AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   192 / 213

573K to 576K   out of 636.6K words

aka samu batare da kawoshi asibitin ba ƙasa cike da idanun sun lalace. Kuka sosai Mabera ya dinga yi, dan shi an masa maganin nasa ciwon kan. Yanda yake darzar kuka haka Sille ma ke kuka. Gasu duk an maƙale hannayensu da Handcuffs babu damar zuwa wajen juna duk da suna a ɗaki ɗaya. Gashi yau da safe ganin da Mabera yayi a labarai cewar Aliyu Darma na cigaba da samun lafiya har ma ya fara magana yay matuƙar tsaya masa a zuciya da ruhi. Har ya gama ƙulla ta yanda zai haɗa baki da cikin ma'aikatan aje ai masa aiki akan Abah ɗin da Kamila. Dan haka yanzu da Nutse ya shigo domin saka musu ƙarin ruwa cikin raɗa yacema Nurse ɗin, “Abokina idan bazaka damu ba muyi magana mana”.
          Nurse dake ƙoƙarin haɗa allurai a cikin ruwan da zai saka musu ya ce, “Ina jinka Alhaji”.
      “Idan na saka ka wani aiki na baka miliyan hamsin zakayi”.
    Shiru Nurse ɗin yay yana kallon Mabera, sai kuma a sace ya kalla alluran daya saka a ruwan nan. Tuna alluran minene ya sakashi sakin murmushi, sai kuma ya kalla ƙofar shigowa. Kafin ya sake dawo da dubansa kan Mabera. Ƙasa-ƙasa ya ce, “Ina jinka, mi kake so ai maka?”.
       “Idan babu damuwa ka bani takarda da alƙalami zan rubuta maka. Sai dai ka sani idan kaci amanata wlhy yarana bazasu barka ba”.
      “Baka da matsala Alhaji in dai nine. Ai kaga dai kullum nike zuwa ina treating ɗinku, sai doctor. To kuwa kasan bazanci amanarka ba dan bazanyi wahalar kamawa ba”.
      “Hakane kuma tabbas”.
   Cewar Mabera cikin gamsuwa.
Takarda da biro Nurse ɗin nan ya bashi, tsaff Mabera ya rubuta masa komai sannan ya amshi aron wayarsa. Wasu numbers yasa yay kira, babu jimawa kuwa aka ɗaga. Sai ga muryar matashi namiji. Mabera ya ce, “Ra'iz Baa! Ne”.
       Cikin matuƙar rikicewa daga can Ra'iz yace, “Baa! Akace an kama ku, an kashe min ku!?”.
      “Ƙarya ne Ra'iz kwantar da hankalinka daina kuka. Muna nan da rammu cikin ƙoshin lafiya kuma. Yanzu abinda nake so da kai ka tsaya ka saurareni da ƙyau.”
       “To Baa! Ina jinka, amma dan ALLAH ina Broth?”.
     “Yana a tare da ni kada ka damu zan haɗaka da shi. Idan mun gama. Akwai wani mutumi dazan haɗaka da shi, shine mai wannan layin dana kiraka. Ka bashi 50m yau ɗin nan. Ka haɗashi da Dr Ozaya zai bashi wani saƙona dake a hannunsa. Akwai wani aiki ne da zai mana. Sannan ka gayama su Ɗan-hau aikin dana basu su aiwatar kawai daga nan zuwa gobe. Kai kuma ka tattara komai namu dake hannunka yanzu zan kira Lawwali gobe yazo ku wuce Niger, zamu haɗu da kai a sabuwar ƙasarmu”.
     Cikin jin kwanciyar hankali Ra'iz yace, “Shike nan an gama Baa! Ina Broth ɗin?”.
     Wayar Mabera ta bama Nurse ɗin nan yace ya bama Sille. Koda ya bashi sai ya dawo ya sakama Maberan nashi ƙarin ruwan, shi kuma Sille suna magana da Ra'iz. Yana kammalawa ya koma kan Sille shima ya saka masa, daga nan ya amshi wayarsa ya fice yana sanar masa sai kuma anjima ya dawo cire musu ruwan..
     Yana fita Mabera yay murmushi, ransa fal farin ciki. Ya tabbatar in har su Ɗan-hau sukai wannan aikin a gobe shi da Sille zasu bar asibitin nan. Hakama zai shafe babin Kamila tunda ita tace mai taurin rai ce......

