Author : Bilyn Abdull Category : Romance
kika samu. Duk da wannan ƙyaƙyƙyawar rayuwar data rayu a cikin kusan shekaru ashirin da tara yanzu ta ƙare a auren ƙauye, ƙazamin mutum irin Alhaji Balala. Haba jama'a miyasa zatai irin wannan mummunan ƙarshe haka mara fasali da daɗin ji koda a labari?. Rashin mai bata amsa yasa ta sake rushewa da kuka. Su dai ƴan rakkiyar amarya har abin nata ya fara gundurarsu. Haka suka iso ƙauyen su Alhaji Balala da bai da nisa da nasu. Duk da dare ne sai ga mata da yara na fitowa kallon mota. Alhaji Balala kam nata washe baki ransa fes amarya ƴar gayu an kuma kawota a mota an ƙara mutuntashi. Sai rawar uwawu yake kai kace shine zai shiga da ita gidan. Haka yay musu jagora har ɗakinta yana haska musu hanya da dalleliyar tochlight ɗinsa da taji sabon zubin battery. Matan nashi ma dai duk suna tsakar gida ransu a ɓace, sai ƴan uwansa mata da matan ƴan uwansa maza cike da gidan sun saka mp wai ana bikin tarewar amarya. Sai kuma surukansa duk su sun kasa sakin jiki da ƙyau saboda iyayen mazansu kar suce suna murnar an musu kishiya. Anyi faten tsaki tun da yamma shi suketa kwasa. Haka aka kai Hajiya Basariyya ɗakinta, aka kawo ma ƴan kawota tuwo miyar taushe na tarba sai kaji har uku akai dan su kaɗai ma akaima tuwon aka ɓoye.
Ganin dare yayi basu zauna ba sukace zasu wuce da tuwon gida kawai. Haka aka kwasa aka kai musu mota sukai sallama suka tafi. Sabon kuka Hajiya Basariyya ta saki musamman data gama bin ɗakin da kallo, gadai kayanta ne na gidan Daddy amma ko ɗakin maigadinsu yafi wannan ɗakin ƙyau da tsaruwa. Wannan abu ya sake tayar mata da hankali. Da girmanta da shekarun ta anfi ƙarfinta an mata auren dole. Tun tana jin hayaniyar gidan har ya koma tsitt. Abinka da ƙauye goma zuwa sha ɗaya ko'ina kake ji yayi shiru. Tana nan zaune abin duniya ya isheta abubuwa da yawa take saƙawa ranta iri daban-daban Alhaji Balala yay sallama ya shigo. Wani irin bugun hancinta da turarensa yayi mara daɗin shaƙa sai da hanjin cikinta suka wantsala. Ga wani irin ƙarni-ƙarni komi ma zata kira abun oho na fitowa daga ledar hannunsa wai kazar amarya. Haushi, takaici, baƙin ciki kamar zata mutu. Kasa masa magana tayi har yanzo kusa da ita ya zauna shirim bayan ya danna ma ƙofa sakata. Da sauri tai ƙoƙarin matsawa, ya damƙota ya riƙe yana faɗin, “Haba amaryata Basari. Yada gudun miji kuma. Ni kin ganni nan wlhy banda haƙuri”.
