Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   25 / 72

72K to 75K   out of 214K words

abokinshi Sale suka zo, wurinta, nan take ce musu ita kam bata son wannan gasar da za'ayi kuma t??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????unda an kafe sai anyi sam ita bazata jeba.
Haka dai sukayi ta hira daga bisani suka tafi.

Washe gari ranar Monday kuwa, tun da sanyin asuba aketa gangamin.
HaWuwa a filin da za'ayi shaWi.
Mutanen sun cika ma?il dan anfi yawan yin gasar da safe, sabida da rana duk makiyaya sun tafi kiwo manoma sun tafi daji.
Tuni matasan Fulani na rugogin nesa da Bani ma sun zo.

Bukar kuwa tunda aka fito sallan asuba yaje. Gidan ArWo Yabani, yaso ace an janye gasar tun randa aka shelanta amman ArWo yaki,
still yanzuma da yazo, bayan sun gaisane ya Wanyi gyaran murya tare da cewa.
"Ha?i?a naso a janye wannan shaWi, domin nasan abun bazaiyi daWin ganiba ace Ba'ana na zane Salmanu Wan ArWo ga wannan rugar, amman ka?i ka saurari zancena,
Dan haka ni ba kada wani abu ya faru ku kuskura kuyi kuka dani, duk abinda Wana yayiwa Wanku kune kuka saya mishi da yawun bakinku kun rigada kun san bazaku taSa samun wanda zaifi ?arfin Wanaba".
Shiru ArWo Yabani yayi yana nazartan kalaman Bukar,
ganin yayi shirune alamun ya gama magarsa cikin sanyi ArWo Yabani yace.
"Duniya da faWi take, Bukar Mai kanwa a kwana a tashi watan-wata-rana zakaji zaka gani da idanunka za'a samu wanda zaifi ?arfin Wan ka, Allah zai bijiro da wanda zai iya jure bulalin Wan ka".
Cikin wani irin yanayi Bukar yace.
"Babu mamakin a samu mai iya, jure bulalin, tabbas babu mamaki. Sai daifa abun da bazai taSa yiwuwa bane har illa masha ALLAH ace an samu wanda zai iya nasara a kanshi babushi babu namijin da zai iya sashi jin zafin bulala bare ya zubda hawayen da zaisa ya rasa Shatu".
Wani dogon numfashi ArWo Yabani yaja tare da cewa.
"Uhummmmmm". Daga nan bai kuma cewa komaiba,
Shi kuwa Bukar tashi yayi ya kakkaSe rigarsa ya juya ya tafi yana faWin.
"In dai kunne yaji gangan jiki ya tsira".
Da ido ArWo Yabani ya rakashi, yana maiji a cikin ransa inma ace yanada dama, inama ace zai samo wannan bulalin da Malam ChuSaWo ya gaya musu, da tabbas ya samu hanyar da zai cire mugun iri a garinshi.

A haka Salmanu da abokinshi, sukazo suka sameshi zaune. Bayan sun gaisane Sule ya Wan matso kusa da ArWo a hankali yace.
"Allah rene, duk wuri an taru mu ake jira, shi Ba'ana tun da asuba yana can, yanzu Iro yazo yake ce mana gacan fili ya cika, mu kaWai ake jira, har wasu nata maganganun wai Salmanu ya ji tsoron Ba'ana ya gudu".
Murmushin da yafi kuka ciwo ArWo Bani yayi dafa tsakiyar kan Salmanun yayi kana yace.
"Kuje Salmanu, Allah ya bada sa'a Ubangiji yaga niyarmu na son tseretar da wannan yarinyar daga fadawa auren wannan mushurkin, ta?adiri in Shatu matarkace Allah ya baka sa'a in kuwa ba matarka bace, Allah ya baiyono mata wanda zai zame mata GARKUWA daga faWawa auren wannan azzalumin".
Amin Amin sukace baki Wayansu kana su sukayi gaba.
Shi kuwa ArWo, saida ya jira su Malam Liman Bappa kenan dasu Ahaji Horu, da Ahaji Umaru da Garbati.
Koda sukazo ba Sata lokaci suka nufi, farfajiyar wurin da aka tanada dan shaWi.

