AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   177 / 213

528K to 531K   out of 636.6K words

jini ya fara zubarmawa zuwa ciki. Kafin kace mi likitoci har uku sun rufu a kanta. Karan farko hawaye masu zafi suka zubo a fuskar Daddy, babbar rigarsa yasa ya sharesu batare daya bari Yazeed dake faman kai-kawo ya gani ba. Dai-dai nan kira ya shigo wayarsa, koda ya duba sai yaga Ammie ce. Ɗagawa yay, cikin danne damuwarsa. Ammie da hankalinta ke a tashe tai masa bayanin Nazeefa fa na cikin mummunan yanayi gaskiya. Ya kamata su dawo gida a kaita asibiti, dan itama Sabuwar da'alama taji ciwo a ƙafa dan ta gagara taka ƙafafunta.
        Sai da Daddy yaja numfashi ya fesar kafin ya fara yima Ammie bayani a nutse. “Asia ku ɗakkota zuwa asibi ku samemu, dan muma muna can Huznah ce babu lafiya”.
     “Huznah kuma? Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Miya sameta? Lafiya da muka fita da ita wajen idi”.
     “Humm Asia sai kun zo kawai”.
  Daddy ya faɗa yana yanke wayar dan baya son yin doguwar magana ma. Abubuwa sun masa yawa sosai a wannan tsakanin. Kawai dai dan yanada tawakkali ne da ƙarfin hali. Ba ƙaramin tashin hankali wannan waya ta saka Ammie ba. Dan haka batai ƙasa a gwiwa ba taje ta sanarma Hajiya Yaya. Itama sai hankalinta ya tashi harda yaran duka, yanzu kam gaba ɗaya suka fito dan zuwa asibitin, sai dai duk da hakan halin da Nazeerake ciki ko'a jikinsu balle Sabuwa da ƙafa ta kumbura tayi dam. Kukan ma ta kasa yi sai hawaye kawai ke bin kumatunta azaba ta isheta. Abu kamar wasa yana neman zama gaskiya..........✍️




