Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   9 / 72

24K to 27K   out of 214K words

bazai yiwuba, kuyi ha?uri masoya, yawan maimata min slm ince wslm ayi sama da sau goma yana sa in share mutun tsakani da Allah sabida kamar bashi da abin faWane so Please na tuba,=?O?


Ido ta zazzaro tare da cewa.
"Hihhhhhhh, ya dahu?". Kanshi ya rausayar tare daci gaba da Sare kwan saida ya Saresh tas ya fito subul gwannin ban sha'awa, sai turiri yaketayi, Junainah ya mi?a.
"KarSi kici kiji mana, kwan ya nuna ne ?anwaliya".
Da sauri tasa hannu, zata amsa, cikin sanyi Aysha tace.
"Ke uwar kwaWayi bazaki ciba".
Rau-rau tayi da idanu alamun zatayi kuka, shi kuwa Ba'ana fuskarshi ya haWa tare da kafeta da ido, da sauri tayi ?asa da kanta, tana mai wasa da ?an yatsun hannunta, dubanshi ya maida kan Junainah tare da cewa.
"Kici abinki Junainah". Fuskarshi ya ?ara haWawa jin Aysha ta kuma cewa.
"Dan Allah Ya Ba'ana kada taci".
Ba tare daya kalleta ba, tace.
"Kema zakici ai bare ita". Da sauri ta Wago kanta tare da girgiza kan tace.
"A a ni kam ngd bazanci abinda ban san da me aka dafashi ba".
juyowa yayi ya kalli Junainah da tuni ta fara cin kwanta, tana lumshe ido baki cike da kwan tace.
"Ya Ba'ana bari inje cikin gida in kawo mana yaji mai daWi Addana bata cin kwai saida yaji".
To yace mata, tuni ta juya tayi cikin gida.

Kallonshi ya maida kan Shatu cikin haWe fuska yace.
"Mata kina tunanin zan cutar da kene?".
A hankali ta jujjuya mishi kai alamun a'a, gyara zamanshi, yayi tare da cewa.
"To baki yarda dani bane?".
A hankali ta buWi bakinta tace.
"A'a ni dai tsoron abun naji, ka toni rami mai danshi da sanyin yashin damina, ka binne Wanyen kwai mai sanyi ka fito dashi da zafi a dafe ni kam ina tsoro ban san da wutan me ka dafashiba".

Fuskarta-ta yayi da kyau kana, ya fara magana.
"Ki yarda dani Mata, bazan taSa cutar dakeba a rayuwa, duk abinda zakiga inayi, zanyine dan kare lfyarki da kuma baki kariyar. Jikin ki, kici kwannan, babu abinda zai miki".
A hankali tace,
"Ni bana cin kwai dama, kuma ai shi kariya Allah ke hadashi ga dukkan bayinsa".
hannu yasa ya amshi robar dakekken yaji da Junainah ta mi?o mishi, wacce yanzu ta dawo wurin.
Wani kwan ya kuma Sare mata, ya mi?a mata, tanaci tana lumshe ido saida taci biyar, sannan tace.
"Ya Ba'ana na ?oshi". Shatu ya Wan kalla tare da cewa.
"Saura biyar kuma nakine, in kin shiga gida kicishi, sannan kuma akwai wani haWin maganin da zan kawo miki kiyi amfani dashi. Ni yanzu zan tafi".
Kai ta gyaWa mishi alamar to, kana kuma tace.
"Ina zakaje yanzu? Tunda naga lokacin tafiya kiwo dai ya wuce".
Mi?ewa tsaye yayi tare da cewa.
"Zan shiga ?auyen Bonon ne".
Da mmki a fuskarta tace.
"Ya Ba'ana me zakayi kuma a ?auye Bonon garin masafa kafurai ?abulun ?achama".
Ido ya zuba mata har saida taji tsoronshi a hankali yace.
"Kema watan watarana zakije, ki tuna da kyau Mamata ?abilar Sachama ce, ?ar garin Bonon kinga kuwa dole inje can tunda kawuneina ?annen Mama da yayunta da iyayenta duk suna can".
Ya ?arishe mgnar kamsr yaji zafin zancen ta,
ganin hakane yasa a hankali tace.
"Kayi ha?uri". Kai ya juya mata alamar babu damuwa.

