AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   126 / 213

375K to 378K   out of 636.6K words

mamaki, dan su Shahidah sunyi matuƙar ƙoƙarin nuna bajintarsu suma. Saboda tunda akace za'aima Maanal biki kafin tarewa suma suka shiga yin wannan tanadi su da Ammie babu wanda yaji ko ya gani sai Nene. Sai yau da ake fiddo kayan arziƙi ƴaƴan su Hajiya Yaya da na Hajiya Basariyya sukai tsuru-tsuru jikinsu na ƙarasa yin sanyi. Dan da gasken gaske an goge musu kaf haddarsu a wannan biki. Hatta su dangin Mamyn abin ya basu mamaki, dan su dai Mamy ta gama sanar musu Maanal ƴar matsiyata ce. Sai gashi a wajen baye hatta su Naufal dake matsayin ƴaƴa sai da aka basu rabo. Haka kaf manyan family na Darma kowa da nashi har su RK dake ƙananun uncle's kuma ta ɓangaren mace ma. Ga kayan gara mota guda, kaf kuma a sashen Oum aka ajiyesu ba'a ajiyewa Maanal komai a cikinsu ba dan sun ɗan saka mata wasu abubuwan a store da su Shahidah sukai dabarar saya suma ta ɓangaren kayan abincin.
Bayan gama rabo aka zagaya da Maanal gaban iyaye. Anan fa suma Darma Family suka sake zuba tasu bajintar. Dan sun sakama amarya kuɗin al'ada sosai, saboda ba kunya Oum ta bada babban basket na kaba tace sotake ta gansa cike da kuɗi iyayen ango da ƙannensa da auntys. Cikin dai raha akai wasa akai dariya. Tuni dangin Mamy suka tsure, dan da alama dai zasu sha kunya a wajen. Saboda su wai a gadarance suka taho da kuɗi mai dubu ɗari mai hamsin Maman Saheeba ma ɗari biyu wai za'a nunama Oum ita ba komai bace koda basa son amarya sai sun bada mamaki sai suka ga yara ƙanana na ajiye 1m da 500k kamar kuɗin banza. (To banda abin talaka ana faɗa da mai kuɗi ko gasa ne akan kuɗi😆😜🥱). Tuni su Mamman Saheeba suka fara ɓoye ƴan dubu ɗari biyu dana hamsin ɗin su, daga baya dai Saheeba data fahimci kunya fa dangin nasu zasu sha tace su haɗe kuɗin waje guda su bata. Haka sukayi, ita kuma ta fita ta ƙundumo 1m a cikin kuɗin sana'arta ta haɗa ta ajiye matsayin na dangin Mamy gaba ɗaya. Tsabar muguntar Hajiya Majdiya sai tace to matan yayyan ango Saheeba da Nibras kenan dole suma su sanya, hatta kuma Najma bata ɗagama ƙafa ba.
      Wannan abu ya girgiza Saheeba. Nibras da duk ta fige ta rame a kwanakin bikin nan uwarta tazo ta ajiye 1m dan itama bata son harkar zubda girma🤣. Ganin haka fa Saheeba aka sake zuwa aka ɗakko 1m aka ajiye itama. Aunty Rufaidah na ganin haka tazo ta ajiye 3m matsayin na Najma tace ta fanshi ɗiyarta itama. Zokaga ihu da ihu na shaƙiyancin yaran family ɗin darma. (NIKO NACE SHEGIYA NERA, ALLAH KA BAMU NERA MAI ALBARKA😆🙏). Wanna abu ya tsayama Saheeba da uwar Nibras a ƙahon zuciya, dan ita Nibras ma hankalinta ba awajen yake ba. Uwarta kuwa tayata kishi take da ƴan uwanta akan Najma. Dan ko bikin nan sun halarci shi ne kawai dan kar ace gashi-gashi. Amma Maman Nibras ta gama shirya bala'in da zasuyi da Mamy jira take kawai biki ya watse taji dalilin yima ƴarta kishiya batare da an sanar dasu ba..........✍️



