Author : Bilyn Abdull Category : Romance
sai ya rasa baki magana. A take Shahidah ta bada tukuyci ita da Amal, wannan tukuyci ya sake girgiza su Nasiba.
Maanal ɗin kanta sai da lefen ya girgizata, dan tabbas ya ɗan tambayeta wasu abubuwa a Chaina, musamman colours haka da sauransu, amma bata ma kawo ma ranta mi zaiyi da shi ba. Haka aka gama murna da kallon kaya aka sanya albarka aka kumayi videos Dan nunama Ammie da Daddy. Maanal dai tun jiya bata sake saka ango a idonta ba har zuwa yanzu da za'a fara shirin walima, bata damu da rashin ganin nasa ba, ba kuma ta tambayi kowa ba. Ita gaba ɗaya ma kasancewar ƴan uwanta a tare da ita ya sakamata farin ciki da mantar da ita komai. A haka lokacin walima yayi, Hajiya Shuwa da mai kwalliya suka shigo, duk da dai yau ma Hajiya Shuwa tace bamai yawa za'ai mata ba. Amma kafin ayin ma tasha turare harda na tsiya, kai Hajiya Shuwa tasan sirrin ƙamshi na kata'i, tsaf aka kwalliyeta aka sakata ta shirya cikin Abaya mai ƙyau fara tas da adon golden. Matuƙar ƙyau Maanal tayi kam kamar ka saceta ka gudu. Ga wani ƙamshi mai azabar daɗi tana bulalawa. Anan harabar gidan aka shirya walimar, dan tabbas gidan su AA babbane matuƙa ta yanda basa jin ko ɗar idan sabga ta tashi. Idan ba irin su dinner ba da wahala kaga sun kama hall ɗa sunan yin wani event a yayin sabgar su. Sosai walima ta ƙayatar dan iya mata ne kawai, sai malamai da aka gayyata suka zuba lectures masu ratsa jiki da saka nutsuwa musamman akan ma'aurata da shi kansa ma zaman auren da daɗin dake cikinsa da ƙalubale.
(Please muɗan yi magana anan mana. Akwai wani abu dake cin raina a duk sanda naci karo da shi a social media. Idan budurwa na nuna ɗokinta da farin ciki a ranar aurenta ko lokacin shagalin biki sai kaga ana faman zaginta ko tsoratar da ita akan al'amarin maza ko auren ma gaba ɗaya a comment section. Hummm jama'a mu fuskanci wani abu fa, ita rayuwa akwai jarabawa da ƙalubale a cikinta, sannan ba lallai abinda kai aka jarabceka da shi a jarabci wani ba. Ba lallai dan ke baƙya jin daɗin rayuwar aurenki kice kowa ma haka take ba ko haka zata faru ga wasu ba. Zata iya yiwuwa ita jarabawarta ba'a rayuwar mijin bane ko halayyar mijinta. Wallahil azim yanda muka san mata da yawa nashan wahalar rayuwar aure da rashin ƴanci a gidan aure to akwai mata da yawa kuma dake jin daɗin aure da farin ciki a cikinsa. Akwai matan da dayawa suke samun soyayya da kulawa ga mazajensu fiye da rayuwar novels. Dan ALLAH mubar karya zukatan yaranmu da ƙannenmu masu tasowa akan abinda UBANGIJI ne kawai mai ilimin saninsa. Mu dinga ƙarfafasu da hakan, koda bata samu yanda take hangeba zuciyarta zata wadatu da abinda taje ta samu, dan shi dama ɗan adam ai ba komai yake samu hundred percent a rayuwarsa ba. Dole idan aka baka farin ciki anan a jarabceka anan kuma. Yanda muka san akwai maza marasa adalci ga mata haka ma akwai adalai masu tausayi da nuna kulawa ga iyalansu da yawa a cikinmu. Akwai kuma hatsabiban matan da suke wahalar da mazan su kuma amma mazajen nasu na haƙuri da su. Dan haka yake ƴar uwa, kada ki wani bari zuciyarki ta raunana kota karaya da tunanin ko hangen gidan miji KURKUKUN AZABA ce, dage kiyi addu'a ki miƙama UBANGIJI lamarinki da zaɓinki ki tsarkake zuciyarki, ki yarda ALLAH mai rahama ne mai jin ƙai, kiyi addu'ar samuwar miji na gari mai addini, mai kamala, mai neman na kansa, wanda ya iya ƙyaƙyƙyawar mu'amula da mutane, mai tausayin iyayensa da ƴan uwansa wlhy in sha ALLAHU, ALLAH zai baki fiye ma