Daga nan ya juya ya tafi, ita kuwa tacewa Junainah su shiga gida.
Suna shiga cikin gidan ta harari Junainah tare da kai mata bugu cikin faWa tace.
"Hegiya kwaWayayya maza ki zubar da sauran kwanan jakar yarinya ai sai ya ciyar dake guba tunda kince ke kwaWayayya ce".
Ihu Junainah ta kurma tare da cewa.
"Wayyoooooooo Inna kin ganta ko tana cin zalina". a guje tayi gaba, ita kuwa Shatu tabi bayanta da sassarfa tana cewa.
"Wallahi sai kin zubda ?oyayen nan".
A haka suka isa har gaban Ummey da inna da suketa tafasa nonon da aka tatsa a sanyin safiyar yau, wanda a ?alla ya kai jarka goms sha uku, so masu gidajen fura da nono na cikin Shikan Win nema suke saya, dan matan gidan Bappa kab bai lamunce da zuwansu tallan nono ba.

Inna ce tayi saurin kare Junainah dan saura ?iris ta abka cikin tafasasshen nono da yanzu aka sau?eshi, cikin tsoro tace.
"Kai ya ilahi ku dai bazaku zauna lfy ba". Cikin nitsuwa Shatu ta zauna gefen Ummey nan ta labarta musu abinda ya faru da yadda ya dafa kwan ta ?ara da cewa.
"Amman da yake Junainah uwar kwaWayi ce, a take a gabanshi taci kwai biyar cas tanaci tana lumshe ido".
Cikin tarin mamaki Inna da Ummey sukayi ta salati tare da tafa hannu, a tare sukace.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun, oh wannan yaron anya kuwa mutun ne ba shaiWan ba?".
Cikin rau-rau da ido, Shatu tace.
"Ni ina jin tsoronshi, bana sonshi bazan aureshiba, mutumin da komai nashi na tsafine Inna ki cewa Bappa ya rabani dashi mana".
Cikin alhini, Inna tace.
"Rashin sani yasa Bappanki dama ke kanki kukayi mishi al'?awarin shine mijinki duk rintsi, gashi yanzu ya zame mana masifa.
Juyowa sukayi suka kalli Ummey da idonta ya ciki da hawaye a hankali tace.
"Dana sani wlh da ban bar haka ta faru ba".
Shiru sukayi cirko-cirko a wurin, saida suka jiyo ?aurin nono na zuba cikin murhune suka dawo haiyacinsu.
Kana suka juya suka ci gaba da aikin su.


A birnin Jalaluddin kuwa ?arfe tara na safiyar ranar, dai-dai jirginsu Sitti da jikanta Sheykh ya tashi zuwa ?asa mai tsarki da sauran taro al'ummar Annabi masu zuwa Umrah.

