Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   55 / 72

162K to 165K   out of 214K words

na Musulmin ?warai ba.
Aunty Juwairiyya Hibba Ummi Ke uwar bacci".
Ya ?arishe mgnar da kallon gefenda Shatu da take zaune tana Wan lullumshe ido,
da sauri ta waresu don a sama taji muryar tasa. Baki ta tura tare da sunkuyar da kanta, shi kuma jenye idonshi yayi daga gefen da take cikin Wan Waga sauti yace.
"Watan Ramadan ya bambanta da sauran watanni.
Domin a cikin watanne daren laylatul ?adir yake, kuma a cikin watanne Allah ya sau?e al'?ur'ani mai girma.
Kana a cikin watar akwai ranakun da malamai sukeyi hasashen a daren laylatul ?adir yake, Daren 21, 23, 25, 27, 29. Sai dai ba'a tabbatar, da sahihin rana Waya tsayeyye ba ?auli mafi rinjaye shine ranar 27.
Abi mafi kyau shine kada mutun ya sake koda dare Waya na Ramadan ya wuceshi.
Mu raya dararen da ibada da ambaton Allah, wajibine mutum ya tsare bakinsa, da munanan zantuka walau a baki walau a rubuce a social media,
Domin mu ribanci watar da ambaton Allah da samun ruSanyar lada, wannan abubuwane da kullum nake gaya muku su, sai dai aiki dasu ya gagareku."
Kusan haWa baki sukayi wurin cewa.
"In Sha Allah zamuyi ?o?arin kiyayewa".
"Allah yasa yace, tare da sallanmansu duk suka fita sai Ya Jafar da Ummi.

Ganin yadda Hibba keta zuba hamma ne ya sashi cewa.
"Muhibbat tashi
Kije ki kwanta".
Kusan a tare ta mike ita da Shatu.
da sauri yace.
"Banda ke". Cikin bacci ta turo baki tare da cewa.
"Ayyah dan Allah fa".
Murmushi Ya Jafar yayi tare da zuba mata ido.
Wanda koda baya mgna ana iya gano yadda yake sonta a ranshi, so kuma irin son da yakeyiwa su Hibba.
Ummi ce ta Wan kalleta tare da cewa.
"A barta tai bacci aiki mukeyi tun Wazu".
Shiru bai kulasuba, ganin haka ita kuma tabi bayan Hibba.
A zatonta bai saniba, har sunje bakin ?ofar taji yace.
"Saura ki bin?ire kiyi ta bacci, kada ki tashi ki raya daren. Sai gari ya waye ki buwayi mutane da ife-ife da rashin kunya".
Ya ?arishe mgnar cikin jin haushinta tare da Binta da kallon fitinenneyar yarinya.

Ganin Ya Jafar ya mi?a ya juya zai fitane yasa yayi saurin.
Bin bayanshi ya rakashi kana ya dawo ya konta.

Ummi ma ta konta.

?arfe Waya da rabi Sheykh ya tashi yayi ta nafilfilinshi tare da jere addu'o'in da neman warakar damuwar rayuwarshi data ahlinshin.

Ummi ma tuni ta tashi. ?arfe uku ta fito.
Falon hango haske a Wakun Shatune ya tabbatar mata sun tashi.

Kitchen ta wuce. gas ta kunna ta Wumama musu miyar, kana ta haWa plate spoons and cups tazo ta jere bisa Dinning table.

Sannan ta koma kitchen ta Wauko musu drinks and water masu sanyi tazo ta jere komai yadda ya dace.

Kana ta dawo falon ta zauna ri?e da carbinta.
?arfe huWu dai-dai su Jalal suka buga ?ofar sanin sune yasa, ta tashi ta buWe musu.
Suna shiga ana buga bindigar sanarda mutanen masarautar JoWa cewa lokacin sahur yayi.
Bayan mintuna talatin kuma za'a kuma sakin bindingar.


