AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   196 / 213

585K to 588K   out of 636.6K words

da kansa, suka saya masa waya dan suna so su dinga jin kowane motsin Babu. Sun kuma sayi kayan daɗi da ruwa mai yawa suka ajiyema Babu, tare da samun mai kula musu da shi zasu dinga biyansa. Da yamma sai ga AA da kansa yazo ɗaukarsu. Maanal tai murmushi kawai, dan tasan a matse yake su dawo haka yake damunta a kwana biyun nan yau har tsokanarsa tayi tace ya barsu sai jibi mana ya balbaleta da masifa, ta tabbatar shine dalilin kamo hanya ya taho ɗaukarsu da kanshi.
     Shatara ta arziƙi aka haɗa musu kuwa dan tsaraba iri-iri babu wacce basu gani ba. Haka mutane suka taru anata saka musu albarka da musu bankwana. ALLAH sarki Babu harda kukansa yana sake neman gafararsu. Gwaggo na son ta roƙi gafara girman kai da shaiɗaniyar zuciya na hanata. Haka har suka wuce bata iya tace musu komai ba....

________★

          Yanayin tafiyar yamma da sukayi yasa sai bayan magrib suka iso Abuja. Damma suna isa Sokoto jirginsu ya taso. Yaya Fawzan ne yaje ɗaukatsu, sai kuma ga Yaya Yazeed shima. Sai kawai su Ammie suka shiga can. Maanal tasa rigimar zata bisu ta kwana Ammie ta korata. Aiko da hawayenta ta shiga motar Yaya Fawzan, dan ta ƙwallafa rai yau ma zasu sha hira da yayunta. Didi Shahidah da take ganin itama tana a cikin Abujan amma ta tafi gidan su Ammie suna isa gida itama baban su Muneef na zuwa. Ko shiga ciki batai ba itama Ammie ta korata...

