Author : Bilyn Abdull Category : Romance
tana da ciki, sai dai a ƙurarren lokaci nasan hakan nima. A ranar da mukaje da abokina wajenta yin sulhu, da yake yana karatun lafiya muna baro wajen ya tambayen nasan kuwa Kamila nada ciki?. Nace masa ciki kamar ya? Yace min ciki dai na haihuwar ɗa, dan shi kallo ɗaya yay mata ya fahimci hakan a gare ta. Da farko na shiga tashin hankali, dan tabbas nasan cikin nan nawa ne, saboda nasan bata mu'amula da kowa sai ni. Ni ɗin ma sau uku ne kacal, sai dai ta zama sanadin da ina neman wasu matan kuma a yanzu. Ganin yanda na rikice sai ya shiga kwantar min da hankali, shine ya bani shawarar yanda muka ɗiba jininta batare data fahimci dalilin hakan ba. Koda muka kai akai gwajin aka tabbatar mana da cikin rikicewa na sake yi, nace ma abokin nawa wlhy dole na biya ko nawa ne a zubar da shi. Amma sai ya ƙwaɓeni, yace Junaid kada ka aikata hakan, dan cikin nan ya wuce batun zubarwa cikin sauƙi, da aje yarinyar nan ta rasa ranta ka saka kanka a matsala gara ka barta da cikin, kawai dai dole mu sanyama duk motsinta ido dan bamu san manufarta na ɓoyeshi ba har a gareka. Da farko dai badan na gamsu da shawararsa ba na ƙyale, sai dai nima dana nutsu nayi nazari sai na ajiye batun zubda ciki, muka sakama duk wani motsinta ido batare da itama ta sani ba. A yanayin da muka ganta da rana a randa zata haihu abokina ya tabbatar min da naƙuda take a tsaitsaye, kuma tabbas zata iya haihuwa daga ranar zuwa kowane lokaci, dama kuma gwajin da yay mata yasa a lissafe muke da watannin cikin. Har taje asibiti ta kaima su kakarta abincin dare ta dawo a biye nake da ita, ganin ta shiga gida ga hadari sai na haƙura na yanke shawarar tafiya gida tunda babu wani labari, amma zuciyata taƙi yarda min da hakan, haka na cigaba da zama a ɓoye cikin layinsu har ruwan nan ya sakko, na gama sarewa akan na tafi kawai sai gata ta fito daga gida tana tafiya da ƙyar tana kuma waige-waige, ko tsoron duhun dare dana ruwan sama da akeyi bataji da alama, sosai taurin zuciyarta ya sake bani mamaki, dan tabbas da ace namiji ce yarinyar nan ba ƙaramar tantiri za'ayi ba. Haka na dinga bin bayanta harta shiga cikin kangon nan, harga ALLAH a lokacin da take naƙudar ni tausayi ma ta bani, sai na dinga jin kamar na fito ma na taimaketa. Amma dai zuciyata na ƙwaɓata, ga ƙaunar yaron data bari yashe a ƙasa ruwa na dukansa ta shigeni, jikina har rawa yake akan naje na ɗaukesa. Na dai daure da ƙyar harta gama hutunta ta tashi ta naɗe yaron a zani ta saka mabiya a leda ta fita a kangon. Cikin sauri nabi bayanta, duk tunanina gida zata koma sai naga ta ɗauki wata hanyar daban babu tsoron komai a tare da ita. Mamaki ya kamani, amma ina dai biye da itan harta isa ga bolar data ajiye yaron ta zuba masa bola tabar wajen. Karo na farko da naji tsanarta mafi muni a zuciyata, tsana irin wadda ban taɓa ma wani mahaluki ba a rayuwata, ina hawaye da komai naje na ɗaga yaron daga bolar har lokacin bai kuka ba, amma kuma alamu sun nuna yana da rai, dan zuciyarsa na bugawa. Haka na rungumeshi nabar wajen da shi har mabiyyar data yarda dan bazan iya barinta a wajen ba, na koma kangon data haihu na kwashe duk