da wanda kika roƙa ɗin in har kema kin kasance tsarkakkakiya, kin wadata zuciyarki da tsoron ALLAH, baki kusanci ZINA ba, kin nisanci MAƊIGO, kin nisanci shaye-shaye, kin nisanci ƙawayen banza da samarin banza ƴan aci duniya a titi. Kin ƙyautatama iyayenki kullum kina zagaye da addu'arsu, kin ƙyautata mu'amularki da kowa, kin cirema kanki hassada da gulma da aibanta wasu ko rayuwar wasu da danne hakkin mutane komai ƙanƙantarsa. Ajiye batun ƙyale-ƙyalen matan media duk buge ne wlhy, mafi yawansu hodace da zanen jagira dana jambaki sai filter da ƙaryar an tara amma komai fanko ne da haɗa-haɗe, mafi yawansu ƴan koda rigima da zubda mutunci ne sai na ɗinka na saka na saya na saka dan na burge mabiyana a media. Wata idan kika ganta a zahirinta da asalin rayuwarta da sanin wacece ita wlhy har gaban abada bazaki sake marmarin zama irinta ba in har kina jin tsoron ALLAH. Dan haka ki rufama kanki asiri, ki gargaɗi zuciyarki daga barin wannan ƙyale-ƙyalen banza da wofin dan ita MEDIA GIDAN KASHE AHU CE, sannan ALALAN GERO CE. Ki dinga tunawa ba farkon ba ƙarshen, da yawa sunyi tashen a mediar da fariyya da alfahari da ƙaryar amma tarihinsu ya shafe ko labarinsu baka sake ji, kuma suna a cikin duniyar ba mutuwa sukai ba, kawai dai an ƙyanƙyaso waɗan da suka fisu iyawa ne dan kowa fanɗarewar wani babban wani ne, wani ma sai dai a kira shi kakan wasu. To kwantar da hankalinki ki ɗaurama dokin rayuwarki sirdi da linzamin banbance abinda ya dace da ruɗanin duniya mara amfani ki rungumi mijinki ki godema UBANGIJI ki ɗaya baki shi, ki wadatu da ni'imar da ALLAH yay miki ta kasancewa a ƙarƙashin bautarsa dan aure dai ibada ce, sai ki zauna lafiya kiyi barci mai daɗin gaske, ana hayya-hayya, ke kina salama-salama saboda UBANGIJI ya tsaya miki. Mu dinga yawaita addu'ar samun zaman lafiya da soyayyar mazajenmu da rage zafin kishi, mu kama sana'a, mu rage buri, mu rage zalunci, wlhy zamu kasance masu nasarori bama nasara ɗaya ba. Karki sake wata banza ta canja miki tarbiyyar uwa da uba akan abinda maybe ita sai da ta saɓama ALLAH ta samu. Ɗaukesu ƴan a kalla ai dariya da mamaki a wuce kawai ba ƴan a ɗauki darasi ba ko yin koyi dan ke dasu tamkar nisan samaniya da ƙasa ne a daraja wlhy. Kina da ƴaƴa, in baki haifa ba ma zasu zo da ikon ALLAH, idan auren ne bakiyi ba zakiyi mijin aurenki duk nisanku sai ya isko ki kada kiyi tunanin sai kin ɗau waccan hanyar zaki sameshi shi mutunci madara ne idan ya zube ƙasa baya kwasuwa. ALLAH ya baku mazaje na ƙwarai, ya haɗamu baki ɗaya ya bamu farin ciki a gidajen aurenmu. Masu fuskantar jarabawa UBANGIJI ya sassauta ya samar da farin ciki da kwanciyar hankali a rayuwar aurenku da mu baki ɗaya. Mu dage da addu'a ƴan uwa, mu cirema zukatanmu son mallakar maza ta kowane hali, mu tashi mu nema sana'a, mu tsarkake zukatanmu mu yawaita istigafari, mu gyara ibadarmu da mu'amularmu da mutane. Dan wlhy a wasu lokutan sharrin da kake aikatawa ga mutanen dake a zagaye da kai ta fuskar rayuwa ko rayuwar social media ɗin nan da muka raina sai kaga ya dawo cikin rayuwarka ka gagara gane komai, harshenka ya kasance mai kaifi a wajen mutane, kai kuma sai mijinka ya zama mai kaifafa maka a cikin gida ko dangin miji. Mu kiyayi bakinmu da hannayenmu musamman a wajen comments ɗin nan na social media da muke rainawa, dan wlhy babu makawa sai an tambayemu, saboda ko (a) kika rubuta sai Mala'iku sun rubuta suma a littafinki. Abin tashin hankalin wani ma ko wata har abada bazaku taɓa haɗuwa ba a zahirin