AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   178 / 213

531K to 534K   out of 636.6K words

tsitstsinta da jinin Mabera da Yaya Fawzan ya nausa daya ɗan ɗiɗɗiga a carpet ɗin falon daya kasance fari harda haƙorinsa ɗaya. Maigadin su Hajiya Shuwa ne ya sake tabbatar da tabbas motoci biyu baƙi sun shiga gidan. Ƙaramar mota bayan dawowarsu massalaci sai da kusan awa guda, motar kuma ta jima a street ɗin sai dai hankalin kowa da yake yana akan yankan raguna ba'a lura ba. Shi kuma daya lura harga ALLAH bai kawo komai ba ganin motar babba ce shiyyasa baiyi magana ba tunda securitys ɗin farkon shigowa sun bari. Sai bus, shi a zatonsa ma dangin gidan ne suka zo salla ko yara tunda yaga sukayi hakan.
         Bayan ɗan sandan ya gama jin maigadi ya juya yana kallon su RK. “Babu cctv camaras a gidan nan ne?”.
      “Babu gaskiya, dan Yaya bai cika maida hankali akan irin waɗan nan abubuwan ba. AA ne ma kwanaki yay ƙoƙarin a saka ɗin amma ba'a saka ba suna nan ajiye. Ban san miya hana a saka ɗin ba”.
           “Amma gida kamar wannan ya dace ace akwai cctv camaras, ban san miyasa manyanmu dake cikin gari like haka suke da irin wannan sakacin ba. Yanzu rayuwa ta canja sosai, yanda suke tunanin tsaron cikin Abujan ba haka bane ba. Sannan kowa zai iya canjawa akan kuɗi”.
     “Wannan gaskiya ne, kawai kasan idan zuciyar mutum a tsarkake take sai ya ɗauka kowa ma haka tashi take. Ba su dake nan cikin Abuja ba hatta mu da muke a Kano kaf family ɗinmu bana jin akwai wani mai camara ta tsaro a cikin gida gaskiya”.
        Sosai mamaki ya kama ɗan sandan, ɗaukaka irin ta family ɗin Darma da yanda sukai suna a ƙasar nan ai da mamaki, sai dai da yake kowa da ra'ayinsa a rayuwa, maybe suna da dalilinsu na ƙinyin hakan. Juyawa yay ga yaransa ya basu umarnin zuwa musu da securitys ɗin dake tsaron gate ɗin shigowa street ɗin da wanda suke a ƙarshe.
      Babu jimawa sai gasu. Tambayoyi suka shiga yi musu ɗaya bayan ɗaya. Wanda suke a ƙarshen gate sun tabbatar basu san da shigowar motocin ba, dan ta farko suka biyo sakamakon gidan Darma shine na biyar a farkon shigowa street ɗin tanan ɓangaren. Ta farkon shigowa kuma sunce ɗan uwansu ne suka bari a gate ɗin abisa lamunce musu zuwa sallar idi bayan shi ya fara zuwa ya dawo, su kuma sai suka tafi massallacin yarbawa. Amma koda suka dawo suma sai basu sameshi ba, sai dai gate ɗin arufe dan har mutane ma na jira, ganin wayarsa a wajen yasa suka ɗauka ko ya zagaya ne, sai yanzun nan da suka ji shirun yayi yawa suma suka farga shine suka fara neman sa sai kuma akai kiransu nan.
      “Ba akwai camaras ba a wajen?”.
  “Akwai Sir har ma guda biyu, ɓangaren shiga da ɓangaren fita.”
    “To Alhmdllh mun samu mafakar kamawa.”

      An ƙara cika street ɗin da ƴan sanda, dan labari har ya fara fita gari. Anan kuma shugaban tawagar jami'an tsaron sun iso gate domin binciken cctv footage, sai dai abinda ya hargitsa musu lissafi sam babu wani footage na shigar baƙin motsicin, hasalima daga 8am da wasu mintuna footage ɗin suka tsaya. Koda suka duba camaras ɗin sai suka ga ai duk an tsaidasu a aiki ne. Hakan na nufin lallai al'amarin babbane, kuma koma suwaye da shirinsu suka shigo shiyyasa komai ya tafi musu akan tsari. Hakan kuma na nufin su kansu securitys ɗin sai an bincike su....