wani abinda ta bari da zai iya zama shaida. Haka na ɗauki hanyar gidan su abokina a ƙafa ga yaron a ƙirjina na naɗesa a cikin leda ta baya, da ƙyar na samu acaɓa ya ƙarasa da ni. Hankalin abokina ya tashi sosai, yayi kuma mamaki da jinjina taurin zuciyar Kamila, haka ya shiga bama yaron taimakon gaggawa da ƙyar muka samu yay kuka. Ni da kaina nai masa wanka muka saka shi cikin babbar rigar abokina muka naɗeshi ya samu ɗumi, asubar fari muka fita zuwa kaishi wani asibitin kuɗi da abokina ya sani kuma yake da alaƙa da su. Anan akai treating yaron na tsawon kwanaki goma, har sai da lafiya ta dawo jikinsa sosai sannan aka salleme mu, ranar ban kwana garin Kano ba na biya kuɗin jirgi na wuce Lagos. Saboda shi na kama ɗaki a anguwar da ba'a sanni ba cikin ƙabilu kuma dan babu bahaushe ko ɗaya ta wajen. Haka na cigaba da rainonsa ni kaɗai, har lokacin daya kamata na sayi kaya na koma gida yayi, sai na rasa yanda zan yi dan bana son mahaifina yaga na saɓa lokacin dana saba komawa, hakan ne ya zama dalilin fara neman mai raino, kasancewar nafi son bahaushiya yasa na sha wahala sosai, sai da ƙyar na samu wata anan anguwar da muke sai dai mai aiki ce a wani gida nan kusa damu, gidan da ban taɓa sanin hausawa bane a ciki sai ranar, duk da dai matar ce bahaushiya, mijin kuma ƙabila ne. Da wannan damar na dinga zuwa kai kaya Kano sai dai bana daɗewa kamar da nake dawowa Lagos, dana dawo rainon yarona ke dawowa hannuna, nine uwa nine ubansa, har ALLAH ya sa yakai shekara biyu da haihuwa. Yayi wayo sosai, kamanina da nashi na ƙara fitowa. Ƙaunarsa na sake tasiri a raina, ina jin kamar bani da kowa a duniya sai shi kaɗai. Shine farin cikina, bani da wani buri sai na naga ya girma. Ban taɓa bama kowa labarin uwarsa ba, idan ma aka tambayeni sai nace ta rasu wajen haihuwarsa. Hatta da mai rainonsa da uwar ɗakinta haka na gaya musu kawai. Ya fara tafiya ina tsaka da wannan farin cikin na taho Kano kawo kaya, na sauka airport na shiga taxi zai kaini gida yaran data saka su kasheni suka taremu a hanya. Bayan sun min abinda ta sakasu harda jefani a ruwa, amma kamar yanda na faɗa mata zan dawo gashi na dawo ɗin. Dan kuwa suna barin wajen cikin yaran data saka suka jefanin ɗaya ya dawo ya fiddani, duk da dai nasha ruwa sosai zuwa lokacin haka ya ɗaukeni ya kaini nesa da anguwar tasu, a wani kango ya bani taimako, kwana uku da yini guda yana tare dani har na dawo hayyacina. Alkairi nai masa mai tsoka. Sai ya bani shawarar nayi nesa da garin Kano, dan tabbas Ɗan-taure hatsabibi ne baya juyama wanda ya bashi aiki baya, sannan yanda ya fahimta Kamila hatsabibiyar yarinya ce komai zaki iya sake aikatawa idan ta tabbatar ban mutu ba. Na gamsu da bayaninsa dan haka na buƙaci yazo muje Legos, dan inada wajen zama acan. Baiyi musu ba muka tafi. Sai dai muna isa ciwo ya kwantar da ni sosai, shine yay jiyyata tsahon watanni bakwai, yarona dana sakama Junaid matar nan da uwar ɗakinta da basu taɓa haihuwa ba ita da mijinta ba na kula min da shi, har ALLAH yasa na warke sarai na dawo normal, dawowar data sakani turo yaron nan yay min bincike akan Kamila da gidanmu. Sai ya samu ALLAH yayima mahaifina rasuwa, sannan