AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   168 / 213

501K to 504K   out of 636.6K words

tafasa, dan ko jin abinda AS ke faɗa ma ba yayi. Da wani irin mahaukacin ƙarfi ya daki desk ɗin nasa, sai da komai na kai ya girgiza kuwa wasu ma har suna zubewa. AS ya zabura, Maanal ta damƙe jacket ɗin suit ɗin AA dan itama har hanjin cikinta sai da suka kaɗa. Shi kansa Sen... Sai da zuciyar ta buga. Yay saurin janye idanunsa daga kallon Maanal ya maida kan AA ɗin. Wani shegen kallo da AA ɗin ke masa sai da yaji zuciyarsa na neman fitowa ta baki. Baima san ya duƙar da kansa ba.  A hankali Maanal ta sassauta riƙon datai masa. Sai kuma tai yunƙurin barin wajen. Hannunta AA ya riƙo, ta juyo tana kallon sa. Sai a lokacin shima ya janye kausasan idanunsa ya maida kanta. Fuska ta marairaice masa kamar zatai kuka. Dan sosai take jin tsoro na shigarta da yanayin nasa. Shima ya fahimci hakan, sai ya ɗan sassauta mata fuskar tashi. Cike da kulawa ya ce, “Ina zaki?”.
     Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke a hankali. Sai kuma ta sakar masa guntun murmushi tare da duƙowa saitin kunnensa cikin raɗa ta ce, “ALLAH ya huci zuciyar NAMIJIN DUNIYA. Har abada kai kaɗai Maanal zata cigaba da kallo a matsayin Namiji kamar yanda ta taso take kallo tun ƙuruciya. Ina ƙaunarka mijina”. Ta bashi sumba a kumatu.
       Wata irin sasaanyar ajiyar zuciya ya saki, yayinda Sen... Bukar yay wani irin runtse idanunsa dan ba ƙaramin sukar sa sumbatar nan tayi ba. Gashi kamar tayi da gayya har sai da ƴar ƙarar moouchh!!.
      Da kallo AA ya bita yana wani murmushin gefen baki harta fice. Tana gama ficewa ya haɗe fuska matuƙa. Yanda Maanal bata ko kalli inda Sen... Yake ba haka shima bai kallesan ba ya ɗauka kan waya yay danne-danne ya kai kunne. Ana ɗagawa cike da isa ya ce, “Ka sameni a office”.
     Daga haka ya yanke. Sake maida hankalinsa yay ga computer ɗinsa. Wani irin ɓacin rai ya turniƙe fuskar Sen... Bukar. Ga ganin Maanal yay masifar motso masa abinda ke kwance a zuciyarsa. Cikin ƙanƙanin lokaci  HOD ya iso. Cikin girmamawa ya ce, “Gani Sir”.
    Batare da AA ya ɗago ba yana cigaba da aikinsa cikin yanayin nan nasa na magana kamar baya so ya ce, “Bana son na sake ganin wannan fuskar a company na. Idan kuma hakan ta sake faruwa zan haɗa har da kai.”
       Sarai HOD ya fahimci Sen... Bukar AA ke nufi, hankalinsa ya tashi, dan wlhy shi bai iya irin rigimar ogan nasu ba. Dan haka cikin ɗan rawar murya ya furta, “Tanka ya daɗe dan ALLAH kazo muje.”
      Sen... Bukar da ransa ya gama kaiwa maƙurar ɓaci, ya kafe AA dake aikinsa kamar ma bai san da su ba da idanu. Sai kuma yay wani murmushi mai ciwo da faɗin, “Ajwaad Aliyu Darma ke nan. Yaro yaro ne. Ni kake tunanin wulaƙantawa dan nazo sayen  hajarka?”.
        “Hajata ta zaratan MAZAJE ce masu juya DUNIYA da iyawa, bata ƴan sai an zubar mu kwashe ba. Da kake faɗin yaro, baka san FURAR DANƘO nake ba, A SHEKARA ANA DAMU BANU FARAU-FARAU. Bana wasa da ƴan jiran jira, dana buga wani game da kai mai ban mamaki. Amma zan ajiye maka magana ɗaya kuma shawara, idan ka riƙe sai tai maka amfani ka kuma tsira da furfurarka, dan furfura kota kafirice ina ɗaga mata ƙafa. Idan kuma kace zaka cigaba da bin SAWUNA, to lallai watara TALALAƁUWAR ƙasar TAƁO zata riƙe maka ƙafa ka nutse cikin ruwan da duk iya lalube babu mai iya tsamoka. Idan ma akai rashin sa'a CIKIN KIFI ne zai zama kabarinka. Karka bari na bayyana maka ainahin kalata, dan jinin DARMA duk inda yake jini ne da ba'a nuna masa yatsa bai karya ba. Duk randa kuma na sake ganin idanunka akam MATATA wlhy saina tsiyayesu da MATSEFATA.”
         Ba Sen... Bukar ba hatta HOD ba ƙaramin razani kalaman AA suka sanya shi ba. Zuciyarsa har rawa take a cikin ƙirjinsa. Sen... Bukar kam abun cewa ma ya ƙare masa, dan haka ya gagara iya furta komai sai juyawa yay ya fita a office ɗin bayan tama AA kallon minti ɗaya cirrr. Da sauri HOD ya ce, “ALLAH ya huci zuciyarka Sir”. Ko kallonsa AA baiyi ba, dan haka ya fito a office ɗin shima yabi bayan Sen... Bukar......

