Author : Bilyn Abdull Category : Romance
sanyi da zafin rana”.
Manaal da kalaman ke tasiri sosai a zuciyarta, amma suna sakata a ruɗani tai shiru tana kallonsa cikin ƙaulani, sai kuma ta kai yatsarta a saman lips ɗinsa ta ɗora, tana masa wani kallo mai sanyi. “Kana ruɗar dani da kalamanka, mu biyu ni da wa kuma Besty?”.
Murmushi ya sakar mata mai daskarar da zuciya, sai kuma ya kashe mata ido ɗaya hannunsa na shafa cikinta tare da sumbatar lips ɗinta, sai kuma ya ƙara rage murya ƙasa ya buɗe baki zai yi magana. Mamy data kasa jurewa ta motsa. Shiru yayi, sai kuma ya kalla wajen. Itama Maanal bayansu ta kalla a karo na farko. Mamaki ya kamata ganin Mamy kwance a kusa da su. Kafin tayi magana Mamyn ta tashi zaune. Manaal kam ta kasa motsi, kamar yanda shima AA kallon Mamyn kawai yake. Ya kasa janye Maanal a jikinsa ya kuma kasa cewa komai. Wani kallo Mamyn ta zuba musu na sakanni, sai kuma batare da tace komai ba ta sauka a gadon tana dafe kai. Yunƙurawa Maanal tai ta tashi, kamar an saita sai ga Oum ta shigo ɗakin.
Hankalinta akan Mamy ta ce, “Suhanallahi kin tashi. Sannu”. Oum ta faɗa tana riƙota. Sai ga Gwaggo Khadijah ma. Itama dai sannu takema Mamyn, sai kuma ta kalla Maanal da Ajwaad ta ce, “A'a Manaal kema kin tashi ke nan. Kai Alhmdllh”.
A hankali Maanal ta jinjina mata kai, ta ƙaraso tana taɓa goshinta. “Alhamdullahi zazzaɓin ya sauka. Ajwaad taimaka mata itama kuje tai wanka a kawo mata abinci taci ta samu ƙarfin jikinta.”.
Cikin yanayinsa na rashin son yawan magana ya jinjina mata kai ƙasa-ƙasa yace, “To Gwaggo”. Haka ya kama Maanal suka wuce sashensu. Mamy ma an kamata zuwa sashenta....
★★
Bayan sallar azhar ƴan Zaria suka sakema Najma nasiha yanda ya kamata, suka mata addu'a suma motar da zata wuce da su tazo ta ɗaukesu. Maman Yaseerah ranta duk a jagule da halin data zo ta samu Yaseerah na ciki a Abuja. Yarinyar sam bata jin daɗin zama. Ga tsohon ciki haihuwa yau ko gobe. Bayan wucewar yan Zaria suma ƴan Kanon shiri suka fara. Dan anayin la'asar zasu wuce, mazan dama duk sun wuce da mafi yawan yara, sai su Baba Sardauna suma akwai abinda ya tsaidasu shiyyasa zasu tafi tare da natan. A lokacin da nan baƙi ke shirin wucewa a ɓangaren Mamy cikin sabon tashin hankalin Sille take. Ga al'amarin su AA da Maanal ya matuƙar tsaya mata a zuciya, ga hirar su Babban Yaya daya tabbatar mata sun kasance da amare. Auntyn ta dai ta zauna ta mata nasiha duk da tasan ba ɗauka zatai ba. Itama ta fara nata shirin dan ƴan Kano zata bi. Ta kuma tabbatarma Nana ta shirya itama su wuce dan bazata barta a gidan ba wannan karon. Shine tace zataje gidan Hajiya Turai ne. Auntyn tace to sai dai nan ɗin.
Kiran da Sille yayma Mamy a karo na biyu ya tabbatar mata gashi a ƙofar gida, kuma wlhy minti goma ya bata yaji alert ko ya shigo ciki ya amshi kash. Hankalinta ne ya sake tashi, dan ta tabbatar tunda yace yazo ɗin yazo. Ita wai ya zatayi da wannan mutumin, har yau tana jin ɗacin rabuwa da 10m ɗinta wlhy. Cikin sanyin murya dan bata da lafiya da gaske ta ce, “Zan saka maka 5m dan ALLAH ka barni, ka fita a rayuwata, ban sanka ba, ka daina damuna, idan ba haka ba zan ɗauki mataki a kanka”.
