Author : Bilyn Abdull Category : Romance
ɗan huce ta masa ɗaurin goro tana mazurai wai bazai fita ba kai kace itace Oum. Oh shi ɗan Aliyu da Fateema yau yaga takansa.
Kallonta ya sake yi, yanda take hura hanci wlhy saika ɗauka duka zata lakaɗa masa. Anya a duniyar nan akwai wanda yakai mata ƙarfin hali kuwa. Ka gansu abu ba abu ba amma fitinarsu da rikicinsu yafi na yaƙin basasa girma. Nan kuma anjima fa idan ta huce sai ta rungumeshi ta masa kiss ƙauna ruwa-ruwa. Nisa'u na rijalu kenan.....
“Ni ka daina kallona”.
Maanal ta faɗa tana fashewa da kuka. Ajiyar zuciya ya sauke, cikin daidaita nashi yanayin ya kama hannun nata ya jata suka koma cikin falon, zaunar da ita yay shima ya zauna. Idanunsa na binta da kallo mai tausasawa ya ce, “Na zauna yanzu mi kike so ayi?”.
Sai da ta share hawayenta sannan tace, “Ni ka barni naje”.
“Besty kima daina ɓatawa kanki rai da batun tafiyar nan dan bayinta za'ai dake ba. In da ace jirgi ne sai na barki, amma tafiyar mota daga nan Abuja har Zaria badani ba wlhy. Ban shirya asara ba gaskiya. Zaɓi dai wani abun”.
“Ni ba abinda nake so, Zaria kawai nake son zuwa. Da da nake tafiya a motar miya saman, sai yanzu zakace wani bazanje ba bayan kuma kowa zaije. A can Dubai wane irin yawo ne bamuyi a mota ba sai anan da yake kana jin mugunta..”
Wai yana jin mugunta abin dariya. Dannewa yay cikin lallashi ya ce, “Ki gane mana Besty, titin Nigeria dana Dubai ai ba ɗaya bane b.....”
Baima gama ba ta sake fashe masa da kuka tana faɗin, “Ni ban yarda ba! Ni ban yarda ba. Kawai sai naje! Sai naje”.
Shi kam yau AA yaga bala'i ai ganin idonsa. Wlhy ta birkice masa gaba ɗaya kamar ba Maanal ɗin ba. Sai kawai ya zuba mata ido ma yana kallon ta. To sai kuma sabon masifa, ita dan mi zaiyi banza da ita. Dan mi tana magana zai yi shiru. Ita bazata yarda ba, ita miye-miye.”
Da yaga abin bana ƙare bane sai ya fara tunanin hanyar da zai gudu. Can dabara ta faɗo masa. Sai yay ɗan gyaran murya yana miƙewa da faɗin, “Bari na kawo miki ruwa ki sha sai muyi magana naga yanda za'ai tafiyar ta yiwu, in ma ni zan kaiki sai na kaiki da kaina”.
Da farko riƙeshi tayi, sai kuma ta sake shi tana share hawaye ta ce, “Kuma mara sanyi nake so, ka haɗo da fresh milk mai sanyi ka saka min inibi da dabino a ciki”.
“An gama Aunty”.
Ya faɗa yana nufar hanyar kitchen. Haɗa mata duk abinda tace tana so yayi, ya buɗe back door ya gudu. A can compound ya samu su Naufal na ball da yaran maƙwafta, sai ya kirashi yace yabi ta back door ya ɗauka abu nan akan work table ya kaima Auntynsu falo tana jira. Shi kuma ya shige mota yabar gidan. Gara yaje ko zagaye gari yayi idan ta huce ya dawo.
🤣🤣AA bawan ALLAH yau Nisa'u sun nuna maka hali kenan😂? Maanal karfa kisa mu Aurama brozan su o'e Nuratu fa. Koda yake ki kiyayi ranar da suka Rijalu zasu murɗa nasu kambun rigimar tommm😂.
