AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   119 / 213

354K to 357K   out of 636.6K words

AA kam yay wani kalar tsaiwa ne yana kallon Yaya Fawzan irin kallon wana kama ɗin nan............✍️




*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖5️⃣8️⃣


______________


.........Dariya yay Fawzan yay tare da shafa kansa ya taɓe baki. AA ya wani ɗan ɗage masa gira. Harga ALLAH abun yazo ma Yaya Fawzan a bazata, dan haka yama kasa magana. Shi kansa AA yanda Yaya Fawzan ɗin yayi ya bashi dariya, amma sai ya dake dan yau shima sai ya ɗan rama ko yayane daga tsiyar da Yaya Fawzan ɗin ke masa kullum.
          “To Abah kallon ya isa haka mana”.
     Ya Fawzan ya faɗa yana hararar AA. Murmushi AA yay a karo na farko, cike da neman magana ya ce, “Yaushe aka fara?”.
          Baki buɗe Ya Fawzan ya ce, “Mi ɗin?”.
    Gira AA ya ɗaga masa tare da faɗin, “Ai ka gane. Yau dai ALLAH ya kama min kai”.
      Dariya sosai Fawzan ya sanya, sai kawai ya rungume AA ɗin. Shima AA ɗin sai kawai ya hau dariya. Kusan minti biyu suna a haka kafin Ya Fawzan yaja hannun AA ɗin suka shiga mota. Ran AA fes da farin ciki ya ce, “Amma Yaya bata maka ƙanƙanta ba?”.
        Murmushi Fawzan yayi idonsa akan ƙanin nasa. “Ajwaad ai ita mace bata ƙanƙanta wa namiji. Kamar yanda mace bata yima namiji girma. Najma sa'ar Maanal ce fa. Kai ba gashi harka galla ma Lilly cizo ba tana mana amaye-amaye”.
      Murmushi kawai AA ɗin yay shima ya girgiza kai. Shima Ya Fawzan ɗin sai yay dariya kawai, dan yasan Ajwaad da rashin son magana. Da ƴar damuwa ya ce, “Ina sonta sosai, dan tanada tarbiyya. Zan iya cemaka ma kusan tarbiyyarmu iri ɗaya ce. Dan abubuwan Aunty Majdiya da yawa suna kamanceceniya dana Oum. A lokacin bikinku muka dai-dai ta, Ajwaad sam bana samun farin ciki irin na magidanci a gidansa. Bawai bamu samu haihuwar bane damuwata, nasan wannan lokaci ne, amma ita Mamy wannan take kallo kawai, shiyyasa ta sake zaɓa min wata matar”.
      Da sauri AA ya kallesa, “Wata matar?”.
      Kai Fawzan ya jinjina masa yana murmushi. “Jiyan nan ta bani hotonta da number ta akan nayi magana da ita. Ajwaad bazan ɓoye maka ba, wasu abubuwa na Mamy a ɗan tsakanin nan na saka zuciyata girgiza. Miyyasa take damuwa da sai itace zata zaɓa mana matan aure? Miyasa Oum ita bata taɓa kwatanta haka ba. Sannan abinda ke cimin zuciya matan ma duk bana ƙwarai ba. Kalla Babban Yaya, ALLAH nasan sam baya jin daɗin zama da Saheeba, kawai dai bazaiyi magana bane. Kalla wannan yarinyar da ake neman manna maka Nuratu, wlhy ban ƙara jin tsanar yarinyar nan ba sai a wannan zaman. Kuna Chaina ɗin nan fa sai da naci ubanta wai ita zatama Oum rashin kunya....”
