AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   171 / 213

510K to 513K   out of 636.6K words

cikin tana shafawa da murmushi. Baza'ace ya fito yanda kowa zai fahimta ba, amma ƙasan mararta ya mata tauri sosai ta yanda ita kanta zuwa yanzu tana sake yarda da eh lallai akwai gudan jinin Bestyn ta a wajen...

      Coffee mai daɗin gaske ta haɗa masa ta juye a ƙyaƙyƙyawan butan shayi na ainahin chainawan farko. Cike da ƙyawun kallo ta jera a saman ƙaramin tray ta haɗa da ƙananun cups na butar shayin ta ɗauka. Saman ta hauro, sai dai a maimakon bedroom yanzu ainahin ƙaton glass window ɗinsu da ya cinye bango guda na bangaren balcony ɗin saman ta nufa. Sai da ta danna wani button labulen wajen ya shiga zuge kansa biyu a slowly ya koma gefe-da-gefe. Sai ga gilashin da ko bullet baya iya fasawa ya bayyana. Tar-tar daga nan ma kake iya hango ainahin gidan musamman sashen Yaya Fawzan dake makwaftaka da nasu. Ido suka haɗa da AA dake Push-up ya jiyo yana kallon ta. Kayan data barsa da sune dai a jikinsa. Wando 3quater da riga armlass dukansu na kamfanin nike. Ba ƙaramin ƙyau da kwanciya a jikinsa kayan sukai ba, sun kuma fidda ainahin surarsa musamman damtsen hannunsa dake a murɗe masha ALLAH. A saman table ɗin da ke a tsakkiyar kujeru biyu dake wajen ta ajiye, AA ya dakata yana kallon ta, dan itama tayi ƙyau sosai cikin wandon jeans dake jikinta da ƴar top mai gajeren hannu. Yanda bayanta da ƙirjinta suka sake cika dole ta birge idanun mai kallo....
       “Besty kallon ya isa mana, kada ka cinye ni”.
     Murmushi yayi da faɗin, “Dama zan iya haɗiyeki ai da nayi hakan ko zan samu sauƙi daga abinda nake ji a kanki Besty”. Yay maganar yana juyawa ya cigaba da Push-up ɗinsa. Baki ta ɗan taɓe tare da sakin murmushi ta na ƙarasowa inda yake. Yana kaiwa ƙasa ta haye bayansa tana faɗin, “Tun yaushe ka gama haɗiyeni Besty, ai saura kawai ya rage maka”.
    Murmushi yayi baice komai ba, tana akan bayan nasa yana cigaba da Push-up ɗin sa tamkar baya jin nauyinta. Daga ƙarshe ma sai ta zame ta kwanta rigingine a bayan nasa a haka ya cigaba dayi, harda saka caca wai idan yayi sau ɗari da hamsin yau zata fita da shi yawo ta bashi atm ɗinta duk abinda yake so ya sayo koda na duka kuɗin ne.
     Dariya yayi ya ce, “Okay fara ƙirga”.
     Haka ya fara ƙirgawa kuwa, a mamakinta ba ɗari da hamsin ba sai da ya kai da saba'in, a hakan ma ita ta dinga roƙonsa ya dakata wai ya gaji shiko yana mata dariya.......

_________★

      Duk wannan abun dake faruwa a idanun Nibras dake maƙale a window ɗin bedroom ɗin ɗakinta ne tana kallon su. Dan ta saitin nan ɗin window ɗin nata yake. Duk da kuwa ta inada suke badan daga Bedroom ɗin take kallo su ba da babu yanda za'ai idan tana nasu balcony ɗin ta gansu. Da farko ma Fawzan ne a balcony ɗin zaune yana aikin office, yana ganin AA ya fito ya fara motsa jiki duk da bawani ganinsa yake sosai ba ya tashi ya shige dan yasan in har kaga WATA dole sai kaga ZARA. Ilai kuwa yana shigewar Maanal ɗin daya tashi dan ita ta fito wajen...
      Hawaye ne masu zafi ke fitoma Nibras, musamman data ga yanda duk style ɗin da AA zai yi Maanal na jikinsa suna hirarsu da dariya cike da farin ciki. Wani lokacin ma su harƙume kokawa, bawai ta danben tsiya ba, irin dai ta ma'aurata mara hayaniya da cutarwa. Sun jima a wajen yayinda ita kuma ta jima tana kallon nasu dan rashin aikinyi. Har suka sha coffee ɗinsu Maanal ta kwashe kayan ta shiga da su, ta sake dawowa tana rigimar AA sai ya goyata ya duƙa kuwa ta haye suka shige ciki abinsu basu ma san da ita ba....
   
