Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   68 / 72

201K to 204K   out of 214K words

ya fuskanceta da kyau a hankali yace.
"Banbancin tsakanin sarautar gefen ?a?an ?a?a maza da gefen ?a?an ?a?a mata.
Shine kamar haka.
1 Galadima (must be a prince )
2 Chiroma (crown prince)first born to the king
3 Tafida ( most be a prince )
4 Santuraki (must be a prince )
5 Sarkin dawaki ( prince)
6 ?an buram
7 ?an isa
8 ?an lawan
9 Durbi
10 Wambai
11 Turaki
12 ?an maje
13 Yarima
14 ?an iya
15 Majidadi.
Dan Wagowa yayi ya kalleta tare da sa?e yatsunshi da yake naWewa yana irga mata yace.
"Wannan duk royal family ne mostly biological sons din sarki ne wasu kuma jikokin sarki kuma kunne biyu sukeyi a rawunansu sabida su ?a?an sarki ne ko kuma iyayensu ?a?an sarki ne.
Kanta ta jinjina mishi alamun ta gamsu tana kuma ganewa.
Shi kuwa a nitse yaci ga da ce mata.
"Anan ake samin chief of staff da kuma senior councillor kamar galadima mostly shine senior councillor shine elders in royal bloodline ana samun galadima yapi sarki a shekaru kuma shi ake bama riqon gari in sarki bayanan.

Sannan duka anan sunayen dana irga miki da fari kowa zai iya yin sarki tunda daga Wan sarki sai jikokinsa na gegen ?a?a maza, shiyasa su kunne biyu sukeyi a rawanunsu.

A hankali ya kalli Ummi data fito da Hijabi a jikinta ta zauna kusa da Shatu.
Tare da cewa.
"To kinji bayanin ?a?an ?a?a maza na sarki."
Kai ta gyaWa tare da cewa.
"Na gane kuwa Ummi, yanzu gaya min na ?a?an yaran sarki mata kuma inji".

Gyara zama Jamil yayi tare da cewa.
"To sukuma sarautar gefen yaya mata sune.

1 Madawaki
2 Garkuwa
3 Makama
4 Majidadi
4 Waziri
5 Matawalle
6 Sarkin yaki
7 Magayaki
8 Jarma
9 Talba
10 Shatima
11 Ubandoma
12 ?an kadai
13 Magajin gari
14 ?an masani
15 Barma.
?an sau?e numfashi yayi tare da ci gaba da cewa.
All of these hakimai ne wanda sukeyin kunne daya a rawunansu.
Kuma wasu a cikinsu jikokin sarki ne ta bangaren mamansu, mum dinsu ce yar sarki kamar dai mu a Masarautar su Sitti ko za'a bamu mulki iya waWannan za'a bamu kinga baza suyi kunne biyu ba shiyasa suke kunne daya amma suma hakimai ne manya kuma yan majalissar sarki also akwai kin makers a cikinsu.
Sai dai su cikin jerinsu babu wanda zai gaji sarautar sarki kamar dai mu yanzu bazamu gaji Jadda ba da masarautar gargajiyace sai dai da yake nasu na musulcine, in Kuma a masarautar JoWa ne sunayen da na ?irga miki na forko cikinsu za'a iya bamu, domin yanzu GARKUWA da aka bawa Hamma Jabeer matsayinsa yafi ?arfin hakan shiyasa Magauta basu damuba."

Ya ?arishe mgnar da cewa kin gane ko Aunty Shatu,
Kinga shiyasa da aka bawa Ya Jafar Galadima cikin kwana goma aka sabauta manashi.
Ana tsoron kada tarihin Sarki Bala da mahaifinshi Madu Wan Sarki Sule ya maimaita kanshi a kan ?a?an Wakinmu.
Shiyasa da aka bawa Hamma Jabeer Garkuwa mu bamu soba.
To sau?in abin ma Waya ne da suga sarautar gefen ?a?an ?a?a mata aka bashi duk da shi jikan Wan Wan Wansa namiji ne".