Filin ya cika ya batse tako ina mutane zuwa sukeyi arna da musulmai fulani da hausawa da ?abulun, ?achamawa, domin duk yankin nahiyarsu an san babu ta?adiri sama da Ba'ana sabida tunda ake gasar ShaWi da kuma gasar kokuwa yayin nunan sabon gero ba'a taSa cin nasara kanshiba, muddin ya shiga gasa tofa shine da nasara.
Har ta kai da in dai ya Waga hannun to babu mai Wagawa.
To sanadinshi aka hana ShaWi a Rugar Bani, tsawon shekaru biyu sai gashi yau an dawo dashi.

Wannan dalilin ne yasa gaba Waya Rugar Bani ta cika ma?il da mutane maza da mata manya da yara,
Ga mai busar sarewa kuma yana tsakiyar taro inda akabar filin da za'a gobza yanata rere kirari wa Ba'ana.

Isowar su ArWo yasa aka basu hanya har suka iso gaba inda aka tanada musu, kujerun zama. Na bencin katako.
Daga nan manyan Dattawan duk suka Zazzauna.
Bisa ?a'idar gasar ShaWi wanda ya fara cewa yana son yarinya shi zai fara duka, in wanda yace yana sonta daga baya ya ?etare bai zubda hawayeba baiyi kukaba, to sai asa kwanaki sai yaje yayi jinya ya worke daga zabgar da yasha, sai ya dawo ya Wauki fansa, to in ya zana wannan yayi kuka shike nan yayi nasara in kuma wannan ma baiyi kukaba za'a sakeyi har sau uku to nan in babu wanda yayi kuka cikinsu sai yarinya ta zaSi wanda takeso, don anada ya?inin duk wanda ta zaSa, zai iya kare kanshi tunda ?arfinsu yazo Waya.

Bayan an gama dai-dai-ta komai, Salmanu ya cire rigarsa kamar yadda ?a'idar gasar take, ya rage dagashi sai gajeren wondon.
Shi ma Ba'ana ya cire rigarshi ya zama dagashi sai gajeren modo, irin masu zuwa har guiwa Winnne.

To dole a ?a'ida Ba'ana ne zai fara duka, amman da yake ya shiryawa abun sai yace, shi ya amince a fara dashi, kuma shima yau zai rama Ba sai an ware kwanakin zuwa jinya ba.


Nan kuwa take al'kalin gasa Barmuji yace an amince.
Daga nan aka zaro bulalin shaWi na cikin tanWun masarautar ArWo Yabani wanda an ?ara tsumasu suma.

A hankali Barmuji ya mi?a wa Salmanu, bulalin,
kana ya Waga hannunshi ya dawo dashi ta bayan Ba'ana.
Shi kuwa Ba'ana tsayuwa yayi ?am tare da Wan ware sawunshi,
Busar sarewar da mai busan yayine alamun a fara,
Ai kuwa cikin kuzari da jaruma Salmanu ya Wan ja da baya,
kana ya tattaro ?arfin shi ga ba daya, ya Waga kitsetsten bulalan nan, ya ta?ar?ara ya zabgawa Ba'ana shi a tsikar bayanshi,
Wanda a take taron matasan dake wurin suka kurma ihu mai karaji,
Yayinda shi kuwa Ba'ana, ?im ya tsaya kamar ba shiba, domin ko idonshi bai ?ebtaba.
Sake ta?ar?arewa Salmanun yayi ya kuma zabga mishi bulalar a inda ya kima mishi na farin.
Still ihu, taron matasa sukasa, tarin ?abilar Sachama kuma dake wurin sai rurrufe idanunsu sukayi da ?arfi sabida wai bazasu iya jurar ganin ana zabgar jakadan suba.
Mai irge kuwa da iya ?arfinshi yake kware baki yana cewa.
"?aya! Biyu! Uku! HuWu! Biyar! Shida! Bakwai!!!".
Haka yaketa irga duk bulalar da aka kaiwa Ba'ana amman wannan tagadirin mutumin ko a jikinshi kamar dutse ake zanawa ba shiba.