Dariya mai ƙarfi Sille yayi, yace, “Ke ko kika sanni, ke kuma kike da alaƙa da ni. Bana jin kuma zan iya yin nesa dake bare barinki. Ɗaukar mataki kuwa ga hanya maza ki saka a ɗauka miki. Kuma 10m nake buƙata ba 5 ba, idan ba hakaba wlhy yau ɗin nan saina gana da Aliyu Darma da tsoffinsa dake gidan. Dan gara muyita ta ƙare su koroki a gidan dole ki dawo gidanmu naci kuɗin da ƙyau. Kuma ki tabbatar ma da ɗanki Ajwaad akwai tamu da shi shima, fansar Ra'iz babu fashi sai na ɗauka akan shi da matarsa.” ƙitt ya yanke kiran.
Rasa ma tunanin daya dace Mamy tayi tayi, sai zuciyarta dake sake mata nauyi. Wata na bata shawarar ta bashi kuɗin kawai daya buƙata ta samu ƴan bikin nan subar gidan sai ta samu tayi tunanin daya dace a kansa. Tunda mai mata bincike yace shima ya kammala gobe zai dawo Abuja. Ya kamata ya hutar da kanta ta samu ta warke daga wannan ciwon kan dan ta samu fita. Da wannan tunanin ta turama masa 10m ɗin zuciyarta na ƙuna. A cikin kwana goma ta rasa miliyan ashirin wannan wane irin tashin hankali ne. Sosai take jin rabuwa da kuɗaɗen nan nata a cikin ƙasusuwanta. Amma ba komai zatai maganinsa, komai daya amsar mata sai ya dawo ta fishi hatsabibanci. Wlhy rayuwa ce ta sauyata kawai da soyayyar Aliyu Darma. Amma badan haka ba shi har ya isa yazo yana mata barazana........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣2️⃣3️⃣
______________
..........A lokacin da Mamy ke sakama Sille kuɗi anan Maanal ce ta ishi AA da rigimar bazataci abinci ba fura take so. Dan yana buɗe abincin ma ta nema fara masa yunƙurin amai sakamakon tuna wancan ƙamshin naman da take kamar dai yanda Ammie tai hasashe. Dole ya fitar da abincin ya shirya ya ɗauka key ɗin mota ya fito duk da bai ma san inda zai samu wata fura ba shi kam, amma dolensa yaje nema ai. Dai-dai ana buɗe masa gate zai fita alert ke shiga ma Sille na Mamy, yay waya irin dariyar data saka AA kallon inda yake a ƙasan bishiyun ƙofar gidan nasu da gaba ɗaya suke a street ɗin daga farko har ƙarshe. Tsaiii yay yana kallon Sille, dan kuwa ya ganesa tsaff shine suka taɓa gani a gidan Hajiya Turai har ya dinga hasashen ya sanshi. Rashin muhimmancin al'amarin yasa ya watsar da batun tun a ranar. Mizai faru Sille na juya baya dan farin cikin shigowar kuɗin yasa bai lura ma da AA ɗin ba, kuma motar ma tinted ce dan duk motocin AA ɗin haka suke baya son gilashi mai haske yasa Sillen ma bai ganshi ba. Yanda Sille ke tafiya sai mai gyaran ruwa na waccan ranar ya shiga dawo masa a zuciya, haka yake da iya ajiye abu a rai in har mai muhimmanci ne. In kaga ya watsar da abu to lallai bai ɗaukeshi serious ba. A fili ya ce, (Tabbas shine na ranar. Hakan na nufin da gaske bamai gyaran ruwan bane kamar yanda nai shakku. To miya haɗashi da gidan waccan matar? Yanzu kuma na ganshi sau biyu a namu gidan?). Nuratu ce tazo masa a rai, tunda yasan tana gidan. To amma randa ya ganshi a can ma ai Nuratu na nan. (Kasani ko nemanta yaje a ranar acan gidan nasu) Wani sashe na zuciyarsa ya ayyana masa. Jiyay ya ɗan gamsu da hakan, duk da zuciyarsa taƙi amincewar kuma, daga ƙarshe dai ya ɗauka wayarsa yay ma sille da motarsa hoto kawai ya wuce abinsa neman furar sarauniya. A ransa kuma yana ƙarfafa dolene ya bincika guy ɗin nan zaifi samun salamar shakkun da zuciyarsa ke ciki har yanzu. Dan daga ganinsa ba mutumin kirki bane ba....
