Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   58 / 72

171K to 174K   out of 214K words

goma. Gobe za'a shiga goma na wuya, an gama na marmari.


Yau kuma makara Shatu tayi.
Ganin har su Jalal sun zone yasa Ummi ta nufi Wakinsu.
Ai kuwa kan gado ta hangosu.
Tadasu tayi kana ta fito.
Tana cewa.
"Shatu kiyi sauri kizo ki kaiwa Sheykh nashi".
Kusan a tare suka diro ?asa.
Brush kawai sukayi suka fito.
Da ?aton hijabin ta fito.
Tana zuwa Dinning area Ummi ta mi?a mata tray'n abincin nasa.

Amsa tayi ya juya ta nufi falonshi.

Tsaye ta sameshi gaban show glass Win dake gefen Fridge Winsa dake Dinning area,
Cup ne a hannunshi cike da madarar gongoni da molt a haWe.
A hankali ta wuceshi kaWan ta ajiye tray'n.
Kana ta juyo da nufin sau?owa, taku Waya tayi a na biyu ta iso gabanshi kenan.
Aka saki bindigar shaidar huWu da rabi tayi.
Wani irin zabura tayi tare da af....!



Littafin GARKUWA na kuWine turo katin mtn na Wari uku kacal ta wannan number 09097853276, domin shiga Normal group wanda a wata Waya za'a, gama Part one. Ko kima kiyi min TRANSFER Win 1k ta asusuna na Jaiz bank, domin samun shiga Special Group wanda a sati biyu cakal za'a gama Part two da izinin ubangiji, 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853297.

Ke mai haushi kin turo Warinki uku, kinzo kinata haushi, nace ki turo ac no Winki in maida miki kuWinki kin tsaya yimin tumasanci shiyasa nayi Black Winki, a rashin Sa'a na haWa da number ki na goge. Kuma baki Turo ac na na meda miki shi ba. To Alhamdulillah a take a lokacin nayi miki sadaka da Warinki uku, ubangijina shine shaidata, banci kuWinki ba, nasan zakiga PAGE Win sabida akwai waWanda basu san darajar Allah da Manzonsa da iyayensuba, zasu fitar, to kiji ni Shatu na sau?e nauyin Warinki uku.



By
*GARKUWAR FULANI*
Cikin tsananin firgita, da tsinkewar zuciya da tsoro, tare da kerman jiki, ta juyo ta fuskanci inda yake tsaye tare da abkawa jikinshi.

Cikin abinda bai gaza one second ba tamkar gilmawar wal?iya ya janye jikinshi ya kauce gefe.
Hakan yasa ta faWa jikin show glass ta ruggumeshi gam-gam cikin tsuma da karkarwa tare da sa hannunta duka biyu ta ri?e kanta, tana mai cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahiwani'imanwakil, Auzubikalimatillahi ta'ammati minsherri makala?a."

Tanayi cikin Wan Waga murya mai baiyana firgicin da take ciki.

Shi kuwa Sheykh Jabeer wani irin masifeffen dariya ne ya taso masa tun daga ?asan zuciyarshi har zuwa kan lips Winshi dole ya taune lip Win shi na ?asa.
Kana sai ya gimtse ya murtu?e fuska cikin tsare gida yace.
"Karki fasamin abuna!".
Sai lokacin hankalinta ya dawo jikinta.
Janye jikinta tayi daga jikin show glass Win da abkawar da tayi kanshi marfinshi ya Wan tsage.
Nannauyan ajiyan zuciya ta sau?e da ?arfi.
Kana ta tura baki sannan ta juya ta fara tafiya tana ?un?unin.
"Allah ya isana banzan al'ada a rin?a razana mutun anasa hanjin cikina na hautsunewa".
Baki ya taSe kana ya zauna bisa kujerar ya jawo tray'n ya Wibi abincin tu?e?en tuwo ne da miyar kase.

Tana fitowa sukayi sahur Win a gaggauce sabida lokacin ya Wan ?ara to.



