Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   32 / 72

93K to 96K   out of 214K words

zancen da cewa.
"Zan datse miki harshe, kika kuma zagar mana uwa".
Cikin tsananin tsana ta watsawa Jalal harara tare da cewa.
"Zaka aikata! Babu musu! Menene Wan giya bazai iya yiba, menene, Wan iska Wan daba bazaiyiba, banza Wan sara suka, gwada datse min harshen ka gani, in akwai wanda zai rage da harshe a zuriyar uwarku".
Jabeer ne ya Wan taune leSenshi tare da kaWa mata yatsa kana yace.
"Kulfa, ki raba kanki da zagin mace mai daraja".
Cikin isa da ?asaita tayi wani irin dariya, kana ta mi?e tsaye, gabansu ta Wan matso kana cikin izaya tace.
"Eh daraja ko? Uhummm lallai kam, aifa sai dai mace mai daraja."
Sai kuma ta Wan ja da baya kana tace.
"Mace mai daraja ko mai zunubi, ai dai kun fara ganin sakayyar Allah tun a duniya, waya san metayiwa ubangiji, y...."
Juwairiyya ce, tasaki wani irin ?ara da yasa duk sukayi shiru.
Ita kuwa ta faWi kasa a sume alamun makaranta sun dawo.
Ganin haka yasa Jakadiyarsu tayi kanta da gudu.
Ita kuwa Gimbiya Saudatu murmushin jin daWi tayi tare da cewa.
"Haka dai. Duk a haka zaku ?are, mulki kuwa sai dai ku ga anayi, GARKUWAN da aka bakanma, zakaga me zai sameka dashi".
Tana faWin haka ta juya ta nufi hanyar fita Hadimanta na biye da ita a baya.
Shi kuwa Sheykh Jabeer murya ya Wan Waga a hankali yadda zata iya jinshi yace.
"Babu abinda zai sameni face dama Allah ya ?addara zai sameni, domin baki isa ki cutar daniba".
Cikin harshen fillanci tace.
"A laran ai, zaka gani ai".
Bai kulataba.
Ita kuma fita tayi.

Jalal da Jamil kuwa, zama sukayi gefenshi, suna mai bin kofar fita da ido.
Haroon kuwa cikin rudu da Waure war kai yake mgnar zuci.
shin wai wannan wacce iriyar fitinenneyar masarautace, mai cike da tsar?a?iya, yanzuma dama a irin wannan yanayin Jabeer ke rayuwa da ?annenshi da yayanshi da mahaifanshi.
To meyasa, bazasu bar musu masarautarba, tunda shi Jabeer bama son wannan mulke-mulken yakeba.
Sassanyan zazza?ar Muryar Sheykh Jabeer ne ta katse mushi nazari, jin yana rere karatun Alqur'ani cikin nitsuwa yake, karanta fatiha.
Bayan ya kai ?arshenta ya kuma yi bisimilla, ya fara Suratul Baqra, wanda yakeyi da Wan ?arfi, tare da fuskantar inda Juwairiyya ke kwance,
Yanayin karatun cike da ta?awa da kekyawan tajwid, shiyasa in ya fidda wani harafin kamarsu Khah sai kaji har ?asan wurin yana amsa amon sautin."
A hankali Juwairiyya ta fara buWe idanunta, tana mai bin karatun da takejin,
Cikin sau?e ajiyan zuciya Jakadiyarsu tace.
"Alhamdulillah Jabeer ta farfaWo".
Ta faWi hakane sabida tasan duk sansa Juwairiyya ta faWin in dai zai mata Rugyag rufe idonshi yakeyi.
Jin Jakadiyarsu tace ta farfaWo ne, tasashi, yin hamandala tare da cewa, Jakadiyarsu ta meda Juwairiyya Side Win ta, kana ya kalli Jalal tare da cewa.
"Jalaluddin kaje, ka kula da Ya Jafar, ka bashi abinci kana ka shirya shi, shirin zuwa sallan jumma'a kaima kaje ka shirya."
To sukace kana duk suka fita. har sunje bakin ?ofar fira yace.
"Jalaluddin kasa kayan mutunci".
Cikin sanyi yace.
"To". Sannan suka fita.
Kanshi ya Wan juya ya kalli, Jamil, tare da cewa.
"Ka gyara mana bedroom."
Yana jin haka ya mi?e ya nufi bedroom Win.
Shi kuwa Haroon ido ya zuwa Jabeer, sabida gaba Waya muryarshi ta tabbatar musu, yana cikin tsananin Sacin rai, kai Haroon ya jinjina ganin Jabeer yasa hannu ya janye hiramin dake kanshi, ya taune lips Winshi, kana ya rufe idanunshi, cikin ?arfi yasa hannunshi ya fara jan bakin hiramin , da yake sabo fil janshi yakeyi alamun zai yagashi.
Shiru Haroon yayi baiyi yun?urin hanashi ba, domin dama yasan za'a rina, sabida shi Jabeer wannan itace babbar alamar tsananin Sacin ransa, muddin fushinsa ya hauhawa to, yakan yayyaga abu da karfi.
Fass haka Haroon yaji sautin, yagewar sabon hiramin nan.
Shi kuwa Jabeer idonshi ya ?ara rumtsewa yanayi mai ci gaba da fatattaka hiramin.
Murmushi Haroon yayi cikin tare da fara Waukar shi video.
Yanayi dan tsokana.