________★
Zuwa Magrib Alhamdullah gida yay shiru kowa ya wuce. A sashen Oum daga su Inte sai Nuwaira dasu Naufal, itama mijinta take jira ya zo su tafi gidansu. Su Naufal kam basu koma hannun Saheeba ba suna nan wajen Oum dai har yanzj. Sashen Mamy ma daga ita sai su Haule, Nuratu ma na sashen Saheeba tana jiyyarta Mamyn ma ta zata bata a gidan ne. Hakama ita Saheeban, daga ita sai Nuratu ta wuni kwance babu lafiya, yayinda Babban Yaya kecan yana jiyyar Ameerah dan yini guda a ɗakinta yayisa bai leƙa Saheeban ba baima san halin da take a ciki ba saboda shi har yanzu yana horata ne, ya gama shirya sai ya sha amarcinsa sannan ko zai ma yafe mata su dawo dai-dai. Suma dai su Maanal su kaɗai ne a nasu sashen. Nibras ma kowa ya wuce sai ita kaɗai sai Najma amarya da take a nata ɗakin. Yau ma ta gama shirya muguntar da zata musu, sai dai bata san shima Yaya Fawzan ɗin ya gama nashi shirin ba tsaf. Dan bedroom ɗin kusa da Nibras ɗin dake upstairs ɗin ya saka su Meeno da Hafsah ƙanwar Najma ɗin mai bi mata suka gyara masa tsaff da rana, suka raba kayan Najma biyu na amfanin yau da kullum suka kai wasu can. Dama bedrooms huɗu ne a saman, ɗaya nashi, ɗaya Nibras, biyun ko babu kowa tunda akai gyaran nan aka zuba musu sabbin kaya tsaff da su babu wanda ya shiga. Dama ha shigar ake ba tunda anyi su ne domin yara. Bedrooms ɗin ƙasa guda biyu kuma dan baƙi. Tunda anyi haka sai kawai ya tsara itama Najma ta dawo saman kawai ƙasan ya cigaba da zama matsayin na baƙin, dan shi bama ba wani son aima Najma sabon ginin anan yake son su zauna gaba ɗaya.
Lokacin da su Hafsah keta wancan aikin Nibras na ɗaki kwance zazzaɓi ya mata rijib saboda kukan data sha akan batun cikin Maanal da wayar da sukai da Mamanta. Sai bayan la'asar ne ta samu ta tashi lokacin har sun gama sun rufo ɗakin, shine ta fara shirya muguntar da zatayi. Tasan dai dole sai ya kai tara kafin ma ya shigo sashen, tunda sai sunci abincin dare a sashen Oum, rashin jin motsin Najma ma sai ta ɗauka ai tana sashen Oum ɗin itama tunda yayar babarta ce. Dan haka bata damu ba ta zauna yin waya da ƙawarta mai bata shawara akan AA...
Anayin sallar isha'i a tare mazajen gidan suka shigo, sun sako Abansu a tsakkiya sunata hira. Hirar da duk ta ta'allaka ne akan batun cikin Maanal. Kamar yanda suka saba kuwa sashen Oum suka nufa, sai dai ko zama bata barsu sunyi ba tace ta yafe hiran yau kowa ya wuce sashensa ta saka an kai musu abinci. Shima Rafeeq yazo ya ɗauka matarsa da nasu abincin gashi nan su wuce. Wani murmushi Abah ya saki yana binta da kallo ƙasa-ƙasa.
