Author : Bilyn Abdull Category : Romance
ra'ayinsa akan business ma. Wannan shine sanadin da muka yanke shawarar fara business ni da Darma, batare da sanin kowa ba muka haɗa ƴan kuɗaɗenmu muka fara saro yadika, takalma, da ƙananun kaya muna kawowa cikin makaranta. Al'amarin kamar wasa sai cinikin ya ɗaukaka, takai har malamai sayen kayanmu sukeyi. Hakan nama wasu zafi ganin anƙi hanamu, bayan kuma dokane yin business ɗin a cin makarantar. Takai wasu har suna ganin dan iyayenmu nada kuɗi ne kawai. Surutunsu bai sa an hanamu ba, mu kuma bamu fasa ba. Ikon ALLAH kafin mu kammala sai ga jari ya zauna mai nauyi saboda kuɗin da dana yanzu darajarsu ba ɗaya ba. Mun kammala karatu mun dawo gida, ga jari mai tsoka a hannunmu, sai dai bamu sanar da iyayenmu ba muna son muyi surprise ɗinsu. Kwatsam mun dawo gida da sati biyu kacal kamar saukar aradu sai naji wai an ɗaurama Fateema da Aliyu aure. Babbar magana, taya haka zata faru bayan iyayensu ɗaya. Hankalina ya tashi mamaki ya kamani nazo ina tambayar Aliyu, bai ɓoyen komai ba ya gaya min alaƙarsa da Fateema. Al'amarin ya zafeni, ya kuma dakeni a zuciya dan ban taɓa tunanin Darma bai ɗaukeni yanda na ɗaukesa ba gaskiya. Kufa gane ba son Fateema nake ba sam. Amma sai kawai na samu kaina da jin haushin auren nasu. Dama ga wani kaffa-kaffa da Aliyu keyi da Fateema tunda muka fara jami'a like baya son na raɓeta saboda yana min kallon mazinaci.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣5️⃣9️⃣
______________
.........A'a al'amarin fa ya fara damuna da min zafi, ya mutum ina tare da shi yasan halina sarai amma yaƙi yarda dani. Bafa gidansu sunfi gidanmu kuɗi bane ba balle yace maula nake masa. Sannan ba ilimi ya fini ba balle tarbiyya balle yace gidansu sunfi namu iya tarbiyya. Gefe ga wani abokina yanata sake zugeni akan wulaƙancin da Aliyu ke min na hantara da nuna ƙyamatar halayena a gaban kowa har baya iya barina na sake da ƙannensa ma musamman Fateema, duk iya ƙyautatawar da nake ma yarinyar sai kaga yana gwaleni. Kawai wataran anyi ruwa muna tare da abokin nawa sai ga su Fateema da ƴan biyu sun taso islamiyya, tanata fama da su ƴan biyu suyi sauri wani hadarin na tasowa amma sunƙi sai ma wasansu suke. Ni uban ƴan gwaninta sai na daukar mata Hussain abokina ya ɗauki Hassan ita kuma na kama mata hannu dan iska ta taso mai ƙarfin gaske har ba'a iya ganin hanya da ƙyau. Taso kwace hannunta sai naƙi saki, nai mata tsawa akan bata ganin iska ko so take ta tafi da ita. Fateema nada tsoro sai ta nutsu, sai dai sai hawaye takeyi alamar dai bata so ko kuma tsawar dana matan ce ta mata zafi oho mata. Mun shawo kwanar layin su sai ga Aliyu a motar gidansu zaije ɗaukar su Fateema. Mun tsaya ina cema yaran yauwa ga yayanku nan ma zaije ɗaukarku kawai naji saukar naushi a fuska, kafin na dawo hayyacina na gama tantance wanda yay min hakan an kwace Fateema da Hussain kawai an hau dukana. Kafin wani dogon lokaci Aliyu ya kaini ƙasa, abokina daya kawo min ɗauki ma ya nausheshi dole ya koma gefe yana ƙoƙarin tare jinin dake zuba masa ta hanci. Ga mutane nata gudun wucewa gida saboda hadari. Sai ƙalilan suka tsaya rabamu faɗan da Aliyu ne kecin nasara a kaina dan ya wanke min fuska da ruwan dagwalon ruwan farko da akayi, ya nannaushe min fuska harda idanu ya fitar min da haƙori ɗaya. Da ƙyar da ƙyar aka ɗaga Aliyu a kaina, yana huci da tabbatar min sai yay ajalina”.
