Author : Bilyn Abdull Category : Romance
shi. Ga zazzaɓi tana ji dan ba dukan wasa yay mata ba harda kamun kunne. Tana son Sille sosai, shiyyasa take iya jure wahalhalun da yake bata da azaba kala-kala da wulaƙanci. Burinta a ƙarshen duk wannan azabobin suyi aure. Wlhy zata jure komai ko a yaya yake dan sonshi take yi da gaske....
_________★
KADUNA
Tun wucewar su Sageer kalamansa ne keta maimaita kansu a kunnen Huznah. Ta kasa samun sukuni gaba ɗaya. Bata san zata iya yin kewarsa ba sai da tazo kwanciya. Sai ta jita tamkar marainiya. Gashi tunda ya kirata yace sun sauka bai sake kira ba. Ita kuma yana tsoron ta kira shi Ummi taji. Haka ta daure da ƙyar barci ya ɗauketa gabannin asuba. Washe gari Hajiya Basariyya da sassafe ta bar gidan zuwa Zaria. Maimakon zuwa gidan su Najma kai tsaye a wani waje suka haɗu da Maman Yaseerah. Ganin yanda ran Maman Yaseerah ke a ɓace Hajiya Basariyya ta ce, Lafiya kuwa naga ranki a ɓace fiye ma da nawa?”.
“Humm Basariyya kenan, gara ke kina da mafita akan Huznah, duk da case ɗinmu akwai banbanci, ke haihuwa ce baki so tayi da Sageer, ni kuma haihuwa nake son Yaseerah tayi da Abdullahi.”
“A'a to minene ba gashi zata haihun ba?”.
“Wace haihuwar kuma bayan jiya ta haihu ɗa babu rai, kina cikin wannan tashin hankalin ne shiyyasa ban kira ki ba. Ga Alhaji ya hanani zuwa dubata ya tura ƙanwarsa da Majdiya yanzu haka suna hanya”.
“Eh lallai babbar magana. Wai mike faruwa damu ne haka? Wlhy ko ganin Huznah bana sonyi tsakanin jiya zuwa yau”.
“Taya zaki so ganinta abin nan fa da ciwo. Duk zamanki gidan Kawu Manu ne ya kawo matsalar nan, amma da tuni mun ɓarar da shegen cikin ai. Yanzu dai yaya ake ciki”.
“Hummm nayi magana da Dr Reyama jiya tace a haka ma za'a iya cire cikin, sai dai ta saka kuɗi masu yawa. Ni kuma wlhy a yanzu banda wannan kuɗin, dan dudu kuɗin account ɗina 300k ne. Suma wanda Yaya ya bani ne na tura miki 200k kinje wajen malamin can dake aiki akan dawowar kayan nan na hannun Yazeed. Shiyyasa nazo ki ara kin 200k na cika dana hannuna su zama 500k ɗin data buƙata. In sha ALLAHU komai na daidaita zan dawo miki da su”.
Shiru Maman Yaseerah tayi fuskanta na canjawa, sai kuma ta nisa. “Shike nan zan baki, amma kina lissafawa ko ya zama 500k kenan harda 300k da aka bama wancan mutumin na bayan tsauni”.
“Na sani bananta ba Aminiya”.
“Yayi zan sa miki a account. Ni bari na koma dan ina cikin damuwa”.
“To ba damuwa. Nima dai idan aka kammala aikin nan na Huznah zanje Abujan na gano Yaseerah ɗin.”
“Okay”.