Fawzan dama bai niyyar zama ba, haka ma AA dan hankalinsa nakan ƴar shagwaɓarsa. Dan haka a kunyace suka fito dan sarai sun gane yau Oum tasan dama bata ita suke ba shiyyasa ta korosu kafin su nuna hali. Kowa sashensa ya wuce. RK da Nuwaira suka fito suma suka shiga mota suka tafi. Abah dake kallon Oum yace, “To su kin korasu suje su huta, ni kuma fa?”.
Murmushi tayi. Ta ce, “Kaima yanzu zan kora ka ai”.
“Aiko ban koruwa, dan nima dai yau anan zan kwana”.
“Ina ɗin?”.
“Sashen Fateema ta”.
Yay maganar yana wani narke idanunsa na girma. Dariya Oum tayi tana ɗauke kai. Shima sai ya dara yana kaiwa zaune a kusa da ita...
_______★
Kai tsaye bedroom ɗin Najma Yaya Fawzan ya nufa. Tana zaune akan abin salla data idar tana tunani. Ko sallamarsa bata ji ba har ya ƙaraso inda take. Sai da ya duƙo ya taɓata tai firgigit. Sai kuma ta sauke ajiyar zuciya. Shi dai kallonta yake, sai kuma ya kamata ya miƙar. A jikinsa ya sakata ya rungume cikin kunneta yace, “Tunanin mi kike Love?”.
Ajiyar zuciyar ta ƙara saukewa, muryarta a sanyaye ta ce, “Tunaninka Yaya”.
Murmushi yayi mai ƙayatarwa, hannunsa na shafa bayanta ya ce, “Abar tunanin gani kusa da ke ai”.
Murmushi tayi tana ƙara ɓoye fuskarta a jikinsa. Fin mintuna biyu ya ɗagota. Sai kuma ya bi ɗakin da kallo. Kafin ya sake maido idanunsa kanta. “Bazamu kwana a ɗakin nan ba Love”.
Kanta a ƙasa ta ce, “Miyyasa?”.
“Kawai dai nafi son muje sama. Dan kema can zaki koma kawai akwai ɗakinki. Bazan iya rayuwa a sama ke kina ƙasa ba”.
Ɗan jimm tayi, sai kuma ta murmusa. Duk da hakan bai mata ba, dan bazata so gata ga Nibras ba gaskiya, gara dai ita tana ƙasan su suna saman. Amma sai ta danne cikin iya magana ta ce, “Yaya duk hukuncin daka yanke a kaina ni mai biyayya ce, umarni kawai zaka bayar na amsa da to. Idan hakan kake so babu damuwa. Sai dai zanso muyi zaman mu a haka wani bai takura wani ba, kasan mu mata a karkace muke, zama gab da juna kuma ƙara karkatar damu yake”.
Ajiyar zuciya ya sauke mai sanyi, sai kuma ya jinjina kansa. “Hakane, amma kin san ɗakina fa yana sama, kuma dole kije koba yanzu ba. Bayan haka ko'ina kowaccenku nada iko da shi a sashen nan. Amma tunda kin zaɓi hakan zan barki anan, sai dai can ma kina da ɗaki. Dan haka muje”.
Batai masa musu ba ta biyoshi suka fito bayan ya kashe komai na nan ɗakin ya ɗauka wayarta ya saka a aljihu. Zasu fara hawa stairscase ɗin kawai ya ɗauketa gaba ɗaya. Ɓoye fuskarta tai a ƙirjinsa, shi kuma yay murmushi da faɗin, “Kin san amarya sarauniya ce, abinci ma kamata yay sai an tauna a bata”.
Siririyar dariya Najma ta sanya da faɗin, “Tabɗin gatan yay mata yawa ai”.
“Ba wani yawa Love. Ko ca kikai na goyaki daga nan har Zaria yau zan iya”.