rayuwa balle ka roƙa gafarar sa, kai wasu ma ba karanta comments ɗin suke ba balle susan dake kin kuma ɗaurama kanki nauyi a banza a wofi dole kuma ki biya bashinsa da ayyukanki ko ke a baki nasu na sharr. Idan kuma ya karanta ɗin kin ƙuntata mata da comments ɗinki ko kin ƙuntata masa har ya kamu da wani ciwo ta sanadinki tofa aiki ya sameki dan sai kin amshi wannan sakamakon koda su ba mutanen kirki bane, balle bamu san tsakanin UBANGIJI da bawansa ba. Wlhy ƴan uwa idan Bamu kula ba muna cikin masifa, dan wayoyin nan dake a hannunmu hummm. Mudai sani bazamu iya biyan bashin zagi, ko aibantawa, ko cin hakkin mutane a ranar gobe kiyama ba, dan yanda muke tunanin lahira ta wuce da sanin mu, UBANGIJI ba abokin wasanmu bane. Hakkin mutane a kanka koda na kallon banza ne ba ƙaramin tashin hankali bane da nauyi mai girma da bazaka iya biyansa a ranar lahira ba. Tsaiwar mala'ikan mutuwa a kanka kawai ya isheka tashin hankali mai girma balle aje ga zare ran😭🙏, amsa tambayoyin kabari😭, kwanciyar kabarin kansa 😭, tsaiwar hisabi, ƙishirwa, zafin rana, karɓar sakamako daga littafinka, haye siraɗi, makomar gaba ɗaya data kasance zaɓi guda biyu na wuta ko aljanna. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un ya RABBI badan halinmu ba ka gafarta mana mu da iyayenmu😭🙏, dan ALLAH duk wanda na taɓa munanawa koda da magana ne, koda a rashin sani ne ya gafarceni, sai dai in kaima ka munana min ne na maida maka murtani, dan mutuwa kullum ƙawace ga mai rai, kamar yau ne zakuji ance babu Bilkisu, na tafi kamar ma ba'a taɓa yina ko yayina ba, na tafi daga ni sai ayyukana, ƙyale-ƙyalen duniyar da ake alfahari da faɗi tashi da wahalhalu duk anan zamu barshi kamar bamu wahala a nemansa ba. Ya rabba, ya arrahaman rabbi mun tuba. Mun tuba ya rabbi.🙏😭. Dan ALLAH mu bar tsorata yaranmu da ƙannenmu da abinda bamu da ilimin sanin gaibu a kansa, rayuwar aure rahama ce mai zaman kanta, ni'ima ce. ALLAH ka bama kowa zaman lafiya da mijinsa da zuri'arsa baki ɗaya. Ina muku fatan alkairi a duk inda kuke tare da fatan ALLAH ya karɓi ibadunmu yasa bamuyi kyakkyawan ƙarshe. ALLAH yasa muna a cikin ƴantattun bayi. Ya rabbi kasa abinda ya rage mana na rayuwa ya kasance mai amfani a garemu duniya da lahira.😭🙏........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖6️⃣8️⃣
______________
.......Alhamdullah walima ta kasance cikin aminci, amarya Maanal tasha kuka jikinta yayi sanyi sosai, dan idan ta haɗa da lectures na nasihar iyaye da gargaɗi da wannan ya sake tabbatar mata da aure ba wasan yara bane. Dan duk abinda akace IBADA ne to lallai dole ne ka shirya da shiri na musamman. Dole ne ka yarda da dariya a cikinsa da kuma kuka a wasu lokutan, ita aljanna bata samuwa a kwance, kamar yanda kasan baka samun kuɗi a cikin mafarkinka sai ka motsa ka nema. Idan har duniya da take ba komai ba bata samuwa a garemu cikin sauƙi, taya zamu yi tunanin aljanna samunta zai kasance mana mai sauƙi. Mata ALLAH mu farka mu ajiye wani ka-ce-na-ce na hallayar maza mu nema aljanna kawai sune a ruwa. Dan aljanna duniyace malam, komai fa akwai a ciki, wohoho Bilyn ku a aljanna ai ba'a magana zamu tsula tsiyarmu in sha ALLAHU. (ALLAH kasa mu ɗin ƴan aljanna ne😭. ALLAH ka sani mun guji iskancin nan a duniya da gudun hakkin mutane duk da yanda suke da daɗi ALLAH kai mana sakamako da aljanna domin rahamarka😭🙏, mun tuba ka yafe mana kurakuranmu ka yafema iyayenmu ya rabbi ya arrahaman, ya arrahim, ya almalik, ya malikil mulki ziljalalu wal'iram😭🙏).