      Labulen ta saki tana rushewa da kuka mai ciwo da zafafa zuciya. Yayinda shaiɗaniyar zuciyarta ke ayyana mata abubuwa masu yawan gaske akan AA. Ciki harda tunkararsa da abinda ke ranta dan ita kam ta gaji da haɗiyewa. A yanzu takai gaɓar da take jin komai zata iya yi domin AA, kamar yanda komai zata iya yi domin Fawzan. Gaba ɗaya zuciyarta ta kasa banbance wa take so a cikinsu. Dawa take buƙatar yin RAYUWA.
     Sai da taci kukanta ta gode ma ALLAH ta fito domin neman breakfast Dan wata irin yunwa take ji tazo kuma ta taras da wata soyayyar mai ainahin gudana a ƙasa tsakanin Yaya Fawzan da Najma. Suna kitchen suna girki a tare cike da farin ciki. Ga dariyarsu na fita cike da nishaɗi. Tai tsaye cak. Sai kuma ta jiyo Najma na faɗin, “ALLAH bazan yarda ba sai na rama love.”
          Shi ko Yaya Fawzan na dariya da faɗin, “Ashe zaki rame ƴar Zaria.” can sai gasu sun fito Najma na binsa da spoon ɗin girki na katako. Shi ko yana dariya da zizzile mata. Ko kusa ko alama basu ga wata Nibras ba ma su sabgar gabansu suke. Aiko da gudu ta koma sama tana kuka. Ta faɗa saman gadonta da rabonsa da gyara yau kwana uku kenan sai idan dare yayi ta haye a haka ta sake kwanciya tana kiran, “Na shiga uku ni Nibras, shike nan babu WAN babu KANIN, mayu sun mamaye ko'ina. ALLAH sai na kashe Maanal da Najma, sai na kashe su..........✍️

      Tirƙashi, ashe su oga AA an kusa yin takaba😎.