ni kuma anyi nema na har an gaji an haƙura da tunanin na rasu, ɓatan nawa ne ma ya saka mahaifinmu a damuwa ya kwanta ciwo har ya rasu, har ma yayuna sunzo sun tattare dukiyar Abbanmu da nake juyawa anan Lagos ɗin sunje sun raba gado iya su kaɗai banda ni. Hasalima zuwa lokacin basa ƙasar, ita kuma mahaifiyarmu wai ta auri ƙanin mahaifinmu sun bar nan Kano suna Bauchi da yake can ne asali mu. Kamila kuwa ta auri Aliyu Darma, har ma tana da ciki a lokacin...........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣6️⃣5️⃣
______________
........Wannan abu yamin ciwo ƙwarai da gaske, dan labarine mafi muni da bazan taɓa mantawa da shi a rayuwata ba. Gaba ɗaya naji na tsani ahalina, dan tabbas basu min adalci ba, musamman ma mahaifiyarmu naji ciwon auren ƙanin babbanmu da tayi, dan baya shiri da babanmu sam sanda yake raye. Amma ta aure shi bayan rasuwarsa ko shekara ba'a rufaba, a lissafi ma tana gama takaba akai auren. Wannan al'amarin shine sanadin canja min tunani, naga babu wani amfanin cigaba da zama na mutumin kirki, na fara rainon zuciyar Junaid da ɗaukar fansa akan mahaifiyarsa, ni kuma na huɗe shafin iskanci ba kama hannun yaro. Na kuma fara shaye-shaye saboda ɓacin rai. Mai rainon Junaid ce taita ƙoƙarin dawo dani kan hanya, tare da nuna min ita zata aureni kodan junaid, amma sai naji bazan iya ba, kamar itama tazo min ne da irin fuskar Kamila. Sai na fara hantararta, amma sai batai fushi ba ta cigaba da bibiyata harna amince da ƙyar da takurawar Junaid a lokacin yana da shekara kusan biyar. An ɗaura mana aure da ita, sai nace mata bana son sake haihuwa. Iya Junaid ya isheni rayuwa. Ta amince da hakan kuma tana bama Junaid dukkan kulawar data dace, idan ma ba'a faɗa maka ba sai ka ɗauka itace ta haifeshi. Kwatsam Junaid nada shekara tara sai gata da ciki, aiko na shiga yi mata rashin mutunci, amma sai Junaid ya nuna bata kariya da son cikin, dole na bari nima na koma bata kulawa tunda dai mai afkuwa ta riga ta afku, sannan akan Junaid komai zan iya amsa na kumayi haƙuri da shi. Tasha wahala a rainon cikin har ALLAH yasa yakai ga haihuwa, ta haifi ɗa namiji, sai dai ko ganin fuskarsa batayi ba ALLAH yayi mata rasuwa. Munci kuka ni da Junaid sosai, sai uwar ɗakinta ce ke lallashinmu da mijinta daya kasance ba wani mazauni sosai ba. Haka shima wannan jaririn na shiga rainonsa tare da Junaid, bana zuwa ko ina kullum ina gida, a hankali yaro da muka sakama suna Ra'iz na girma zuciyata na ƙara mutuwa daga barin neman na kaina, sai dai na daina shaye-shaye dana fara, sai danfarar mutane kuɗi. A hankali hakan ya fara min daɗi, sai ya zama itace sana'ata mafi shahara. A haka Ra'iz da kusan Junaid ne ke rainonsa shima ya fara girma, sai uwar ɗakin mahaifiyarsa da itama take taka rawar gani a kammu dan mafi yawancin lokaci suna a gidanta ne koda yaushe idan suka taso makaranta, kawai sai tsautsayi ya gitta min a tsakanin, na damfari wani mutumi aka kamani, bayan shari'a ta kwana ɗaya kacal aka turani prison. Wannan shine dalilin yin nesa da yarana guda biyu, kulawarsu ta koma hannun uwar ɗakin matata, ba kowa bace kuma face wannan shegiyar matar Hajiya Turai.....”
