Author : Bilyn Abdull Category : Romance
da mummunan kallo. Ya fahimci itama kuma Ameerah ta lura dan yaga sanda ta shafe cikinta da addu'a har sai da abin ya saka shi murmushi ma.
Wannan abun ya saka shi ji a ransa dole ya sakama Saheeba ido akan cikinsa, dan bai san mi take rayawa ba, shiko wlhy akan cikin nan na jikin Ameerah zai iya faɗa da kowa, ciki harda ita kanta Ameerah ɗin ma balle wata Saheeba can. Ta rufama kanta asiri kawai, idan ma bata son ɗansa ko ƴarsa ta kauda kai kawai sai su zauna lafiya. Amma yin yinƙurin cutarwa nan ne zai nuna mata asalin kalarsa kuwa.
Haka da yaje yima Ameerah sallamar kwanciya da ya dawo sai da Saheeba ta canja fuska harda yin magana a kaikaice. Ya jita sarai amma ya watsar da ita dan shi irin wannan shirmen ba'a yinsa da shi. Kaɗan daga aikinsa ya watsakkata ɗakinta wlhy. Itama fahimtar hakan da sanin halinsa yasa ta kama kanta, dan magana ta ALLAH a buƙace take da shi ga magani tasha harda na tsiya. Sai kawai ta basar da komai ta miƙa wuya....
__________★
E lallai da gaske Hajiya Shuwa ta shirya tsaff, dan kuwa gyara na jijjiga zukatan makiya taima Maanal a wannan daren, dama ga ƙyawun da jego ya sakata gana canjin iskar inda suke. Hatta gashinta da lalle duk a daren aka gyara akayi su, harda kukanta kuwa a gyara kai dan duniya Maanal ta tsani taɓa kai. A hakan ma sai da Didi Shahidah tai mata masifa sannan. Ƙunshi kam tana barci ana zana mata ƴar gata. Hussein shine mai rigima sosai, koda ya farka madara suka bashi yasha ya koma barci, hakan ya basu damar yin komai yanda ya kamata. Kitso dai sun san ba yarda zatai ba shiyasa babu wanda yay gigin cewa ai mata.
Washe gari aka sakama yara suna *_Muhammad da Ahmad_*. Sunayen da Babban Yaya ne ya zaɓa musu. Yara sun sha addu'oi yanda ya kamata, tare da albarka da fatan alkairi. Kasancewar Maanal ta koma barci bisa umarnin Hajiya Shuwa bayan sallar asuba bata farka ba sai goma. Dai-dai lokacin da gift ɗin Daddy dana Yaya Yazeed ke isowa gidan Darma. Babu wanda bai jinjina al'amarin ba dan kuwa dai sun taka rawar gani kwarai da gaske. Su Gwaggo kuwa ai neman zarewa sukai. Ga hassada ga mamaki. Sai kawai Sailu ta saka kuka. Ashe bataga komai ba, dan kuwa yanzu ne aka fara wasan. Su kansu su Shahidah sunji daɗin abinda su Daddyn sukayi, duk da suka a duk haihuwarsu yana musu tagomashin arziƙi.
AA kam sai ma ya rasa abin faɗa, sai dai kuma gift ɗin Yazeed fa ya sosa masa rai alamar jin kishi. Sai da Babban Yaya ya kwaɓesa da nuna masa Yazeed fa a yanzu matsayin yayan su Maanal yake, sannan koba komai ya taka rawa a rayuwarsu, ya kamata ya cire ma kansa kishinsa. Tabbas AA ya fahimta, ya kuma gane yaso yin ajizanci ne irin na ɗan adam. Dan haka ya sauke ajiyar zuciya ya kuma tsarkake ransa akan ƙyautar.
An gama murnar nasu Daddy da sanya albarka kayan barkar uwar miji Hajiya Fateema Abubakar Darma (Oum. Mrs Aliyu Darma) suma suka iso sashen Maanal. Kayan Barka ne a matsayin uwa, a kuma matsayin uwar miji. Yo ƴan Giro rikicewa sukayi, kai basu kawai ba hatta su Shahidah mutuwar zaune sukayi. Kai anya kuwa alhalin Darma sun san ciwon kuɗi kuwa? Wannan al'amari kamar bada wahala aka tara su ba........✍️202
.........Wannan kayan Barka na uwar miji sun rikita kowa, sun kuma shiga media yanda ya kamata. Maanal ma dai sai da tai hawaye, tana sake jinjina al'amarin wannan baiwa a zuciyarta. Tabbas har abada masu hallaya irin ta Oum bazasu taɓa su taɓe ba duniya da lahira in sha ALLAHU.