Ya ALLAHU. Bakin Alhaji Balala ai duniya ne a wajen wuri, anya mutumin nan ya taɓa brush ko asuwaki a rayuwarsa. Kawai sai Hajiya Basariyya taji tana neman sumewa. Shi ko ango Alhaji Balala ko'a kwalar rigarsa, da yake ma bashi da man kai yana fassara yanayin nata ne da kunya. Bawan ALLAHn nan ya bari ko ƴar kazar aci ayi hirar baƙinta ina kawai ya mamuƙeta jiki na ɓari shi kawai angwanci zai yi. A wannan gaɓar roƙon ALLAH Hajiya Basariyya keyi da magiyar ya ɗauki ranta ta huta. Duk da tana da jiki itama amma ko rabin Alhaji Balala batai ba. Dan kuwa dai yafi ƙarfinta, haka kuma yayi amfani da ƙarfin ya turmushe uwar mutane, ƙanwar mutane kuma ƴar Kawu Manu. Nauyin da ƙirjin Hajiya Basariyya yayi yasa yanzu ma ta kasa yin kuka, har yay bidirinsa ya gama ya sauka a gadon bakinsa har kunne. Sai kuma yaja gyalenta ya ɗaure ƙugu yana tulewa a ƙasa yaja ledar namansa ya hau ci yana faɗin, “Kai kai kai Basari ALLAH yay miki albarka. Ai irinku ku ake kira da hurulanin duniya. Kinga taso kici naman nan karya huce amarya taso na samu na kammala abinda ya dace kafin alfijir waɗan nan jarabbbun matan da ƴaƴansu su hanani rawar gaban hantsi. Ai banyi ƙyan kai ba gaskiya, da nasan haka ne dana ajiye ki a ɓangarenki daban na saka ƙyaure yanda dan uban mutum dole su barni na shaƙata. Amma bari kiga gari na wayewa yanda kika san kajin bashi haka zasu ishemu da kaya-kaya gida da sai kace ana bikin suna mtsowww. Yoni ace tun farkon aurena irinki na samu banga abinda zai sa na ƙara aure ba. Wannan al'amari haka cakwai malam. Ai babu abin faɗa ga wannan miji naki sai ALLAH ya shi mishi albarka...” duk fa wannan surutu yana yi ne yana danna nama a baki. Kafin ya kai ƙarshen labaran nasa na rashin kangado yakai ƙarshen kajin biyu tas sai kasusuwa. Sai kuma ya hau salati da faɗin, “Oh ni Balala, kinga dai Basari na cinye miki kajin sayen bakin yo dama yunwa nake ji, matan nan najin haushi na yau babu wadda ta bani tuwo. Kinga taso ki suɗe ko ƙashin ne na miki alƙawarin gobe zan kawo wasu. Idan ma tsiren Hashibu kike so sai na haura gobe na sayo miki a Ingawa.”
Ko motsi Hajiya Basariyya batayi ba, haka ya daddafa ya tashi da ƙyar yana tura ciki gaba ga hakki da nishi ya sake ɗare gado inda take. “Haba basariri na wai fushi kike na cinye kazar? Kwantar da hankalinki kinji ai nace zan sayo wata”. Yana maganar ne fa yana ƙoƙarin sake haike mata. Itako abinda ya tokare mata ƙirji ya hanata ko motsi. Haka ya sake bidirinsa babu batun yin wanka ko yin alwala ma balle addu'ar kasancewa da iyali. Dama ɗazun baiyi ba.
Kafin wayewar gari Hajiya Basariyya ta sake tabbatar da Annabi Isa ba ɗan ALLAH bane. Daddy kawai take tunowa tana rusar kuka dayin dana sanin wautarta, bata taɓa sanin rabuwa da Daddy zai zame mata masifa da bala'in rayuwa ba irin yau. Sai yanzu nasihar Kawu Manu ta wancan karon ke dawo mata a rai da zuciya. Ashe gaskiya suke gaya mata ta dawo a hayyacinta kafin lokaci ya ƙure mata. Gashi ko ya ƙure matan, Daddy ya mata saki uku wani ƙaton banza ƙaton ƙauye ya aureta. Haka tasha kuka da rashin barci, ana kiran sallar farko ya tattara kayansa ya ɗauki butar ta ya fita. Daga haka bata sake jin ɗuriyarsa ba. Itama dai haka taje tayo wankan ranta duk tsantsamin banɗakin dana Alhaji Balala data kwana a ciki. Sai ko da tayi amai taji daɗi. Ai gidan Kawu Manu gidan ƴan gayu ne sosai, dan ko ina shafe yake da siminti sai wajen dabbobinsa kawai. Sannan banɗakinsu tsaff yake dan iya akwai tsafta. Balle ma basu da yaran da zasu ɓata musu. Bayan ta idar da salla barci ɓarawo ya ɗan saceta a wajen. Kawai zuwa can gari yayi shaaa sai taji kawai an faɗo mata ɗaki. Firgigit ta buɗe ido tana tashi. Wata busashiyar mata ce a kanta kayan jikinta idan wankewa za'ai saci omo jakka biyu. Tana wani yamutse-yamutse ta ce, “Sunana Deluwa, uwargidan Alhaji Balala. Munji shiru ne baki fito kin ɗora ɗumamen tuwo ba ga yaranmu sun fara kukan yunwa”.........✍️
To gafa Hajiya Deluwa uwargida ran gida ta iso jama'a 😂🤌.
