Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   13 / 72

36K to 39K   out of 214K words

guje masane Shatu, kina son ragon mijine?".
A hankali tace.
"A a Ya Salmanu zai cutar da kaine nake tsoro".
Da sauri ya katseta da cewa.
"Babu mai rayawa da kashewa sai Allah, ko yaya zaiyi bashi da ikon kasheni sai in kwana-nane ya ?are. Ko ciwon kai bai isa ya samin ba".
Shiru tayi tana kallonshi.
Sai kuma tai maza ta mi?e tsaye ganin kamar daga sama aka jefo Ba'ana gabansu.

Kallon kallon sukeyiwa juna shida Ya Salmanu, cikin wani irin mugun kallo mai cike da mugunta yayi kwaffa tare da cewa.
"Uhummm Salmanu manyan gari, wato har an samu wani mai yar guntuwar jarumtar da zai iya haWa so dani a kan Shatu, to bazan ce maka komaiba, amman ka shirya ranar litinin zamuyi shaWi muddin ka cini na bar maka ita duniya da lahira, zan kuma bar garin Bani, da ?asar nan gaba Waya zan koma ?asar Cameroon, in kuwa na cika zaka bar duniya baki Wayanta!".
Cikin tsananin tsoro da kaWuwa Shatu tace.
"A a fa Ya Ba'ana wlh ba sona yakeyiba, karatu yake koya min".
Da sauri Salmanu ya katseta da cewa.
"Sonta nakeyi Ba'ana so kuma na aure, na kuma yarda zan shiga gasar ShaWi da kai a ranar Litinin na amince".
Wata irin muguwar dariya yayi wacce har tasa Aysha kowa cikin gida da gudu, shi kuwa saida yayi dariyar mai isarshi kana yace.
"Lallai gidan ArWo Yabani na gab da rasa motsin Wana miji".
Yana faWin haka ya murza layar zananshi, sai gashi ya Saci.

Cikin ?arfin hali Salmanu ya nufi gida.

Shi kuwa Ba'ana yana Sacewa a tsakiyar dottawan Fadan ArWo Yabani ya baiyana,.
Wanda badon tsoffin makiyayene sun saba ganin abinda yafi haka ba tabbas watsawa zasuyi.

So amman suka dake, cikin kamala Bappa ya kalleshi tare da cewa.
"A a Ba'ana lfy kuwa?".
Sunkuyar da kanshi yayi kamar mutumin kirki, cikin danne fushinsa yace.
"Ku gafarceni Bappa nazone da batun neman al'farma fagen shaWi, nida Salmanu Wan ArWo zamuyi gasa kan Shatu, na kuma yarda, muddin yayi nasara akaina na bar mishi Shatu zan kuma bar Rugar Bani baki Waya".
Da sauri Bappa yace.
"A a".
Da sauri ArWo Yabani yace.
"A a Malam Liman ba komai, na amince na basu damar yin gasar ShaWi mai nasara yaci gasar".
Jin haka yasa dattawan nan duk sukayi shiru.

Shi kuwa Ba'ana cikin tarin ?eta jikinshi har tsuma yakeyi yana maganar zuci.
"Uhumm zan kashe Salmanu kuwa kisa mafi muni zaku gane kurenku hegun fulani kunzo garin daba nakuba kun fisu dukiya zan kashe Salmanu irin kisar da ban taSa yiwa waniba kisan da zaisa har abadan babu wanda zai sake cewa yana son Shatu".
A zahiri kuwa, godiya yayi musu kana ya juya ya tafi.
Nan dattawan kuma sukaci gaba da tattaunawa yadda ShaWin zai kasance.


Washe gari ranar asabar da sanyin safiya akayi shelar sanar da gasar ShaWi da za'ayi jibi litinin, da kuma, waWanda zasuyi gasar da sunan wacce za'ayi dan ita.