Washe garin da rana bayan anyi sallan azahar.
Ya shigo kamar ko yaushe.
A falo ya samu Ummi da Hibba ita kuwa Shatu tana Wakinta tana karatu so take ta samu izu uku a wunin yau Win.
Gefen su ya ratsa kana ya zauna bisa kujerar zamanshi.
Bayan sun mishi sannu da zuwa ne, ya kalli Hibba cikin kula yace.
"Muhibbat ya azumin".
Cikin langwaSe kai tace.
"Da wuya".
Kanshi ya jinjina kana yace.
"Jeki kira Aunty Juwairiyya".
To tace tare da mi?ewa da sauri ta fita.
Shi kuwa wayarshi ya ciro ya kira Jalal dasu Imaran yace suzo su sameshi a falo.

Jim kaWan duk suka shigo.
Key ya zaro daga al'jihun tattausan jallabiyar dake ?asan al'kyabbar jikinshi ya mi?a wa Jamil tare da cewa.
"?auko min briefcase a kan Bedside drower'n."
To yace kana ya juya ya tafi.
Shi kuwa Ummi ya kalla tare da cewa.
"Ummi me dame kuke bu?ata ne?".
Cikin kulawa tace.
"Akwai komai, sai zam-zam Win kane ya ?are saura baifi gora biyarba".

Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"Ba matsala zai isa".
Lokacin Jamil ya iso. Mi?a mishi jakar yayi, tare da zaunawa gefenshi.
Shi kuwa buWe jakar yayi.
Murmushi Jamil yayi ganin tana ci?e ma?il da rafan dubu-dubu sabbi dal-dal.
Rafa huWu ya mi?awa Jamil hakama Jalal da Imran da Sulaiman.
Sannan ya kallesu tare da cewa.
"Kuje KMC plaza ku zabi kayan sallan.
Sai ya kuma kalli Aunty Juwairiyya yace.
"Aunty Juwairiyya, kuje tare dasu, da Ya Jafar ayi yadda aka saba.
Sannan ku zaSi abin bu?atar ku."
Gyara zamanta tayi tare da cewa.
"To mu gode, kuma za'ayi yadda kace."
Sai kuma ya kalli Ummi yace.
"Ummi kada ki manta da su Saratu".
Murmushi tayi tare da cewa.
"In Sha Allah babu abinda za'a mance".
Kai ya jinjina kana ya zaro rafan guda biyar ya mi?a mata, sannan ya mi?a wa Aunty Juwairiyya wasu rafofin kana ya bawa Hibba biyu.
Daga nan sukaci gaba da tattaunawarsu.


Washe gari kuwa da safe, suka shirya tsab zasu fita.
Aunty Juwairiyya ta Ummi cikin yin ?asa da murya tace.
"Ko zan kirawo Shatu mu tafi tare da ita ne?".
Da sauri Ummi tace.
"A a mijinta baice muje da itaba mujata mu tafi. Muje dai mu zaSo mata duk abinda takeso".
Cikin gamsuwa da hakan tace to.

Hibba kuwa cikin sanyi tace.
"Ayyah Ummi muje da ita".
Fitowar Shatu ne ta samesu a tsaye cikin shirin tafi yasa ta kalli Ummi cikin sauri tace.
"Ummi ina zakuje?".
"KMC plaza".
Ta Bata amsa a ta?aice cikin sanyi tace.
"Nima inzo muje, in samu in fita insha iskan woje".
Jalal ne ya Wan kalleta tare da cewa.
"Boss ya hana". Ido ta zuba mishi kana ta juya ta kalli Ummi cikin sanyi tace.
"Shike nan Ummi kuje, Allah kiyaye hanya."
Amin Amin sukace har sun juya zasu tafi sai kuma tace.
"Ayyah Ummi dan Allah karku daWe".
To sukace kana suka fita.


Shiru ta zauna a falon ba kowa hakane yasa ta kunna TV tashar Zee world.
Wani film mai daWi ta samu sukeyi, sai dai bata san forkonshiba, bisa alamu duk sabone.
Konciya tayi bisa 3 str tana kallo wayarta na hannunta.
Tana mgna da Rafi'a.

A haka bacci yayi awon gaba da ita.