      ALLAH sarki idan kaga halin da su Baba suke ciki dole ka tausaya musu. Bama su ba har maƙwafta da sauran mutanen anguwa al'amarin ya ɗaga musu hankali ya kuma basu mamaki ƙwarai da gaske. Gashi babu wata makama ko zare da aka kama akan al'amarin, maigadin su Hajiya Shuwa da yace yaga motocin bai iya riƙe ko number ba sai kalarsu kawai. Dole aka maida hankali akan maigadin su da masu aikin nama dake asibiti, dan yanzu sune kaɗai zasu bada abinda ake buƙatar sani. Gashi basa a hayyacinsu.....

________★

       A nan Kaduna kam abubuwa sun kwaɓe matuƙa, musamman akan Nazeerah. Ƙiri-ƙiri ga haihuwa a kusa amma ta kasa haihuwar sai jini ke zuba na tashin hankali, da ƙyar likitoci suka samu nasarar tsaida shi aka fara shirye-shiryen yimata cs. Yazeed yaso botsarewa akan saka hannu, dan yace shi a yanzu ba matarsa bace ba, tunda ya dawo hayyacinsa ya rubuta mata saki uku. Kuma a tambayeta tunda suka dawo gida ya sake yarda ya mu'amulance ta? Kai ko hannu bai ƙara kaiwa a kanta ba. Hankalin Sabuwa yay ƙololuwar tashi da jin zancen Yazeed, zata fara zage-zage ma'aikatan asibiti sukace zasu saka a fitar da ita duk da itama bata da lafiyar. Dan ana shirye-shiryen yimata ɗori ne a hannunta da Yazeed ya karya. Shiru tayi kodan securitys ɗin da aka kirawo. Amma sai ta shiga laluben wayar mijinta..........✍️




*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣5️⃣6️⃣


______________



.......Daddy ne ya tursasa Yazeed saka hannu domin yima Nazeerah cs, haka badan yaso ba ya sanya. An shiga da ita babu jimawa suna zaune shiru sai Sabuwa dake ta faman neman layin mijinta yaƙi shiga, Nusaiba na latse-latsen waya ta gano abinda ke faruwa a ƙasar. A matuƙar ruɗe a fili ta furta, “Mun shiga uku familyn Darma kuma?...”
      A tare duk suka juya suna kallonta. Basira tace, “Miya faru da familyn Darma ɗin kikema mutane ihu a asibiti?”.
     Gaba ɗaya jikin Nusaiba rawa yake, ta muƙama Salima dake a kusa da ita wayar. Salima da taji kamar an bugar mata kai da ƙarfe a diririce ta miƙe tana faɗin, “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un Daddy wai anyi kidnapping ahalin Aliyu Abubakar Darma gaba ɗaya dake Abuja yau bayan sakkowa sallar idi”.
       Kaɗan ya rage Daddy ya faɗi saboda yanda ya zaburo ya amshi wayar hannun Salima. Ammie kam sumar tsaye tayi dan wani irin dokawa zuciyarta tayi da ƙarfi. Sauran yaran ma duk a firgice suke. Dai-dai nan kuwa sai ga kiran Shahidah ya shigo wayar Daddy. Da ƙyar ya iya ɗagawa ya kai kunne. Cikin kuka Shahidah ta sake maimaita masa abinda suka gani yanzu. Sai kawai Daddy ya zube a kujera jagwab, sai Yaya Yazeed ne ya amshi wayar......