Cikin gudu Shatu ta fito falon jiki na rawa, kiciSis tayi da Ummi da takeda niyar zuwa ta ta kirasu suzo suyi sahur.
Ruggume Ummi tayi ?am-?am tare da neman inda zatasa ranta.
Allah ya sani tana tsoron ?aran abu biyu, ?aran aradu da wal?iya da kuma ?aran harbin bindiga".
Cikin mamaki Ummi tace.
"Oho Aysha duk wannan tsoron na ?aran harbin bindiga ne, lallai kuwa in baki sababa kafin Ramadan ya ?are zakisha wuya."
Hibba ce ta fito tana dariya tace.
"Allah ko Ummi ana Waukan alha?in Aunty Aysha".
Babban Falon suka nufo yayinda duk jikinta ke karkarwar."
Dinning area Suka wuce.
Bayan duk sun zaunane Ummi tace Hibba tasa musu abinci.
BuWe kulolin tayi.
Jolof Win taliya da kifi Aunty Juwairiyya tayi, sai kuma
Flaks Win kunun gyaWa.
nasu kuma tuwon semo da miyar Wanyar kuSewan sai tea da sauran kayan sha.
Ta zubawa kowa abinda ranshi keso.
ita dai Shatu mamakin abincin Aunty Juwairiyya na yau takeyi sabida idonta bai gano mata wani mugun abu a cikiba.

Haka yasa itama shi taci. Da kunun.
duk sunyi nisa a yin sahur Win. Amman shi bai fitoba,
Sai ?arfe huWu da rabi ya fito.
A hankali ya iso Dinning area Win gaban washing hand Baby ya Wan tsaya tare da wonke hannunshi.
Ita kuwa Shatu tana ganinshi ta Wanyi gyatsa tare da cewa.
"Alhamdulillah kana ta mi?e".
Kujerar dake gefen Jalal ya zauna,
Yana zama ita kuma ta juya ta nufi cikin falon.
Shi bai ma kalli inda takeba.
Cikin falo ta koma hannunta ri?e da cup Win kunun da take sha.
Cikin kula Ummi tace.
"Sai yanzu?".
ta ?arishe mgnar tana zuba mishi tuwon semo da miyar Wanyar kuSewar da yaji nama da kifi da man shanu.
gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"A jinkirta sahur a gaggauta buWa baki Ummi Manzon Allah yace."
Murmushi tayi tare da cewa.
"Hakane".
Bismillah yayi tare da gyara zaman shi, ya fara cin abincin.
yaci mai Wan yawa dan daren jiya baici komaiba.
tea ta haWa mishi.
Hannunshi ya wonke kana ya amshi tea Win ya fara sha.
Jalal, Jamil, kuwa ci sukayi sukayi hanin?an kana suka mi?e zasu tafi.
Cikin kallonsu yace.
"Kadafa kuje ku kwanta, kuyi al'wala ku wuce masallaci."
To sukace kana suka tafi.
Shi kuwa yana gama yin sahur Win ya koma Side Winsa,
Wonka yayi tare da al'wala kana yayi shigarsa ta farar jallabiya.
Bayan sun idar da salla gari ya Wanyi hasken ya taso ?eyansu, suka dawo gida.

Side Win su suka wuce. raka Ya Jafar yayi har Side Winsa kafin yazo ya shiga sashinsa.
Shiru falon babu kowa, bisa alamu kuwa tuni Ummi ta kimtsa ta share da goge ko ina, ta sassake labulaye, tare da sa turaren wuta mai ?amshi.
Kana ta kashe hasken ko ina, babu abinda ke tashi sai ?amshi da sanyin A/C da karatun Alqur'ani mai girma da kuna.

Falonshi ya nufa yana shiga,
ya zauna a falo, Dua Azkar ya fara yi cikin zazza?an muryarshi.
Bayan ya isane kuma ya fara karatun al'?ur'ani. Sai bakwai da rabi dai-dai ya shafa addu'a kana ya wuce bedroom Win shi.
Wutan ya kashe tare da ?ara ?arfin gudun AC.
sannan ya nufi luntsumemen gadonshi ya kwanta bisa gefen damanshi tare dasa hannun ya jawo blanket ya rugu.
A hankali lips Winshi ke motsawa, alamun tasbihi yakeyi.
Cikin 13 minute bacci mai daWin gaske ya kwasheshi".

Haka can wurinsu Shatu ma, saida tai karatun al'?ur'ani sosai kafin ta konta hakama Hibba.