     Wani irin kallon ɓacin rai AA kema Yaya Fawzan, shifa da'a taɓa Oum garama duk uwar ubanda za'ai ayi. Fawzan ya cigaba da faɗin, “Wlhy kuwa, amma abinda ya bani mamaki da naje ina zaginta a sashen Mamy sai Mamy ta canja fuska, har tana faɗin muma ni da babban yaya yanzun mun fara koyon halinka na ƙin danginta. Nayi ƙoƙarin ta fahimta amma wlhy tama korini wai na bar mata sashe. Na jima abin nan na cimin zuciya. Ni yanzu babban tashin hankalina ban san yanda zan yi da wannan yarinyar data kawo ba, nama rasa ina tasan yarinyar wai daga gidan sarkin kano take, ko miye alaƙarta da ƴan gidan oho”.
        Gaba ɗaya ma AA ya kasa magana, dan bai taɓa tunanin Mamy zata bar sauran ƴan uwansa su fara fahimtar wacece ita ba. Ya jima shiru, kafin ya kalla Yaya Fawzan da shima ya tafi tunani. Cikin lallashi ya furta, “Yaya badai kana son yarinyar nan ba?”.
      Cikin sauke ajiyar zuciya Ya Fawzan ya ce, “Sosai Ajwaad, ɗan zan iya cewa bayan Amaal Najma itace mace ta biyu da nake jin sonta har ƙasan zuciyata.”
        “Tunda har kana sonta ka daina damuwa da batun Mamy, sannan kada kama yarinyar magana barni da su.....”
      “Uhm-uhm Ajwaad bana son kama nuna ma Mamy na maka wannan maganar, dan bayan ni ɗin bana son ta fahimci wani yasan wata matsala makamanciyar wannan game da ita, sannan ka sani Mamy duk da ta bama Oum mu na har abada hakkinta na uwa na nan a kammu bai kau ba, kuma dole ne mu saukesa in har muna son zama lafiya. In har auren yarinyar shine zai sakata a farin ciki zanyi sai na haɗa da Najma ɗin”.
     Murmushi mai ciwo AA yayi, sai kuma ya girgiza kansa. “Yaya in dai har ba kaine ke da ra'ayin tara matan haka ba baka da wani dalilin yin hakan saboda umarnin Mamy, eh ita uwace, komai zamu iya yi a gareta, amma addini bai yarda harda cutuwa ba. Koka faɗa ko kai shiru kai hakan a gareka cutuwa ne. Ban sani ba ko ni kaɗai ne keda wannan matsalar a cikinku, bazan iya zama da mace fiye da ɗaya ba dan ina da ƙyanƙyami, zan ma iya rantse maka bayan Manaal bazan iya haɗa jikina da kowace mace ba, dan ita kaɗai ce nake jin yin nutsuwar hakan batare da jin komai a raina na ƙyanƙyami ba. Amma mizaisa kace zaka haɗa mata uku kaje wajen waccan kai amfani da ita ka koma wajen waccen like wani namamajo haba. Ai ko addini daya bamu damar yin hakan yace idan zamuyi adalci, sannan ga waɗanda basa iya kauda kansu ga wasu mata. Ni kuma harga ALLAH ma nasan ko na sakan ɗaya bazan iyama wata adalcin haɗata da Maanal ba. Dan haka Yaya be a man Please, ka rasa soyayyarka ta farko kayi haƙuri kayi juriya daga kai har Babban Yaya da ni na kasa a cikinku, sannan kunyima Mamy biyayyar amsar zaɓinta, ya kama a wannan karon ka bama zuciyarka abinda take so kodan ka samu farin ciki, dan banga ta inda wannan wawuyar matar taka zata canja ba (Kayi hakuri na zageta a gabanka)”.