Ajiyan numfashin tayi kana a hankali tasa hannunta ta tallaSe habarta, cikin alamun nisan zango na tunani da nazari.

A hankali Ummi ta matso kusa da ita cikin sanyi da kuma yin ?asa da murya tace.
"Shatu ni kuma in tambayeki wani abu mana".
Kanta ta jujjuya a hankali ta buWe baki tace.
"Na sani! Ummi nasan abinda zaki tambayeni! Zakimin tambaya ne kan menene yasa da na shiga Wakin Yah Sheykh na suma na fita haiyacina, ko?".
Ta ?arishe mgnar wasu hawaye masu Wumi suna kwaranyo mata a fuskarta.
Cikin sanyin jiki ganin Ummi ta gyaWa mata kai alamar eh.
Jamil ma jiki a mace ya zuba mata ido.
Tafin hannunta tasa ta sharce hawayenta murya na rawa alamun tana son danne kukanta tace.
"Ummi Wakin Yan Sheykh Wakine mai cike da hatsara a rayuwarshi.
Tabbas dan Allah yayi shi mutun ne mai ibada da imani da kekyawar zuciya, da yawan ambaton sunan Allah da zama da al'wala wlh da badan wannan nagartar da Addu'o'in da suka zame mishi abokan rayuwa suka zame mishi GARKUWA ba, kamar yadda Manzon Allah yace.
"Addu'a'u saiful muminin da tuni sun kasheshi sun sabauta rayuwarshi.
Ummi ban san komai ba kan masarautar JoWa.
Amman dan al'farma Annabi da darajar Umaymah.
Zan taimaki Yah Sheykh iyakar iyawata.
Zan taimake shi akan abinda Allah ya bani ikon gani".
A hankali Jamil ya zamo ya zauna a ?asa.
Yana mai jin tsikar jikinshi na tashi.
Itama Ummi zamowa tayi ta zauna ?asa.
Hakama Shatu a hankali ta zauna gaban Ummi hannunta tasa.
Ta kamo hannun Ummi cikin muryar kuka tace.
"Ummi ku yarda dani, ku bani haWin kai, zan tone duk abun cutarwa dake Wakin Yah Sheykh. Bazan cutar dashi ba, zan taimake shi kamar yadda Bappa na yake bani umarni duk sanda mukayi mgn dashi.
Ummi keda Jamil ina bu?atar taimakon ku.
Amman kafin nan ki gayawa Umaymah in ta amince,
sai inyi aikin amman kada a gayawa Yah Sheykh dan bazai yarda ba."
Cikin tsoro ido cike da hawaye Ummi tace.
"To Shatu me zancewa Umaymah, me kika gani a Wakin har ya firgitaki yasaki suma?".
Cikin kuka tace.
"Ummi kada ku tsaya bincike a kaina.
Ni dai ku yarda dani bazan cutar da kowaba na cikin Masarautar JoWa sai wanda ya cutar da kanshi Ummi bamu da sauran lokaci mai tsawo fa, komai zai iya faruwa da Yah Sheykh".
Cikin tsoro da firgici Jamil yace.
"Ba matsala mun yarda dake, ni yanzu taimakon me zan miki?".
Cikin sauri ta share hawayenta tare da juyowa ta kalli shi kana tace.
"Yauwa Jamilu zaka samo mana mai saka tayis, yazo da katon Waya na tayis Win irin na bedroom Win Yah Sheykh sak da sak.

Sai kuma kayi ?o?arin mu samu ya Sheykh in ya fita ya wuni sai dare zai dawo".
Cikin sauri yace.
"Tayis da mai sawa ba matsala, batun in ya fita sai dare ya dawo kuma inaga.
Sai zuwa jibi ranar ne zaije asibitin gwamnatin Genaral Hospital.
To in yaje can wuni yakeyi wani lokacin sai dare zai dawo".
Cikin gamsuwa da hakan tace.
"To ba matsala.
Ummi ke kuma ki kira mana Umaymah ki sanar mata, muyi abun da saninta."

