AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   208 / 213

621K to 624K   out of 636.6K words

ya saka aka sakan kema wlhy sai ya sake ki sannan zan bada yaran nan”.
       Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, wlhy kan Maanal neman bugawa yake yi. Ga cikinta na zafi, kanta na juya mata alamar jininta ya haura sama. Yuuuu duhu ya fara mamayeta,  kawai sai jinta sukai ƙasa yiffff. Ai Alhaji AA ne ya fara zabura kanta, sai Abah da Oum.
     Shima Yaya Fawzan da Babban Yaya suka sanya salati. Da wannan damar RK ya fara jan ra'ayin Nibras da baƙar magana. Aiko sai hankalinta ya rabu biyu, kan Maanal da Yaya Fawzan ya ɗakko ruwa za'a zubawa, da RK da take zagin, babban Yaya na matsawa a hankali a hankali har ya zo bayanta, a bazata ya damƙe yaran, ai ko sai ta shiga kokawa da shi, shima bai san ya wanke mata fuska da mari ba, babu arziƙi ta saki yaran, dai-dai AA na miƙewa ya maida Maanal jikin Oum sai ihun Nibras kawai suka ji ya wani ɗauketa da mari. Hankalin RK da Babban Yaya nakan yaran, Yaya Fawzan da su Oum na kan Maanal, su Umma na ƙasa, ai ko ALLAH ya sake bama AA dama yajata ƙiyyy yay kitchen da ita, ihu take na neman ceto, dai-dai nan sauran mazan suka nufoshi dan amsarta kawai ya danna ƙofar kitchen ɗin ya saka key. Ya kuwa ɗora daga inda ya tsaya a jibgar Nibras.
Gaba ɗaya hankalin kowa ya ƙara tashi, wasu suna dukan ƙofa ana kiran sunan AA kar ya kasheta ya saka kansa a masifa amma ina baya ma ji........✍️209



...........Tun suna jiyo kukan Nibras har suka bari, sai da ya sumar da ita sannan ya buɗe ƙofar ya jawota ƙeyyyy kamar kayan wanki, duk wanda yazo zai tareshi kawai sai dai ta hankaɗa shi gefe, sai dai kaji mutum teemmm a ƙasa. Dai-dai inda ta tsaya dasu twin's yazo kawai ya ɗagata cak ya wantsala ta tayi ƙasan down stairs, dan kwashe mata ƙafafu AA yay ya hankaɗata ta wajen. Gigitaccen ihun data saka ne ya farfaɗo da Maanal, gaba ɗaya suma suka miƙe akai kan AA wasu na rige-rigen sauka downstairs.
      Shiko ko a jikinsa sai ma wani irin zubewa da yay zaune ya jingina da glass ɗin wajen ya zauna kansa a duƙe irin na matsanancin mutum a baƙar zuciyar nan kawai sai ga hawaye. AA fa akwai zuciya ta bala'i, kawai idan baka taɓo abinda zakaga zuciyar bane ba sai ka ɗauka mai rangwame ne miskilancin kawai ya iya.
          Da gudu Maanal data zabura tayi wajen, ta inda yake tazo ta leƙa ƙasan, sai kuma ta ɗago ganin Nibras wanwar a downstairs ɗin, kodan idonta a birkice suke bama ta gane akan mi Nibras ɗin ta faɗa ba, zabura tai zata bar wajen AA ya riƙe hannunta batare daya ɗago ba. Tai ƙoƙarin fisgewa kawai ya fisgota ta faɗa jikinsa. Sai kawai ya ƙanƙameta....