Kawai Maman Yaseerah tace tai ficewarta. Sai abin ya tsayama Hajiya Basariyya a rai. Amma batace komai ba ta fito ta shiga mota ta kama hanyar Kaduna. Dan bama taso kowa ya farga da rashinta a gidan har ƴaƴanta...........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣4️⃣7️⃣
______________
.........Koda Hajiya Basariyya ta koma gida batace da Huznah komai ba. Hasalima ko gaisheta tayi sama-sama take amsawa. Sosai Huznah ta shiga damuwa, har wata ƴar ramar dole tayi. Baiwar ALLAH sai dai kaga tayi tagumi shiru ko ƴan uwan nata ma ta kasa sakin jiki da su. Duk abinda ke faruwa babu wanda ya sani. Duk da dai Huznahr na ƙoƙarin shiga gaida Daddy a sashensa. Yanda yaga ta ɗan rame sai abin ya bashi mamaki, gashi bata da walwala. Sai yake tunanin ko kewar mijinta ne. Bai dai ce komai ba ya barma cikinsa. Amma ita Ammie haka kawai tasha jinin jikinta da yanayin Huznah ɗin. Sai ta fara jan yarinyar jikinta dan akwai tausayi, tana fama da ciki kuma ana sakata a damuwa. Hakan sai ya saka Huznah ɗin fara saki jiki da Ammie, har in tana son abu sai ta faki ido taje sashen tace Ammie ta bata ko Aunty Sakeena. Wani lokacin ta zauna taci anan, kota ɓoye ta tafi da shi......
________★
Bayanin komai Daddy yay ma Yazeed. Aiko sai kuka yake da hawaye shaɓe-shaɓe yana roƙon Daddy ya yafe masa. Ya ringa yima AA kuma godiya. AA ya nuna masa babu komai, akan Ammie komai zai iya yi dan tamkar mahaifiya take a wajensa. Kawai dai yana bashi shawara ya ƙara dagewa da addu'a a kwanakin nan, dan zasu fara bibiyar Mabera. Dan haka za'a koma da shi Kaduna kuma zai cigaba da acting like har yanzu yana a cikin wancan halin. Yanzu idan sunje Kaduna ɗin ma za'a maida shi gidan da Nazeefa take sai a fiddosu tare ta yanda zata ɗauka a gida ɗayan suke daman.
Ɗari bisa ɗari Daddy da Yazeed sun gamsu da shawarar AA ɗin. Dan tabbatas Mabera shegene al'amarinsa sai da bada ƙafa. Tunda har ya iya irin wannan ƙullin a jikin Yazeed ɗin to komai fa zai iya yi. Sun sake tattaunawa sosai da tsara abubuwa masu yawa kafin AA ɗin yay musu sallama ya tafi. Suma zuwa yamma zasu wuce. Amma shi Daddy zai tafi a mota yanzu, shi kika Yazeed yabi tarain ɗin dare....
________★
Kusan lokaci ɗaya su Maanal da AA suka shigo gidan. Sun raka Oum ne yin jajen haihuwa gidan su Abdull, daga can suka wuce asibiti suka duba Yaseerah dake tare da su Hajiya Majdiya. Sai suka shiga wajen Nuwaira data tarkato ta biyosu dan RK yayi tafiya yau da safe zuwa Jos. Kuma zai yi kwana biyu dan sai ana jibi salla ma zai dawo...
Duk da Maanal taji daɗin fitar hankalinta a rarrabe yake akan lamarin mutumin can data gani ɗazun ya shiga sashen Mamy. Tata saka ido taga an kira Nuratu ko wajenta yazo amma bata ga hakan ba har suka fito, dan hada ma Nuratun suke tare. Saheeba dai ana can ana rawar ƙafar haɗama Babban Yaya abinci yau yace tayi girki. Shiyyasa ma taƙi ta bisu..
AA ya iso kusa da Oum yana kama hannunta da mata sannu. Murmushi tai masa da faɗin, “Sannunmu Auta. Kaima sai yanzu kake shigowa?”.
Sai da ya kalla Maanal da ke kallonsa a kaikaice sannan ya ce, “Ki bari kawai Oum uziri ne ya riƙeni sosai. Amma kukan kun daɗe halan yawo suka sakaki kukaitayi?”.
Sai da suka fara tafiya yana rike da Oum ɗin take bashi amsa da, “Babu laifi mun ɗanyi yawon kam. Dan munje gidan Hajiya Batoola ma, kafin muje asibitin. Kasan Majdiya ta maƙalemu da surutu ta hanamu fitowa shine kuma muka leƙa Nuwaira ashe ma tana shirin tahowa nan ne. Sai kuma muka biya yaran nan suka sayo kayan kwaɗayi”.