“Wannan kalma itace ta fusata mamana da yayyuna sukace bazasu yarda ba, ga raunikan daya jimin. Munje gidansu kawai muka samu har lokacin ana fama da Aliyu akan shi sai ya biyoni har gida ya kasheni wai na taɓa Fateema bayan ni mazinaci ne. Ai nasan matar aure ce, miye-miye. Wannan abu yamin ciwo, ya kuma daki zukatan iyayena, suka tsareni akan kalmar mazinacin da Aliyu ya kirani babana harda marina, na dinga rantsuwa ban taɓa aikatawa ba, na kuma ce aje ayi bincike. Yayuna ne sukai dukkan binciken daya dace, suka kuma tabbatar ban taɓa aikatawa ba sai dai ina huɗa da matan a zamantakewar yau da kullum, a jami'a kam wannan normal ne ai, sai abun yay musu ciwo basuyi shawara da kowa ba suka ɗauki ƴan sanda sukaje har gida aka kama Aliyu, sai da yay kwana biyu a rufe sannan muka sani. Hakan baima iyayenmu daɗi ba, amma ni sai naji farin ciki, koba komai yanzu Aliyu yasan nafi ƙarfinsa, kuma wlhy sai na rama dukan da yay min da abu mafi ciwo a rayuwarsa da zan bar masa tabon tunawa na har abada. Bayan an fito da shi kusan da wata guda na gama shirya dukkan abinda zan masa na ramuwa na zagaye naje na sameshi na bashi haƙuri. Da farko yaƙi saurarena, dan nafi wata guda ina binsa kafin na samo kanshi. Na masa bayanin komai daya faru ya fahimta daga ƙarshe muka sasanta har ya kaini wajen su Baba suma na sake basu haƙuri na kuma yi musu bayani hatta na rufe shi da akai a police station nace babu wanda ya sani a gidanmu ma sai su Yayun nawa da sukayi. Ban san miyasa suka yarda dani ba kai tsaye a lokacin, har Baba ya shirya yaje ya samu Abbana shima suna sasanta. Wannan shine dalilin sake dawowar tarayyarmu sai dai ba kamar da can ba dan Aliyu baya taɓa barina da Fateema, yayuna kuma idan suka ganni da Aliyu sunta zagina kenan da kirana mara zuciya. Kai cikin gidansu ma yakan daɗe bai bari mun shiga ba. Haka dai muka kammala karatu muna cigaba da Business ɗin mu, dukkanin kuɗaɗen kuma na hannuna, bayan dawowar mu gida sai komai ya tsaya, maganar business kuma na cinye kuɗin bai mun magana ba nima ban masa ba. Matsalar da muka samu a result ɗinmu mu duka yasa sai da muka sake komawa makaranta mukai gyara na shekara ɗaya, bayan nan ma munfi shekara ɗaya a gida kafin mu sake komawa makaranta mu jona Masters ɗinmu. Lokacin da muke kammalawa ne kuma Fateema ke kammala tata secondary ɗin, kawai sai ga batun wai tana da cikin Aliyu. A zahiri na tayashi murna, amma a ƙasan zuciyata kishi da ɗacin hakan nake ji, sai kawai naji a raina ga hanyar dazan rama abinda Aliyu yay min kenan. Abokin nan nawa daketa nuna min illar tarayyata da Aliyu na samu da shawara, aiko ya bani mai ƙyau ya kuma nuna min hanyar dazan aywatar. Budurwarsa na aikin asibiti, ita yasa ta kawo mana wasu ƙwayoyi, yace nayi duk yanda zan yi na canja maganin da Fateema kesha da wannan maganin. Nace masa na miye? Yace bana komai bane sai na lalata mahaifar Fateema, kuma a hankali maganin zai dinga aiki baza'a taɓa farga ba sai ya gama mata illa ta fara zubar jini.......”
