Author : Bilyn Abdull Category : Romance
ta ɗago sai dai babu alamar zata fito. Dan tana ma kallonsa tai saurin kauda idonta. Bakinsa ya ɗan taɓe tare da sake matsawa jikinta kaɗan, ta yanda ita kaɗai zata ji ya furta, “Goyo ki ke so ne?”.
Batama bari ya kai ƙarshen zancen nasa ba ta yunƙuro domin fita, dama ta dakata ne saboda mararta data ƙulle taɗan saki, (Bafa ƙaramin gyara Hajiya Shuwa tama Maanal ba, sakamakon sanin Maanal ɗin ba cikakkiyar budurwa bace. Komai baice ba ya taimaka mata ta karasa sakkowar sannan ya gyara mata alƙyabbar yanda yake buƙata. Dan neman magana abokansa sai video suke musu kuwa. Dai-dai nan Oum ta ƙaraso, fuskarta cike da murmushin farin ciki ta haɗasu ta rungume hawaye na cika mata ido. Kafin ta ɗago su batare da tayi magana ba ta shiga tsakkiyarsu hannayensu a cikin nata su duka. Itace ta shiga da su har cikin hall ɗin abokan ango biye da su. Shigowarsu cikin hall ɗin hasken camaras duka ƙaru a kansu, sai Maanal taji daɗin after dress ɗin daya saka matan, dan daba dan yayi hakan ba gaskiya akwai damuwa, zata ji matuƙar takurar shigowa wajen da rigar jikin nata, ita kanta Oum taji nutsuwar ganin Maanal ɗin a haka, dan dama yanayin da taga rigar tayi mata a jiki sanda zata shiga mota ya tsaya mata a rai.
Har inda aka tanada dominsu Oum ta kaisu, koda ta zaunar da su duk sai suka ƙi sakar mata hannaye. Musamman Maanal ma data riƙe da hannu biyu. Dariya ma suka bama Oum, da ƙyar ta danne ta saki murmushi kawai. Tare da ɗaura hannun AA a saman na Maanal ɗin ta rumtse sannan ta zame nata a hankali. Cike da tsokana da murmushi a fuskarta ta ce, “Banda faɗa, in ba haka ba asha bulalar Oum”.
Murmushi sosai AA ya saki mai ƙayatarwa, haka itama Maanal ɗin ƙasa ta sake yi da kanta sosai. Ita dai Oum dake ƴar dariya ta bar musu wajen. Hannunta dake cikin nashi ya ɗan matsa ta yanda dole ta ɗago fuska a yamutse ta dubesa dan taji zafi. Shima kallon nata yake, dan haka ya ɗan ɗage mata gira irin na (kallon fa?) harararsa tayi kaɗan ta sake ɓata fuska tare da ƙoƙarin janye hannun nata amma yaƙi bata dama, sai ma sake damƙesa da yay da ƙyau.
