Author : Bilyn Abdull Category : Romance
taimaka mata bata da wani ƙarfi a jikinta wlhy ƙarfin hali ne kawai.”
Zai yi magana ta ɓata fuska dan ta sanshi da gardamar tsiya idan bashi ne yay niyyar abu ba da kanshi. Rigimar Asiya daban take a gareshi, darunta na musamman ne babu hayaniya babu hauragiya. Amma idan ta sakaka a gaba dole kayi yanda take so ko kai baka so. Dole yay shiru ta fice ta ja musu ƙofar..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣2️⃣6️⃣
______________
.........Ganin Yazeed daya fito ya raɓe gefe abin tausayi kamar wani boyi-boyin gidan sai ƙwalla suka cika mata ido. Batare komai ba ta wuce zuwa sashenta, babu jimawa sai gata da goran ruwan addu'a da dama take ta neman hanyar fara bashi yana sha amma bata samu ba saboda koyaushe yana nane da matarsa. Ba kuma cin abincin kowa yake ba yanzu a gidan balle su samu su bashi ko yimasa girki da shi. Cike da kulawa da murmushi Ammie tai kiran sunansa. Ya ɗago yana kallonta, kujerun dining ta nuna masa tana faɗin, “Bismillah zomu zauna anan ko kafin ta fito”.
A mamakin su bai mata musu ba, koda suka zauna sai ta buɗe ruwan ta miƙa masa. Nan ma amsa yay ya kai baki, zai sha kawai tace, “Kayi bismillah mana”. Sai yay shiru kamar wanda ya manta ma da bismillahr, hakan ya bata tabbacin an kaɗe masa hankali daga ibada ƙwarai da gaske. Dama tana lure baya zuwa massallaci sam yanzu. Sai su wuni su kwana ma uku suna sashensu shi da matarsa basu fito ba. Bismillahr ta maimaita masa, sai ko ya faɗa kamar yanda ta faɗa sannan ya sha ruwan. Kamar zai sha kaɗan ya ajiye sai gashi ya shanye tas ya ajiye goran. Ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi kamar yanda itama Ammien ta sauke tata a ɓoye. Sai cayay mata “Ammie ruwan nan da daɗi sosai”.
Murmushi Ammie tayi, ta ce, “Sosai kuwa. Nima da naje bikin nan aka bani na shashi daɗin da naji yasa na sayo mana. Idan kana so ka dinga zuwa kana amsa kullum a sashena kaji ko”.
Kai ya jinjina mata alamar to, dai-dai nan Daddy ya leƙo yace su shigo. Duk mikewa sukai, yaran suka shige cike da zaƙuwa. Ammie harta miƙe ganin Yazeed bai motsa ba ta juyo tana kallon sa. “Taso mana muje yayansu.”
Shiru yay kamar zai ƙi, sai kuma ya miƙe ya bita, da sukaje bakin ƙofar sai ta bashi dama ya fara shiga sannan ta shiga. Hajiya Yaya zatai magana ganin Yazeed sai tai shiru, ta zuba masa ido tamkar yau ta fara ganinsa. Shi kuma ya tsaya cak kansa a ƙasa cike da rashin gaskiya. Duk da bawai abinda ya aikata yake iya tunawa ba, dan kaf abinda yay a daren jiyan tamkar an goge shi ne da ga brain nashi bai iya tuno komai. Kai hatta kai-kawon nan da ake na ƴan sanda da wani tambayoyi shi ba fahimtar komai yake ba fa. Ganin kallon da Hajiya Yayan kema Yazeed ɗin na neman yin yawa Ammie ta katse yanayin ta hanyar mata sannu, sannan tace Yazeed ɗin ya matso ya gaida Hajiyan shima. Kamar dai bazai zo ɗin ba sai kuma ya matso batare daya kalleta ba yace, “Sannu”. Daga haka yay shiru. Kai kawai Hajiya Yaya ta ɗauke batare da tace komai ba. Sai kuma zuwa can ta kalla yaran a sanyaye ta ce, “Kuje falo zanyi magana da Daddyn ku”.