_________★

       Daga Abuja su Mabera Kaduna suka nufa. Ransu fes musamman ma Sille dake jin burinsa na duniya ya kusan cika. Dan an raini zuciyarsa ne da ƙiyayyar Kamila tun yana a tsumman goyo, dan haka ya girma da burin ɗaukar fansa a kanta. Sun iso cikin Kaduna huɗu ta wuce, sarai Mabera na ganin kiran Sabuwa amma yaƙi ɗagawa saboda hankalinsu ya tashi da ganin cikin ƙanƙanin lokaci labarin kidnapping ɗin ahalin Aliyu Darma ya karaɗe ko'ina na media. Abin ya basu mamaki, dan yanda suka tsara komai basuyi tunanin hakan ba. A ganinsu ko za'a farga da abinda ya faru sai irin zuwa gobe ɗin nan haka. Amma sai gashi ko awa biyar ba'a cika ba al'amarin ya fito. Wanene ya buɗe musu aiki haka ne?.
       Sun riga sun shigo Kaduna, dan haka babu ɓata lokaci suka wuce gida da taimakon Sille suka tattara komai daya shafesa mai muhimmanci da nata ita kanta sannan ya rubuta takarda ya ajiye mata suka fice dan basu da isashen lokaci. Sake ɗaukar hanyar Abuja sukayi, gudu na tashin hankali Sille yake yi, lokacin da magrib tayi sun iso dikko junction. Hanyar Niger state. Hanyar suka ɗauka suka nausa, sannan suka ɗauki hanyar cikin jejin lambata sosai. Ashe tafiya ce mai zurfi sosai, dan basu iso inda aka ajiye su Abah ba sai bayan isha'i...
           Zuwa lokacin yaran su sun kunna fitulu, dan akwai sola babba a wajen, babu mai neman salla balle su taimaki su Abah da aka zube a ƙasan bishiya suyi. Su su AA ma allurar da akai musu ta bugar da su sun kama barci tuni. Sille na gama faka motar yaran sukai musu caaa, kowa na musu barka da isowa. Cike da isa suke amsawa, musamman Mabera dake bin su Abah da kallon ɗaɗɗaya. Ya sauke idonsa akan Mamy, sai kawai ya kwashe da wata shegiyar dariya. Takowa ya shiga yi har inda take yasa ƙafa ya shureta a wulaƙance.
       Bata ko kalleshi ba, hasalima bata ɗaga kanta dake duƙe ba. Dama kuma tunda aka kawosu wajen ta koma gefe ta ware kanta, gaba ɗaya ta riga ta tsargu, cin zarafin da Junaid yay mata a Darma House gaban kowa shi da Sille dafa mata zuciya yake matuƙa. Zuciyarta har raya mata take ta kashe kanta kawai, sai dai idan ta tuna Abah yaci gubar data saka masa a abinci sai taji babu amfanin hakan, wannan baƙin cikin da tashin hankalin na lokaci ne ƙalilan komai zai wuce. Musamman data tuna alluranta na jikinta da zataima su Junaid na guba....
        “Oh wai yau kuma kin zama Saliha ne Kamila”. Sille ya faɗa cike da iskanci. Dariya suka sakeyi da ubansa, ita dai bata ko motsa ba balle ta kulasu. Sille ne ya shureta a karo na biyu, tare da mata tsawa. “K dalla tashi ki haɗa wuta ga gawayi can ki samun ruwan wanka”.
       Yanzu kam dole Kamila ta ɗago tana kallonsa idanunta cike da hawaye, Sille ya zuba mata kallo mai firgitarwa tare da jan kunamar bindigar hannunsa ya ɗanata. “Ko bazaki tashi ba sai na fasa miki ƙoƙon gwiwar ƙafa ne”.
      Shaaaa hawaye suka gangaroma Mamy, ta kalli sashen Oum da Abah suke taga ita suke kallo, haka ma su Maanal. Nana kuwa kamar ma tana murmushi ne duk da Saheeba dake fama da kanta barcin wahala ya ɗauketa na jikinta. Sai kawai taji ta gama muzanta, ta gama ƙasƙanta. Dole kuma ta tashi dan ta tabbatar Sille zai iya aikata mata abinda ya faɗa ɗin.
    Mabera daya kai zaune a kujerar da aka kawo masa ko'a jikinsa ya maida dubansa ga Abah yana faɗin, “Kar kaga ina cin uban matarka kaji haushina My Darma, dan baka san abinda tai min bane ba. Kai kanka data samu dama sai ta aikata maka irin wanda tai min ɗin. Bamu da wani isasshen lokacin ɓatawa anan dan mu ba masu zama bane ba. Nan da kwana biyu kacal zamu bar ƙasar nida ɗana. Dan haka Darma kana da zaɓi biyu zuwa uku. Bayan na baka labarin alaƙata da Kamila da sanar dakai ainahin wacece ita zaka biya diyya da maƙudan kuɗaɗe masu yawan gaske kai da zuri'arka dan nasan kuɗi ba matsalarku bace. Kuɗi nake so BALIDAN kuɗi da zasu wadatar da ni ni da ƴaƴana biyu a rayuwar turai kar ƙarshen numfashi mu. Nasan dai ka fahimceni. Na uku dole ka bani ƙaramin ɗanka na huce dukkan takaicina a kansa na ramawa ɗana abinda ya aikata masa a shekarun baya saboda waccan fitsararriyar matar tasa...” ya nuna Maanal. Harararsa Maanal tayi babu tsoro babu shakka. Ta yamutse fuska da taɓe baki ta watsar da banza.