Duk abinda suke idanun mutane da yawa a kansu ne musamman ƴan ɗauka a waya, dan yanzu waya ta zamewa kowa jarabawa, ta bakin wani malami yace yanzu da wayarka kawai aka barka a yayin hisabi ka shiga uku, dan yanda muke ɗaukarta kawai abar muyi nishaɗi ko amfani mu ajiye abin ba haka bane ba, inma bamu sani ba mu sani, akwai hisabi tsakaninmu da abinda muka aikata da su waɗan nan dai wayoyin. Dan haka sai mu shirya, aikata alkairi ko sharri duk UBANGIJI na sane da motsin mu.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖6️⃣6️⃣
______________
......Nibras da dole ta sakata zuwa wajen dinner ɗin dan tangazo ƙeyarta Fawzan yayi sai taji kawai hawaye na cika mata idanu, ita kaɗai tasan irin baƙin kishin Maanal da take ji a zuciyarta, ga maganar Najma ɗin nan, duk da bata zafafa ba sosai abun fa na damunta ta ƙasan rai. A kwanaki biyun nan ji take kamar ta ɗauka wuƙa ta kashe kowa daga ita sai AA su rayu a wannan duniyar. Tayi kuka har bata san adadin hawayen data zubar ba ma. Ita da Fawzan kam sam babu zaman lafiya tace sai ya saketa, shi kuma yace aurensu auren zobe ne ai ba saki ba yaji, sai ma ya tattarata ya watsar ya maida hankalinsa ga hidimar bikin kawai, gefe kuma ga Najma na girmama farin cikinsa, dan ma tana noƙewa wai tana jin kunya. Ba Nibras ke cikin irin wannan halin ba kawai, dan halin da Saheeba ke a ciki zamu iya cewama yafi na Nibras ɗin, dan abu goma da goma ne ita ya haɗe mata, sosai take taya ƴar uwarta kishi, gefe ga hassada da baƙin kishin nan na facalanci dake da tasiri a duniyar malam bahaushe. Na farko dai bama su dake kwana suna tashi da AA a gida ɗaya ba mutanen dake waje ma sun san AA yafi sauran ƴan uwansa arziƙi na dukiya duk da suma suna da gwargwadon nasu, yana da connection da manyan mutane a duniya ma ba Nigeria kawai ba a dalilin business ɗin nashi musamman na agogo. A gidan kaf kowa sonshi yake soyayya irin wadda bata ɓoyuwa, dan a zahirance da baɗini AA ɗan gata ne a wajen iyayensa da ƴan uwansa, kusan shine ZUCIYAR zuri'ar Aliyu Darma. Bazaka fahimci hakan ba sai wani abu ya taɓa rayuwarsa ko mai ƙanƙantarsa zakaga illahirin hankalinsu ya koma kacokan garesa ne. Yan uwansa sun fisa hasken fata, amma shi kuma ya fisu ƙyau ta yanda ko baka san ƙyau ba sai ka iya banbancewa. Shiyyasa tun farko takema ƴar uwarta fatan samunsa. A wani gefen kuma tana taya Mamy faɗa ne da kishin Oum da faɗa akan su AA. Ga ita kanta shegiyar Maanal ɗin wata irin ƙauna Darma Family ɗin ke mata bama iya su zuri'ar Aba kawai ba dan son AA ɗin ya shafeta ga kowa. Koda yake sun san aikin asirine wannan, lokaci suka bata komai sai ya rushe ta zama mujiya a dangin dan ubanta. Bari dai a gama bikin za'asha kallo dan sabon wasa ne zai tashi a gidan Aliyu Darma kamar yanda suka shirya...
Mamy kam ji take kamar zuciyarta zata baro ƙirjinta ta fito ne kawai. Taso ƙin zuwa wajen dinner ɗin, Maman Saheeba ta tunzurata akan gara suzo ayi komai akan idonsu ai kamar jiya dan su san ta hanyar da zasu yaƙi Oum. Wannan dalilin ne ya sata zuwan duk da bata da lafiya ƙarfin haline kawai, yanzu haka kamar kanta zai fashe dan ciwo...
Yau ma dai ƴan discussion house cike suke da wannan waje cikin kwalliya ta ƙasaita da aji da halin girma. Can na hango muku su Aisha yuguda. Asiya salihu. Fauzarh collection. Hafsat adam651. Maman khairy2003. Lubabatu miss. Maryam Muhammad. Zuwaira muktar limanci. Shafa'atu limanci. Sadiya Ibrahim merariya. Maman meema. Deryer012
Mrs Suraj. Bilqeesu. Oum moh'd. Sa'adatu ibrahim mua'zu . ام الصديق. Ummu aslan&asala. Fateema Umar.. kai sunada yawa fa masha ALLAH, dan hada ZAFAFANKU ba'a barsu a baya ba...