Can Cikin bacci take jin alamun kamar mutun na tsaye a kanta, cikin magagin baccin ta buWe idonta.
Gabann Tv ta ganshi ya kashe TV kana ya juyo ya kalleta a fizge yace.
"Ba salla sai kallo da bacci".
Jin haka yasa ta mi?e zaune tana gyara mayafin kanta.
Shi kuwa tuni ya wuce Side Winsa.

Tana idar da salla ta fito. Nan ta samu Saratu tazo, kitchen Suka shiga suka fara aikin yamman.


Sai gab da la'asar su. Ummi suka dawo da kaya ni?i-ni?i. Nan suka ajiye sukayi salla kana suka shiga kitchen Win.

Hibba kuwa yashuwa tayi a ?asa tana birgima kamar bazata kai magriba.

Sai bayan sallan isha'i sun gama aikin sahur Win ne.
Suka dawo falo, nan Ummi ta nuna mata Winkunanta da aka bada tun Umaymah bata tafiba.
Sosai taji daWin kayan da Winkunan, lallai tana son dogayen riguna Amman tana son surkawa da Shadda, atampa, leshi, musamman WaWan nan Winkunan sunyi masifar kyau. Ko wanne dai-dai jikinta kamar an gwada ta.
Daga nan kuma suka nuna mata gellulluka da hibai da takalma da sara?unan da suka zaSo mata bayan sun zaSawa kansu.
Sun nuna mata nasun ma.
Ummi ta ?ara da cewa.
"Duk zannuwan da abun Winkawan kuma an bawa Kabir telen suma duk cikin KMC suke.
Nanda salla dai komai zaizo dai-dai.
Cikin jin daWi tace.
"Ngd matu?a Ummi Allah ya saka da al'khairi".
Amin Amin tace. Kana tace.
"Sheykh zakiyiwa godiya".
Shiru tayi kamar bataji ba.
Hibba kuwa cikin jin daWi tace.
Aunty Shatu na zaSa mana wani Shadda lace mai masifar kyau iri Waya na Wauka mana Royal blue and white Golding color. Nace a tsantsara mana dogayen riguna".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Kai kinko kyauta mana".
Daga nan suka tattara tarkacen suka nufi makoncin baccin su.

Zaune take gefen Ummi tana ri?e da waya cikin murmushi tace.
"Allah ko Umaymah munyi kewarki".
Cikin jin daWi Umaymah tace.
"To ko zaku zomin Barka da sallane".
Da sauri tace.
"Eh Umaymah Allah in ya yarda zamuzo ki tambayan mana shi".
Cikin dariya Umaymah tace.
"Yoh mace da mijinta sai wani ne zai tambayar miki".
Cikin sanyi tace.
"Uhummm".
Ita kuwa Umaymah cewa tayi.
"Ina Umminku?".
Da sauri tace.
"Gata ta ?arishe mgnar da mi?awa Ummi wayar.
Cikin fara'a suka gaisa kana Umaymah ta tambayeta ya yaran nata, tace duk suna lfy.
Nan take ce musu ta cewa Shatu ai a saudia zasuyi salla.
Sosai Shatu ta tayasu Murna.

Suna cikin hirar Hadimai guda uku suka shigo da jakukkunan guda uku.
Rusunawa sukayi bayan sun gaidasu ne,
suka ajiye jakukkunan tare da cewa.
"Gashi biyun inji LamiWo Waya kuma Gimbiya Aminatu ce tace mu kawo miki".
Sukarishe mgnar suna kallon Shatu.
Godiya tayi musu kana ta kalli Hibba data mi?o mata kuWi sun kai dubu biyar.
Ta gane manufar Hibba shiyasa ta amsa ta basu.
Godiya sukayi kana suka tafi.


Jim kaWan Hadiman Hajia Mama sukazo da sa?on Hajia Maman.
Sosai Shatu tayi godiya ta mashi kuWi a hannun Hibba ta basu.

Nan Hibba ta tattara kayan ta shigar dasu, zata shigar dana HAJIA MAMA tace
"A Hibba barsu zan shiga dasu."
Gefe ta nuna mata tace ajiyesu anan.