________★
A lokacin da AA ke fita anan ɓangaren Mamy ta fito wanka ne ta samu wayarta na ringing. Koda ta duba taga number ce kawai babu suna ajiyewa tai tana jan ƙaramin tsaki. Sai dai me kiran sai ya cigaba da shigowa babu ƙaƙƙautawa harta ji haushi ta ɗaga a fusace. Tana fara masifa Sille ya wani kwashe da dariya daga can. Sai tai tsai tana saurarensa zuciyarta na bugawa dan ta gane sa. A ranta tace ubanwa kuma ya bama wanan ɗan iskan number ta. A fili kam cikin ƙarfin hali ta ce, “Malam waye kai?”.
“Ai kin san waye ni Mrs Darma. Karki wani yi pretending. A tunaninki kin kashe waccan wayar kin tosheni ke nan. To ai abinda baki sani ba ni kamar kurege nake bana hanya ɗaya. Hanyoyine dani kashi-kashi harta inda bakiyi zaton zan fasa ba. Ina muka kwana ina muka tashi? Bake ba kuɗina mike faruwa?”.
Tsaki mai kauri Mamy taja. Cikin dakiya ta ce, “Kai bari kaji na fika iskanci wlhy, kai ubanwaye daka isa ka sani yin abinda banyi niyyar yi ba. Anƙi a baka kuɗin, kuma anƙi a yarda a ganka ɗin yi duk abinda kaga zakayi”.
Wata irin mahaukaciyar dariya Sille ya sanya daga can. Tare da faɗin, “Oh haka kikace? Shike nan zanko baki mamaki. Amma bisa wasu dalilai zan baki dama ta mintuna talatin yanzun nan kacal. Koki fito yanzu ki sameni a bayan gidanku da kuɗina 10m, ko kuma yanzu na nuna miki ni bana magana biyu, dan zaki ganni har cikin ɗakin barcin ki, sai ki fara ƙirga lokaci.....”
Ƙittt ya yake kiran. Ba ƙaramin bugawa zuciyar Mamy tayi ba. Tai shiru kamar mai nazari tsahon sakanni sai kuma ta taɓe baki da faɗin, “Ɗan iskan banza, su masu gadin dake gate ɗin wawayene irinka da zasu barka ka shigo har nan”. Hankali kwance ta shiga shafa manta. Kafin ta miƙe ta nufi closet ɗinta dan saka kaya. Harda su kallon agogo kuwa tana sake jan tsaki. Ta gama shirinta tsaff ta fito dan gidan wata tsohuwar aminiyarta take son zuwa. Da bala'in sauri tai baya zata fasa ihu jikinta na rawa saboda ganin mutum zaune a bakin gadonta.
Sille dake kallonta yay wata shegiyar dariya da faɗin, “Haba relax mana Mrs Darma. Sai kace bake ɗin ba.”
A rikice matuƙa Mamy ta nufi ƙofa, ta danna mata key sannan ta dawo inda yake. Bakinta har rawa yake ta ce, “Ubanwa ya shigo da kai har nan?”.
“A ƙafafuna mana. Ai na faɗa miki ni bana magana biyu kamar ubana nake.”
“Waye uban naka? Kai wanene ma kai? Mi kake so a wajena?”.
“Tofa irin wannan tambayoyi haka wacce zan amsa a ciki”. Sai kuma ya zame hular rigarsa data rufe masa fuska yana cigaba da faɗin, “Kalla fuskar baƙya buƙatar bayani”.
Kaɗan ya rage Mamy kuwa ta zube ƙasa tsabar razana. Junaid fa take gani, Junaid dai Junaid. Amma taya Junaid zai cigaba da zama a iya wannan shekarun har yanzu. Wannan fa bazai wuce talatin da tara ba haka. Dan zai girmi Fadeel gaskiya kamar da shekara biyu ma. Jiri ke neman ɗibarta ga numfashinta sai wani fisga yake da ƙyar. Shi dai Sille kallonta kawai yake. Sai da yaga kamar zata sume sannan ya miƙe zai kamata. Hannunsa ta bige tare da faɗin, “Karka taɓa ni”. Hannayensa ya ɗaga sama tare da ja baya ya koma ya zauna inda ya tashi, itama ta daddafa ta kai zaune cikin sofa, ruwan dake a saman table ta ɗauka tasha tana hakki ga idanunta sunyi jazur. Da ƙyar ta iya sake furta, “Wanene kai? Miya kawoka waje na?”.
