AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   130 / 213

387K to 390K   out of 636.6K words

kuma na samu nutsuwa, sai dai ban kai gareta gaba ɗaya ba saboda ruɗanin data shiga har tana yi kamar ma numfashinta zai bar gangar jikinta. Domin wancan tsoron har yanzu yana a tare da ita.”
          Cike da nazari RK yace, “Ajwaad karka damu da tsoronta, ka samawa kanka nutsuwa kawai, idan ba hakaba akwai matsala. Dan wannan halin da kake gani kana ciki komai zai iya faruwa da kai. Ba kamar na baya bane da kake shiga ka fita. Nutsuwar farko daka samu saboda tsahon shekarun daka ɗauka a ciki ne dole dama hakan zai kasance maka. Amma a zuwa na biyun jikinka da zuciyarka dama ƙwaƙwalwarka zasu samu dukkan dai-daiton daya dace. Kai a yanzu ka fita kasancewa a haɗari saboda ba shine na farko a gareta ba....”
        Sai da AA ya runtse idon azaba da cije lips kafin cikin ƙarfafa kai ya furta, Rafeeq! Manaal is actually a virgin!”. Babu abinda ya faru a waccan ra...nar”. ya ƙarasa da ƙyar saboda wani irin ƙullewa da cikinsa yayi.
      A hankali RK ya wani irin lumshe idanunsa yana sakin murmushi mai sanyi da sauke ajiyar zuciya mai nauyin gaske, a da hasashe kawai yake yi amma yanzu yaji tabbaci, tabbas wannan shine plan c, dole ne kuma yayi duk yanda zai yi AA ya yajema Maanal gaba ɗaya a wannan daren kodan ahalinsu dana Mamy dake a gidan su san hakan suma. Dan abu ne dai na sirri ko, amma ALLAH sai ya fasa ƙwai anyi shagalin jinsa gobe a gidan Darma. Dan hakan zai wanke AA da Maanal ɗin kanta ya cirema kowa shakku, masu aibantata suji kunya. Cikin ture tunaninsa ya ce, “Ajwaad maza ka tashi kaje ga iyalinka, ka ajiye wani tausayi gefe dan hakanne kawai zai baka damar tabbatar ma Maanal kai ba mai laifi bane a gareta, a binda take tunanin ka ƙwata da ƙarfi ita kuma ta rasa yana a tare da ita. Abinda take tunawa taji tsoro yana nan dai. Karka damu babu abinda zai sameta yanzu kaine a gaɓar haɗari. In sha ALLAHU da asuba zanzo da Nurse ta duba ta. Maza ka tashi baka da isasshen lokaci dan yanayi ka ya tabbatar min ka fara zuwa matakin ƙarshe”.
      AA yasan gaskiya RK ya faɗa masa, dan numfashinsa har ya fara fisga kamar mai shirin suma. Anan ya jefar da wayar, ya juya da ƙyar yana kallon Maanal da barcin wahala ya kwashe. Da yake kuma wayar da yake yi magana yake a hankali bata ko motsa ba. Ji yay wani karfi yazo masa, ya kalla agogon dake a side drawer ƙarfe uku da mintuna biyar, gaba ɗayansa ya yunƙura, ya saluɓe bathrobe ɗin jikinsa ya yar anan, ya yaye duvet ɗin da take ciki ya kwanta kusa da ita. Hargitsatsun idanunsa ya ƙura mata, zuciyarsa na bugawa da ƙarfin da bai taɓa ji ba. Hannunsa ya dafa gefen fuskarta a hankali kamar yana lallabar zuciyarta.