To Ummi tace kana a wurin ta kira Umaymah tayi mata bayani.
Ba wani neman ba'asi tace.
"A barta Ummin Jabeer na amince, tayi duk abinda ya dace a kan mijinta da yayanshi da ?annenshi dama duk wani abu nashi".

Cikin jin daWi ta jinjina kai lokacin da take jin mgnar Umaymah.

Wani irin dogon numfashi taja mai ?arfi sai gata ta tafi luuuh kan...!



Wasa farin girki? Shatu kadafa allura ta tono garma.




By
*GARKUWAR FULANI*GARKUWA




PAGE 25

"Da Mamaki kwallo a ma?abarta.
Wato dai haka za a cigaba da gwara kawunan mutanen. Masarautar JoWa ana mayar da su marasa tunani?".
Gimbiya Saudatu Ta faWa tana ya mutsa fuska don ta kasa kallon ?wayar idon Sheykh.
Banza ya yi da ita duk da ya waiwayo ya kalleta, ya so tanka mata, amman sai ya share yaci gaba da takunshi cikin nitsuwa yana tafe yana tasbihi.
A hankali ya isa falon.

Kanshi ya Wan juyo ya kalli tsakiyar falon.
Sam bai hango Shatu da Ummi ba dake zaune a falon.
A nitse ya maida kanshi ga inda ya nufa ya juya zai shiga corridor'n da zai sadashi da falonshi. "Ba ka ji me nace bane? Dutse ne kai ko waliy? Wata da watanni a kawo maka mace a ce sai yau ake bada kyautar budurci dan rainin wayo tuntuni kallon hoto kake mata ko me.
Ba ma wannan ba, wanne irin munafurci ne ya sa aka bada kyautar dawakai amarya da ango? Duk yana cikin sahun munafurcin da boye-boyen.."
Cikin tsawa ya dakatar da ita da cewa.
"Bana son shirme fa! Fitar min a gida tunda ba wancan tsohon ne ya gina min shiba".
Da sauri tace.
"Zan fice ba sai ka koreni ba."
Ta ?arashe mgnar cikin tsananin takaicin tsawar da ya yi mata don sai da hantar cikinta ta kaWa.
A dake ta jujjuya idanuwanta tare da cewa.
"To wai Waga Muryar na meye ne? Tambaya fa kawai nayi nake son amsa.
Wannan sar?ar kuma ta mece ce? Ta asalince wacce ta Sace Sat ko in ce ta yi Satan-dabo, ko kuma wata ce ta dabam aka ?ir?iro, don nasan waccer dai bata kai labari ba, daga wuyan waccer ts..."
Bai bari ta cigaba ba ya tare ta da muryarsa a nutse cikin iya sarrafa harshe, ya lumshe idonshi kana ya buWesu a hankali yace.
"Dakata, tsaya kiji."
Da sauri tace.
"Uhum ina jinka".
Rausayar da kanshi yayi kana a hankali yace.
"Kyauta ce ta girmamawa, wacce ba kowacce mahalu?iya ce take katari da irinta ba a cikin Masarautar JoWa, duk da kyautar ta yi kaWan a wajen wacce ta cancanci ninkin hakan, bana ji akwai abinda za a iya biyan macen ?warai da abun duniya ba ko da kuwa za a bata kujerar masarautar Joda wanda wasu wayayan mazaunan cikinta ke wawasun nema ba. Darajarta da kimar kyautar data bada yafi ?arfin tukuicin da masararutar ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????JoWa ke badawa, ita ba irinku bace ta wuce hakan".

Shiru Ummi tayi tana mai jin kalamanshi tare da yin wani sassanyan murmushi.