     A downstairs kam tuni su Umma sun kai ƙasa. Hajiya Majdiya ta saka yatsarta a hancin Nibras da sam bata numfashi. A ruɗe ta ɗago, dai-dai itama Mah-mah na saka hannunta a wuyan Nibras ɗin. Ta ce, “Da ranta suma tayi ku bani ruwa.”.
     A guje aka kawo ruwa aka sheƙa mata, a gigice ta fasa wani ihu, sai kuma ta kasa cigaba saboda wahala da yanda illahirin jikinta ya amsa. Tabbas badan ALLAH ya taƙaita al'amarin akwai katifa da aka sanya ba babu abinda zai hana ɗayan biyu faruwa. Kodai Nibras ta mutu, ko ta karairaye, kota samu matsalar laka. A hankan ma wani gigitaccen ihu ta sake saki da aka motsata sai kuma tayi ɗiff alamar ta sake suma.
      A sama kam kowa hankalinsa nakan twins. Yaga kayan jikin su twins kawai Babban Yaya da Yaya Fawzan sukayi dan basu da haƙurin zaman cirewa. Suka shiga dudduba yaran RK da su Oum na tayasu, Muhammad ne yaji ciwo a hannu, shiyyasa kukansa ma yafi na Ahmad yau. RK dake ɗan matsa hannun yaran na sake saka kuka yace, “Yaji ciwo a hannu, bara na duba wake asibiti ta ɓangaren ƙashi sai yazo yanzu a duba su kar yay tsami”.
        Sai lokacin suka sakko ƙasa suma, dan falon sama bai kai girman na ƙasan ba yayi musu kaɗan. Mamy da a karo na farko taji wani irin nauyi a ƙirjinta tana zaune a wheelchiar ɗinta ta zubama Nibras idanu kawai, batace tana son su twins ba saboda daga jikin Maanal suka fito, amma wlhy jitai zuciyarta ta mata nauyi da abinda Nibras tai musu. Sanda AA ke magana cikin ƙarajin nan jininta tsitstsinkewa ya dinga yi, da gaske fa tana son AA, kai tana son yaranta ma fa, karo na farko zuciyarta motsawa take da shauƙi mai girma akansu dakan mahaifinsu da take ƙoƙarin ganin ta danne a tsakanin nan.
         A sama kuwa AA da Manaal ne kawai suka rage. Dan tunda ya jawota jikinsa ya matseta ya wani lumshe ido sai furzar da huci yake akai-akai kawai ya kife kansa a jikinta, itama bata da ƙarfin ƙwace kanta dan azabar da take ji a wajen cs ɗinta. Cikinta ma ya ƙulle. Babban Yaya na tsaye a hanyar benen dan in har suka bar wajen dukansu AA ya tashi ba suma ba ko mutuwa Nibras tayi kanta zai sake yi. Idanunsa idan ya buɗe sai in kana da juriya da jarumta ne zaka iya cigaba da kallonsu saboda yanda suka kaɗe suka juye gaba ɗaya. AA fa akwai masifar nacin faɗa, yanda kasan kurma haka yake a naci faɗansa baya mutuwa. Shiyasa ko zamanin Maanal ta takalo faɗa ya tafi ramako kwana da kwanaki yake yana bibiyar yaro shiyasa ake tsoron faɗansa...
      Nauyin da Maanal tai masa a jiki da wani irin fisga da numfashinta yayi ne ya ɗaga masa hankali, ya ɗagota da sauri yana kallon ta, ina ta sake sumewa fa, girgizata ya shiga yi yana kiran sunanta, hakan yasa babban Yaya matsowa da sauri inda suke, akan hannun Maanal idonsa ya fara sauka ta dafe wajen cs ɗinta har jini ya fasa kayan barcinta ya nuna a hannunta. Hankali tashe ya ce, “Jini kuma?”.
     Da sauri AA ya kallesa, babban yaya ya nuna masa hannun Maanal, cikin sauri ya kama hannun ya ɗaga, jinin ne kam tabbas, rigar ya janye jikinsa na ɓari, tabas wajen ne kuwa ke jini. Ai sai ya fasa ƙara sosai yana miƙewa da ita, su Oum na ƙoƙarin dawowa saman ya sauka da ita. Da sauri Babban Yaya dake biye dasu ya musu bayani.
    RK yace, “Ai kawai muje asibiti”.
  Ai kafin ma su fito AA ya saka Maanal a mota, ALLAH yaso key na hannun drivern Abah dan motarsa ce. A tsawace ya ƙwala kiran sunan Drivern, sai gashi da gudu dan su basu san mike faruwa ba. Gaba suka yi, aka bisu da su twins da Nibras. Sannan mazan ne kawai suka bisu ance matan su zauna tunda dare ne, duk da ma asuba ta gabato, dan kusan uku da arba'in lokacin. Haka suka haƙura dole badan sun so ba......