Fita duk sukayi, Yazeed shine farko ma, Ammie zata bisu Hajiya Yaya tace ta tsaya harda ita zatai maganar. Dole ta koma ta zauna. Sai da suka gama fita suka rufo musu ƙofar sannan ta dubi Ammie da Daddy. Idanunta na zubar da hawaye ta ce, “Ammien yara yaushe kuka dawo?”.
Ammie bata ɓoye mata komai ba ta labarta mata kiran da yara sukama Daddy da zuwa ɗaukarsu da yay ita da Hajiya Basariyya dama ɓarnar da suka tarar a gidan mai ban mamaki daban tsoro. Zuwan ƴan sanda da hasashen yara na cewa Nazeerah ce. Murmushi Hajiya Yaya tayi mai ciwo, idanunta na zubda ƙwalla tace, “Ba Nazeerah bace Yazeed ne”.
A firgice Daddy da Ammie suka kalleta. Daddy ya ce, “Yazeed!!”.
“Tabbas shine, dan yazo nan da akwatin ɗakinka, nima shine ya ɗaureni saboda na masa magana. Bana raba ɗayan biyu shine ya shiga sashen Basariyya ma. Itama Asiya dan sun kulle ko'ina ne shiyyasa inaga ya rasa hanya. Amma tabbas shi za'a bincika yasan komai”.
Idan akace hankalin Daddy bai tashi ba a wannan gaɓar ma ƙarya ne, sunma rasa taya zasu fassara al'amarin. Hajiya Yaya kam kuka take sosai, dan zuwa yanzu al'amarin Yazeed ɗin kam ya gama daga mata hankali matuƙa. Sai Ammie ce ta koma lallashinta. Daddy kam yayi shiru yana faman lissafi a zuciya da yake shi namiji ne, kai tsaye suke tunani ba kamar mu ba da za'aita haɗo gabas haɗo yamma.......
_________★
Washe gari AA ya tashi da shirin zuwa Kaduna ganin jikin na Maanal da suƙi sosai. Amma bai gaya mata kadunar zai je ba, yasan zata iya tayar masa darunta. Sai yay shirin kamar office, duk da ganin ya saka manyan kaya sai da tayi magana. Sai ya ce mata dan tana so ne ya saka. Da haka ya kashe bakin nata. Da yake ita yau ba office ɗin zataje ba yace ta bari sai zuwa gobe ta sake jin ƙarfin jikinta. Dan tun jiyan sai yamutse-yamutse take yi, idan ya tambayeta tace naman jiya take tunawa. Abinci ma taƙi ci sai fura da fresh milk. Duk kankambar girkinta yau ko kallon kitchen bata son yi, koda sukaje sashen Oum su Oum na kitchen ƙin shiga tayi. Shi AA ma hakan daɗi yay masa, dan inba hakan ba ALLAH bazata nutsu ba.
Breakfast yayi shi kaɗai, dan yau babu babban Yaya babu Yaya Fawzan duk ana can ana tattalin amare. Maanal kuma tace bazataci ba, ko dining ɗin ma bata zo ba tana daga falo sai shi da Oum ne kawai data haɗa masa komai. Murya a ƙasa dan kar Maanal ta jiyo yace, “Oum Kaduna fa zanje.”
Cikin jin daɗi Oum tace, “Kai Alhamdullah naji daɗin hakan kuwa. Ya kamata kam a bisu dan da dare munyi waya da ƙanwata al'amari babba ne gaskiya.”
AA ya ce, “Nima dana kirata bayan sallar isha'i take mun bayani, abinda ya tsaya min a rai da tace tana zargin saka Yazeed ɗin akayi bayin kansa bane. Kuma nima gaskiya bana tunanin zai aikata. Tunda nayi huɗɗa dashi a watannin baya yana da nutsuwa da cikar kamala sosai. Kodan halallacin da yay a rayuwar su Ammie koda shi ya aikata zan masa uziri. Balle yanda Ammie ta musalta min jiya na kwana ina tunani da nazarce-nazarce. Shiyyasa zaije gara a tari abun da wuri dan duk inda mai saka aikin yake yana kusa da su gab. Ga Daddyn tace ya kasa ɗaukar kowanne mataki dan abin ta bigesa sosai”.