A firgice ta farka sakamakon saukar hannunsa akan fuskarta dan dama barci bamai nisa bane, jikinta na ɗan rawa ta juyo tana kallonsa da hargitsatsun idanunta da suka sha kuka ga barci data fara. Baki ta buɗe da nufin yin magana a firgice ganin ya sake kwanto jikinsa a nata. Bakinta ta motsa kamar za ta yi kuka, sai ya ɗan matsa baya kaɗan, yana fitar da numfashi mai ɗumi akan fuskarta, da matuƙar zurfin murya mai taushi da santsi kamar ba tashi ba ya ce, “Shhhiii!!... kada ki ce komai, Manaal... ki barni na karantar dake cikakken karatuna daga kundin littafina dana daɗe da tanada domin ke kawai...” Sai ya runtse ido, ya sake matsawa a hankali ya sumbaci laɓɓanta da tausayi, kamar yana tambaya ne ba tilastawa ba ya cigaba da faɗin, “Ki bar zuciyarki ta saurari tawa. Kada ki ce komai, bari zuciyata ta gaya miki babban ajiyayyen saƙon da take ya faman ajiyar. Domin dai-dai wannan shiru tafi buƙata...”
Kai ta shiga girgiza masa, hawaye kuwa tuni sun ɓalle, ta sake yunƙurowa zatai magana ya ce, “Shhhiiii!!! ki bar ni in koya miki KARATUN da ya fi kowace magana Please My half...”
Kafin ta sake yunƙurowa ya rufe mata baki ruff da nashi, ya riƙe mata hannun da take ƙoƙarin kai masa duka da tureshi, zuciyarta ko wani irin mugun bugawa take har yana ji, jikinta ya fara rawa sosai sai ga hawaye na shararowa har akan tashi fuskar. Eh lallai ashe Maanal bataga komai ba ɗazun, dan tamkar wasan yara akayi a yanzu ne AA ɗin ke tabbatar mata da kansa a Ajwaad Aliyu Abubakar Darma. A yanzu ne ya zama kurma na gaskiya kuma makaho. A yanzu ne ya tabbatar mata da dukkan abinda yake faɗa mata na zuwan wannan ranar. A yanzu ne yake tabbatar mata dole ta cika alƙawari. A ɗazun da sauranta tunda bakinta a buɗe yake har tana iya kiran sunaye da neman ɗauki..
     Ya rabba, Maanal bata taɓa sanin akwai wata azaba da jiki zai iya fuskanta ba sai a yau, a yau ɗin ma a yanzu. Tun tana some-somen shiɗewa harta sume masa gaba ɗaya batare daya sani ba. Dan shi ɗin kansa baima san mi yake yi ba. Baya gane komai, baya fahimtar komai, baya ji baya gani. Baya ma tuna kansa a matsayin kansa...........✍️


