Author : Bilyn Abdull Category : Romance
wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖7️⃣6️⃣
______________
.........Ganin hankalinsu ya raja'a akan Nuratu Haule ta zame jikinta ta fita. Ƙasan bene ta maƙale tai kiran Sille. Bugu biyu ya ɗauka, yanda taji muryarsa kuma ya tabbatar mata da wata macen yake tare. Kishi ne ya turnuƙeta, amma tasan ko giyar wake tasha bata isa yin magana ba, kaɗan daga aikinsa yasa taje har gida yay mata dukan tsiya. Sai kawai ta fara masa bayani cikin rawar murya..
“Dear ya kamata ka baro Lagos ɗin nan tunda ka gama aikin daya kaika ka dawo Abuja, dan abubuwa nata faruwa. Kaga dai anci biki an gama yau ango ya shiga ɗaki ga Nuratu can taje ta jiyoma kanta abinda ya dame ta. Hakama Hajiya Kamila kaca-kaca suka shigo da ita cikin jini, ban sani ba ko itama daga sashen AA ɗin ne oho. Dan Mamar Saheeba da Saheebar sun kima ƙarya.
“Naji”.
Ya faɗa a taƙaice yana wani shiii da baki na iskanci ya yanke wayar. Duƙewa Haule tai a wajan ta sanya kuka......
__________★
Iskar sanyin asuba ce ta farfaɗo da AA, dan yana kaiwa border shima ya sume. A hankali ya shiga buɗe idanunsa da suka masa wani irin nauyi na masifa. Bishi-bishi ya ke kallon Maanal, sai kuma a hankali ta fito masa a cikin ido. Gabansa ne ya faɗi, ya zabura duk da bashi da wani ƙarfi ya matsa daga jikinta. Hannu ya kai ya kunna lamp ɗin dake side drawer, kafin ya kai yatsarsa sai tin hancinta amma babu numfashi, zuciyarsa ta shiga tsitstsinkewa da rarrabewa, gefen wuyanta ya maida ya taɓa jijiyar wajan, nan ma babu motsi. Ji yay kamar shima zai ƙara sumewa. Sai ya ɗora kunensa a saitin zuciyarta... Bugun da tashi zuciyar take ai tamkar zata faso ƙirjinta ta fito a yanzu. A karo na farko ya yunƙura zai tashi, amma hakan ya gagara saboda wani irin ɗaurewa tamau da cikinsa yay masa. Ga jiri yana ji ga ciwon kai mai tsannanin gaske da bai taɓa fuskanta a rayuwarsa ba. Kan ya dafe da hannu ɗaya, ɗayan na riƙe da cikinsa. Ba irin ciwon cikin jiya bane ba, yanzu ji yake tamkar an ajiye masa dutse ne. Sai da yaja fin minti biyu kafin ya sake yinƙurawa cike da ƙarfin hali da jarumta. Aiko ji yay kamar ya fasa ihu dan azaba, amma ina bazai iya zama yana kallon Maanal a haka ba. Da ƙyar ya miƙe a galabaice ya nufi bayi, ruwa masu zafi ya daidaita ya sakarma kansa na shower. Yafi mintuna biyar a haka sannan yay wanka yay na tsarki cikin ƙarfin hali ya fito yana dafe da cikin nasa, dan ko iya miƙewa da ƙyau baya yi ma. Ga idanunsa kamar zasu faɗo idan ya buɗe saboda ciwon kai. Bashi da kaya a ɗakin, sai dai in wanda ya cire zai maida. Ba kuma zai iya haka ba. Haka ya daure ya fita cikin haɗa hanya ya koma ɗakinsa, jallabiya kawai ya ɗakko ya dawo. Yana ƙoƙarin zama dan ya ɗago Maanal duk da shi yasan da wahala ya iya hakan saboda cikinsa yaga wayarsa na haske. Kamar zai share sai kuma ya tuna Rafeeq yace zai kirashi da asuba. Da ƙyar ya iya kai hannu ya ɗauka, Rafeeq ɗin ne kuwa. Ɗagawa yay batare da yay magana ba, daga can RK ya ce, “Ajwaad!”.
