Author : Bilyn Abdull Category : Romance
haushin ya shafesa. Shi babban Yaya nasa abokan hamayyar na wajen aiki basu isa shiga cikin jiga-jigan azzaluman ba shiyyasa babu yanda suka iya da shi.
Kusan misalin ƙarfe biyun dare Mabera ne a ɗakin kusa da nasu Abah zaune yana karanta sakwannin da aka tura masa game da halin da ake ciki, ƙasa tako ina ta ɗauka talakawa da manyan dake jikin su Abah. Yanda masu turo sakwanin ke jinjina girman al'amarin haka Mabera ke jinjina wa. Ƙaramar waya ya ɗauka ya haɗa sim card a ciki ya saka battery ya lalubo layin wani abokinsa da shima keda hannu a cikin aikin. Bugu biyu aka ɗaga.
“Humm kai barci ma kake yi ni ina nan cikin jaje sauro na cinyeni lallai Kaugama”.
Cike da kasalar jiki wanda aka kira Kaugama ya ce, “Bazaka gane ba, tun ɗazun nake jiran kiranka amma shiru, bakaga saƙona bane”.
“Na gani, kasan sai da na koma Kaduna na tattaro komatsaina, dan ina gamawa da su gobe zuwa jibi zan bi ta Niger na wuce. Sai ku kuma ku ɗora da naku.”
“Oh wai kana akan bakanka kenan?”.
“Kaima kasan bana magana biyu Kaugama. A nawa tsarin kuma dukiyar Darma kawai nake hari sai rama abinda ɗansa yayma nawa ɗan, da. Shi na rama wanda yay min tuni. Itako Kamila dama zan ɗauketa ne ba'anan zan horata ba. Kaga manufarmu ta banbanta”.
“Haka ne. To yanzu ya ake ciki?”.
“Komai na tafiya anan normal, dan zuwa gobe zan zauna da su, zan kuma ajiye musu tabon da dole zasu bani kuɗaɗen dana buƙata da wuri. Na gama magana da Lawwali yanzu haka a shirye yake can bakin border yana jiran isata”.
“Okay shike nan, muma dai anan normal ne, dan basu gano bakin zaren ba har yanzu. Sunata dai buge-bugen tudun dafawa. Kasan babbar dabarar da mukai shine lalata camaras ɗin nan. Sai dai ka kula sosai, dan yanzu duk wani mai TAKUN SAƘA da su za'a hau bincika, shiyyasa kaga na bada ƙafa na bar ƙasar tun satin daya gabata.”
“Karka wani damu, dan ni babu wani mahaluki da zai ce inada alaƙa da Darma ta zahiri.”
“Hakan yayi na barka lafiya. Zamu cigaba da tura maka kowane motsi na yanayin da ake ciki”....
_____★
A lokacin da Mabera ke waccan wayar anan su Abah sun duƙufa ne kaima UBANGIJI kukansu, dan ruwan da aka kawo musu ya taimaka musu ƙwarai da gaske sai suka kama alwala da shi. Babu wanda yabi takan bread ɗin nan sai Nana da su Naufal da suke kukan yunwa. Cikin amincin ALLAH gabannin asuba suma su AA suka farka, sai masu ibadar suka ƙaru, dan suma duk da rashin ƙarfin jiki da suka tashi da shi basu biye ba suka fuskanci UBANGIJI, dan a wannan gaɓar shine kawai zai kuɓutar da su a halin da suke ciki. Ba kansu suke ji ba, matansu da yaransu ne damuwar, ga Saheeba da itama ta farka a gigice da zubar jini. Hankalinsu ya tashi matuƙa, Nana kuka Nuratu kuka. Da wannan tashin hankalin suka wayi gari. Dan tabbas in har Saheeba bata samu taimakon gaggawa ba komai zai iya faruwa da ita. Tsabar iskanci irin na Mabera koda kukan su Nana daya ishesu ya sashi leƙowa kallo ɗaya yay musu ya watsar zai koma da baya. A bazata yaji Abah ya furta,
“Na amince da dukkan sharaɗin ka. Amma kukai yarinyar nan asibiti ko ku nemo mai kula da ita”.