Babban Yaya ne yay addu'a mai tsayi ga ma'auratan, Fawzan ya bada kaɗan daga tarihin ango da nasarorin daya samu a rayuwa. Ya kuma bada na amarya dan yace itama ƙanwarsu ce. Ya kuma ɗora da taƙaitaccen tarihin rayuwar ƙuruciya ga waɗan nan ma'aurata daya taɓa zukatan jama'ar wajen matuƙa musamman wanda basu san da hakan ba irinsu CFO, su Zaharadeen, su Yaƙub kai kaf ma ma'aikatan MAAWAD COMPANY jikinsu yay sanyi, CFO ta gama mutuwar zaune harda hawaye dan ta fahimci a lallai AA na Maanal ne. Yayinda ake nuna hotunansu a ƙaton magijin dake bango guda. Wani hoton dole mutane ke dariya, dan su kansu basu ma san an ɗaukesu ba a wasu wajajen, kuma ba kowa bane da wannan aikin sai Fawzan a wancan lokacin, dan yayi jarabar ɗauke-ɗauken hotuna da camara ɗinsa kasancewarsa mai son hakan shima, aka ce shi Salim ɗin Uncle Mahmud ya gado, shiyyasa wasu hotunan su kansu su AA ɗin basu san da zamansu ba sai yanzu. Maanal sai faman ɓoye fuska take dan AA sai tsokanar ta yake. Komai ya ƙayatar da mutane kamar yanda Fawzan yay fata, dan haka aka shiga tsakkiyar shagali cike da shauƙi. Komai ya tafi a nutse a kuma ilmance, babu wani rawar kai ko aikata abinda ya zarce Shari'a, hasalima ango da Amarya basu tashi daga wajen zamansu ba ko sau ɗaya balle yin rawa. Duk wanda zai musu liƙi anan wajen zamansu yake samunsu yayi. Aiko doller tayi kuka na gaske, dan abokan AA da manyan mutane sun nuna masa shi ɗin fa shine, yayinda matar shugaban ƙasa Raudha Ramadhan Taura ta danƙarama amarya ƙyauta ta musamman. Mawaƙa sun zuba capacity iya iyawa musamman Halifa sk ɗorayi daya maimaita mana waƙar bazani daina kuka ba, suma sauran mawaƙa irinsu Ado gwanja, Umar m Sharif, breaker, Sarkin waƙa, sun zubar mana galan-galan munsha rawa. Hotuna ba'a magana. Video kam tuni sun karaɗe media kamar ba gobe. Kafin kace mi wannan dinner ta zama on top a wannan dare. Al'amarin sai ya zama abin mamaki da tattaunawa musamman da ba kowa yasan da ɗaurin auren ba dinner ɗin ce kawai tayi girgizar bazata.
Abinka da manya na waje ba'a wani daɗe ba aka tashi, dan shaɗaya da rabi da yawan mutane ma sun kama hanyar gidajensu. Su Oum ne ƙarshen baro wajen, yanzu kam Fawzan ne ya ja motar da suke ciki, dan haka Najma ta kasance a kusa da shi dan Nibras tuni ta koma gida wai kanta ke ciwo, su Mamy ma ba'a tashi da su ba. Ita Hajiya Majdiya ma sai al'amarin yaso fara bata dariya. Dan zuwa yau ta sake yarda lallai akwai abinda ya kamata su sani game da Mamy. Shin wannan aurerrakin take ma ƙiyayyar, ko kuwa bayan shi akwai wani abu a ƙasa daya kamata ace sun sani?.
Najma ce ta taimaka ma Maanal suka shige, dan kan Maanal ɗin ciwo yake mata sosai jikinta kansa ya ɗauki zafi, dauriya kawai take yi koshi AA ɗin taƙi yarda ya fahimta. Dan tunda ta samu ya sakar mata hannu bata sake yarda sun haɗa jiki ba har aka tashi. Shima fahimtar a takure take ya sashi bata space ɗin da take buƙata, a gefe kuma akwai nauyi da kunyar su Oum dake a wajen. Ko yanzu Fawzan nata masa shaƙiyancin wai ko ƴar rungumar sai da safe baima Lillyn ba amma yaƙi kulashi. Dan shi bama wannan ba, gargaɗin da Mamy ke masa da idanu da mugun kallon da yaga sunama Oum ita da yayarta ne ya tsaya masa a zuciya. Dan tuni hankalinsa yabar kan dinner ɗin ma ya koma ga Oum kaco kan da da su Mamyn. Dan shi fa ya yarda komi Mamyn zatai tayi masa amma karta taɓa masa Oum ɗinsa, sam bashi da jarumta ko ƙarfin zuciya akan a cutar Oum ko Manaal, shi mai rauni ne akan soyayyarsu.....