________★

         Maanal na kwance jikin AA ya gama hutawarsa hannunsa akan cikinta daya fara tasawa dan har ana ganin tudunsa. Ganin yanda ya fara sauke numfashi a hankali yasa a shagwaɓe faɗin, “Wai barci zakayi ma?”.
     Kansa kawai ya jinjina mata. Itako ta sake shigewa jikinsa tana tura baki. “Ammafa in ta gaskiya za'ayi ba haka mukai da kai ba Besty. Dan ALLAH ka tashi muyi wanka sai muje shan furan. Daga can basai muga idan su Ammie sun iso ba?”.
           Cikin Muryar son yin barci yana sake riƙota jikinsa ya ce, “Besty zamuje, Please ki barni na ɗanyi barci kaɗan”.
       “Ni gaskiya a'a ai ba haka mukayi da kai ba”.
    Shiru ya mata, zata sake magana yasa tafin hannunsa ya rufe mata bakin, dole tai shiru. Duk mutsu-mutsun ta kuma bai barta ba. Tun tana masa ƙananun duka har itama barcin yaci ƙarfinta. Dama yasan shi take ji, rigima ce kawai da fitinarta. Shi yanzu yanda garin nan ke ɗaure da hadari ina zai ɗauketa suje. Su Ammie kuwa tun ɗazun sun iso, baya son yaje ne tace zatai aiki shiyyasa yace mata basu iso ba sai an jima.
      Barci kuwa suka sha sosai, dan kwanakin nan gaba ɗaya basa samun isashen barci. Raba dare suke a nafilfili da addu'oi. Da safe kuma ba dama gida cike da mutane ga zuwa asibiti. Balle kwana biyun nan lamarin mutanen Giro shima yana cin lokaci su sosai.
      Lokacin da suke farkawa yana kallonta kawai yaji dariya tazo masa. Dan tai wani irin zubawa agogon ɗakin idanu ne hawaye share-share a fuska. Ya tabbatar idan yay dariyar nan matsala za'a samu. Dan haka ya ɗauka ƙasa yay kneeling ya kama kunnuwansa duk biyu. Pillow Maanal ta ɗauka ta fara kai masa ƙananun duka. Shi ko ya shiga kare kansa yana dariya. Da ƙyar ya kamata ita da pillow ɗin ya rungume gaba ɗaya.
       “I'm sorry Sweetheart, na tuba na tuba...”
     “Ba dariya kake min ba, shine ka tuba. Ni ka sakan babu ruwana da kai, kuma ALLAH saina haɗaka da Abana”.
           “Nace fa kiyi haƙuri, ki rufa min asiri da haɗani da Abah ɗin nan, haka kawai ya sake amshe min ke sai bayan wata biyu ya bani. Wlhy bazan iya jurewaba wannan karon, sai dai Oum ta haɗamu duka ta riƙe kawai dan nima sashen nata zan koma”.
      “Basai na koma Kano ba”.
   Ta faɗa tana dariya cike da ƙeta. Fuska ya ɗan ɓata. “Oh dariya ma kike min?”.
      Jikinta ta janye a nasa tana masa gwalo, ya bita zai kama ta zille. Haka ya tashi ya bita suka shige bayi. Sun jima a ciki kafin su fito, kowanne da rigar wanka alamar shi sukayi. Da taimakon juna suka gyara jikinsu. Sukai shirin barci. Tea kawai suka sha suka sake komawa gado suka kwanta bayan sunyi shafa'i da wutri dan yau zasu ɗan yi barci. Yana rungume da ita suna hirarsu ƙasa-ƙasa akan haihuwarta barci yay awon gaba da su kusan lokaci ɗaya. Basu sake sanin kansu ba sai asubahi.....