     ★ Yaya Fawzan ne yayta lallashin Maanal, AA kam takaici ya sashi yin shiru, tun ma da ya shiga motar ya kwantar da bayansa a sit tare da lumshe idanunsa bai sake motsawa ba. Har sukazo gida bai tanka ma kowa ba, zuwa lokacin kuma Maanal ta daina kukan tana bama Yaya Fawzan labarin Giro.
     Tarbar data samu wajen Ameerah da Najma da Maimoon data shigo musu ya sake mantar da ita kukan rashin bin su Ammie. Nan fa suka rungume juna kamar wanda sukai wata batare ba. Sosai haɗin kan matan ke saka su Babban Yaya a farin ciki. Manaal taje ta gaida Babban Yaya cike da girmamawa, yanata tsokanarta. Daga nan sashen Mamy ta nufa, ta gaida Aunty, ta samu Mamy har tayi barci saboda bata barci yanzu sam sai an mata allurar barci, shiyyasa ake mata ita da wuri 8 nayi. Koda ta baro can sashensu ta nufa, dan AA tuni ya shige abinsa dama shi kam. Ko ina an gyara mata tsaff, aikin su Najma ne, sun saka mata turaren wuta masu daɗin ƙamshi. Ga abinci an ajiye musu a dining. Sama ta haura tana murmushi, ta nufi bedroom kai tsaye, dai-dai AA na fitowa a wanka. Kallonta yay ya ɗauke kai, sai itama ta tsaya tana binsa da kallon. Kamar zatai magana sai kuma ta fasa, itama ta ajiye hand bag ɗinta ta wuce closet domin rage kayanta. Daga can ta shiga bayi tai wanka da alwala. Sanda take fitowa yana salla, itama sallar tayi. Ta idar yana zaune bakin gado yana waya da RK, kallonta yake a ƙasan ido yana wani lulllumshe idanu, itako tayi kamar bata ganshi ba ta wuce, ga iskar hadari na tasowa da ƙarfi sosai. Fita tai ta haɗo musu abinci ta kashe komai ta rufe duk windows sannan ta dawo. Sun kusa yin karo dan shirun da yajita ya ɗauka ko barin masa sashen tayi, sai kuma ya ganta da abinci a hannu. Juyawa yay ya koma ciki, itama ta shigo. Tana tuttura baki da ɓata fuska ta zuba abinci dai-dai cikinta ta hau ci dan yunwa take ji ta bala'i, zuwa yanzu sam bata da jimirin yunwa. Tsayawa yay kawai yana kallonta, itama jin kaifin idanunsa a kanta yasa ta kalleshi a karo na farko. Sai kuma ta sake ɓata fuska idanunta na cika da hawaye tace, “Ni ka daina kallona”.
      “Ke da wane idon kika kallan har kika san ina kallonki”.
    Baki ta murguɗa masa.
“Oh ni kike murguɗawa baki?”.
“Ni yaushe nace da kai nake. Kawai dan kana neman faɗanka sai ka huce a kaina, to bazanyi ba. Kuma ALLAH ya dawo da Abah duk sai na faɗa masa abinda kake min”.
       “Sharri kuma kika koma Besty?”.
    “Bawani sharri sai gaskiya”.
“To naji! Faɗi da abinda da abinda nai miki?”.
      Shiru tayi ta ɓata fuska tana cigaba da cin abincin ta. Sai da ta ƙoshi sannan ta kallesa. Cike da rigima tace, “Wai bazaka daina kallona ba?”.
         “Ai bake kika biya min sadaki ba balle ki saka kin dokar kallonki.”
   Ya faɗa yana harararta. Fuuu ta miƙe zata bar waje, ya riƙota, sai ta sakar masa kuka tana ƙoƙarin kwace jikinta. Karo na farko abin nata ya fara bashi dariya. Wai shi da akama laifi baiyi kuka ba sai ita. Kai jama'a mata dabban ne. A haka kuma suke iƙirarin komi namiji yayi zasu iya? Ta ina? Bayan UBANGIJI ya ajiye kowa da komai a huruminsa. Akwai abinda basu iya yi da maza keyi ba, akwai abinda suma zasu yi mazan basu isa yi ba. Saboda yanayinta yasa dole shi ya sakko ya koma lallashi, amma sai da taci kukanta iya iyawa, daga ƙarshe kuma aka koma faranta ran juna cike da kewa duk da dudu kwana biyu ne.
      Tana kwance a jikinsa lamo a cikin kunenta ya raɗa mata, “I miss you bestie”.
          Sai da tai murmushi da ɗan jan hancinsa kaɗan sannan ta furta, “Kayi missing ɗina kake nemana da faɗa kuma?”.
       “Ai ke ɗin ce kike saka muyi faɗan. Kwana biyu fa ban ganki ba sai ta waya, banji ɗuminki ba, gaba ɗaya bana jin daɗin kaina. Har bana son nazo nace zan kwanta amma ke ko'a jikinki. Shiyyasa a kullum nake gaya miki soyayyar da zuciyar Ajwaad ke miki tafi taki......”
       “Ban yarda ba gaskiya, kuma bazan taɓa yarda ba”.
    Murmushi yay mata hannunsa riƙe da fuskarta, ya sumbaci lips ɗinta kaɗan. Ya ce, “Nima ban yarda ba ai”.
     Ƴar siririyar dariya tayi da faɗin, “Tom shike nan kowa ya riƙe nashi. Gobe zan koma office ba.”
      “Tun baki huta ba?”.
   “Bana tare da wata gajiya in har ina tare da kai. Kallon kyakkyawar fuskar nan taka kawai sakani take a ƙololuwar farin ciki da nishaɗi. Besty ALLAH yasa ko mutuwa tazo ta ɗaukemu a tare”.
        “Amin ya rabbi Besty wannan shine addu'a ta nima a kullum. Ya rabbi kasa ƙaddarar mutuwarmu a tare take. Dan ni da ke tamkar numfashi ne da gangar jiki, ɗaya bazai taɓa tabbata babu ɗaya ba”.
      Hawaye ne suka ziraro a idanunta suna sauka akan ƙirjinsa, babu abinda take tunawa sai azabar wahalar rabuwa na shekaru takwas da suka fuskanta. Kai bazata iya yafema su Gwaggo da Mamy a kan wannan ba koda zata yafe musu komai da komai. Shi kansa irin tunanin da yake yi kenan yana sauke ajiyar zuciya da shafa matashin cikinta.......✍️188