A can sashin Hajia Mama kuwa, ganin shiru-shiru Jabeer bai shigo bane, kamar yadda ya saba in yayi tafiya ya dawo yakan,
Batul kuwa, ta gaza zaune ta gaza tsaye, ta ?en?esa ado da kwalliya tamkar mai zuwa gasar kyau.
A karo na barka tai ta kalli Hajia Mama, cikin za?uwa tace.
"Yakura, muje, side Winshin mana, mu duba lfy kuwa har yanzu bai shigoba."
Ajiyar zuciya Hajia Mama ta sauke, tare da mi?ewa tace.
"Muje Batul ni kaina, na banyi zaton zai kai iwar haka bai shigoba, dole akwai abunda ya tsareshi".
Da haka suka fito, suka nufi sashin Jabeer Win.

Kasan cewarta matsayin uwa, yasa sam bata da hijabi da sashin, haka yasa, sarkin ?ofar na ganinta suka rusuna tare dayi mata kirari kana ta wuce.

A falon suka samesu, zaune.
Haroon ya tasashi gaba da kallo da wayarshi, shi kuwa Jabeer, idonshi a rumtse, bakinshi na motsawa a hankali, yana maimaita, tasbihen daya zame mishi abokan rayuwa.
Kana hannunshi nata yage sabon hiraminshi.
Haroon ne ya amsawa Mama sallamarta, tare da cewa.
"Barka da fitowa Hajia Mama".
Da sauri ta ?arasa gabansu, kujerar dake kusa dasu ta zauna,
cikin tarin kula tace.
"Haroon da kai ake tafe kenan? Ya yar uwata, yaushe ka dawo?".
"Haroon lfy kuwa me akayiwa Jabeer? Waya taSa minshi? Waya taSo Wan lelen Umaymah'nshi Da Sitti'nshi?".
Cikin lumshe ido Haroon yace.
"To Hajia Mama wacce tamSaya Waya zan amsa miki, ta ?ar uwarki ko ta Wan rigimarku, mutun in yayi fushi sai yayi ta yage-yage, wannan in ya samu dama in yayi fushi ya samu ya dam?i ?ar mutane a hannunshi tabbas zai yageta, dan ko namiji da kyar zai iya ?watar kanshi".
Murmushi mai cike da kulawa tayiwa Haroon kana,
ta kalli Batul da zauna gefenta, ta zubawa Jabeer idonu tamkar zata cinyeshi Wanye,
wani irin sonshi da ?aunarshi takeji, jiki da zuciyarta,
Kekyawan sumar kanshi ta zuwa, idanu a hankali ta dawo da idon kam tattausan sajen da yayi fuskarshi ?awanya, har kan gashin gemunshi da ya kai kamu Waya, yayi ba?i sitib dashi ya konta lib sai she?i yakeyi, jajayen laSSan bakinsa, da suke motsawa ne ta zubawa kwayar idanunta.