A wannan gaɓar a mugun firgice, a kuma tsorace Abah da Oum ke kallon Mabera. Abah daya gama kaiwa wuya zai yi magana Mabera ya katse shi da faɗin, “Ai bakaji komai ba, da zakai haƙuri dana kaika fiye da inda kake son ji.”
A hankali AA ya riƙe hannun Abah, Yaya Fawzan kuma na Oum da take kuka sosai. Ita kanta Mamy zancen ya daketa, dan Junaid bai taɓa gaya mata shine ya aikata hakan ba.
Cikin rashin damuwa Mabera ya cigaba da faɗin, “Wani irin daɗi naji a raina, haka na amsa cikin farin ciki, na kumayi duk yanda ya dace har sai da na saka maganin nan a maganin da Fateema ke sha na asibiti da suke bata akan rainon ciki. Shiru-shiru zanji wani sakamako banji komai ba har abin ma ya ban haushi na zazzagi wancan abokin nawa da kiransa maƙaryaci. A dalilin haka muka rabu da shi. Kullum cikin ɓacin rai da tunanin hanyar dazan rama abinda Aliyu yay mun nake har akace Fateema ta haihu kuma ƴan biyu ma, sai dai ɗaya ya rasu. Naji farin cikin mutuwar ɗayan, na kumaji baƙin cikin haihuwar ɗayan, amma na saka a raina yanda ubansa yay iƙirarin kasheni nima sai na kashe shi. Inata ƙullawa da kwancewa ban samu hanya ba sai da sukaje saudia wajen iyayenta dake zaune a can suka dawo sannan. Naje yi musu sannu da zuwa na shaƙama yaron abinda ya sanadin kawo masa murar da ta zama ajalinsa....”
Babu wanda a wajen nan baya ma Mabera mugun kallo da tashin hankali. Kai ita kanta Mamy baki ta saki da hanci tana kallon Junaid ɗin. Shi ko babu wani damuwa a tare da shi ya cigaba da faɗin, “Bayan mutuwarsa mukai shirin tafiya hidimar ƙasa. Har lokacin kuma ban huce ba, dan a ganina shima dole Aliyu yaji a jikinsa, amma sai nai shirin barin komai har sai mun kammala saboda anyi rashin sa'a shi Aliyu an turashi kudancin ƙasar, ni kuma anan Kano aka barni saboda tsayawar babana. Burina akan Aliyu akan dukiya ne kawai, amma kwatsam sai aka sake cewa Fateema nada ciki, tashin hankali wanda ba'a saka masa rana kenan, ai anyi ba'ai ba kuwa. Aiko sai na bazama neman mafita. Sai dai kafin ma na samota sai labari ya sameni akan Fateema babu lafiya, an kaita asibiti kuma sunce sai an cire mata ciki da mahaifa gaba ɗaya dan tana da wani ciwo har ma Babanta yazo Nigeria shima Aliyu ya dawo Kano, amma ko sanar min baiyi ba. Farin cikin dana tsinta kaina a lokacin baida misali, nan fa na shiga neman abokin nan nawa amma na gagara samunsa a ko'ina. Daga ƙarshe ma akace min yana Lagos ai. Nayi takaici, abinka da babu waya, nai masa wasiƙa dai na bayar akai masa dan kuwa dai magungunan wancan karon ne suka jawo hakan ga fateema. Bayan cirema Fateema mahaifa da ciki babu jimawa muka kammala hidimar ƙasa. Inda a hidimar ƙasar ne kuma lokacin da Kamila ta shigo rayuwata sai naji a raina zata min amfani ta min aiki musamman ganin ba ƴar kowa bace ba, sannan ita a karan kanta makwaɗaiciya ce, gata dai ƴar ƙarama kuma a fuska shiru-shiru amma shaiɗaniyar kanta ce. Kamar yanda a baya Aliyu kemin zargin ina bin mata kuma banyi haka akan Kamila ban taɓa sakama raina zan lalata mata rayuwa ba, ita da kanta ta bani kanta ta hanyar zuba min abu a lemo nasha. Koba haka ba!!??”.