Ba Mabera kawai ba, hatta su Oum kallon mamaki suke ma Abah, shi mutum ne mai sauƙin kai a zahiri, amma Abah akwai kafiya da dagiya, shi kansa Mabera sanin wannan halin nasa da yayi ne ya sashi kafa waɗan nan sharuɗɗan da bai yaɓa tunanin Abah zai amince da su cikin sauƙi haka ba. Oum zatai magana Abah ya hanata. Shi ko Mabera dariya ya shiga tuntsurawa. Sai kuma ya ɗan tsagaita yana faɗin, “Anya My Darma ba wani abu kake shiryawa ba kuwa. Kai ne zaka amince haka cikin sauƙi. Kai ban yarda da kai ba wlhy”.
Kallonsa Abah yay cikin ido, sai kuma yayi murmushi mai ciwo. “Junaid ke nan, kai kasanni ai, kuma kasan abinda zan iya tun kafin kazo nan damu. Amma ka sani zan iya sadaukarwa saboda zuri'ata, ciki harda RAYUWATA...”
A matuƙar gigice kowa yake kallon Abah. Mabera kam dariya ya sake sanyawa, sai kuma ya taɓe baki da faɗin, “Wannan kai ya shafa, yarana zasu zo su fita da ita, kuma sai ku karya ku fito domin fara zartar da shari'a”.
Babu wanda ya kulashi balle tanka masa. Yana barin wajen baifi da mintuna biyar ba wasu ƙartai suka zo zasu ɗauki Saheeba. Babban Yaya ya motsa da niyyar yin magana duk da bashi da wani ƙarfi Abah ya riƙeshi ya hana. Dole ya haƙura suka ɗauketa suka fice. Nana zata bisu sukai mata tsawa, hakama Anum. Oum dake hawaye ta ce, “Gadanga miyasa zaka amince musu? Idan zaka iya basu dukiya kenan zaka iya sallama musu su cutar da Ajwaad kamar yanda suka faɗa?”.
Shiru Abah yay mata kamar bai ji ba. Su Babban Yaya da basu fahimci zancen ba sukace, “Oum mike faruwa? Wane irin sharaɗi ya kafama Abah akan Ajwaad?”.
Kuka Oum ta sake fashewa da shi, ta shiga zayyane musu komai da Mabera ya faɗa a jiya da dare suna barci. Cikin zafin rai Yaya Fawzan ya ce, “Miyasa zaka amince masa Abah?”.
“Hakan da yay shine dai-dai Yaya Fawzan. Ko kuna son ita Saheeban ta rasa rayuwarta. A yanzu rayuwarta ce mai muhimmanci fiye da komai.”
“Amma kasan wannan ALADEN mutumin zai iya aikata komai daya faɗa ko Ajwaad”. Cewar babban Yaya a fusace shima.
Murmushi AA yayi idonsa akan Maanal dake barci, sai kuma ya lumshesu ya buɗe akan Babban Yaya da Yaya Fawzan. Ya maida kan Abah da kansa ke ƙasa. “Yaya na fiku sanin mutumin nan ƙwarai da gaske. Na san kuma zai iya yin fiye da abinda yama faɗa. Karku damu ALLAH na tare damu ai.”