?a'idar bulalin shaWi Hamtsine akeyi.
Haka Salmanu yake ware iya ?arfinsa yana zabgar Ba'ana, yana tsaye ?i?ama. In wannan bulalan ya lauye, sai a bashi wani bulalan.
Har akaje arba'in da takwas ko gezau.
Gaba Waya hankalin mutanen kirki ya gama tashi, domin sun sadakar da nasara ta kubcewa, Salmanu.
Shi kuwa Salmanu tattaro sauran ?arfinshi kab yayi,
ya narka mishi bulala ta 49-50".
Amman shirunshi.
Ihun da kafuran ?abilar Sachama suka sakine ya tabbar an gama, nan take suka shigo filin da gudu ruggumeshi suketayi suna shafa bayanshi, da yayi shati-shati.

Shi kuwa Salmanu gaban ArWo yaje ya zauna, nan aka basu ruwa sukasha gaba Wayansu.
Hutun 30 minutes sukayi aka koma fagen fama.

Da ?arfi mai busan sarewa ya busa alamun a fara,
wani irin kafurin murmushi Ba'ana yayi tare da gyara ri?on da yayiwa bulalar tashi.
Cikin tsananin mugunta ya Wan koma da baya, kana ya Wago bubalar da masifan karfi ya zabgawa Salmanu ita a tsakiyar fatan bayanshi.

Wani irin gan tsarewa Salmanu yayi, sabida wani irin masifeffen azaba mai girgiza zuciya da yaki yana ratsa dukkan sasasan jikinshi.
Bai gama dawowa daga gigi da azabar bulalar forkoba, yaji ta biyu,
Rumtse idanunshi yayi da azaban ?arfi, gaba Waya inda bulalar ya taSashe, harbin kunama yakeji yana ratsashi.
Wani irin numfarfashi yaka lokacin da aka zabga mishi bulala ta goma.

Gaba Waya hankalin mutane ya tashi domin kowa yaganshi yasan yana jin azaba.
Bulala ta ashirin da biyar da akayi mishine ya sashi buWe idanunshi da suka koma jajazir dan azaban da yakeji.
Su kuwa kafuran nan sai ihun farin ciki sukeyi.
Shi kuwa Barmuji zagayawa yayi gaban Salmanu wai yaga ko idonshi ya kawo ruwa,
babu ruwa kam sai azabar da yakeyi tamkar idanun zasu faWo ?asa, ci gaba da irgens yayi.
"Ashirin da uku! Ashirin da huWu!!".
Wani irin tsalle Ba'ana ya buga da iya ?arfinshi ya tsulawa Salmanu bulala ta ashirin da biyar.
Wani irin duhune ya rufe ganin Salmanu, saiga wasu zafafan hawayen azaba sun kwaranyo masa, ihu ya kuma zurma jin zafin bulalar ta isa kan mazantakanshi.

Gaba Waya su Bappa dama matasan kowa rufe ido yayi sabisa dukan da akewa Salmanu dukane na son Waukan rai.

Aysha kuwa tana gidansu kamar kullum tajiyo ihun Ya Salmanu kamar yadda kullum ihun wanda ake gasar dasu ke shaida mata sun faWi.

Cikin kuka konta bisa cinyar Ummey tare da cewa.
"Shike nan Ummey zai kashe ya Salmanu".
Tuni itama Ummey da Inna hawayen suke zubdawa.