Shi kuwa Sh?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? eykh Jabeer, sanadin tasbihin da yakeyi ne, yaji zuciyarshi tayi fes,
fushin da yakeji duk ya kau. A hankali yakejin tsikar jikinshi na amsa sautin yam-yam tana sanar mishi ana kallonshi.
Yun?urowa yayi ya tashi zaune, kana a hankali ya fara buWe idanunshi.
Da sauri ya kauda ?wayar idanunshi sabida ganin kwayar idanun Batul cikin nasa,
Hajia Mama kuwa, cikin sanyi tace.
"Innallaha ma'assabirin".
Idonshi ya kuma lumshewa, wannan abu shike ?ara sashi jin ?arfin guiwar zama cikin masarautarsun. Sabida yayi dace, da uwar da take ?ara bashi tarbiyar da yasan itace dai-dai tana danne dukkan ba?in cikinta, domin ta sama mishi nitsuwa. Duk da kasancewar shi malami.
Tana ?ara nusar dashi.
A hankali yace.
"Barka da safiya Mama".
Murmushi tayi kana tace.
"Barka dai, Muhammad Jabeer. Garkuwa mai nagarta,
Yau na tashi da tsantsar farin ciki , tunda maji muryarka da asuba, meya Sata maka rai daga dawowa?".
Cikin sanyi yace.
"Babu komai Mama, Sheykh Abdulkareem, da ahlinshin duk sun gaisheki".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Tsoho mai ran ?arfe, kakanmu bawan Allah, yana lfy ko?".
"Alhamdulillah". Yace mata, yana mai sa hannu ya Wauki hular da Jamil ya ajiye a kusa dashi ya Waura a kanshi, sabida wani irin kallo da yaga Batul nayiwa suman kanshi.
Ita kuwa Batul ido ta Wan lumshe, ganin yadda ya tam?e fuskarshi ya watsawa gefen da take kallon, ?asaita.
A hankali ta buWe idonta kana ta sau?esu kan sajenshi,
Wani gajeren tsaki yaja,
tare da kauda fuskarshi.
Ita kuwa Butul mgnar zuciya takeyi.
"Masha Allah, Ya Jabeer, komai kayi kyau kakeyi, ya Allah ka tabbatarmin da mafarkina mana, wannan kekkyawan bawa naka ya zamo mijina, domin shine mijin daya dace dani, mijin kece raini da nunawa sa'a, Uhumm jin kai da ?asaita ba, kayi naka, kafin ka shigo hannuna, in sha Allah, sai na zama sarauniya ka zama bawana."
A hankali tace.
"Ya Jabeer ina kwana".
Shiru yayi kamar bai jitaba,
Allah ya sani ya tsani kallo a rayuwarsa ta duniya, baya kuma son mace, da rashin kamun kai.
Hajia Mama kuwa ganin yadda ya takurene yayi kici-kici da fuska, yasa ta Wan, kalleshi tare da cewa.
"Jabeer Batul ke gaidaka, itama jiya tazo".
Kanshi ya Wan rusunar tare da mi?ewa tsaye, cikin sanyi yace.
"Masha Allah".
Daga nan ya Wanyi taku biyu zuwa uku, kana yace.
"Mama barin inje inyi shirin jumma'a".
Murmushi tayi tare da cewa to. Dan ta fahimci zillewa yakeyi.

Daga nan shi dai yayi, ciki.
Su kuma suka, fita.

Haroon kuwa Data ya kunna,
Umaymah ya turawa video Win da yayiwa Jabeer da yana cikin fushin.