    ★ Zuciyar Sen... Bukar yi take kamar zata fito daga ƙirjinsa. Ba kalaman AA bane kawai ke razanata, ganin Maanal ne. Bai ƙara tabbatar da mahaikacin so yake ma yarinyar nan ba irin yanzu. Ji yake ko ƙasa da sama zata haɗe bazai iya haƙura ba sai ya mallaketa. Dan mallakar tata kawai zai bashi dama kai AA Darma har ƙasa. Dan haka ya ɗauki ɗamarar koyama wannan ƙaramin ƙwaron hankali a cikin Abuja. Ɗaya daga cikin wayoyinsa ya ɗauka ya shiga danne-danne. Dai-dai kan sunan Rabilu ya danna kira.
      Rabilu da rayuwa taima gwatson ƙyanwa ya zama abin tausayi a tsakanin nan dan dama dai Sen... Bukar ɗinne taƙamarsa na zaune yana hamma yunwa ta ishesa tsohon kwana shida kenan ba'a ɗora tukunya a gidansa ba. Jiya matarsa ta tattara ƴaƴanta tai wucewarta ƙauye tace bazata iya ba. Babu irin roƙo da magiyar da bai mata ba harda tsugunawa amma bata sauraresa ba. Abin duniya ya ishesa ya rasa mafita gashi ba wata sana'a ya iya ba, dama direbanci ne shine ma dalilin haɗuwarsa da Sen.. Bukar ɗin daga nan ya zama kawalinsa. Jikinsa har rawa yake da ganin number ɗin Sen... Koda ya ɗaga kiran ma duk ya daburce sai haɗa gabar da yamma yake wajen gaisheshi. Cikin ɓacin rai Sen... Ya ce, “Ka sameni a gida yanzu nan”.
      “To... To to to ranka ya daɗe”.
Rabilu ya faɗa cikin rikicewa. Ai Sen... Na yanke wayar a guje ya tashi yay hanyar gidansa. Ya kamfaci ruwa ya hau wanke ƙafa da fuska da hannuwa, daƙile dai irin na ƙazaman mata. Fal-fal yay ɗaki, su dai sauran ƴan hayar gidan na kallon ikon ALLAH. Cikin mintuna biyar ya gama shiryawa sai gashi ya fito yana baza uban ƙamshi. Anci wankakken yadi gogagge harda hula. Wajen mai shagon ƙofar gidansu yaje ya ari dubu uku, da ƙyar ya bashi dan yana binsa bashin kuɗaɗen kayan abinci da yay ta amsa. Ko yanzu ma ya yarda ya bashin ne saboda in dai kaga Rabilu da shigar kaya haka to zaije wajen maigidansa ne da gaske. Aiko ya tare mashin aka kaisa in da zai hau motar da zata shiga cikin gari. Dan shi yana zaune ne a die-die. Sai faman aangale haƙora yake yana ƙara rayama ransa dole ne ya koma ya ƙarama malamin nan kuɗin aikinsa. Dama ya tabbatar masa daga randa yay masa aikin nan ya zuba ido Sen.. zai kirashi da kansa. Gashi kuwa ya gani. Ya wani sake damƙe aljihunsa yana murmushin mugunta. Ai wlhy babu ragi wannan ragowar maganin ma duk yanda zai yi sai yayi ya juye ma Sen... Bukar a inda zai taka dan dole ne ya mallakesa ta yanda har gaban abada bazai sake gangancin rabuwa da shi ba kona minti ɗaya.........✍️