      Murmushin takaici Mabera yayi da faɗin, “Zan gyara miki zama yarinya. Zan kuma koya miki tarbiyya da yanda ake girmama na gaba....”
         “Ka fara koyama kanka mana. Kuma Besty da Abah sunfi ƙarfinka wlhy, kadai ji da wadda kace kana da alaƙa da it.....”
      Bata rufe baki ba wani ya kawo mata duka da bakin bindiga Abah ya kare. Da sauri Oum ta riƙota jikinta itama. A nutse Abah ya kalli Mabera dake dariya. “Junaid ka kawo mu nan ne dan ka illatamu, ko ka kawomu nan dan biyan buƙatunka? Na rantse maka da ALLAH, idan wani abu ya samar min yara bazan taɓa na yafe maka ba”.
          “Amma kaga rashin kunyar da take min ai”.
     “Kazo da siffar da za'ai maka hakanne ai”.
   “Oh kana goya mata baya kenan Aliyu”.
         “Kai ba goyon bayan naka ɗan kake yi ba”.
    “Shike nan ni banda lokacin yin sa'insa da kai yanzu. Amma ina baka shawara ka kimtsa bakunan surukanka da ƴaƴanka idan sun tashi in har kana buƙatar dukanku kubar wajen nan da rai da kuma lafiyar jikinku. Idan ba haka ba waɗan nan fusatattun karnukan nawa basa jira. Su sha yanzu magani yanzu ne idan aka taɓani, kar kaga yanzu ta tsallake. Na baka daga nan zuwa safiyar gobe idan ka yarda da sharruɗɗana zamuyi komai mu gama a goben. Dan na faɗa maka banda isashen lokaci. Kai ku tattara su ku kaisu ciki, a haɗe min su a ɗaki guda...”
      Daga haka ya miƙe yabar wajen. Su kuma yaranshi suka zo suka zagaye su cikin tsawa suna faɗin su tashi. Su Nuratu ne farko tashi, suka kakkama Saheeba. Abah da gaba ɗaya zuciya ta kumeshi ambaton ALLAH kawai yake a zuciya shi da Oum ya jinjina ma su Ameerah da sukaƙi motsawa kai ganin su Abah ma basu motsa ba. Tashi sukayi suma, haka aka sakasu gaba zuwa cikin gidan. Ashe ƙaton gaske ne, akwai mutane kuma a cikin gidan zaune alamar suma kidnapping ɗinsu akayi, jikinsu yayi dauɗa sosai, wasu a rame, wasu ma ciwo ya ci su ya cinye. Bayin ALLAH kallonsu Abah kawai suke har aka shige dasu ɗaki, a zukatansu ayyanawa suke waɗan nan dai ƙila manya ne shiyyasa ba'a kawosu cikinsu ba. Daga ganin mutanen kuma dama dai kasan suna tare da jin daɗi, duk da darene ba wani sosai suke iya tantancesu ba.
        Ɗakin dai ginin ƙasa ne kuma rufin ƙasa. Ko daɓen ƙasa babu ƙasace rubuɗi zube jajir, sai dai akwai hasken sola har anan. Haka suka zazzauna. Sai ga su Babban Yaya an kawo, babu tausayi haka suka dinga sakinsu a ƙasa. Baiwar ALLAH Oum sai idanu ta runtse hawaye na sakko mata. Abah kam idanu ya zubama zaratan mazajen ƴaƴansa abin alfaharinsa. Manya-manyan bread guda kusan goma cikin yaran nasu wani ya kawo ya watso musu, sai ledar ruwa ɗaya. Cike da wulaƙanci ya bisu da kallo a yatsine yana faɗin, “Wannan karramawar oga ce, badan haka ba wlhy yanda na tsani masu kuɗin ƙasar nan tuwon ƙasa zakuci, ni ne nan zan ma tuƙa muku shi da hannuna yan iska ɓarayin kuɗaɗen mu. Kum tsare komai kun tare ko ina daga ku sai ƴayanku da jikoki”.
        Karo na farko Abah yay murmushi, dan harga ALLAH tausayi yaron ya bashi, dudu bazai wuce shekaru ashirin da huɗu ba. Sam baiga laifinsa ba, dan abinda ya faɗa gaskiya ne, sannan kuma maybe bai san su ɗin su wanene ba, dan a Nigeria kawai idan kayi kuɗi sunanka ɓarawon gwamnati a wajen wanda bashi da su. Alhalin kuma ba haka bane ba........✍️