💃“Ragargaza! Rigirgiza! Dagargaza! Wuta direba aljanna tamai rabo ce....”.

Wannan waƙarfa da akeyi idan za'a kai amarya wani gari a mota ko🥱🥱. Saura wani ya fassara min waƙa ƴan sanda ne zasu rabamu😏😏🥱🏃
     



*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖7️⃣5️⃣


______________


.......Mamy na zaune a inda Maman Saheeba ta barta idanunta a lumshe, tun ɗazun so take ta motsa tama ɗauka wayarta ta kirata saboda jinta shiru amma ta kasa. Knocking ƙofar da akai ya sata kallon wajen. Aka ƙara na biyu sai ta bada izinin shigowa. A mamakinta Babban Yaya ne ya shigo bakinsa da sallama. Taɗan zuba masa ido, sai kuma cikin ƙarfin hali ta ce, “Kai kuma lafiya a daren nan?”.
       “Lafiya Lau Mamy, Saheeba ce tace kin kirata a waya, na ji shiru kuma shiyasa nai tunanin ko babu lafiya”.
     A zuciya Mamy tace (Saheeba kuma...?) a zahiri kam rasa ma abin cewa tayi, sai kuma ganin yanda ya zuba mata ido ta ce, “Yanzu Fadeel dan na kira matarka shine ka taso ka biyo ta?”.
       “Lah Mamy ki fahimta mana, nace najita shiru shiyasa nai tunanin koba lafiya ba. Yanzu fa magana ake ta sha biyu ta wuce. Kinga dole nai tunanin akwai damuwa. Amma tunda lafiya ai Alhamdullah sai da safe”.
    Daga haka ya juya ya fice abinsa. Da kallo ta bisa kawai abu uku na mata kai-kawo a zuciya masu ɗaci. Na farko miyyasa Saheeban zatai ƙarya cewa itace ta kirata? Sannan ina taje a daren nan to?. Na biyu yanda sam su Fadeel basu damu da ita ba, yanzu ace a yanayin nan daya ganta bazaiyi tunanin bata da lafiya ba, ta inda Ajwaad ya ɗarasu kenan, ko yaya yaga canji daga gareta sai ya gane. Hawaye suka ziraro mata. Tamkar wadda aka bama ƙarfi sai gashi ta yunƙura ta tashi. Dolene taje ta duba Saheeban da Nana ma da taji shiru babu ita babu Ajwaad ɗin. Da ƙyar take tafiya saboda ƙafafunta da suka kumbura suntum, ga ciwon kai gana ƙirji da yake mata kaɗan-kaɗan shima. Shiru tsakar gidan babu kowa, haka ta dinga tafiya cike da ƙarfin hali tana haɗa hanya, tama rasa ina zata dosa, shawarar da zuciyarta ta bata na zuwa sashen Ajwaad tabi, dan gwara ta fara duba Nana tasan halin yaron nan ba ragama ƙanwar tata zaiyi ba.
    Ta ƙofar kitchen tabi itama, tunda dama tannan ta bama Maman Saheeba shawarar bi. Itama sai da tabi komai na kitchen ɗin da kallo tana taɓe baki, kafin ta shige sai dai falon ƙasan shiru ne babu kowa. Amma fitula a kunne. Kuka-kuka da kiran sunan kamar Nuratu da taji anayi yasata nufar upstairs ɗin da ƙyar dan ƙafafunta sun mata nauyi sosai. Ai kamar jira ake ta gama hawowar kunnuwanta suka jiye mata abinda ya sakata tsayawa cak a firgice. Dai-dai nan kuma su Maman Saheeba suma suka ganta duk sai suka ƙara firgicewa. Jikin Mamy rawa yake sosai, takai hannu ta toshe kunnenta amma abinda take gudun jin tamkar a ƙwaƙwalwarta ake zayyanawa. Idanu a rufe tai wani irin juyawa gaba ɗaya domin komawa a bisa tsautsayi tai tsallaken taka step ɗaya, sai kawai ji kake rikicaaaa manyan mata sun kife.
       A wani irin mugun tashin hankali Saheeba da Mamanta suka bar Nuratu suka kai kan Mamy da har ta fara mulmulawa tana yin ƙasa. Da shegen gudu suka shiga binta, tana gab da ƙarasa direwa ƙasa gaba ɗaya suka samu nasarar riƙota. Sai dai ina aikin gama ya riga ya gama dan gaba ɗaya jini ya wanke mata fuska, kuma sam bata numfashi.