*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣3️⃣9️⃣


______________


..........A ɓangaren Oum maimakon kalaman Mamy su sakata a ɓacin rai da baƙin ciki a wannan yini sai UBANGIJI ya canja mata da saɓanin haka. Bawai bata juya su a zuciyarta bane ba. A'a tanata mata uziri akan akwai dai abinda ke faruwa da bata sani ba. Dama shekaran jiya sai da sukai rigima da Abah akan rashin girkin Mamy, bama ta ganin tana zuwa sashensa. Amma sai yaƙi ce mata komai. Daga ƙarshe ma ya gargaɗeta akan ta daina damunsa barci zai yi. Shiyyasa a yau da Mamyn taso mata da wannan batun sai ta sake yarda akwai wani abu dake faruwa da bata sani ba. Kuma ta fahimci Mamyn na cikin fushi ne shiyyasa zatai mata uziri daga nan zuwa wani lokaci sai ta sameta suyi magana ta hankali.
       Wannan kyakkyawan tunanin nata ne ya kawo ma zuciyarta masalaha. Kasancewar Najma da Ameerah a tare da ita kuma ya ɗauke mata hankali. Sai kuma ga Nuwaira da Saheeba da Nuratu. Duk da zuwan Saheeba da Nuratun ya bata mamaki sai ta ƙyautata musu zato. Ta kuma dinga jansu da hira da kulawa kamar yanda sukeyi da su Nuwaira. Duk da Najma da Nuwaira sun ƙi sakin jiki da su Saheeban. Ita ko Ameerah zuciyarta ta gama raya mata abinda taji a wajen Hajiya Turai su Saheeban ke son fara aiwatarwa shiyyasa suke son shiga jikin Oum ɗin. Dan haka tai matuƙat sakama dukkanin motsinsu ido, musamman a lokacin da suka shiga kitchen yin girkin rana.
      A lokacin zaman cin abinci da Babban Yaya da Yaya Fawzan suka shigo su kansu sunyi mamakin ganin Saheeba da Nuratu a sashen Oum ɗin kuma ana hirar arziƙi. Ganin babu Nibras Fawzan ya cije baki kawai. Kamar Oum tasan tunanin da yake yi ta ɗauka waya ta kira Nibras ɗin tace tazo sashenta. Babu jimawa kuwa sai gata. Duk ta rame daka ganta kasan bata da lafiya. Ga kumburin bakinta na bubbugewar da yayanta yay mata jiya har yanzu bai gama sauka ba. Komai Oum batace mata ba bayan amsa gaosuwarta, ta gaida Babban Yaya shima sannan ta zauna. Sauran kam yanda bataima kowa magana ba babu wanda ya kulata. Sai hakan baima Oum daɗi ba, tasa a ranta dole ne tai iya ƙoƙarin ta ba ganin ta haɗe kansu waje guda. Dan wataran sune gidan, idan babu haɗin kai a tsakanin taya zasu bama ƴaƴansu tarbiyya..
      Sunci abincin a nutse, Yaya Fawzan na faɗin yayi kewar auta da Lilly. Babban Yaya ya ce, “Kayi kewarsu ko kayi kewar takura musu”.
     Dariya su Oum sukayi. Oum ta ce, “Ai wlhy kam kamar ka sani kuwa Fadeel, Fawzan ya saka min autoci a gaba matuƙa. Dan ma yanzu Auta yayi baki ramawa yake yi”.
     Babu wanda baiyi dariya ba, idan ka cire Saheeba dake na yaƙe, sai Nuratu da hankalinta ya rabu biyu. Tana jin daɗin hirar AA tana jin zafin sunan Maanal da ake sakkowa a ciki. A haka dai suka kammala, Nuratu da Saheeba da Nibras zasu tashi kamar yanda suka saba a barma ƴan aiki wahala Nuwaira tace, “Oya mu tattare kayan muje kitchen a wanke. Suma su Inte a rage musu aikin suna ƙoƙari”.