      Murmushi Fawzan yayi, wata irin ƙaunar ƙanin nashi na ratsa shi. Tabbas sune yayunsa, amma Ajwaad ya fisu ƙarfin zuciya da rashin tsoro, shi fa in dai addini bai hanashi abububa to babu mai tankwarashi yinsa. Ko iyayensu bazai ce bazayi ba kai tsaye, amma zai bi ta hanyoyi daban-daban ya gujema abin. Kalla aurensa da Nuratu, kusan shekara shida fa kenan ana abu ɗaya amma yaron nan yasan duk ƙulumboton da zai yi ya zame. A yanzu ma da yake tunanin ya miƙa wuya gashi yana tabbatar masa bazai taɓa haɗa Maanal da wata ba, shi ƙyanƙyamin ma matan yake, chai akwai badaƙala kenan a gidan nan, yanda dangin Mamy suka shiryama auren nan ashe AA zai taro musu match. Aiko duk ma mi za'ayi sai dai ayi suna bayan ɗan ƙaninsu....
       A hankali ya kai hannu ya dafa kafaɗar AA dake danna waya yana wani ɗan munafukin murmushi. Sai kuma ya ɗan leƙa yaga uwar mi yake kallo. Hotunan Maanal ne da alama kuma yanzu take turosu, yana leƙowar AA ya kife wayar cike da shagwaɓa ya ce, “Yaya ba ƙyau fa leƙen asiri”.
     Dariya Fawzan yayi sosai, ya ce, “Ganin Lillyn ne leƙen asiri kenan. Kai ni fa wlhy kallon Maanal nake kamar tare aka haifemu a gidan nan, dan ko sanda bama tare sai na dinga jin kamar an cire mana wani ɓangare na gidan ne, data dawo sai naga mun cika cif, kai tsaye mu huɗu nake kallo a matsayin ƴaƴa a gidan nan. Ban sani ba kodan a gabammu ta tashi ne oho”.
     Murmushi AA yayi yana sauke ajiyar zuciya kawai. Yaya Fawzan ya cigaba da faɗin, “Na gamsu da shawarar ka Auta, amma kai ya kake ganin zamu ɓullowa al'amarin, ni bana son Mamy ta fito da al'amarin nan fili harma wani ya kalleta da wani abu daban, dan tunda har na fara wannan tunanin na miyasa take son zaɓa mana mata ALLAH wasu ma zasuyi. Ko kai na tabbata zakaje kaita tunane-tunane ne yanzu”
        Tausayin yaya Fawzan AA yaji a ransa, dan da yasan yanda yasan wacece Mamy da bai faɗi haka ba. A fili kam sai ya ce, “Karka damu ka bar komai a hannuna”.
      “Ka faɗa min me zakayi mana?”.
“Zanyi magana da Aba, bayan sallar nan kawai ayi biki”.
     “Kai baiyi kusa ba Auta, yarinyar fa bata kammala makaranta ba”.
“Ba wani kusa Yaya, makaranta kuwa ta gama a ɗakinta. Ai aure bai hana karatu, haka karatu bai hana aure. Mu shaida ne akan hakan tunda Oum hatta Secondary a gidan aure tayi”.
          “Hakane na fahimta. ALLAH ya shige mana gaba”.
    “Amin ya rabbi. Yanzu yarinyar mika bata na gift ɗin salla”.
        “To baban soyayya, ka manta nace maka ko Oum bata sani ba”.
    “Tadai barku Yaya, Oum ai ba uwar banza bace idonta na'a kan dukkan notsinmu. Manta da wani kar kowa ya sani muje a saya mata gift”.
    Yay maganar yana kallon agogon hannunsa. Murmushi kawai Fawzan yayi, a ransa yana jin daɗin samun Ajwaad a matsayin ƙani. Key ya lalubo a jikinsa ya tada motar suka fice a gidan......