_______★

          Anyi gwajin yaran Hajiya Zahedah duka, dana Salima ƴar Sabuwa. Hakama Bakori mijinta. Haka sukai zaman jiran result ana ƴar hararar juna. Sai dai babu damar yin magana dan akwai jami'an tsaro a tare da su. Mizai faru kawai an tura su wajen likitar da zata musu bayanin result ɗin Hajiya Zahedah taci karo da abinda ya hargitsa mata lissafi. Domin kuwa dai likitar nan ba kowa bace face ƴar aikinta data kamasu ita da Mabera a shekarun baya har Mabera yay mata fyaɗe.
    Kar-kar jikin Hajiya Zahedah ya shiga rawa. Itako likita tayi ma kamar bata santa ba, haka suka zauna duk tana a ɗarare. Shi kansa Bakori da ita kanta Sabuwa kallon sani sukema likitar, amma yanda ta kame babu alamar wasa a tare da ita ya saka suka nutsu. Waya ta ɗauka tayi kira, babu jimawa wata matashiya kamarta tare da dattijuwa suka shigo. Dattijuwar ta kalla cike da girmamawa tana tashi a kujerarta ta bata, ta ce, “Mama bismillah,”
     Wadda ta kira da Mama ɗin tace, “Miya faru Jameelah?”.
    “Babu komai Mama, result ɗin ne dai ke ya kamata ki faɗa saboda wani dalili. Ban buɗeba gashi nan suma suna gani, sannan ban san su waye ba sai yanzu da aka tura min su. Dan haka ki fara dubawa su san sakamakon kafin nai muku bayani”.
     Baki Hajiya Zahedah ta buɗe zatai magana security ɗin dake tare da su ya daka mata tsawa. Dole kuwa taja bakinta tai shiru.
       Zama Mama tayi, ta buɗe duka result ɗin tana dubawa, sannan ta miƙama ɗayar da suka shigo tare tace tai musu bayani.
    Aiko dalla-dalla waccan tai musu, daga ƙarshe ta tabbatar ma da Bakori yara manya mata guda biyu na farko sune ƴayansa. Amma sauran guda ukun duk ba nashi bane ba. Suna da alaƙar jini da Salma ƴar Sabuwa. Cike da borin kunya Hajiya Zahedah ta tashi zata fara hauka mijinta ya kwasheta da mari. Zai ƙara na biyu aka rirriƙeshi.
     Dr Jameelah tai murmushi mai ƙayatarwa, cike da nutsuwarta da kamewa tace, “Hajiya Zahedah kenan. A ganina ai lokacin wani kai-kawo da pretending ai ya ƙare kuma. In ce shima tsinannen kwarton naki yana hannun hukuma ne. To miya rage, kema ki miƙa wuya kawai zaifi miki sauƙi ai.”
        “To ke ina ruwanki? Ke wacece?”.
    “Ke kin san ni wacece, domin tun shigowarki ofishin nan kin shaida hakan. Alhaji nasan kaima dole kana min kallon sani, to kwantar da hankalinka yanzu zaka sha labari. Ina fatan baka manta da Jame ba mai aikinku shekaru kusan goma da suka shige zuwa sha biyu. Yarinya ƙarama da aka kawo muku daga ƙauyen soba daka hana na dinga taɓa maka duk wani abinda ya shafi abincinka”.
        Shiru Alhaji Bakori yana nazari, zuwa can ya ce, “Tabbas anyi haka baiwar ALLAH. Daga baya kuma na nemeki na rasa lokacin kin fara tasawa da canjawa tunda a ƙalla kin kai shekara biyar a tare damu”...........✍️181