Gaba Waya magarna ta cika Rugar Banin da kewayenta, duk wanda yaji yana firgici,
Maman Salmanu kuwa tuni taketa kuka tana cewa ita kam so ake a ?arar mata da yaranta an kashe mata Hashimu yanzu kuma ace da Salmanu za'ayi gasar ShaWi da mutun da sun san ba'a taSa nasara a kansa a.,
Mutanen sauran rugogin Fulani dake mutunci da ArWo Yabani kab sai gudumowar magunguna suke kawo na dauri dan a tsuma jikin Salmanu.

Sosai kuwa babanshi da yayunshi mata da maza da abokanshi keta tsumashi.

Shi kuwa Ba'ana tun ranar ya Wauki tun?ur ?asar da yake tsuma bulalinshi, ya kaishi ?auyen Bonon, gaban dodon tsafinsu,
Anan tukunyar ta kwana bulali tamanin dake cikin tunkuyar nan aketa tsumawa da tsafi.
Kana an jikasu da ruwan gishiri sannan an juye kunamai sama da Wari a ciki, irin ba?a?en kunamun nanne masu mugun dafi, an sasu ciki sunata harbin bulalin nan suna sa dafinsu a jiki. ranar lahadi da yamma ya amso tukunyar,
Har zauren gidansu Shatu yaje yasa aka kira mishi ita bayan ta fitone yace ta le?a cikin tukunyar, a hankali tace.
"Me zan gani a ciki?".
Kanshi ya jinjina mata tare da cewa.
"Nazo in nuna miki bulalin shaWi nane, ki gansu da kyau, dan ki cewa wancan koWeWden ya shirya shan zabga".
Kai ta jujjuya tare da cewa.
"Ni ba sai na ganiba".
Murmushi yayi tare da buWe tukunyar kana ya karkatar mata shi gabanta.
Da sauri taja da baya tare da cewa.
"In......




Littafina na kuWine turo katin mtn na Wari uku kacal ko karanta a nitse.





By
*GARKUWAR FULANI*=???
=?J??=?????=?
?>?4?
*GARKUWA*

PAGE 10

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

=??????=?
?>?4?

LITTAFIN GARKUWA NA KU?INE, TURO KATIN MTN NA ?ARI UKU KACAL ta number 09097853276 domin samun cikekken labarin, ko kiyi min transfer Win 1k Wan samun SP GROUP ta asusuna 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number 09097853276


FREE PAGE

Cikin tashin hankali tace.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun. Ya Ba'ana me wannan, abu kamar macizai". Da sauri ya meda ya rufe kana ya mi?e cikin yin ?asa da murya yace.
"Kinga ni kada ki tayarmin da hankali kinsan bana son ganinki cikin tashin hankali, in sha Allah nine da nasara ko dai bakya so nane".
Da sauri ta girgiza kanta tare dasa tafin hannunta ta rufe bakinta.
Ganin haka ya kwashi abinshi ya tafi.

Ita kuwa koda ta shiga gida, gefen Inna ta zauna tare da cewa.
"Inna ku cewa Bappa ya cewa ArWo ya hana gasar nan, kada a cutar da Ya Salmanu".
Cikin sanyin jikin da duk kwanan haka inna ta zama, a hankali tace.
"Uhumm ba komai Shatu in sha Allah duk abinda zai faru da sanin Allah.
Yanzu ke yaushe nema zaki koma hutunmu?".
Kanta ta gyaWa a hankali tace.
"Rana ita yau zan koma kimga saura mako Waya kenan".
Ummey ce dake gefe ta Wanyi ajiyan zuciya gami da cewa.
"Alhamdulillah ni in kin komama hankalinmu zaifi konci, domin muddin kinanen sai Ba'ana yayi ta kalato fitina".

Shiru sukayi baki Wayansu, jin an fara kiran sallane tasa, duk kowa yayi al'wala haraman salla.