Nan ma dariyar take, dai-dai suna kai ƙofar ɗakin. Abisa tsautsayi, dan tsautsayin kam zamu kirashi sai ga Nibras burum ta fito, dan dakonsa take dama tun ɗazun, motsin da taji sai tai zaton ɗakinsa zai wuce yana shiga ta kullesa ta baya tunda tasan yau dole ne ya shirya kare kansa akan abinda ya faru jiya. Daburcewar da tai, da yanda kanta ya sara a lokaci guda saboda abin yazo mata a bazata ya sata bugewa da bango jikake ƙumm. Wani makirin murmushi Yaya Fawzan ya sakar mata yana wani lumshe idanu da buɗewa a kanta, ga kuma Najma daketa taɓashi ya sauketa ya ƙi.......✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣2️⃣4️⃣
______________
........Tsabar ma son sake ƙular da Nibras yay kamar zai ɗan saki Najma ɗin a ƙasa, ita kuma gudun faɗuwa yasa ta ƙara rukunƙumesa tana ɓoye fuska a jikinsa yanda ya kamata. Cike da iskanci ya wani lumshe ido ya buɗe akan Nibras da kishi ya kume, dan ƙuru-ƙuru yau Yaya Fawzan ke ganin matsannacin kishinsa a cikin idanunta dama fuskarta gaba ɗaya. Dama Nibras akwai saurin kuka, sai ko ga hawaye sharrr suna sauka. Yaya Fawzan ya sake taɓe baki yay wucewarsa kai ka rantse ma bai ganta ba, ya tura ƙofar da ƙafa suka shige. Sai da ya kaita har saman gadon daya sha gyara sannan ya sauketa. Shima ɗakin yayi ƙyau sosai, dan baida maraba da wancan nata na ƙasa, kamar ma wannan zaifi girma. Yanda komai yake sabo acan, nan ɗin ma sabon ne fil, sai ƙamshin sabuntar kaya dana turaren wuta ma ɗakin keyi, su Meeno sun gyarashi yanda ya kamata. Zama yay kusa da ita yana faɗin, “Yanzu minene first?”.
Kanta tsaye ta ce, “Kawai kaje ɗakinka ka kwanta, nima zanyi shirin barci na kwanta”.
Zuru yay yana kallonta, sai kuma ya sanya dariya da faɗin, “Wannan gangan ne Love. Kalli ciki idanun mijinki ki gani”.
Daburcewa tai amma yace sai ta kalla. Kaɗan ta kallesa ta duƙar da kanta. Ya ce, “Mi kika gani a ciki?”. Kai ta girgiza alamar bataga komai ba. Ya ce, “Kin tabbatar bakiga komai ba?”. Sai ta kasa amsawa yanzu. Sai ya saki murmushi kawai. Batare da ya sake cewa komai ba ya tashi ya fita....
Nibras kam ƙyarma jikinta ya farayi dan abu ne na bazata, kuma batai zaton Yaya Fawzan ɗin zai aikata ba ganin yanda yake lallashinta a kwanakin nan duk iskancin da take masa, sannan shi mutum ne mai kawaici ƙwarai da gaske, koda yace sai ya rama batai zaton irin wannan ramuwar ba ce, sai ta dinga jin yuuu-yuuu kanta na neman juyewa, dan bata taɓa sanin tana tsananin jin kishin mijinta ba sai yau. Tana jin zai fito cikin sauri ta nufi ɗakinta gaba ɗaya ma ta ruɗe hanyar ma ta kasa gani. Ji kake ƙummm a jikin bango ta sake buga goshi, azaba ta sata sakin kuka da ƙara duk a lokaci guda tana kiran “Wayyo Momy”. In ma Mamiyo ce yau ba jinta zatai ba. Da ƙyar ta lalubi ƙofar ta shige ɗakinta. Gado ta faɗa, ta yayumi duvet ta shige ciki har kanta, ta kawo pillow ta danne kan da shi, sai dai ta makaro, dan abinda ta gano ɗin ya riga ya shiga idanun nata ai, sannan ya rubutu a ƙwalwarta tsaf ta yanda zata shekara dubu tana tunawa. Musamman murmushin da Fawzan ya mata da yanda Najma ta wani sake