Author : Bilyn Abdull Category : Romance
ɗaure mata baki, itama ya ɗaureta a jikin gado. Yanda hankalin Hajiya Yaya ya tashi ALLAH dai ya kiyaye zuciyarta bata bugaba. Dan ita kam a gaban idonta ya tattare komai da komai nata dana ƴaƴanta kasancewar yasan inda suke kuma itama bata barin yara da su anan take adanawa yay ficewarsa ya barta a ɗaure. Cikin matuƙar takaici ya hararari sashen Ammie da bai samu nasara ba. Sai kuma ya nufi sashen su Hameed. Tsaf ya hargitse komai amma bai samu ko atm ba kam ya fito cikin takaici. Babban Nazeerah ya kira yace gasu duk ya haɗa, sai dai Ammie ta kulle sashenta nata ne kawai babu. Duk da Babban Nazeerah yaji takaici sai yace ba komai fito ka kawo min ina waje. Haka Yazeed ya buɗe gate ya fita. Babban Nazeerah kam yana nan a mota yana jiran nashi, yayi mamakin samuwar komai cikin sauki dan bai san haka aikin zai zamo ba ai da tuni ya saka Yazeed ɗin yayi an wuce wajen. Koda ya amsa kayan sai ya amshe har wayar Yazeed. Sannan ya kallesa cikin gargaɗi.
“Kaga idan za'a kasheka kace nine na sakaka ka kawo min abubuwan nan sai na wulakanta rayuwarka. Ka ɗauka bama ka taɓa sanina a rayuwarka ba har abada. Kaje zan nemeka bayan na gama dubasu na tantance masu muhimmanci, zan saka kai min signing a Wanda kake da damar haka dan nasan kaine next of king na ubanka. Wanda kuma bakai bane ɗaya bayan ɗaya zan sace ku kuyi min signing. Na gama da ubanka kuma sai next, gidan Darma bye”.
Yazeed kamar robot haka yayma Babban Nazeerah godiya ya juya cikin gida.......
Tirƙashi🤔 nama rasa abin faɗa🥺
________★
Dangin Mamy sune suka fara shirin wucewa. Koda sukazo yima Oum sallama kamar yanda ta saba ta haɗa musu alkairi mai yawan gaske. Cikin su Ajwaad babu wanda ta gani tasan kowa na barcin gajiya. Balle ma Babban Yaya da Fawzan bai yiwuwa a kirasu, ya kamata a basu damarsu. AA ne ma mai ɗan dama-dama yau dan haka ta shiga kiran tashi wayar....
Da ƙyar AA dake rungume da Maanal ya iya buɗe idanunsa ya ɗauka wayar. Badan ringtone ɗin Oum bane ma bazai ɗaga ba. Shiyyasa ma shi yafi yarda da saka waya a vibration koma a silent gaba ɗaya saboda bai ƙaunar damuwa. Wannan wayar ce kawai yake bari a buɗe da ɗan ring ƙasa. Jin yanda yay sallama murya a shaƙe Oum ta ce, “Oh sorry Auta baka tashi ba ne kaima”.
“Oum an gaji ne shiyyasa, amma yanzu na tashi ina kwana”.
“Lafiya lau, ya Baby”.
“Lafiya lau Oum ta tashi normal kamar yanda Uncle ya faɗa”.
“To Alhamdullahi ALLAH ya kiyaye gaba. Dama baƙine zasu wuce ya kamata a nema musu mota mai ƙyau, nima banyi zaton tafiyar wuri zasuyi haka ba”.
“Okay Oum suyi haƙuri su jirani bara na ɗanyi wanka.”
“Okay tom sai ka fito”.
Ta faɗa tana yanke kiran. Tana yimusu hakane dan su san muhimmancin dangin Mamyn a wajensu. Kuma Alhamdullah hakan yana yin tasiri sosai. Dan ita dai Mamyn ba damuwa tai ta sakasu suyi masu alkairin ba. Sai Maman Saheeba kawai da Aunty, Maman Saheeba ɗin ma tafi ci. Suko wannan itama ɗan bata da yanda zata yi ne take yarda ana nuna su a ƴan uwanta saboda talakawa ne. Idan ma sun yi musu alkairin idan ta amsa sai ta gadama take basu, gara ma ɗan rabon azumi tana basu abinda ya samu sauran ta rabama wanda take so...