     Babu alamun damuwa a tare da Ameerah da Najma, dama su sunyi niyyar yin hakan. Amma Nuratu, Saheeba, Nibras abin ya musu ciyo, kamar su matan gida za'ace suyi wanke-wanke inama laifin girkin da sukayi. Oho Nuwaira ma batasan sunai ba. Fawzan da Babban Yaya kam daɗin abinda Nuwaira ɗin tayi aukaji sosai. Hakama Oum hakan ya mata daɗi.
       Sun gama wanke-wanken kenan akai kiran sallar la'asar. Dan haka kowa ya nufi sashensa domin yi. Su Saheeba na gab da shigewa sai ga Haule tazo kiransu wai inji Mamy. Ameerah dake gabansu sarai taji, amma sai tai wucewarta kamar bata jin ba. Su kuma kallon juna sukayi, kamar zasu magana sai suka ma suka fasa. Saheeba tace, “Ki gaya mata idan munyi salla zamu zo”.
    Har Haule ta amsa zata tafi sai kuma Nuratu taja hannun Saheeba suka bi bayan Haule. A falon sama suka sami Mamy, Haule na gaya mata saƙon su Saheeba ɗin sai kuma ga sakkanarsu. Itama sai da tayi mamakin bama Mamy ɗin kawai ba. Sai kawai ta haɗiye sauran bayanin da takema Mamyn ta fito ta bar musu falon.
      Yanda Mamy take zaune a kujera zaman ƙasaita haka suma suka zauna. Kit ɗin magani a gabanta da kofi alamar tasha shayi. Hakan na nufin bata da lafiya, sannan kayan data fita da sune a jikinta, hatta handbag ɗinta na kusa da ita ajiye ba'a kai ciki ba. Ganin basu da niyyar gasheta cike da takaici ta ce, “Lalacewar tawa takai har gaisuwa ku daina min kenan?”.
       Baki Saheeba ta taɓe, dan tafi jin matuƙar zafin Mamy fiye da Nuratu, a gadarance ta ce, “Mamy kin kiramu nan ne damu gaisheki ke nan?”.
    Tsuru Mamy tai tana kallon Saheeba. Ta jinjina kai tana mai cije lips. “Hummm Saheeba kenan, naga kwana biyun kanki na rawa a gidan nan.....”
      “Ashe ma sai yanzu kika lura”.
Saheeba ta faɗa a gatsine. Yanzu ma kallonta Mamy tayi zuciyarta na sake yin nauyi. A ranta sake jinjinama Nana take yi, wato ta gama tsarama yaran komai. Shike nan zata nuna mata cewar ta isa da gidanta. Kallonta ta maida kan Nuratu. Cikin gargaɗi da  sake kausasa harshe ta ce, “Ki shirya kayanki yau ɗin nan ki koma gidanku. Itama ƴar uwar taki tana hanyar biyo ki”.
         Maimakon Nuratun ta bata amsa sai Saheeban ta kwashe da dariya. Cike da iskanci da raini ta ce, “Ai ba gidanki bane Mamy, sannan ba wajenki take zaune ba. Nan ɗin gidan auren ƴar uwarta ne, zama daram babu fashi. Da kike cewa nima zan bita, sai dai mu bita tare ni dake. Dan kin san dai duk kanwar ja ce ai. Ta wani fannin ma gara ni, duk abinda nake yi kece kike sakani yi, sannan koba komai zan tsira da ƴaƴana. Kiji da damuwarki kinji. Idan kuma kikace zaki kafa mana karan zuƙa a gidan nan to wlhy tare dake zamu zagwanye. Sis... Tashi mu tafi”.