A can Rugar Bani kuwa, yau tun safe, su Shatu suka baro asibitin, sabida, matasan maya?an cikin garin Shikan Win sai kai komo sukeyi, cikin asibitin. kana sai zuwa sukeyi maja'iunsu, suna mitin.
Bisa dukkan alamu, sunada wata manufa, ganin hakane, yasa likitoci musulmai, suka bada shawarar a kwashi marasa lfyar a medasu cikin asibitin babban birnin ?adamaya, sabida su nan babban likitansu ya hanasu duba kowa.

Da wannan shawarar ne, aka kwashi duk marasa lfyan da taimakon yan agaji aka shiga dasu cikin Adamawa.
Dan an fara rade-raWin wai fulanin Rugar Bani sunce zasu Wauki fansa, to shisa ?abilar Sachama suma suketa guzurutsoma, har ta kai da matakin in dare yayi matasan hausa fulani na cikin garin ma zauna cikin garin Numan, sai su futo suyi ta yawo da makawai suna kare amguwanninsu.
Kana suma ?abilar Sachama sai su fito da makamai suna kare amguwanninsu.

Shatu kuwa basu wuce cikin ?adamaya ba, sabida Ummiy ta dawo hayyacina ta, hakama Junainah ta dawo haiyacinta da ?arfin addu'o'in da Aysha da Bappa keyi.
Dan haka su cikin Rugarsu-suka koma.

Shatu kuwa, tunda Junainah ta gaya mata batun Sacewarsu Ya GiWi da kuma kashe ya Lado da akayi, har zuwa yanzu bata daina kukaba.

Koda Ba'ana yazo wurinta daren jiya, da yaji lbrin sun dawo babu abinda takeyi sai kuka.
Shi kuwa Ba'ana, ba?in cikinsa shine da Ummiy ds Junainah da Bappa suka rayuwa,
Shiyasa yanzu, yayi musu nasu shirin mutuwa namu samman.

Inda Bugulu Maman Ma'ans ta gasa zabbbin da Ba'ana ya yanka, kana ta daka musu, yajin borkono, da busasshen kan maciji.
Ta barbaWa musu, kana ta yaryaWa man shanune da ya gauraya da dafin macijin cikin man shanun da tayi musu gashin dashi, kana ya nufi, bakin garkensu, da akoshin gasassun zabbin.
Sannan ya aika aka kira mishi Shatu,
cikin kuka Rafi'a tacewa Wan aiken yaje, ya zazzaSi ke damunta.
Koda yaron yaje ya gaya mishi,
sai yace zai a kira mishi Junainah,
Koda yazo ya gaya musu,
Sai Junainah ta mi?e tabi bayan Wan aiken.
Kasan cewar garken nasu ba nisa, tafiya kaWan tayi ta isa, ta isa ta zauna a bakin ?ar bukkarsa da yake, cikin.
cikin disashewar muryar hawaye na zuba tace.
"Ya Ba'ana, kaje ka dubo jikin Ya Junaidun ne?".
Juyowa yayi ya fuskanceta da kyau, cikin sanyi yace.
"Eh naje na dubashi, jikinshi da sau?i, ke ya naki jikin? Ya Ummiy da jiki".
Cikin sanyi tasa hannu ta share hawayenta dake shatata kana a hankali tace.
"Ummiy jikinta da sau?i sai dai har yanzu bata mgn, Adda Shatu kuma sai kuka takeyi".
Hararanta yayi a fakaice, ji yake kamar ya jawota ya caka mata mashi ya mata kisan zahiri sai kuma ya fasa,
Kanshi ya kauda tare da tura mata akoshin gasassun zabbin nan kana yace.
"Ayyah sannu Junnuna, kiyi ha?uri dena, kuka, kici nama, sai kije kicewa Mata, tazo zan gaya mata inda su ya GiWi suke".
Cikin rawan jikin jin yunwa tace.
"Yauwa bani inci dama yunwa nakeji, tun jiya banci komaiba, tunda muka dawo, bamuyi girkiba."
Da sauri ya turo mata akoshin tare da buWe mata fefeyin.
Cikin rawan jiki irin na masu jin yunwa tasa hannu ta...!