Tunda ya fara wayar Maanal ta farka. Yana ajiyewa ta buɗe idannunta. Dama barcin dole aka sakata bayan ya gama yamutsata, amma ita barci safe a yanzu dai sam bayinsa take ba. A hankali ya hure idanun data zuba masan. Sai ta lumshesu ta sake buɗewa. Da muryarta ta barci ta ce, “Waye ya kira?”.
Cikin raɗa yace, “Oum. Wai baƙi zasu tafi, nasan ƴan jigawa ne ƴan uwan Mamy”.
Wai ƴan uwan Mamy, ita dariya ma ya bata. Amma sai batayi ba itama cikin raɗan tace, “Kai banda kai?”. Kumatunta ya ɗan matsa, bakinta tada cuna masa ya ƙara dan tsukewa waje ɗaya kamar yara na shagwaɓa. Yay murmushi da sumbatar bakin ya ce, “Sarkin fassara zance ni bance ba”. Idanunta ta ɗan juya zuzu sai kuma ta murmusa tana janye hannunsa dake matse mata kumatu, sai ta kai yatsarsa cikin bakinta ta ciza kaɗan”.
“Ouch! Besty wace mugunta ce haka?”.
Ƴar dariya tayi kaɗan. “Sorry, ALLAH kawai jinai ina sha'awar in cijeka. In gani wajen yayi jini”. Ƙin bata ta gani yayi sai ma ya ɓoyeshi yana ɓata fuska. Ita kuma ta hau dariyar ƙeta tana ƙoƙarin kamawa da tsiya. A haka suka rikice da ƴar kokawa, ta dage sai ta gani shi kuma yaƙi. Ta koma saman jikinsa. Sai kawai ya shiga yimata cakulkule tana dariya sosai shima yanayi. Sai da suka gajiyar da kansu kowa idonsa ya ware daga barcin sannan ya ɗauketa suka wuce bayi suna dariyar ƙasa-ƙasa. Sun ɗan jima kafin suka fito, dan a bayin ma ba'ai wankan kai tsaye ba. Da taimakon juna suka shirya. Sunyi ƙyau kamar ka sacesu ka gudu. Ga wani sirrikan ƙamshi mai ratsa zukata. Shi ya fara fita ita kuma ta gyara ɗakin sannan tabi bayansa....
Ta sami su Umma a falo suna breakfast harda Ammienta da su Hajiya Basariyya, sai AA zaune a dining yana waya RK a kusa da shi yana shan abu a kofi shima. Oum na daga tsaye. Zuwa Maanal tai ta fara gaishe da su Umma sannan ta je ta rungume Oum. Cike da shagwaɓa tace, “Oum yunwa cikina kamar anmin sata”.
Cike da kulawa Oum ta shafa kanta tana murmushi, yayinda RK ke mata dariya. AA kam kallonta yake kawai yana wayarsa. Oum da kanta ta haɗa mata abinci, ta zauna tana ci AA ya kammala wayar yana kallonta yanda take cin abincin da sauri-sauri, sai kuma ya ɗauke kansa ya maida ga Oum. “Oum su shirya gashi nan zuwa. Gashi babu kash a jikina na kuɗi dole zan fita na samo”.
RK yace masa nawa kake so? Faɗa masa yayi. Shi kuma ya jefa masa key yana faɗin, “Za'a samu a motata ka duba”.
“Yauwa thanks you Uncle”.
“Munafuki, ka dai nema Uncle ɗinka bani ba”.
