AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   158 / 213

471K to 474K   out of 636.6K words

ta labarta masa komai. Dariyar mugunta yayi da faɗin, “Ai na daɗe da gane shegiyar matar ƙanin nan naki mayyar kuɗi ce. Shashasha kafin ƴaƴan nata su gama haihuwa mazan nasu su mutu ni na gama tatikesu tas. Dan sai na ƙarar da abinda kamila ta tara kaf ta koma amso na ƴaƴan nata tana tura min, ƙarshe ta fara satar na mijinta shima dan ubana ma nada haƙƙi a ciki ai....” sai kuma ya wani kwashe da dariya cike da mugunta. Hajiya Turai na tayashi. Dama Haule ta kira shi ta gaya masa komai na zancen ciki da faɗuwar Mamy yanzu babu jimawa....

_______★

       Barci Babban Yaya ya bar Ameerah nayi, dan haka bata san wainar da ake toyawa ba sai kusan sha ɗaya ta farka. Wani irin zazzaɓi take ji a jikinta, ga ciwo da ko'ina ke mata. Tunda taga babu Babban Yaya a ɗakin tasan ya fita ne. Sai dai akwai wayarsa ɗaya ajiye bed side drawer. Cikin dauriya ta ɗan kintsa ɗakin ta shiga bayi tai wanka ta sake gasa jikinta yanda taga yayi mata ɗazun. Sai kuma cikin ikon ALLAH taga maganin da Mommy ta dinga dafama Maanal tana sit bath. Tunanin itama tayi amfani da shi ne yazo mata. Dan haka koda ta fito a wankan sai ta zura dogon hijjab ta ɗauka ɗauri ɗaya ta fito cike da dauriya domin dafawa a kitchen. Gida cike da mutane ai bataso a shigo a ganta tana wannan tafiyar gwale-gwalen ba. Sannan ai ya kamata ta fita ta gaida su Oum amma take a haka ai da kunya. Dan duk wanda ya ganta ALLAH sai ya gane abinda ya faru. Ga idanu a kumbure tasha kuka. A bisa tsautsayi ta fito ɗin ne tana shiga kitchen taji wayar da Hajiya Turai keyi, kuma tas taji abinda ta maimaita ma wanda suke wayar da Nana ta faɗa. Mamakin duniya ya zagaye zuciyar Ameerah. Gabanta ko sai faɗuwa yake. Da sauri ta baro kitchen ɗin ta koma ɗakinta zuciyarta na kai-kawo da fasa maganganun dalla-dalla. Tofa babbar magana, shin Maman kishiyar tata ba uwa ɗaya uba ɗaya suke da Mamy bane? Kamar dai haka ta sani tun tuni. To kenan akwai wata a tsakaninsu kokuma AJIYA A DUHU Maman Saheeban keyi batare da sanin Mamy ba. Wato su bazasu haihu ba sai ƴaƴanta kawai. Turƙashi. Eh lallai tasan yau ta shigo family house aure kam. To lallai akwai tsallen baɗake kenan. ALLAH sarki Maanal ashe ciki gareta, ta tayata murna sosai ita da Yaya AA, kuma sai inda ƙarfinta ya ƙare wajen kare cikin nan. Za kuma ta sanya ido akan su Saheeba ƙwarai d gaske..........✍️
    

