AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   176 / 213

525K to 528K   out of 636.6K words

iya cewa komai sai gabansa ke faɗuwa ma waya kawai ya ɗauka yay kiran wani mutuminsa dake airport. Kai tsaye ya buƙaci jirgi zuwa Abuja yanzun nan. Koda wancan yay masa bayanin sai yamma jirgin zai tashi zuwa Abuja, sai yace suna buƙata gaba ɗaya kawai. Yana ajiye wayar suka fito iya su mazan. Dan Umma kawai Baba Sardauna yayma bayani ya kuma ce su cigaba da sabgar sallarsu dan baya son kowa ya fahimta dan kar hankalin sauran yaran da matan ya tashi.
      Yaran maza ma bada kowa aka tafi ba, an kuma gargaɗesu. Daga Baba Sardauna ɗin, sai Baba, sai Abbu, Uncle Mahmud da Uncle Hassan, Hussain, sai Uncle Najeeb, Yaya Sulaiman, sai shi RK. Duk da su duk sun girmeshi amma tunda shi yasan tushen matsalar dole aje da shi.......

__________★

        Tsaki Daddy yayi ya zaro wayarsa da aka damesa da kira. Yana gama fiddowa tana katsewa, har zai maida wani kiran ya sake shigowa. Number ya tsaya kallo, sai kuma ya ɗaga tare da kaiwa kan kunne yay sallama. Sai dai me kafin ya gama rufe baki kukan Huznah ya dakar masa dodon kunne. Ga mararta a dai-dai lokacin tai wani irin matsanancin ƙullewa. Maganar ma ta kasa fita da ƙyau, ga Hajiya Basariyya na buga ƙofa da ƙarfi kamar zata ɓallata. Huznah ta durƙushe a ƙasa murya a yayyanke ta ce, “Daddy ka zo ka taimake ni zan mutu, Huznah ce, Ummi wani gida ta kawo ni suka min allurar zubar da cik.....” ta kasa ƙarasawa saboda yanda juwa ta kwasheta ta ƙarasa zubarwa a ƙasa. Wayar ta faɗi ta tarwatse a ƙasa komai yay nashi waje...
       Gaba ɗaya Daddy sai yay cak yama kasa motsawa, sai wani irin zufa dake faman tsatstsafo masa tako ina na jikinsa. Yanda kasan ana kwarara masa tafasasshen ruwa a tsayen da yake haka yake jin kalaman Huznah na dawo masa a cikin kunne ɗaya bayan ɗaya. Dai-dai nan su Ammie suka fito da Nazeefa daga sashenta, sai kuma ga Sabuwa na shigowa tare da likitoci har biyu dan Nazeefa ta kirata kafin jikin yay tsanani, ita kuma bata gida sunje wani ƙauyene ita da ƙawarta akan zaman Nazeefa ɗin dake neman sauya salo a gidan.