Ita kuwa Aysha a hankali ta lumshe idonunta tanajin kalamanshi masu sanyi da sanyaya zuciya.

Gimbiya Saudatu kuwa. Wani irin ba?in ciki ne ya turni?e ta, da kyar ta iya saita numfashinta cikin karkarwar jiki da rasa abin cewa ta ce, "Wannan wanne irin yabo ne haka har sai ka haWa da sarautar gidan nan?"
Yanayin ta ya kalla ya yi Murmushi, wanda ya ?ara tunzirata kana a nitse yace.
"Dan na tabbatar miki da ?imarta da darajarta ne, ina son kuma hakan ya zauna a cikin ?o?on ranki har illa masha Allah..."
Cikin takaici tace.
"Wannan kuma ka yi kaWan ka sani adana shi a raina"
Kallon da yake mata ne ya hana ta ?arasa zancen, don daga inda take tana iya jiyo sautin hucin da yake, muddin ta ?ara sa maganarta tsab zai iya wanka mata marin da zai sa ta rasa jinta na awanni.
Da hannu ya nuna mata ?ofa alamar ta fice mishi a gida.
Kamar munafuka ta wuce simi-simi tana gunguni.

Juyowa yayi ya nufi cikin, sai kuma ya Wan juyo ya kalli cikin falon jin alamun akwai mutun a ciki.
Juyowa yayi cikin falo.
Cikin nitsuwa ya kalli Ummi da Shatu.
Da alamun Ummi lallaSata take taci abinci,
Idonshi ya Wan lumshe, haka nan yaji wani irin sanyi har cikin ransa yake jin daWi.

Wani Wan guntun Murmushi yayi bayan ya kalli fuskar Shatun data ke kwaSe har da turo baki.
Wayar Ummi ce ta fara suwa juyowa tayi ta Wan jawo wayar,
tana dubawa taga Umayma cikin farin ciki ta Waga, tare da karawa a kunne kana tace.
"Assalamu alaikum, Umaymah Sheykh."
Cikin tarin jin daWi Umaymah tace
"Wa alaikassalam Ummin Sheykh ina yaran naki? Ya jikin Wiyar tawa"!".
Murmushi Ummi tayi kana tace.
"Alhamdulillah suna lfy, Wiyarki jiki da sau?i gatasu ma kusa dani".
Cikin kula tace.
"Bata wayar".
To Ummi tace kana ta mi?awa Aysha wayar.
Tare da cewa.
"Ga Umaymah".
Amsa Aysha ta yi ciken jin sanyi tace.
"Assalamu alaikum Umayma barka da rana."
Cikin tsananin kulawa Umaymah tace.
"Waalaikumus salam Habibty, sannu Aysha Addana, Allah ya yi miki albarka, Allah ya saka miki da al'khairi, na ji daWi sosai, in sha Allah al'khairi da haske yanzu zai bayyana, sannu kin ji my dear, ki kula da kanki sosai, ki dinka shiga ruwan dumi akai akai, sannan kada ki yi wasa da kunun nan da Ummi take miki, kin ji ?ata ki yawaita cin gashin naman da zatanayi miki da shan kunun har na tsawon kwana uku kinji ko Aysha."
Wata azababbiyar kunya ne ta rufeta.
A kunyace tasa Wayan hannunta ta rufe fuska tana jin inama ?asa ta tsage ta shige cikinta.
Da ?yar ta iya ce wa,
"To Umayma."
Jin Muryarta ya sa Umayma yin dariya don tasan kunyace irin na ?a?an Fulani ne yasa ta yin shiru.
Cikin murya mai baiyana jin daWin da take ciki tace.
"Yauwa Aysha, Allah ya yi miki al'barka."
Cikin sanyi da jin daWi tace.
"Amin Umaymah".
Kana daga nan
Suka yi sallama ta kashe.