Tofa, sabon wasa kenan tsakanin su Saheeba da Ameerah 🥱😂



*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣2️⃣1️⃣


______________


.........Turo ƙofar da akai ya katse mata tunaninta. Ta ɗago tana kallonsa. Shima dai kallonta yake cike da wani yanayi mai sanyi. Sai kuma ya cigaba da takowa a hankali zuwa inda take. Zama yay kusa da ita ya sanyata a jikinsa cike da kulawa ya ce, “Kin tashi?”.
     Kanta ta jinjina masa kawai, dan bata jin ma yin magana sam. Zafin da yaji a jikinta ya sashi faɗin, “Ya salam zazzaɓi ne jikinki haka? Aiko bara na kira Uncle Rafeeq ya duba ki”.
    Ganin duk yanda ya rikice ta riƙo hannunsa tana ɗan girgiza masa kai. Cike da shagwaɓa da disa-sashshiyar muryar ta ta ce, “Bafa sosai bane zan warke baga maganin daka bani ba ɗazun zan ƙara sha Yaya”.
      “Bazai yiwu ba Ameerah”.
Babban Yaya ya faɗa yana ɗaukar wayarsa. Layin RK ya kira. Lokacin suna fitowa shi da Fawzan daga sashen Oum saboda dangin Mamy da sai yanzu ne zasu wuce. RK ya ɗaga, babu wasa a muryar babban Yaya yace ya tura masa likita zata suba Ameerah bata da lafiya. Jimm RK yayi, sai kuma ya danne dariyarsa da ƙyar yace, “Okay bara na bincika wake asibiti a yanzu cikin matan, ALLAH ya bata lafiya”.
Da Amin babban Yaya ya amsa.
   Yana katse wayar suka kalli juna shi da Yaya Fawzan. “Babban ɗa fa yayi aika-aika da alama”.
        “A haba dai?”.
Cewar Yaya Fawzan.
RK ya ce, “Gashi ya kira a nemi likita amarya babu lafiya, sai dakewa yake bai san na harbosa ba. Wai kai dan ƙaniyarka ma mika zauna jira ne ana hayya-hayya kai kana nan gulma a cikin gida”.
     Fawzan da dariyar Babban Yaya ke cinsa ya ce, “Oh mudai munga takanmu ALLAH ya bamu kawun banza. Haba shiyyasa naga Babban Yaya ya kasa zama hankalinsa duk yana can ashe yasan yabi dare kai jama'a girma yayi tangal-tangal”
     Dariya shima RK ɗin yake yi, ya ce, “Kaima fa a ne wlhy Son. Amma ba komai zuwa zan na haɗe kai da Ajwaad kaima mu maka tas gobe. Sai muga yaya naka girman zai yi tangal-tangal ɗin kaima”.
      “Karen hauka ya cizan kusan nayi, ai nasan Auta ma wannan shiru-shirun da yake jirace yake dani munafukin, shiyyasa ɗaukarta zan mubar gidan, gara muje honeymoon ma dawo muku da result”.
     Kiran wayar da akai ta hana RK bashi amsa ya danne dariyarsa da ƙyar ya daga kiran ya fara magana. Dai-dai nan kuma Najma ke fitowa daga sashensu ita da su Lailah zasu rakata gaida su Oum daga nan ta duba Maanal dan har an baza mata labari. Gaba ɗaya hankalinsa ya koma kanta. Tayi wani shegen ƙyau daka ganta kaga amarya. Ya zubama lips ɗin daya gama morewa ɗazun da safe idanu. Haɗa ido da sukai da Najma ya sata duƙar da kai cike da kunyar abinda yay mata da safen itama, sai take jin kamar kowa idan ya kalleta zai gane ne. Kanta a ƙasa ta ƙaraso inda suke ta gaida RK cike da girmamawa. Kamar ba shi ba ya wani dake yana amsawa da kulawa. Ta ɗan kalli Fawzan ƙasa-ƙasa tace “Sannu Yaya”.
      Shima ƙasa-ƙasan ya ce, “Yauwa sannu ƙanwa”.
     Kallonsa RK yayi baki buɗe. Fawzan ya hararesa. Sai kuma ya maida kallonsa ga Najma, “Je ki dubasu wajen akwai zafin rana”.
     Kanta ta jinjina a kunyace ta wuce. RK yace, “Eh lallai yau naga bariki, bafa Ajwaad bane kawai ƙwallo a gidan nan kowa kwar-kwar ɗin kansa ne na lura”.
      “Ai karatunku muke bi kaida Yayunka su Abah. Idan bamu zama kwar-kwar ɗin ba zamu ƙara muku yawa ne. Ka jimin sa ido, kai mafa ko ɗaga ƙafa babu mukaga Aunty Nuwaira na amaye-amaye ga ƙaninmu nan na shiga wata na shida a ciki”.
         “Oh, nima iskancin zaka min to nayi nan”. Dariya Fawzan ya sanya. Cikin ɗan ɗaga murya yace, “Ai yau kaima sai kaji a jikinka bari dai Auta ya gama jiyyar ya fito”.
     RK dake shigewa sashen Abah ya ce, “Idan kun ganni kenan”. Ya ƙarasa shigewa....