Ba lectures ce kawai ta gudana a wajen ba, anci ansha tare da raba souvenirs masu ƙyau da ɗaukar idanu. Abinda zai baka dariya da birgeka hoton AA da Maanal suna yara ne a jiki. Sai mutane da yawa basu ma fahimci ango da amaryar bane ba a jiki, ita kanta Manaal abin ya bata dariya da birgeta, har sai da ƙwalla ta cika mata idanu dan kuwa hoton dake jikin ita kanta bazata iya tuna sanda aka yisa ba, tana ƙarama sosai, sai su Amaal ne keta ƙoƙarin ma tunowa suma suna dariya. Bayan kammala walima amarya Maanal ta koma ciki, yayinda su Nene suke shirin wucewa. Amma Oum tace ina ai saifa gobe da safe in sha ALLAHU kowa zai tafi, dan haka suma dole hakan zasuyi, anjima da dare ma akwai event na ƴammata da yaran Darma Family suka haɗama amarya. Rasama abin faɗa Nene tayi, wai su mutanen nan basa tausayin kuɗaɗensu ne...
Dan shima dai acan ango wani ɗan biki-biki matasan Darma Family suka shirya iya su maza, shiyasa ma abokansa suma dai duk sai gobe zasu tafi. Shi dai dauriya kawai yake dan harga ALLAH a takure yake. Hajiya Shuwa ta haɗa masa bomb da turaren da take zazzagama Maanal a jiki, shiyasa ma yaketa kauce-kaucen haɗuwarsu a yau gaba ɗaya. Sosai abokan nasa suka saka shi a gaba musamman abokan karatunsu na primary da Secondary da suka san wacece Maanal a wajensa, tunda mafi yawansu sun sha duka da rashin arziƙinsa akan taɓa ta, ga rashin kunya itama ba raga musu tayi ba duk da sun girmeta. Haka suma dai wanda sukai karatu a tare na jami'a duk da bai taɓa zama ya bama wani labarin a cikinsu ba kai tsaye, sun dai tsinta wasu a cikin abubuwan da suka shafetan a wajensa sai kuma jiya sukaji komai da ganin hotuna a wajen dinner. Duk iskanci da shaƙiyancin da suke masan bai yarda ya kula ko wannensu ba, to kuma dama dai sun san halinsa na rashin son yawan magana. Yakan ɗan murmusa dai dan shi kam duk sun addabesa, badan Oum datace yau ya kwana anan ba dan su Nene sun kasa sakewa saboda jiya ya kwana a gidan da tuni ya fece gida abinsa.....