Sunkuyar da kanta tayi tare da mikawa Ummi waya, don izuwa yanzu kunya ta gama ji?eta, kallonta Ummi ta yi tana jin dadi aranta tana kuma addu'ar Allah ya nuna musu ranar da ?wai zai fasha, don ga alamun nan suna ta tabbata.
Shi kuwa Sheykh ajiyan zuciya mai sanyi ya sauke kana ya juya ya nufi falonshi.

Ummi kuwa Kitchen ta wuce da tray'n a hannunta.


Ita kuwa Aysha Anan falon ta zauna tana tunani kala-kala musamman akan masarautar sam ta kasa gane mata.
A kullum da kalar sur?ullen da zai bayyanar mata, ko meye ma'anar zantukan da suke yawan yi wanda bata gane masa ba?.
Dazu tajiyo Gimbiya Saudatau da Sheikh maganganunta sun bata mamaki, lallai akwai wani babban al'amari a cikin gidan nan, wanda da sannu zata fahimci menene wannan abu.
Kuma zata tambayi Ummi wani abu ko zata gaya mata, ko ta samu sau?in Tsarkakkiyar dakw cinnzuciyarta.
Tana nan zaune har aka kira sallar la'asar ta tashi da?yar don har yanzun bata jin dadin jikinta.
Bedroom Win ta ta wuce.
Kai tsaye Bathroom ta nufa.

Al'wala ta Wauro don har masallacin masarautar sun tada kabbara.

A hankali take taku sabida har yanzu tanajin jikinta na mata zafin rabuwa da budurci.
Sallaya ta shimfiWa kana itama ta tada kabbara.

Bayan ta idar da sallah ne,
ta kuma mi?ewa a hankali ta fito falo, sabida ta gaji da baccin kwanciya tayi bisa kujera da wayarta a hannunta, tana mgna da Junaidu.

Ummi kuwa tana kitchen.

Murmushi ta Wanyi jin Junaidun na cewa.
"Dan Allah Adda Shatu kicewa su Bappa su dawo haka nan, zamansu a waccar ?asar ya isa.
Ina kewar Junainah, Rugar Bani gaba Waya muna kewarsu dan Allah su dawo".
Gyara konciyarta tayi tare da cewa.
"To Junaidu in sha Allah zan gaya musu, su dawo maka da masoyiyarka dan nima nayi kewar Junnu ina kewar Ummey na".


Ummu dake kitchin ne ta Wan tsagaita daga motsa naman da take fasawa Aysha
Sabida jiyo sallamar Hajiya Mama da Aunty Zuwairiyya.
Haka yasa ta fito tai musu barka da zuwa kana suka gaisa tare.
Sannan tace su isa Aysha na ciki.

To Juwairiyya tace kana tai gaba Hajia Mama na biye da ita a baya.

Ita kuma Ummi ta koma Kitchen dan kawo musu ruwa.

Ba a jima ba sosai Ummi ta debo drinks ta fito da nufin kai musu.
Sai kuma sukayi kiciSis a bakin ?ofar falon Ayshan. Sun fito falon Shatu fuskarsu a murtuke, da alamun ransu a Sace, suka wuce ta.
A hankali ta bisu da ido, tare da tambayarsu.
"Har kun fito ko ruwa baku shaba".
Dukansu babu wacce ta kulata suka fice.
Ajiyan zuciya ta ja ciki da mamaki, sai kuma ta juya ta nufi falon Ayshan.
Tana gab da shiga falon ta ji sautin muryar Aysha na faWa da Wan Waga murya take cewa. "Mitssssss munafukan banza masu fuska biyu mugaye masu ba?a?en zuciya. In sha Allah sai Allah ya toni asirinku!".
Da sauri Ummi ta ?araso gareta tare da ajiye tray'n hannnunta bisa stoll cikin kula tace.
"Lafiya dai Shatu Meya faru?".
Girgiza kai Shatun ta yi cikin jin haushi ta ce
"Ummi nace bana son su, bana son ganin sun shiga rayuwata, bana son su rin?a zuwa inda nake saboda na tsani mu'amala da mai fuska biyu."
Ajiyar zuciya Ummi ta yi tana jujjuya zancen Shatun, da kuma tsananin mamakin takun sakar dake tsakanin Aysha da Hajiya Mama.
Numfashin ta Wan fesar tare da dafa kafaWarta kana a hankali tace.
"Shike nan ki yi hakuri yanzu ai sun fita."
?wafa Aysha ta yi tare da kishingiWa sosai tana mamakin yanda mutanen gidan suka kasa fahimtar komai tana matu?ar mmkin in ance wai Hajia Mama itace Mamansu Sheykh kuma ita har yau bata yardaba bata kuma jin zata yarda har gaban abadan.