________★

        Su Ammie sun iso Kaduna lafiya. Sadda suke isowa gida sun sami ƴan sanda na jiransu. Hajiya Yaya kuma ta farfaɗo an sakata barci dan jininta daya haura ya sauka. Sai da suka fara zuwa suka dubata yaran sukai musu bayanin iya abinda suka sani suma ganin ɗakin Hajiya Yayan kaca-kaca yasa babban ɗan sandan faɗin suma ya kamata su duba sashensu duka ko za'a samu wani abu. Dan maigadi ma dai an bugar da shi ne har yanzu barci yake. Likita kuma daya dubashi ya tabbatar musu tun kusan takwas na dare aka bugar da shi ɗin.
    Al'amarin ya sake bama Daddy da su Ammie mamaki. Badai suce komai ba kowa ya nufi sashensa dan dubawa. Hajiya Basariyya ce ta fara fitowa a haukace tana kuka da ihun ta shiga uku an yashe mata komai. Babu abinda aka bar mata kaddararta sai sutura. Sai ga Daddy ma ya fito a rikice. Yace ai shima komai an yashe, takardunsa da duk wani abu mai muhimmanci babu shi. Dama su Amrah sun faɗa musu na sashensu duk an tattare suma. Fitowar Ammie tace ita gaskiya ba'a ma shiga ba dan komai yana a yanda yake yasa Hajiya Basariyya dake kuka riris sake fasa ihun tashin hankali. Yanda take kuka da ihu sai da abin ya bama kowa mamaki, can kuma sai gata ta zube a ƙasa babu numfashi babu alamarsa. Babbar magana, babu shiri su Ammie sukai kanta, yara suka kawo ruwa aka zuba mata ta kawo numfashi, sai ta hau sambatu kamar wadda kan ya taɓu. Faɗi take shike nan an talauta su, ita babu Daddy babu, miyasa ita Ammie ba'a ɗiba nata ba. Ƙilama itace ta saka aka kwashe musu.....
     Wata gigitacciyar tsawa Daddy ya daka mata. Cikin matuƙar faɗa ya ce, “Halan kin haukace ne Basariyya? Matar tawa kike jifa da wannan mummunan aiki. To ki iya bakinki idan ba hakaba wlhy zakiyi kuka biyu shashasha kawai da bata da girma sai na jiki”.
       Yanda yake faɗan sai da kowa ya nutsu, sai Ammien ce ke lallashinsa ma da ido. Amma yaƙi kulata itama dan harga ALLAH yaji matuƙar haushin kalaman Hajiya Basariyya. Ko ina ƴan sanda saida suka shiga, suka ga komai daya faru sukai hotuna da aune-aune dan a bincika ko za'a samu hoton yatsu. Duk wannan bidiri da akeyi babu Nazeerah babu Yaya Yazeed. Suna sashensu kamar ma basa gidan. Hajiya Basariyya dake a birkice dan sai kika take ta ce, “Wlhy bazan yarda ba, a binciki matar Yazeed, mudai itace baƙuwa a gidan nan, yaranmu duk mun san halinsu”.
     Kallonta Ammie da Daddy sukayi, sai kuma suka kalli hanyar sashen Yazeed ɗin. Salima ta ce, “ALLAH Ummi nima nayi wanan tunanin, kuma fa tun ɗazun duk ihun kukan da muke ko leƙe bata fito ba, dama shi Yaya sai ta bashi umarni zai yarda ya fito”. Ta share hawayenta. Da yake yaran suma babu wadda suka tsana yanzu a duniya irin Nazeerah ɗin duk sai suka goyi bayan zancen Hajiya Basariyya. Ɗan sanda yace, “Waye Yazeed ɗin wacece Nazeerah?”.
        Daddy ya gyara tsaiwarsa da faɗin, “Yarona dai daka sani, ita kuma matarsa ce”.
       “A to ya kamata su fito, munata kai-kawo tun ɗazun sunyi shiru, ni nama zata yaran nan ne kawai a gidan ai Alhaji. Kai kofur Hamza yi musu knocking”.
      Wanda aka kira da kofur Hamza ya amsa da faɗin, “Yea sir”. Yana nufar sashen Yaya Yazeed.
     Knocking yayi har sau fin biyar sannan aka buɗe a fusace. Nazeerah zata fara bala'i taci karo da kofur Hamza. Dama fuskar marasa mutunci ce da shi ai da gudu ta haɗiye abinda tai niyyar faɗa. Sai dai cikin ƙarfin hali tace, “Lafiya”.
      “Lafiyar ce ta kawo haka, ku fito ke da mijinki ana nemanku”.
    Ɗan jimmm tayi, sai kuma ta saki ƙofar tana faɗin, “Yana ciki bari na kirashi”.
          “Basai kin koma ba kirashi daga nan inda kike”.
    Rasa yanda zata yi tai, gashi sai mazurai yake mata. Dole ta ɗaga murya daga nan ta ƙwalama Yaya Yazeed kira. Sai ko gashi ya fito da saurinsa daga kitchen, da alama girki yake mata. Mamaki ya kusa halaka kofur Hamza, ganin har ɗan duƙawa Yazeed yay yace mata “Gani”.
        Batayi magana ba ta fito, sai shima kofur Hamza ɗin yace masa ya fito. Amma Yazeed yay tsaye yana kallon Nazeerah. Dan in batace ya fito ba bazai fito ba. Kofur Hamza ya sake jinjina kai yana gaskata maganar yaran can, kai wannan koba ita ta aikata ba itace ta saka aka aikata dole. Tsawa yay mata, tai tsalle gefe tana tura baki gaba ga ciki tirtsi-tirtsi. Ta kalla Yaya Yazeed tana kumbura baki ta ce, “Malam ka fito fa akace”. Ai a zabure ya fito kuwa. Sai Kofur Hamza ya sake mutuwa a tsaye a ransa yana ayyana (Kaga mata ƴan wuta ƙuru-ƙuru tun a duniya. Yo wannan ta mutu a haka ai tasan makoma itama). Haka dai ya tasasu a gaba har inda su Daddy suke. Babu wanda Yazeed ya gaida yana tsaye a gefen Nazeerah. Itama kuma bata gaida kowa ba. Daddy ya girgiza kansa zuciyarsa na masa zafi sosai. Ammie kam ƙwalla ne suka cika mata ido ranta fal tausayin Yazeed da Hajiya Yaya.........✍️
    