Bayan sunyi sallan azahar sun fito zasu Fara aiki ne ta kalli Ummi tace.
"Ummi bari inje inyi godiya wurin Hajia Mama".
Cikin tsareta da ido tace.
"Ki bari mana sai ansha ruwa sai in rakaki daga nan kiyiwa LamiWo ma godiya.
Duk dai wannan kyauta da yakeyiwa duk ahlin masarautar JoWa in lokacin salla ya gabato amman muje kiyi godiyar."
Da sauri tace.
"No Ummi ba sai an rakani ba, zanje ni Waya ma, kinga nasa al'kyabba".
Daga nan ta fice, cike da mamaki suka bita da ido.

Bayan kamar 37 minute ta dawo cike da fara'a sukaci gaba da aikinsu.

Can da suka fito dan yin sallan la'asar,
Ba kayan ba dalilinshi. Da sauri Hibba tace.
"Aunty Shatu kin shigar da kayan ne?".
Ci gaba da tafiya tayi tare da cewa.
"Maisu ta aiko an kwashe mata abunta dai".
cikin mamaki sukabi bayanta.


Yau azumi goma sha huWu gobe 15 in Allah ya kaimu.

Bayan yaci abinci ne ya kira Umaymah nan yake ce mata.
"In Allah ya kaimu gobe iwar haka ?arfe goma na dare zuwa sha Waya jirginmu zai tashi Umaymah".

"Kai da waye zaku tafi ne?".

"Nida Dr Aliyu, da Barrister Kamal, sai kuma Ya Hashim da Galadima, da Wambai da Abba na da cimgan Win shi".

Da sauri tace.
"To wai kana nufin kai bazaka je da taka cingam Win bane?".

Cikin sanyi yace.
"Kiyi ha?uri Umaymah dan Allah na ro?eki kada kice inje da kowa, dan Allah a barni mana in huta in na bar ?asar kam".

Shiru Umaymah tayi saida taji ya kai ayane tace.
"Shi kenan Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy, kuma muna nan tafe".

Amin Amin yace kana sukayi sallama.


Washe gari kab mutanen masarautar JoWa masu zuwa Umrah sun gama shirin su.


Bayan ansha ruwa anyi sallan isha'i ne suka shiga kitchen dan aikin sahur, koda ta Wauko Foodflaks Win da akasa mishi abin buWa baki ko buWe su baiba.
Hakane yasa Ummi tace to maza ta dafa mishi wani abun.

To tace kana ta juya ta Wauko, kaza, kwai, dankalin turawa kaWan, maggi, gishiri, tattasai, attaruhu al'basa mai Curry,
Duk ta matso dasu kusa.
Sai kuma ta Webo Kabeji karas.
Ta mi?awa Saratu tace.
"Yauwa Sara goga min su ?ananan, kada ki haWasu wuri Waya, kana ki yayyaka min al'basa sannan ki jajjaga min wata."
Ta faWin tana tura mata Attaruhu da al'basan.
Cikin nitsuwa Saratu tace.
"To Aunty ba matsala".
Ita kuwa Ummi meda hankali tayi kan girkin sahur Win.