       A fusace Sabuwa ta dirgo a mota, aiko ta tuzguɗe ƙafa har sai da ƙashin yay ƙara. Itama ƙarar tayi tana mai dafe mota da sauri har sai da likitocin suka riƙeta aka kamata aka zaunar a ƙasa. Amma ina hankalinta nakan su Ammie da Yazeed da Aunty Sakeena da suka kinkimo Nazeefa. Cikin matuƙar masifa da ɗaga murya ta ce, “Ku ajiye min yarinyata anan matsiyata munafukai. Idan ba hakaba na rantse da ALLAH na tashi sai na baku mamaki”.
        Hummm a gayama Yazeed zuciya, dama a ƙufule yake da Nazeefar ma balle su. Kawai yana pretending ɗin dole ne saboda mahaifinsa. Ai cikin rufewar ido kawai ya saki Nazeefar a ƙasa ji kake timmm. Wata irin wahalliyar ƙara ta saki kuwa. Ko kallonta baiyi ba ya juya yana zubama Sabuwa mummunan kallo. A fusace yace, “Ƴarki ɗin banza ƴarki ɗin wofi Sabuwa. Ammie ku ajiye mata ita dan ALLAH ta kwasheta su bar mana gida. Idan ba haka ba ni yau zan bata nawa mamakin shegiyar mata ƴar iska”.
     Yanda Yazeed ke magana babu wanda bai firgita ba, ƙannensa kuwa da Hajiya Yaya har rige-rigen fitowa suke yi daga sashenta. Wani irin galala Sabuwa tai tana kallon Yazeed ɗin, sai kuma ta harziƙo cikin matuƙar zafin rai ta ce, “Lallai Yazeed ni kake zagi da kira ƴar iska, to bari kaji ni uwarka ma tamin kaɗan balle kai, gata nan ka tambayeta wlhy nafi ƙarfinta.....”
      Bata gama rufe baki ba ya kama hannun da take nuna Hajiya Yaya da shi a bazata sai ji kowa yayi hannu ya bada ɓasss. Na ƙarar karaya. Wata irin gigitacciyar ƙara Sabuwa ta fasa. Yazeed ya ce, “Ke kin isa ki nuna min mahaifiya ban karya hannunba dan ubansa. Zaki kuma an zageki kiyi abinda zakiyi, koba ƴar iskar bace ba ke ɗin. Na baki minti goma ki kwashi ƴarki kubar gidan nan ke da wannan tarkacen idan ba haka ba kuma zan baki mamakin”.
      Yana ƙoƙarin barin wajen Daddy ya dakatar da shi ta hanyar riƙe hannunsa. Baice masa komai ba ya jashi suka fita a gidan gaba ɗaya, batare da Daddy yace ko uhum ba akan ihun Sabuwa balle abinda Yazeed ɗin yay mata ko halin da Nazeerar ke ciki.
    Murmushi Hajiya Yaya keyi, hakama yaranta babu wanda bai dara ba. Sai Ammie ce ke ƙoƙarin yima likitocin da Sabuwa ta kawo magana akan su taimaki Nazeefa. Gaba ɗaya numfashinta kamar ya ma bar gangar jikinta, Hajiya Yaya zata hana Ammie ta shiga roƙonta, dole tai shiru dan yanzu ganin girman Ammie take sosai, likitocin nan suka kama Nazeefa da taimakon Ammie da Sakeena aka sake maidata sashenta, dan sun tabbatar idan ba hakan ba kafin aje asibiti zata iya rasa ranta.....