*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*




*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣2️⃣2️⃣


______________



........Tambayoyi ƴan sandan suka fara musu. Sai dai Yazeed baya amsawa sai Nazeerah. Sai da kofur Hamza yace, “Idan bata bashi umarni ba bazai taɓa magana ba fa sir.”
     Mamaki ya kama ogansu, ya kalla Daddy. Sai kawai Daddy ya ɗauke kansa. Ya fahimta, dan haka baiyi magana ba yay shiru. Cigaba yay dama Nazeerah tambayoyi, tana bashi amsa kai tsaye cike da rashin kunya. Bai dai kula ta ba ya gama tattara bayanan. Yacema Daddy zasuje anjima idan Hajiya Yaya ta tashi zasu dawo. Su kwantar da hankalinsu koma wanene in sha ALLAHU za'a kamashi, dan duk yanda akai yana da alaƙa da su yasan sirrinsu ne natuƙa.
        Addu'a su Daddy sukayi da godiya. Ƴan sandan suka wuce suka barsu jigun-jigun, sai shashshekar kukan Hajiya Basariyya. Babu abinda take hangowa sai gwalwagwalnta dana yaranta da takardun filayenta. Da farko Nazeerah bata ɗauki abun wani serious ba. Sai da Baban su Hajiya Yaya da Yayanta da Baban su Najma suka iso gidan sannan ta fahimci al'amarin fa babbane. Sashen ta ta koma tai kiran Mamanta Sabuwa tana labarta mata abinda gidan nasu ke ciki. Itama Sabuwar hankalinta ne ya tashi. Yo an tattare dukiyar gida gaba ɗaya su kuma minene ribar wahalarsu. Yau sunga ɓuturewa. A rikice ta katse wayar ta kira mijinta tana sanar masa. Munafukin sai ya nuna ya fita rikicewa ma. A birkice yace masa ta sameshi a gidan Chalawan shi yayi gaba ma. Haka kuwa ta yayibi hijjab ta fice dan harga ALLAH a rikice take jinta. Yo duk fa wannan wahalar tasu da kasa zama waje ɗaya da bin malamai da bokaye akan dukiyar ne dai fa. Idan babu ita ai babu magana. Suda suke jira kawai Nazeerah ta sauka lafiya suga mi aka samu. Dan tsoron ma kar ace masu mace ce ya hanata ɗaukar Nazeerah suje a duba musu. Sai kuma suji wanan ɗanyen aikin da rana tsaka haka ai basuga ta zama ba kam gaskiya.....