“Ta ina kam zai iya ɗaukar wani mataki, ai yama yi jarumta, idan wani ne zubewa zai yi ALLAH sai dai kwanan asibiti. Baga abokiyar zamanta da sukazo nan ba Hajiya Basariyya jiya kaji sai da aka kwana kanta, da yake kuma bata da hankali wai Asiya ce tasa akai musu da yake bataji Yazeed ɗin bane da farko.”
“Mtsoww! ALLAH Oum na tsani matar nan, shashasha an faɗa mata irintace mayyar kuɗi, Ammie ta damu da irin wannan abubuwan ne, kafin taga dukiya ita Ammien ta gani ai tunda mahaifinta ya bar mata azzalumin miji ya cinye”.
Murmushi Oum tayi da faɗin, “Kasan idan mutum nada halin banza ɗauka yake kowa ma haka yake. Ni har ka tuna min ma da Habib ɗin, ya kamata ka sanya lokaci ka ɗauka Baby kuje Giro su san da auren nan naku”.
Ɓata fuska yay sosai ya ce, “Oum miyasa?”.
“Haka ya kamata Auta, ai ko ba komai shi uba ne, abinda yayma Ammien ku wannan tsakaninsu ne, tunda gashi ALLAH yay mata canjin alkairi, ku kuma yaƴane, dole ku sauke haƙƙinsa dake kanku. Anyi bikinku babu kowa daga ɓangaren su, bai kamata ba sam.”
Shiru AA yay dan kawai bazai iyama Oum musu ba. Amma baya ƙaunar abinda zai sake haɗa hanyarsa da su Babu da shegiyar Gwaggon nan daya fi tsana fiye da kowa. Haka dai ya kammala suka miƙe, koda sukazo falon a mamakinsu barci Maanal ma takeyi. AA ya kalla Oum yana ɗan murmushi. “Da alama Babynki ta zama kasa Oum”.
Dariyar itama Oum tayi, ta ce, “Ta zama kam. Dan barci baya mata wahala sam yanzu. Kaga ɗaga min ita zuwa ɗaki kwanciyar kujerar nan zata iya sakata ciwon jiki”.
Amsawa yay da to yana ɗaukar Maanal ya kaita bedroom ɗin Oum ɗin, sai da ya sumbaci goshinta da lips ɗinta sannan ya raɗa mata bye-bye a cikin kunne ya lulluɓeta ya fito. Bai zauna ba yayma Oum sallama dan drivern sa ya shirya shine zai jashi. Har compound ɗin Oum ta masa rakiya, ya kalla sashen Babban Yaya dana Fawzan yay murmushi, ransa fal gulma. Yayi sallama da Mamy dan sai da suka fara zuwa suka gaisheta ita da Abah sannan sukaje sashen Oum, itama dai bai gaya mata Kaduna zai je ba, sallamar zuwa office kawai ya mata, duk da ma dai sama-sama yau ta amsa musu gaisuwa dan Maanal ma bata shiga ba a falo ta tsaya, da farko ma Haule catai barci take yi, sai dai shi ya wuce bedroom ɗin ya dubata dan yasan takai haka a kwance sai dai in babu lafiya, sai ko ya shiga ya sameta zaune tana waya, sai dai yana yin sallama ta katse. Ya fahimci ita tace ma Haule tace musu tana barci, dan haka ya gaisheta shi kaɗai ya fito yace ma Maanal ɗin tana barcin, Maanal kam sarai taji a jikinta itama idon Mamyn biyu, kawai dai ta ƙyalesa ne...