A can gidan ArWo Yabani kuwa inna laure Maman Salmanu, kuka takeyi tamkar zata shiWe domin yaranta mata sun zo sun gaya mata halin da yake ciki.


A can wurin gasar ShaWi kuwa, ganin tu?uru Ba'ana so yake ya kashe Salmanu ne yasa,
matasan Fulani sukayi kanshi dan dukanshi yake harda tattakashi kuma tuni ya wuce balali hamsin Win ?a'idar gasar.

Koda matasan Fulani suka shiga dan crton ran Salmanu kawai sai ga ?abilar Sachamawan nan, sun fara zaro makamai sun rufa duk wani ba fulatani da duka da saran wu?a.

Lokaci Waya wurin ya hargitse gaba Waya.
Aka kaure da faWa saida.

Ganin wurin ya hargitse ne yasa,
Gaini yayi saurin kiran hukuma mafi kusa ya sanar musu.
Cikin ?an?anin lokaci kuwa suka iso.
Hakane yasa duk ?abilun ?achamawa suka gudu.
Allah ya takaita faWan baiyi nisa ba, a take Waya daga cikin police Win wanda yake abokin Salmanu ne ya kwashesu suka tafi asibi.

Bayan garin ya lafa, kowa ya dawo haiyacinsa ne.
Isa ?anin Salmanu ya tafi asibiti dan jinyar Wan uwanshi kuma Alhamdulillah da yake ya samu taimakon gaggawa komai yazo da sau?i.

Shi kuwa Ba'ana daga nan izayarsa ta ?aru manufarsa shida ?abilar Sachamawa shine. Su tarwatsa al'ummar fulanin Rugar Bani baki Wayansu.

Zuwa yanzu kuma ko ?udane in dai na mijine to bazai sau?a kan jikin Aysha ba,
sabida asirce, asircen da yakeyi da kuma tsoronshi da akeji.

Aysha kuwa ko zuwa dubo Salmanu ya hanata domin yace muddin taje a bakin ransa.

Yau kwana huWu da faruwar abun, ya da faruwar abun kuma yau ta kasance jumma'a ne.

Kasan cewar jummace yasa gaba Waya makiyayan suka taso kiwo da wuri, sabida son samun jam'in sallan jumma'a.

Iro Waya daga cikin yaran Ahaji Horo, wanda yake yayan Binto da kuma Junaidu.
Kusan shine karshen dawowa kiwo.
ya taso ya taso tarin dabobbin sa a gaba kenan ya haWu da gungun matasan ?achamawa, har sun wuceshi, sai kuma suka bishi a baya, cikin izaya babban cikinsu yace.
"Kai Wan fullo nan garin ubankane ko garin ubanmu?".
Cikin jarumtar jinin fulani yace.
"Gari dai da daji namune tunda iyaye da kakannimu sun saya, in kuma kuna maganar tushen nasabane, to Adanawa Yola dama kewayenta duk namune fulani".
Cikin mugunta Waya daga cikinsu ya kai mishi mari da addan dake hannunshi".
Murmushi Isa yayi cikin hausar fulani yace.
"Kada ka sake dukana".
Kusan a tare suka haWa bakin wajen cewa.
"In mun dakeka sai me?".
A kufule yace.
"Wallahi sai in rama, yawanku ba shine abin tsoro ba".
Ai kafinma ya rufe baki suka haushi da duka,
da sauri ya fara kare kanshi tare da kai musu duka,.
Kamar da wasa su rai shida sun gaza ji da Wan lenge-lengen saurayi matashi Wan Fulani.
Ganin kamar zaici galaba a kansune, yasa, Waya daga cikinsu ya dawo baya-baya ya zaro wukar dake ?ugunshi, da ?arfi ya dawo kan Isa, ya luma mishi wu?an a cikinsa wani irin ?ara isa ya sake, sai dai babu mai jinsa bare ya kawo masa agaji domin.
Dai-dai wannan lokacin duk wani musulmin wannan yankin yana masallacin jumma'a,
Da wannan damar suka samu suka kashe isa,
wanda suka daddatseshi da wu?a.
Daga nan suka kira Ba'ana a waya, nan take ya kaWa shanayen yace. "Yauwa aikinku yayi kyau, yanzu kuyi maza kuyi gaba da shanayen kasar Cameroon, zaku nufa birnin Yahunde kuna isa bakin boda yarana na kasar zasu amshi shanayen ku kuma sai ku dawo, kafin nan ma komai ya lafa baza'a zargekuba".
Haka kuwa sukayi, suka kaWa kan shanu suka fasa daji, suka nufi hanya, shi kuma ya dawo cikin gari ya wuce Wakinsa bayan ya bawa uwarsa lbri.