Wanke rabin kazar tayi, tare da sata a tukunya ta watsa al'basa da maggi da tafarnuwa da citta da kanamfari kaWan.
Sannan ta rufeshi. Tasa wuta yadda ya kamata.
Kana ta jawo robar dankalin ta fara ferewa tare da cewa.
"Allah aikin nan yana yawa Ummi, kusan wuni muke a kitchen mu kuma kusan kwana shima wai bazaici abuba sai sa mutane aiki".
Tayi mgnar cikin gajiya da kuma iya gskyar ta, dan muddin kasha ruwa tafa burinka ka samu ka huta.
Juyowa Ummi tayi ta Wan kalleta tare da cewa.
"A'a ai bakya son hutun tunda kikaje kika samu Juwairiyya kikace ta huta taji da aikin gidanta, nan zaki rin?a yi, sannan in Hajia Maman ta aiko ki kora Hadiman dashi, ko kisa Hibba ta kaiwa bayi shi.
Kinga duk sun gaji sun daina kawowa, sai Na Gimbiya Aminatu, shi kuma Sheykh yace a dena kawowa tunda kice zaki iya da aikin.
Yanzu da kin bari suna kawowa dai da wata ranama sai munga dama mushiga madafa".
Sunkuyar da kanta tayi tare da yin shiru kamar bata nan.
Yes ta san duk abinda Ummi ta faWa hakane.
?arisa feree dankalin tayi kana ta won?eshi fes ta Waurashi a wuta, ya dafu sosai kana ta sau?eshi a gefe.
Zuwa lokacin kazar ma tayi lugub, haka yasa ta sau?eshi ta juyeshi a plate, zare ?asusuwan tayi duka, sannan ta ajiyeta gefe kusa da dankalin.
Jajjageggen Attaruhu da al'basan da Saratu ke mi?a mata ta amsa.
Cikin plate Win dafeffen dankalin ta juyeshi kana tasa kazarma a ciki.
Sannan ta jujjuyasu ta ca?uWasu da kyau, kana tasa Maggi gishiri Wan ?an?ani, sai kuma Curry.
Kwan dake gefe cikin Wan wani kwanon tangaran ta jawo, ta fasa kwan ta juye cikin haWin kaza da dankali da jajjagen ta Wan gwarayasu.
Hibba data shigo yanzu ne tace.
"Yauwa My Aunty dama kwaWayi ne ya koroni nazo in shiga kitchen."
Murmushi tayi tare da cewa.
"To matso ki tayani aikin Wan zuba min ruwan zafi kan Karas Wincan.
In yayi Wumi ki juye ruwan cikin kwandon kabejin nan ruwan zafin ya Wan razana ganyen, sai ki mi?o min shi nan".
To tace tare da fara aikin.
Ita kuwa Shatu Wiban haWin ta rin?ayi tana mul-mulawa kamar Yan boll,
saida ta gama sannan, ta Waura man gyaWa.
yayi zafi ta fara suyasu,
saida ta soyasu duka tasa a Foodflaks kudun kada yayi sanyi ta matsar dashi gefe.

Kana ta matso ta ta amshi Kabeji da Karas Win.
Mai tasa kaWan a tare da al'basa, kana tasa jajjagen kaWan, ta soyasu, sannan ta Wauki sauran murmusheshen kazar tasa a ciki kana ta juye Kabeji ta Karas Win, sanna tasa Maggi, mintuna biyu zuwa uku ta sau?esu.
Ta zubawa Hibba da Ummi kana tasawa Sara.
Sanin ya dawone yasa ta shirya mishi komai a tray'n.
Kana ta nufi Side Winshi.

Ummi kuwa da Hibba a falon suka zauna suka fara ci suna santi.
Ita kuwa Saratu tattare wurin tayi ta kimtsa komai ta goge sauran kwanuka kana ta tafi.


Shi kuwa Sheykh Jabeer, tuni ya gama kimtsa komai da zai bu?ata in yayi tafiyar.
Bai wani Wauki abu da yawa ba.
Komai na Wauki shi ya kimtsashi bisa tsari.
A hankali ya taso daga bakin gadon hannu yasa ya shafa cikinsa,
Yunwa yakeji kuma ya gaji da masan shiyasa yau bai kulaba.
Folon ya nufo tare dasa kuWin dake hannunshi a al'jihun jallabiyarsa.
A hankali ya tura ?ofar ya fito.
A dai-dai lokacin itama ta turo ?ofar shigowa falon .
A hankali ta shiga

Tsakiyar falon ya nufa,
bisa kujera ya zauna, ita kuma kanta a sunkuye ta iso inda yaken.
?an sunkuyowa tayi ta ajiye tray'n kan santa table Win, gabanshi.
Kana a hankali ta fara mi?ewa zata tashi.
Kanshi ya Wan juyo ya kalleta, da yatsarshi ya nuna mata ta zauna.
Cikin kwaSe fuska tace.
"In zauna?". Kanshi ya gyaWa mata alamar eh.