Uhummm Allah kaimu gobe lfy, mu ?ara sa free page, daga PAGE 15-16 an gama.






By
*GARKUWAR FULANI*
=???
=??=?J?????=?
?>?4?
*GARKUWA*

PAGE 15

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

=??????>?4?

*Littafin GARKUWA na kuWine, daga wannan PAGE 15 da 16 FREE PAGE sun ?are, turo katin mtn na Wari uku kacal ta wannan number 09097853276, ko ki turo dubunki Waya rak dan shiga Special Group, wanda anfi yawan posting, ta wannan asusun zaki turo 1k Win 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853276.*

```Dan Allah da Manzonsa da darajar iyayenki in dai kin san kin sayi littafina ne ko zaki sayane Wan ki fitar min dashi na ro?eki da Allah da Manzonsa=?O?

Akwai kayyakin gyara namu mata setin amare da masu jego, da masu kwaskwarima, idan kina bu?atar saya ko sari, tuntuSi wannan number tawa 09097853276.


Hannu tasa ta jawo pepeyin jin yana ce mata.
"Kici kije da gudu ki kira Mata, tazo in gaya mata, su Ya GiWi sun kusa dawowa ta dena kuka, anji lbrin inda suke".
Rufe akoshin tayi kana ta mi?e da sauri tace.
"Da gaske ya Ba'ana an ji inda suke?".
Cikin haWe fuska yace.
"Na taSa yimiki ?arya ne?".
Da sauri ta jujjuya kanta kana tace.
"Bari inje in gaya mata tazo sai inci naman a gida".
Da sauri yace.
"A a jeki kirata, in tazo sai ki tafi da naman, kije kuci keda Ummiy da Bappa da ita ?awar Mata, ita kuma zan bata nata a nan".
Ai tana jin hakan ta juya ta tafi, da sassarfa.

Tana isa gida, ta kamo hannun Shatu, cikin haki tace.
"Adda Shatu taso, taso muje ya Ba'ana zai gaya miki inda su ya GiWi suke, yace anji lbrinsu".
Wani irin zabura tayi, hakama Rafi'a dake bakin ?ofar kitchin Winsu.
Cikin tarin kaWuwa tace.
"Ke Junainah, kada kiyi mana ?arya".
Cikin haki tace.
"Wallahi tallahi, haka yace min zo muje kiji".
Da sauri ta kamo hannun Rafi'a tace.
"Adda Rafi'a kema zo muje tare".
Cikin jin daWi Rafia tace.
"A a Junainah kuje, Ni kuma kafin ku dawo nayi mana abinda zamuci, da sauri tace.
"A a Adda Rafi'a ki bari kar kiyi girki, Innar ya Ba'ana ta aiko mana gasassun zabbi yanzu zan amso mana su sai muci".
Murmushi tayi kana tace.
"To sai kinzo".
Ita kam Shatu tuni ta fita, ta nufi Garkensu Ba'ana.

Ita kuwa Ummiy ido kawai ta zuba, musu tana son ta kira Shatu ta hanata zuwa amman ta kasa.

Ita kuwa Rafi'a kitchin Win ta shiga.

A can garkensu Ba'ana kuwa.
Yana hango Shatu, ya saki wani irin ajiyan zuciya, ido ya zuba mata,
Gaba Waya ta rame tayi fiyau da ita, fuskarta tayi jazir alamun yawan kuka, kana, ga kumbura da idanunta sukayi.
Da sauri take tafiya, sai dai tanayin takun a hankali ne, doguwar rigace a jikinta ta atampa, hijabi da ta saka wanda yazo mata har guiwa.
Ta Wan ja hulan kan hijabin dan ya Wan kare mata kumburarrun idanunta.