*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖6️⃣9️⃣


______________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Shin kuna Neman in da zamu samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?kayan yara masu kyau unique na yan gayu ? To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo! Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi tanayi🥳🥳

___________

..........To su dai su Shahidah sunyi godiya sannan aka kai Maanal sashen Mamy, Mamy na bedroom, su Shahidah suka zauna a falo. Kasancewar tare suke da Aunty Suhaima, da Aunty Zainab, sai Aunty Kursiyya matan Uncle Hassan da Hussaini da Uncle Mahmoud kenan suka shiga har cikin suka mata magana kasancewarsu matan ƙannen miji. Dole Mamy ta danne ta fito sanye da hijjab, dan kwance take ciwon kai ya addaba mata. Ganinsu warr a falon suka cika mata ido, dole ta aro murmushin yaƙe ta yafama fuskarta. A gabanta aka zaunar da Maanal dake lulluɓe. Da ƙyar ta iya daurewa tace ALLAH ya sanya albarka kawai. Wai ai tasan duk wanda ya isa ya mata nasiha ita basai tace komai ba.
    Shahidah da a yanzu Maanal ta gama nuna mata wani abu kaɗan daga Mamyn sai tai murmushi kawai, tare da fassara zancen nata da ƙyau a zuciya. Ita kanta Nene yau dai kam tasha jinin jikinta akan Mamyn, amma batace komai ba suka fito da Maaanal. Sashenta suka maidata, aka ƙara mata nasiha sukai sallar la'asar suka firfito dan tafiya. Kuka sosai Maanal keyi abin tausayi, dan ma Amaal na nan tare da ita sai Aunty Sakina. Sai zuwa magrib su zasu koma gidan Shahidah su sake kwana gobe su wuce kd.
       Sashen Oum suka koma yimata sallama. Sosai Oum tai mamaki ganin wannan tafiya tasu ta yamma haka. Ta shiga lallashinsu akan su bari sai gobe da safe Nene tace ina ai in sha ALLAHU yau a Kaduna zasu kwana, abin ai sai ya koma rashin kangado kuma. Anyi komai an gama ai suma sai a barsu su huta haka nan abi yara da addu'ar zama lafiya.. Badan Oum taso ba ta haƙura, nan fa aka shiga shirya musu kayan biki da aka tanada domin su, dan hatta Ammie sai da Oum ta haɗa mata nata. Sashen Maanal ɗin suka sake dawowa tare da ita, acewarta ya kamata suyi sallama da AA dan ta kaisu sunyi da Abah yanata musu godiya, a can kuma suka sami Mamy itama. Kiran wayar AA datai a kashe kuma Fawzan ya tabbatar mata yana gidan sanda suke buɗar kai ya shigo ya sata biyosu.
      Rungume Maanal dake zaune a bakin gado ta takure waje guda tana sharar hawaye har yanzu tayi, cike da tausasawa ta shiga lallashinta. Kafin ta bata umarnin hawa sama ta kira musu AA ɗin. Mayafin lafayarta ta gyara da ƙyau, tayi ƙyau sosai, duk wanda ya ganta kuma yaga amarya, dan ƙamshinta daban ne, ga ƙunshinta raɗam yanata ɗaukar ido daga baƙin har jan, fatar jikinta kam da tasha gyara ba'a magana, sai wani irin glowing take a idanun mai kallo kamar ka lasheta. Ita kanta Oum kallonta kawai take tana murmushi, ta jima bataga ma'auratan da suka dace da juna ba irin Maanal da Autan ta, sai dai ai musu fatan zama lafiya mai ɗorewa kuma. Tare da Oum suka baro bedroom ɗin nata suka haura sama. Zuciyar Maanal bata ƙarasa fashewa ba sai da ta hawo upstairs ɗin, ya subahannallah komai yaji, ga wani mayataccen ƙamshi mai ratsa zuciya. Zama Oum tayi a ɗaya daga kujerun, Maanal ɗin zata zauna itama ta katseta tana nuna mata kofar bedroom ɗin AA. Jikinta cike da sanyi ta nufa ƙofar, tana gab da isa sai gashi an buɗe. Cak ta tsaya tana kallonsa. Kamar yanda shima yake kallonta irin na mamakin nan dan ko motsinsu bai jiba. Yama fito ne zai fita dan dama wanka ya shigo yayi rabonsa da wanka tunna safe manyan kayan jikinsa sun takurasa shiyyasa yazo yay wankan ya canja da ƙananu. Juyawa kawai Maanal tai tabar wajen, shima sai bai ce komai ba ya biyota saboda hango Oum zane a falon.