Yay maganar a tsawace yana kallon Kamila. Ganin bata da niyyar amsa masa Sille ya take ƙafar dai-dai inda ya harbeta. Wahallen ihu ta saki zufar azaba na sake keto mata tako ina a jikinta. “Zakiyi magana ko sai na sake fasa ɗayar ƙafar”.
“Zanyi-zanyi. Wlhy zan faɗa musu komai nima bazan ɓoye ba”.
“Oh da kikace ke shegiya ce”. Cewar Sille yana komawa ya zauna. Sai da Mamy taja mintuna biyu hankalinta ya ɗan dawo jikinta sannan ta fara faɗin,...........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣6️⃣0️⃣
______________
........“Duk abinda Junaid ya faɗa game da haɗuwarmu haka ne, shi malaminmu ne, kuma nice na sameshi nace ina son shi. Bayan ya amince min yabar makarantar mu, ya kuma hanani ni na bari kamar yanda nai niyya, shine ya cigaba da ɗaukar ɗawainiyar makarantar tawa, ya kuma fara saya min kaya irin na ƴammata. Dan yaje har gidanmu ya nuna kansa ga mahaifina da kakata a matsayin malaminmu ne shi, tausayina ya sashi son taimaka min. Hakan da yayi ya tayar min da hankali ya kuma bani haushi, dan haka naje na samu ƙawata na gaya mata komai. Sai tace min anya kuwa Uncle Junaid na sona. Taya munyi maganar soyayya zai je gidan mu yace tausayina yake ji. Nace mata nima abinda ya rikitani kenan. Sai tace naje na samesa na tambayeshi dalilinsa nayin hakan. Na yarda da shawararta, naje nai zaman jiran zuwansa dan gidanmu yake zuwa bai taɓa yarda mun haɗu a wani waje bayan nan ɗin ba. Amma sai shiru-shiru bai zo ba har sati guda, hankalina ya tashi na shiga damuwa har kakata ta fahimta dan ko abinci bana ci na kirki, ta tsareni da tambaya sai na gaya mata gaskiya, shine take min bayanin ai Babana ne ya hanashi zuwa, dan bai yarda da alaƙar daba ta neman aure ba tsakanin namiji da mace. Idan har sona yake ance ya turo, amma saɓanin haka baba yace yayi haƙuri. Ni kaɗai nasan halin dana shiga da jin wannan mummunan labari, dan a lokacin wlhy ji nake idan ban auri Junaid ba kamar zan iya rasa rayuwata ma gaba ɗaya. Haka naje ina kuka da bama Babana haƙuri, amma sai yaƙi ma saurarena. Wannan shine sanadin fara neman gidan su Junaid ta hanyar malam mu da nasan sunyi huɗɗa tare. Da ƙyar malam Yusufa ya gaya min, ranar weekend muka ɗauki ƙafa ni da ƙawata sai anguwarsu. Kamar yanda Malam Yusufa ya gaya mana gidansu ba ɓoyayye bane a anguwar muna tambaya kuwa aka nuna mana. Sai dai mun kasa shiga ni da ƙawata. Dan bamu san idan munje mi zamu ce ba, sannan ma babu lallai a barmu dan gidan harda maigadi. Muna a wajen muna shawarta yanda zamuyi cikin sa'a sai ga Junaid ya fito. Ba ƙaramin rikicewa yay da ganinmu ba, ya shiga yimana faɗan miyasa zamu biyoshi gida, bamu da hankali ne. Ƙawata ce kawai ke ƙoƙarin bashi haƙuri da masa bayani, amma ni nayi shiru. Koramu yay yace muje gida zai zo ya sameni. Sai lokacin nai magana. Na tabbatar masa idan da har bai zo ba zan dawo kuma har cikin gidan sai na shiga. Yace zaima