Koda aka taso sallan jumma'a, anyi mmkin ganin isa bai dawoba, shiru-shiru dai har akayi sallan la'asar babushi, tofa daga nanne hankali ya ?ara tashi.
Cikin kiWima suka fara shiga daji a duba ko lfy bai dawoba.

Ai kuwa nan maza matasan Fulani suka watse cikin daji,
Bayan sun gama bulayin nemane babushi babu shanunshi, suna cikin zagayawan ne Sale yayi arba da gawar Isa dake malale cikin jini.
Nan suka Wauki gawa suka koma cikin gari dashin.

Wannan rana hankali Fulanin Rugar Bani yayi masifar tashi, gaba Waya ma sai ba'amaida hankali kam Satan shanunba,
Hankali ya tashi, Wauki Wai-Wai da akeyi musu ya fara hautsuna musu tunanin,
Gashi kisane da babu wanda za'a iya kamawa, koda aka sanarwa hukar cikin Numan sai suka korasu da case Win, sabida a lokacin da suka zo shigar da report babu musulmi a police cikin officers Win shiyasa suka korasu da batun.
Salmanu wanda shine Wan bokon da kan iya jagorantan lamarinsu, yana gadon asibiti, bisa ?ar?ashin kulawar abokinshi badon hakaba da tuni Ba'ana ya kasheshi.

Koda fulani suka hatsala kamar kullum haka ArWo Yabani ya tarasu ya taushi zuciyarsu, da kuma shawarar, su kai kukanmu ga sarkin Numan Win, tunda ya hanasu samun damar ganin sarkin Nuruddeen Bubayero.

Koda sukaje masarautar Numan Winma abin da akayi musu a police station, fiye dashi akayi musu.

Dole suka dawo suka nade hannun suka kai kukansu ga, Allah, sai dai sun Wauki mataken kare kai da kai, bisa shawarar daddatawa cewa kada makiyayan ko manoma su yarda su rin?a rabuwa a daji ya zama suje tare su dawo tare da hakane zasu gane mai ke musu Wauki Wai-Wai Win.

Yau la'hadi tunda safe, Aysha keta shirin komawa makaranta. Sabida hutunsu ya ?are.

Tafiyan safe takeso tayi shiyasa ta gama shirinta da wuri.

gaba Waya suna tsakiyar gida Yayunta maza sune zasu rakata bakin hanya.

Haka nan taji bata son tafiya ta barsu, tsoro mai yawa ya rufeta Especially in tayi tunani da yadda ake kashe makiyayan.