      _________★

       YAU TAKE SALLAH

    Ta kowane ɓangare yau bakunan ɗaukacin musulmai a buɗe yake da murmushin farin cikin zagayowar wannan babbar rana da akan risketa ne sau biyu rak a shekara. Farin ciki ne da baya ɓoyuwa a fuskokin yara da manya maza da mata. Tako ina anguwanni sun kacame da ƙamshin girke-girke na musamman. Sai kuma shiri da kowa keyi na sallatar idi.
      Anan gidan Darma ma hakan take, dan tunda akai sallar asuba Oum bata bar kowa ya koma barci a yaran ba. Tuni masu wanka sun fara, masu taya aikin haɗa abinci sun fara. Zuwa bakwai kowa ya gama shirinsa gwanin sha'awa kamar ka sacesu ka gudu. Baka jin komai sai ƙamshin turarurruka masu ratsa zuciya. A irin wannan ranar tako wace shekara abincin da ake karyawa da shi kafin tafiya sallar idi ana samar da shi ne daga sashen Mamy, dan haka kowa na kammala shirinsa can yake tafiya. Dama masu aiki duk can suke tattaruwa a haɗa abincin. Su kuma masu haɗa abincin salla suna anan sashen Oum ne, idan an dawo anan ake yada zango.
Tuni Hajiya Oum tauraruwar Abah ta kaɗa kan yammatanta zuwa sashen Mamy ɗin. Tayi ƙyau harta gaji, kodan Oum ɗin ba haihuwa tayi akai-akai ba tana nan da ƙyanta da ƙyawun jiki kai kace ma itace amaryar gidan. Dan koda suka shigo harga ALLAH sai da Mamy taji zuciyarta ta motsa da salon gayun Oum ɗin, ba yaune farko ba, koda fita zasuyi tare har shakkar kwalliyar Oum take ji dan Oum akwai gayu. Cike da dakewa Mamy ta ƙawata fuskarta da murmushin dole suka rungume juna ita da Oum ɗin tare da yin happy salla. Dai-dai nan Abah da Yaya Fawzan suka shigo, babu kunya ya rungume Oum yana raɗa mata happy salla a kunne. Murmushi tayi ta amsa masa cike da jin nauyin yaran. Matsawa yay ya rungume Mamy data cika tai fam a zuciya itama. A bayyane yace mata happy salla, sai hakan ya sake ƙuntata ta taji a ranta wani abu ya faɗama Oum ita bai faɗa mata ba. Fawzan ma Oum ya ɗan fara rungumewa yay mata Happy salla kafin Mamy, sai Nibras data shigo yanzu cikin kwalliya dan yin hakan kamar al'adar gidan ce a duk irin wannan ranar. Sam hankalin Nibras a son ganin AA yake kawai, dan haka a fisge tacema Fawzan ɗin happy salla kawai ta matsa ta rungume Oum sannan ta matsa ga Mamy, Abah kuma ta risina ta gaisheshi shima tamai happy salla. A lokacin da Fawzan ke rungume Nibras ido suka haɗa da Najma. Ta wani ɗauke kai gefe idanunta cike da kishi. Murmushin yayi, kafin ya nufi ta inda take cike da iya taku yay kamar zai ɗauka abu a dining, cikin kunneta ya ce, “Sorry love a huce happy salla”.
      Dai-dai nan Saheeba da Babban yaya da yara suma suka shigo........✍️








