AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   202 / 213

603K to 606K   out of 636.6K words

duniyar mutane na😩😩.198


........Ba ƙaramin tashin hankalin RK yayi ba da bayanin likitan, cikin rashin yarda ya ce, “Dr. Hamaad, how could you say that? She's my family. I can't believe this! This can't be true. Ta ina zata samo wani HIV?”.
       “I'm sorry Sir, shiyasa na fara samunka da maganar dan nima abin ya taɓani sosai.”
      “No, I think it's the machines namu na lab na buƙatar canjawa. Amma kaga muje zan duba da kaina”.
   Ba musu Dr Hamaad ya miƙe suka fita tare, dan shi dai bashi da haufi aikinsa nakan dai-dai gaskiya. RK da kansa ya sake ɗibar jininta ya wuce lab ɗin. Anan ɗin ma komai da kansa yayi. Abin mamaki result ɗin ne dai irin na ɗazun yanzu ma ya fita. A rikice ya sake komawa ɗakin da Mamy take tare da Nurse, yawunta suka ɗiba, duk da a yanzu basa amfani da fitsari wajen gwajin HIV dan ya zama tsohon yayi haka yasa tayo fitsari. Nan ma aka sake gwajin yawu da fitsarin. HIV dai ta ƙara bayyana. Ya subahannallah mike shirin faruwa haka. Idan matar nan nada wannan ciwon a ina ta samu? Yayansa da Auntynsa kuma fa?. Karo na farko da a cikin aikinsa na likitanci ya ji abu mai girma da nauyi ya cushe nasa zuciya. A duk bibiyar Mamy da yake na tsawon shekaru da aƙalla yanzu akai huɗu bai taɓa kamata da sabga ta bin maza ba, wanda tayi kafin aurenta daban. A wannan gaɓar zai shedeta, bata bin malamai, bata bin maza. Tsantsar mugunta ce kawai a ranta da busashiyar zuciya. To a ina aka faɗi a ragaya kenan?.
     Kasa bayyana ma kowa wannan magana RK yayi, dan washe gari ma su Umma suka iso Abuja daga Kano ita da Gwaggo Khadijah. Sai ƴammatan family ɗin su biyar da masu aiki. Gidan Darma aka shiga gyarawa lungu da saƙo. Da yake Nibras na nan Umma tace ta gyaro ɗakin Yaya Fawzan, su Lailah kuma suka gyarama Najma nata. Itama Saheeba ta gyara na babban Yaya, nan ma su Lailah suka gyara na Ameerah. Sashen su Maanal babu kowa, aka gyara falon sama sai ƙasa zuwa bedrooms na ƙasa da kitchen. Sai bedroom ɗin dake sama babu kowa ciki aka fidda kayan ciki tas aka gyarashi ma yara, komai na ciki bibbiyu aka saka ɗakin yay masifar ƙyau, kai daka gani kasan kuɗi yayi aikinsa. Sashen Abah ma ko'ina an gyara banda bedroom ɗinsa. Oum kuwa ko'ina an gyara mata fes itama. An ma flowers ɗin gidan gyara zuwa garden sannan aka zuba decorating na tarbar baƙin duniya. Kai daka ga gidan kasan yasha gyara. Motoci kaf bola sai da ya gama wankesu aka maida kowacce muhallinta tunda masu ita zasu dawo.
     Duk wannan bidirin gyara da akeyi su Umma ne kawai ke abinsu. Amma karka tona zuciyar Saheeba, Nuratu, Nibras kaga yanda suke a ƙuntace. Kai dukansu babu wanda baiyi addu'a a zuciyarsa ALLAH yasa jirgin da zasu shigo yay haɗari ba tsabagen baƙar zuciyarsu. Oho su suka san sunayi, family na Darma basu san sunayi ba kam...