     Anya Saheeba da uwarta sun taɓa shiga irin wannan tashin hankalin kuwa a rayuwarsu. Dan Maman Saheeba bama tasan ta fashe da kuka ba tana kirama kanta ta shiga uku. Saheeba da itama jikinta ke rawa kaf-kaf ta ce, “Mama mun mutu, yanzu yaya zamuyi, wlhy idan bamu fitar da su a sashen nan ba akwai matsala. Kada fa ki manta duk ƴan kano suna a gidan nan. Sannan wlhy Ajwaad baida mutunci komai zai iya yi idan yazo ya gammu da uwarsa kwance a wannan halin, zai ma iya cewa mune muka turota. Mama aurena, dan ALLAH ki taimaka ni bari na tafi wlhy suka ganni anan zasu saka Fadeel ya sakeni, kuma shima nace masa Mamyn ce ta kirani.....”
      Itama Maman kukan ta fashe da shi, “Yanzu Saheeba sai ki tafi ki barni cikin wannan bala'in? A tunaninki idan ni sun zo sun sameni auren naki zai tsira ne. Ki kamata mu kaita sai mu dawo mu ɗauki Nuratu itama”.
       “Mama tayaya zamu iya? Ta yaya bayan kin san dai matar nan itama ba laifi ƙatuwa ce. Gwara-gwara ma Nuratun. Mafita ɗaya garemu kawai ki kira Aunty”.
     “Baki da hankali Aunty kuma?”.
“To wlhy itace kaɗai mafitarmu, idan ba haka ba ni dai zan tafi gaskiya. Dan wlhy ina son mijina da ƴaƴana. Bazan so barin gidan nan ba, yo ko kishiya bana fata balle barin gidan kina dai ganin sun haɗa kai an aurama Fawzan ƴarsu shima Fadeel ɗin zasu iya yin haka”.
    Ran Mama ya ɓaci amma sai ta danne. Da ƙyar ta iya lalubo number Auntyn su, cikin barci ta ɗaga wayar, roƙonta kawai Maman Saheeba ta shiga yi akan tazo sashen Ajwaad ta biyo ta kitchen akwai matsala.
        “Sashen Ajwaad kuma? Ke kuwa miya kaiki sashen Ajwaad a wannan daren Nana?”.
     “Bani kaɗai bace ba fa harda Aunty Kamila”.
     Kamar dai Aunty bazata tanka ba sai kuma ta yanke wayar, ita kanta lokacin da take isowa falon saman abinda ya fara shiga kunnenta duk sai taji ta gigice. Ta ƙoƙarin juyawa Maman Saheeba daketa sheƙama Mamy ruwa taƙi ta farfaɗo ta riƙota. Cikin ɓacin rai Aunty ta zubama Maman Saheeba mari. “Ku daƙiƙan inane zakuzo ma yara sashe a irin wannan lokacin, ƙarfe biyu saura fa. Mike damunku ne? Kun haukace daga ke har Kamila ne”.
       Duk da Maman Saheeba taji zafin marin nan matuƙa ta ce, “Ni dai dan ALLAH Aunty kiyi haƙuri, ko kamata mu fita da ita karma yaron nan ya fito ya gammu, ko wani a gidan nan ya fahimci muna nan. Nuratu ma tana a sama a sume”
        Rasama abin cewa Aunty tayi, dan sai lokacin ta iya hango Saheeba dake wajen Nuratu ɗin a yanzu. A fusace ta ce, “Ai gara ma asan kuna nan ɗin, wannan ai jahilci ne da rashin sanin mutuncin kai, ya ALLAH na shiga uku na, wai mi kuke son ku zama ni kam Nana?”. Aunty ta faɗa tana nufar hanya, cike da magiya da roƙo Maman Saheeba ta kamota, Aunty ta watsa mata wani mugun kallo. Da ƙyar dai ta yarda suka kamata suka fita su ukun. Aunty taja ƙofar kitchen ɗin ta rufe. Sun zo kusan tsakkiyar gidan kawai sai sukai ido biyu da Abah. Gaba ɗaya rikicewa sukai, suka saki Mamy a ƙasa babu shiri. Aiko sai gashi ta farfaɗo, taja wani wahalallen numfashi, sai kuma ta fashe da kuka tana kiran, ta shiga uku.
        “Shiga uku? Ai da sauran lokaci”.
   Abah ya faɗa yana sakarma Maman Saheeba da Aunty wani murmushi ya juya zai bar wajen. Sarai kuma abinda ya faɗa a kunnen Mamy. Ai ko sai ƙirjinta ya shiga dukan dubu-dubu jikinta na rawa sosai gashi bata gani da ƙyau saboda jini daya ɓata mata fuska. Aunty kuwa cikin sauri ta ce, “Aban Fadeel wlhy ban san komai ba, yanzu suka kirani a waya ina barci ma”.
     Juyowa Abah yay ya kalleta, sai kuma yayi murmushi kawai ya cigaba da tafiyarsa. Mamy da ke jin kamar zata sake suma muryarta na karkarwa ta ce, “Na shiga uku da gaske shine?”.