Murmushi AA yay yana tashi ya fice. Maanal da Oum kuma na musu dariya.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣1️⃣8️⃣
______________
......Koda AA ya ɗiba kuɗin a motar RK sashen Mamy ya nufa. Ya samu duk sun kammala shiri jira kawai suke. Ya gaishesu da girmamawa, tare da godiyar ƙoƙarin su sannan ya basu haƙuri na jinkirin daya sakasu. Yace ga wanda zai kaisu nan zuwa. Aunty ya bama kuɗin yace ta basu. Aiko sunata godiya da sanya albarka. Tare da addu'ar zaman lafiya su da iyalansu. AA da addu'ar tasu tai masa daɗi ya amsa da Amin yana miƙewa da tambayar ina Mamy. Dan bata a falon. Shine aunty Babba tace masa tana ɗakinta. Ɗan jim yay na mamaki, sai kuma baice komai ba ya haura saman. A falo ya samu Maman su Saheeba da Nuratu suna magana. Suna ganin shi sukai shiru. Shima kallo ɗaya yay musu ya wuce abinsa ko gaida Nana baiyi ba. Cike da takaici ta bishi da kallo, dan ta fahimci ɗan iskan yaron nan fa ya daina gaisheta yanzu. Nuratu kam tamkar mayya haka take kallonsa zuru, wani irin sonshi na ratsa mata zuciya da ɓargon jiki, jitake kamar taje ta rungumeshi wlhy....
Knocking ƙofar ɗakin Mamyn ya ɗanyi, ta zabura daga tagumin data zuba abin duniya ya isheta. Musamman maganar Sille dake tsaye a ranta. Tana son taƙi bashi kuɗin tana jin tsoron yazo ya mata tonon silili gida cike da mutane. Ko bai ce komai ba wani ya ganshi ya shigo mata ai sai ma ai mata wani zargin daban, balle gashi da suffar tantirai. Jin an ƙwanƙwasa ƙofar sai da gabanta ya faɗi, sai ta dinga tunanin ko Sille ɗinne ma. Yana ƙara kwanƙwasawa ta dirgo a gadon jikinta har rawa yake ta buɗe kofar. Sai sukai ido biyu da Ajwaad. Wata irin ajiyar zuciya mai nauyi data bashi mamaki ta sauke. Sai kuma ta juya ta koma ciki. Bin bayanta yay ajiyar zuciyar tata na tsaya masa a rai. Koda ya zauna a cikin sofa sai da ya sake kallonta. Sai ramarta ta fito masa sosai yau a idanun. Gaisheta yay cike da kulawa, ta amsa masa sama-sama. Ya ce, “Mamy baki da lafiya ne wai?”.
Shiru tai masa, kusan minti ɗaya sannan tace, “Ƙalau nake miya kawoka?”.
Shiru ya ɗanyi jimm. Sai kuma ya girgiza kai da faɗin, “Babu komai, kawai nazo gaisheki ne na kumayi sallama da baƙi da sukace zasu wuce”.....
★★
A nan sashen Oum kam bayan ficewar AA a bisa tsautsayi Nuwaira ta ɗakko naman kai da taima RK farfesu dan yana sonshi, kawai tana gamawa sai ta ɗakko tukunyar gaba ɗaya ta fito da ita ta ajiye a dining ɗin tana faɗin, “Yauwa to Yaya naman kanka yayi”. Maanal ta tsaya cak da cin abinci, Ammie dake daga falo ma tana jin furucin Nuwaira sai da ta ɗan juyo ta kallesu, dan tabbas tasan in dai hasashensu gaskiya ne, kuma irin ɗaukar cikinta Maanal tayi to akwai matsala dan bata shiri da naman kai da soyayyan ƙwai. Aiko tunanin nata bai kai ƙarshe ba Nuwaira na buɗe tukunyar ƙamshin naman ya wani bigi kan Maanal dan anyi rashin sa'a ta inda take iskar ke kaɗawa, ai da wani kalar sauri ta miƙe tana mai sakin spoon ɗin hannunta jikinta har rawa yake nason barin wajen. Duk kallonta sukai, Oum tai ƙoƙarin riƙota tana faɗin, “Subahannallahi Baby lafiya? Kuwa”.
Kai Maanal ke girgiza mata, idanunta sun wani kaɗe sunyi jazur lokaci guda. Tana buɗe baki zatai magana kawai sai amai.
“Ya ARRAHIM”.