Soyayyar da Sitti keyiwa Sheykh soyayyace mai tarin yawa, wanda ko uwa iya son da zatayiwa Wanta kenan, tana ji dashi tamkar ranta, wata ?il hakan baya rasa nasaba da tsananin kamanni da yakeyi da mahaifinta wanda shine baida lfy yanzu kuma shine tsohon Limamin Harami yanada zuriya mai tarin yawa yayansa na cikinsa zalla su arba'in da bakwai.
Bar jikoki da ?anne da yaran yan uwa, sai dai ya tsufa sosai tun shekaru ashirin da suka gabata ya Waura babban Wanshi wanda yake ?anin Sitti ne uwa Waya uba Waya a matsayin shi.
Zuwa yanzu tsotsai tsufa ya kama Sarki Abdulkarim, Hairan wanda yake da shekaru Wari da biyar a duniya, sai dai sufarsa suface mai tsabta tsuface da ka gani kasan an rainin ?uruciyarta da tsoron Allah da ibada. Shiyasa babu gigita ko fita haiyaci, yana son diyarsa Sitti kakarsu Sheykh kenan so mai tarin yawa ko dan tayi nesa da shine, wacce ita kuma tun tanada shekaru ashirin da uku, Sarkin Musulmai na ?asar Kautal na wancan ?arnin yazo da babban Wansa, Jalaluddin wanda a nan yaga UmmuKulsum Sitti kenan, ya sota, kuma Allah cikin ikonsa suka dai-dai ta, haka yasa kafin ya koma ma da amaryarshi ya koma dan sitti ta kafe ita dai tana son Bahaushen ga, duk da tasan yanada mata biyu, tace ai a gidansuma bata tashi ta samu mahaifiyarsu ita Waya ba.

Tuni ita kam Allah ya mata rasuwa mahaifiyar Sittin kenan, yanzu mahaifinta ne kadai a raye, sai kuma ?anninta da yake matsayin Waya daga cikin manyan limaman harami a yanzu sai sauran zuriyarta da yayu da kannenta.
Kowa na ahlinsu yasan Sheykh domin Sitti tana yawan zuwa dashi tun yana ?arami, kana tana zuwa da sauran ma baki Waya, to shi Jabeer anan ?asar saudia ya haWa digiri Winshi na forko dana biyu. Shiyasa ya zama duk zuriyar an sanshi farin sani, ga kuma tarin kama da yakeyi da mutanen zuriyar wanda da zaran ka ganshi kasan jininsu ne.


Tafiya mai tsowo sukeyi cikin sararin samaniya suna keta gajumare, a ?alla tsawon aha huWu kenan suna tafiya.
Kafin suka sau?a cikin babban Airport Win jidda, wanda yake tamkar zai fashe da jirage, ko wacce ?asa ta duniya tanada jirginta cikin wannan babban Airport Win, tashin jirage da hawa da sau?ansu tamkar babu wani abun hawa a duniya sai jirgi.

Koda suka fito daga jirgin, wani jirgine na musamman suka shiga wanda yake daga fadar Mai Alfarma masarautar garin. Wanda ya turo a tarSi ?ar uwar abokinshi da mahaifinsu keta begen gani.
A take suka shiga jirgin ya wuce dasu, asalin cikin garin makka, wanda pilot Win kuma Wane ga Umaymah ?anwar Mamansu Sheykh wato shima jikan Sitti ne Wan Umaymah sai kuma Jannart wacce ta biyo Haroon Dan tarban kakar tasu wacce ita kuma ?ace ga babban Wan Sitti wato ?anwar Juwairiyya ce kuma anan take karatu.