Tsabar son ida tarwatsa zuciyar Mamy haka Saheeba ta ɗauka komai a waya duk da itama fa baƙin cikin taf ranta taje tana nunama Mamy. Koda Mamy taso ƙin kalla sai Uwangale ta zabga mata harara. Ai da sauri ta amshi wayar tana kallo hawaye na cika mata ido. Sai kuma ga Aunty ta shigo tana jin jina al'amarin da sake labartama Mamy komai batare data damu da yanayinta ba....
______★
Anan kuwa su AA gagarimin walimar taron suna da aka shirya na iya su maza ne suke shirin tafiya. An gayyaci mutane daga sassa daban-daban da ko wani bikin albarka a tara mutane hakan. Shugaban ƙasa kanshi zai halarci wajen. Tunda garin ALLAH ya waye Maanal bataga AA ba, amma Didi Amal ta sanar mata ya shigo tana barci. Kuma an kai masa coffee da yace a haɗa masa. Breakfast kuma yace zaiyi da su Babban Yaya an shirya musu a waje. Dan haka basu bashi ba.
Sai wajen 11 yay kiran wayar Shahidah yace a shirya yara dan dasu za'aje wajen walimar. A lokacin ne yake tambayar Maanal ta tashi?. Wayar kawai ta sakama Maanal ɗin a kunne. Daga can zai sake magana yaji Maanal ɗin tai sallama. Sai yay shiru kawai yana sauke ajiyar zuciya. Cikin sanyin murya tace, “Ina kwana Besty”.
Shima ƙasa-ƙasa yace, “Shalele kin tashi?”.
Murmushi tayi mai sautin da har yaji, tare da faɗin, “Yau kuma sabon suna na samo Abiee!”.
Har cikin rai yaji sunan Abiee ɗin ya ratsa shi, ya ƙara maida muryarsa a maƙoshi sosai. “Besty kin wuce Shalele ai, kawai na rasa mizan ce ne na tsaya a iya nan. Shine kin tashi koki kirani ma naji muryarki”.
“Kayi haƙuri, ina tashi alkairan Daddy da Oum ya ɗauke hankalina matuƙa, amma kana raina. Yanzu kuma mai kwalliya ce tazo za'a shirya ni”.
“Ni kuma wazai shirya ni?”.
“Ai ka zama Abiee da kanka zakayi”.
“Ban yarda ba, kema ai kin zama Oum amma za'ayi miki. Please kizo ki shirya ni kona ƙi zuwa walimar”.
“Besty rigima fa babu ƙyau”.
Ta faɗa tana ƴar dariya ciki-ciki data nema sake kwance masa lissafi. Ai babu arziƙi yace, “Okay shi ke nan bari na shirya gasu Yaya na kirana, zan shigo na ganku kafin na wuce”. Kafin ma tace komai ya yanke kiran. Tai murmushi dan sarai ta gane a halin da yake ciki, tasan halin mijinta zuwa yanzu, tana gane dukkan yanayin da zai iya shiga. Ita har tsoro ma take ji ta gama jegon nan balle gashi cs ne ma, yanda tai juriya da ciki ya sakata tasan a yanzu ba lallai ta iya da fitinarsa ba. Amma ALLAH ya bata ikon kwatantawa dai.
Kamar yanda ya faɗa bayan ya gama shiryawa sai gashi ya shigo musu, lokacin za'a fara zana mata tata kwalliyar. Dole mai kwalliya ta fita ta basu waje dan wlhy tsoron AA take yi. Idan ya haɗe fuskar nan babu alamun rahama ga kwarjini da cika waje dole kaji shakka da tsoronsa ma kai tsaye. Dan irin mutanen nan ne marasa ɗaukar raini. Randa taga yana wasa da Maanal abin ya jima yana bata mamaki, wato soyayya daban ce, in ba ita ba mizai karya lagon AA har yayma wata murmushi da dariya ma da tsokana, ai sai dai soyayyar.