*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣4️⃣4️⃣


______________


............“Barka da zuwa Baa!”.
     “Barka dai Son. Fatan na sameka lafiya?”. Mabera ya faɗa yana bin ɗakin bacha ɗin sille da kallo. Shima Sille ɗakin yabi da kallo, sai kuma yay ƴar dariya da faɗin, “Normal ne Baa.”
     Mabera ya jinjina kansa, kafin ya kafe Sille da ido. “Yanzu Son bazaka bar cikin tsohon companyn nan ba ko? Na gaya maka zama a wajen nan akwai haɗari, sannan kowane jaki da doki zai maka kallon wani ƙasƙantacce ko karen ƴan siyasa ne. Amma ka kasa fahimta ta. Kaje ka kama hotel na shekara guda yafi min”.
       “Hummm Baa! bazaka gane bane. Shifa mugu shine yasan makarantar mugu. Idan naje hotel na zauna ya zan yi da waɗan nan karnukan farautar nawa ne? Idan na barsu su kaɗai anan ALLAH kowane banza ma zai kawo musu hari ne musamman waɗan nan masu baƙaƙen kayan. Kawai ka barni anan ina samun yanda nake so, kallifa ɗakin nan, minene marabarsa dana hotel ɗin. Ac yaji, solar taji, daga waje ne kawai zaka ɗauka bacha, amma a ciki ko ɗakin Kamila ai albarka”.
         “ALLAH ya shirya min kai Son, Kamila fa itace ta kamilo min kai duniya tun karana bai kai tsaiko ba.”
     “Hhhhhh!! Kai Baa, kuma fa kun tsula tsiya a ƙarninku dai-dai gwargwado. ALLAH dai yasa tuban da akai yanzu ya zama kaffara ce. Muma ALLAH ya maidamu danshin ku mu tuba a dai-dai muna cika 45, dan kasan shifa walakirin lahirar nan ba gajiya suke da ɗimar mutane ba. Kar muje ana hayya-hayya a aljanna mu muna ƙofar gate ana bamu horo, ai al'amarin baiyi daɗi ba wlhy. Koda yake koda rinto da wawa ai sai munje kusa da MANZON ALLAH”.
        “(S.AW). ALLAH to yasa. Amma gaskiya to, ba'ace komai ba dai Son, kasan nima dai nayi islamiyyar nan kiranyen sheɗanne kawai kasan shi mai rabon wahala yake ɗauka. Amma dai kai, anfayi al'amura, koma ace ana kan yi, amma dai gab muke ai da tuba ba komai. Yanzu yaya kuke ciki da Kamila?.”
      “Hhhhh sai da kai Baa! Langa-langa mugun ƙarfe, ƴan gwangwan na rainaka amma shine uwar cinikinsu. Rumfa makara ɗaki, ko baki kare ɗan kwarai ba ƙya kare shege, yo shima ai shegen da ubansa tunda ba'a ruwa ko a tuwo uwar ta shawosa ba ko taci. Kaga ƙwan jimina ba'a ganinka sai gidan masu kuɗi, coge takalmin mata gajeru na rubibinka dogayen ma sakawa suke dan su ƙara tsayi. Marfin tukunya mai rufe sirrin ƙazamar miya koda arniya ce ta rufu, kaga Junaid, baban Junaid mijin Sabuwa baban Nazifa da Sa'adatu. Ogan Kamila kota amsa ko jiki yay tsami”..
      “Son baka da dama ALLAH yanzu mike tafiya a wajen Kamilar? Menene shiri ka kuma”.
        “A gareni komai normal ne, a gare ta kuwa tana can tana haukar nemana yanzu haka. Dan na toshe ko'ina. Sai dai ina samun imformetion ɗin komai a wajen Turai ”. 
        “Turai? Son har yanzu kana tare da Turai ken nan?”.
     Kai Sille ya sauke ƙasa yana shafa keya. Ya ce, “Baa matar nan fa nada amfani sosai a garemu kaima ka sani. Kayi haƙuri ka yafe mata wancan kuskuren da tai....”
       “Amma kasan wacece Turai ai ko”.
“Na sani Baa, kar kuma ka damu dan a tafin hannuna take wlhy, a yanzu haka komai daya shafi mijinta har mutuwarsa na sani, shiyasa ko ɗar bana ji a kanta dan har yanzu abinda naso ta sani kawai take sani. Kamar yanda kai treating ɗinta a baya nima haka nakeyi yanzu. Kasan mugu shine ya san makwantar mugu.”
         “Hakane. Shike nan ina jin ka.”
     “Yauwa normal ne Baa. Kamar dai yanda na gaya maka tsarin wasan a baya shine......” tsaff ya sake maimaita masa komai da suka tattauna a waya ranar. Mabera ya jinjina kai da sauke ajiyar zuciya. “Tsarinka duk yayi, sai dai dole ne mu canja dukkan wasan. Dan a yanzu mun zo wata gaɓa ne bata hawainiya ba gudun barewa zamuyi. Kamar yanda ka faɗa yaron nan Ajwaad shege ne. Kasan iya buge-buge na har yanzu mun gagara sanin ina ƙanwarka take da Yazeed. Ƴan sandan ma suna neman maidamu mahaukata. Yanzu haka zancen da nake maka Sabuwa na kwance a asibiti kwana biyar kenan. Daga ni har ita Chalawa ya hana a barmu mu shiga gidansa, ƴan sanda ma ke gadin gidan. Hakama yaransa makarantar boko da islamiyya jami'an tsaro na tare da su. Matansa ma idan zasu fita haka ne. Matarsa ce ta tsakkiya ce dai ma jiya kaɗan ya rage na cafketa a asibitin doctor Dev.. sai kuma na fasa dan na fahimci akwai abinda take ƙullawa. Kasan shegiya ce itama, kuma ta hasala ƙwarai da gaske akan kwasar kayanta musamman da Yazeed ɗin bai iya kwaso na amaryar ba sai take tunanin da sanya hannunta a ciki. Shiyyasa a yanzu haka na shirya yin aiki da ita, kuma nan da kwana biyu kacal nake so ta shigo tarko na.....”
        “Sai da kai Baa! Shiyyasa bana gajiya da maka kirari dan ka cancanta, ALLAH kuwa ubana yafi na kowa dan nawa kowace ɓaranɓarama ya haɗa. Ga ilimin bokon gana arabi amma yafi jahili jahilci. Ka tafka tsiya a ƙarƙashin ƙasa a zahirin rayuwa ko damo baya nuna maka haƙuri sai jinin Mabera tushen aiki...”
      Wata dariya Daddyn Nazeefa ya sanya mai ƙarfi, Sille na tayasa da iya iyawa, sai kuma suka cafke. Cike da so da ƙauna ya ce, “Son ALLAH yay maka albarka, in dai bakin iyaye nada tasiri akan ƴaƴa koda kuwa iyayen tantirai ne to kai dai bakai babu taɓewa. Dan kamar uban kamar ɗansa, idan kaji ana ainahin TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE to Mabera ne da ɗansa, wato Junaid ɗan Junaid ”.
      “Yess Baa! Sai da kai. Fitaaaa manaaaa!”.
     “Tuni na fice Son. Dan haka bayan wancan shirin nawa naka wasan na haɗaka ne ni da kai. Manta da wannan video ɗin bazai baka kuɗin da kake buƙata ba aiki zamuyi mai ɗungum a lokaci guda da zai mallaka mana Alhaji Usman Chalawa da da tsohon Ambassador kuma ɗan kasuwa Alhaji Aliyu Abubakar Darma, abokin ƙuruciya kenan, rayuwar jami'a ai ba wasa ba, wannan abotar tamkar ƴan uwan taka take. Lokaci yayi da zan maida murtani da ƙarfin ƙwanji, sannan da ƙarfin basira. Ta ƙarshe Kamila, itace zata fi kowa amsar sakamakon wannan wasan, dan gaba ɗaya ma wasanta ne, Aliyu Darma ya biya nashi tuni harda gyara, yanzu albarkacin ta zaici shima shi da ƴaƴansa”
        Wani irin cafkewa sukayi kamar ba uba da ɗa ba. Daga haka Mabera ya fara tsarama Sille bayani filla-filla.....