       Kwanan su Umma uku a gidan aka sallamo Mamy, zuwa lokacin komai ya gama dai-daita a gidan. Sam bata so aka sallamota ba muguntar RK ce kawai, dan yace wlhy sai tazo ta zauna a gidan komai na shagalin suna so yake ayi akan idonta. Dan haka ma yasa aka sallameta akan doctor zai cigaba da zuwa gida dubata. Batun result na HIV kam bai gayama kowa ba ya adana ya ajiye har sai su Oum sun dawo suma ya musu gwaji.
    Kwana biyu da sallamo Mamy ahalin Darma suka fara isowa daga Kano, dan kuwa zuwa jibi ake saka ran saukar ƴan saudia suma. Babu kuma wanda ya leƙa Mamy a cikinsu har su Umma data samu a gidan. Washe gari Amaal ta iso itama, dole Shahidah da Aunty Sakeena, sai Salimar Hajiya Yaya suka dawo nan suma sashen Maanal, dan zuwa yamma ƴan Giro zasu iso suna hanya Daddy ya aika musu da mota ta ɗakkosu tunda basu halarci bikin ba ayi bikin suna da su. Harda Babu za'a taho dan zasu ƙara ganin likita shi da su Gwaggo dan haka har da su. Kai Harda Sule da Haƙila dake fama da ciki ta dage sai tazo itama. Da yake babu mai iya saka su ko hanasu dole aka barsu.
      Dole Amaal ce ta buɗe bedrooms ɗin su Maanal ta gyaro tsaff, babu wanda ya hau musu upstairs duk suna a ƙasa. Ƴan Giro dama gida Daddy ya bayar can za'a saukesu. Washe gari aka tashi da shirye-shiryen suna dana tarbar masu jego duk da dai ba gobe ne sunan ba....

_________★

          Gaba ɗaya al'ummar Giro ruɗewa sukai da ganinsu a garin Abuja. Yo wannan al'amari haka kamar ba'a duniya ba. Basu ƙarasa zarewa ba sai da aka iso dasu masaukinsu. Gida ne dake da komai a ciki Daddy ya bayar aka saukesu. Ɓangaren mata da ban na mazan daban duk da mazan basu da yawa sosai duk yayun su Maanal ɗin ne ma sai wanda ke matsayin kawun nan su biyu. Sai Babu da Sule. Dukansu dai mazan su goma ne. Matan ne dai fa suna da yawa damma an hana zuwa da yara. Masu goyo ma in dai ba ƙaramin ɗane da kai sosai ba ance su barsu gida, tafiyar kwana uku dai ALLAH na tuba. Kuma dama dai masu tsara tafiyar sai da suka zaɓi waɗanda  suka dace gudun zuwa a zubar da mutunci.
     Ammie da Hajiya Yaya da Nene suka tarbesu a gidan sun tarbesu da lafiyayyen abinci, dan girki akai musu sosai na gani na faɗa. Aifa ba wasa sukaci sukai nak, daga haka akai zaman gaishe-gaishe da barkar samun ƙaruwa. Duk da Sule yabi jama'a ya nuna musu hoton yara a waya da su Amaal suka tura masa haka Hajiya Yaya ta sake nuna musu. Aka kuma sanar musu sai gobe in sha ALLAHU mai jego zasu iso daga saudia. Jinjina kawuna suka dinga yi, kowa a ranta tana sake yarda Asiya da ƴaƴanta sun sami duniya. Yanzu haihuwar ma baza'ayi ba sai a wata ƙasa. Duk da dai dama sun san Maanal ɗin bata ƙasar tun dawowar su Giro.
      Hajiya Yaya ce kawai ta koma gida, amma Nene da Ammie anan zasu kwana tare da su. Sailu da Gwaggo abin duniya ya ishesu, duk sun tsangwami kansu, to dama babu mai shiga sabgarsu. Koda suka taho zuwa Abuja nan ma kowa ƙin zama yay a kusa da su doke sai a gaban mota aka haɗosu su biyu. Kai daka ga yanda suka rame suka bushe sunyi baƙi kasan babu lafiya. Garama ita Sailu an ɗorata a magani daman, Gwaggo ko sai yanzu za'ayi mata gwaji a tabbatar da HIV ɗin ko babu.. Haka suka dinga kukan zuci suna bin Ammie da kallo. Sun dai tabbatar da yanzun kam WITSIYAR RAƘUMI tayi nesa da ƙasa. Ammie ta zame musu RAINA KAMA KAGA GAYYA musamman ma Gwaggo. Yau babu Lubabatu da Umar data tsana a duniya ga ƴar Lubabatu da Umar ta zame mata ɗan hakkin daka raina......