Ummi kuwa wonka tayi tayi al'wala ganin bakwai ta wuce ne tayi walahan ta raka biyu.
Kana tayi karatu sai ?arfe tara da rabi ta konta take kuwa bacci yayi awon gaba da ita.


?arfe goma dai-dai ya tashi daga baccin da yakeyi.
Wonka yayi tare da al'wa kana ya fito ya kimtsa cikin shiga ta al'farma. Turare mai Wan sanyi ya fesa kaWan kana.
Ya Wanyi tafiya kaWan zuwa gefen Bedside drower'n dake tsakanin gini da gado, wanda akwai tazarar fili mai Wan faWi ana yake shimfiWa sallayarsa wurin ya zama keSantaccene.
Walaha, yayi raka biyu kana yayi addu'o'in yau da kullum ya shafa, mi?ewa yayi ya Wauki System Winshi ya ri?e a hannunshi, kana ya Wauki woyarshi Waya cikin su huWu da suke bisa Bedside Win.

A hankali yake taku, har ya fito tsakiyar falon. Shiru gidan tamkar babu mai rai a ciki.
A haka ya buWe ?ofar ya fita, tare da ja musu ita ta baya.
Koda ya fito asalin farfajiyar masarautarma ko ina shiru kakeji, sai Wan zirga-zirgan fadawa da hadimai masu tattara Wan sharan dake ko wanne bakin part.
Suma kowa a hankali yake aiki alamun akwai bacci tare dasu.
Motarsa kirar Tolls Royce, wacce kuWinta zai iya kai kimanin Billion 4, 959,630, naira. Baba Lado shine Drevernshi da sauri ya taso yana suka tafi.
Daga nan masallacin jumma'a na kasuwa ya wuce.
Sha Waya saura ya isa, inda ya samu tuni masallacin ya cika yayi ma?il da al'ummar Annabi maza yara da manya tsoffi da tattawan, yan kasuwa sun cika sunyi ma?il iso warshi kawai dama ake jira.

Motarshi na gama tsayuwa yan agaji suka rufa mishi baya, babban cikinsu ne ya buWe mishi marfin motar tare da Wan rusunawa yace.
"Barka da safiya Malam".
Cikin tsananin kulawa Sheykh Jabeer ya kalli dottijon da ya kai ya haifeshi.
Hannu ya mi?a mishi tare da cewa.
"Barka dai Baba Sule Ya ibada".
Cikin jin dadi yace.
"Alhamdulillah".
Sai kuma ya kalli sauran wanda yawanci bazasu wuce sa'annim ?aninshi mai binshiba Affan kenan,
Murmushi yayi tare da basu hannun yana mai tuna cewa tabbas da Affan yana ?asar nan To bana a ?adamaya zaiyi azumi, kuma ya sani da yanzu suna tare anan, dan shi ba irinsu Jalal bane.
Zagayeshi sukayi suna buWa mishi hanya yana wuce.
Ta kofar da liman ke shiga ya shiga.
sit kakeji da yake duk mazane, gashi kuma ansan ?a'idarshi shi baya son surutu in yana tabsir.
Zama yayi tare da kallon Wan agajin dake sa?ala mishi abin Waga sauti mgn a jikin al'kyabbar jikinshi.
Yayinda wasu kuma suka koma bayanshi wasu suka tsaya gefenshi, yan Waukan awazin kuma na gidajen Radio da TV duk sun kafa na'ura su a gaban table Win da yake zaune.
Bayan an gama kimtsa mishi komaine, ya gyara zamanshi tare da kallon alaramma Abdul?adir wanda shine zai jamishi ba?i.
System Winshi ya buWe tare da gyara mata zama, haka shima Alaramma Abdul?adir yayi da Qura'an Win gabanshi.