_________★

         A can Sille da ubansa na ƙullawa, anan Kamila ma ƙullawar take yi. Dan shiri take yi sosai na wasan ƙarshe akan Oum, Abah, da yaranta uku zaratan mazaje. Plan b Nana da ƴaƴanta. Sille da mahaifinsa sune plan c ɗinta in har ta tabbata Junaid na a raye dolene ta maidashi gaba da inda ta aikashi a baya. Dan haka a yanzu shiri ne na gaske, dan ta shirya karɓa daga rasa Aliyu Darma amma kuma dole ne ta tsira da Fadeel, Fawzan, Ajwaad Aliyu Abubakar Darma. Dan bazata yarda tai 2-0 ba. Sai dai Fateema ta ɗauki wannan makin wlhy. Dan tabbas in dai tana raye dole ne Fateema ta rasa ALIYU DARMA, da ƴaƴan ALIYU DARMA. Ita zata mallaki ƴaƴan, Aliyu ya mutu, Fateema ta ƙarasa rayuwarta a ciwo. Dan bazata taɓa rayuwa a wannan duniyar Aliyu Darma na raye shima a wannan duniyar ba tare da wata ba ita ba. Dan haka kowa zai rasa, sai dai ita zata tashi da ƴaƴan Aliyu Darma kamar yanda ta faɗa.
      Tai wani makirin murmushi, fuskarta data gama lalacewa da rama na sake bayyana tayani muninta a fili.....