Oum ta faɗa tana riƙota dan neman zubewa take ƙasa. Duk mikewa su Mah-mah sukai suma suna nufo dining ɗin, Ammie kam ta fuske kamar bata san mike faruwa ba. Sai dai zuciyar nakan Maanal, dan tasan yau kam zata ɗan ɗana kuɗarta, dan in ba sa'a akaci ba sai tai kwanaki tana jin ƙyanƙyamin abinci. Dan zatai ta tuna wannan ƙamshin naman ne. A farkon ciki da wahala ka gane mata dan bata wani laulayi ko ciwo da sauransu, sai yawan barci da shagwaɓa da neman rigima da buƙatar miji a kusa da ita matuƙa, kamar dai yanayin Maanal. Amai ko wani zubar da yawu duk batayi. Sai dai duk randa taji ƙamshin naman kai ko soyayyan ƙwai babu zaman lafiya. Sai tai kwanaki tana fama. Sai ciki ya shiga irin wata bakwai ɗin nan take fara ɗanɗana kuɗarta. Bazata sake lafiya ba sai kuma ALLAH ya rabasu.
Yanda Maanal ke amai kamar zata zubo da kayan cikinta waje sai da tabama kowa tausayi, ga kuka tanayi da faɗin, “Wayyo Oum zan mutu” sai wani ya sake yunƙurowa sai ta rirriƙe Oum ɗin. Gaba ɗaya hankalin Oum ya tashi jitake kamar tai mata kuka. Shi kansa RK duk ya daburce kamar ba likita ba. Ƙamshin naman dake shiga mata hanci yana hawar mata kai yasa aman yaƙi tsayawa, su kuma kowa bai fahimci ƙamshin naman ne bata so ba. Kamar ya tsaya Oum ta kamata ta miƙar sai ya ƙara bugarta, ai da sauri ta koma ta sake duƙewa. Sai lokacin ne Ammie dake daga falo har yanzu bata taso ba tace ma Aunty Sharifah matar Uncle Modibbo. “Wannan naman ne ke sata aman, idan ta daina jin ƙamshin zata bari”.
Aiko cikin haushi Gwaggo Khadijah da taji Ammien ta fara mata faɗa. Murmushi kawai Ammie tai ta ce, “Ayi haƙuri Gwaggo”.
“Ƙyace fa haka, dan rashin tausayi yarinya na wahala kin san miye matsalar sai kiyi shiru saboda ALLAH Asiya. Sai kace wata ƴar fari. Auta ce fa. Kawaicinki yayi yawa ALLAH sai kace wata bafulatana”.
Ammie dai murmushi kawai tai bata sake cewa komai ba. Ana kuwa ɗauke naman Maanal ta daina jin kanshi ta daina yunƙurin aman. Sai dai tayi laushi gaba ɗaya ta zube a jikin Oum tana sauke wahallen numfashi ga hawaye sunƙi su tsaya. Dai-dai nan AA ya shigo, dangin Mamy biye da shi zasuma Oum sallama. Ganinsu sun tattaru waje ɗaya yace, “Lafiya?”.
Meeno datai kwale-kwale kamar zatai kuka tace, “Yaya Auntyna ce keta amai”.
Yasan Maanal take cema auntynta. Gabansa ya faɗi ya bi ta gefe ya shigo inda Oum take riƙe da ita tana hawaye da riƙe ciki. Gaba ɗaya idanun AA ya rufe, ita ɗin kawai yake gani cike da tashin hankalin halin daya ganta a ciki. Gabansu yazo ya tsugunna ita da Oum ɗin, fuskarsa na bayyana matsananciyar damuwa. Inte na gyara wajen da Maanal ɗin ta ɓata. Ƙamshinsa kawai taji, sai ta ɗago daga jikin Oum dake shafa mata baya kamar yanda RK yace a mata ta kallesa. Sai ta sake fashewa da kuka ta ce, “Besty cikina.”