Sai da motar ta fice sannan Oum ta koma ciki tana murmushi........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣2️⃣7️⃣
______________
......Da asuba da ƙyar Najma tabar Yaya Fawzan fita massallaci, kasancewar basu samu wani isasshen barci ba saboda rigimarta ana kiran salla suka farka su duka. Ta rigime masa da kukan ita kanta, ita jikinta na ciwo, ita miye ita miye. Shi ko biye mata yake cike da lallashi da ƙauna. Albarka kam babu kalar wadda bata sha ba a wajensa, harda ƙyauta ta musamman. Tunda ya dawo sallar asuba kuma ya lalace a taimaka mata, tayi salla rakin da take masa ya sake zaman gasa mata jiki ya bata magani tasha suka sake kwanciya. Sai a lokacin ne suka samu barcin mai nauyi sosai. Ba kuma su tashi farkawar ba sai sha ɗaya. Shima kiransa Nibras ta dingayi a waya har sai da ya farka. Koda ya kai kunne ta saka masa kuka wai yazo ya bata sakinta. Tsaki ya ja mata mai ƙarfi ya yanke kiran. Ya ajiye wayar zai sake maida kansa ya kwanta suka haɗa ido da Najma. Luuu yay da su ya buɗe a kanta, cikin magana a hankali ya ce, “Love kin tashi?”.
Kanta ta jinjina masa. Ya sakar mata murmushi da kai hannu ya shafa kanta. Cike da tsokana ya ce, “Love rigima, Yaya na tuba, Yaya kaji tausayina, Oum kice masa yaji tausayi na, Mommy, Yaya AA kaga baiji maganar ka ba. Wayyo Babban Yaya wayyo Abbana..... ”
Da sauri ta juya masa baya tana murmushi. Dan exactly yanda tayi haka yake kwaikwayon muryarta. Shima siririyar dariya ya saki da matsowa ya rungumeta ta bayan ya sumbaci kanta. “ALLAH yay miki albarka kinji, yanda kika sakani farin ciki a duniyata kema ALLAH ya dawwamar dake a cikinsa. Najma ina ƙaunarki, ina ƙaunarki harma ban san taya zan musalta ba. Amma in sha ALLAHU zan kwatanta ta yanda zaki cigaba da yarda Fawzan na ƙaunarki. Dan ALLAH ki zame min mar'atussaliha, wlhy zakisha mamakin yanda zan koma miki tamkar raƙumi da akala, ba sai kinje wajen kowa ya baki lakanin mallaka ta ba. Na mallaka miki kan nawa gaba ɗaya kiyi duk yanda kike so”.
Murmushi Najma keyi, wani daɗi na ratsa ta. Sai dai kunya ta hanata magana. Sun kai tsahon lokaci yana jera mata kalamai masu sanyi da taushi kafin ya ɗauketa zuwa bayi sukayi wanka. Yanzu ma ya sake sakata a ruwan zafi sosai. Koda suka fito anan ɗakin ya shirya kansa ya fita ya amso abinci a sashen Oum daya samu ta ɗan kwanta. Koda ya dawo da kansa ya bata taci shima yana ci sannan ya sake bata magani yace ta kwanta ta huta. Tace tana son zuwa ta gaida su Oum.
Ido ya ɗan waro mata, sai kuma yace, “A'a love zuwa wajen su Oum da wannan tafiyar akwai ƙura. Yanzu ma da naje barci take yi ita da Lilly. Kiyi haƙuri zuwa yamma kin ɗan ware kumburin idon nan ya sauka”.
Batai masa musu ba, shima sai yay zaman aiki kawai tana kwance a kusa da shi. A haka Nibras tazo tana musu knocking, kunnen uwar shegu Yaya Fawzan yay mata, ya kuma hana Najma tashi...
Sosai Nibras ta sake haukacewa. Data fahimci bafa fitowar zai yi ba ta koma sama ta ɗakko akwati ta dinga jawo kaya yana afakawa ciki tana kuka. Wani irin mahaukacin kishi take ji, ko barci batayi ba a daren jiya. Shiyyasa ta tashi wujiga-wujiga. Haka taja akwatin ta ɗauka key ɗin mota ta fito. Gidan shiru anata barcin gajiya, mota ta shiga ta wuce gidansu, dan gwara ko tsakkuwa ta tauna dan aya taji tsoro.....