Ƙasa magana AA yayi, sai da ƙyar ya ce, “Uhmm”.
“Babu dai wata matsala ko?”.
Nan ma ya daɗe kafin ya iya furta, “Akwai, bata numfashi sam. Nima kaina da cikina na ciw....”
Ya kasa ƙarasawa saboda kansa dake kamar ana bugawa da wani ƙarfe.
“Wannan sakamakon dama shi nake tsoratar maka tun jiya. Yanzu dai bara muyi salla gani nan zuwa gidan”.
“Uhmm”.
Kawai yace ya kife wayar batare daya yanke kiran ba, sai RK ɗinne ya yanke daga can. Duk yanda yake tunanin taimakawa Maanal bazai iya ba, ga salla ana ƙoƙarin shiga. Kuma har cikin ransa bazai iya kiran kowa ba. Dama ace cikin ƴan uwanta akwai wani ko Amaal zai iya sawa tazo ta taimaka mata. Baya son wasa da salla, dan haka ya tashi ya gabatar da ita a zaune. Yana zaune ya jingina da gadon idanunsa a lumshe sai dai bai rufesu ba duka yana ɗan kallon Maanal kiran RK ya sake shigowa wayar. Hannu kawai ya kai ya ɗauka, yana ɗagawa RK ya ce, “Zaka iya buɗe ƙofar?”.
“Ko sakkowa bazan iya ba”.
“Okay ina zuwa, bari na samo keys wajen Aunty. Ka ɗan daure kaɗan saka mata kaya masu kauri, dan zamu shigo ne koda Aunty haka”.
“No! Rafeeq kar kai min haka Please ”.
“Dole ne ayi hakan Ajwaad, dole ne laifin da kowa ke kallonka da shi na tsawon shekaru ya shafe a yau....”
Kafin AA ɗin ya sake magana ma RK ya yanke wayar. Idanunsa ya lumshe tare da cije lips da ƙarfi. Fahimtar babu wani isasshen lokaci ya sashi mikewa cike da ƙarfin hali, closet ɗinta ya nufa, ya samo riga mai kauri sai dai ba wadda zata dameta ba ya fito. Sai da ya ɗan zauna kansa ya lafa kafin ya iya saka mata rigar da ƙyar, ya tattare gashinta dake a baje ya tufke waje guda. Bargon ya sake ja ya rufa mata ya maida hannunsa a goshinsa ya dafe kansa yana kallonta da idanunsa da suka canja launi gaba ɗaya....
★Kai tsaye RK sashen Oum ya nufa. Ƙofar a buɗe take, dan haka ya shiga kawai. Babu kowa a falon ƙasan amma yana jiyo motsin su Mah-mah dake a bedrooms ɗin. Ɗan jimmm yay na tunanin wazai samu, sai Umma ta faɗo masa, tunda koba komai a yanzu tamkar itace uwa a family ɗin kasancewarta matar Baba Sardauna dake matsayin uba. Wayarsa ya ciro a aljihu yay kiran layinta. Sai da ta kusa tsinkewa ta ɗauka, gaisheta yay, a ɗan rikice ta amsa tana tambayarsa lafiya dai ko kira da asuba yace ba komai gashi a falo ne...
Baima gama sauke wayar ba ƙofar bedroom ɗin tsakkiya ta buɗe. Umma ta fito sanye da zabgegen hijjabi idonta akan RK. Yanda take sauri kamar hijjabin zai taɗeta ta faɗi ya sashi saurin tararta yana faɗin, “Umma relax ba wani abu bane ba fa”.
“Ka tayar min da hankali Rafeeq mike faruwa?”.
Hannunta ya riƙo ya ce, “Kwantar da hankalinki. Nace babu komai fa. Dama su Ajwaad ne ke buƙatar taimako, dan akwai matsala. Yanzu haka ma nace ya buɗan ƙofa ga doctor nan zata zo amma bazai iya sakkowa daga sama ba dan shima bashi da lafiya. Ita kuma ta suma”.