Cikin turo baki ta harari gefen fuskarshi, kana ta Wan rusuno a hankali ta zauna.
Bakin kujerar dake bayanta.
Cikin muryar ?un?uni tace.
"Bacci nakeji".
Bai kulata ba, sai ma gyara zamanshi da yayi ya nuna mata plate Win gabanshi.
"Cikin cinna bikin sama tace.
"Bana gane kurmanci".
Juyowa yayi ya watsa mata narkakkun idanunshi da bata iya gano meke cikinsu cikin nata.
Karon forko kenan data ga zahirin yadda kalar ?wayan idonshi suke, sosai kwarjinshi da haibarshi ya danne tsiwarta, a hankali ta matso kusa da inda yake.
Rusunawa tayi har ?asa a hankali ta buWe plate Win data shirya mishi Chechen balls da ganyen Fork ta ajiyeyi mishi gefen plate Win kana tasa hannun zata Wauki flaks alamun zata samunshi tea a cup Win.
Yatsarshi manuniya ya Wan Waga tare da kaWa mata ?atsar alamun bai sataba.
Yamutsa fuska tayi tare da turo baki cikin yin ?asa da murya can cikin ma?oshinta tace.
"Karkaci ma in kaga dama".
Ta gefen idonshi ya kalleta ba tare da ya juyoba yana kallon yadda takeyin mamul-mamul da lips Winta,
Gyara zamanshi yayi tare dasa hannun ya Wan Wauki Fork Win Chechen ball ya Wan soka
kana ya Wago alamun zai kai bakinshi sai kuma ya maida cokalin ya ajiye.
?ago kanshi yayi ya zuba mata ido na 3 second kana ya nuna mata idonshi tare da lumshesu alamun ta rufe idonta tako gane abinda yake nufi.
Cikin gunaguni tace.
"Nifa zan tafi bacci nakeji, ba sai na rufe idona a nanba zan tafi kaci abinci k".
Shiru tayi ganin kallo da yake mata da mayun idanunshi.
tura bakin tayi tare da sunkuyar da kai kana ta murguWa bakin.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, numfashin ya Wan fesar kana a hankali ya muskuta ya gyara zamanshi, kaikaicewa ya Wan yi yasa hannunshi cikin al'jihun jallabiyarsa. rafan dubu-dubu sabbi dal-dal ya fito dasu guda shida.
Mi?o mata su yayi.
Hannunta ta mi?o a hankali ta amshi kuWin.
Gyara zamanshi ya kumayi kana yasa yatsunshi biyu ya jawo Waya plate Win ya rufe Wayan.
Tsuke fuskarsa yayi da kyau tare da kafeta da ido cikin kakkausar murya yace.
"Yau zanyi tafiya daga yanzu, zuwa ?arfe biyu. Duk inda naje inada lbrin gidan nan duk abinda zakiyi zan sani, duk motsin masarautar JoWa.
Saboda haka ki kiyayi kanki da yiwa mutane tijara,
Bana son fitsara da rashin sanin darajar manya, ki tsaya matsayinki, bana son shishshigi cikin al',amuram rayuwata.
Ki kuma kiyayi murguWa wannan bakin fitsarar in ba hakaba wata rana in kin murguWa minshi bazai dawo dai-dai ba haka zai zauna a murguWe a karkace, Allah ya nuna miki matsayi da darajar miji."
?asa tayi da kanta tare da cewa.
"KuWin na meye ne".
A da?ile yace.
"Na yagawa ne, kije ki yaga ki zubdasu".
Kallonshi ta Wan yi ganin hankalinshi baya kantane, ta mi?e tsaya ta juya ta fita.
Shi kuwa bayanta yabi da wani irin kallo.

Sosai yaci Chechen balls Win dan yayi daWi sosai, kuma gashi rabanshi da abinci tun jiya iwar hakan, dan haka yaci iya abinda zai iya ci, kana ya mi?e yaje yayi wonka ya fara shiryawa.

Ita kuwa Shatu tana fitowa a falo ta samesu gaba Wayansu harda Ya Jafar da Aunty Juwairiyya da kuma. Su Jalal da Hajia Mama.
ganin hakane yasa ta Wan juya ta nufi falonta

58 / 72