________★

        A hankali Maanal ke buɗe idanunta. Tuni ruwan da aka saka mata ya ƙare an cire shi. Barcinta kawai take a jikin AA shi kuma yanata aikin danna waya da kallonta. Mamy ma dai barcin wahala yay gaba da ita tun ɗazun bayan ta gama kwasar takaicin hirar su RK. Sai dai yanzu kamar abin almara Maanal na farkawa itama ta farka. Sai dai batai motsi yanda zasu fahimta. Su kaɗai ne a ɗakin dan ƴan Kano ma dai shiri suke yau zasu wuce. Jirgin yamma zasu bi shiyyasa. Yanzu babu jimawa ƴan Katsina daga gidan Hajiya Shuwa suka shigo sukai musu sallama suka duba Maanal da Mamy.
      Luuu Maanal ta buɗe idanun ta tana kallon AA da shima yake kallonta, sai kuma ta sake lumshesu. Tsahon sakanni sannan ta sake buɗewa dai still a kansa. Kallon juna suke da wani irin shauƙi da kwanciyar hankali, kafin AA ya motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, “Kin tashi?”.
       Idanun ta sake lumshewa ta buɗe masa alamar amsawar kenan. Sai kuma ta motsa lips ɗinta kaɗan ta ce, “Bestie”.
       “Na'am zuciyar Ajwaad”.
     Ya faɗa a cikin raɗa sosai yana riƙe fuskarta a cikin tafukan hannunsa. Idanunsa na ƙara narkewa a kanta. “Yaya jikin?”.
       “Ni lafiyata ƙalau, kawai ƙamshin wancan abun ne bana so”. Ta faɗa fuska a yamutse kamar yanzu ne take jin ƙamshin naman.
     Shima fuskar tasa ya ɗan ɓata cike da tausayinta ya ce, “I'm sorry, bazaki sake jinsa ba in sha ALLAH a gidan nan Besty. Ko ɗanyanesa bazaki ƙara gani ba balle dafaffe har sai in ke kika buƙata”.
     Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi, sai kace wadda akama albishir da wani babban abu. Shi ko yana kallonta a narke matuƙa. Karo na farko ta kai hannunta ta shafa kwantaccen gashin sajensa. Idanunta na lumshewa da buɗewa ta ce, “Miyasa kake kallona haka? Idanunka kuma kamar kayi kuka kodan banda lafiya ne?”.
       Inda Mamy take ya ɗan kalla, ganin har yanzu tana a yanda take ya sake maido idanunsa kan Maanal ɗin, sai kuma ya duƙo ya sumbaci lips ɗinta kaɗan. “Ina kallonki ne saboda kece duniyata Besty. Kece farin cikina, kece ƙaunata. You're my everything Maanal. Besty kin bani wata ƙyauta da ban san me zan saka miki da ita ba, sai dai in ce miki ki yarda dani, ki barni in koya zama UBA daga yau. Zan raine ku a hankali da ƙauna da dukkan kulawa, da addu'a da ƙarfina da dukkan abinda na mallaka. Manaal ina kaunar ki fiye da yanda baki bazai iya furtawa ba. Yanzu ku biyu ne a raina. Zan kare ku kamar yanda ake kare farar fata daga

158 / 213

Chapters