_______★
     
       A ɓangaren su Abah Mamy na ficewa hankalin su Oum na kan Abah ita da su AA Mabera yay kiran waya. Kafin su farga kawai sukaga ƙarti na shigowa falon cikin baƙaƙen kaya fuskokinsu a rufe da mask. Ga bindigu a hannunsu sun zagaye su. AA sarkin zuciya tuni yayi wani masifaffen yunƙuri akan Mabera, sai dai yana kawo hannu zai shaƙi wuyansa shi kuma ya caka masa allura a damtsen hannunsa. Azabar zafi bata saka AA ya saki wuyan nasa daya damƙo ba, sai dai ya runtse idanunsa da ƙarfi, da wannan damar Mabera ya tatse ruwan allurar a cikin jikin AA ɗin yana wata irin dariyar ƙeta. Cike da mugunta ya fincike ƙarfen allurar ya jefar dai-dai gaba ɗaya jikin AA na saki lagaf. Aiko sai ya turashi yay baya-baya sai da Yaya Fawzan ya tare AA. Mabera dake dariya ya ce, “Ai dama na fahimci kai ne hatsabibin gidan shiyyasa na shirya maganinka.” ya kalla yaransa yay musu signal da ido.
        A bazata Yaya Fawzan yay wani kalar bama Mabera naushi gefen fuska. Gaba ɗaya ya tafi zai kifa abinka da jikin girma, jini ya ambulo ta bakinsa sai ga haƙoransa uku a ƙasa tare da jinin. A take yaran Mabera suka zagaye Yaya Fawzan da Babban Yaya dake shirin kai dukan shima. Dan idanunsa sunyi wani masifar kaɗewa na tashin hankali kamar yanda na Abah da Fawzan ɗin sukayi. Oum kam ai tayi sumar tsaye, ashe al'amarin babbane har haka.
      Yanda sukai musu zobe kunamin bindigu duk a ɗane ya saka Abah yima su Yaya Fawzan magana. Ga AA yana kallon komai amma bashi da ƙarfin koda miƙewa. Sai dai idanun nan sun koma tamkar garwashin wuta, jijiyiyin kansa sun mimmiƙe. Dai-dai nan wata tawagar ƴan iskan ta shigo da su Maanal da aka tattaro a compound ita da Ameerah, Najma, sai su Inte masu aiki da su Bola da mai gadi. Zuwa can sai ga Nuratu riƙe da Saheeba dake tafiya da ƙyar hannunta duka biyu riƙe da cikinta tana kuka. Ameerah ta saka mata ido kamar yanda kowa ke kallon Saheebar. Naufal ya miƙe zai je gareta cikin yaran Mabera wani ya hankaɗa yaron baya yana daka masa gigitacciyar tsawa..
      Wayoyinsu aka karɓe su duka aka kashe, sannan suka mamayi Babban Yaya da Yaya Fawzan ta baya suka musu irin allurar da sukama AA, dan Mabera ya tabbatar da waɗan nan fusatattun yaran da jinin Aliyu Darma ke yawo a jikinsu ba bindigu ba ko bomb ne zasu iya masa tarar aradu da ka. Wani irin mummunan kallo Abah ke yima Mabera, shiko ya kwashe da wata ƴar iskar dariya, yana zaune a kujera da kumburarriyar fuska dan ba ƙaramin dakuwa yay da naushin Yaya Fawzan ba. Dariyar kanta ta ƙarfin halice kawai ga inda hakwaran suka fita babu ƙyawun gani.  Su Abah duk suna ƙasa ne shi yana a kujera like boss.
        Duk wannan abun da ake hankalin Maanal nakan AA, ta yunƙura yafi sau huɗu zuwa gareshi suna ɗaura mata bindigu a saman kai,  sai AA ɗin kuma ya girgiza mata kai kawai alamar ta zauna. Cikin ƙunar zuciya takai hannu ta share hawayen da suka zubo mata. Dai-dai nan wani cikin wanda suke tsakar gida ya shigo shima da bindiga a hannu. Cikin girmamawa ya risina yana sanarma Mabera, “Sir ga wasu mata su biyu wai Nana da Hajiya Turai. Mun koresu amma sunƙi tafiya”.
        Dariyar ƙeta Mabera yayi, da faɗin, “Shigo da su suna da amfani suma”.
     “Okay Sir”.
  Yaron nasa ya faɗa yana komawa da baya. Bai fi mintuna shida da fita ba sai gashi ya dawo shi da wani sun taso ƙeyar Nana da Hajiya Turai da gaba ɗaya suke a rikice a kiɗime. Suna shigowa falon Hajiya Turai tai arba da Mabera sai ta tsaya turus tana kallon sa. Muryarta na rawa ta ce, “Ju...j...Junaid!”.
      Wani banzan kallo Mabera yay mata ya watsar. Zata ƙara magana wanda ke bayanta ya dakamata tsawa tare da ɗora mata bindiga a wuya. Jiki na rawa ta maida hannayenta a sama ta zauna a ƙasa kamar kowa. Dama tuni Nana ita takai ƙasan harda ɗan fitsarinta a zani idonta akan Saheeba dake kwance a ƙasa ta riƙe ciki azaba ta isheta sai zufa take yi kamar an jiƙata da ruwa........✍️




