Author : Bilyn Abdull Category : Romance
Shi dai sau ɗaya ya amsa kuma daga kallo ɗaya bai sake musu na biyu ba. Sun shiga har ɗakin Hajiya Yaya, Amrah na zaune na bata abinci, ta gaishe da AA cikin girmamawa da tambayarsa ina Maanal. A mamakin su Ammie sai gashi yama Amrah guntun murmushi, yace mata Maanal na lafiya amma suna fushi da ita tunda bata sake zuwa musu ba, ga biki ma anyi bataje ba. Amrah na murmushi ta ce, “Ai min afuwa Yaya AA, ina yin exam ne shiyyasa, amma na gama in sha ALLAHU zan zo muku hutu ma”.
Cike da kulawa AA yace mata, “Muna maraba da zuwanki”. Sai kuma ya shiga gaida Hajiya Yaya. Ƙwarai da gaske yaron ya cika mata ido ya kuma mata kwarjini, sai taga yama fi yanda yaran ke faɗa, wannan fa shine ikon ALLAH yafi gaban wasa. Ta hana Maanal auren ɗanta saboda tana ganin yafi ƙarfinta sai gashi taje ta auri wanda ya fishi komai. Kaga yaro Masha ALLAH santalele da shi, daga gani kuma kasan dukiya ta zauna masa...
Ammie ce tai mata bayanin komai akan AA da abinda suka tattauna. Ta gamsu ƙwarai da gaske, cikin sanyi tace, “Ajwaad karka damu, zamu baka goyon baya ɗari bisa ɗari. Kada ka damu akan ni na haifi Yazeed kaji”.
Murmushi AA ya mata. Zuwa can kuma ya nisa, yana mai jinjina kai ya ce, “Idan har zancen yaran nan ko nace hasashensu ya zama dai-dai saka Yazeed akai aikin nan. Amma abinda ya ruɗani anan matarsa tayi ƙanƙantar yin irin wannan tunanin gaskiya, dan wannan aikin daga gani kasan na mai hankali ne. Idan har itace ɗin ta sashi yayi to lallai itama sanyata akayi kuwa. Wannan kuma shine dalilin da yasa aka juyar masa da hankali gaba ɗaya”.
Shima dai Daddy irin tunanin AA yake yi, sai dai kamar shi kai tsaye bazai ce ga wanda yake hasashe ba, dan abin zai iya zama kowa ma. Amma sai furicin Hajiya Yaya ya kashe tunanin nasu su duka. Dan kai tsaye ta ce, “Sabuwa nake zargi nikam harga ALLAH. Wannan shine dalilinta na sanyani a gaba Yazeed ya auri ƴarta”. Hawaye suka zubo mata
Ammie ta ce, “Kai tsaye ba ace haka ba Yaya. Dan zai iya zama kowa ma. Musamman itama yarinyar bamu gama sanin wacece ba ai.....”
“Ammien yara kamar yanda Ajwaad ya faɗa ne yarinyar tayi ƙanƙantar wannan tunanin, sannan nasan abinda Nazeerah zata iya nasan wanda Sabuwa zata iya. Amma ban musa miki ba, baka shaidar ɗan yau musamman yanda samari kan saka yaranmu aikata mana abubuwa da yawan gaske sai daga baya su dawo suna dana sani idan sun shiga tarkonsu. Dan ba kowane namiji bane ke zuwa ga yarinya dan asalin soyayyarta, wani abinda ya hango zai ƙaru da shi yake biyowa kawai. Daya samu kuma shike nan. Walau a wajen, walau a gidan auren. Amma lallai nafi ɗora alamar tambayata akan Sabuwa, dan hatsabibiyar kanta ce, duk da take ƴar uwata uwa ɗaya uban ɗaya nasan zata iya fiye da abinda yafi hakan”.
Shiru ɗakin yay na tsawon lokaci, Daddy dai nata sake auna batun sabuwar a zuciya. Ammie kuma wani tunani take daban. Hakama AA yana sake faɗaɗa maganganunsu ne a zuciyarsa. Sai zuwa can ya ce,..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣2️⃣8️⃣
______________
.........“To in dai haka ne mizai hana mu jefa tsuntsu ɗaya da dutse biyu a wannan gaɓar”.