Tana kuwa fita ya sakar ma Maanal dake kallonsa galala murmushi mai sanyi. Sai kuma ya shiga takowa a hankali har zuwa inda take zaune a kujerar mai kwalliya. Tun daga haɗaɗɗun takalman ƙafarsa masu shegen ƙyau da ɗaukar idanun mai kallo ta fara bi da kallo har zuwa bugaggen tattausan yadin jikinsa zuwa designer agogon sa ƙirar Maawad Company, sosai ɗinkin ya zauna masa a jiki ya fidda ainahin buɗaɗɗen jikinsa na ingarman namiji, sai rigar saman kayan da zai ɗora tana a hannunsa ninke, ba babbar riga bace ba, an yi ta ne like ƴar shara sai dai rigar ciki dake jikinsa dogon hannu ce, hular ma bai saka ba tana hannunsa tare da ƴar saman rigar. Luuu ta sauke idannunta akan ƙyaƙyawar fuskar sa da gashin kumatunsa ke kwance luf-luf alamar samun gyara har zuwa lips ɗinsa sannan ta sauke su cikin tsakkiyar idanunsa dake kallonta a sangarce. A hankali ta sake lumshe nata idanun ta buɗe cikin nasan dai, tabbas ko maƙiyi ya kalli mijin nata yasan yayi ƙyau, ainahin madarar ƙyau kuwa. Karon farko ta miƙe kawai ta rungumeshi. A tare suka sauke ajiyar zuciya, cike da shagwaɓa da kulawa tace, “Mijina daban ne a cikin mazaje. Sai dai ina kishin kwalliyar nan daba ni kaɗai zanta gani ba”.
Murmushi yayi sosai yana sake ƙanƙameta. Cike da sanyin murya ya ce, “Umarni kawai zaki bayar a canja shigar sai a canja Besty”.
“Bazance a canja ba saboda yau ranar farin cikin mu ce. Ranar da bayan ta aurenmu itace ta biyu a tarihin da bazamu taɓa mantawa ba. Yau Besty na ya zama cikakken uba har na ƴan biyu”.
“Nima Besty na ta zama cikakkiyar uwa harta ƴan biyu”.
Dariya sukayi a tare, ta amshi rigar ta saka masa harda hular, sannan ta saka masa turare duk da ya saka daga ɗaki. Wajen yaran yaje da aka gama shiryawa sunyi ƙyau sosai kamar ka lashesu, haka ya durƙusa ya musu kiss ya bata tai musu hotuna shi da su, itama ta shiga sukayi sannan ya kwashi yaran suka fice tana binsu da kallo fuskata da murmushi. Shima ya jaddada mata tayi ƙyau kafin ya dawo fa...
Ba ƙaramin abin kallo AA ya zama ba, daga wajen ƴan Giro harma da ahalin darma. Daga mazan har matan. Kai harda ƴammatan Gidan Chalawa sun gama yarda Maanal ta kwashe komai. Nibras da gaba ɗaya ta kasa zama a sashenta saboda shi ji tai zuciyarta tai mata nauyi, a kaikaice ta dinga masa hoto batare daya sani ba. Ba ita kaɗai ba Nuratu ma na raɓe a gefe tana kuka sosai, kuka irin na kayi min nisa na har abada. Anyi hotuna a tsakaninsu su maza kafin su Abah su fito da tawagar su Baba Sardauna, Dan daga walima su Baba zasu wuce Kano ne.
Abinda zai baka mamaki ya tabbatar maka sun ƙullaci Mamy a rai babu wanda ya shiga dubata. Kai hatta matan da sukai kwanaki a gidan babu wanda yako kalli sashen Mamy. Aunty kuma faran-faran suke mata babu wani abu da suka nuna mata sam. Dama shi Abah sai ka rantse yama manta da Mamy na raye. Ko kallo sashenta bai isheshi ba. Oum kaɗai taje ta duba ta yau da safe, dan jiya data shiga har tayi barci. Itama Oum ɗin bata jima ba saboda mutane, gaisuwar kawai sukai ta fice. Ai ko sai da Mamy tai kuka, musamman ganin yanda Oum ɗin tayi wani shegen ƙyau da sake komawa ƴar 40y can. Uwangale ta dinga zabga mata kirarin daya nema ƙarasa kassara zuciyar Mamy. Kaida kaga Oum kasan tana cikin farin ciki da kwanciyar hankali ƙwarai da gaske. Tana fita Uwangale ta dingama Mamy dariyar mugunta wai ta ruɓe ga Oum na lokacin ta.