197
........Mamaki ne ya nema kashe Hajiya Basariyya, yo gari fa bai gama wayewa ba ma. To wai ma ita da aka kawo jiya ake jiran ta fita ta saka ɗumamen tuwo ne komi ma. Maimakon tai magana sai ta zubawa matar ido kawai tana kallon ta, ALLAH tsabar ramarta tasan idan kamata zatai sai ta karyata. Yo ai tayi biyar ɗinta. Takaici ya hanata bata amsa ta maida kanta kawai ta sake kwanciya.
Cike da rashin hankali matar ta ce, “Ikon ALLAH, yoke haka keyi ki shige da miji ɗakin tun farkon dare har ketowar alfijir amma ace ki fito kisa ma mutane abinci a wuta kiyi banza. Ke mu fa nan babu ruwanmu da wata ƴar masu kuɗi ko hajiyanci daka mace zamuyi wlhy. Idan Kinga bazaki iya ba ce ya sakeki kiyi gaba mu tafi nono fari a wajenmu. Aikin ɓur inji tusa. Kina son nuna birnancin naki miya hanaki zama gidan mijinki lafiya da kishiyoyi, su can sun rabu da alaƙaƙai munan kuma an kwaso an kawo mana. To wlhy mu basu bane ba bazamu ɗauka ba ehe. Garama ki shirya ki ɗaura ɗamarar zama gidan Alhaji Balele sai jaruman mata”. Ta wani buga labule ta fice abinta.
Eh lallai yau kam Hajiya Basariyya taga mata, ashe Hajiya Yaya Sayyada ce, Asiya ko ai sai dai a kirata waliyya. Tofa, wai yanzu akan wannan kucakin mijin ake wannan tada jijiyar wuyan? To ita wlhy bataga mata ba anan. To jama'a shifa ƙauyen ma nada ƙauye, wannan ai sune asalin ƴan ƙauyen ga jahilci ga rashin sanin ciwon kai. Yo idan ƴan ƙauyen su Kawu Manu na kiran nan ƙauye sai taita mamaki, ashe-ashe sunada hujja. Babbar bala'i ALLAH ya jiƙan Hajiya Yaya da Asiya badan sun mutu ba. Tana a cikin wannan jimami sai ga Alhaji Balala da wani tsohon kofin silba da leda. A gabanta ya ajiye yana washe baki da faɗin, “Tashi amar sugun-sugun tashi na sayo miki shayi da burodi ne da ƙosai, har fa garin kawunki naje yanzu da safen nan nine ɗibar farko a tukunyar shayin nan. Sabi'u nasa ya kaini a mashin ai nasan kin kwana da yunwa bakici komai ba”.
Gaba ɗaya maganarsa hawa mata kai yake yi, dan haka tace, “Nagode”. Daga haka taja bakinta tai shiru.....
😂🤌Gaskiya Basari kina cikin ƙaulani, nace dole na baku First night na Alhaji Balala da Basari bazanci amanarku ba😂 sai ku tabbatar kun min godiya da sanya albarka, dan bana son harkar shiru anan tom🤣😜.
__________★
Canjawar Sageer a gidan ta saka Huznah a matuƙar tashin hankali. Gaba ɗaya sai taji duniyar da komai basa mata daɗi. Babban tsoronta kada ya gayama Daddy abinda ke faruwa ma. Tana son yi masa magana amma tana jin tsoro dan yaƙi bata fuskar yin hakan. Zaman gidan ma kwana biyu ya rage yi, baya dawowa sai dare sosai, baya cin abincinta. Komai zai sayo ya ajiye kamar yanda ya saba amma ya barta da su. Daga sallar asuba idan ya fita baya dawowa sai sha ɗayan dare. Daga sannu idan tai masa ya amsa ciki-ciki baya ƙara kulata. Sai ta shiga wata irin rama. Idanunta kullum a kumbure alamar kuka. Ta tattara wayarta ma ta kai ɗankinsa ta ajiye duk dan ya gane ta haƙura da komai amma yaƙi kulatan dai. Hatta ɗansa da yake ƙulafuci da bama kulawa kwana biyun nan ko ɗaukarsa baya yi.
