number Daddy ta sake kira, dai-dai nan Hajiya Basariyya ke buga ƙofar bayin tana kiran sunanta da zaginta, ta tabbatar mata kuma in dai ta ƙirga goma bata buɗeba ALLAH sai na lahira ya fita jin daɗi....

_______★

       A lokacin da Huznah keta kiran Daddy a waya hankalinsu na nan a tashe da yanayin da Nazeera ke a ciki. Dan sun kammala cin abinci bayan gama yankan raguna Yazeed ya nufi sashen nasu. Kawai yaci karo da Nazeerar ta rarrafo cikin falo ga jini yanata zuba har takai numfashi take da ƙyar. Wani kalar faɗuwa gabansa yayi, babu shiri ya zaro waya a aljihu yay kiran Ammie. A rikice suka iso ita da Aunty Sakeena. Yaran Hajiya Yaya kam babu wacce ta motsa balle na Hajiya Basariyya. Hajiya Yayan ma tayi kamar ma bataji abinda Ammien ke faɗa ba.........✍️




*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣5️⃣1️⃣


______________



...........Tun Maanal bata hankaltu da irin kallon da Saheeba da Nuratu ke mata ba har ta fahimta. Sai dai duk sanda ta ɗago ta haɗa ido da su sai su ɗauke kai su basar. Mamaki ya kamata, zuciyarta ta fara wasiwasi, sai dai batace komai ba. Ashe ba ita kaɗai ba, hatta AA ya fahimta, dan duk motsin Maanal ɗin idanunsa na'a kanta shima. Wani irin ƙyau yau ɗin ta ƙara masa, ga cikin ya sata haske sosai jikinta ya ƙara wani ƙyau da zaunawa. Ga fatarta ko nesa da ita kake sai ka ga yanda take glowing. Wani sashin zuciyar AA na raya masa ƙyawun da Maanal ɗin ta ƙara ne ke ɗaukar hankalin su Saheeban suma, wani sashe kuma yaƙi aminta da hakan. Dan kallon yayi kama da irin na wanda ke jiran tsammani ne. Ana cikin haka Abah ya kira Oum, dan haka duk suka miƙe suka fito zuwa sashen Abah. Su Oum ne a gaba, har sunyi gab da shiga akai kiran Mamy a waya, sai ta ja gefe tana amsawa har duk suka shige. Cikin matsannacin mamaki AA ke kallon Mabera, shima kallon nasa yayi da murmushi a saman fuskarsa. Hakama Maanal kallon Mamaki take ma wannan mutumin mai kama dana ranar sak, sai dai wannan yafi wancan shekaru nesa ba kusa ba. Yayinda itama Oum ke mamaki da ganin Mabera yau a gidansu. Cikin kamun kanta da dattako takai zaune tana faɗin, “Gadanga yau babban baƙone haka damu a gidan?”.
      Abah yay murmushi da faɗin, “To kin dai ganshi nan nima har yanzu mamaki yaƙi sakina Fateema.”
       “Ai dole kam yaƙi sakinka, irin wannan bazata haka shekara aru-aru”. 
     Yanzu kam ƴar dariya Mabera yayi, idanunsa akan su Babban Yaya cike da makirci ya ce, “Ai ni bata ku ma nake ba, shin duk yaranmu ne waɗan nan? Kenan Darma!”.
         Abah ya ɗan murmusa yana bin duk yaran da kallo. “Dukansu yara na ne, ga Fadeel nan shine babba, ga iyalinsa nan guda biyu, sai yara biyu gasu nan. Sai Fawzan, wannan sune nashi iyalin shima, ALLAH bai kawo haihuwar ba munata dai addu'a. Sai Auta Ajwaad, ga matarsa nan shima. Fateema dai ka santa, akwai ɗayar maman tasu”___ya juya yana kallon Oum yace, “Ina Kamila”.
       “Tana waya ne, yanzu zata shigo”.
  Cewar Oum kai tsaye. Kafin Abah ya sake cewa komai Mamy ta shigo falon da sallama. Sam bata lura da baƙon ba sai da ta iso tsakkiyar falon idanunta dana Mabera suka shiga cikin tsakiyar na juna, cak taja ta tsaya kamar wadda akaima tsawa. Illahirin jinin jikinta ya fara tsinkewa. Wani shegen murmushi Mabera yay ya ɗauke kansa daga gareta, ƙasa-ƙasa yace ma Abah, “My Darma kana nufin wai aure ka ƙara?”.
        Maimakon Abah ya bashi amsa sai yay murmushi kawai. Mamy kam da ƙyar ta iya jawo ƙafafunta gudun karta yanke jiki ta faɗi ta ƙarasa a kujera ta zauna. AA da gaba ɗaya yake a tsarge yabi Mamy da ido, ya sake maida kallonsa kan Mabera dan sarai yaga irin kallon da sukai ma juna shi da Mamyn, yanzu ma gani yay yana kallon Mamy ne a kaikaice, sai AA ya sake jin zuciyarsa na harbawa da sauri-sauri...