Suna sau?a a Airport Win,
suka fito, a jere, yana gaba yana rike da hannun Sitti tana biye dashi a hankali tana taka step Win Jannart kuwa tuni itace a gaba.
Haroon ne wanda yake biye dasu a baya yana kallon yadda kakar tasu ke taka step da kuma yadda Wan uwan nashi ke rike da hannun ta, murmushi yayi tare da jingina a ?ofar bakin jirgin cikin harshen larabci yace.
"Ko dai zaka goyeta ne ka sau?ar da ita".
Sheykh bai kulashi ba, har saida suka sau?o ya gyarawa Sitti tsayuwarta, kana ya mi?awa Jannart hannun Sitti alamun ta rike musu ita. Cikin jin daWi Jannart ta riko hannunta tare da cewa.
"Ana Uhubbiki ya Sitti". Cikin jin daWi da son jikokin nata tace.
"Ana". Sai kuma suka juyo suna kallon Sheykh dake tsaye cikin shiga ta al'farma shigar salihan bayi, wata dandatsetsiyar al'kyabbace mai masifar kyau ruwan ?asace al'kyabbar sai surfani da aka sarrafa a jikinshi wanda yake da kalan gold, haka takalmanshi da hiraminshi duk masu ratsin Golding color ne, cikin tsananin jin daWi Haroon ya fara sau?owa daga step Win, yana kallon Wan uwan nashi manda suke sa'anni, ruggume juna sukayi, cikin jin daWi Haroon yace.
"Marhabin da zuwa Al'Sheykh, ya gida?, ina ?annena? Yaya jikin Ya Jafar? Ya Hajja Mama da kowa da kowa."
KwaSe fuska ya Wanyi tare da janye jikinshi daga na Haroon cikin sanyinshi yace.
"Duk in kana son ganinsu kaje Nigeria zaka gansu, kana nan kullum sai yawo a jirgi kamar turuwa a daji, duk ?asashen duniya ka gama zagayesu".
Murmushi Haroon yayi tare da cewa.
"To ai dama na sani bakinka Waya da Umaymah'nka, zan koma ne in sha Allah, zan koma inyiwa ?asarmu aiki, suma ai suna bu?ata na".
Fuskarshi ya Wan kauda tare da cewa.
"Da yafi kam". Juyowa sukayi jin Sitti na cewa.
"Kai Haroon ku taho mu tafi, ka tsareshi da surunka tun daga nan ko?".
murmushi Haroon yayi kana ya nufi inda take tare da cewa.
"Oyoyo My Sitti". Kai ta juya tare da cewa.
"Rabu dani ba kaga Wan uwanka ka shareni ba".
Ruggumeta yayi ta baya tare da cewa.
"Na isa in share uwar gida ran gida a gidan Sarki Jalaluddin". Jannart ce tai dariya tare da cewa.
"Sitti karki yadda da daWin bakinshi".
Hannunshin yasa ya Wan dungure kan Jannart tare da cewa.
"Kishi ko dan kinga gani ga uwar gida".
murmushi Jannart tayi tare da jan hannun Sitti sukayi gaba, shi kuwa Haroon baya ya dawo ya saita da Sheykh suka fara tafiya a jere,
duk wanda yaga salo da tsarin tafiyar Sheykh zai gane cewa jini na sarauta na gudana a jikinshi, zai kuma gane nitsuwa ta addinin musulunci da kamala da haiba na hasken imanin ya game jiki da zuciyarshi.

A haka suka jera suna tafe, suna hira wacce ?arfinta duk Haroon ke yinta.
Suna tafiya kaWan.

Nan suka samu wasu irin zafafan tsala-tsalan motoci masu masifar kyau da tsada, suna jere a ?alla sun kai goma sha biyu, motocine masu azabar kyau da sabunta da she?i da kyelli suna jere.
Kana ga kekkyawa fararen larabawa yan uwa da abokai
Da sauri suka rinka Wan rusunawa suna, gaidasu Sitti da jikokinta, wani cikinsu ne da yake jikin wata dan datsetsiyar mota ?irar Mercedes Benz maybach Exelero wacce kuWinta zai kai kimanin $8 million dollars.
Motace mai masifar kyau da tsada, tana da in?ancin da ko bilet baya shigarta. Bisa dukkan alamu kuma sabuwa ce dal.
Direban dake jingine da ita ne yayi maza ya budewa Sitti bayan ta, a hankali suka ?araso gaban motar gaba Waya ma'akatan sunyi musu ?awanya, cikin so da ?aunar jikokin nata, ta yiwa Sheykh nuni daya fara shiga, ba musu kuwa ya shiga, motar, kana itama ta shiga sannan Haroon ya shiga, ya zamana sun sata a tsakiya,
Jannart kuma gaba ta shiga gefen drivern, suna gama shiga aka maida ?ofofin motar aka rufe.
Kana duk sauran hadiman suka shishiga motocin.
Kana suka fara tafiya a jere-a jere, tafiya sukeyi cikin salama da nitsuwa da bin doka da ?a'idar tu?i, kai tsaye suka wuce tushen ahlin nasu.