Bata taɓa tunanin hakan zata kasance da ita akan Sageer ba. Rayuwa kenan, wannan shine ashe magabata ke cewa kayi hankali kafin duniya ya koya maka karatunta. To ita dai ta koya daga duniya a tsakanin nan kam. Karo na farko ta yanke shawarar tunkarar ƙanwarta Madeena da matsalarta. Bayan ta kammala gyara gidan dan yanzu kam zagewa take tayi ta shiga ɗakinsa, inda ta ajiye wayarta tana nan a wajen har yanzu bai taɓa ba tabbacin fushin yake da ita sosai. Ajiyar zuciya kawai ta sauke. Ta ɗakko wayar ta fito. Fodio na a falo kwance a ƴar katifarsa yana barci itama ta zauna a ƙasan. Wayar ta kunna, ta sayi kati a account ɗinta harna dubu biyu yanda zai isheta sannan tai kiran Madeena. Sai da ta kusa tsinkewa ta ɗaga, cikin muryar barci tace, “Aunty Huznah”.
Murmushi Huznah tayi tausayin ƙannen nata na ƙara kamata, dubesu a gidan mahaifinsu babu cas babu as na wahala sai dai suci suyi barci a binsu, su suna ganin gata ne sai an kaika gidan wani ka gane ALLAH ɗaya ne. Cikin sauke ajiyar zuciya ta katse tunanin nata da faɗin, “Madeena har yanzu baki ma tashi ba?”.
Miƙa Madeena tayi tana tashi zaune da ɗan jan tsaki, ta ce, “Wlhy jiya ban kwanta da wuri bane ba. Fatan dai lafiya kema kira da safen nan ina Daddyn mu?”.
“Gashi yana barci, magana na kira muyi Madeena. Dan haka ina son ya kasance ke kaɗai ce a wajen”.
“Babu damuwa ni kaɗaice a ɗaki na kuma kulle ina jinki.”
Komai Huznah bata ɓoyema ƙanwar tata ba saboda akwai shaƙuwa sosai a tsakaninsu. Babu abinda Madeena ke nanatawa sai kalmar innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Kafin tace, “Amma wlhy ban san har yanzu baki da wayo ba Aunty Huznah. Yanzu dan ALLAH dama baki cire tunanin bawan ALLAHn nan a zuciyarki ba har yanzu. Haba aunty Huznah haba dai kamar wadda bata da ilimin addini. Ki daina biyema Ummi fa wlhy kina dai ganin yanda ta kasance mata. Jiya Uncle ke gaya min wai tayi aure a ƙauyen gaba da su Kawu Manu.....”
“Aure kuma?”.
“Eh wlhy, yo in ba ƙauyen ba wazai yarda ya auri Ummi da wannan halin nata. Ai taima mutun nasiha da nuna masa gaskiya amma ya dinga rufe ido yaƙi fahimta. To wlhy ki dawo hayyacinki kar ki zama mai irin wannan halin. Aunty Huznah ALLAH ya miki gata, ya baki miji mai sonki da kula dake, kalla yanda yake rawar jikin kiyaye dukkan haƙƙokinki, wlhy ɗan zaman da mukayi haihuwar fodio bakiji yanda zamanku ya birgeni ba, sai naji ina addu'a ALLAH ya bani miji ko bai kai Yaya Sageer ba. Dan ba auren mai dukiya bane ke nuna ka more aure, masu auren masu kuɗin nawa ne a cikin bala'i da masifar rayuwa, mazan ma basu da lokacin su kullum suna yawon ƙasashe, kuma bazasu iya tsare rayuwarsu ba sai sunbi wasu matan. Wanda kuma ke ma yawo a iya Nigeria ko Africa shima zaki samu ƙalilan ne masu iya riƙe kan nasu. Gamu nan an ce mu fito da mazan aure munma samarin magana duk sun tarwatse kamar anyi ruwa an ɗauke, ka rasa ubami ke kawosu gunka da idan ba auren ba. Amma ke kin samu mai tattalin rayuwarki mai sonki kina wasa da damarki kuma akan haramun ma son wani a gidan aurenki. Haba aunty Huznah ni wlhy duk sai ma kika bani kunya, nazata ai a wuce wajen zuwa yanzu. Ni dai shawarar dazan baki ki koma ga ALLAH, ki koma gayama UBANGIJI kukanki ki shirya tsarkake zuciyarki da rayuwar aurenki ALLAH zai dafa miki ya cire miki Yaya AA a zuciyarki, ya kuma saka miki son mijinki. Shi yana can yana farin ciki da matarsa, Maanal gashi har ta haihu jiya twin's ke kina nan kina ɓata ƙyaƙyƙyawar rayuwar da ALLAH ya baki. Kiyi ƙoƙari ki bama Yaya Sageer haƙuri ki nema yafiyarsa, dan wlhy ko Yaya Yazeed kika bari ya gayawa sai ya ɓata miki rai balle Daddy. Ki cire ZUCIYARKI daga wannan AJIYA A DUHUN ki maidata cikin haske ALLAHU zai haskaka ki ya haskaka rayuwar aurenki ya haskaka jikinki da zuri'ar da kuka fara tarawa...”