Gaba ɗaya shima idonsa ya kaɗe, ya riƙo mata hannu sai kawai ta shige jikinsa ta ƙanƙamesa tana sakin sabon kuka. Ina shi wlhy yama manta da wani batun iyaye a wajen, ya ƙanƙameta idanunsa na sake juyewa. Yanda take kukan cikinta-cikinta yasa RK faɗin, “Ajwaad ɗauketa muje ciki ina zuwa”. Ya fita da sauri. AA ɗin kuma ya miƙe ya ɗagata cak. Sama ya nufa da ita bedroom ɗin Oum. Kukan da take na kekketa masa zuciya. Ammie ta girgiza kai kawai a zuciyarta tana ayyana (Indai haka za'ai renon cikin kowama zaiji jiki a gidan naku kenan).
Hajiya Basariyya ta kalla Maman Yaseerah, Maman Yaseerah ta kalleta, gulma fal cikinsu da hassada. Ƙasa-ƙasa Maman Yaseerah tace, “Tab ɗin, wannan fa daga gani ciki ne”. Sosai gaban Hajiya Basariyya ya faɗi, har taji ta gagara iya cema Maman Yaseerah komai.
Bayi ya wuce da ita, da taimakon Oum suka ɗauraye mata fuska da baki dan bata ɓata jikinta ba. Kafin ya sake ɗakkota suka dawo ɗakin ya sata a gado, yanda taƙi yarda tabar jikinsa dole ya zauna a gadon shima tana a jikin nashi. A haka RK ya shigo, allura ya haɗa ya bama AA yay mata. Sai kuma ya haɗa wani ɗan madaidaicin drip da wasu alluran. Da yake ba tsoron allura take ba lafiya lau akayi, shima ruwan AA ɗin ya saka mata a hannu bayan ya ɗiba jinin da RK ɗin ya buƙata duk tana lafe a jikin nasa. A hankali ciwon cikin ya fara raguwa sai kuma jikinta ya fara saki sai barci. AA dai na faman riƙon hannunta dan karta tunɓuke ruwan. RK kuma ya miƙe yana faɗin zaije asibiti ya dawo dan a gwado jinin.
ALLAH sarki ana gayoma su Abah suka taso suka fito, a karo na farko na tarihi yau Baba Sardauna da Abbu, da Baba har bedroom ɗin Oum sun shigo a dalilin Maanal. Sai yanzu ne AA yaji ɗan nauyi dan gaba ɗaya Maanal ɗin a jikinsa take kwance. Oho su Baba Sardauna babu ruwansu, cike da kulawa da nuna damuwa suke mata addu'a. Mamy ma dai dole ta fito jin gasu Baba Sardauna can a sashen Oum ɗin. Tsoron kar Abah yay mata wata ƙullatar dole ta fito tazo dubantan itama. Kamar an saita sai ga RK ya dawo abinka da masu abu yana zuwa asibitin abinda ya dace yayi. Yanda yake wani makirin murmushi yasa Uncle Mahmud yin magana. Sai kawai RK ya miƙa masa takardar hannunsa yana kashema AA dake kallonsa shima ido ɗaya.
“Woww!! Alhamdullahi! Alhamdullahi! ALLAH to ya bada lafiya ya kuma inganta mana.” Uncle Mahmud ya faɗa bakinsa na washewa da fara'a, kowa yasan son haihuwa a jinin Darma Family take. Ya miƙama Baba Sardauna dake kusa da shi result ɗin yana faɗin, “Baba ƙaruwa ce muka samu ai, ALLAH ya bata lafiyar raino ya kuma raba kafiya”.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣1️⃣9️⃣
______________
.......Lokaci ɗaya bakin kowa ya washe a ɗakin, duk da Oum tana hasashen hakan daman a hankali takai duƙe tai sujidar shukur, hakama Abah daya kasa haƙuri. AA kam ƙasa yay da kansa idanunsa cike da ƙwalla. Ya zuba ma Maanal ido yana jin wani abu mai nauyi na mamaye masa zuciya da jinin jiki. Shima sujidar shukur ɗin ya kamata yayi, sai dai tana jikinsa dole ne yay haƙuri. Su Umma ma sai ambaton Alhamdullah suke cike da farin ciki. Yayinda wani irin jiri ke ɗibar Mamy sai da ta lafe a jikin bango...
Hajiya Basariyya kam jitai gaba ɗaya duniyar ta mata nauyi, karo na farko tayi dana sanin zuwanta Abuja. Dan da tasan wannan mummunan labarin zataji a