_________★

        Anan Kano kam rayuwa ta ladabtar da Huznah. Dan horon da Sageer yay mata yayi matuƙar tasiri a kanta, duk da shima dai ya wahalu kwarai da gaske saboda mutum ne mai yawan buƙata. Duk wanda yaga Huznah a yanzu dole ta bashi tausayi, ta canja matuƙar canjawa ta maida al'amarin ta ga UBANGIJI. Kullum cikin sallar dare take, karatun Alkur'ani da sadaka. Duk abinda Sageer ke so tana ƙoƙarin yi masa, duk wanda baya so tana ƙoƙarin kiyaye wa. Abubuwa da bata iya ba haka ta dinga binciken online class's tana shiga domin koya. Sai ga Huznah yanzu harda ƙulla ƙawance da maƙotamsu su Zubaidah. Yayar Zubaidah bata da matsala sam, haka ta amsheta hannu biyu bata nuna mata komai ba kuma data musu a baya. Sai ma ƙoƙarin jan Huznah take a jikinta kamar ƙanwarta.
    Ta canja alƙarta da ƴan gidansu gaba ɗaya. Ƙannensa su Khadijah da wanda ke gidan aure har wanda suke uba ɗaya yanzu jansu take a jikinta. Haka zatayi abinci duk juma'a yaji nama ko kifi ƙular Baba daban ƙular ƴan gidan daban taje ta yini ana wasa ana dariya tana taya surukan nata ayyuka duk da suna hanata sai yamma idan ya tashi aiki yaje ya ɗauketa su wuce gida. Yan Abuja ma haka take kiran Hajiya Yaya da Ammie ta gaishesu. Suma hakan yana saka su a farin ciki, dama tsakaninta da ƴan uwanta yanzu normal ne, har su Shahidah da Amaal kira take, har Manaal ma tama barka. Waɗan nan canje-canjen da Sageer ya gani a tare da ita ya sashi fara sakkowa shima. Da wannan damar tayi amfani wajen bashi haƙuri da neman gafararsa, tun tanayi baya tanka mata harya fahimci  da gasken take komai ya wuce. Sai kawai ya haƙura suka shirya, ranar dai taci ƙaniyarta a wajen maza, dan sai da ta gwammaci kiɗa da karatu. Kwana biyu yana biyan bashin sa tayi laushi sosai a hannunsa kafin ya ɗauketa sukaje shopping ya kaso musu kuɗaɗe ita da Fodio ɗinsa. Sannan yay mata batun aiki da aka samar mata. Farin cikin sosai tayi tana rungumesa. Yay murmushi da sumbatar kumatunta yana lakace hancin Fodio dake gefensu.
     “Babana kaga mamanka zata karyani ko”.
    Huznah tai murmushi da faɗin, “Babansa dai zai ƙare min ruwan jiki”.
“A to tunda haka ne zona ƙarasa ƙarar da shi sai muje asibiti a ƙara mana wani”.
    Zillewa tai tana dariya, sai da ta shige kitchen ta leƙo tai masa gwalo. Sassanyan murmushi ya saki yana mai lumshe idanu da buɗewa. Finally Huznah ta zama Sageer, Sageer ya zama Huznah. ALLAH ya cigaba da basu zaman lafiya da haƙuri da juna. A tsakanin nan kam har ya fusata aure zai ƙara amma yanzu ya haƙura. Babu batun kishiya, zai tsaya tsayin daka su gina rayuwarsu kodan mahaifiyarta tasan dan ka aurama ƴarka talaka ba shike nufin watarana bazasuyi arziƙin ba, ba shike nufin bazasu samu farin cikin rayuwa ba, ba shike nufin aurensu bashi da darajar kaiwa na auren kai kuɗi ba.
     Tun daga wannan lokacin farin ciki mai girma ya wanzu a gidan man Sageer. Matuƙar gatanta Huznah yake, da safe su shirya su tafi aiki tare bayan sun ajiye Fodio a gida wajen mamansu da abincinsa. Bayan sun taso su biyo su ɗaukesa su dawo gidansu, su raba dare suna kashe juna da soyayya da ƙauna. Basu zauna a haka ba ya fiddo musu hanyoyin kasuwanci, dan haka suka dinga sayen atamfofi, yadika, sarƙoƙin da takalma suna kaiwa wajen aikinsu, karshen wata idan an ɗauki albashi a haɗa musu kuɗinsu. Abin kamar wasa sai ga shi har da bags, veils, da wasu abubuwan ma duk suna kawowa. A'a basai suka fara planing buɗe shago ba anan anguwarsu koda ƙarami ne, aiko sai UBANGIJI ya sanya musu hannu shago ya tabbata. Kafin kace mi *_FODIO COLLECTION_* ya zama wani abu. Hakan ya saka Daddy farin ciki ya ƙara musu jari mai nauyi, sai kawai suka sake buɗe wani shagon ma da wajen kiwon kaji. Huznah kuma aka ɗan fara amaye-amaye. Hankalinta zai tashi ga yaro bata yaye ba man Sageer yace karta wani damu yana son kayansa. Dole itama ta kwantar da hankalinta, ta kuma fahimci ta samu cikin nan ne lokacin da suka shirya akan faɗansu ya dinga mata punishment. Abin ma sai ya dinga bata dariya, shi kansa data ɗakko masa labarin dariyar ya dinga yi da tsokanarta. Ta rungumeshi tana ɓoye fuskarta a jikinsa dan taji kunya..........✍️