_________★

        A nan Saudia kam Maanal da twin's na samun dukkan kulawar data dace ta ɓangaren lafiya da na family, dole Oum da su Ameerah suka wuce Dubai a washe garin cs ɗin, dan lissafin ya canja, dukkan sayayyar da akai a baya ta yaro ɗaya ce. Yanzu kam dole a ƙara tunda ALLAH yay musu ƙyautar biyu. Anan kuma su Yaya Fawzan sunata haɗa abinda ya dace suma sun tura komai Nigeria, sai Abah da AA ne ke tare da Maanal da Babies duk da bama wani barinsu ake koda yaushe suna ganinsu ba sau ɗaya ne a rana. An bama Maanal isashen lokacin hutu ita da yaranta. Aiko tana shan barci sosai bana wasa ba, dan yunwa kawai ke tashinta hakama yaran da ake ba nn da ƙyar tana mita da shagwaɓar zafi-zafi. Wani lokacin dole Doctors ɗin ke neman taimakon AA idan za'a basu abincinsu. Sai ya zauna yana lallashinta da bata baki take haƙuri su sha yanda ya kamata. Gashi kuma Alhamdullah suna wadatuwa da abincinsu. Duk da ma AA ɗin tausayin Maanal yasa kai tsaye ya nema shawarar likitar akan haɗa musu da madara tace hakan yayi. Dan haka yaje ya kwaso irin wadda ta dace ana haɗa musu da ita. Da rana kawai suke shan nn, da dare kuma madara dan ta samu tayi barci ta huta itama. Aiko tsarin yayi, da alama hakan kuma zai tafiyar da tarbiyyar yaran akan cin abincin dare dake jikin mahaifiyarsu. Maanal nada jiki mai ƙyau, a kwana shida kacal abubuwa suka fara daidaita mata sai dai abinda ba'a rasa ba dan cs ba'a rabashi da tsarabe-tsarabe a jikin wanda akaimawa. Kawai dai wanda basu gane bane suke ɗauka cs yafi haihuwa sauƙi. A kwana na tara suka bata sallama, a kuma ranar su Oum suka dawo saudia, dukan sayayyarsu sun turata gida Nigeria. Babu zama suka fara shirin wucewa suma washe gari dan dangi sun ƙosa su koma. Suma dai a ƙage suke da komawa ƙasar haihuwarsu haka nan musamman Abah da Oum dake neman watanni bakwai.
        Alhamdullahi a yau da Maanal ke cika kwanaki goma ciff da ciro mata kyawawan yaranta jinin Darma da kallo ɗaya zaka shaida haka babu tambaya suka iso gida Nigeria. A mamakinsu sun sami zuri'ar Darma dana Chalawa cike da airport sun zo tarbarsu. Babies na hannun Babban Yaya da Yaya Fawzan, AA angon ƙarni na riƙe da Bestynsa. Yayi ƙyau cikin ƙananan kayansa na fama, itako tana sanye da Abaya ƙirar Egypt kalar oxblood datai mata masifar ƙyau, dan jegon ya sakata zama wata shar da ita. Kumburin nan da tayi duk ya saɓe sai wani uban haske da glowing fatanta keyi like wata laɓuɓuwa can. Bata wankan jego ba wani shan kunu da su miye-miye namu na gargajiya tsabar kulawar data samu a asibitin ce da abincin da suka tsara mata tana ci ne da nutsuwa waje ɗaya, ga isashen barci babu wata hayaniyar ƴan barka ta sakata komawa hakan. Ƙanshi kam da Oum ke dafata da shi ya zauna ɗaram kamar ba maijego ba ya subahannallah........✍️