Bayan ta idar da sallar isha har yanzun jikinta ba kwari haka tana jin ciwo a gabanta musamman in ta mi?e tana tattakawa, mi?ewa ta yi a ciccije, "Wash Allah na!".
Ta faWa haWe da mi?ewar ta fara tafiya tana gwale-gwale kamar ?ar kaciya, kallonta Ummi ta yi tana nazarinta, bayan ta shige Waki ta tashi ta bita Wakin.

A tsaye ta sameta gaban drower'nta.
Juyowa tayi ta kalli Ummin dake matsowa kusa da ita tare da cewa.
"Aysha kin sake shiga ruwan Wumi kuwa?".
Kai ta jujjuya mata a hankali tace.
"?azu da yamma dai na shiga".
Kai Ummi ta jinjina kana tace.
"Yauwa to kije yanzuma ki shiga ruwan Wumi zakiji sau?in abin sosai."
Ya mutsa fuska ta yi irin na mai jin ba daWi kana cikin sanyi tsce.
"Ummi bana jin daWi kwata-kwata."
Kusa da ita ta matso cikkn kula tace.
"Na sani, amma shiga ruwan Wumin zai tai maka kwarai wajen jin daWinki, don zaki sake sosai, duk wannan ciwo-ciwon zaki daina ji." Kwafe fuska ta yi kamar zata yi kuka.
Yanayinta Ummi ta kalla, ta so yin dariya sai dai kuma danne tare da cewa.
"Yi ha?uri kin ji Ayshs, daure kada ki zama raguwa mana."
"Uhmm".
kawai tace ta mi?e ta shige cikin bathroom.

Ita kuma Ummi ta wuce kitchen tare da Wauko haWaWWen kunun gero wanda ake yinsa na musamman kuma shi ake bawa amaren masarautar haWe da farfesun farararen tattabaru, wanda shi ma wani haWi ne na sirri mai tsuma mace, da yajin da ake barbaWawa akan tattabarun wanda yake ?arawa mace wani WanWano na musamman.

Ita kuwa Aysha ta daWe cikin ruwan Wumin tana jin wani irin daWi na ratsa ta, lumshe ido ta yi, tare da mi?ewa tayi wanko fes kana ta fito.

Tana buWe toilet Win ta ji Wakin na ?amshin wannan gashin tattabarun da Ummi ta kawo mata su har Waki.
A hankali ta matso gefen Ummi dake cewa.
"Yauwa kin fito ko Aysha?".
Kai ta gyaWa mata tare da cewa.
"Eh Ummi".

"To yanzu ya kikaji jikin naki?".
Ummi ta kuma tambayarta.
A kunyace tace.
"Alhamdulillah naji sau?in".
Cikin gamsuwa Ummi tace.
"Toh zo ki zauna ga wannan kici duk za su ?ara miki ?warin jiki." Girgiza kai tayi alamar bazata ciba.

"Yi ha?uri ki daure kici." Ummi ta daWi mata cikin lallami.
Zama Ummi tayi tare da janyo flask Win ta

68 / 72