________★

         “Mama magani ya iso yau da safe yaya tsarin yake ne?”.
    Saheeba ce mai maganar tana leƙe-leƙe gudun kar wani ya jita. Daga can Nana ta ce, “Duka kowa akwai tsarin da zaki bashi nashi batare da fahimtar kowa ba. Amma yanzu zaki fara da matar Ajwaad ne. Dan zubar da cikin jikinta zai saka hargitsi da tashin hankalin mutanen gidan ta yanda zakiyi amfani da ruɗewarsu ki ciyar da sauran nasu tsarin. Saheeba kada kiyi wasa. Ki nutsu dan ALLAH kiyi abinda ya dace. Kinga kayan nan kaf abinda na tara na kadara da wanda kema kika saya ne dana Nuratu harda aron kuɗi na sake yi a wajen Hajiya Turai duk na haɗa. Dai-dai da sarƙoƙin ki na gwal da jarin sana'arki duk suna a wannan kayayyakin, to ku lura ke da Nuratu, kuyi komai da lura dan abinda muka rasa ba komai bane kamar yanda malam ya faɗa. Muda babban kaya zasu shigo hannunmu a dare ɗaya. Kedai kiyi komai da lura musamman akan Kamila, kin san dai shegiyar kanta ce matar nan a ɓangaren gina sharri da tuggu da mugunta da makirci kanta naja matuƙa. A yanzu haka dukkan motsinku akan idonta ne. Kamar yanda suma sauran mutanen gidan na tabbatar duk da wannan kwantar da kan naku bawai sun yarda daku bane ɗari bisa ɗari”.
         “Hakane Mama muma mun san hakan, musamman shegiyar Maanal ɗin nan wlhy ƴar bala'i ce yarinyar, yanda kika san aljana haka take. Akwai wankakken ido da kwalwa mai kaifin haddace da gane abu. Yanda kika san tana ji a jikinta, shiyyasa ma nake tunanin kamar tana da aljanu”.
     “Aiko zamu sauke mata su”.
  “Nima haka nace Mama, sai batun Daddyn Naufal, Mama har yanzu duk da yace ya haƙura ko ɗakinsa naje baya ko taɓa ni, wlhy duk a matse nake da shi na rasa yanda zanyi. Amma shi ko'a jikinsa saboda ya samu wata sai da ya kwanta ya shari barcinsa hankali kwance.”
         “Karki damu wannan aikin nasa shima mai zafi ne, in dai kin jure kinyi yanda ya dace, yanda kikaga ubanku baya iya tsallake karan dana gitta haka shima zai koma miki.”
     “Kai da naji daɗi Mama aiko nagode sosai. Kunnenki ya zama a buɗe, hakama wayarki, dan a kwana a biyun nan kacal dole kiji karam kwacam ɗan Ajwaad yabi rariyar ruwan gidan DARMA”.
          “Dako na kwana ina saka miki albarka. Dan haka sai na jiki, amma nafi son komai ya kankama ranar salla zaifi bada amrmashi”.
“Yanda kika ce haka za'ayi Mama”.
    Nana na yanke wayar Saheeba tai wata dariyar ƙeta da faɗin, “Lokacin yaƙin basasa a gidan Darma yayi, Maanal dake wasan zai fara a ranar babbar salla”.............✍️

       🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🏃🏃🏃🏃🏃🏃🏃🏃Yau ba magana nayi Nan. Lamarin Saheeba da Nana, Sille da Baa ɗinsa, Mamy ai shiru na ma shine zaifi alkairi kawai kuma kun sani😮‍💨.




*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣4️⃣5️⃣


______________



...........“Wai saurin mi kake yi ne haka? Naga kamar ma farin ciki kake zaka fita ka barni a gida”.
       Murmushi AA yay yana mai saka maɓallin jikin gab da wuyan rigarsa. Ƙiri-ƙiri an maida shi mai saka manyan kaya na dole. Sai in office zaije ne kawai yake tsira. Fuskar Maanal dake ta ɓata fuska hannunta rike da lins ɗinsa ya shafa, cike da lallashi ya ce, “Haba Matar AA ina ni ina murna zan tafi nabar zuciyata anan. Kinfa

171 / 213

Chapters