Wanda kafin su zoma, duk labarin zuwansu ya riski al'ummar family, kamar yadda aka saba, haka aka shirya musu tarba ta musamman an gyara sashin na musamman wanda nanne masaukin Sitti asali kuma sashin mahaifiyartace, anan cikin sashin kuma duk ahlinta da zaizo daga ?asar Kautal nanne masau?inshi, kuma kullum hadimai da bayin dake kula da wannan wurin suna nan suna tsabtace wurin. Suna isa fadar mai darar Sheikh Aliyu da kanshi ya fito tarbar babbar yayarshi wacce take a madadin uwa a gareshi a yanzu.

A wani falo da yafi dacewa da a kirashi al'jannar duniya, suka haWu, a hankali Sheykh Aliyu ya Waga hannunshi alamun dakatar da ko wanne hadimi, a tare suka rusuna tare da komawa baya gaba Waya su.
Da sauri ya karaso gaban Sitti Ruggumeta yayi irin ruggumarsu ta jinin larabawa,
murmushi mai cike da jin daWi ?auna haWida bege Sitti tayi tare dasa hannunta tsakiyar kanshi tace.
"Masha Allah, Wan uwana na sameku lfy?".
Saketa yayi tare da ruggume Sheykh yana murmushi tare da cewa.
"Alhamdulillah yar uwata, Barka da zuwa lfy".
Cikin kula da za?uwa tace.
"Yaya jikin Baba".
Murmushi ya kumayi still yana ruggume da Sheykh yana shafa bayanshi, yace.
"Alhamdulillah jikin baba da sau?i kewarkice tafi damunshi".
Sai kuma ya kalli Sheykh bayan ya sakeshi yace.
"Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero, barka da zuwa Doctor, ya gida ina Jafar da ?annenka".
Cikin son dottijon Sheykh ya Wanyi wani Wan guntun murmushi wanda shima sai yayi tsawon lokaci bai yishiba, cikin sassanyan murya yace.
"Suna lfy, sun gaidaka".
Haroon ya tura baki tare da cewa.
"Wato mu ko ?ar ruggumar ma ta zumunci baza'ayi manaba, dan mu mun dade, nima zamu koma ?asarmu mu rin?a kawo muku ziyara jifa-jifa dan naga ba?i farinjini garesu a ahlinmu".
Dariya sukayi baki Wayansu,. Yayinda duk mgnar da sukeyi da harshen larabci sukeyi.


Wani faffaWan corridor mai girma suka ratsa, wanda suka riski wani babbanshi na musamman, inda gaba Waya yayan family suke nan zaune dan mahaifin nasu a tsakiyarsu.
Wanda yake tsakiyar gatan duniya, farin dattijone wanda tsabar tsufa har ya juye ya koma tamkar ?aramin yaro, ya ?an?ance, yana hango Sitti, ya rin?a sakin murmushi tare da mi?a mata hannunshi alamun tazo.
Da sauri ta nufi inda yake su Sheykh na biye da ita a baya, yayinda duk sauran mutanen ketayi musu barka da zuwa.
A gaban tsohon ta rusuna, tare da sunkuyowa, hannunshi ya saka bisa kanta yana jero mata addu'o'in da sanya mata al'barka, ita kam sitti da sauran ?annenenta wanda a ?alla sun kai arba'in sai Amin Amin suke amsawa,
Koda ya gama da Sitti jawo Sheykh yayi ya manna kanshi da cinyarshi,
Shikuwa Sheykh. Motsoshi yayi da kyau Cikin wani irin mashahurin daWin da sai in yana gaban tsohon nan yakejin daWi yasa hannunshi biyu ya kamo hannun dattijon ya Waura tsakiyar kanshi kana ya ?ara manna kanshi da cinyar tsohon tasbihi yakeyiwa Allah mai rayawa mai kashewa.
Ya sani shi kanshi da macece shi da yanzu yanada ya budurwa amman gashi wai a gaban kakan mamanshi, ga kuma kakar tashi da sukewa kallon tsohuwa itama gata gaban mahaifinta wannan abu shine abu Waya da yake sashi kuka muddin yana gaban tsohonda kullum in yazo irin gaisuwar da sukeyi kenan.
Shi kuwa Sarki Abdulkareem cikin rawan jiki irin na tsoffi yake shafa kan Sheykh tare da kallon taron ahlin naahi cikin muryarsa da bata fita sosai yasa suke san?ala mishi na'urar Waga sauti a jikin alkyabbarsa, shiru sukayi gaba Wayansu suka dakata da ruggume-ruggumen da sukewa Sitti,
Cikin rawan muryan da alamu tsohon kuka yakeyi a hankali yace.
"Ku bashi dukkan kulawarku, domin yana cikin Magauta, yanada tarin ?unci da ?una a rayuwarshi, matsalolin rayuwar duniya sun mishi ?awanya, saukinshi Waya Allah yayi mushi dafa'i da hasken imani da ri?o da ibada, damuwar tana da?ushe duk wani farin cikin rayuwarsa rashin fara'a ba izza bace damuwace, yana cike da al'hinin kula da ahlinshi,".
Shiru ya Wanyi tare da zubawa gaba Waya ahlin nashi idanu, sawon wasu da?i?u shiru falon babu sautin komai sai sassanyan sautin shesshe?an kuka da Sheykh a hankali, sai kuma sautin ?aran A/C.