Sosai Huznah ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, “Nagode sosai Madeena, Nagode da tunarwarki, wlhy wani lokacin rashin mai gayawa mutum gaskiya shike sake dulmiye tunainsa a wahalar rayuwa. Na jima da son jin ina son na cire soyayyar AA Darma a raina amma na rasa tayaya zanyi hakan, ta ina ma zan fara. Amma yanzu kam kin haska min hanya, kin cireni daga duhun dana shiga nakai zuciyata AJIYA A DUHU. In sha ALLAHU zan dage da addu'a, dan wlhy nima nasan na fara son Yaya Sageer, amma wancan ke danne zuciyata. Amma ina sha ALLAHU zan canja, zan canja daga waccan Huznah fandararriyar zuwa Huznah nagartacciya jinin Usman Chalawa.”
“ALLAH ya tabbatar Aunty Huznah ki daina kuka. Nima zan tayaki da addu'a kuma zan saka a islamiyya a tayaki a kuma yi miki saukar Alkur'ani. Amma kema ki dage da addu'a jarabawace in sha ALLAHU zaki cinyeta. Nima zan kira Yaya Sageer na bashi haƙuri ”.
“Nagode Madeena idan kikai min hakan kin taimakeni ƴar uwa ta. Ngd sosai. In ce dai baku da wata matsala?”.
“Wlhy Alhmdllh babu matsalar komai, Mamma da Ammie na iya ƙoƙarin su a kammu, hakama Yaya Yazeed. Shima Daddy, Dan yanzu haka ma ni na dawo sashen Ammie ne”.
“ALLAH sarki ALLAH ya saka musu da alkairi. Amma da Ummi tasa muyita zaginsu da kallonsu mugaye, gashi yanzu bata kusa kuma sun riƙeku da zuciya ɗaya. ALLAH yasa wannan auren ya zame mata izina itama ta canja”.
“To amin”.
Sun jima suna hira da tattauna abubuwa akan mahaifiyarsu kafin sukai sallama. Sai Huznah taji nauyin zuciyarta ya ragu sosai sai sauke ajiyar zuciya take yi.......
_______★
Anan gidan Darma kuwa tunda labarin haihuwar Maanal yazo musu tsakanin Saheeba, Nuratu, Mamy babu wanda baiji tashin hankali, baƙin ciki da hassada ba. Dan Mamy batayi kwanan gida ba a daren jiya sai asibiti. Sosai abu ya birkita mata zuciya sai aman jini. Haka aka kwasheta dan ALLAH ma yaso Aunty tazo Abujan ne jiya da safe, kamar yanda ta saba zatai kwana biyu ya koma. Sai kuma ga wannan al'amari dan AA da kansa yay kiran aunty ya sanar mata. Da yake kuma tana da babbar waya ya tura mata hoton yaran. Anan ne fa take nunama Mamy, su kuma su Saheeba a media suka gani.
Kawai Mamy na ganin hoton yara ta fara jan numfashi da ƙyar, abu kamar wasa tari ya sarƙeta sai ga aman jini. Ba Aunty kawai ba shi kansa RK da aunty taima bayanin komai mamakin baƙin zuciyar matar nan yake yi. Ya tabbata wlhy itace zata kashe kanta da kanta. Yanzu idan dukkan abinda ya faru bai zame mata izna ta koma ga ALLAH tana neman tuba da roƙon gafarar duk wanda ta zalunta ba mi kuma take buƙata? To lallai kuwa aiki ya ganta. An tsayar da aman jinin nata da ƙyar kuma sai ga sabuwar magana a gwajin da akai mata na jini dan doctor dake dubata yace a gwada ko akwai maleria a tare da ita. Sai kuma sakamako ya nuna akwai ciwon HIV...........✍️
Tirƙashi, wasu na murnar haihuwa. Wasu na kukan kabari ya tunkarosu. Wannan fa itace ainahin