Duk kallonsa sukai cikin bashi hankalinsu. Ya jinjina musu kansa. “Tunda har Hajiya taga Yazeed ne ya aikata, kuma mun riga duk mun yarda wannan ba aikinsa bane, to lallai wanda ya sakashin dole zaiyi bi baya idan ya gama tantance takardun da abinda zai zame masa dukiya. Na sayarwa irin su gold da sauransu zasu siyu, amma documents dole ya nema mafitar sanya hannu. Idan muka shiga tunanin koma wanene shirinsa na gaba kowama a gidan nan zai iya zame masa abin hari. In ma yay garkuwa da wani a cikinku ko yara ta hanyar turarasa su, su saka masa hannu a takardun. Ko kuma ya dinga saceku ɗaya bayan ɗaya kuna saka masa, ko kuma ya shirya irin matakin da suka ɗauka akan Yazeed wato gusar muku da tunani ta hanyar asiri, ko kuma yazo har cikin gidan nan ya muku barazana ta yanda ya shirya koda kuwa kashe wani ne a cikinku. A yanda nake hange kai tsaye bazai yi kowane irin yunkuri ba a yau ko gobe daga nan ma har kwanaki huɗu zuwa biyar, amma bazai bari ku sakankance ba kuyi irin wannan tunanin na cewar zai jima kafin ya dawo zai dawo ɗin. Tunda ALLAH ya bamu dama anga Yazeed, kuma yara sun ɓunta zargin matarsa a gabanta mizai hakan ƴan sanda suyi kamar sun kama su, sai a kaisu mabanbanta waje a ɓoye su. Musamman ma Yazeed dan a dage akansa da addu'a har ALLAH ya maidashi hayyacinsa. Hakan zai raba hankalin koma waye biyu akan ku yanzu, har ALLAH yasa mu cimma manufa mukuma, dan na tabbatar in har ALLAH ya warware abinda ke tare da Yazeed koma waye zamu sanshi kai tsaye batare da shan wahala da kai-kawon ƴan sandan nan ba harma mutanen gari su farga da halin da ake ciki”.
Ɗari bisa ɗari Daddy da Hajiya Yaya da Ammie sun gamsu da bayanin AA. A take kuma Daddy ya shiga sanya masa albarka, sannan ya ɗauka waya ya kira dpo sukai magana da AA ɗin. Ai mintuna Ashirin ba'a cika ba sai ga jami'an tsaro. Lokacin su Sabuwa sun fito zasu wuce gida jin babu wani motsi daga mutanen gidan. Musamman ma mijinta, dan ita dai kam da yake ba sanin gaskiyar lamarin tai ba damuwarta kawai shine zasu tashi a tutar babu ne.
Duk fitowa akai waje har Hajiya Yaya da aka kamo, yaran Basariyya ma sun iso daga Zaria babu jimawa. Sabuwa da Hajiya Yaya sai ƴar kallon kallo. Mijinta kam da yake ɗan bariki ne sai yaje yana gaida Hajiya Yayan. Dakewa tai ta amsa itama ta nuna masa ta fisa iya barikin. Sannan ta kalla ƴan sandan dake jeho mata tambaya tana amsa musu. Yayinda AA yay mutuwar tsaye yana bin mijin Sabuwa da kallo. Zuciyarsa har wani motsawa take a ƙirjinsa dan mamaki. Dan fuskar jiya ce ke dawo masa a wannan fuskar tsaff, sai dai ita wannan akwai shekaru a tare da ita. Kai shi ko ya shiga ruɗani a karo na uku, ganin guy ɗin can a gidan Hajiya Turai ya hasaso ya san fuskar, amma ba a Abuja bane a kano ne, amma ya rasa a ina? kuma ya akai yasan fuskar? Jiya sai ga guy ɗin a ƙofar gidansu, ya kwana ya tashi da tunanin miya kawosa nan ɗin dan ma al'amarin su Ammie ya danne masa nashi, yau kuma sai ga mai irin fuskar anan kaduna. To miye matsayinsa anan ɗin?. Rashin mai bashi amsa da bayanin da ƴan sanda sukema Hajiya Yaya ya katse masa tunani, sai ya koma yima Baban Nazeera kallon ƙasan ido da nazartar dukkanin motsinsa......