zo. Haka muka tafi gida bamu zanta komai da shi ba. A ranar bai zo ba, sai washe gari da yamma ƙawata tazo ta kirani gidansu, da farko nace ban zuwa dan damuwar rashin zuwansa ta sakani a wani hali, sai da ta sanar min shine yazo sannan na tashi da rawar jiki na bita. Ko kakata dake tambayar lafiya ina zamu ban kulata ba. Baƙaramin farin ciki nayi da ganinsa ba, bayan mun gaisa nai masa ƙofarin abinda yaje yace ma baba. Sai yay min bayanin shi yayi hakane saboda ya fahimci baba aurar dani yake sonyi, shi kuma karatu yake son nayi sai zuwa nan gaba muyu maganar aure dan a gidansu a yanzu baza'a masa aure ba sai nan gaba. Na fahimceshi na kuma amince, naji zuciyata tayi sanyi. A wannan zaman ne yace min zamu dinga haɗuwa gidan Malam Yusufa dake quarters ɗin malamai cikin makaranta, amma lokaci-lokaci zai dinga zuwa yana gaida baba kodan hidimar karatuna da yake son cigaba da ɗauka. A take na amince da hakan, dan haka duk juma'a muke haɗuwa a cikin makarantar mu, gaisuwa ce kawai ke haɗamu sai kuma ya duba litattafaina yay min gyara akan abinda ya gani ba daidai ba. Baya min wani hirar soyayya sam, ni kuma abinda nake so kenan dan haka abin ya fara damuna. Na samu ƙawata akan ta bani shawara. Ta girmeni sosai, dan asali ba ƙawata bace ƙawar Auntyna ce, bayan barinsu ƙasar sai bata daina zuwa gidanmu ba sai kawai muka ƙulle. Ita tana talla dan haka idannunta a buɗe suke sosai ta fini buɗewar ido. Koda na gaya mata halin da muke ciki ni da Junaid sai tace dani gaskiya akwai matsala, kuma tabbas wataran zan iya neman Junaid na rasa a rayuwata. Dan ta fahimci ba sona yake ba tausayina kawai yake yi. Amma da zan yarda da wata shawara data bani, dan itace kawai zata riƙe min Junaid ya kasa kuɓucewa daga hannuna harna samu damar aurensa. Balle gashi dan masu kuɗi. Cikin rashin damuwa nace ta faɗa min ko minene zanyi. Tace kin tabbatar? Nace kwarai ma kuwa. Tsaff ta zauna ta zayyane min komai, na tsorata matuƙa, nace mata idan yaki fa?. Tace lallai baki da wayo, an gaya miki akwai namijin da zaki bama kanki a wannan zamanin yaki, balle ma shi yace gidansu ba aure za'ayi masa yanzu ba, yaga kinzo kin nuna masa wannan kulawar ai da gudu zai amsa kuma zakisha tattali. Nace idan ya gudu fa? Tace ta ina zai gudun? Aike yanzu indai hakan ta faru kin gama samun makamar riƙeshi gam-gam wlhy, koda yayi yunkurin hakan sai ki masa barazana da cewar zakije ki sanar a gidansu. Ke harma ki dinga masa ƙaryar kina da ciki. Amma kije kiyi tunani dai.”
“Sosai hankalina ya rabu biyu da zancen nata. Ban tsaida zuciyata waje guda ba har sai da na sake tuntuɓar Junaid akan aure ya nema ɓata min rai sannan. Sai kawai na yarda da maganarta, dan haka ta koya min duk yanda zan masa. Banyi kasa a gwiwa ba na aiwatar, sai dai me, ƙiri-ƙiri Junaid ya nuna min baima gane inda na dosa ba. Daga ƙarshe ma ya kakkaɓe rigarsa yay gaba. Ban sake ganinsa ba