*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*




*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣5️⃣4️⃣


______________



.........Kiran da Mabera yayma Sille a waya shine ya ceci Mamy da Haule a hannun sa. Babu ko kunya ya ɗauki Haule sukaje bayi wai zata tayashi wanka. Sai wani lallashinta yake tsabar iskanci abinda bai taɓa yi mata ba. Suna shiga Mamy ta kinkimi akwatin kayan data haɗama Sille kadarorinta cikin sanɗa ta buɗe inda ta ajiye keys ta ɗauka. Ƙofar ta buɗe ta fice tana haɗa hanya kamar wadda ta fara shiga buguwar maye. Tana fitowa cike da sassarfa ta nufi hanyan gate, sai dai ko rabi compound ɗin batai ba yaran Mabera suka tareta da bindigu. Abin ya gigitata da bata mamaki, dan a sanin data masa can baya shi dai ba ɗan fashi bane ba, sannan ba ɗan daba ba. A ina ya samo waɗan nan tiƙa-tiƙan yaran da bindigu haka?. Bata da mai bata amsa sai ma tisa ƙeyarta da sukayi sashen Abah har su huɗu kamar wadanda suka kamo ɓarayi. Koda suka iso falon baƙi da aka tsare su Abah sai tai tsuru-tsuru tana kallon kowa. Suma duk kallon nata sukeyi musamman ma Abah, Babban Yaya, AA da Yaya Fawzan, duk da allurar da akai musu ta kashe jiki kai daka kalla idanun zaratan mazaje kasan duk ubanda suka damƙa sai ya daina numfashi. Oum kam kanta a ƙasa yake tanata addu'a, hakama su Maanal addu'ar sukeyi duk da Maanal na kusa da AA dan duk barazanar da suke mata daga ƙarshe dole suka barta ta koma kusa da shi saboda ƙiri da muzu ta nuna musu sai dai su kasheta wlhy.
      Mabera dake kallon Mamy da wani irin ƙasƙantaccen yanayi ya wani kwashe da dariya. Cike da gadara yace ma yaransa, “Ku hankaɗo min ita gabana”.
     Aiko hankaɗota ɗin sukayi, ta dirƙushe gaban Mabera dake zaune a kujera shi kaɗai ƙafa ɗaya kan ɗaya, ga kayan ciye-ciye an jera masa like wani saraki. Tsabar wulaƙanci kafa yasa ya ɗago haɓar Mamy dake gurfane a gabansa kamar wata kasƙantacciyar baiwarsa. Daga Babban Yaya har Yaya Fawzan da AA idanu kawai suka lumshe, zukatansu kam tafasa sukeyi, ji suke a ransu idan suka damƙi mutumin nan bazasu taɓa barinsa da numfashi ba. Yanda Mamy ke kallon Mabera ga ƙafarsa riƙe da haɓarta sai Maberan ya tuntsure da dariya, dan wlhy abun ya masa suga. Cike da iskanci ya ce, “Kamila! Kamila! Ke har kina da ƙafar guduwa ashe. Kin manta na gaya miki zan dawo. Kin manta na faɗa miki bana barin bashin gaba! Kin manta na faɗa miki ba'a cin amanata! Kin manta na faɗa miki kina da Ajiyar da kikai a duhu kuma zan dawo miki da ita! Kin manta na faɗa miki zan warware miki aiki a dai-dai gaɓar da kike murnar cin nasara! Amma duk kika toshe kunnenki a tunaninki duk labari nake baki ko? Humm Kamila baki sani wanene Junaid ba. Kaɗan kika sani daga abinda zan iya, ko kina tunanin ƴar damar dana baki da ƴar ƙofar dana buɗe miki ta shiga jikin Fateema har wani abu ne daga cikin abinda na iya ko sirrina. Kinyi kuskuren fahimta gaskiya, sannan ƙuruciya ya kwasheki matuƙa. Ki tambayi mijin naki da kika gujeni domin sa kiji, zai gaya miki wanene ni, duk wayon Aliyu, da wani zafinsa da kike gani shi ba komai bane a kaina, dan na dama shi na shanye karon mu ma na baya akan abubuwa da yawa ban raga masa ba balle ke shashasha ƴar gidan matsiyata faƙirai....”
          “Kai ne matsiyaci faƙiri Junaid. Sannan idan kana tunanin ka iya taka Aliyu a baya ai ni baka taka ni ba, sai ma na zame maka RAINA KAMA... (Bilyn Abdull book) tunda a bazata na kaika ƙasa, ƙasan data saka ka ɓoye kanka tsahon shekaru, ai da kai tataccen ɗan iskane kamar yanda kake faɗa ba guduwa zakai ka ɓoye ba sai yanzu ka dawo, zama ya kamata kayi mu fafata. Amma da yake nafi ƙarfinka, sharrin daka koyar dani na fika ƙwarewa na ɓoyekan kuma ka ɓoyu, na kuma auri Aliyu Darma harda ribar aure ka gansu nan ZARATAN MAZAJE har uku. Wanda a yanzu idan aka barkada Ajwaad kawai dake ƙaraminsu wlhy sai dai buzinka. Kaga kuwa duk abinda zakayi a yanzu a banza yake a ma wofi dan naci wannan WASAN...”
       “Tassss!!!!!”.
   Kake jin saukar mari mai masifar ƙara a fuskar Mamy har sai da bakinta ya fashe. Tai dariya tana goge jinin idonta akan Mabera ta ce, “A banzan dai, dan na riga na maka illar da komi zakayi a yanzu tamkar wanke ciwon dake ruwa ne. Kaga kuwa a banza tunda dai an riga da an sami ciwon, koda za'a wankesa dan neman waraka dole a jure zafi da raɗaɗinsa. Wawa butulu da bai san halacci ba.....”