*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣5️⃣7️⃣


______________



.........Tabbas a rayuwa shi alkairi danƙo ne, baka kuma gane masoyi na ƙwarai sai a gaɓar da wata jarabawa ta rayuwa ta sameka. Hakama baka gane alkairi ga marashi rahama ce da jin ƙai sai a gaɓar da kake cikin wani bala'i na rayuwa. Shiyyasa ko yaya mu kasance masu alkairi ga wanda basu da ƙarfi ko basu kaimu ƙarfi ba. Idan kina da dubu biyar daure kiyi alkairi kona ɗari biyar ne zakiga ribarsa koda ba'a lokacin da kikayi ba.
       Tabbas shuka alkairi da ahalin Abah keyi da shi kansa a wannan gaɓar sai ya zam suna girbarsa ne da addu'oin bayin ALLAH akan halin da suke ciki. Dan ta ko'ina addu'oin fatan kuɓuta daga azzalumai ake musu. Masu saukar Alkur'ani nayi musamman makarantun da suka tallafawa da alkairansu. Gaba ɗaya media labarin ɗaukesu ya danne na shagalin bikin salla. Haka ahalinsu sun duƙufa addu'oi a wannan dare. Idan akace maka wani yayi barci to sai dai ƙaramin yaro, amma mazansu da matansu sunyi kwanan zaune ne agaban UBANGIJI suna kuka da fatan kuɓutar ƴan uwansu.
      Yayinda jami'an tsaro suma basu zauna ba. Dan shugaban ƙasa da kansa ya kira IG hankali tashe ya bashi umarnin amsar case ɗin. Kowa yasan yanda AA Darma keda kima da mutunci a idon shugaban ƙasa, hakama mahaifinsa. Dan haka wannan ba wani sabon abu bane ba ko abin mamaki. A ganin mutane ma wannan shine halaccin da shugaban ƙasar zai nuna ga ahalin Darma gaba ɗaya dana Kashim Kura dan sun taka rawar gani akan hawansa mulki ƙwarai da gaske ta ƙarƙashin ƙasa da dukiyarsu. Duk da ba kowa yasan hakan ba dan a zahiri babu wani ahalin Darma dake da alaƙa da siyasa. Shi kansa AA da aka bama muƙami a gwamnatin kowa na ganin yanda yake wasarere da shi da masa ɗaukar kashin kaji....

    ______★

       Dukkan wani motsin dake faruwa a cikin gari waɗanda suka tallafawa Mabera a aikin saboda nasu dalilan suna isar masa da saƙo. Abin zai baka mamaki idan akace maka kuma a wasu manyan jiga-jigan ƙasar ne. Yawancinsu kuma haushinsu akan AA da Abah ne. Sai Yaya Fawzan dake harkar kwangila shima ta wani fannin

178 / 213

Chapters