Kafin wani a cikinsu ya sake cewa wani abu Sille da yaransu suka zo fita da su. Har yanzu jikin su AA Baida wani ƙarfi, dan sai da ma aka kamasu. Da alama allurar zatai kwanaki a jikinsu kafin ta sake su. Gaba ɗayansu tsaye sukai suna kallon Mamy daketa aikin girka abinci a waje cikin rana kuma ƙatuwar tukunya, dama tun jiya Oum ke tambayar ina take Abah yay mata shiru. Duk kuma inda ta motsa yaran Mabera na biye da ita da bindigu. Duk tayi wani irin wujiga-wujiga dare ɗaya kacal, kai daga gani kasan ubanta take ci a hannun su Sille. Basu AA ba hatta Oum zuciyarta tafasa take da halin da Mamy ke ciki, haka aka kaisu ƙasan watsa bishiya da Mabera ke zaune a kujera kamar wani sarki ana faman danna masa ƙafafu. Yasa laptop a gaba yana kallon Film sai dariya yake yi kamar mahaukaci. Ga kayan ciye-ciye an baje masa. Gefensa Sille ne zaune shima yana haɗa bindiga yana zuƙar sigari. Komai basu ce musu ba har sai da Mamy ta gama uban girkin nan ta zuzzubama yaransu. Tsabar yanda ta jigata layi take kamar zata faɗi, haka suka rakota wajen inuwar. Amma tsabar mugunta sai Sille cewa yay ta koma rana tai kneeling. Ai wani irin zaburowa AA yayi sai dai bashi da ƙarfin tashi, Abah ma ya riƙeshi yana girgiza masa kai.
Sille dake kallon AA yay dariya da faɗin, “Kai fa na lura ɗaukar kanka kake wani tsagera ne. Karka manta kai ƙanina ne na uku, ko shi wannan Fadeel ɗin dole yabini balle kai haihuwar taliya. Dama ka shanye fushinka dan ba amfani zai maka ba anan, ko an gaya maka a banza muka saka kuɗi muka sayi allurar da mukai muku hahhhaaha”.
Lips kawai AA ya cije, tsabar yanda zuciyarsa ke hasala sai ga hawaye sun cika masa ido. Mabera da duk ke saurarensu ya kashe laptop ɗin yana gyara zama da kallon AA, kamar ba shi ba a dake ya ce, “Ajwaad ka daina damun kanka da yanayin da kake ganin wannan matar, dan wlhy a yanzu idan ka gama jin wacece ita sai kafin sauran ƴan uwanka tsanarta. Ban sani ba ko mahaifinku ya taɓa faɗa muku alaƙata da shi. In ma baiyi hakan ba ni yanzu zan faɗa muku dan zakufi fahimtar abinda nake son ku fahimta a wannan shari'ar.”
“Sunana Junaid Abubakar Mabera. A......”
Maganar ta maƙale a maƙoshinsa sakamakon isowar yaronsa a guje har yana faɗuwa. A tare Mabera da Sille suka miƙe, Sille ya daka masa tsawa.
“Are you Mad?!!”.
“Sir akwai matsala, an YANKA TA TASHI, an kama su Bakure da matar nan mai zubar da jini, yanzu haka shi ya gudu amma sun bishi yace muyi takamm...”
Wani murmushi Abah ya saki, yayinda Mabera ya rikice, a tsawace ya ce, “A saka kowa a mota yanzun nan...........”✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣5️⃣8️⃣
______________
.........Gaba ɗaya wajen ya rikice da kai-kawon yaran mabera. Dan danan suka shiga fito da mashina da motoci dake lulluɓe da yayin ciyawa. Harda nasu Abah guda biyu da akazo da su jiya har sun ɓoyesu shegun. Mabera da Sille sai faman kai-kawo sukeyi suma hankalinsu a masifar tashe. An gama fiddo motoci da mashina zasu fara saka su Abah kawai suka fara jiyo ƙarar jirage masu saukar angulu na tunkaro jejin. Koda suka fara dube-dube sai suka fahimci ai takowane bango ne zobe ake shirin yi musu. Mabera ya wani cije baki yana mai yarfar da hannayensa irin na ta ƙwaɓe ɗin nan. Babban yaron su ya kalli Sille da gaba ɗaya ma ya gagara cewa wani abu shi kam.
“Boss mutanen nan sun riga sun cimmana fa, mafita ɗaya ce damu a yanzu da zamu iya tsira a hannunsu”.
Mabera da ya kallesa da sauri yace, “Wace irin mafita ce? Kasan da mafitar amma ka zuba mana ido tun ɗazun muke neman rikita kammu!!”.
“I'm sorry Sir! Nima yanzu dabara yazo min, inaga mu koma da mutanen nan cikin gida kawai. Wannan shine plan a ”.