*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣5️⃣3️⃣


______________


........Ruwa mai yawa Sille ya juye kan Mamy, ta kawo wani kakkauran numfashi kuwa, tana buɗe ido taci karo da fuskarsa ta maida ta rufe. Baki ya taɓe tare da shurin ta ya ce, “Dalla malama buɗe idanu. Kona haɗa surukuta dake balle kice kina jin kunyata? Ko kuwa lokacin da kikaje kika ajiyeni a bola ido rufe kikayi. Yanda kika yaddani idonki a ƙeƙashe, zuciyarki a bushe haka zanyi duk abinda naga dama a gabanki nima zuciyata a ƙeƙashe azzaluma muguwa kawai. Mintuna biyar na baki ki tashi ki tattaro min duk wani kayan kuɗi dake sashen nan, idan ba haka ba ALLAH sai nabi gaɓɓan jikinki ɗaya bayan ɗaya na fasa da bullet mai zubin ƴan wuta kawai”.
      Jikin Mamy na rawa ta tashi zaune jin yana jan kunamar bindiga. Dai-dai nan Haule ta fito daga bayinta alamar wanka tayo. Mamy ta kauda kai ziciyarta na mata zafi, wai itace yau mai aikinta tai wanka a cikin bayinta ba wanke mata ba, wankan ma ba wankan soso da sabulu ba, sannan wani ƙaton banza yay zina da ita a kan gadonta. Wannan wane irin yanayi ne mai azabartar da zuciya....
       “Oh bazaki tashin ba kenan?”.
   Sille ya faɗa yana kai bindigar saitin kanta. Da sauri ta daddafa bango ta miƙe, haka ya tasata gaba daga shi sai gajeren wando har cikin closet ɗinta. Da farko abubuwa marasa daraja sosai ta ɗan fara tsakuro masa, aiko ya falle fuskarta da mari mai zafi da gigitarwa, ga hannunsa ƙaton gaske. Tsabar azaba sai da ganinta ya gushe na wuci gadi, babu shiri ta sakama loka ɗinta na sirri security ta buɗe masa. Gwala-gwalai ne na garari a ciki, dan duk fitar da Abah keyi da ita ƙasashen duniya sai tayo ma kanta tsarabar gold's, dan tana samun alkairi sosai a tafiyar. Itako Oum ko madadin abinda ya kashema Mamyn ya bata akan su AA kuɗin ke ƙarewa. Babu abinda ya dame ta da wani sayen gold ta ajiye matsayin kadara, mafi yawan lokuta ma tafi son fashion fiye da gold ɗin a kwalliya. Bayan gold's akwai tarin documents ɗinta na filaye da gidaje da taita saya a Kano batare da sanin ko Abah ba, sai na hannayen jari a companys daban-daban. Haka ya sakata ta tattara masa su a cikin akwati yana faɗin, “Uhm lallai an tara mana da yawa. Zubasu dan wlhy bazan raba da waɗancan ba tunda babansu yafi babana kuɗi. Munafuka ko guda ɗaya baki saka sunana a kai matsayin next of king naki ba saboda kin zata kinyi nasarar kasheni ko? To nine zan kasheki ƴar iska mai haihuwar yara a titi tana jefarwa a bola. Azzaluma mara imani da tsoron ALLAH. Oya yimin kneeling anan”.
      Jikin Mamy na rawa haka tai kneeling, yace ta daga hannu sama. Duk yanda yace haka take yi kamar television da remote. Haule da abin duniya ya dama da tsannanin mamakin dama Mamy ce ta haifeshi ta kume a waje ɗaya ya kira, jiki na rawa itama tazo inda yake, zam yay cike da sheɗanci ya ɗora Haule akan jikinsa ya kunna sigari yana busama Mamy hayaƙin. A gigice Mamy tai shirin rufe ido jikinta na rawa dan hayaƙin har tsakiyar ƙwalwar kanta.
Tsawa ya daka mata. “Wlhy kika rufe ido sai na aikaki lahira shegiya. Sanda kikai naki iskancin wa kikaji kunya? Ko sanda zaki binne ni a bola kin tuna ALLAH na kallonki, ai tun a duniya zaki fara amsar gashi a hannuna kafin kije kici ubanki a wajen mala'iku.”
      Tabbas yau Mamy taga masifa irin wadda bata taɓa kawoma rayuwarta zata gani ba. Tayi dana sanin sanin Junaid a rayuwarta balle haɗa jini da shi, duk da har yanzu bata yarda wannan shaiɗanin a suffar mutane wai ɗan data haifa bane, taya ma hakan zata kasance? Tun tana kuka harta koma ajiyar zuciya da jan numfashi sama-sama, jininta kam da kansa ma yake hawa yake sauka. Ita kanta Haulen kuka take yi, dan duk iskancin Sille data sani bata taɓa tunanin ya shahara irin haka ba. Ai ko ba mahaifiyarsa bace shekarun Mamy sun kai a rangwanta mata, kai ko ita ɗin karuwa ce bai kamata yazo yana mata waɗan abubuwan ba. Yau kam taji tai matuƙar tsanarsa, tsana mafi munin tsana, tsoro kawai ya hanata yin kowane irin yinƙuri. Duk rashin jinta tana girmama iyayenta, a kullum fatanta ALLAH ya daidaita ta da nata suyi aure da Sille, amma a yau ta tabbatar bazata iya aurensa ba.....