Ƴan sanda kam koro ma Hajiya Yaya bayani sukai akan samunta da akai a ɗaure shin waye ya ɗaure ta? Kai tsaye ta ce, “Yazeed ne”.
A firgice kowa ya kalla Yazeed har mijin Sabuwa da shi kanshi Yazeed ɗin da ke kallon Hajiya Yaya shi kuma. Hajiya Basariyya da duk ta firgice tai wujiga-wujiga tace, “Yazeed kuma? mun shiga uku, yanzu ka rasa suwa zaka daiɗaita sai mu. Dama haka kake ko yanzu ne ka koya halin zama da wannan matar taka?”.
Tsawa yayanta yay mata, dole tai shiru, amma wani irin hararar Yazeed takeyi, tana jin kamar taje ta shaƙuresa sai ya fito mata da arziƙinta. Dpo ne ya katse tunanin kowa da faɗin, “Kenan shine ya ɗiba abubuwa a ɗakinki? Dan kin ganshi shiyyasa ya ɗaureki har kika suma”.
“Kwarai kuwa ko shakka babu shine. Kuma shine ya ɗebo na sashen Daddyn su dama na sauran duk ɓangarorin, dan na ganshi da akwatin Daddynsu......” tsaff ta zayyane duk yanda akayi wanda ta gani, sannan ta ɗora da faɗin, “Bana raba ɗayan biyu matarsace ta saka shi yin hakan, dan yanzu yana a ƙarƙashin control ɗin ta ne sai abinda tace yayi yake yi. Koda wuta tace ya shiga na tabbatar muku zaije ya shiga ne. Idan baku yarda ba ku gwada kuma”.
Da sauri kofur Hamza yace, “Hajiya ni ganau ne ba jiyau ba wlhy,
Dan jiya da nai kiransu abinda kika faɗa hakan ce ta faru. Fitowa ma ya biyo mu waje sai da tayi magana sannan”.
“To Alhmdllh ma tunda kun gani da idanunku. Sai kuje da su shi da ita su fito mana da kayayyakinmu dan ni dai bazan yafe ba.....”
“Balle ni da ban haɗa komai dasu ba, daga matar uban ina dalili ina ɗan mafari zasu min irin wannan takaitawar duk wahalata ta tsawon rayuwa. Haba mina muku da zafi haka dan ALLAH Yazeed”. Sai kuka sharr. Hajiya Basariyya ce mai maganar a harzuƙe tana rusar kuka. Dan magana ta ALLAH tana son dukiyarta, itace taƙamarta da duk wani tunƙawonta fa. Rana tsaka sai ace an salwantar yo kai taci, ko dusa ce a cikin kan nata da zata hakura. Kawai ayi duk ma uwar da za'ai a baje mata hajarta a rabu lafiya, idan ba haka ba wlhy kare jini biri jini bazata ɗauki asara ba tunda uwarsa ma yace bazata yafe ba.
To da yake dai da zuciyarta take ƙullawa da kwancewar babu wanda yasan tanayi ma. Sai Sabuwa datai tsalle ta dire akan wlhy bazata yarda a tafi mata da yarinya da tsohon ciki ba. Sai dai aima duk abinda za'ayi ta shirya”.
Kai tsaye ɗan sanda yace, “To bismillah sai kiyi ɗin. Kai Kofur ku tattara min su biyun muje mota yanzu. Duk wanda yay yunƙurin shiga gaban ku ni na baku dama ku harbeshi a ko ina kuka samu”.