“Eh lallai kunsha yawo kam, ɗazun da safe muke magana da Uncle R ɗin yace uzirin gaggawa ya taso masa zuwa Jos zata taho nan na aika driver ya ɗakkota baya son tai driving saboda jikinta. Tunda ta biyoku ai shike nan.”
Dai-dai nan Mamy ke fitowa daga sashenta ita da wata mata. Ta zuba ma AA da Oum ɗin ido, sai kuma ta janye cikin takaici zuciyarta na mata nauyi da zafi matuƙa a cikin ƙirji. Oho su bama su ganta ba, dan har sun shige su Maanal biye da su, sarai Maanal taga Mamy, hakama Najma da Nuratu, amma duk sai suka watsar da ita suka shige. Ameerah da hankalinta bai kai ba tana waya ma ta shige, dan harga ALLAH ita kam bataga Mamyn ba sam...
Kasancewar lokacin sallar la'asar yayi zama kaɗan sukai kowa ya fito ya nufi sashensa. Dama AA baima zauna ba shi. Yana raka Oum ya fito, Maanal da dama ta ƙagara su su haɗu itama ta biyo shi. Su Najma na mata dariyar iskanci ta juya ta musu daƙuwa ta fice. Nuratu kamar zuciyarta zata fashe. Itama sai ta kallaɓa ta fice ta nufi sashen yayarta. Dan yanzu ko kallon sashen Mamy bata yi..
AA na shigowa Maanal na shigowa, bai san tana bayansa ba dan haka ya zuba mata ido, sai kuma ya buɗe mata hannayensa tazo ta shige jikinsa. A tare suka saki ajiyar zuciya. AA dake shafa mata baya ya ce, “I miss you bestie”.
“I miss you too”.
Ta faɗa a hankali.
“Kin gaji?”.
Kai ta gyaɗa masa. Sai yay murmushi ya ce, “Na goya ki?”.
Nan ma kai ta gyaɗa masa. Ya fahimci miskilan ne a kusa dan haka bai sake magana ba shima ya juya ta hau bayansa ledar furarta da kilishi na hannunsa da handbag ɗinta suka haura sama. Da taimakon juna suka rage kayan jikinsu musamman ma shi da nasa duk suka damesa. Ganin yanda tayi shiru kamar mai tunani yazo kusa da ita ya zauna. Tagumin da tayi ya cire. Cike da kulawa ya ce, “Mike faruwa ne?”
Ajiyar zuciya ta sauke, sai kuma itama ta juya tana fuskantar sa. “Besty sanda kake fita kaga wani na shigowa gidan nan ɗazun?”.
Kansa ya girgiza mata alamar a'a. Miya faru”.
“Bayan fitarka baifi da mintuna uku zuwa huɗu ba ina tsaye a inda ka barni ina waya.......”
Ta kwashe komai ta faɗa masa. Cikin matuƙar zuba mata ido AA yace, “Sashen Mamy fa?”.
“Wlhy kuwa, ni kaina abin ya dameni ƙwarai. Nata saka ido naga zai kira Nuratu a waya amma shiru. Ina tsaye a window sai gashi ya shigo kalla ka gani har video nai masa ai”.
Tai maganar tana miƙa masa wayar. Tabbas kuwa mutum ne, dan duk da ya rufe fuska da hula kamar ranar bai mance tafiyarsa ta ƴan iska ba. To mike kawo guy ɗin nan gidan nan? Har kuma sashen Mamy ma? Da wa yake da alaƙa a sashen?”.
Rashi mai bashi amsa ya sashi ciwo wayarsa a aljihu. Kira yayi, babu jimawa kuwa aka ɗaga masa. Daga can aka shiga gaisheshi cikin girmamawa. A taƙaice ya amsa, tare da faɗin, “Yusuf akwai wata number mota zan tura maka yanzun nan ina son a bincika min motar wacece. Tare da dukkan bayanai akan mai motar A-to-Z”.