A daren ranar kuwa Ya Salmanu da abokinshi Sale suka zo, wurinta, nan take ce musu ita kam bata son wannan gasar da za'ayi kuma tunda an kafe sai anyi sam ita bazata jeba.
Haka dai sukayi ta hira daga bisani suka tafi.

Washe gari ranar Monday kuwa, tun da sanyin asuba aketa gangamin.
HaWuwa a filin da za'ayi shaWi.
Mutanen sun cika ma?il dan anfi yawan yin gasar da safe, sabida da rana duk makiyaya sun tafi kiwo manoma sun tafi daji.
Tuni matasan Fulani na rugogin nesa da Bani ma sun zo.

Bukar kuwa tunda aka fito sallan asuba yaje. Gidan ArWo Yabani, yaso ace an janye gasar tun randa aka shelanta amman ArWo yaki,
still yanzuma da yazo, bayan sun gaisane ya Wanyi gyaran murya tare da cewa.
"Ha?i?a naso a janye wannan shaWi, domin nasan abun bazaiyi daWin ganiba ace Ba'ana na zane Salmanu Wan ArWo ga wannan rugar, amman ka?i ka saurari zancena,
Dan haka ni ba kada wani abu ya faru ku kuskura kuyi kuka dani, duk abinda Wana yayiwa Wanku kune kuka saya mishi da yawun bakinku kun rigada kun san bazaku taSa samun wanda zaifi ?arfin Wanaba".
Shiru ArWo Yabani yayi yana nazartan kalaman Bukar,
ganin yayi shirune alamun ya gama magarsa cikin sanyi ArWo Yabani yace.
"Duniya da faWi take, Bukar Mai kanwa a kwana a tashi watan-wata-rana zakaji zaka gani da idanunka za'a samu wanda zaifi ?arfin Wan ka, Allah zai bijiro da wanda zai iya jure bulalin Wan ka".
Cikin wani irin yanayi Bukar yace.
"Babu mamakin a samu mai iya, jure bulalin, tabbas babu mamaki. Sai daifa abun da bazai taSa yiwuwa bane har illa masha ALLAH ace an samu wanda zai iya nasara a kanshi babushi babu namijin da zai iya sashi jin zafin bulala bare ya zubda hawayen da zaisa ya rasa Shatu".
Wani dogon numfashi ArWo Yabani yaja tare da cewa.
"Uhummmmmm". Daga nan bai kuma cewa komaiba,
Shi kuwa Bukar tashi yayi ya kakkaSe rigarsa ya juya ya tafi yana faWin.
"In dai kunne yaji gangan jiki ya tsira".
Da ido ArWo Yabani ya rakashi, yana maiji a cikin ransa inma ace yanada dama, inama ace zai samo wannan bulalin da Malam ChuSaWo ya gaya musu, da tabbas ya samu hanyar da zai cire mugun iri a garinshi.

A haka Salmanu da abokinshi, sukazo suka sameshi zaune. Bayan sun gaisane Sule ya Wan matso kusa da ArWo a hankali yace.
"Allah rene, duk wuri an taru mu ake jira, shi Ba'ana tun da asuba yana can, yanzu Iro yazo yake ce mana gacan fili ya cika, mu kaWai ake jira, har wasu nata maganganun wai Salmanu ya ji tsoron Ba'ana ya gudu".
Murmushin da yafi kuka ciwo ArWo Bani yayi dafa tsakiyar kan Salmanun yayi kana yace.
"Kuje Salmanu, Allah ya bada sa'a Ubangiji yaga niyarmu na son tseretar da wannan yarinyar daga fadawa auren wannan mushurkin, ta?adiri in Shatu matarkace Allah ya baka sa'a in kuwa ba matarka bace, Allah ya baiyono mata wanda zai zame mata GARKUWA daga faWawa auren wannan azzalumin".
Amin Amin sukace baki Wayansu kana su sukayi gaba.
Shi kuwa ArWo, saida ya jira su Malam Liman Bappa kenan dasu Ahaji Horu, da Ahaji Umaru da Garbati.
Koda sukazo ba Sata lokaci suka nufi, farfajiyar wurin da aka tanada dan shaWi.