199


........Suna ƙarasa fitowa inda mutane suke akai musu caaa. Tsabar iya shege irin na oga AA yaƙi sakin Maanal, duk ma wanda zai zo rungumeta sai da ya rungumeta a hakan. Har gwada cire hannunta tayi a nashi saboda kunya amma bawan ALLAH yaƙi bata dama ya katantane. A haka kuma ya jata har gaban su Ammie da su Umma suka gaishesu. Kunya kamar ta nutse shiko ko'a kwalar rigarsa. Yo tunda bai barta ba a gaban Abah da Oum ai dole kowa ma ya shafama kansa lafiya.
     Kowa ya shiga mota, RK ya ɗauki maijego da angon ƙarni a mota ta musamman da aka tanada domin su. Ashe a can ma gida danƙare yake da mutane ƴan suna domin tarbarsu. Dan yau har ƴan Giro an kaisu can gidan ne. Duk da magrib na neman rufawa sai da Maanal taga garin ya canja mata. Gaskiya Nigeria muna buƙatar canjin shugabanni adalai, masu zuciya da son inganta rayuwarmu da zuciya ɗaya. ALLAH yayi mana dukkan arziƙin da zamu gina ƙasarmu ta kamo waɗan can ƙasashen koma ta fisu amma son zuciya ya hana manyanmu hakan. Mutum ɗaya sai ya handame kuɗaɗen da zasu wadatu mutanen jiha guda. Amma dan mugunta da son zuciya ya tafi wata ƙasa ya zube musu su su ƙaru. Ƙasarshi da al'ummar sa kuwa ko oho. Idan ka shiga ƙasashen duniya kaga fariyayyar da manyan ƙasarmu keyi da dukiyiyinmu su da ƴaƴansu dolene kaji ka tsanesu ka raina tunaninsu. Amma ba komai ai ALLAH baya barci...
         Kissing ɗin kumatunta da AA yayi ne ya dawo da ita hayyacinta, ta kallesa suka sakarma juna murmushi. Cike da raɗa ya ce, “Mi Bestyna ke tunani ne? Bayan gani a kusa da ita”.
        A hankali ta sake lafewa a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya, bata ɓoye ba ta sanar masa komai. Shima lips ɗinsa kawai ya cije a hankali. Dan irin wannan ciwon da raɗaɗin halayyar mayan ƙasarmu ya jima da zama gyambo a zuciyarsa. A haka suka iso gida, tun a gate suka fahimci lallai an shirya musu tarba ta musamman, dan gate ɗin kansa yasha decorating, ga wani ƙaton Symbol da aka rubuta sunansa dana Maanal ɗin da hasken wuta, ƙasa kuma na ƴan biyu abin masha ALLAH. Sai suka sauke ajiyar zuciya a tare da har ta saka RK da Uncle Modibbo dake gaba yin ƴar dariya.
     Maigadi ya wangale gate suka shige, wani irin ƙyau gidan yay musu ga ko'ina cike da dangi. A farkon shigowa RK ya tsaya, basu fito a motar ba aka kawo musu yaran sannan kowa ya amshi ɗaya. Suka ɗan zuba musu ido sai kuma suka ɗago suna kallon juna. Murmushi sukayi AA na wani kashe mata ido ɗaya. Sai abin ma ya bata kunya ta kauda kanta gefe tana cije lips da murmushi. A dai-dai lokacin aka basu damar fitowa. A tare suka fito a nutse, yaran na jikinsu AA ya zagayo inda take tsaye ɗauke da Hussain, shi kuma Hassan ne a hannunsa. Koda yazo sai ya maida yaran a hannunsa ɗaya ya rungumota da hannu ɗaya itama jikinta na'a rabin jikinsa. Ai ƴan Giro sai suka saki baki da hanci suna kallonsu, tab ɗin yo wannan rashin ta ido har ina?. Oho basu san sunayi ba, suko Darma Family ko'a jikinsu. A nutse Maanal suka shiga takawa gaban kowa daki-daki suna gaisuwa ana kallon yaran a haka. Dan Hajiya Shuwa ta kawo shawarar, Abah da kansa ya bada goyon bayan kafa wannan dokar sakamakon zuwa yanzu Mamy ta busar masa da zuciya baya jin yarda da kowa kai tsaye. Duk wanda sukaje gabansa zaima yara addu'a yay musu congratulations na samun ƙaruwa. Har ƴan Giro da Maanal taji masifar daɗin ganinsu. Hakama ƴan uwanta duk suna nan har ƴaƴan Daddy, Huznah ce kawai babu amma har Yaya Yazeed yazo.