Murmushi Sille yayi mai haɗe da dariya. Sai kuma ya taɓe baki da faɗin,.....✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣0️⃣3️⃣
______________
.......“Zuwa yanzu ko baki san wanene ni ba kin san daga ina na fito. Kin kuma fahimci zan iya aikata komai idan baki min yanda nake so ba. Sunana Junaid ibn Junaid, kuma ɗan Kamila”.
Da wani irin razani Mamy ta kallesa yanzu ma har yawu na neman sarƙeta ta ce, “Wace Kamilar?”.
“Bayan ke akwai wata Kamila anan ne? Ki maida tunaninki baya, 39years da suka wuce, ranar lahadi ƙarfe sha ɗaya da arba'in na daren litinin, cikin kangon jikin makarantar allon Malam Bello ɗan Bichi dake bayan anguwarku. Budurwa ƴar kimanin shekaru goma sha bakwai, ana ruwan sama mai yawan gaske, ita kuma tana durƙushe tana naƙudar haihuwa data fara tun yammaci, fahimtar haihuwa zatai ya sata zuwa wannan kangon ta ɓuya, bata sha wata wahala ba ta haihu, tsabar taurin zuciya ta yanke cibin jinjirin da kanta sannan ta naɗeshi a zani ta koma gefe ta huta batare da ko kallonsa tayi a matsayin sa na wanda ya fito a jikinta ba, kafin ta tashi ta sake ɗaukar jaririn ta fita a cikin dai wannan ruwan ta tafi can bayan layinsu a ƙafa ko tsoro bata ji ta tona bola ta ajiye shi. Babu ko tausayi balle imani a tare da iya ta zuba tarin bolar nan a kansa ta rufe ta juya tabar wajen ranta ko gezau babu na nadama balle jin tausayi ta koma gidansu. A zatonta shike nan shike nan tayi AJIYA A DUHU na har abada, sai dai kuma shi ALLAH babu ruwansa, yayi alƙawarin saina more wannan duniyar, harna taka ƙasa nazo inda take da ƙafafuna a yau a yanzu..”
Tunda Sille ya fara wannan bayanin jikin Mamy ke mazari. Zufa kam ba'a magana tai mata sharkaf. So take tai magana amma ta kasa, dan gaba ɗaya lissafinta ya birkice... Sille dake kallonta ya wani kwashe da dariyar ƙeta yana miƙewa. “Bara na barki haka, dan na fahimci ƙwaƙwalwarki na buƙatar yin cikakken tunanin daya fi wannan bayanin nawa. Kuɗina kuma daga yanzu zuwa safiyar gobe ki tabbatar kin haɗa min su. Idan ba haka ba zan sake dawowa na amsa da kaina, idan na dawo kuma zan fara ganawa da Alhaji Aliyu Darma ne kafin ke. Dan ya kamata shima fa ya tuna da abokinsa na yarinta Junaid, ya kuma san alaƙar Kamila da Fateema ta asali. Na barki lafiya mahaifiya”....
Iya kwatanta muku Mamy a cikin tashin hankalin da take ciki abu ne mai wahalar gaske, kawai dai kowa ya ƙiyarsta a ransa, dan kuwa Sille ya tafi ya barta a wani irin mummunan yanayi ne mara kwatankwacin kintace. Binne sirri mai girma irin haka a kai kaɗai batare da kowa ya taɓa sani ba, sai bayan tsahon shekaru kwatsam wani yazo yace maka shine wannan sirrin naka, har ya labarta maka exactly abinda ya faru a shuɗaɗɗen yanayin, bayan kayi imanin babu wani mahaluki daya ganka, tunda gashi har tsawon shekaru babu wani daya taɓa kwatanta maka ya sani ko'a fuska, shi kuma wannan yaron jariri yake sabuwar haihuwa da baya magana baya gane komai ai ruɗanin bashi da kwatankwaci. Yo ko gulma kayi da miji ko ɗa ta fita ya kake shiga ruɗanin mamaki balle irin wannan na Mamy, ai sai ka rasa ina zaka kama ina zaka riƙe ma gaba ɗaya. Ga zancen Sille ya tabbatar mana akwai alaƙa tsakanin Abah da Junaid ubansa, kenan dai akwai AJIYA A DUHU tsakanin amintakar Kamila da Oum ma tun asali tun fari. Babbar magana. Kumuje zuwa kudai, sannu a hankali komai zai warware kansa dai....