.......A Giro tamkar jira ake su Maanal su baro garin wanda suka san matsalar su Gwaggo suka fasa ƙwai. Hadda batun fyaɗe da cutar dake tare da su. Amma sai basu faɗi na Babu ba. Dan haka kawai sukaji bazasu iya tozarta mahaifin waɗanda sukai musu rana ba. Amma Talle dama kowa nada cikinta, hakama Sailuba kodan wahalar da su Sule ke basu bazasu raga mata ba. Abinka da ƙaramin ƙauye cikin abinda bai wuce awa biyar ba labari ya zagaye kowanne gida. Dan danan gutsiri tsoma ta tashi, tun anayin ƙus-ƙus har zance ya fito fili aka tabbatar ma su Gwaggo ansan komai fa daya faru dasu. Ruɗewa kuwa sukayi, zasu fara rantse-rantse mijin Gwaggo ya ce, “Karma ku rantse, dan nima an min bayanin komai akan dolene fa na sakeki idan ba haka ba zaki goga min. Dan haka saki uku”.
    Sosai Gwaggo ta rushe da kuka, amma ko tausayinta babu wanda yaji. Abinka da ƙauye kowa ya fara gudunsu, dan ance musu ko taɓasu sukayi shike nan sun kamu. Kai ko abu suka taɓa ka taɓa shike nan ka kamu. Harda masu cewa ko magana kayi da su. Kai hatta da Sule gudunsu yake yi, ba ruwanshi da lamarin Gwaggo da Sailu. Babu kawai yake taimakawa shima dan su Maanal su gani su ɗaukeshi su maida gidansu. Dan kullum dukansu sai sun kira video call an haɗasu da Babu. Wani lokacin ma haɗuwa suke a tare kowa ya kira sai suyita hira da shi Sule na nane da shi yana musu soki burutsunsa.
      Rayuwa tama su Gwaggo zafi matuƙa. Tsangwama da tsana da ƙyama da hantara tasa sai rama suke a tsaye. Kullum cikin kuka suke da dana sani. Dan kuwa kai tsaye kowa ke gaya musu alhakin su Maanal ne. Ashe sune ƴan iska masu karuwanci amma sukace Maanal ce. Gwaggo kuka take tana ƙari da rantsuwar bata taɓa iskanci ba, wanan ma daya faru tsautsayi ne. Amma babu wanda ya kulata. Nan kuma ƴan tsubbun da Sailu ke bi suna iskanci da ita da wasu a mazan gari dama na wasu ƙauyikan ne hankalinsu ya tashi. Kafin kace mi ƙwai ya fara fasuwa. Gaskiya ta fara fitowa. Dan danan kuma sabon zance ya tashi, ana cikin wannan cece kuce sai ga Haƙila ta dawo daga nata yawon tambaɗar da ciki. Ai kaɗan ya rage Sailu bata haukace ba. Abin bai tsaya a kanta ba aka haɗa harda Gwaggo. ALLAH sarki Babu al'amarin ya ɗaga masa hankali sosai. Amma haka su Maanal suka dinga lallashinsa da magana masu daɗi har ya samu nutsuwa. Kai ko kallon Haƙila baya son yi, yarinya ƙarama da cikin shege a gaba. Iyaye sun taru aka tsare Haƙila a gidan maigari, ganin za'a bata kashi ga babu goyon bayan Sule a yanzu, Sailu tayi sanyi bata da tacewa itama Haƙila tayi bayani. Ciki dai na Temo ne mai shago, ashe shine ya ɗauketa ya tafi da ita, dan sanda abin nan ya faru shi da ita suna rufe a shago suna iskancinsu sai da sojoji suka wuce da daddare ya lallaɓa da ita suka gudu. Daga baya akazo aka kwashe masa kayansa da ƴan sanda. Can ya wuce da ita wani ƙauye a garinsu can yankin kudanci. Yace ma ƴan uwansa matarsa ce, haka tana ji tana gani yake ɗaukarta suje coci, ya shiga maida mata ɗabi'u irin nasu. Da farko abin ya fara mata daɗi saboda ƙuruciya, kwatsam ranar ta jiyoma kanta abinda ya tashi hankalinta, dan kuwa Temo da abokinsa taji suna zanta za'a kaita gidan wani boka zai musu tsafi da ita suyi kuɗi, wai dama bokan yafi son mai ciki. Dan haka abokin yace masa ya shirya ya fara kaisa wajen bokan tukunna. Wannan tafiya ta bata damar gudowa, akwai wani bahaushe a garin yana harkokinsa taje ta sanar masa komai da daddare. Hankalinsa ya tashi dan bai taɓa sanin ita ɗin bahaushiya bace musulma ƴar arewa sai ranar. Bawan ALLAH duk da yasan zai iya shiga cikin matsala amma ya taimaketa ya fito da ita daga ƙauyen ya kawota bakin titi inda yasan manyan motocin na wucewa kuma hausawa ne drivers ɗin. Da ƙyar suka samu wani ya tsaya, a gurguje ya sanar masa komai, shima an dace mutumin kirki ne ya ɗakkota shi kuma wancan ya koma. Wannan shine sanadin dawowar ta gida. Dan direban ya kaita kano daga can ya sakata a motar Kebbi..
       Wannan labari na Haƙila ya girgiza kowa, Sailu tace zata zubar da ciki maigari yace kull, idan kuma taje ta kashe ta wajen zubar da cikin fa. Ai dole haka zasu amshi ƙaddara ta haihu. Idan kuma wani abu ya samu ciki to sai sun kai ƙararta Suru wajen hakimi, a hakan ma maigari ya tabbatar da sai ya gayawa hakimi komai gudun abinda zai iya zuwa ya dawo koda nan gaba. Wannan fa takunkumi da akaima Sailu ne ya hana a zubar da cikin Haƙilah. Dole ta cigaba da rainon sa zuciyarta babu daɗi ta uwarta babu daɗi. Ga halin da suke ciki akan hiv. Dan itama Haƙilar na jin haka ta janye jikinta daga Gwaggo da Sailu. Tace bazasu goga mata jaraba ba.....