Ba ƙaramin ƙyau dattijan sukai ba, suka sake amsar yaran suka sanya musu albarka, dan tun safe da suka iso aka kai musu su sashen Abah, sunfi awa biyu kafin a maida su, sai kuma yanzu da za'a wuce da su walimar. Uncle Lamiɗo da Yaya Fawzan ne suka ɗauke su. Lokacin da suke isowa hall ɗin da za'ai walimar ya gama cika da manyan mutane jiga-jigan ƙasar. Abokan kasuwanci da abokan karatu. Na Abah, na babban Yaya, na AA, na Yaya Fawzan. Sai ƴan uwa daga Darma Family, su Babu ƴan Giro duk da basu da yawa, sai tawagar Daddy shima dan gayya yayo sosai. ALLAH sarki Babu sai da yaji kuka yazo masa. Ya wulaƙanta ƴayanshi, gashi UBANGIJI ya ɗaga darajarsu ta inda basuyi zato da tsammani ba. Yanzu duk yawan wannan taron domin haihuwar jikokinsa ne kawai.
AA yaje ya gaishesu cikin girmamawa da risinawa. Dan duk da haushin Babu daya jima yana ji bai taɓa tunanin wulaƙantashi ba. Kai shi fa duk abinda ya shafi Maanal komai muninsa baya iya wulaƙantashi. Sai dai idan ka taɓa masa ita kaima fa zai taɓa ka. Su Sule anyi gayu a kayan da su Shahidah suka ɗinka mishi. Har ya ɗan fara kilin, shiyyasa ya sama ransa wlhy bazai koma Giro ba yazo gida kenan. Hannunsa AA ya kama babu wani damuwa, Sule sai washe baki ake ɗan gayu ya kama shi. Haka ya dinga zagaya manyan mutane suna gaisawa hannunsa riƙe da na Sule. Kafin su zauna a inda aka tanada masa. Sai kuma Sule yaji duk bazai iya zama tsakkiyar su AA ɗin ba. Cike da wayo ya zame ya koma kusa da su Babu. Sosai Babu yaji daɗin abinda AA ɗin yay akan Sule. Dan yana fatan ma yaransa shiriya kamar sauran ƴan uwansu, ba su suka aikata laifin ba sune suka aikata yana fatan iya wanda suka girba daga lalacewarsu ta baya ya zama iyakar kenan.
Anci an sha cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Manyan malamai suka lectures masu kaɗa zuciya akan haƙƙin ƴaƴa da tarbiyyarsu dake kan iyaye. Sai Babu yaji kamar da shi ake. Ba shi kaɗai ba kusan a wajen kowa sai da ya tsargu. Musamman manyan da bama su da lokacin damuwa da abinda yaransu suke aikatawa a cikin al'umma marasa ƙyau ko saɓanin haka saboda kuɗi da mulki. Wani ma sai yay watanni baiga ɗan nashi ba ko ƴatsa. Daga baya akai hotuna sosai, a nutse aka zagaya da yara wajen iyayen ƙasa suka saka musu albarka yanda ya kamata. Anyi rabon manyan agoguna ƙirƙirar Mawaad kuma masu nauyin gaske ba na talakawa ba irin mu. Dan hatta su Sule ba'a tsallake su ba duk da basu san darakarsu ba. Aiko sai daɗi suke ji. Ƙarfe ɗaya dai-dai aka tashi, za'aje ai salla azhar daga can kuma kowa sai ya kama gabansa.........✍️
😀Ba sai mun buɗe sunan nan komai da komai ba. Dan mu samu damar dunƙuke komai daya rage a ɗan sauran pages ɗin mu in sha ALLAHU. Wajen su Maanal ma ataƙaice zaizo saura kuce ba haka ba dan wlhy na gaji😭🏃🏼♀️
203