____★
Motar AA dake dawowa gida na shigowa gida Sille na ficewa. Da mamaki yake kallonsa, duk da ba fuskarsa ya gani da ƙyau ba kamar a gidan Hajiya Turai. Amma gaba ɗaya zubin mutumin da wata tafiyar rangajin tantirai da take bata mai ba. Kasa haƙuri yay sai da ya tambayi maigadi wanene?.
Kai tsaye maigadi yace, “Ranka ya daɗe mai gyaran ruwa ne. Pipe ne ya fashe a sashen Hajiya ƙarama shine ya gyara.”
Jimmm AA yay yana kallon Sille da yay nesa da gidan kaɗan ta cikin mirror ɗin motar, a ransa yana jinjina kalmar mai gyaran ruwan ƙwarai da gaske. Dan zubin mutumin sam bai masa kama dana mai aikin arziƙi irin wannan ba. Amma sai bai takura ba yaja motar ya shige ciki. Tarkacen daya sayoma ƴar rigimarsa ya ɗiba ya wuce sashensu. Samunta yay tana barci anan falon inda ya barta, ya sauke ajiyar zuciya yana girgiza kai. Kitchen ya wuce da kayan ya ajiye komai a inda ta dace, sannan ya dawo ya kwashe abubuwan data baza na ciye-ciyen da tayi suma yakai kitchen ɗin ya ɗauraye na wankewa ya ajiye na ajiyewa. Koda ya dawo ɗaukarta yay gaba ɗaya ya haura sama da ita. Dan yasan wannan kuma barcin in sha ALLAHU ita da farkawa sai kusan sha biyun dare, koda yayi barci shima sai ya tashi saboda wanka kawai take yi da salla tazo ta kanannaɗe jikinsa. Tana samun yanda take so zata sake komawa barci. To daga fa sallar asuba kuma bazata sake kwanciya ba sai wata yammar kamar wannan, idan kuma anyi sa'a ta daure yanayin magrib zata kwantan. Oum ma data fahimci yanayin nata ko nemanta batayi idan yamma tayi taji shiru. Wani lokacin kuma acan sashen take barcin sai sun gama hira da cin abincin dare yake ɗakkota su dawo nan..
______★
Washe gari tunda wuri ya mata wayo suka bar gidan zuwa MAWAAD. Ta haka ne ƴan kai lefe suka tafi lafiya bada saninta ba. Lokacin da suke dawowa gida bayan la'asar kuma sama-sama ta gaida Oum ma ta shige bedroom ɗinta ta kwanta sai barci.
Da daddare sunyi zaman cin abinci Babban Yaya ke tambayar Lilly fa? Dan tun jiya rabonsa da ganinta a gidan, kwana biyun nan kuma ya fahimci Nuwaira da Oum ke girkin dare banda Maanal ɗin. Oum ta ce masa tana barci a ɗakinta tunda suka dawo aiki. Dan ko sashensu ma bataje ba. Mamaki ya kama Babban Yaya, yace, “Bata da lafiya ne? Barcin yamma haka”.
Kafin Oum tai magana Yaya Fawzan da bakinsa baya iya shiru ya ce, “Anya Babban Yaya Lilly na lafiyar nan kuwa?. Barci dai barci dai maybe akwai malaria tare da ita”.