      😂Haka duniya take dama. Huznah dai ta bamu kunya ta kanainaye man Sageer ɗinta. To wlhy ƴammata izna a gareku, Kinga auren talakan nan ko auren dole da kike ganin iyaye sun miki dan sun zaɓa miji, wulaƙanta namiji dan yazo gunki bashi da ko sisi ko gidansu bai kai naku gidan kuɗi ba, rufawa kanki asiri ki barma UBANGIJI zaɓi, wataran sai kiga komai tamkar mafarki kamar yanda Huznah ta gani a yau. Bada kuɗi kawai ake samun farin ciki ba. Bamu ce ki auri wanda baida abinyi ba, a'a wannan kuma ganganci ne hajiyata. Mai neman nakansa muke magana, ba ƴan zaman kan layi ana irga motoci ba da rantsuwar sai na sayi irinta nan gaba. Koda zaman kashe wandon zai sayi irintan ban sani ma ɗan ƙaniya ba. Duk abinda kikaga bai zo hannunki ba to ki yarda ba alkairi bane a gareki sai ki zauna lafiya. ALLAH ya tsaya mana akan dukkan al'amuran mu, talakan dai wataran shike zama Dangote 🥰🥰🥰😘👍.210



.......A nan Abuja kam tabbas al'amarin yaso ɓaci musamman a ɓangaren Maanal. Dan Doctors fin biyar ne a kanta harda RK, ƙarshe ma tun a daren RK ya kira Abbu ya sanar masa halin da ake ciki. Bawan ALLAH ga shekaru amma haka suka biyo hanyar Kano zuwa Abuja a mota dan ya bincika jirgi sai kusan 12 ma zai tashi zuwa Abujan. Ai ko sai gashi 7:30 a cikin asibitin tai masa. Zuwan Abbun ya sake tabbatar ma da su Abah al'amari fa babba ne. Shiyyasa a rayuwa taurin kai ma baida amfani wani lokacin, maybe da AA ya amsa kawai yana son yarinyar nan tunda sun san ba haka bane ba su da ba'akai haka ba, amma gashi nan sanadin hakan yana neman rasa Maanal ɗin. Sai kuma da suka kalleshi sai ya basu tausayi, dan ya zauna ne kawai shiru kansa a kife a kafaɗar Uncle Hussain idanunsa a rufe. Shi kaɗai yasan a halin da yake ciki.
       Su dai su twins an dubasu tuni an ma Muhammad gyaran nashi ciwon, gari na wayewa ma su Oum suka iso aka basu su dan zuwa gida a musu wanka. Dole Hajiya Majdiya da Aunty Sumayya suka koma da su. Itama Nibras ƴan uwanta sun iso asibitin. Mahaifiyarta nata kuka da kumfar baki bazasu yarda ba sai sun maka AA a kotu wlhy. Sannan sun matsa sai an basu ita sun canja mata asibi duk da an gaya musu tayi karaya a ƙugunta da ƙafa, sai kafaɗarta ma akwai ciwo. Sai ciwukan da yaji mata suma dai duk an yi treating ɗinsu. Sawun belt kam gashi nan raɗau tako ina harda fuskata abinka da fara. Da sukaga anƙi kulasu sai suka je suka ɗakko ƴan sanda wai su kama AA. Yayanta Asad na nuna musu adaiyi haƙuri sai an zauna anji mita aikata amma mamansu taƙi kulawa. Daga ƙarshe ma tace zata iya tsine masa idan bazai goyi bayansa ba.
     Koda ƴan sanda suka zo ko kallonsu AA baiyi ba, suma kansu ganin wanda aka ce suzo su kama sai abin ya girmi kansu dan wlhy bazasu iya ba. Bawai dan AA yafi ƙarfin doka bane ba, a'a sai dan alkairinsa da sanin wanene shi a mutunta rayuwar mutane. Su uku a cikinsu da taimakon ALLAH da tsayawarsa suka samu aikin ƴan sandan, dan su ƴaƴan talakawa ne amma ya tsaya musu. Kuma akwai ire-iren su da yawa da yay ma wannan hidimar.