★Gajiya sosai ta saka kowa neman makwanci domin hutawa. Alhamdullah Mannal tayi farin cikin ganin ƴan uwanta na tare da ita anan zasu kwana dan Oum ta hana kowa komawa gidan Shahidah, tace tunda amarya tazo gida anan ake biki anan zasu zauna har a kammala kodan a ɗebema Maanal ɗin kewa, ta kuma ji a ranta itama amaryace da aka kawo yau gidan miji ce kamar kowace amarya. Anan ɗakin da aka ajiyeta take tare da su Amaal dan suna so suyi magana da ita, duk da Nene ta shigo tace su maidata sama ɗakin mijinta itako ta sanya mata kuka da roƙon ita dai a barta anan dan ALLAH, dariya su Shahidah suka dinga mata, yayinda Nene ta saki baki tana kallonta.
“Amma fisabillahi Maanal kada yaron nan yaga rashin hankalinmu, tunda aka kawo ki ance kina sashen Hajiya Fateema Alhaji yay masa ƙarfa-karfa ya riƙeki kin zaune a sashenta, yau kuma ace an kawoki inda yake mu mun riƙeki bayan yayi kawaici iya kawaici”.
Baki sosai Maanal ta sake turawa gaba tana hawaye. Sai Shahidah da tausayin Maanal ɗin ya cikama zuciya ta ce, “Nene ayi haƙurin, shima ai yasan kamawa tayi tunda Oum ta maida bikin sabo fil. Ba yau bane kawai sai gobe. Shina kuma bana ma zaton yana a gidan nan dan ban gansa ba tunda muka dawo. Maybe ma bazai kwana a gidan ba tunda yasan da baƙi”.
“To ai shike nan tunda kun zama yayun banza kuma”. Nene ta faɗa tana miƙama Maanal abu a kofi, koda ta tsaya kallon kofin sai Nene tai mata daƙuwa, dole ta amsa ta shanye abinda ke cikin. Amsar kofin Nene tai ta fice ta barsu suka cigaba da hirarsu. Ita dai Maanal ma kwanciya tayi abinta dan itafa komai yimata yake kamar a mafarki musamman yanzu da aka maidota wannan sashen wai da sunan sashenta da zata rayu matsayin matar aure, auren ma na Ajwaad Bestyn ta...
Wajen ƙarfe ɗaya gidan ya ƙara zama shiru mafi yawa anyi barci dan an gaji. Hakan ya bama AA damar shigowa ya haye sama ya kwanta shima. Nene data gansa dan ta fito zata ɗauki abu data ajiye anan falo tai saurin komawa da baya. Sai da ya gama hayewa ta fito tai abinda zatai. Maimakon ta koma ɗakin da zata kwana sai ta nufi na Maanal, ganin har sun kwanta bai hanata ƙoƙarin tada Maanal ɗin ba ta hanyar kiran sunanta. Maimakon ita ta farka sai Amaal ce ta farka, barci cike da idonta ta ce, “Nene Lafiya dai ko?”.
“Lafiya Lau koma barcin ki. Maanal nake son ta tashi ta wuce ga mijinta can dai a gida zai kwana, ɗazu nayi magana kum kakkare cewar ba'a gida zai kwana ba tunda yasan nan zamu kwana. Ni na taɓa ganin irin wannan ƙarfa-karfa yaro a hanashi matarsa tsawon wata biyu kamar aure fulani”.
Amaal da abin yaso bata dariya ta danne da ƙyar tana tashi zaune. “Kai Nene wai kamar auren fulani. Nene a barta dan ALLAH, ba yau bane kawai dai, gobe iyanzu in sha ALLAHU mun bar musu gidan ai. Shima nasan bazai ce anyi ba daidai ba. Kuma bama tada lafiya sai da tasha magani ta kwanta taɓa jikinta kiji”.