Filin ya cika ya batse tako ina mutane zuwa sukeyi arna da musulmai fulani da hausawa da ?abulun, ?achamawa, domin duk yankin nahiyarsu an san babu ta?adiri sama da Ba'ana sabida tunda ake gasar ShaWi da kuma gasar kokuwa yayin nunan sabon gero ba'a taSa cin nasara kanshiba, muddin ya shiga gasa tofa shine da nasara.
Har ta kai da in dai ya Waga hannun to babu mai Wagawa.
To sanadinshi aka hana ShaWi a Rugar Bani, tsawon shekaru biyu sai gashi yau an dawo dashi.

Wannan dalilin ne yasa gaba Waya Rugar Bani ta cika ma?il da mutane maza da mata manya da yara,
Ga mai busar sarewa kuma yana tsakiyar taro inda akabar filin da za'a gobza yanata rere kirari wa Ba'ana.

Isowar su ArWo yasa aka basu hanya har suka iso gaba inda aka tanada musu, kujerun zama. Na bencin katako.
Daga nan manyan Dattawan duk suka Zazzauna.
Bisa ?a'idar gasar ShaWi wanda ya fara cewa yana son yarinya shi zai fara duka, in wanda yace yana sonta daga baya ya ?etare bai zubda hawayeba baiyi kukaba, to sai asa kwanaki sai yaje yayi jinya ya worke daga zabgar da yasha, sai ya dawo ya Wauki fansa, to in ya zana wannan yayi kuka shike nan yayi nasara in kuma wannan ma baiyi kukaba za'a sakeyi har sau uku to nan in babu wanda yayi kuka cikinsu sai yarinya ta zaSi wanda takeso, don anada ya?inin duk wanda ta zaSa, zai iya kare kanshi tunda ?arfinsu yazo Waya.

Bayan an gama dai-dai-ta komai, Salmanu ya cire rigarsa kamar yadda ?a'idar gasar take, ya rage dagashi sai gajeren wondon.
Shi ma Ba'ana ya cire rigarshi ya zama dagashi sai gajeren modo, irin masu zuwa har guiwa Winnne.

To dole a ?a'ida Ba'ana ne zai fara duka, amman da yake ya shiryawa abun sai yace, shi ya amince a fara dashi, kuma shima yau zai rama Ba sai an ware kwanakin zuwa jinya ba.


Nan kuwa take al'kalin gasa Barmuji yace an amince.
Daga nan aka zaro bulalin shaWi na cikin tanWun masarautar ArWo Yabani wanda an ?ara tsumasu suma.

A hankali Barmuji ya mi?a wa Salmanu, bulalin,
kana ya Waga hannunshi ya dawo dashi ta bayan Ba'ana.
Shi kuwa Ba'ana tsayuwa yayi ?am tare da Wan ware sawunshi,
Busar sarewar da mai busan yayine alamun a fara,
Ai kuwa cikin kuzari da jaruma Salmanu ya Wan ja da baya,
kana ya tattaro ?arfin shi ga ba daya, ya Waga kitsetsten bulalan nan, ya ta?ar?ara ya zabgawa Ba'ana shi a tsikar bayanshi,
Wanda a take taron matasan dake wurin suka kurma ihu mai karaji,
Yayinda shi kuwa Ba'ana, ?im ya tsaya kamar ba shiba, domin ko idonshi bai ?ebtaba.
Sake ta?ar?arewa Salmanun yayi ya kuma zabga mishi bulalar a inda ya kima mishi na farin.
Still ihu, taron matasa sukasa, tarin ?abilar Sachama kuma dake wurin sai rurrufe idanunsu sukayi da ?arfi sabida wai bazasu iya jurar ganin ana zabgar jakadan suba.
Mai irge kuwa da iya ?arfinshi yake kware baki yana cewa.
"?aya! Biyu! Uku! HuWu! Biyar! Shida! Bakwai!!!".
Haka yaketa irga duk bulalar da aka kaiwa Ba'ana amman wannan tagadirin mutumin ko a jikinshi kamar dutse ake zanawa ba shiba.