Babu wanda bai kalli Hajiya Turai ba, ita ko ta duƙar da kai kamar ta ALLAH. Cikin jin zafi sosai Mabera ya cigaba da faɗin, “Tunda aka sakayani a prison karatunsu Junaid ya tsaya, matar nan ta dinga shagwaɓasu sai abinda suke so take musu. Junaid ya fara bin abokan banza, gashi dama na karantar da shi wacece ainahin mahaifiyarsa wannan al'amarin ya zauna daram a zuciyarsa. Tun bai gama balaga ba ta dinga bashi magani ya fara amfani da ita saboda ita tsinanniya ce azzaluma ta biyu. Har takai idan mijinta baya nan Junaid ya zame mata kamar shine mijinta. Taso fara lallata Ra'iz ɗin shima amma Junaid ɗin ya taka mata burki, da yake ya fara zama gawurtaccen mara ji sai ta fara tsoransa... A lokacin ne na fito a prison, gatan da naga Turai na bama su Junaid ya sakani cikin farin ciki da jin daɗi mara misali batare dana san ainahin alaƙarta da Junaid ɗin ba, ban zauna ba ganin yarana na samun kulawa duk da tarbiyyarsu ta canja na baro Lagos dan na fito prison ne da dabarun yaƙi kala-kala, nazo kano cikin shigar ɓurtu, nai binciken komai daya shafi Kamila a yanzu, ban zauna ba dan yanzu kam arziƙi na fito nema kodan ƴayana na kuma maida murtani ga ahalina, dan hatta su sai da na bibiyi al'amarin kowannensu nasan halin da yake ciki da abinda yake yi yanzu. Mahaifiyata ta rabu da ƙanin babbanmu bayan ya cinye duk abinda ta gada, tana aure a kaduna yanzu. Wannan shine dalilina na zuwa Kaduna na jinginu da Alhaji Bello dake aminin mijin data aura,(Baban su Hajiya Yaya). Sai da na fara karantar halayensa tsaff sannan naje gareshi da siffar neman taimako, yako taimakeni ɗin ya haɗani da babban yaronsa Alhaji Usman Chalawa. Da farko naso kwantar da kai a jikin Chalawa, amma lissafin ya canja ganin ya sanya min ido yana faman kaffa-kaffa da dukiyarsa, kawai sai na fara masa ɓarna, amma yakai ƙarata ga Alhaji Bello ya tsawatar min, sai na bari na zama mutumin kirki adalilin ƙyalla idanuna akan ƴarsa a ranar, yarinyar bata da kunya, da ganinta kuma idonta a buɗe yake, na koma ta bayan gida domin nemanta ta nuna min ita ba ƴar iska bace, sai na wayance nace mata nima da aure nazo ai. A mamakina sai ta amsheni hannu biyu, ba kuma tai jiran komai ba taje ta sanarma mahaifinta, shiko babu wani ja'in ja ko jin ra'ayina ya bani aurenta, wannan shine dalilin aurena da Sabuwa, a kuma nan ne naga mahaifiyata, itama ta ganni sai dai naƙi saurarenta, na kuma tabbatar mata idan ta nuna tana da alaƙa dani sai na tona asirinta ga mijin aurenta nace itace ta kashe babana ita da ƴan uwana da ƙaninsa nima suka kasheni dan naƙi basu haɗin kai. Wannan barazanar da nai mata ce ta sakata shiga hankalinta, akasha biki aka bani wajen zama nace kano zan zauna. Haka Alhaji ya kama mana haya muka koma Kano, ba wani zama nake sosai ba, dan inata kai-kawon harhaɗe kuɗaɗen mutane, sannan ina shiga cikin ƴan siyasa. Ina kuma zuwa Lagos akai akai duba yarana dake hannun Hajiya Turai da mijinta. Ban gayama kowa a cikinsu na ƙara aure ba har na saki Sabuwa, a lokacin kuma ta haihu yarinya mace. Sai dai ashe da wani cikin ma a tare da ita. Kawai a wata waiwayowa da