Yanda RK yay maganar kansa a ƙasa yasa Umma tsohuwar arziƙi ta fahimci komai, sai dai kuma zuciyarta ta shiga wasiwasi. Amma batace komai ba tace kawai “Muje”.
Kansa ya jinjina mata, sai kuma yace, “Bara na amsa key wajen Aunty ya kulle ne”. Zama Umma tayi, shi kuma ya haura sama. Kai tsaye bedroom ɗin Oum yay knocking, Hajiya Basariyya tazo ta buɗe. Ganin shine sai tai wani shock. “Rafeeq lafiya kuwa?”.
“Lafiya lau Aunty, zan amsa key ɗin sashen Ajwaad ne”.
“Key! Wani abu ya faru ne?”.
Kafin ya bata amsa Oum tazo wajen jin an ambaci sunan AA. Ganin Rafeeq kuma sai ya sake rikita ta. Ta ce, “Majdiya bashi hanya ya shigo”. Shiga RK yayi, Oum da duk take a rikice tace, “Rafeeq miya faru da su Ajwaad ɗin ake neman key?”.
“Babu abinda ya faru Aunty ku kwantar da hankalinku. Ya kulle ƙofar ne kuma bazai iya sakkowa ya buɗe ba. Shi da Maanal ɗin kuma duk suna buƙatar taimako”.
Daga Hajiya Majdiya har Oum shiru sukai suna kallon RK cike da nazari, sai kuma suka kalla juna. Oum ce tai ƙarfin halin faɗin, “Bara na ɗauka maka”.
Hajiya Majdiya kuwa sai ta jeho masa tambaya. “Rafeeq mike damun su?”.
Kafin ya bata amsa nan ma Oum ta dawo, key ɗin ta miƙa masa. Sai kawai ya juya ya fice dan ana kiran wayarsa ya kuma san doctor ce. Yana gama sakkowa Umma dake falo na jiransa ta miƙe, a tare suka fito, Umma ta nufi sashen AA shi kuma ya nufi motar Doctor dan ya faɗama maigadi daman ya buɗe mata. Tana hangosa itama ta fito. Mace ce babba dan zata iya kaiwa ma sa'ar su Oum, ya gaidata da girmamawa sannan suma suka nufi sashen AA ɗin da har Umma ta buɗe ta shige.
A falo suka samu Umma tsaye, Doctor Ruƙayya ta gaida Umma cike da girmamawa, itama ta amsa da kulawa tana mata godiyar tasota da akai da sassafe haka. Dan gari ya fara haske zuwa yanzu. Wayar AA RK ya sake kira, yana ɗagawa ya ce, “Gani tare da Umma da Doctor. Ka koma wani ɗakin zan sameka su sai su dubata”.
“Uhmm”.
AA ya faɗa a ƙasan maƙoshi. Har ya yunƙura zai miƙe sai kuma ya ɗan matsa ya sumbaci goshin Maanal da lips ɗinta. Murya a shaƙe ya furta, “I'm sorry Bestie. Please for give me. You bloomed in my childhood, and you rule in my forever, my sweet Everbloom. ALLAH yay miki albarka. Yay miki sakamako da mukullin aljanna, ya shayar dake farin ciki na har abada fiye da wanda kika shayar da ni a daren jiya. ALLAH ya hanani ikon munana miki har abada”. Ya sake sumbatar lips nata a hankali sannan ya miƙe da ƙyar. Fita yay yana waiwayenta, shi kaɗai yasan irin nauyin da yake ji zuciyarsa ta masa. Sosai yake jin haushin kansa. Ɗakinsa ya buɗe ya shiga, dai-dai nan su RK ke haurowa, sun kuma ji ƙarar rufe ƙofar da yayi. Sai duk suka fahimci shine, dan haka RK ya nufi can yana nuna musu ɗakin kusa dana AA ɗin. “Inaga tana nan Umma ku shiga. Bara na ganshi shima”.