Gyara murya Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero yayi tare da fuskantarta taron al'ummar dake gabanshi cikin Wan Waga sauti yace.
"Bismillah rahmanirrahim. Assalamu alaikum warahmatullahi wa barka tuhu.
Innal hamdalillah nahmaduhu wanasta inuhu wanastagfiru wana uzubillahi min shururi am fusina wa sai'yi ati amalina. Manyahadillahu fala mudillah, famanyuddul fala hadiyala wa asshahu'alla'ila'ha'illalahu wahdahu lasheri kallah, wa asshahadu annamuhammadan abduhu warasulu.
Ya ayu allazina amanutta?ullaha ha??a tu?atil wala ta mutunna illah wa antum muslimun ya ayu hannasu ta?u rabbakum.
Kalakum min nafsin wahida, wa kala?a minha zaujaha wa bassa minhuma rijalan khasiran wa nisa'ah watta?ullah lazitasa'aluna bihi, wal'arhama innallaha kana alaikum ra?iba, ya haiyu allazina amanuta?ullah wa ?ulu ?aulan sadidah yuslahlakum amalakum wayagfirlakum zunuba kum, waman yuWillah wara sulahu, fa?adfaza fauzan azeema ambaduhu fa inna'asda?al hadisi kitabullah wa'ahsanal hadi hadiyu Muhammadin (S.A.W) wa sharal umuri muhdasatuha fa innakulla mudasatin bidi'a wa kulla bidi'atin balala wa kulla balaltun finnar."
Nufamshi ya sau?e mai Wan nauyi sabida jan dogon numfashin da yayi, kana ya kalli taron al'ummar musulmi dake zaune gabanshi manya da yara, masallacin yayi ma?il har woje.
Kusan gaba Waya taron jamar suka haWa baki wurin cewa.
"Wa alaikassalam warahmatullahi wa barka tuhu".
Kanshi ya Wan rusunar tare da ci gaba.
Gyara masa?alin abin sautin mgnar dake wuyan al'kyabbar jikinshi yayi tare da cewa.
"Alhamdulillah. Kamar yadda aka saba haWuwa a wannan masalaci mai Al'barka bana kuma Allah ya ?addara dani za'ayi.
Kamar yadda aka fara a wancan shekarar, zan Waura a kan darasin da Malam Abubakar ya fara, duba da kasantuwar mafiya yawa yan kasuwa ne, to zamuyi maudu'in bisa ha??in tauye mudu, da kuma barin salla ta wuce dan gudun cinikayya ya wuce ka."
Daga nan ya shiga cikin shirin gadan-gadan.
Yayinda gaba Waya mutane sukayi tsit suna jin nasiharsa da hujjoji da yake jawowa daga al'?ur'ani zuwa ahadisai, yana shigarsu yana ratsa musu jiki, jini, da zuciya.
Musamman dama mutane nason wa'azinshi.
Haka yasa koda lokacin tashi yayi sai suka ga kamar miti biyar sukayi ba awa Waya ba.

Yana tashi a wurin yan agaji sukayi mishi rakiya, har bakin motarshi.
Daga nan Masallacin Masarautar JoWa ya nufa.
Sha biyu dai-dai tayi mishi yana cikin masallacin
tuni an shirya an kimtsa komai yadda abu zai tafi, shiyasa yana isa shida Alaramma Abdul?adir suka fara.