.........A nan gida ma an gama zanama Maanal kwalliya ta dukan zukatan maƙiya. Didi ta bata wani ubansun lass da aka saya da kuɗi masu nauyi sky blue da kwalliyar peach a jiki. Skirt ne da helf bubu, ya bala'in jin stones. Ɗauri akai mata daya zauna fem, sannan akabi kunnenta zuwa hannuwa da wuya da muguwar sarƙar gold ɗin kayan da Oum ta kawo. Da masu karatu zasuji nauyin kuɗin sarƙar nan sai sunce (Bilyn Abdull ta fara zuba mana ƙwayayen ƙarya🥱. To kawai mubar komai a rufe ni kaɗai na sani🤣🏃🏼♀️). Ba mai kwalliya ba hatta ƴan uwanta tsayawa kawai yau sukai suna kallon ƴar ƙanwar tasu. Ita kanta Maanal data kalli kanta a mirror sai da hawaye suka cika mata idanu. Rayuwa kenan, kai dai an haifeka amma baka san wanene kai a shekarun girma da hankali ba. ALLAH dai yasa mu dace. Amma musani an haifeki a ƙauye ko gidan talauci ba shike nuna ALLAH bazai ɗaukaka ba watarana, ko al'umma su dinga ji a ransu baka isa ka kai haka ba. Waye kai da, miye-miye hassada a bayyane mtsowww!!. Takalman ta masu ƙaracin tudu da suka zauna da shigar tata aka bata ga saka, sai dan siririn gyalenta a gefen kafaɗa. Wlhy ko maƙiyi yaga Maanal a yau sai ya haɗiyi yawu balle mu masoyanta. Hajiya Shuwa tazo ta sake tirareta da ƙamshi na musamman. Daga haka suka sakko ƙasa aka sake gyara saman dan ba'a so kowa ya hau musu can sirrinsu ne, shiyasa ma su Amal suka gyara mata bedroom ɗaya a ƙasa da zata zauna har taro ya tashi.
Da su Zeezah da Aneesa ta fara karo, wanda isowarsu kenan daga Kaduna. Wani kalar ihun farin cikin ganin Juna suka saki. Rabonta da su ko'a waya tun kafin su bar ƙasar. Sai kuma ga ƴan Giro an kwasosu daga masaukinsu, dan wasu ne anan da aka bari kawai su uku suka kwana. Ana haka tawagar yaran gidan su Ammie suma suka iso. Abu kamar wasa sai ga zuri'ar Nene itama, sai kuma ga ƴan uwan Hajiya Yaya. Lallai su twin's sunyi gishi. Kowa ya kalli Maanal sai ya ambaci masha ALLAH. Hajiya Yaya da Nene da Hajiya Shuwa da Hajiya Majdiya ne tsaye akan komai ta nan ɓangaren ta. Sai su Ameerah, Najma, Amaal, Shahidah dasu Aneesa suka fuskanci shirya wajen da za'ayi walima dan anan cikin gidan ne. Tacan ɓangaren Oum ma ahalin Darma sunata nasu ƙoƙarin. Gaba ɗaya sai ya zam babu mai kallon sashen Mamy balle tunawa da ita, haka su Saheeba sun zama kamar an waresu ma. Balle Nibras da ita zuciyarta ma ta gama dagargajewa. Jitake kamar ma tabar gidan idan an gama sunan sai ta dawo. Duk wanda yazo yay cigiyar yara ace suna tare da babansu a wajen walima. Sai ƙarfe ɗaya da kusan rabi ana shirin fara walimar mata mazan ke shigowa. Mamakin ganin gidan sukai taff, dan kamar wasa bikin suna dai yayi mugun yin armashi.
Lokacin da idon AA ke sauka akan Maanal sai ya tsaya cak, ya subahannallah matarsa duniyar ƙyau ce da cikar kamala da ƙyawun haiba. Bai sani ba ko tsananin ƙaunar da yakema yarinyar nan ce yasa yake ganinta da tazara mai yawa tsakaninta da sauran mata? Shifa magana ta ALLAH idan har Maanal na waje kallon sauran matan wajen yake kamar mata maza (😲🤕 AA ka fita idonmu🙄).
Ba AA kawai ke kallon Maanal ba, itama kallonsa take yi cike da shauƙi da ƙauna mai girma. Sai da Yaya Fawzan ya zunguresa cike da neman magana ya ce, “Kai malam kula kada ka yadda min yaro ƙasa fa”.
Dariya mutane suka sanya. A hankali Maanal ta kauda kanta tana murmushi itama.
A wani irin slowly AA ya lumshe idanunsa masu hasken madarar nan tamkar an zuba oil a ciki.