?a'idar bulalin shaWi Hamtsine akeyi.
Haka Salmanu yake ware iya ?arfinsa yana zabgar Ba'ana, yana tsaye ?i?ama. In wannan bulalan ya lauye, sai a bashi wani bulalan.
Har akaje arba'in da takwas ko gezau.
Gaba Waya hankalin mutanen kirki ya gama tashi, domin sun sadakar da nasara ta kubcewa, Salmanu.
Shi kuwa Salmanu tattaro sauran ?arfinshi kab yayi,
ya narka mishi bulala ta 49-50".
Amman shirunshi.
Ihun da kafuran ?abilar Sachama suka sakine ya tabbar an gama, nan take suka shigo filin da gudu ruggumeshi suketayi suna shafa bayanshi, da yayi shati-shati.

Shi kuwa Salmanu gaban ArWo yaje ya zauna, nan aka basu ruwa sukasha gaba Wayansu.
Hutun 30 minutes sukayi aka koma fagen fama.

Da ?arfi mai busan sarewa ya busa alamun a fara,
wani irin kafurin murmushi Ba'ana yayi tare da gyara ri?on da yayiwa bulalar tashi.
Cikin tsananin mugunta ya Wan koma da baya, kana ya Wago bubalar da masifan karfi ya zabgawa Salmanu ita a tsakiyar fatan bayanshi.

Wani irin gan tsarewa Salmanu yayi, sabida wani irin masifeffen azaba mai girgiza zuciya da yaki yana ratsa dukkan sasasan jikinshi.
Bai gama dawowa daga gigi da azabar bulalar forkoba, yaji ta biyu,
Rumtse idanunshi yayi da azaban ?arfi, gaba Waya inda bulalar ya taSashe, harbin kunama yakeji yana ratsashi.
Wani irin numfarfashi yaka lokacin da aka zabga mishi bulala ta goma.

Gaba Waya hankalin mutane ya tashi domin kowa yaganshi yasan yana jin azaba.
Bulala ta ashirin da biyar da akayi mishine ya sashi buWe idanunshi da suka koma jajazir dan azaban da yakeji.
Su kuwa kafuran nan sai ihun farin ciki sukeyi.
Shi kuwa Barmuji zagayawa yayi gaban Salmanu wai yaga ko idonshi ya kawo ruwa,
babu ruwa kam sai azabar da yakeyi tamkar idanun zasu faWo ?asa, ci gaba da irgens yayi.
"Ashirin da uku! Ashirin da huWu!!".
Wani irin tsalle Ba'ana ya buga da iya ?arfinshi ya tsulawa Salmanu bulala ta ashirin da biyar.
Wani irin duhune ya rufe ganin Salmanu, saiga wasu zafafan hawayen azaba sun kwaranyo masa, ihu ya kuma zurma jin zafin bulalar ta isa kan mazantakanshi.

Gaba Waya su Bappa dama matasan kowa rufe ido yayi sabisa dukan da akewa Salmanu dukane na son Waukan rai.

Aysha kuwa tana gidansu kamar kullum tajiyo ihun Ya Salmanu kamar yadda kullum ihun wanda ake gasar dasu ke shaida mata sun faWi.

Cikin kuka konta bisa cinyar Ummey tare da cewa.
"Shike nan Ummey zai kashe ya Salmanu".
Tuni itama Ummey da Inna hawayen suke zubdawa.

A can gidan ArWo Yabani kuwa inna laure Maman Salmanu, kuka takeyi tamkar zata shiWe domin yaranta mata sun zo sun gaya mata halin da yake ciki.