    Da Mom ɗin Nibras ta fahimci bazasuyi ba, wai sun ce AA ɗin yazo office kawai kafin nan kafin zuwa dare sai ranta ya ɓaci taje ta ɗakko masa dss kamar wani ɓarawo. Anan ɗin ma ankai ruwa rana sosai kafin ya yarda ya bisu. Sai dai bai tafi shi kaɗai ba harda su Babban Yaya. Suna zuwa station ɗinsu kuma ogansu yaga wa aka kawo dan shi kuma aminin Babban Yaya ne sai abin ya girmi kansa, awa ɗaya sukai a station ɗin akai ƴan bayanai aka sallami AA akan sai matarsa ta samu lafiya ayi maganar. Nan ma abun ya ƙonama Mom ɗin Nibras zuciya ta wuce kotu kawai ta maka AA. Basu san mi ake ciki ba suna asibiti aka kai masa sammaci gida.
        Sai zuwa dare aka samu dai-daituwar al'amarin Maanal. AA kuma kawai aka bari ya shiga ya dubata. Kawai yanda ya ganta sai yaji hawaye na zubo masa. Haka ya durƙusa a gabanta ya kifa fuskarsa akan tata suna sauka mata. Sai gashi ta buɗe idanun a hankali, sun kumbura sosai sunyi ja. Wani kallon fisha tai masa ta maida su ta sake lumshe wa kawai dan bata a hayyacinta allura sukai mata mai ƙarfi.
     Sosai ya bama RK tausayi, hakama Abbu daya kamashi ya rungume yana lallashi. Yace yay mata addu'a in sha ALLAHU komai zai zama labari kamar ba'ayi ba.. Da ƙyar aka lallaɓa AA sukaje gida, babban Yaya yaje da shi har sashensa, an gyara komai ya koma need kamar ba jiya shine suka hargitsa ba. Har bedroom ɗinsa ya masa rakkiya Yaya Fawzan ya haɗa masa ruwa yay wanka. Suka saka shi a tsakkiya suka bashi abinci yaci. Shima maganin suka tursasashi sha dan zazzaɓi ne ma a jikinsa. Daga nan suka sami nasarar yay barci sannan suma suka wuce nasu sashen suka kimtsa. A lokacin ne Abah yay kiransu akan batun sammaci da aka kawo ma AA daga kotu. Yaya Fawzan yay tsaki da faɗin, “Amma mutanen nan jakuna ne ko? Shike nan zan nuna ma matar nan na fita hauka da rashin ji”.
       Tausarshi suka farayi, dan Yaya Fawzan akwai sauƙin kai, amma idan ya fusata yafi AA da babban Yaya zafi wlhy. Abah yace “Wannan ba maganarka bace ba ma. Barni da ita zan kira su iyayen yarinyar dangin mahaifinta da sukai waliccin aurenta,  dan ya kamata su san komai daya faru tunda uwarta bata nema mata rufin asiri”.
     Wannan shawarar ta Abah tama kowa, dan haka washe gari kuwa Abah yay kiran ƙanin mahaifin su Nibras yace yana son zuwa gidansa suyi magana. Cike da girmamawa yace, “Haba-haba ranka ya daɗe, in sha ALLAHU zan zo ni na sameka har gida, dama banzo nayi Barka ba na ƙaruwa da aka samu bana ƙasar ne.”.
     Murmushi Abah yayi, dan yaronsa ne ƙanin mahaifin Nibras ɗin. Aiko zuwa rana sai gashi da wasu dattijai biyu da yayun Nibras ɗin da ita kanta Mom

208 / 213

Chapters