________★
Su AA sun isa Kaduna da wuri, dan gudu sosai drivern sa yayi. Sha ɗaya ma a gidan su Ammie tai masa. Tarba ya samu ta girma daga Ammie, dan tasan da zuwanshi. Suna baro gida ya kirata a waya ya sanar mata gashi nan a hanya. Aifa saita miƙe ta shiga aiki ita da Aunty Sakina dan ta dawo jiya da daddare itama. Abinci aka masa sosai, shima Daddy da yake yana anan sashen Ammien saboda ƴan sanda sun buƙaci yabar sashen nasa sai an gama bincike, Ammie ta sanar masa zuwan AA ɗin. Dan haka ya fasa fitar da yay niyya ya zauna jiran isowarsa.
Cikin sa'a kuwa sai gashi ya iso da wuri. Ya fito tarbarsa ne yake ganin motar mijin Sabuwa alamar shi ko Sabuwar wani yana gidan kenan, dan can ya hango Yazeed bakin sashen nasu zaune kamar wanda aka koro. Korosan kuwa akayi, dan yau ma Baban Nazeera da Sabuwa ne suka zo wai jin yaya ake ciki. Ita Sabuwa hankalinta akan kasonsu ne, shi ko mijinta so yake ya dinga sanin kowane motsin su Daddy ɗin ne dan nashi shirin ya tafi masa dai-dai. Yau ma basu shiga sashen kowa ba sashen yarsu suka wuce. Yazeed na shara suka koroshi waje shine yazo ya zauna inda Daddy ya gashi abin tausayi.
Ɗauke kai Daddyn yayi ya wuce inda motar AA take fuskarsa da murmushin ƙarfin hali. Drivern AA ya fito da sauri ya buɗe masa ƙofa. Fitowa yay a nutsensa, yayi ƙyau cikin manyan kayan dake jikinsa harda hula. Yaro a shekaru amma babban mutum a cikar kamala da ƙyawun haiba. Cike da girmamawa ya rissina yana gaida Daddy. Daddy dake murmushi ya riƙosa yana faɗin, “Barka da zuwa Son. Ammien ku ta tadoka da sassafen nan kaida ke fama da gajiyar hidima”.
Murmushi AA yay cike da girmamawa ya ce, “Daddy ai kamawa takeyi. Kuma bawani nisa bane nan da Abuja”.
Murmushin Daddyn yay shima, ya kama hannunsa suka nufi sashen Ammie. ALLAH sarki sai Yazeed dake hango komai ya bisu da kallo. A falon Ammie akaima AA masauki, sun gaisa cikin girmamawa, ya tambayi ina su Waleed Ammie tace sun wuce makaranta. Baici komai ba sai ruwa da ya sha yace sai anjima dan yayi breakfast kafin ya taho. Babu wanda ya takura masa suka fara tattaunawa. AA yay shiru cikin zurfafa tunani, sai zuwa can yace, “Ammie! Daddy inada wata shawara da nake ganin zata bamu mafita, amma idan ba damuwa nafi son mu tattauna har ita Hajiya mahaifiyar Yazeed. Dan dole sai da haɗin kanta komai zai tafi mana yanda ya kamata.”
Cikin gamsuwa Daddy yace ba damuwa, suje sashen nata su sameta dan bazata iya zuwa nan ba bata da lafiya. Hakan sukayi, suka nufi sashen Hajiya Yaya. Su Basira duk suna falo sai yanzu ma suke breakfast. Gaba ɗayansu sai da suka zubama AA ido, duk da sun sanshi a bikinsa shi da Maanal sai ya wani sake tafiya da imaninsu. Dan wani irin ƙyau da kwarjini ya sake musu mai cika ido sosai. Sai da Daddy ya musu magana suka shiga gaishe da AA ɗin zukatansu duk suna rawa.