“Okay Sir! Ba damuwa”...
________★
A lokacin da AA ke nan yana bincike anan Haule ce ta tafi aikar Mamy. Taxi ta hau bayan ta haɗa mai taxi ɗin da waya sukai magana da wanda zata amshi aikar a wajensa. Dan ita kanta Mamy bata san address ɗinsa ba. Sanda zata bashi aikin ma a wani waje suka haɗu.
Abinda Haule bata sani ba mai taxi ɗin ma turoshi akayi, dan haka yay ɗan pretending kamar an gaya masa wajen ya miƙa mata wayar kawai ya fara tafiya. Wani kwana-kwana da ya dingayi da ita tun tana gane inda suke shiga da fita harta sallama. Kafin daga ƙarshe suka iso wata sabuwar anguwa da ake gina manya-manyan estate guda kusan biyar. Babu abinda Haule ta fahimta, sai dai me guy ɗin na shigowa inda take drivern ya fita shi kuma ya bata box ɗin hannunsa kawai taga fuskar data sani. Tabbas tasan guy ɗin kuma tare da Sille ta sanshi, sai dai shi bai santa ba.
Kayan ya bata batare da yayi magana ba ita kuma ta buɗe handbag ɗin hannunta ta ciro ledar da Mamy ta bata ga bashi. Yana amsa ya fice abinsa. Drivern ya dawo ya tada motar yay reverse suka fice a wajen. Sosai Haule keta tunane-tunane, ina Mamy tasan mutumin nan? Rashin mai bata amsa yasa tai shiru da bakinta. Kamar ko an saita taxi ɗin na isowa ƙofar gidan Darma ana kai raka'ar farko ta salla. Ta bama mai taxi kuɗi ta fita ta shige cikin gida. Babu kowa a compound dan haka hankali kwance ta wuce sashen Mamy. Tana bedroom dan haka taje takai mata ta fito. Maimakon wucewa ɗakinsu sai ta fice gaba ɗaya a sashen tana ƙoƙarin kiran Sille a waya. Sai da ta kusan tsinkewa ya ɗaga. Miryarsa kamar da ɗan maye-maye a ciki ya ce, “Ya akayi?”.
“Baby na amso mata aikar, amma kasan wajen wa kuwa?”.
“Malama muje magana sak”.
“Sorry Baby. A wajen Gaga ne fa”.
“Gaga! Gaga Gaga dai nawa?”.
“Ƙwarai kuwa. Kasan bai sanni ba ai.”
“Minene kima amso?”.
“Wlhy ban sani ba, wani abu ne an ya nannaɗesa da ƙyau, da gani kasan mai muhimmanci ne sosai”.
“Yayi, idan Kinga wani motsi ki kirani”.
Daga haka ya yanke wayar...........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣4️⃣8️⃣
______________
.........Sille na katse kiran mahaifinsa ya kira. Yay masa bayani kamar yanda Haule tai masa. Mabera na wani makirin murmushi yace, “Tabbas akwai abinda take shiryawa. Amma ka binciki Gaga ɗin mu fara jin minene harƙallar tasu.”
“Okay Baa! An gama.”
Sille baiyi ƙasa a gwiwa ba yay kiran Gaga a waya yace yazo ya sameshi. Gaga yaron Sille ne sosai, dan ogansa ne a harkar ƙwayoyi. Shi yake bashi kuɗi maƙudai su zuba harka saboda Gaga ɗin ya san ƙwayoyi. A zahiri Gaga ba ɗan iska bane ba. Hasalima likita ne masanin magunguna kuma babba. Yana aiki a Genaral hospital ne nan cikin Abuja. Ta ƙarƙashin ƙasa suke sayar da muggan ƙwayoyi ga irinsu Sille. Shi Sille kasancewar yaron Minister ne kuma babban ƙwaron kansa yana kaiwa wasu manyan ƙasar da yaransu harma da matansu irin wannan kayan ƙwalewa shiyyasa suka ƙulle da Gaga har suka haɗa jari. Gaga shike wahalar sayowa, shi kuma Sille ya rabama masu so.