_________★

         Da taimakon gps app su Daddy suka gano inda su Hajiya Basariyya suke, gashi sunata kiran layin da Huznah tai kiran Daddy ɗin amma yaƙi shiga. Sai dai motar Hajiya Basariyya data sake tabbatar musu da suna a cikin gidan da gaske. Yazeed ya ce, “Daddy kodai kiran Ummi ɗin zamuyi ne kawai”.
     Ɗan jimm Daddy yayi, sai kuma yace, “Okay bari muga to idan zata ɗaga.” yay maganar yana danna kiran Hajiya Basariyya. Sai da ta kusa katsewa ta ɗaga. Kamar ba ita ba faran-faran ta shiga faɗin “Daddyn Huznah badai harka ga ƙosawar daɗewarmu ba ko. Wlhy munzo hirar zuminci tai daɗi na samu wasu ƴan uwa anan shiyyasa”.
     Kai kawai Daddy ya girgiza, cikin dakewa yace, “Gani nima a ƙofar gidan naku fito kimin iso”.
    Hankali tashe da in ina Hajiya Basariyya ta ce, “ Ƙofar gidanmu fa, kana nufin gidan Yaya?”.
           “Kuna da wani gida ne bayan nan?”.
     “A'a .. a'a daman na shiga maƙwafta ne, ina zuwa gani nan zuwa barka naje, oh haihuwa akai sorry....”
      Duk ta rikice ta diririce. Ko uffan Daddy baice mata ba ya yanke kiran. Yazeed dake sauraren komai ya ce, “Amma Daddy miyasa kace mata haka?”.
       “Saboda bamu da damar shiga nan ɗin, amma hakan da nai mata zata tsorata tace bari ta fito ta koma can ta hakan zamu sami damar ceton yarinyar.”
     Daddy bai gama rufe baki ba kuwa sai ga Hajiya Basariyya a rikice, ita da likitar sun kamo Huznah data fara fita a hayyacinta da ciwon ciki. Sai da suka zo gab da motar Hajiya Basariyya sannan ta farga da motar kusa da su, motar ta tsurama ido, sai kuma takai dubanta ga number, gabanta yay bala'in faɗi. Kafin ta iya cewa wani abu Daddy da Yazeed suka fito. Ai bama tasan ta saki Huznah ba. Ta tafi ƙasa zata zube Yazeed ya zabura ya riƙeta. Riƙe Yazeed ɗin tai da ƙyau jikinta na rawa ga azaba tasa kukan ma ta kasa. Ta ce, “Yaya ka kaini asibiti, sun yimin allurar zubar da ciki, yaya zan rasa babyna, yaya zan mutu cikina ciwo yake min.”
        Cak Yazeed ya ɗauketa yana faɗin, “In sha ALLAHU bazaki rasa ba Huznah. Kuma zaki rayu ki haifoshi duniya” haka ya sakata a bayan mota ko kallon Hajiya Basariyya baiyi ba. Shi ko Daddy Hajiya Basariyyar yake kallo kawai, sai dai baice mata uffan ba. Itako ta nutsu waje guda idanunta rissine a ƙasa zufa gaba ɗaya ta jiketa ta firgita, dan ba ƙaramin tashin hankali take jin kanta a ciki ba musamman da idanunta suka gane mata tsagwaron bala'in dake a cikin idanun Daddy. Haka Yazeed ya tashi mota suka wuce suka barta a wajen da Doctor data gama rikicewa. Dan ita kanta a yanda taga fuskar Daddy da Yazeed tasan ta shiga uku. Sauri-sauri ta koma cikin gida, kayanta ta shiga haɗawa dan wlhy gara tabar garin, dama yaranta biyu duk suna boarding school ne. Mijinta kuwa yana wajen aiki a Niger state. Daga ita sai mai aikinta. Gudu-gudu ta sallami mai aikin ta fito, har lokacin Hajiya Basariyya na tsaye, ko kallon inda take batayi ba ta shiga motarta ta buɗe Hajiya Basariyya da ƙura ta wuce abinta....

         Gudu bana wasa ba Yazeed yayi zuwa asibiti, tun kan su isa Daddy ya kira family doctor ɗinsu. Aiko babu ɓata lokaci suna shigowa aka ɗauki Huznah da

176 / 213

Chapters