     Koda suka iso gaban Nibras da Saheeba da Nuratu dake a waje ɗaya da ƙyar suka haɗiye abu daya tsaya musu, shakkar AA ta sakasu gaishe da Maanal, duk da dai ita kafin ma suyi magana ta gaishe da Nibras da Saheeba, Nibras da Nuratu sun ƙure AA da kallo kamar zasu cinyeshi, shi kuma yayi kicin-kicin da fuska kamar ba shine ke ɗan sakin murmushi kaɗan ma mutane ba. Manaal da duk ta lura da su ta girgiza kai kawai. Sun ma yaran addu'a da ƙyar, Maanal ta amsa AA kam ko uffan bai ce ba. Daga haka suka wuce sashen Mamy Aunty biye da su dan ita bata fito ba bata jin daɗi. AA baiyi niyyar zuwan ba Maanal ta ɓata fuska da jan hannusa dole ya haƙura suka shiga.
        Shegiya Uwangale makiran duniya, tana zaune a ƙasa ta kama ƙafar Mamy dake zaune a wheelchiar tana daddana mata. Nan ko da zaginta take tana jin motsin taɓa ƙofa ta kama ƙafar. A kallon farko da Maanal taima Mamy zai da zuciyarta ta motsa. Shi kansa AA ɗin sai da yaji tsigar jikinsa ta tashi. Uwa uwace duk lalacewarta. Amma haka ya daure ya dake bai nuna a fuskarsa ba, dan sun gama haƙƙaƙewa a ransu hakan da suke mata suna nuna kamar basu damu da ita ba maybe ya canja mata zuciyarta mai cike da tsatsa.
       Itama kallonsu take, kallon dake bayyana abubuwa da yawan gaske a cikin idannunta. Amma haka Maanal ta dake ta je har gabanta ta duƙa tare da ɗaura mata Hussain dake cikin ƙyawawan kaya farare ƙal masu haɗe da showal, ga wani ƙamshi mai sanyin daɗi da sakarma zuciya nutsuwa na fita a jikin yaron. Sun huce abinsu sun ƙara ɗan girma fiye da sanda aka haifesu ƙananu da su fit-fit. Wani irin harbawa zuciyar Mamy tayi tamkar zata fasa ƙirjinta ta fito. Kawai sai taji ma jikinta na neman fara rawa dai-dai shima AA ɗin na ranƙwafowa ya ajiye mata Hassan kamar yanda yaga Maanal tayi. Sai kawai Mamy ta zubama yaran ido, a karo na farko wasu hawaye masu azabar zafi da gudun tsiya suka shiga rige-rigen cika mata idanu dan sai taga kamar twin's ɗinta data haifa bayan haihuwar AA suka rasu, sai kuma gasu da gudu sun zubo suka ɗiga akan yaran. Abin kamar wani almara Hussain ya wani ɗaɗe da kuka kai kace ruwan dalma aka zuba a kanshi.
       Gaba ɗaya sai Mamy ta rikice. Cike da suɓucewar harshe tana kallon su AA da sauri tace, “Wlhy ba abinda nai musu” sai kawai ta fashe da kuka. A hankali AA ya maida kansa ya duƙar, Maanal kuma ta sake matsawa ta kama hannun Mamy data ɗaga sama kamar wadda tai surrender ta riƙe cikin nata. Cike da lallashi da tausasawa ta ce, “Mamy Please calm down. Mu ma mun san babu abinda zaki musu, haka Hussain yake da rigima sosai. Dan ALLAH ki daina kuka”.
      Wani shegen murmushin ƙeta Uwangale ta saki, Maanal da ko kallon Uwangalen batai ba tunda ma suka shigo ta cigaba da faɗin, “Mamy ina yini? Ya ƙarfin jiki?”.
      Zafi sosai Mamy ke ji a ranta, zafi irin wanda kamar ta shaƙe Maanal da waɗan nan yaran da suka mamayeta suka zo duniya a gaɓar da rayuwarta ta gama rugurgujewa. Maanal dai da ta tsana, taƙi alaƙarta da ɗanta mafi soyuwa a ranta yau itace ta haifa yara har biyu da shi. Hakan na nufin bata fita da komai a gidan Darma ba a yanzu. Miyasa ƙaddara zatai mata haka, miyyasa? Saboda mine....
        A zuciya take duk wancan tunane-tunanen. A zahiri kam muryarta na rawar tahowar sabon kuka batare data amsa Maanal ba ta zubama AA ido tare da kiran sunansa. Shiru yayi yaƙi ɗagowa tamkar bai ji ba, tsahon minti ɗaya sannan ya ɗago babu wasa akan fuskarsa ya kalli Uwangale.

202 / 213

Chapters