A hankali Dottijon yaci gaba da cewa.
"Kanshi akwai wani abu mai girma a tare dashi, yanada manyan baiwowi a jikinshi, sai dai kuma akwai tarin ?alubale, zai Wauki nauyi da yawa a kanshi".
Ya ?arishe mgnar yana shafa tattausan suman Sheykh.
Shiru sukayi baki Wayansu Sitti kuwa Hannu tasa bisa haSar Sheykh tana share masa hawaye, Haroon kuwa Umaymah ya kira tun shigarsu tana jin duk kalaman kakan nasu haka yasa taketa kuka.

Sosai yayi jawabai masu ratsa zuciya kafin daga bisani, ma'aikatan gidan suka shigo suka rin?a gabatar musu da abubuwan ci da sha a nan suka zauna ana Wan ciye-ciye da taSa hira,
Ganin lokacin salla yayine kab kowa ya mi?e dan yin al'wala su tafi harami.

Kamar koda yaushe Sashin Sitti suka wuce wanda yake a gyare, Jannart da Sitti side Waya suka shiga.
Haroon da Sheykh kuwa Side Waya suka shiga.
Ruwa suka Wan watsa sannan duk sukayi al'wala suka fito suka kimtsa cikin manyan alkyebbars masu taushi da masifar kyau wanda sabbine dal akazo aka shirya musu a drower'n. Koda suka gama a tare duk mazan suku tafi Harami.



Haka dai rayuwa tai ta gudana a cikin kwanakin nan.

Randa suka cika kwana uku da zuwa a ranar ne Sitti ta samu mahaifinta da ?aninta a kan batun tana son kafin tabar ?asar nan ayiwa Sheykh aure, ta kuma bada zaSin yaran yan uwa wanda suke larabawa, nan take kuma Sheykh Aliyu da kanshi yace ya bawa Sheykh Jabeer auren diyarsa Jazrah...

Rugar Bani ?adamaya state.

Yau kusan kwanan Shatu biyar da dawowa hutu, kuma kullum da salon da Ba'ana yake zuwar mata dashi, wannan abu shine abinda yafi tada hankalin Malam Liman Bappa kenan, wanda yana yawan tattauna matsalar da Ardo Bani kamar yadda yanzuma haka suke tare su daddatawa biyar,
Cikin kamala da harshen fillanci ArWo Bani yayi gyaran murya tare da cewa.
"Koda Hashimu ya rasu, in sha Allahu bazamu zuba ido a aurawa Shatu wannan fasi?i fajiri mushirkin

9 / 72