A can wurin gasar ShaWi kuwa, ganin tu?uru Ba'ana so yake ya kashe Salmanu ne yasa,
matasan Fulani sukayi kanshi dan dukanshi yake harda tattakashi kuma tuni ya wuce balali hamsin Win ?a'idar gasar.

Koda matasan Fulani suka shiga dan crton ran Salmanu kawai sai ga ?abilar Sachamawan nan, sun fara zaro makamai sun rufa duk wani ba fulatani da duka da saran wu?a.

Lokaci Waya wurin ya hargitse gaba Waya.
Aka kaure da faWa saida.

Ganin wurin ya hargitse ne yasa,
Gaini yayi saurin kiran hukuma mafi kusa ya sanar musu.
Cikin ?an?anin lokaci kuwa suka iso.
Hakane yasa duk ?abilun ?achamawa suka gudu.
Allah ya takaita faWan baiyi nisa ba, a take Waya daga cikin police Win wanda yake abokin Salmanu ne ya kwashesu suka tafi asibi.

Bayan garin ya lafa, kowa ya dawo haiyacinsa ne.
Isa ?anin Salmanu ya tafi asibiti dan jinyar Wan uwanshi kuma Alhamdulillah da yake ya samu taimakon gaggawa komai yazo da sau?i.

Shi kuwa Ba'ana daga nan izayarsa ta ?aru manufarsa shida ?abilar Sachamawa shine. Su tarwatsa al'ummar fulanin Rugar Bani baki Wayansu.

Zuwa yanzu kuma ko ?udane in dai na mijine to bazai sau?a kan jikin Aysha ba,
sabida asirce, asircen da yakeyi da kuma tsoronshi da akeji.

Aysha kuwa ko zuwa dubo Salmanu ya hanata domin yace muddin taje a bakin ransa.

Yau kwana huWu da faruwar abun, ya da faruwar abun kuma yau ta kasance jumma'a ne.

Kasan cewar jummace yasa gaba Waya makiyayan suka taso kiwo da wuri, sabida son samun jam'in sallan jumma'a.

Iro Waya daga cikin yaran Ahaji Horo, wanda yake yayan Binto da kuma Junaidu.
Kusan shine karshen dawowa kiwo.
ya taso ya taso tarin dabobbin sa a gaba kenan ya haWu da gungun matasan ?achamawa, har sun wuceshi, sai kuma suka bishi a baya, cikin izaya babban cikinsu yace.
"Kai Wan fullo nan garin ubankane ko garin ubanmu?".
Cikin jarumtar jinin fulani yace.
"Gari dai da daji namune tunda iyaye da kakannimu sun saya, in kuma kuna maganar tushen nasabane, to Adanawa Yola dama kewayenta duk namune fulani".
Cikin mugunta Waya daga cikinsu ya kai mishi mari da addan dake hannunshi".
Murmushi Isa yayi cikin hausar fulani yace.
"Kada ka sake dukana".
Kusan a tare suka haWa?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? bakin wajen cewa.
"In mun dakeka sai me?".
A kufule yace.
"Wallahi sai in rama, yawanku ba shine abin tsoro ba".
Ai kafinma ya rufe baki suka haushi da duka,
da sauri ya fara kare kanshi tare da kai musu duka,.
Kamar da wasa su rai shida sun gaza ji da Wan lenge-lengen saurayi matashi Wan Fulani.
Ganin kamar zaici galaba a kansune, yasa, Waya daga cikinsu ya dawo baya-baya ya zaro wukar dake ?ugunshi, da ?arfi ya dawo kan Isa, ya luma mishi wu?an a cikinsa wani irin ?ara isa ya sake, sai dai babu mai jinsa bare ya kawo masa agaji domin.
Dai-dai wannan lokacin duk wani musulmin wannan yankin yana masallacin jumma'a,
Da wannan damar suka samu suka kashe isa,
wanda

13 / 72