      Bata zauna ba, sai tai kamar ana kiranta a waya ta gudu ta barsu dan ta basu damarsu. Murmushi kawai Oum tayi danta fahimci wayo Maanal tayi ya gudu babu wani kiranta da akayi. Bedroom ɗinta ta wuce inda su Nene suke. Bata wani jima ba Oum ta shigo da sallama itama. Ta sanarma Nene ga AA zai shigo suyi sallama. Gyagygyarawa suka shiga yi kafin ya shigo bakinsa da sallama. Duk suka amsa banda Maanal datake kallon hotunansu a wayar Aunty Sakina. Cike da girmamawa ya rissina ya gaida Nene, hakama Aunty Sakina duk da ba girmarsa tayi ba, amma tunda akace matsayin ƙanwa take a wajen Ammie yake girmamata. Shahidah ta ce, “Oh mu baza'a gaishemu ba Ajwaad”.
    Hararrata yay ya ɗauke kai. Su Nene suka sanya dariya. Oum da itama ke dariya tace, “Gaskiya fa Shahidah ta faɗa Auta, dan yanzu babu batun ƴar gaddamar cewa bata girmeka ba matsayin yaya take dai”.
       “Ni banzanyi Auntys da su ba Oum, Aunty Sakina ta isheni”. Yay maganar ƙasa-ƙasa yana hararar Amaal itama. Dariya kowa keyi, Amal ta ce, “Ni dai na haƙura ma Yaya Ajwaad basai kace min Aunty ba, dan nasan bama cewar zakai ba. Kuma nima bazan so kace ba dan kai Yayana ne”.
     Oum ta ce, “Amaal yada saurin sallamawa haka”.
       “Oum gara na sallama wlhy, dan kozan mutu na dawo Yaya Ajwaad bazai ce min Aunty ba kema kin sani”.
     Nan ma sosai suke dariya. Shi ko ya fuske abinsa. Sai ma satar kallon Maanal yake ta ƙasan ido. Itako tayi kamar bata san ma da shigowar tashi ba, rabin fiskarta ma gyalen ya ɗan rufe. Godiya sosai AA yayma Nene, tare da alƙawarin zuwa gaisheta nan kusa in sha ALLAHU ita da su Ammie. Sosai Nene taji daɗin hakan ta kuma sake yaba AA ɗin dan tarbiyyar sa ta birgeta sosai. Leda dake a hannunsa ya miƙama Oum, yace ta basu, bai jira cewar kowa ba ya miƙe bayan Oum ta amsa ledan ta miƙama Nene tana murmushi. Amasar ledar Nene tayi tana faɗin, “Tofa mi muka samu kai ɗan nan.....”
     Ta kasa ƙarasa maganar sakamakon tozali da tai da kuɗaɗe ƴan dubu bugun Abuja sabbi fil. Da wani irin sauri ta kalla Oum, sai kuma ta girgiza kai tana miƙa mata ledar. “Bazamu amsa ba ɗiyata. Ai abun ma sai ya zama rashin hankali”.
    Roƙonta Oum ta shiga yi itama, amma Nene ta dage akan bazasufa amsa ba. Sai ma ta miƙe tana ficewa tunda su Amaal da Aunty Sakina anan za'a barsu su ƙarasa gyara mata gidan sai zuwa anjima kafin anguna su shigo dan ba'a barta ita kaɗai ba.  Shahidah dai zata bisu saboda sai sun koma ta gidanta. Suma su Maanal ɗin fitowa sukai yi musu rakkiya, tuni AA ya haɗa motocin da zasu kaisu can gidan Shahidah su ɗauka sauran kayansu sai su kaisu train station. Haɗa ido yay da Maanal dake sharar hawaye Aunty Sakina riƙe da hannunta. Su su Aneesa nata tsokanarta wai sai sun dawo Abuja suna bata kulasu ba. Suna ma haɗa ido da AA ɗin ta risinar da idannunta ƙasa. Haka suka shishshiga mota Oum ta danƙa ledar a hannun Shahidah, zatai magana ta harareta da mata alamar tai shiru. Dole tai shirun kuwa suka wuce. Ciki su Amaal suka koma da Maanal dake kuka sosai, AA ya girgiza kai kawai ya shiga mota ya fice a gidan dan zaije wajen abokansa dake shirye-shirye tafiya suma. Wasu dama tun safe duk sun wuce sai wanda suka rage da zasubi flight ɗin yamma....