Sille da Gaga sun haɗu a inda suke haɗuwa. Dan babu wanda yasan akwai wata alaƙa ta zahiri a tsakaninsu. Ita kanta Haulen wani karo ne data rutsa tana tare da Sillen Gagan na masa neman gaggawa har ta sanshi.
“Oga sai wani ƙara fresh kake fa miye sirrin”. Gaga ya faɗa cike da tsokanar Sille. Dariya Sille yayi irin ta basawa, tare da faɗin, “Yau kuma tanan zaka silleni kenan Gaga. To bazakaji ba. Magana mai muhimmanci ce tasa na kiraka. Bana son kai min ƙarya dan nima ban taɓa maka ba. Koda inada alaƙar sirri da mutum ka nema sanin waye shi ina buɗa maka”.
“Hakane Oga”.
“Yauwa, ina son sanin alaƙarka da matar Darma”.
“Matar Darma kuma? Bani da wata alaƙa da wani a wannan gidan ma koda mai aiki gaskiya. Wanine yace maka ina da alaƙa da su?”.
Ɗan jimm Sille yayi na tunani, sai kuma ya juya yana kallon Gaga da ƙyau. “Ɗazun ka bada saƙon wata mata wacece?”.
“Tofa! Ya akai kasan wannan Oga”.
“Karka damu kai dai bani amsa kawai.”
“Okay tabbas anyi hakan, sai dai ni bansan wacece ita ba saboda ainahin harƙallar bada ita nayita ba. Da wata mata ce kama santa Mrs Ƙurami. Itace tazo da ita kwana goma da suka wuce akan suna son allurar guba da gubar kanta da za'a iya ciyar da mutum da ita tai kwana kamar biyar a jikinsa kafin ta fara aiki. Sannan koda takai mutum ƙasa kada wani signing ɗin da za'a fahimci guba ce ta kashe shi ya nuna. Ita kuma allurar zata busar da mutum jikin kamar mai pralayses, amma tafi pralayses ɗin ma illa. Dan komai na mutum zai bar aiki ne sai iya idanunsa like irin jiyyar da Sarkin gagara badau kakan sarki mai ci yanzu ya taɓa yi.”
Cikin jinjina kai ya ce, “Okay, amma wa kake ganin zasuma amfani da gubar?”.
“To basu fito fili dai sun gaya min ba. Amma a randa na fara zama da su naji kamar ita ƙawar Mrs Ƙurami da ke da kayan tana faɗin mijinta zata bama guba ɗin. Ita kuma allurar wasu zatamawa harda mace”.
Haka kawai Sille yaji a ransa harda shi a cikin allurar nan da mahaifinsa ma tunda tasan yana raye. Ɗayar kuma baya taba ɗayan biyu kishiyarta zatai mawa, dan in dai ta yarda ta kashe Aliyu Darma to bazata bar matarsa ba. Amma matar nan shegiya ce, shiyyasa babansa ke kiranta da suna ƴar kunama kuma balbela. Ita kenan duk wanda yay mata rana sai tayi masa dare. Hummm ai ko zai tabbatar mata ta haifo dai-dai da ita kuwa.....
“Oga akwai matsala ne?”.
Gaga ya katse masa tunani. Kai ya girgizama Gaga ɗin da faɗin, “No ba damuwa. Ina fatan dai ka gama haɗa mata komai?”.
“A komai da komai na bata mun warware.”
__________★
AA bai samu kiran Yusuf ba har washe gari. Sai kusan sha biyun rana suna zaune a compound shi da Babban Yaya da Yaya Fawzan suna tsara yanda sayen ragunan layya zasu kasance musu sai shanu biyu da suke yankawa kiran Yusuf ya shigoma AA. Ɗagawa yay, bayan sun gaisa Yusuf ya fara masa bayani kamar haka.
“Sir gaskiya Guy