      Zuciyar Mamy kam duka take, duka mai azabar ƙarfi da tashin hankali. So take ta danne ta riƙe yanayinta amma hakan na neman gagara, dan koda Mabera ya gaisheta da kansa bata iya ta amsa ba, dan haka kowa sai ya kalleta a karo na biyu. Yanda take yasa kowa fahimtar hankalinta ma ba'a kansu yake ba. Sai Oum ta ɗan taɓata da faɗin, “Mamy lafiya kuwa?”.
     Firgigit tayi, sai kuma ta kalla Oum, ta sake juyawa ta kalli Abah da Mabera, wani ɗan iskan murmushi ya sakar mata girarsa a sama. Sai Mamy taji wani abu mai matuƙar nauyi yazo ya tsaya mata a cikin maƙoshi, wani irin tsoratata da hargitsata murmushi Mabera ke yi. Dai-dai nan kiran Sille ya shigo mata a waya, sai ta zabura gaba ɗaya ta diririce. Diriricewar da kowa ya zuba mata ido harta miƙe zumbur. Oum da yanayin Mamyn duk ya tsoratasu suma ta miƙe tana ƙoƙarin riƙota da yin magana. Amma mi wata irin hankaɗawa Mamyn tai mata. Har sai da Abah ya tashi da mugun sauri ya tare Oum a jikinsa. Dole su Maanal duk sukai ƙasa da kawuna. Su AA dukansu ukun suka miƙe suma sukai kan Oum.
    Mamy kam idanunta sun gama rufewa, tsabar yanda take cikin ruɗani irin na bazata, bama tasan ta ɗaga wayar Sille ba balle ture Oum. Cikin matsanancin rufewa idanu dana zuciya ta fara magana a matuƙar tsawace, “Kai tsinannen matsiyaci miyasa kake kirana, bana faɗa maka kada ka sake kirana a waya ba, kada ka sake kuma zuwa min gidana ba Junaid! Kake ko ubam mi? Mi ka taka har kake jin kanada karfin gwiwar saka rayuwata gaba wai?!!”.
       A yanzu kam babu wanda bai miƙe a falon yana kallon Mamy ba, hatta su Maanal da su Babban Yaya da suka zaunar da Oum Abah na bata ruwa duk Mamyn suke kallo zuciyar kowa na bugawa da sauri-sauri.
       Wata shegiyar dariya Sille ya saki daga can, tare da faɗin, “Ubana dake a gabanki duk zai iya baki amsoshin tambayoyinki ai Madam Kamila matar Darma. Idan kuma daga wajena kike buƙatar amsar ai ina ɗakin barcinki sai kizo na baki dalla-dalla”.
        “Sashena?”.
   Cewar Mamy a matuƙar rikice tana juyawa ta kalla Mabera. Kafaɗa ya ɗage mata da taɓe baki irin na i don't care. Abah daya gama kaiwa wuya ya daka musu tsawa, cikin matsanancin ɓacin ran yanda Mamy ta hankaɗe masa Oum, da fahimtar lallai akwai sanayya a tsakanin Mamy da Maberan ya ce, “Mabera miya kawoka gidana?”.
      Babu ko ɗigon damuwa a fuskar Mabera ya ce, “Bani ya kamata ka tambaya ba Darma. Matarka ya kamata ka tambaya ai.” yay maganar yana nuna Mamy da idanunta sukai matsanancin kaɗewa. Ji take kamar zata yanke jiki ta faɗi. Brain ɗinta kam wani irin harmutsawa take yi tana jin tamkar zata haukace. Ganin Abah yana takowa inda take ta shiga jan jikinta baya. Oum data fahimci yau ran ƴan maza sun motsa da sauri ta miƙe ta tare gaban Abah, zai yi magana kawai ta riƙeshi. Sai kawai Mamy ta fita da gudu, dan zuciyarta gaya mata kawai take taje ta tattare abubuwanta tabar gidan.
       A wannan gaɓar su Yaya Fawzan duk sunyi sumar tsaye ne, musamman ma AA da yake jin tamkar zuciyarsa na kumbura a cikin ƙirjinsa. Gaba ɗaya haɗa 1+1 yake amma sun kasa bashi abinda ya dace. A ɓangaren matan ma su Maanal a firgice suke, dan tuni sun miƙe tsaye jikin kowa na rawa. Cikin ƙarfin hali Oum tace su fita. Ai kafin ma ta gama rufe baki duk sunyo waje, dan kowa hanyar fitar dama yake nema...
       Saheeba da Nuratu duk sashen su Saheeban suka nufa kowanne na ƙoƙarin kiran waya. Hakama Najma RK take kira a waya dan ta fahimci al'amarin babba ne. Maanal kam da bango kawai ta jingina tai shiru tana kallon Najma, fuskar AA take mata kai-kawo a zuciya. Abubuwa uku data san sun sani akan Mabera da Sille na tisa mata kansu a zuciyar...