nayi Kaduna saboda mutuwar mahaifiyarmu na samu Sabuwa ta ƙara haifa min yarinya mace harma an yaye ta, wannan shine dalilin maida aurenmu da ita dan na fahimci zata min amfani a tafiyata, a kuma lokacin ne naje Lagos na samu Turai zataje Kano da su Junaid. Naso hanawa, sai dai rokon da yaran sukaita min yasa na barsu. Ashe zuwan zai yi amfani, dan kuwa a wannan zuwa da tayi Kano dasu na gano akwai alaƙa tsakanin Turai da Kamila, ƙanwar Kamila Nana na auren ƙanin Turai uwa ɗaya uba ɗaya harda haihuwa a tsakaninsu, hasalima ƴar yarinyar da Turai ke riƙo ɗiyar Nana ce, nayi farin ciki sosai, dan haka na samu Turai na ƙara bincike sosai akan Kamila naji harma abinda ban sani ba game da zamanta a gidan Aliyu, burinta na son ƙwace ƴaƴanta a hannun Fateema data bata na har abada. Burin son kai Fateema a ƙasa ta mallaki Aliyu ita kaɗai sai ƴayanta. Dan ana ma shirin yima yaran nata aure babu jimawa da wasu yaran maƙwaftansu. Amma ita Kamila bata so hanyar da zata dakatar da hakan take nema, ta fison babban ɗanta ya auri babbar ƴar Nana. Ta ce a lokacin ma suna ta ƙulla abubuwane amma ita Nana ɗin ce ke gaya mata komai, dan bata da wata alaƙa da Kamila sai ta gaisuwa da zumincin dake tsakaninta da Nana. Naje inata nazarin yanda zan ɓulloma wannan al'amari sai ga Turai ta kirani a waya tana sanar min Nana fa ta sameta da batun shirinsu. Har sun bata damar samo musu wai wanda zaima wata yarinya fyaɗe a ƙannen yaran da za'a aurama ƴaƴan Kamila. Dariya abin ya bani sosai, na kuma tabbatar da Kamila tayi nisa bata jin kira, ba kuma zata taɓa sauyawa ba kwarai da gaske. Amma zan mata kamun kifi a wannan gaɓar, wato na jefa mata ƙaramin kifi dake jikin fatsa, idan ta kama domin ci sai ni kuma na kamata. Kai tsaye nacema Turai mu zamu amshi aikin, kuma Ra'iz shine zaiyi, dan haka ta kaishi gidan a matsayin ɗan ƙanin mijinta, su kuma tace musu bata da alaƙa da shi. Da yake yaran nawa duk sun juye da suffar ƙabila hausar ma tasu a gurɓace take tana kai Ra'iz suka aminta, har ma aka zube masa kuɗin aikinsa dama ƙari a sama. Ke dan ubanki Turai koba haka akai ba?”.
Jikin Hajiya Turai na rawa kanta a ƙasa ta ce, “Hakane, duk abinda ka faɗa gaskiya ne. Kuma wlhy ni babu ruwana, sai da suka gama ƙulla shirinsu su biyu Nana da Kamilar sannan na sani. Kai kuma da nazo na gaya maka ka tsara yanda za'ayi, na kai Ra'iz wajensu matsayin ɗan ƙanin mijina, koda aka haɗashi da Ajwaad sai Ajwaad ɗin bai kulashi ba, shine akace ya zauna wajen Fauzan. Shima da farko Fawzan ɗin yaƙi sai da Kamilar tai masa faɗa sannan. An shirya komai zai faru a ranar ɗaurin aure, su Kamilar suka aiko da zoɓo da aka dafa a gidan makwafciyarsu da sunan ta kawo gudummawa ma Fateema, sai dai anyi hakanne kawai saboda ita yarinyar da za'ama fyaɗen wai tana son zoɓo, abinda aka zuba a zoɓon da sunanta kawai akayi dan haka ita kaɗai aikin zaici. Danni lokacin ma ganin abun naitayi kamar bazai yiwu ba, amma sai Nana tace min na jira na gani, ai wanda yay aikin ya iya aiki sosai. Ko ba haka akai ba Kamila! Nana gaku dai da ran ALLAH ba ƙarya na muku ba.....”
Nana ta share hawaye