RK dake danne dariyarsa da ƙyar yay fuska da faɗin, “Sai fa malaria ɗin. Saurayen ne na yanzu ɗika-ɗika, da sun ciji mutum kuma sai ciwo ba sauƙi. ALLAH dai ya ƙaremu da lafiya”.
Harga ALLAH Oum bata gane shaƙiyancin RK ba. Kai shi kansa Yaya Fawzan bai hasko komai ba sai da yaga babban Yaya yayi wani miskilin murmushi kawai. AA ma da bai fahimta ba da farko ya ce, “Inaga ya kamata ai feshi a gidan nan gaskiya. Dan ɗan zaman da mukai jiya a waje nima sai da naji kamar zanyi zazzaɓin alamar nasha cizo”.
A wani ɗage RK ya ɗan dubeshi ya ce, “Ai tunda baka kwanta ba da alama kai naka cizon na musulmin sauro ne. Wanda ya ciji ƴar gidan Oum dai kamar yafi iya cizo”.
Yanzu kam sosai AA ya kallesa, hakama Yaya Fawzan. Ido RK ya kashema Fawzan. Yaya Fawzan ya kwashe da dariya dan ya gano kam yanzu. yace, “Ohhhhh na gane na gane, lallai wanan sauro kam ya iya cizo gallari”. Sai suka sake kwashewa da dariya shi da RK. Ƙasa-ƙasa suke zancen shiyyasa Oum bata jinsu. Shi kuma AA a tsakkiyarsu yake. Babban Yaya na kusa da Oum. AA da sai yanzu ya fahimci inda iskancin nasu ya dosa ya girgiza kai kawai. Bai sake magana ba saboda Oum da babban Yaya dake wajen, amma yayi alƙawarin sai ya rama su duka..
________★
Washe gari ƴan Kano da suka rabu biyu wasu suka tsaya Zaria gobe idan ALLAH ya kaimu zasu taho da amarya Najma, wasu kuma suka wuto nan abuja dan anan za'a ɗaura auren Ameerah da Maimoon dan sauƙaƙama mutane. Zasuyi tafiyar yamma ne saboda bikin da zasuyi suma can Zariya, anan kuma Abuja gobe za'ai kamu in sha ALLAHU anan gidan Darma. Asabar a ɗaura aure ai dinner, lahadi walima da safe, da yamma ai buɗar kai shike nan amare su shige daga ciki.
Ƴan Kano na gama hutawa aka kai lefen Ameerah. Lefen ya ƙayatar da kowa dan su Maanal sunyi ƙoƙarin saka abubuwa na girma. Sosai kuma Hajiya Shuwa da ahalinta da suka iso da ƴan Katsina suma da sukace komai ya wuce suka dai-daita da Hajiya Shuwan tun kai kuɗi da su Baba Sardauna sukai. Tukuyci mai tsoka su Maanal suka samo. Babu dai dangin Mamy ko ɗaya a ƴan kai lefe hakama Nibras ko ƴan Kano bata zo ta gaidar ba. Suna dawowa daga kai lefen Ameerah aka kuma biyosu da lefen Maimoon. Hummm shima dai su Hajiya Shuwa sun rigirgiza kayan arziƙi sai dai ace sambarka kam. Sai kuma abi ma'auratan da addu'ar zaman lafiya da zuri'a masu albarka.
A ɓangaren Mamy yaƙe kawai take da dauriyar dole har ta fito ta gaishe da ƴan Kano su Mah-mah, dan su Umma sune a Zaria zasu taho da amarya Najma gobe idan ALLAH ya kaimu........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣0️⃣4️⃣
______________
.....A yanzu gaba ɗaya hankalin Mamy ba'a kan auren nan yake ba. Dan Sille ya gama rikita mata al'amari gaba ɗaya. Amma dai tana ta ƙoƙarin danne yanayin ta dan bata fatan kowa ya san halin da take ciki a wannan gaɓar. Abinda ya bama Abah mamaki yanda ta sake ba kamar bikin Maanal da AA ba. Amma dai baice komai akan hakan ba.
A ɓangaren Sille kam a yanzu itace mai nemansa a waya