Can ɗin suka shiga, shi kuma yay knocking ɗakin AA, fin sakan biyar kafin ya tura ya shiga. Wutar ɗakin da AA bai kunna ba ya kunna. Can ya hangosa a saman gado ya dunƙule waje ɗaya. Can ɗin ya ƙarasa, batare da yay magana ba ya zauna a kusa da shi. Hannunsa ya ɗauke a hankali daga saman cikinsa daya riƙe, ya maye gurbinsa da nashi ya ɗan danna wajen. Ai da ƙarfi AA ya wani cije lips yana sake matse idanunsa dan azaba.
“I'm sorry”.
RK ya faɗa a hankali. Kansa ya jinjina masa kawai, sai da yaƙi buɗe ido ya kallesa. RK ya ɗan girgiza kai da sake faɗin, “Kanka na ciwo. Kuma da alama akwai zazzaɓi tare da kai”.
Shi dai AA bai ce komai ba, shima RK bai damu ba. Sai ma wayarsa daya zaro a aljihu ya shiga kiran wayar Oum. Bugu biyu kuwa ta ɗaga. A taƙaice ya ce, “Please Aunty zamu samu ruwan lemon tsami da lipton?”.
Cikin sanyin murya mai nuna damuwa Oum ta ce, “Za'a samu Rafeeq yaya jikin nasu?”.
“Alhamdullah da sauƙi karfa ki damu. A ɗan haɗa da shayi mai kauri sosai cikin yaran nan wani ya kawo min”.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖7️⃣7️⃣
______________
.........Yana ajiye wayar ya tashi ya fara buɗe kit ɗin daya shigo da shi, wanda Doctor ce tazo masa da shi dan daya kirata ya sanar mata dukkan abinda yake buƙata. Drip ya fito da shi da allurai kusan kala uku, sai syringe guda biyu da kan allura. Allurai yayi a cikin ruwan AA na kallonsa ta ƙasan ido, sai dai zaka iya ɗauka barci ma yake. Amma azaba ce keta nuƙurƙusarsa. Ga sanyi yana ji har cikin cikinsa. Ga ciwon kai da zazzaɓi. Tsaf RK ya gama haɗa komai, ya miƙe yana hanging ruwan a jikin hanger daya ɗakko a closet ɗin AA ɗin akai knocking. Sai da ya ƙarasa sannan ya nufi ƙofar ya buɗe. A mamakinsa sai yaga Oum ce da kanta. Sai kawai ya matsa mata ta shiga, cikin sauri AA yaja filo ya saka a wajen tare duvet ya rufe jikinsa da bai gama dai-daita ba. Dan a kallo ɗaya zaka fahimci hakan kodan jallabiyar jikinsa mai ɗan santsi ce. Dariya RK ya danne kawai ya kauda kansa, wato shi aka raina sai ba'a rufe ba. Kayan hannun Oum daya amsa ya ajiye, ita kuma ta zauna kusa da AA tana kai hannunta saman kansa da duk jijiyiyin sukai raɗa-raɗa. Muryarta a sanyaye sosai ta ce, “Sannu kaji Auta?”.
Tab ɗin, ai ji AA yay kamar ya nutse dan kunya. A karo na farko na rayuwarsa ya kasa buɗe idanu ya kalli Oum. Itama ta fahimci yanayin nasa amma sai ta shareshi. Hannunta ya riƙe cikin nashi, idanun nasa still a rufe murya can ciki ya ce, “Oum ina kwana”.
“Lafiya lau! Ya jikin naka?”.
Kasa amsawa yayi, RK dai yay murmushi. Ruwan lemon tsami da lipton ɗin ya zuba masa a kofi yana faɗin, “Tashi kasha wannan sai ka sha tea ɗin musa drip ɗin”.
Ƙasa motsawa AA yay sai da RK ya taimaka masa, da jikin gadon ya jingina shi, sai lokacin ya ɗan buɗe idonsa dake jajur ya ɗan kallesa, RK ya ɗage masa gira ɗaya. Harararsa AA yay ya amshi kofin kawai. RK yay dariya da faɗin, “Ka dai ji da shi, kana halin ciwo kana masifa da idanu”.