Tab ɗin jan babbar magana. Yo ALLAH na tuba bindiga kota film ce ai razani gareta balle ta zahiri. Dan haka ai kowa tashi ta fishesa kawai. Kuka sosai Sabuwa ta koma yi da kururuwa tana ma mijinta magana wai ya hana. Maimakon ya hana ɗin sai ya riƙeta yana lallashi wai tayi haƙuri zasu bisu station ɗin su amsosu. Babu wanda ya kulasu a tsakanin su Daddy, haka aka wuce da Yazeed yana kallon Ammie da Daddy yana hawaye. Dan Hajiya Yaya an riga an kaɗar masa hankali a kanta. Akan komai baya tunawa da ita ma sam. Yaran kam hankalinsu duk ya tashi harna ɗakin Hajiya Basariyya, dan harga ALLAH suna matuƙar so da ƙaunar Yazeed har cikin ransu. Ya musu rainon ne irin na uwa ɗaya uba ɗaya a gidan. Bai taɓa zama nuna banbancin ƴan ɗakinsu su duka duk wanda yay ba daidai ba gyara masa zama yake yi. Haka idan kai abin arziƙi ma zai ƙyautata maka.
Waleed da suka dawo makaranta Daddy yaje ya riƙe yana kuka ya ce, “Daddy dan ALLAH ka hana, karka bari a tafi mana da yayanmu. Wlhy Yayanmu baya cutar da kowa. Muma ko laifi mukai masa sai ya fara mana nasiha idan bamu bari bane sai ya dake mu.”
Tausayin yaron ya kama Daddy, sai ya kamashi ya rungume, shima Hameed kuka yake, haka sauran yaran ma duk hankalinsu a tashe yake. AA kansa sai yaji tausayinsu, dan kuwa ya fahimci Yazeed ya gina ƙyaƙyƙyawar alaƙa a gidan tsakaninsa da yaran. In sha ALLAHU zai taimakesu kodan Yazeed ɗin ya fita a halin da yake ciki.
Bayan an wuce da su Yazeed kowa ya nufi sashensa, AA da Daddy suka fita massallaci dan lokacin sallah yayi. Mijin Sabuwa yabi AA da kallo a kaikaice. A ƙasan ransa yana mamakin abinda ya kawo ɗan gidan Darma a wannan maganar. Wani gefe kuma na zuciyarsa na murna da ganin wata dama ce fa tazo musa cikin sauƙi. Dan tabbas bayan Daddy Darma ne abin harinsa. Yana da ajiyayyen wasa a tsakaninsu shima na tsawon shekaru. Gida yay niyyar su tafi dan yana son zuwa yay lissafi akan wannan kama Yazeed da ƴarsa ɗin saboda a farko baya cikin nashi lissafin, baima kawo cewar wani yaga Yazeed ɗin ba. Kai koda an ganshi a tunaninsa kawai zasu tsaya bincikene anan iya cikin gidan, shi kuma yay amfani da shagaltar tasu ya ƙarasa cimma burinsa. Amma sai ya ga anan lissafin ba haka bane.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣2️⃣9️⃣
______________
.......A tare sukai salla da su AA, koda suka fito sai gashi yazo yana musu sallama harda miƙa hannu. Daddy kansa ya ɗauke kawai, AA kam da yake ɗan ƙunar baƙin wake ne amsa yay harda bashi haɗin kan yima juna kallon ido cikin ido. Ya sakar masa wani ɗan iskan murmushi daya tsayama Baban Nazeera a ƙahon zuciya. Kuma har cikin tsakiyar ransa yaji kaifi da kwarinin idanun yaro, dan kai tsaye Aliyu Darma ne ya dawo masa sak. shi a karan kansa bai san sanda zuciyarsa ta suɓuce ya ambata NAMIJI DUNIYA ba.
AA ya bishi da kallo harya ɓace, kafin suka shige cikin gida batare da yacema Daddy komai ba a kansa, duk da yana son yin tambayar.
Koda suka shigo ɗin ma dai dining Ammien ta saka suka wuce, sai ga Waleed ya kawo ma AA waya yana faɗin, “Yaya Auntynmu nata kiranka tun ɗazun da kuka fita salla, na tafi da ita na baka ban ganku ba.”