Wannan fa shine mai neman nutsewa a ruwa ko maciji aka miƙa masa zai kama a matsayin igiya domin ceton kai. Babu wanda ya tambayi minene plan b suka tattara kowa suka maida cikin gidan, suma duk suka shige suka zagayesu da bindigun. Kawai sai Mamy ta hau dariya kamar zararriya. Cikin takaici Sille yasa ƙafa ya kwasheta sai gata wanwar a ƙasa, ya ja kunamar bindigarsa kawai ya danƙara mata harbi a kan ƙafa. Zai ƙara wani Mabera ya hana...
Wani irin gigitaccen ihu Mamy ta saka, hakama su AA a tare sukai shirin zabura yaran su Sille suka riƙesu. Cikin matsanancin zafin rai Sille yace, “Baa! Ka barni na kashe azzalumar na huta. Da bataje ta haifeni a titi ta yarda a bola ba da ban zama haka ba. Wlhy in har yau zan mutu a jejin nan kema anan zaki mutu wulaƙantacciyar baiwa. Ya sake ƙoƙarin gwada harbinta...
“Son barta barta, ai babu abinda ya rage ma wannan sai jiran mutuwa. Amma bazata mutun ba sai waɗanda take taƙamar da su a yanzu sun san ita ɗin wacece. Ku tattara waɗan nan mutanen da basu da alaƙa da wannan case ɗin ku maida min su gefe.”
Hakan kuwa akayi, asalin waɗanda akai kiddinapping tuni aka tattare su aka maida can gefe. Iya Abah da zuri'arsa ne kawai a wajen. Gaba ɗaya Mamy ta jiƙe sharaf da zufa, Oum kam sai share hawaye take yi, su AA idanu sun gama kaɗewa jazur tamkar an watsa musu wuta.
Mabera dake kallonsu ya ce, “Koda ace zan mutu a yau bazanyi baƙin ciki ba, dan ko yanzu na nunama Kamila tabbacin alƙawuran dana ɗauka mata na zan dawo na cika su. Na dawo mata da AJIYA A DUHUN da tayi daya ruguzata a gaɓar da take ganin ta gama cin nasara. So hakan kuma yamun daɗi dan koba komai za'ayi komai a gaban shari'ar da take ganin itace ƙarfinta a yanzu, al'amarin kunga ai zaifi romon daɗi ma. Zan dawo da baya domin wanda basu san ni wanene ba anan su sani. Musamman alaƙata da amini na kuma ɗan uwa. Dan ban taɓa amini ba a rayuwata sai Darma, bayan shi kuma ban ƙara yi ba dan bamma sake yarda da kowa ba hatta kaina. Sai abota kawai”
“Da farko dai sunana Junaid Abubakar Mabera. An haifeni a cikin garin Kano, anan na tashi, anan nai karatun primary na, nayi Secondary school boarding a garin Bichi local government. Anan ne na haɗu da Darma. Dan muna shekarar ƙarshe, wata shidan ƙarshe ma da muke shirye-shiryen fara ssce aka kawoshi shima zai zana jarabawa damu. Ni ne shugaban ɗalibai na wannan shekarar dan haka vice principal ya damƙa Darma a hannuna akan na kula da shi saboda ta hannunsa aka kawo Darma. Na amsa da hannu biyu, domin Darma dai ƙyaƙyƙyawane, a kallo ɗaya zaka fahimci ɗan masu kuɗi ne. A lokacin bawai dan kwaɗayin shi ɗan masu kuɗin bane yasa naji ina sonshi, nima daga gidan kuɗin na fito, kawai dai ina ganin abotarmu zata kasance ta ƙwarya tabi ƙwarya ce. A cikin sati guda sabo da shaƙuwa ta shiga tsakanina da Darma. Har ina kiransa My Darma shi kuma yace My Mabera. A yanda mukai gaggawar ƙullewa kowa a makarantar sai ya ɗauka dama can muna da alaƙar sanayyar juna ko zumunci ma mai ƙarfi na jini. Bamu taɓa musama kowa ba muka bar abin a haka. Ba wani isasshen lokaci ne da mu ba muka fara exam. Cikin ikon ALLAH har muka kammala. Tun zuwan Darma bashi da labari sai na ƙanwarsa Fateema. Duk motsinsa zai ce Zarah kaza, da yanzu Zarah tai kaza. Tun sunan Fateema na shiga kunnena da labarinta muyi dariya kawai harya fara tasiri a cikin zuciyarta, dan nasan dai bai wuce ƙanwarsa ba. Bawai ina nufin tasiri na soyayya ba, a'a nima dai ina mata so irin na ƙanwa.