Murmushi Oum tai da faɗin, “ALLAH Rafeeq kai ke ja Auta na ƙin yin uba dakai, dan uban banza ne anan”.
“Aunty dama ai baƙya ƙi goya masa baya ba, amma wannan yaron da kike gani baida kunya, ba komai zan daina masa dariya”.
Harararsa AA ya sake yi. RK ya kwashe da dariya ya ce, “Ka cigaba da hararata zan barka da ciwonka ne”.
Shi dai bai sake kulashi ba. Ya gama shan ruwan lemon tsamin ya miƙa masa kofin, tea ya sake miƙo masa. Amma sai ya girgiza kansa alamar bazai sha ba. “Aiko dole kasha wlhy, kuma yanzu nan dan so nake ya saka ka amai. Hakan ne kawai zai bamu abinda muke so a tare da kai”.
Lallashin AA Oum ta shiga yi, saboda ita ya daure ya sha fin rabi, aiko kamar yanda RK ya faɗa sai amai ya fara taso masa, da sauri ya kamashi suka wuce bayi. Sosai yayi sa har kamar zai amayar da Kayan cikinsa. RK ya taimaka masa ya wanke fuskarsa da bakinsa suka fito. Sannu Oum keta jera masa cikin damuwa. Shi ko ya wani riƙe mata hannu kamar yaron da bai son gusawa daga jikin mamansa. A haka aka ɗaura ruwan bayan ya masa allurai biyu a hannun ya kumayi biyu a cikin ruwan... Kamar jira barci yay awan gaba da shi cikin sakanni......
★A ɓangaren su Umma suna shiga suma kan Maanal sukayi, hankalin Umma ya tashi sosai ganin yarinyar mutane a sume. Sai da doctor tace ta kwantar da hankalinta zata farfaɗo sannan. Amma a hakan ma sai faɗa take akan wautar yaran zamani. Wane irin abu ne ka kama yarinya har sai ta suma kamar abin cin rabo. Haba ai rashin tausayin yayi yawa. Yarinyar ma da ba budurwa ba ai mata irin wannan wahalarwar haka, to da virgin ɗin take kuma sai yaya.
Doctor dai dake shafama Maanal ruwa a fuska ta kuma warware gashinta tana zuba mata a cikin kan ta ce, “Ai sai dai haƙuri Mama, yaran yanzu sam basa saurare. Kawai su a rana ɗaya suke buƙatar yin komai, haka muke ta fama da cases ɗin nan na amare a daren farko. Amma ta taɓa aure ne naji kina faɗin ba budurwa ba”.
“Bata taɓa aure ba, ƙaddara ce ta gitta tsakaninta da shi tun suna yara dai”.
Doctor ta fahimci mi Umma ke nufi, amma sai tai mamaki a ranta. Kafin kuma tayi magana Maanal tai wata irin zabura alamar farfaɗowa. Da sauri Doctor ta riƙeta, sai kuma ta sake watsa mata ruwa a fuska. A firgice ta saki ƙara, muryarta a matuƙar dusashe dan ko fita batayi ta shiga roƙo da magiyar AA ya barta, Oum da Ammie suzo su taimaketa, saboda ta suma ne a wannan yanayin na kuka da kiran sunayen dangi🤭 shiyyasa ta farka da abin. Da ƙyar Doctor ta iya rungumeta cike da lallashi da kulawa ta ce, “Relax my baby, ba Ajwaad bane nice. Kwantar da hankalinki ai ya barki, babu kuma abinda zai sake miki okay”.
A cikin kunne take mata maganar, dan haka ta shiga sauke ajiyar zuciya masu ƙarfi ga hawaye na zuba kamar an buɗe fanfo (Su Hajiya Maanal ke da kikace babu ma wani wuya🤣). Shafa bayanta Doctor ta cigaba da yi a hankali a hankali har sai da ta nutsu sannan. Gaba ɗaya tausayin Maanal ya rufe Umma, ta gama ɗaukar alwashin sai taci mutuncin Ajwaad yau ɗin nan basai gobe ba. Kwantar da ita doctor tayi ta nufi bayi ta