        “Ke kuma miza'a kiraki idan shi butulu ne Kamila matar Darma?”. Sille dake shigowa ya faɗa. Gaba ɗaya juyawa sukai suna kallonsa, banda Mamy dako ganin fuskar Sille bata ƙaunar sake yi. Dan haka tai banza da shi batace uffan akan maganarsa ba har ya ƙaraso inda suke. Kafa yasa ya daki bayan Mamy ta kife akan ƙafafun babansa. Wata dariyar ƙeta Maberan ya saki yana faɗin, “Sai Junaid ɗan Junaid, kuma ɗan Kamila”.
        “Mtsowww!! Baa! Daina haɗani da wannan azzalumar matar, wlhy da ana iya maida baya ta dawo bazan taɓa yarda nai zaman wata tara a cikin wannan matar harta haifoni takai bola ta yarda ba”.
     Da wani irin bugun zuciya kowa ya kalla Mamy, itako jikinta sai ya kama rawa, amma tai ƙoƙarin hana hakanta, sai ma yima Mabera da ɗansa wani irin kallon tsana da take yi. Suko wani kallon banza suke mata a ƙasƙance. Sille yaja tsaki da faɗin, “Baa! Wai mi muke jira ne? Kawai mu tattare abinda ya dace muyi gaba kasan muna da ayyuka a gabanmu ai. Shi dai gadona gashi nan na tattaro kuɗin bankinta kawai zata min juye.”
       “Oh sune ta ɗakko zata gudu kenan?”.
    “Shashashar ba, sune. Ta ɗauka mu irinta ne masu aiki da zuciya. Mu Brain da Heart muke haɗawa a ayyukanmu wawuya, wato Heartbrain.”
           Dariya Mabera yayi sosai. Tare da bama Sille hannu suka tafa. A karo na farko Abah daya nutsu a nazarin komai ya zubama Mabera da Mamy ido sosai. Cike da nutsuwa ya ce, “Junaid miya kawoka gidana?”.
       Murmushi Mabera yayi da gyara zama yana fuskantar inda Abah yake, yace, “Yauwa My Darma irin wannan tambayar ya dace kamin tun asali tun fari. Da bamu kai ma wannan matakin ba ai. Nazo nan ne bisa dalilai HUƊU. Na farko akanka da ɗaukar fansar BASHIN GABA. Na biyu wajen wannan munafukar matar taka  mai fuska biyu, dan dole ne itama ta amshi sakamakon aikinta da cin amanata da tayi. Na uku fansar ɗana Ra'iz da ɗanka ya illata. Na huɗu babban ɗana kuma ɗan matar ka Kamila ya ɗauka fansar zaluncin da uwarsa tai masa na haihuwarsa ta yarda abola bayan koni ubansa ban sani ba....”
        “Ɗa?! Na Kamila? Kuma kai ne UBANSA?”.
     “Kwarai ma kuwa Darma. Dan ni nan ni na aiko Kamila jikin matarka Fateema saboda kai amma taci amanata. Kuma ita ɗin KARUWA tace dan har da ribar hakan ta samar min gashi nan Junaid ɗan Junaid. Idan kuma ta isa ta musalta gata nan ai. Sannan kai da kanka ka rantse idan ka sameta a cikakkiyar budurwa dan ALLAH. Ni nasanka, nasan halinka, ka rufe wannan sirrin ne kawai saboda wani dalilinka”.
       Gaba ɗaya su Maanal duƙar da kawunansu sukai gabansu na faɗuwa. Yaya Fawzan kam hawaye ne masu zafi suka shiga ziraro masa dan shi yana da rauni. Babban Yaya da AA kam da yake suna da zuciyar jaraba launin idanunsu ne kawai suka sake sauyawa.
    Bamera ya cigaba da faɗin, “Dole ne kasan komai a yau a yanzu dan ni kotuna mai adalci ce, bana cutar da kowa sai wanda ya cutar dani, bana taɓa kowa sai wanda ya taɓani. Ko waɗan nan sauran da kaga na gurfanar anan nayi hakan ne saboda zuri'arka ne. Amma masu laifi kai da Kamila da ɗanku Ajwaad ne kawai zasu amshi hukunci na. Sai Hajiya Turai idan ta kama”.
       Babu wanda bai maimaita sunan Hajiya Turai a zuciyarsa ba tare da juyawa suna kallonta. Nana ko matsawa tai daga kusa da ita. Mabera ya cigaba da faɗin, “Sai dai ba'a nan ba, dan dole ne a fara biyana diyya a kanku. Dan haka Son! A tattara min su zuwa mota bamu da isashen lokaci. Uwar nan taka ta ɗauki kayan nan a kanta kuma”.
       “Baa! Ka daina kiran wannan matar da Babata zamu ɓata”.
   Dariya Mabera yay da faɗin, “Na daina ɗan Baa! ALLAH ya huci zuciyar maza. Oya zamu iya tafiya”.
     Bin kowa na falon yay da kallo, ƙarshe ya sauke idonsa akan Maanal. Ya wani kafeta da idanu yana lashe baki, wani banzan kallo Maanal tai masa cike da tsiwa ta ce, “Ka kalli ubanka ɗan iska tsinanne ɗan wuta.....”
     Kafin ta rufe baki yaransu sunyi kanta da bindiga sun zagaye har AA da take a kusa da shi. Sille yay wani shegen murmushi da gyara tsaiwa. “Kin birgeni, dan ina son tsayayyar mace mara tsoro. Yanda mijinki yake haka kike. Baa! Idan an gama shari'ar nan ina son yarinyar nan matsayin ganimar yaƙi”.
       Dariya Mabera ya sanya, hakama Sillen. Yayinda AA ke musu wani irin zazzafan kallo da tabbas badan allurar da sukai masa ba babu fashi a wannan gaɓar sai wani ya mutu a cikinsu. Maanal kam kai tsaye ta ce, “Ɗan akuya jaki ni nafi ƙarfinka wlhy. Kai in sha ALLAHU da wannan hannun nawa zan kasheka yau”.
           Salute ɗinta Sille yayi, batare daya amsa maganarta ba. Sai ma wata dariyar iskanci yake yi. Haka aka tattara su gaba ɗaya akai waje da su. Su AA basa iya tafiya dan haka yaran Mabera suka ɗauke su. Nana da Hajiya Turai suka kama Saheeba da azaba ta isa..........✍️