__________★

        A yau su Maanal suka wuce ƙasar Saudia. Ita da Ameerah, Najma, babban Yaya, sai Yaya Fawzan da AA. Dan har yanzu Nibras na gidansu suna neman mafita ita da uwarta. Sai zaryar asibiti sukeyi daga ƙarshe suka samu Yaya Fawzan wai zasu kaita Egypt ganin likita kwararre. Bai hanasu ba yace ALLAH ya kiyaye hanya. Shi ko Babban Yaya babu ma wata kwana-kwana ko neman dalili ya gaya ma Saheeba ga inda zasuje, zata ɗaga masa hankali yaja mata gargaɗi da tuna mata halin da take ciki na jiyya da shan magani. Dan har yanzu ko turaka bata koma ba, duk da  taso yin hakan likita ne ya kafa mata sharaɗin sai ta kammala shan maganinta. To a yanzu dai tana gab da kammalawar, sai kuma ga batun wannan tafiya da take ganin Babban Yayan ya samu na makalewa. Taso zuwa takai ƙara ma Aunty, Nuratu ta kwaɓeta. Tace ta barsu suje mana kwana nawa sun dawo. Tace ita tana son zuwa taga Naufal ne. Nuratu tace, “Idan suka dawo basai muje ba”.
        “Da wane kuɗin? Bayan kin san komai bamu da shi yanzu?”.
     “Shi Yayan zai biya mana ai. Muma sai muce zamuje duba Aban, shi yaƙi ai ɗan zamba ne ko”. Da wannan karatun Nuratu ta kwantar mata da hankali. Sai dai ita Nuratu tana da nata shirin ne shiyyasa bata damu da tafiyar mutanen gidan ba. Hasalima daɗi taji dan hakan zai bata damar yin komai yanda ya kamata. Haka kuwa suka wuce suka barsu gidan shiru. Aunty duk sai taji zaman babu daɗi, gidan ya musu girma. Haka ma su Saheeban. Ashe mutane rahama ne.
       Aunty na basu shawarar dawowa sashen Mamy caraf Nuratu tace to. Kallonta Saheeba ta tsaya yi, dan ita kam ta kasa fahimta da gane mi Nuratun ke nufi a kwanakin nan take son maida alaƙarsu da sashen Mamy. Koda ta nema ba'asi sai Nuratun tace babu komai. Kawai dai ita tana jin tsoro ne gaskiya. Badan Saheeba ta gamsu ba ta amince. Haka suka tattara suka koma can. Mamy zatai magana Aunty ta hanata. Dole tai shiru amma dawowar su Saheeban sashenta ya sosa mata zuciya. Abinka da mugu shi yasan makwantar mugu sai ta kasa aminta da su. Dan haka ta saka sabuwar mai aikin da su AA ɗin suka kawo tana taimaka musu da abinci da gyare-gyaren sashen saboda kar abubuwan suma Aunty yawa ta saka musu ido. Sai dai kuma an samu matsala, dan kuwa a yanzu Mamy bata da ko sisin bama mai aiki tai mata aikin da take so koda na mugunta ne kamar su Haule, ita wannan ɗauka ma take taimakon su Mamy ɗin akai aka kawosu gidan dan daga ƙauye aka kawota bata san abinda ya faru ba. Sai dai irin ƙwarƙwararrun matan nan ne da komai zasu iya aikatawa akan kuɗi. Tsaff kuma Nuratu ta fahimci hakan dan haka ta fara janta a jiki, sannan ta dinga yima Mamy hidima har Aunty ta ji ta gamsu da Nuratu ta canja ne. Sai kawai tace bara ta ɗan je kano taga yara ta dawo. Dan duk da sun girma suna karatunsu kuma babansu na kula da su da abokiyar zamanta, sun kuma zo har sau uku sunga Mamyn itama ya dace taje ta gansu. Mamy zata nuna mata isa wai bazataje ba Aunty tace “A dalilin mi. Ba gori ba Kamila idan bani ɗin ba wazai zauna dake? Ko kinga a cikin dangin nan namu wani ya kiraki ko a waya ya miki jajen abinda ya faru balle jin yaya kike? Wata kusan huɗu ai kyamin adalci da kanki ma kice naje naga nawa iyalan, ko kin manta miji ne dani nima”.
       Shiru Mamy tayi dan kalaman sun mata zafi kuma. Itako Aunty ta watsar da ita tai shirinta ta wuce ta barta da su Nuratu......