         _________★

    Mamy dai ciwon kai ya hanata sukuni, gashi tasha magani babu wani canji, dole Hajiya Turai ta ƙara turo musu Nurse ɗin nan ta dubata. Cikin damuwa ta ce, “Hajiya akwai matsala fa gaskiya, in dai bazaki rage wannan damuwar ba bp ɗinki fa bazai taɓa ya sauka ba. Gashi zuwa yanzu hatta bugun zuciyarki ya canja. Jininki kuwa ba'a magana wlhy, shiyyasa ma kike ganin dishi-dishi ciwon kan kuma yaƙi sauka. Dole zan sake miki allurar barci mai ƙarfi sosai dan ki samu barci, amma ki sani allurarnan barci kawai zata sanya ki, kwanciyar hankalinki shine maganin matsalar ”.
      Ita dai Mamy komai tama kasa cewa, dan abun duniya ne ya taru yama zuciyarta rubdugu. Haka Nurse ta mata allurar barci. Tun tana kallonsu da saurarensu har barci yay awon gaba da ita.....

    Oum bata san wainar ba ake toyawa ba, tana a tsakkiyar ƴan uwanta dan duk dai zuwa gobe in sha ALLAHU zasu wuce su kuma. Itama Oum ɗin bata kawo komai a ranta ba tunda taga Mamyn na zagaye da nata ƴan uwan ne. Duk da dai duk yau bazatace tama ga giccin Mamy ba, koda yake ko Abah ba bi take takansa ba tanata hidimarta.

★ Bayan sallar isha'i su RK da ire-irensa dake sa'oin su AA a family ɗin na Darma suka iso gidan domin masa rakkiya. A dai-dai lokacin ne su Amaal ke fitowa cikin shirin tafiya ita da aunty Sakina. Sun sake gyara ko'ina na sashen sun baza uban ƙamshin da har a compound ana jinsa masha ALLAH. Sai da suka shirya Maanal ɗin itama da taimakon Hajiya Shuwa. An mata wanka da turare iya wanka fiye da yanda ake mata shi tun fara gyaran jikin nan. Kafin Hajiya Shuwa ta naɗeta a cikin sabuwar wata lafayar ƴar ubansu mai shegen ƙyau kalar peach da ɗan fari-fari, sai uban stones saketa walƙiya a jiki, an mata kwalliya ƴar dai-dai a fuska aka sake mata turaren turare. Sai ɗauri daya zauna mata akai sannan aka rufeta da lafaya ɗin. Suka saka mata ac dai-dai misali aka zaunar da ita a tsakkiyar kadon ɗakin nan ƙasa ɗin, Hajiya Shuwa tace su barta anan idan AA ɗin yazo da kansa sai ya mata jagora Upstairs ɗin idan ƴar rakiyar tasa sun tafi. Suna jin shigowar motocin su AA suka fito dan dama su suke jira. Suka ma Maanal wayon cewa bara suje wajen Oum kafin su AA ɗin su gama. Dan tun ɗazun take roƙonsu su kwana anan, ganin zata botsare musu da kuka sukace sunji zasu kwana. Shine suka mata wannan wayon suka gudu. Dan ko sashen su Oum ɗin basu koma ba ganin can su AA suka shiga....