*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣5️⃣5️⃣


______________


........Su Aba naji na gani Mabera da yaransa suka kwashesu kaf a motoci, badan anfi ƙarfinsu ba sai dan bindiga da aka zagayesu da ita. Ga yaransa an karya musu garkuwa jiki da allurar da bai san wace iri bace. Ga maganganun Mabera da abubuwan Mamy sun tsayama kowa a zuciya da ruhi. Ba'a bar gidan dasu ba sai da aka rufe musu idanu, haka motocin suka fito a jere kai kace ahalin gidan ne zasu fita wata ziyarar salla. Maigadi da masu gyaran nama da tsautsayi ya afkawa kawai aka bari a gidan bayan an musu dukan tsiya. Lokacin da motocin suka fice ko iya ɗaga hannu wani baya iya yi a cikinsu saboda dakuwa. Wasu ma sun suma dan wahala..
     Tafiya sosai motocin keyi batare da su Abah sun san inda aka dosa da su ba. Sai dai tun kunnensa na jiye musu kai-kawon motoci da tafiya a kan lafiyayyen titi har suka fahimci a hanyar wani jeji suke. Tafiya mai zurfin gaske sannan suka iso wani gurin da basu san inane ba. Umarnin cire ƙyallayen da suka saka musu suka basu, haka suka shiga cirewa musamman su Maanal. Su AA kuwa sai da aka cire musu, hakama Abah da suka sakama handcuffs sai kace wasu jami'an tsaro (ƴan iska🙄). Babu wanda cikinsu hankalinsa bai tashi da ganin inda aka kawosu ba. Jeji ne iya ganinka babu wani alamu na motsin mutane ko ƙauye a kusa. Sai gidan laka ɗaya tallin tal a wajen da alamu suka nuna sun daɗe ana amfani da shi. Zagaye da gidan  mutanene da bindigu kamar waɗanda suka je gidansu, sai wasu irinsu dake group-group wasu na shaye-shaye a ƙarƙashin bishiyoyi, wasu na buga karta.
         Kai tsaye kowa ya fahimci inda aka kawosu. Nuratu da su Nana suka fara kuka mai ban tashin hankali. Ga Saheeba ta fara zubar da jini kaɗan-kaɗan. Ameerah tsigar jikinta sai tashi take yi, ta maƙale jikin Oum tana kuka. Maanal da Najma kam abin mamaki zukatansu a dake suke, haka ma Oum da su AA. Hajiya Turai kam idan anayin kukan jini to yau shi take yi, ta rasa yaya zata fassara al'amarin Sille da Junaid da suka nuna ma kamar basu taɓa saninta ba, balle akai gasu Haule. Mamy kanta ta sare matuƙa, ga ƙirjinta yay mata nauyi alamar ciwon zuciya. Abinda ya basu mamaki kuma babu Mabera a cikinsu babu Sille. Yaran nasu ne kawai da suka fahimci kodai hayarsu aka ɗauka saboda aikinsu ne, ko kuma Maberan ne ya ajiyesu suke ta'asar tare shine ogansu.. babu mai basu wannan amsar dan haka kowa ya cigaba da karanto addu'ar data zo masa a baki. Musamman Hasbunallahu wani'imal wakil da La'ilaha illa antassubahanaka inni kuntu minazzalumin.
      Tunda aka zube su a ƙasan wata bishiya babu wanda yace musu komai a wanda suka kawo sun balle wanda suka taras, sai ma bikin cin abincin da suka kwaso a gidan su sukeyi da ɗanyen nama da suka tattaro duka na ragunan da sa....