       Wata banzar dariya Nuratu tai tana miƙewa da faɗin, “Ai naga faɗan na surukai ne ni bai kamata na shiga ba sai idan na shigo daga ciki.” itama ta kalla Mamy ta watsar. Sai suka kwashe da dariya. Wani irin fisga numfashin Mamy keyi a ƙirjinta. Tsabar mamaki da kaɗawar zuciya ta gagara iya yin magana ma har su Saheeba suna neman ficewa, wani irin yunƙurowa zuciyarta tai ta miƙe ta finciko Saheeba baya. Ta ɗaga hannu zata wanka mata mari Nuratu ta cafke hannun ta murɗeshi har sai da Mamy tai ƙara. Dama kuma wanda ta taɓa jin ciwo ne har yanzu yana motsa mata musamman idan zata kunna ac sanyi ya shigesa.
      Nuratu ta yarfar da hannun Mamy har sai da ya bugu da kujera. Yayinda Saheeba tai wata dariya tana kallon Mamyn cikin ido. “Oh da marina zakiyi? A tunaninki wanda kikayi a waccan ranar gaban mijina ma zan barshi ne ya tafi a banza. To ki rubuta ki ajiye zan rama shi a gaban kuma ɗan naki. Sannan ki kiyayi cewa zaki kai hannunki jikina. Dan walhy watarana sai na ɓallashi ɓas fiye da yanda stairscase yay masa a randa kika kunnenki ya jiyo miki abinda yafi karfin kanki tsohuwar banza. Ni ba Maanal bace da zata iya miki kara da kawaici wlhy hadda zan goge miki tas kin san dai ni ɗin rainon SHARRINKI CE. kin san ko masu iya magana kance makwaikwayi yafi ma'iyi iyawa idan ya ƙware. Sai ki kiyaye gudun abin kunya ki sani a bakin duniya ace na mari yayar uwata, kishiyar uwar mijina dan ke kam ai ba uwar bace ba. Su kansu ƴaƴan bake suke ɗauka uwa ba matsayin kishiyar babarsu suke kallonsu. Dattijuwar arziƙi ƴar girma data gaji halin girma kenan Oum. Mtsowww!!! Ƴar wahala kawai....
        Gaba ɗaya Mamy ma ta kasa fahimtar a sume take, ko an busar mata da jinin jiki ne ta yanda jikinta ya daina motsawa dan ta koma tamkar gunki a wannan gaɓar. Saheeba ta gama goge mata hadda tas da Nuratu.....
       (Nace hummm mutane na haka fa rayuwa take, shiyyasa duk tsanani kada ka sake ka raini zuciyar kowa da mugunta koda ɗan daka haifa ne. Idan ba haka ba bayan ya gama maka taka farautar wlhy kai zai dawo ya farauta. Kuma wadda zai maka sai tafi wadda kake sanya shi yanama mutane. Kuma babu yanda ka iya, dan ya sanka ciki da bai ɗin ka ta yanda garkuwar da zaka kare kanka ma sai ta maka wahalar nema balle samo takobin yaƙi da shi. Kun san shi ance sharri ɗan aike ne, duk inda ka aika shi, ko mai nisa da nisan shekaru sai ya dawo ya tabbatar maka yaje. Tsarkake zuciyarka ka zama mai barma UBANGIJI komai sai kasha mamaki. Koda harara karki cutar da kowa wlhy kina barci ALLAH zai tare miki faɗa da tarnaƙin kowacce irin guguwa. Kumuje zuwa muga yaya Mamy zata ƙare da nata karnukan farautar😂🤣)..........✍️
        
    
   




*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣4️⃣0️⃣


______________



........Tunda Hajiya Basariyya ta shigo falon taga baƙin da aka sakata zuwa gaisarwa tai wani kicin-kicin da fuska. Zama tai nesa da kowa, Daddy yay mata wani irin kallo ya ɗauke kansa. A maimakon gaishesu sai cema Daddyn tai gata. Idan kujerar dake falon ta motsa to Daddy ya amsata, yama watsar da ita tamkar bai ganta ba. Dan yanzu ya ƙudurtama ransa bazai sake ɗaukar iskancin kowacce ba ga ƴan uwansa. Dolene ya

168 / 213

Chapters