__________★
Kuce dani ina hajjaju Mamy ne? Tana can a sashenta abin duniya ya matuƙar isarta, dole kuma ta danne ta haɗiye saboda wasu a cikin ƴan Kano a sashenta suke zaune. Badan ALLAH ba dole ta taushe tafashen azabar baƙin cikin dake zafafa zuciyarta tanata yaƙen dole ga ciwo na cinta a tsaitsaye jiya ma sai dare akabi aka saka mata drip da allurar barci a ciki sannan ta samu ta rutsa, amma abinda ya faru a wajen dinner ɗin nan ya matuƙar tsaya mata a rai. Kowa Oum yake tayawa murna matsayin uwa, komai za'ai ta ɓangaren uwa Oum Mc ke ambata. Babu mai kallonta, babu kai tunawa ita ta ɗauka cikin Ajwaad wata har goma sai a cikin na sha ɗaya ta haifesa. Tsabar ma an maida wulaƙantaciya ita aka dinga nunawa matsayin step Mom ɗinsa wai. Ya rabba wannan abu ya Zafafa mata zuciya. Har sai da taji idonta na gani bishi-bishi alamar jini ya haura mata sama sosai. Shiyyasa suka baro hall ɗin kafin ma a tashi. Koda suka shigo gida saita sakar ma Babban yayarsu dake riƙe da ita kuka dan can suka baro maman Saheeba tace sai taga komai. Ita kanta yayar tata wata irin masifa take ji na tafaso mata daga ƙirjinta, amma dole ta danne ta shiga lallashin Mamyn da nuna mata kuka fa ba shine mafita ba. Dole suzo susan abinyi dan al'amarin na Oum fa na neman zame musu ɗan zane. Ga tsagwaron rainin hankali a ciki, yo inba rainin hankali ba taya zata shirya wannan abubuwa haka batare da ita Mamyn an nuna wani matsayinta ba matsayinta na mahaifiyar Ajwaad balle su danginta, sannan ga auren Fawzan da shima akai matuƙar raina musu wayo a gefe, wanda da ƙyar suka taushi Mamy ɗin akan kar tace komai har a gama wannan taron kowa ya watse sannan su zauna da Abah. Dan basu so kowa ya tafi dasu a baki akan hakan.
Yau ranar walima yanda Mamy ta nema ɗaga hankalinta yasa suka taru a kanta harda dangin mahaifiyarsu da sukazo wajen biki suka dinga tausarta. Wasu suna gaya mata gaskiya da tuna mata itafa ta ɗauka yaran ta bama kishiyar tata. Miyasa kuma zataji zafi dan yanzu an danganta yaran da ita. Wasu ko goyon bayanta suke da tayata kishi. Haka dai sukaita cece kunesu batare da su Oum sun ma sani ba. Koda lokacin walima yayi tace bazata fita ba ƙyaleta kowa yayi. Tabbas Oum ta lura bataga Mamy ta fito ba, sai kuma hayaniyar mutane da maƙwafta masu shigowa da abokan arziƙinsu nan cikin abujar ya ɗauke mata hankali. Ana gama walima kuma sallar magrib kawai akai aka shiga shirin faty na yaran family ɗin da suka shiryawa amarya. Anan cikin gidan shima akayi a garden, yanzu ma amarya Maanal tasha ƙyau harta gaji cikin doguwar rigar atamfa data mata ƙyau sosai. An gudanar da komai cikin aji da halin girma. Amarya Maanal tasha kyaututtuka daga ƙannen ango dan mafi yawan yaran family ɗin mata su AA sun girmesu, sai dai kamar iyaye irinsu Majdiya, ko su Nuwaira matar su RK matsayin iyayen su AA ɗin suke ai. Ƙarfe goma an tashi kowa ya nema makwanci. Yau ma cike da murna Maanal ta kwanta ƴan uwanta zagaye da ita.
Washe gari kam da wuri Nene tasa suka gyara ko'ina na sashen Maanal. Dai-dai nan mota ta iso daga Kaduna ta kayan gara daga Daddy sai kuma kayan rabo da zasuyi na buɗar kai. Dan zuwa ƙarfe ɗaya na rana an gama shirya Manaal cikin wani arnen lafaya da yay mata ƙyau. Ana idar da sallar azhar sama-sama sukaci abincin da aka kawo musu na lunch, sannan sukai zaman sake yima amarya Maanal daketa hawaye nasiha. Bayan sun kammala sashen Oum suka nufa da Maanal dan acan za'ai buɗar kai. Dole suma dangin Mamy nan suka zo aka haɗu gaba ɗaya. Anyi buɗar kai, tare da damƙama su Oum kayan rabo na al'ada daya bada