A can cikin masarautar JoWa kuwa.
Dai-dai lokacin Shatu ta fito cikin Wakinta ta nufi falo.
Shiru babu kowa, haka yasa ta wuce kitchen da nufin yin wonke-wonken da sauran gyara-gyare ganin komai tsab-tsab ne yasa ta dawo falonta.
A hankali ta nufi Wakin Ummi.
daga bakin ?ofa ta tsaya tare da yin sallama.
Cikin kula Ummi ta amsa mata tare da cewa.
"Ki shigo mana".
To tace kana ta shiga, cikin sanyi tace.
"Ina kwana Ummi".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Lfya lau Alhamdulillah, amman yanzu dai ina wuni ne ko".
Cikin murmushi tace.
"Eh hakane fa, yanzu har sha biyu da rabi tayi".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Ai tunda naji Sheykh ya fara tabsir nace to rana ta tsala".
Shiru suka Wan yi tare da kasa kunne, ras muryarshi ke tashi sabida ansa amsa kuwa ta cikin masarautar.
shiru Shatu tayi tare da yin ?asa da kanta tana mai lumshe ido, Allah yasani tana masifar son tabsir Win shi, in taji yana jan ba?i sai take jinta kamar a harami take.
Ummi ce ta Wan kishin ?iWa tare da cewa.
"Gyara zamanki muji wa'azin."
Kai ta Wan Wago tare da cewa.
"Ummi naje kitchen zan mana wonke-wonken na samu an gyara komai ba dai ke kikayi aikinba?".
Cikin maida hankalinta ga sauraron tabsir Win tace.
"Nice nayi, amman daga yau Saratu zata na zuwa tanayi wanke-wanke da share-shere da yan gobe-goben da dai sauran ?an wasu aiyuka, kamar fere dankali ko doya da tsinkan ganyen ko wanke wake ko ji?a shinkarfa masa da kai markaWe, duk itace zatayi mana, mu kuwa in munyi azahar mu shiga kitchen,
zatake Wan taimaka mana da wasu aiyu kan. Amman banda girki, hadimar Gimbiya Aminatu ce, amman duk azumi nan ake bamu ita".
Cikin gamsuwa da hakan tace.
"To ba damuwa Ummi, amman dan Allah in Sata zoba, kada kice zakiyi aikin ki barshi ni zanyi".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Zama tazo, kullum da asuba ana idar da salla zata zo.
In ta gama aiyu kanta kafin ?arfe goma dai zata tafi, sai anyi sallan azahar kuma zata zo.
Daga nan kuma sai mun gama aikin buWe baki, ta tafi dana Gimbiya Aminatu da nata, sannan sai ansha ruwa anyi sallan isha'i da asham sai ta dawo tayi yan wonke-wonken da taimaka mana aikin sahur, to in ta tafi kuma sai washe gari in anyi sallan asuba ta dawo."
Cikin Wan fito da idonta tace.
"Wannan zirga-zirga haka Ummi to ta zauna anan kawai mana ta huta".
Juyowa tayi ta Wan kalleta kana tace.
"Mijinki ba irin waWannan mutanen bane, baya son a turo mishi yara suzo suyi ta zirga-zirga a kanshi, kinga duk lokutan da take zuwa basa haWuwa."
Baki ta Wan taSe tare da yin mgna a zuci.
"Kai mutun komai tsari, wannan babu shakka baida gskya ne wannan Soye-Soyen waya sanima ko cin zan-zanane a jikinshi da saWaure wata ?il shiyasa yake kima tabka-tabkan Al'kyabbar ajikinshi dan ya boye abubuwan".
Murmushi Ummi tayi dan ta lura Shatu bata san mgnar ta fito fili ba.

Shiru Shatu tayi ganin alamun Ummi na jin wa'azin,
Hakane yasa tayi shiru sabida kada ta takura mata.

?arfe Waya dai-dai na rana, akayi addu'a aka rufe taron sai kuma Goben in Allah ya kai rai.

Da yawa mutane basu fitaba,
mafi akasari Kur'anai suka Wauka suna karatu.
Kamar yadda Sheykh yakeyi.

?arfe Waya da rabi aka kira sallan azahar.

Mi?ewa Shatu tayi tare da cewa.
"Ummi bari inje inyi salla zan zo muyi wata mgna".
Cikin binta da ido Ummin tace.
"To".

Bayan anyi sallan azahar an idar ne, ta fito ta nufi Wakin Ummi, ganin bata nan ne, yasa ta nufi falo, nan kuwa ta sameta zaune bisa kujera.
g???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?efenta taje ta zauna.

Tana zama wata ?ar matashiyar budurwa ta shigo,
cikin nitsuwa tazo ta rusuna gabansu tare da gaidasu, Cikin kula Ummi tace.
"Yauwa Saratu kin zo ko?".
Cikin nitsuwa tace.
"Eh Ummi nazo Wazu bakwa nan sai na koma sai yanzu na kuma zuwa".
Kai ta jinjina tare da cewa.
"Yayi kyau,". Inda Shatu take ta Wan kalla tare da cewa.
"?iyata ga Saratu. Saratu ga Saiyada Shatu matar Sheykh Jabeer".
Cikin mamaki da dariya sunan da Ummi ta li?a mata wai Sayyada, ta kalli Saratu tare dake gaisheta cikin ladabi da biyayya,
fuska a sake ta amsa.