       Saheeba na tsaka da gayama Nana abinda ke faruwa a gidansu cikinta yay wata irin ƙullewa. Da sauri ta duƙe a wajan tana mikama Nuratu wayar. Bata fahimci halin da take ciki ba ta amsa. Bayani ta cigaba da yima Nana. Sai yay dai-dai da fasa ƙarar Saheeba tana jan wani irin wahalallen mugun numfashi mai riƙe ƙirji. Da sauri Nuratu tayo kanta tana kiran sunanta. Saheeba da azaba ta isa ta ce, “Nuratu cikina, bani ruwa na sha na shiga uku. Da gudu Nuratu ta fita ya ɗibo mata ruwa ta kawo mata...

      Mamy kuwa gaba ɗaya bata gane komai, a hargitse ta afka sashenta. Kai tsaye tai upstairs, a can ɗin ma bata tsaya ko'ina ba sai bedroom ɗinta. Ƙofar ta danna da ƙarfi, juyowar da zata yi kawai tai ido huɗu da Sille na sille Haule a saman gadonta, su duka tsirara haihuwar tsoffinsu. Sai kawai Mamy ta fasa ƙara tare da tafiya luuuu kawai ta baje a ƙasa sumammiya. Ko'a kwalar rigar Sille. Hankalinsa kwance ya cigaba da abinda yake yi, Haule ko duk da ta tsorata bata da damar nunawa dan tsoronsa take ji matuƙa. Dama tun da ya sata tazo ɗakin ya nuna ga abinda yake so a gareta ta saka masa kuka, aiko ya bata maruka ya kuma sakata cire kaya.....

_________★

       Kiran Najma ya shigo wayar RK dai-dai lokacin da suke a gidan Baba Sardauna. Bashi kaɗai ba kusan kaf dangi suna nan dan haka suke taruwa a kowane bikin sallah. Dan ma babu ƴan Abuja a wannan karon sunce sai new year ta musulunci. Yanda falon na Baba Sardauna yake cike da su ƴaƴa da iyayensu su Abbu yasa ya bai tashi ba. Kuma bai kawo komai a ransa game da kiran ba sai tunanin barka da salla Najma zatai masa. Dama yanzu ake jajen rashin kiran kowa daga Abuja Uncle Mahmud ya kira Abah bai ɗaga ba.
     Abinda Najma ta fara sanar masa ya sashi miƙewa tsaye babu shiri. Har ya maimaita abinda Najma ɗin ta faɗa. Dama tunda ya miƙe kowa ya kallesa, abinda kuma ya sake maimaitawa yasa kowa ya zuba masa ido sosai. Batare daya tuna a inda yake ba yace ma Najma, “Kinga ki kwantar da hankalinki in sha ALLAHU yanzu zan bincika jirgi, idan ma ban samu ba zan taho a mota. Ki tabbatar dai kowane motsi na gidan kina sanar min”. Wayar ya katse batare da ya jira amsar ta ba. Yana ƙoƙarin fara tsallaka mutane ya fita Abbu ya kira sunansa a nutse.
     Tsayawa cak RK yayi, sai kuma ya kalla Abbu ɗin. Ganin yanda Baba Sardauna da Baba ma duk suka zuba masa ido sai ya kasa jurewa yay ƙasa da kansa. Abbu yace, “Miya faru? Ina zakaje?”.
       “Yasan babu batun wani ɓoye-ɓoye yanzun kam. Dan an kai irin gaɓar da yake so kuma yake fata tunda Mabera ya kai kansa. Kuma Mamy ta bayyana kanta da alaƙarta da Maberan kai tsaye. Yasan ainahin Mabera da abinda zai iya, tunda har yau kai tsaye yaje gidan Abah to ya shirya fito-na-fito ne tsakaninsa da Mamy dama Aban kansa. A hankali RK ya koma ya zauna yana kallon kowa na falon, ganin duk manyan ne babu yara a hankali ya furta,..........✍️



*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣5️⃣2️⃣


______________


.........“Abbu akwai matsala ne a Abuja”..
    A kusan tare kowa yace, “Matsala?”.
  Kai RK ya jinjina, “Tabbas matsala babba ma kuwa. Kuyi haƙuri banda isashen lokacin yi muku bayanin da zaku gane, dan jinkirinmu na nufin komai ma zai iya faruwa daga yanzu zuwa kowane lokaci. Dole ne na tafi Abuja yanzun nan”.
      “Dole ne dai mu tafi Abuja Rafeeq”. Cewar Uncle Mahmud hankali a tashe. Baba Sardauna daya gagara

175 / 213

Chapters