*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖5️⃣9️⃣


______________


.......Suma dai haka sukaje suka rungume su Oum Babban yaya harda Abah ita kuma ta risina ta gaida Abah, Fawzan da Babban Yaya ma suka rungume juna. Kamar an saita dai-dai nan AA ya shigo shima. Da Abah, Babban Yaya, Fawzan, AA ɗin duk farrar shadda ce da akaima ɗinkin babbar riga na zamani, sai dai kowa da kalar nashi design ɗin. AA bai damu da saka manyan kaya ba, shiyyasa idan ya saka sai su masa wani masifar ƙyau. A haka ma bai saka babbar rigar da hular ba duk suna a hannunsa. Sai wata ƴar shopping bag mai shegen ƙyau da tambarin MAWAAD a jiki a hannunsa. A kaikaice ya gama kalle falon amma bai hango zinariyarsa ba. Cikin dakewarsa ya ƙarasa ya fara rungume Oum tare da mata Barka da salla. Ta shafa fuskarsa da murmushi ta amsa masa. Shima murmushin yayi ya buɗe bag ɗin hannunsa ya fiddo wani ɗan ƙyaƙyƙyawan box fari tas ya buɗe. Haɗaɗɗen agogo ne new design daga MAWAAD ya ciro, hannunta ya kama ya cire agogon data saka ya saka mata wannan tare da zobensa shima mai ƙyau, sai ya kama hannun ya sumbata. Hawaye ne suka cika idon Oum, ta sake rungumesa tana sanya masa albarka.
      Gaban Abah dake kusa da Oum shima yaje, ya rungumesa ya masa Barka da salla shima ya saka masa nasa agogon. Albarka sosai Abah yake saka masa harma da sauran ƴan uwansa. Sai Mamy data gama cika da kishi da baƙin ciki, a ganinta ita ya dace AA ya fara yima haka ba Oum ba. Sarai ya fahimci hakan a cikin idanunta amma sai ya basar ya mata murmushi itama yay hugging ɗinta yay mata barka d salla ya saka mata nata agogon. A taƙaice tace ALLAH yay masa albarka. Bai damu ba ya ƙarasa ga babban Yaya, shima dai haka yay masa, sannan Yaya Fawzan. Dai-dai yana sakin Yaya Fawzan dake masa raɗar shaƙiyanci a kunne Maanal da Batool suka shigo. Dama ta tsaya yima Batool ɗin kwalliya ne saboda barci data koma da ƙyar aka tadata tai wanka. Wani irin harbawa zuciyar Nuratu da itama take fitowa a lokacin cikin matsananciyar kwalliya da Nibras da AA sukai a lokaci guda. Dan harga ALLAH Maanal ɗin tayi shegen ƙyau a Abayar data sanya fara tas da ɗan kwalliyar ash kaɗan like kalar aikin jikin shaddar AA, sai handbag ɗinta itama ash mai shegen ƙyau designer, hakama takalman ƙafarta, duka suna cikin kayan da AA ya bata jiya kuma shine yace ta sanya su yanzu. Bata fahimci ma'anar hakan ba sai yanzu ta gane ashe anko yake son suyi. Sai ma taji kunya ta kamata ALLAH. Amma sai ta basar ta dake. Suna ma haɗa ido ya wani ɗage mata gira sama sai ta kauda kanta tana guntun murmushi ciki-ciki.
      Abah ta fara risinawa ta gaida, ya amsa mata da kulawa, tai masa barka da salla ya sanya mata albarka. Sai ta matsa ta rungume Oum dake ta kallonta dan kwalliyar ta mata ƙyau sosai. To dama kowa ai yasan Maanal da shegen son gayu da ƙyale-ƙyale. Duk da Hararar da Mamy ke mata a kaikaice yitai kamar bata gani ba taje itama ta rungumeta. Kafin ta gaishe da Babban Yaya sai Yaya Fawzan. Ta haɗa Saheeba da Nibras da duk ciwon hassada ya kamasu da ganin kaya masu mugun tsada da Maanal ɗin ta sanya a jikinta tun daga kan abayar har bag zuwa takalmi. Dan a yau kam sun sake tantance lallai AA yafi mazansu kuɗi, saboda ita Saheeba tana saida kaya tasan nauyin kowane irin kaya. Musamman su abayas, lass's, atamfa, da shadda da yadi na maza. Ita ko Nibras uwarta ƴar gayu ce kuma ƴar ƙarya da son ƙyale-ƙyale dan haka irin wannan manyan kayan tun suna yara koda bala'i uwarsu kan haɗa ta siyama kanta, ko koda kuɗin cuwa-cuwa na mutane😆😜.
       Kan Maanal a ƙasa ta juyo domin gaida AA kawai bawan ALLAH ya rungumeta. A kunne ya raɗa mata, “Barka da salla and matsowar shiga daga ciki Mrs Ajwaad. You look great in white”. Gaba ɗaya sai taji ta daburce. Balle ma da Yaya Fawzan ya wani ce. “Aouwwwww!! Kaga Masoyan asali”.
       Sosai kunya ta sake dabaibaye Maanal. Ta janye jikinta tana ɓoye fuska da veil ɗinta da tai rolling yay mata ƙyau kamar ka saceta ka gudu. Hannu AA ya kai zai ƙwace wayar Yaya Fawzan dake musu video. Yay saurin sakawa a aljihu yana dariya. Ganin haka sauran yaran dake musu hoto da videos suma suka shiga ɓoye wayoyin suna gimtse dariya. Oum, Abah, Babban Yaya ma dai murmushi duk suke. Yayinda

119 / 213

Chapters