.......“To Alhamdullah tunda har ka tuna. Na ɓace ne a duniyarku sakamakon wannan matar taka da kwartonta Mabera. Dan kuwa tun farkon zuwana gidanku duk da banda wani isasshen wayon sanin mi suke aikatawa na fahimci komai. Saboda da zaran ka fita aiki yara sun wuce makaranta shi kuma zai shigo gidan. Haka zasu kwashe a wanni a ɗakinta ko naka. Da yake da haɗin bakin maigadinka yake shiga hatta da daddare idan kai tafiya zuwa yake gidan ya kwana. Da farko rashin wayo yasa nai tunanin ko ana auren maza biyu ne, sai kuma koma tunanin shi ɗin ɗan uwanta ne ko naka. Sai a hankali a hankali na gane cin amanarka fa akeyi. Ina son faɗa maka ina jin tsoro, har takai abun nasu ya isheni ranar na fito na kamasu a falo babu kunya babu tsoron ALLAH nace sai na tona musu asiri. Shine ya kamani yay min fyaɗe a gabanta suka ɗaukeni suka kai garinmu da gargaɗin idan na sake dawowa cikin Kaduna sai sun kasheni. Da yake UBANGIJI ba azzalumin sarki bane sai ya haɗani da Mama, sunje garinmu wani aikin asibiti mamana ta kaini asibiti saboda halin da nake ciki da suka gane kaina bayan sunyi maganin aljanu, sunyi na mayu dan ban faɗama kowa ba sai suka ce bari su gwada na asibiti. Anan ne Mama ta gane fyaɗe akai min. Ta tsareni da tambayoyi, naso ɓoye mata itama amma ta nuna min taimakona zatayi. Hakan shine sanadin komawata yanda nake a yanzu. Dan kuwa ta ɗakkoni daga ƙauyenmu tazo tai min magani, bayan na warke sarai ta sakani a makaranta har ALLAH ya kaini ga kaiwa wannan matsayin na likita. Yanzu haka inada aurena harda yaro ɗaya gani da cikin na biyu, ina auren babban likita da ayanzu haka shine akan case ɗin Mabera dan shi ne ma ke kula da shi”
     Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un Bakori kawai ke faɗa, bai ma san sanda ya damƙo Zahedah ya shaƙe ba yana kuka da dukanta yana tsine mata albarka ita da Mabera. Da ƙyar aka amshi Zahedah a hannunsa, har ma ta suma dan wuya. Kafin kace mi ƴan jarida sun iso asibitin. Dan yanzu komai ƙanƙantar abu akan Mabera ba'a wasa da shi musamman ga ƴan jarida da ƴan sa kai masu ɗauka a wayoyi.
       Abu kamar wutar jeji dandanan gari ya ɗauka, abubuwa suka fara yawo a media da gidajen tv. Kowa sai sake yin ALLAH wadarai yake da al'amarin Mabera. A karo na farko kuma bbc suka buƙaci yin hira da Bakori. Bai ko musa ba ya bada haɗin kai....

Idan kunji ana zazzaga to ita Bakori yay ma Mabera a wannan rana. Dan kuwa wasu manyan sirrikan Mabera da babu wanda ya sani sai UBANGIJI sai shi dake abokinsa, shima kuma bawai ya fito ya sanar masa bane kawai dan bakorin na bibiyarsa ne ya sani yau ya buɗema duniya su. Ciki kuwa harda kashe mahaifiyarsa da Maberan ne ashe yasa akayi, da ƴan uwansa biyu maza suma daya kashe a shekarun baya. Ya kuma tabbatar da Mabera na tare da manyan ƴan siyasa ne ta ƙarƙashin ƙasa shiyyasa yake aikata duk abubuwan nan batare da an taɓa ko kamashi ba. Hatta kidnapping daya kafa sansanin yi duk da shi yana gida kwance shike bada information ɗin da yaran ke bi su kama mutum su amshi kuɗin a kawo masa ya basu abinda ya gadama ya raba sauran da iyayen gidansa. Anyi-anyi Bakori ya faɗi su waye iyayen gidan nashi yace shi baza'a ji mutuwar sarki a bakinsa ba. Su jami'an tsaron da suka kamashi su bincike sa mana ai ya musu sharar fage tunda ya fito musu da ainahin wanene Mabera batare da shan wahalar bincike ba. Daga ƙarshe yace akwai babban yaron Mabera dake zaune a Niger sunansa Lawwali shike masa safarar kaya daga Niger zuwa Libya, Sudan, har zuwa Nigeria. Sai yaronsa ƙarami da baida ƙafafu yana a Lagos shima shegen kansa ne dan babban dila ne na ƙwaya....

_______★

         Wannan saƙon hira ya isa har kunnen Mabera a television ɗin dake a ɗakin jiyyarsa, rawa jikinsa ya fara yi kar-kar, dan kuwa Bakori ya gama kwance masa komai daya rage. Ashe dama shegen mutumin nan da yake kallo sakarai yana amfani da shi ne ashe komai ya sani game da shi amma ya dinga kwantar masa da kai uwa wani gara. Ai ko wlhy sai ya kashe shi. Hankalinsa ya tashi matuƙa, addu'a kawai yake Nurse ɗin nan ya shigo cire musu ruwan daya saka musu ya amshi wayarsa yay kiran Ra'iz yace ya gudu. Sai dai ina ita ƙarshe sunanta ƙarshen ne kawai. Babu abinda ke canja ƙaddarar ƙarshe wlhy. Dan ko munƙi ko mumso dole-dole wataran sai an iskema wannan ƙarshen...