Cikin sanyi Saratu tace.
"Ummi me za'ayi ne?".
Gyara zama Ummi tayi tare da cewa.
"Ki wonke shinkafar masa dama na ji?ata, kana ki gyara mana ganyen alaiyahu, sannan ki fere Arish.
Sai kuma ki jajjaga kayan miya, ki yanka al'basa mai Wan yawa."
Cikin nitsuwa da bin umarni tace.
"To Ummi".
Ta ?arishe mgnar tare da mi?ewa ta nufi kitchen, tana shiga ta fara aiyukan da aka sata.

A falon kuwa, gyara zama Shatu tayi tare da kallon Ummi cikin sanyi tace.
"Ummi dama mgnar da zamuyi ko!."
Sai kuma tayi shiru tana nazari, jin muryar Ummi nace mata,
"Uhum ina jinki faWi".
Sunkuyar da kanta tayi a hankali tace.
"Uhumm dama cewa, zanyi in ba matsala a rin?a yin abun buWa bakin ana kaiwa masallacin Masarautar JoWa mana, tunda dole talakawan gari na zuwa nan sallan magriba."
Murmushi mai yelwa Ummi tayi tare da cewa.
"Allah sarki, Shatu mai tausayi, ba matsala amman ki tambayi mijinki in ya amince dai ba matsala, dama kuma ana fitar da abinci a sashin Gimbiya Aminatu, da Gimbiya Saudatu da kuma gidan Galadima, da Hajia Mama.
Da gidan Dr Aliyu da sauran duka, kuma ko Juwairiyya ma tanayi".
Murmushi ta Wanyu tare da cewa.
"To Ummi muma ai muna son ladan wannan aikin".
Da sauri tace.
"A sosai ma kuwa. Sai dai ki sanar da maigidankin in ya yarda yanzu incewa Saratu ta ?ara hannun sosai".
cikin kwaSe fuska tace.
"To Ummi shi wannan sarkin zirga-zirgan ina zan ganshi?".
Cikin yin ?asa da murya Ummi tace.
"Yana falonshi yanzu ya dawo, yana wucewa kina fitowa, jeki sameshi da sauri kada yayi bacci ya zama kin tadashi a bacci dan babu abinda yafi Sata mishi rai sama da ya fara bacci a tadashi".
Cikin juya ido tace.
"Ummi to ni me zan ce mishi?".
Murmushi Ummin ta kumayi kana tace.
"Abinda kika cemin shi zaki ce mishi, tashi kije musan yadda zamu fuskanci aikin".
Ta ?arishe mgnar tana mi?ar da hannunta, a hankali ta mi?e tsaye, doguwar rigar jikinta ta gyara tare da yane mayafinshi.
Ganin ta tsaya ne yasa Ummi cewa"
"kije mana." Allah yasani badon tana son ladan aikin ciyar da marasa ?arfi da basu abin buWa bakiba da bazata sake zuwa tambayar abu wurin wannan kurman ganganWinba, tun randa taje tana mishi mgnar yacewa Umaymah ta bar musu Hibba ya shareta take jin haushinsa in ta ganshi kamar ta Wirka mishi dundu a baya.
Muryar Ummi data kuma jine yasata, juyawa, ta nufi corridor'n da zai sadata da falonshi.

A hankali take taku, tana jin sanyin tayis Win wurin na ratsa mata ?afa,
sallama tayi a bakin kofar tare da kutsa kai ciki, tana mai murtu?e fuska.
Bisa 1 str ta sameshi zaune, da alamun waya yakeyi da Umaymah.
Dan taji yana kiran sunanta.
Gefenshi ta Wan tsaya tare da kallonshi ta wutsiyar ido.
Shi wai ko shi kaWai ko a Wakinshi shi Waya sai ya zauna da kima-kiman riguna, ganshi wata ?il basa damunshi".
Haka taketa maganar zuci, har ya gama wayar da yakeyi bata, saniba.
shi kuwa baibi ta kantaba yaci gaba da Wan aikin da yakeyi a wayar.
Jin shirune yasa ta Wan kalleshi, ganin ya gama wayar da yakeyi ne yasa, cikin dakiyar murya tace.
"Uhummm dama

55 / 72