________★

        Oum da Abah da kansu sukaje taro zaratan mazajen ƴaƴansu da matansu har jidda. Cike da farin ciki su AA suka rungume Oum, kafin su koma kan Abah, su Maanal suma suka rungume Oum, sunyi kewarta matuƙa irin yanda baki ma bazai iya muslatawa ba. Haka itama tayi kewarsu, ga farin cikin ƙaruwar da aka samu ƴaƴayen nata duka uku da cikunnansu. Shi kansa Abah wani irin farin ciki yake ji, dan ya tabbatar da zuwa yanzu yaransa sun sami irin farin cikin auren daya jima yana musu addu'a da fatan samu. Sun sami irin matan da yake fatan ganin su a ƙarƙashin ikon su. Fatansa ALLAH ya saukesu lafiya daga alkairin da suka ɗauka. A tare suka duƙa suna gaishesa. Da sauri yace, “Haba yaran albarka ku tashi ku tashi abinku, muje mota kun gaji ayi gaisuwar a gida. Babu musu suka shiga haɗaɗɗiyar motar da akazo ɗaukarsu suka ɗauki hanyar Madina inda su Aban suke..........✍️189


......Sosai gidan da su Oum suke yayi ƙyau, ba wani babba bane ba kuma mai hayaniya ba. Ga abinci kala-kala Oum ta shirya musu. Dama duk yunwar suke ji, dan haka babu ɓata lokaci kowa ya baje sukaci suka ƙoshi musamman Maanal da yanzu sam bata wasa da cikinta. Suko su Najma ma abincin sai da suka zaɓa, musamman Ameerah cikinta nada tsurfa, ba komai take iya ci ba.
     Su Maanal ne suka tattare komai zuwa kitchen, duk da akwai mai aiki suka taimaka mata aka wanke komai aka maidashi inda yake. Sai lokacin aka gaisa sosai aka ɗaura da hira. Abah babu ruwansa, shi kallon ƴaƴa yake musu ba surukai ba, dan haka jansu yake sosai a jikinsa da labari masu ma'ana. Sanin sun gaji Oum tace suzo suje masauki ayi hirar bayan sun huta. Basu musa ba dan tabbas sun gajin, musamman ma matan da kowa ke fama da kanta...

         Masaukin da inda su Oum suke ba wani nisa

196 / 213

Chapters