★★★

      Ba Mabera kawai wannan saƙon ya isar mawa ba harda tawagar su Sen... Bukar. Dan su saƙon ma bibbiyu suka samu. Wannan na batun Mabera da kuma batun kama Rabilu da sai a yau suka sani. Dai-dai nan kuma sai ga Oler a guje ya shigo musu. Cikin hakki da kallon bayansa ya ce, “Alaji muyi ta kammu, dan kuwa yanzun nan Bad ya tabbatar min an kama duka yaranmu dake tsare da mutanen can. Yanzu haka an ɗauke mutanen zuwa asibiti.”
        Idan ba kayi bani guri, yau ake asalin GUDUN YADA ƘANIN WANI. Dan kuwa sai ga manyan ƙasa da babbar riga suna cika mata iska🤣. A guje suka dinga fitowa suna shiga motocin su. Dan danan drivers ɗinsu suka shiga reverse a haukace suna fita daga guesthouse ɗin da suke na sirri. Sai dai suma anan ɓangaren ɗin ƙarshen ce tazo da gasken gaske. Dan kuwa iya kuɗinka iya shagalinka akayi, kowane driver na fitowa a ƙarshen titin street ɗin dole yake taka birki. Dan amma titin ɓam da jami'an tsaro riƙe da bindigu, haka ma ta bayansu. Gaba dai kura kawai baya sayaƙi.
     Haka suna ji suna gani aka ram da su, drivern ɗaya daga cikinsu ma da yay ƙoƙarin danna kan motar wai ya wuce bisa umarnin ogansa kawai aka sakarma motar wuta. Haka akai musu dugu-dugu da ruwan bullets sai gawarwakinsu aka fitar. Dan wanan umarnin aka bama jami'an daga sama. Sun kuwa cika dai-dai yanda ya dace. Sai ga su Sen... Bukar an kama idanu wuƙi-wuƙi kamar kwaɗina a ruwan zafi. Ƴan jarida da tuni sun cika wajen da jama'ar gari ƴan bani na iya sai ɗauka suke suna bazama duniya komai.
     Sai kuma ƴan siyasa suka fara tsalle-tsalle da iface-ifacen an shirya hakan ne domin cin zarafin su Sanata ɗin. Ai siyasa ce kawai miye-miye. Ai tuni IG ya tara manema labarai, yay bayani gamsashe tare da tabbatar ma mutane duk ɗan siyasar daya sake fitowa yace wai kama su Sanata Bukar siyasa ce wlhy shima sai sun kama shi. Domin hakan da zai yi na nufin shima yana tare da su ne kenan. Idan kunne yaji jiki ya tsira. Mutanen gari kuma su kwantar da hankalinsu baza'a ja wannan al'amari da nisa ba a gobe-gobe za'a kai su Sanata kotu. Dan kuwa itama jihar Kebbi ta shigar da Sanatan da abokansa ƙara game da ɓata mata sunan mutane da yin amfani da sojin su wajen yin aikin da bai dace ba akan kama mutanen garin Giro. Dan gaba ɗaya kwanakin nan tako ina ka shiga media babu abinda kake gani sai justice for the Giro people. Ba mutanen gari ba hatta hukumar kare hakkin ɗan adam da kungiyoyin lauyoyi ta ƙasa sun fito tsaya musu. Hakama manyan mutane sunata tofa albarkacin bakinsu akan al'amurin ana ƙalubalantar gwamnatin jihar da yin sakaci alhalin basujiba basu gani ba. Hakan kuwa shine ya sake fusata gwamnansu da muƙarrabansa suka shirya ɗaukar mataki na musamman. Aka kuma sallami duk wanda aka kama da maƙudan kuɗaɗe da tarin alkairai, a kuma tabbatar musu za'ayi musu titi a kuma kai musu wutar lantarki da ƙaton DAM na ruwa domin samun abin dogaro da kawunansu ta harkar noma. Yaransu matasa da sukai karatu aka ɗauki nauyin su zuwa ƙasashen duniya ƙaro ilimi dama nan gida Nigeria.
       Wannan fa shine GOBARAR TITI A JOS. Ai su jama'ar Giro babu abinda zasuce da UBANGIJI sai godiya. Wannan abu ai gwara da akayi. Gefe ƙaunar Asiya da dana sanin abinda suka

192 / 213

Chapters