Cikin waro idanu waje AA ya ce, “Subahanallahi Autan Ammie ka ɓallo ruwa, inji dai baka ɗaga ba taji muryarka?”.
Dariya Daddy ya sanya batare da yay niyya ba, hakama Ammie dake zuba musu abinci sai da ta murmusa. Sai kuma suka haɗa ido da AA ɗin. Fuska ya shagwaɓe mata kamar zai saki kuka. Ammie tace, “Ni yanzu ina ruwana daka tsareni da ido Ajwaad, ai kunfi kusa kai da ita”.
Fuska AA ya sake marairaicewa ya ce, “Ammie wlhy bazaki gane ba, bafa tasan nan na taho ba, duk zatonta ina office ne. Daddy kawai ka shirya kai min rakkiya Abuja in ba hakaba yau ƴar Abah da Oum sai ta sauke Tinubu a mulkin ƙasar nan, dama gashi a ɗofane yake”.
Ammie kanta yanzu kam ta kasa daurewa, sai da tai dariya sosai. Daddy ya ce, “Haba Son yada karaya haka da wuri. Sai kace ba namiji ba”.
Ƙasa-ƙasa AA yace, “ALLAH na tuba Daddy Mazantaka ai a gaban Maza ake nunata kawai, ita kuma Lillyn Baban Yaya da Yaya Fawzan sarauniya ce. Ko bata buɗe baki ba idanu kawai sun isa isar da hukuncinta ga mai laifi”.
Waleed dake dariya shima ya ce, “Lah Yaya wai tsoron Auntyn namu kake ji, koda yake jarababbiya ce, muma data koma Abuja ba gashi munyi ƙiba ba. Ai ban ɗaga ba, baka bari na ƙarasa gaya maka bane ba fa”.
Hararsa AA yayi yana sauke ajiyar zuciya, tare da kai masa rankwashi a ka. Waleed ya gudu yana dariya. Ammie dai data fiske yanzu murmushi kawai tayi ta tura musu abinci shi da Daddy, sai Daddy ne dai har yanzu yana tashi dariyar ciki-ciki. Sai shima AA ɗin ya murmusa a karo na farko. Sannan ya ɗauka wayar ya tafama Maanal gajeren saƙo ya ajiye. Sosai yaci abincin Ammie dan abinda yake so ta girka masa, bai kuma cutama kansa ba yaci abinsa saboda yayi missing ɗin girkinta sosai. Dan shi kam a duniya idan ana iyaye uku to shi ukune da shi, yana jinsu a ransa matan nan uku matuƙa. Oum, Mamy, Ammie.
Bayan sun kammala cin abincin ne suna a zaune a dining ɗin basu tashi ba AA ya ce, “Daddy mutumin nan miye matsayinsa a wajenka bayan surukuta? Shekararka nawa da saninsa? Minene sana'arsa ko aikinsa? Asalinsa ɗan ina ne”.
Shiru Daddy yayi na ɗan lokaci, sai kuma a hankali ya sauke numfashi da gyara zama yana fuskantar AA da ƙyau......
________★
A Abuja barci sosai Maanal tasha ita da Oum, har ma abin ya bata mamaki dan yanzu bata barcin safe dana rana sai na yamma. Amma yau gashi sai kiran sallar azhar ne ya tasheta. Wayarta ta fara ɗauka, a mamakinta babu miss call ɗin AA ko ɗaya, sai saƙonsa guda biyu kawai. Baki ta tura gaba dan taji haushi, ta ajiye wayar ta tashi ta shiga bayi tayo alwala tazo sukai salla ita da Oum. Tana idarwa ta sake ɗaukar wayar, sai faman tura baki take. Oum na lure da ita, tai murmushi kawai ta miƙe ta bar mata ɗakin, dan wannan rikicin na Auta da Baby ba shigarsa take ba sam. Idan ma ka shiga sai ka matse dan basa cika awa