_______★

          Tunda suka iso airport RK ke ƙoƙarin kiran wayoyin su AA amma babu wacce ma ta shiga. Dole suka shiga taxis zuwa Darma house. Dukansu babu abinda zukatansu keyi sai faman bugawa da sauri-sauri. Sam sun gagara samun nutsuwa kota sakan. A ƙofar gate duk suka sauka, Uncle Hussain ya sallami masu taxi. Su baba Sardauna suka nufi gate. Suna tura ƙofar ta buɗe, babu ɓata lokaci suka danna kai ciki. Duk wanda idanunsa suka sauka akan su maigadi dake watse a compound kamar gawawwaki sai yay turus zuciya na bugu. Sai RK ne yay ƙarfin halin matsawa inda suke ya ɗan durƙusa tare da kai hannu yana taɓa jijiyoyin wuyansu. Idanu ya ɗan lumshe tare da sauke ajiyar numfashi, dai-dai nan Uncle Mahmud suka iso inda yake.
      “Basu da rai ne?”.
   Uncle Mahmud ya tambaya.
Tsaye RK ya miƙe yana bin gidan da kallo, sai kuma ya furzar da iska. “Suna da rai Yaya, sai dai gidan nan bana jin akwai mutane a cikinsa”.
     Harga ALLAH babu wanda a cikinsu zuciyarsa bata motsa ba saboda furucin RK, sai suma suka fara bin gidan da kallo. Kaf motsicin gidan suna nan, sai guda biyu kawai dama su Mabera suka ɗauka. Rarrabuwa sukayi kashe-kashe, sai dai abin mamaki maganar RK ta tabbata, dan babu kowa a gidan, yau har bedrooms sai da suka dinga shiga na kowane sashi. Su Baba ga tsufa amma dasu akaita kai-kawo.
       “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un!!”. Baba Sardauna ya shiga maimaitawa yana neman yanke jiki ya faɗi sai da aka riƙesa. Zaunar da shi Uncle Mahmud yayi ya ɗauka masa ruwa a fridge. Sauran kuwa kowa ya kasa magana sai ƙoƙarin kiran ƴan sanda da RK keyi. Abinka da al'amarin manya cikin abinda baifi mintuna ashirin ba jami'an tsaro sun iso. Sai Ambulance ta asibitin su RK domin kwasar su maigadi da sukaci duka. Zuwan ƴan sanda ya fargar da mutanen street ɗin halin da ake ciki, musamman su Hajiya Shuwa. Masu gadin gidajen kusa-kusa suka fara firfitowa.
     Tsaff aka ƙara bincike gidan babu alamar mutum mai numfashi, sai hargitsatsen falon baƙin sashen Abah da sashen Mamy cikin bedroom ɗinta da Sille ya hargitsa. Sai ƙananun abubuwa da aka ɗan

177 / 213

Chapters