Tare da Darma muka tafi gida, duk da anzo ɗaukata nima amma sai na shiga motar gidansu drivern gidanmu ya bimu a baya. A'a mizai faru, cikin ikon ALLAH ashe anguwarmu ɗaya, layi ne kawai ba ɗaya ba. Hakan ya mana daɗi sosai, mun kumayi farin ciki. Har gida na shiga na gaida su Baba da Umma, na tambayi Fateema akace tana makaranta. Da yake nima ina zumuɗin son tafiya gida ne ban daɗeba na fita drivern gidanmu daya biyo mu a baya ya ɗaukeni sai gida. Dawowarmu gida ta sake ƙulle abotarmu, a gidansu Darma kowa ya sanni, hakama a gidanmu kowa ya san Darma. Nakan je gidansu na yini wani lokacin ma har kwana. Yakan je gidanmu shima sai dai bai taɓa kwana ba. Nine auta a gidan mu, dan haka nake matuƙar son ƙannen Darma musamman Fateema. Haka ni da shi zamuyita goya ƴan biyu, hatta Mahmud ma mune komai nasa dan lokacin shima yana Secondary. Jarabawar mu ta fito, muka kuma ce makaranta ɗaya muke so dan haka babana ya amshi takarduna mu kasancewar yana da alaƙa da harkar ilimi ya nemar mana makarantar tare. Bamu sha wahalar komai ba kuwa komai ya daidaita, da farko dai zuwa muke mu dawo, daga baya muka koma hotel. Kowa ɗauka yake munada alaƙa ta jini, duk da bama kamanni sam. Sannan halayyar mu ta banbanta sosai. Babu ruwan Darma da mata, hasalima baya sakar musu fuska sam, niko gaskiya ina son mata, ina huɗɗa da su sai dai ban taɓa taɓa ƴar kowa ba. Amma ni kaɗai nasan hakan, dan yanda nake mu'amula da su hatta shi Darma bai yarda bana bin mata ba. Duk da nasha yi masa rantsuwa da ALLAH idan yana mun nasiha ko faɗa amma sai yace bai yarda ba. Tun ma ina damuwa da masa bayani da son ya fahimta harna haƙura na ƙyalesa muka cigaba da karatunmu, ban kuma daina shiga cikin mata ba ayi shewa da arerewa. Sai dai a duk lokacin daya zauna yana tuhumata abin na ƙona min zuciya, dan ina ganin kamar yana son ƙasƙantar da ni ne ko nuna min ya fini sanin ALLAH da tsoronsa. Sai kuma yanda matan kullum suke roƙon na haɗasu da Darma, gashi fa ina a cikinsu ina ƙyautata musu amma su hankalinsu nakan Aliyu da ko kallon su bayayi. Wata ma a cikinsu bai taɓa magana da ita ba. Da naga abin nasu fa na gaske ne sai kawai na fara business da su. Idan kikace kina son Darma na dinga tatsarki kudaɗe kenan akan zan daidaitaku. Haka na dinga haɗa kuɗin matan nan ina ci tun abin ina yinsa a raha har ya fara tasiri da mun daɗi a zuciyata, kun san dai kuɗi da shiga rai. Yanda nake damun Aliyu akan ya dinga kulasu ko kaɗan ne sai muka fara samun saɓani da shi, ya fara janye jikinsa daga gareni, bana son rabuwa da shi dan tarayyarmu na kankaro min mutunci saboda nutsuwarsa, gashi da ƙoƙari akan karatu, sai kawai na daina masa maganar matan na koma jan