      Banza Auntyn tai mata, dan harga ALLAH murmushin Abah ya matuƙar dakarta. Ita kanta Maman Nana jitai murmushi na girgiza mata zuciya, balle Saheeba da tun cin karo da Aban tai saurin juya baya dan ita ta fara sakin Mamy a ƙasa ma. A karo na biyu Mamy da jini ke rinjaya ta sake sume musu. Aunty da bata fatan bayan Abah wani ya sake zuwa ya gansu kuma, dan gara shi idan tai masa bayani maybe ya fahimceta a zafafe ta ce, “Sai ku kamata muje, kuma wlhy sai dai ku dawo ku ɗauki Nuratu”.
      A wahale suka kaita sashenta, Haule da motsinsu ya sakata leƙowa ta bisu da kallon mamaki, ganin fa abun mai girma ne zaram ta fito. Gaba ɗaya sunma manta wacece ita sukace ta taimaka musu dan Mamyn ta musu nauyi sosai. Haka ta kama suka haura da ita sama. Suka shimfiɗeta a ƙasa, Aunty sai zagin Maman Saheeba take, ita kuma tanata rantse-rantse Mamy tace ta rakata zatama Ajwaad magana.
       “Ai kin rakata, kunje kuma kun jiyo abinda kuke buƙatar ji, kun kuma samo sakamakon daya dace daku. Yanzu sai ku jira shima randa yaron zai san su wanene ku marasa hankali kawai tunda ubansa yau ya sani. Kuma sai dai ku koma ku ɗakko Nuratu wlhy bazan koma ba”. Daga haka ta jawo kwalin tissue dake a table ta fara goge ma Mamy jinin daya wanke mata fuska har ya fara jiƙa gaban rigarta. Ashe rauni taji a goshi da haɓarta sai gefen idon dama. Haule ta aika ta kawo mata first ald box tai mata ɗan abinda zata iya ta saka mata audiga da bandage dan a samu jinin ya tsaya kafin dai safiya...
      Dai-dai nan su Saheeba suka dawo ɗauke da Nuratu, a falo suka ci karo da wata cousin sister ɗinsu Mamy. Motse-motse ya sata fitowa. Da mamaki take duban Maman Saheeba da Saheebar sai Haule data fito da kayan da aka gama gogema Mamy jini. Sai kuma ta kalla wanda suka ɗako da alamu suka nuna kamar bata numfashi.
        “Subahanallahi. Nuratu kuma? Nana daga ina haka?”.
     Hawaye Maman Saheeba ta share, tana kaiwa zaune kusa da Nuratu da suka shinfiɗar anan falon, zatai magana caraf Saheeba ta karɓe. “Aunty Mariya yanzu drivern gidansu ya kawota, wai ta matsa ya kawota nan shine ta suma a hanya. To ya kirani a waya da wayarta na fito sai ga Mama itama shine muka shigo da ita”.
        Matar da yake akwai kwakwazo ta ce, “Innalillahi... Amma miyasa Hajiya Turai zata barta ta fito a wannan tsohon daren? Koda motar gida ce ai akwai haɗari. Haule kawo ruwa”.
     Da sauri Haule ta wuce kitchen, babu jimawa ta dawo da gorar ruwa masu sanyi a hannu. Saheeba ce ta amsa ta shafama Nuratu. Amma ko gezau, sai da Aunty Mariya nan ta bata shawarar a watsa mata da ƙarfi sannan Saheeba ta zuba da yawa a hannun ta ta watsa mata. Aiko wani irin nannauyan numfashi ta ja mai ƙarfi sai kuma ta sake komawa lagaf. Hankalinsu ne ya ƙara tashi. Saheeba ta ce, “Kodai za'a duba Rafeeq ne”.
      Da sauri Mamansu dake sharar hawaye ta ce, “ALLAH ya kiyaye, jini Fateema bazai taɓa min yarinya ba wlhy”.
       Rasama abin faɗa kowa yayi suka sake watsa mata ruwan mai yawa sai gashi ta sake farfaɗowa. Kuka ta fashe da shi tana wani irin zaburowa zata tashi Maman ta maidata, zatai magana nan ma ta rufe mata baki. “Basai kince komai ba dan ALLAH Nuratu, kiyi shiru baki da lafiya”. Kuka ta sake fashe wa da shi mai ƙarfi, wannan kuka ne ya farkar da mutane da yawa duk suka shiga fitowa suma. Nan fa aka zagaye Nuratu.
    Caraf wata dattijuwar mata ta ce, “Kai yarinyar nan ba lafiya ba tanada iska.” ai jin wannan batu sai su Maman Saheeba suka laƙe, nan fa kowa ya shiga mata tofi, wani ma babu abinda yake karantawa motsa bakin kawai yake yi ya tofa yawu hankalinsa kwance🤣.........✍️
     




*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin

130 / 213

Chapters