Rasa abin cewa Nene tayi ita kam. Dan ta kula wannan yayun na Maanal sai a hankali, sam basa ganewa. A taƙaice ta ce, “Shike nan sai da dafe” ta juya ta fice. Cikin raɗa Aunty Sakina data farka itama ta ce, “Da alama dai Nene ta ƙagara ango ya angwance, irin wannan damuwa haka”. Dariya Amaal tayi kaɗan, tare da faɗin, “Bata san tana sake firgita ɗiyar tata bane, dan gaba ɗaya auta a tsorace take tun ɗazun wlhy.”
Murya a sanyaye Shahidah ta ce, “Nima tausayi take bani ALLAH. Ita da ba wani jikin azo a gani ba tana tafiya kamar zata ɓalle, sauƙin ma Ajwaad ɗin azumi ya ɗan sakashi raguwa, amma ya mata yawa ni dai nake ga mutum a murɗe haba jama'a”. Ta ƙare maganar a sanyaye kamar zatai kuka. Dariya sosai Aunty Sakina keyi, ta ce, “Yayun ƙarshen zamani kenan, dama namiji nama mace yawa ne? Kuna nan zata baku kunya nan da wata tara mu dawo suna. Balle ma Maanal mace ce, koda take da rashin ƙiba ai tana da jikin cikakkun mata. Ga gaba ga baya ko'ina Alhamdullah. Amma fin wata biyu an hana bawan ALLAH matarsa kai jama'a a tausaya masa mana ga uban gyara tasha”.
Dariyar shaƙiyanci suka sanya, duk da da gaske har cikin ƙasan rai tausayin Autar tasu suke ji. Duk abinda suke faɗa Maanal na jinsu, dan itama tun shigowar Nene ta farka. Gaba ɗaya sai taji tsoron na ƙara tasiri a ranta. Dan da gaske gaba ɗaya a firgicen take, yau har addu'a tayi ALLAH yasa jininta yazo, amma bawan ALLAHn nan shiru kake ji. Sai kawai taji hawaye na ciko mata idanu, musamman data tuna abinda ya dinga faruwa a tsakaninsu a watanni biyun nan, musamman a Chaina daya kusa samunta har karo biyu ALLAH dai ya ƙwaceta da ƙyar. Gashi idonta ya rufe da soyayya har tana wani ɗaukar masa alƙawuran randa aka kawota zatai miye-miye ko ubanwa ya aiketa..........✍️
🤣🤣😂😆Kya dai gayama ƴan Giro Manaaluwa😛
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖6️⃣7️⃣
______________
........WASHE GARI kamar waɗanda ke akan ƙaya Nene ta azalzalesu suka fara shirin gyara gidan. Duk abubuwan dake a kwalaye aka ciresu, tun daga bedrooms na sama banda ɗakin AA saboda girmamawa, sunce in ma akwai abinda yake buƙata idan sun tafi ita da shi sa sanya a ciki. Amma bedrooms biyu nata da wanda ke matsayin na yara duk an gyara su, an shirya mata kayanta a closet, falon sama ɗin ma komai an saka har labuloli, aka goge ko ina aka saka ƙamshi. Ƙasa ma sun sake gyarawa, akama canja zaman kujerun gaba ɗaya sannan suka shiga kitchen, kayan da bazata buƙata a kusa ba aka danƙare su a store, sannan aka sake shara tsaf anan ma aka baza ƙamshi. Koda aka kawo musu break fast ma sun gama gyaran ko'ina. Suna gama ci aka shigo da kayan lefen Maanal da AA ya haɗa mata, mamaki ya kama kowa, ganin anfa kai lefe a wancan karon, amma sai Hajiya Majdiya ta tabbatar musu ango yace wannan nasa ne. Haukacewa ƴaƴan su Hajiya Yaya suka sake yi dan mamaki da ruɗani. Musamman da aka fara buɗe akwatina ana fiddo fitinannun kaya naban mamaki designers na manyan matan masu kuɗi ƴan gata. Ya subahannallah kowa