Wani zafi yakeji a ransa, Allah ya sani baya son ganin Shatu cikin damuwa duk ?a?antar-ta, yakanyi komai na zalumci, amman baya yi kan Shatu, shi kanshi ya yarda shi tantirine, azzalumi, kuma mugu, hakanan kuma ya yarda so gsky ne kuma so Waya ne tak kuma ya sani duniya ta sani yana son Shatu,
yana son sama mata farin ciki a rayuwarta, yana son su rayu tare. Shiyasa yake son rabata da kowa nata wanda suke ?o?arin ganin sun hanasu Kasancewa mata da miji.
Wani farin buzu ya shimfiWa mata a bakin ?ar bukkartasa, tun kafin ta ?ara so.
Tana isowa, murya can ?asa tace.
"Assalamu alaikum."
Ido ya zubawa fuskarta cikin tausayawa yace.
"Mata ki zauna". Murya a disashe tace.
"Ya Ba'ana ka amsa sallamar mana".
murmushi ya Wanyi kana yace.
"Mata na amsa bakijini bane".
A hankali ta zauna bisa buzun, cikin sanyi ta lumshe idonta da takeji sun tsastsafo da zafafan hawaye, murya na rawa tace.
"Ya Ba'ana, wai anji lbrin su ya Gaini?".
Matsowa yayi bakin bukkar, ido ya Wan zubawa fuskarta, sabida lumahe idon da tayi batasan yana kallontaba ganin hawayenta na zubowa ne yashi yin mgna, a hankali yace.
"Mata, kiyi ha?uri, ki kontar da hankalinki, in dai yayunki suna raye, zan nemisu, ko dan farin cikinki, ki bar kuka Mata, bana son ganin hawayenki inajin ?una a raina".
Ya ?arishe mgnar murya can ?asa.
Cikin rawan murya tace.
"Ya Ba'ana, ya zanyi? Ina zansa raina in ji sanyi, zuciyata tana ?una, Yayuna huWu kab na rasasu lokaci Waya, bani da wa wanda zan nuna a faWin nahiyar nan ince ga wani na a duniyar, babu ya GiWi, wanda shine tamkar aboki ?awa aminiya, abokin faWata abokin dariyana, Babu ya Seyo, yaya mai kamar uwa, sabida yawan tausayinshi da nuna ?aunarshi gareni, ko uwa iya abinda zata nunawa Wanta kenan, babu ya Gaini da yake tamkar uba, babusu babu gawansu babu lbrinsu.
An kashe min ya Lado da yake GARKUWA a gareni.
Ya Ba'ana, ya zanyi in banyi kukaba, Ina zan fara nemansu, Ni macece inada rauni, ta ina zan nemosu? An kashe mana Innarmu".
Ta ?arishe mgnar tana mai kife kanta bisa guiwowinta ta saki wani irin kuka mai tsuma zuciya, cikin kuka taci gaba da cewa.
"An kashe Inna, sanadin haka Ummiy na ta zama tamkar zautacciya, duk gidan dake cikin Rugar Bani babu gidan da ba'a kashe a ?alla mutun biyarba a ?aramin kari, suwaye ne ya Ba'ana, me mukayi musu? Me suke nema damu? Me muka tsare musu? Me laifinmu dan mun kasance Fulani makiyaya?".
Karon forko a rayuwarsa da yaji rauni har ta kaishi ga zubda hawaye, koda yake raunin soyayyace, cikin zubda hawaye murya na rawa yace.
"Mata gani, zan zame miki madadin uwa, uba, yayunki, Inna, zan zame miki Garkuwa, in sha Allah bazan bari ki cutuba, zan bada raina domin kare naki, zan nema miki farinciki da dukkan abinda na mallaka na duniya, zan zame miki adalin miji, Mata ki dena kuka, kiyi ha?uri".
Cikin shesshe?an kuka ta Wago kanta, ta zuba mishi ido, tabbas kuka yakeyi kamar yadda ta zata, cikin mamaki tace.
"Ya Ba'ana meyasa kake kuka?".
Hannun yasa ya sharce hawayenshi, karon forko a rayuwarsa

32 / 72