★Su AA sun shiga falon Oum a dai-dai lokacin da dukkan mayan matan family ɗin ke zaune zaman jiran su, dan dama ƙa'ida kenan ga duk wani angon family ɗin a lokacin masa rakkiya ɗakin amarya. Kuma abinda zai birgeka isu-isu sukema juna rakkiya ba abokai ba. Su duka su a ƙasan carpet suka zauna dan duk iyayene. Yayinda AA yaje gaban Oum ya zauna, cike da sanyi ya ɗaura kansa a saman gwiwoyinta ya wani lumshe idanu. Abin mamaki sai ga hawaye. Murmushi sosai Oum tai saboda jin saukar hawayen nasa a saman ƙafarta, cike da kulawa da tsantsar so irin na uwa ga ɗa ta duƙo ta leƙa fuskar tasa. Kukan kuwa yake yi da gaske, itama sai taji hawaye sun cika mata ido. Ta dai daure tasa bakin mayafinta ta share masa su. Kafin a hankali cike da kulawa ta ce, “Haba Auta na yau ai ba ranar kuka bace, ranar farin ciki ce mun mallaki Maanal na har abada in sha ALLAHU. Dan haka bana son ganin hawayen nan kaji Babyna, addu'a zamuyi mu godema UBANGIJI daya nuna mana wannan rana bayan jarabawoyin da muka tsallake Abaya. Harma mu haɗa da sadaka domin nuna farin cikin mu ga ALLAH okay”.
    Kansa ya jinjina mata, sai kuma ya buɗe idonsa yana kallonta, tare da kamo hannunta ya sumbata...........✍️





*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖7️⃣0️⃣


______________


........Cike da tsokana RK ya ce, “Ikon ALLAH, amarya na kuka idan za'a kaita gidan miji yau ga ango nama mamarsa kuka za'a kaisa wajen matarsa”.
     Aiko sosai falon ya kacame da dariya, AA ya ɗauka fillo ya jefa masa. Cafewa RK ɗin yay yana masa gwalo. Aiko sai suma su Mama da Umma da Mamma da Gwaggo Khadijah suka shiga masa tsokana irin ta kakkanni, nan fa su Oum suka shiga karesa suma. Anyi wasa anyi raha kafin a koma nasiha da gaba ɗaya ta ta'allaƙa ne ga AA ɗin, ta yanda zai zama mai haƙuri akan mace, ta yanda zai ƙyautata mata, ta yanda zai shagwaɓata ya riritata, ya sauke haƙƙokinta da ƙyautatata mata. Ya tattala soyayyarsu kullum taita ƙara danƙo a maimakon rauni da maza da yawa ke saka soyayyarsu yi saboda sakacin sauke haƙƙoƙin da suka dace akan iyalansu. Sun nuna masa muhimmancin sauƙaƙama mace saboda kasancewarmu masu rauni. Suka kuma tunasar da shi zaman aure zaman ibada ne ba zama irin na saurayi da budurwa ba, yanzu maganar ƴakin soyayya da farautarta ya ƙare. Lokacine na tabbatar da ita ta jaddadata domin ta ƙara nauyi a sikeli da danƙo fiye da sufagilu. Haƙuri da kura-kuran mata dan mu a karkace muke, wanda ya dage ko fariyyyar son ganin ya lanƙwasamu mun miƙe to ya tabbata sai dai mu karye ɓas. Dan haka ya kula yasan miya dace ga zaman auren, ya zama mai tausasawa sai yaci ribar zaman har yay nisan zangon kaiwa wasu shekarun da za'a ringa lissafi shekarun aurensu suma. Daga ƙarshe aka rufe da addu'a mai tsaho da ratsa jiki, sannan aka sallame su dan zasuje sashen Abah su masa sallama da su Babban Yaya. Kasa tashi AA yayi, har sai da Oum ta miƙe tana murmushi ta kamasa ta miƙar. Sai kawai ya rungumeta. Harga ALLAH

126 / 213

Chapters