Dur?ushe take gaban Bappa yana yi mata masiha mai ratsa jiki da zuciya ya kare nasihar tashi da cewa.
"Allah ya miki al'barka Shatu, Allah ya kaiki lfy."
cikin sanyin murya tace.
"Amin Amin Bappa ngd matu?a".
Sai kuma ta kalli Ya GiWinta da ya zuba mata ido tamkar bai taSa ganintaba, cikin sanyin murya yace.
"Yanzu shike nan zaki tafi ki barmu, ki tafi can ke Waya ki zama baki da kowa naki a kusa".
Haka nan kalamanshi ya karyar mata zuciya, sai kuma taji hawaye nason zubo mata.
A hankali tace.
"Ya GiWi bazan daWe ba zanzo".
Cikin sanyi Seyo yace.
"Allah yasa ki samemu in kinzo Win".
Da karfi ?rjinta ya bada wani sauti mai karfi, ta buWi baki zatayi mgna kenan Ya Lado ya Wanyi murmushi cikin sanyi yace.
"To Shatu Ni zan tafi inje in kunce dabobbin, bazan samu daman rakakiba, Allah ya kaiki lfy, ya ?addara saduwarmu kan al'khairi, ki yafe".
Kawai sai taji hawaye na zubo mata, cikin dariya ya Gaini yace.
"To kunga kun sata kuka, Shatu ko dai bakya son komawane?".
Cikin rawan murya tace.
"Inaji bana son rabuwa daku".
Murmushi inna tayi tare da cewa.
"Ai kuwa dole ki rabu damu, domin lokaci yazo".
Ummey dai ido ta zuba musu.
Shi kuwa Ya Lado da murmushi a fuskarshi ya fita yana Waga mata hannu.
Bappa ne ya Wanyi murmushi cikin sanyi jiki yace.
"Maza tashi ki tafi, ki gaida Aminiyarki Rafi'a, Seyo GiWi Gaini ku rakata har bakin titi".
Da sauri suka mi?a.
Ita kuwa Aysha kamo hannun Junainah tayi wacce tayi kasake tana kallonta cikin sanyi tace.
"?anwaliya, sai na dawo".
Kai ta gyaWa mata cikin sanyin da sam ba Wabi'arta bane a hankali tace.
"Addana, bana son ki tafi".
Shafa kan Junainah tayi, kana ta faWa jikin Inna, tana zubda hawaye, sake Inna tayi sannan ta faWa jikin Ummey, murya can ?asa Ummey tace.
"Tashi ku tafi, Allah ya sadamu da al'khairi, Shatu".
Da kuka ta fita, ta barsu jiki a mace.


A hankali suke tafiya tafiya, suna hira, kayan lambu da suka cika mata bakko dashi na hannun GiWi, jarkan nonon kuma na hannun Seyo, ya Gaini kuma, jakar kayantane a hannunshi, da kwaryan kwan zabbi, kamar dai yadda suka saba, suna tafe suna, hira suna gab da bakin hanya.
Ba'ana ya isosu aka ci gaba da tafiyar,
suna isa motar da zata wuce cikin Yola (?adamaya) na isa,
saida suka samata kayanta, kafin, tazo har zata shiga taji GiWi na ri?e da hannunta juyowa tayi ta kalleshi cikin murmushi yace.
"Kinsan abinda zamu iya aikatawa a duniya da abinda bazamu iya aikatawaba".
Kai ta gyaWa mishi alamar eh, murmushi yayi kana yace.
"To ki ?ara yarda zamu zamu zama GARKUWA'nki muddin muna raye."
Murmushi tayi cikin Wan jin daWi tasan akan mgmar auren Ba'ana yake nufi.
Ido ta zubawa Ya Seyo shi kuma sai murmushin shi nan yake mata,
Ya Gaini kuwa hawayene ya cika masa ido shiyasa ya juya ya bata baya.
Cikin sanyi Seyo ya matsota kana a hankali yace.
"Ki sanarwa duniya halinda muka ciki in kin samu dama Aysha, ki sanarwa duniya Fulani ba ?an ta'adda bane ba ?an bindiga daWi bane ba kuma ?an Garkuwa da mutane bane, wasu kesa rigar Fulani ke wanzar da Sarna da wasu ?alilan na mugayen daji."
Cikin rauni ta zuba mishi ido tana kallon kekyawar fuskarsa, da gyaWa mishi kai.
Ba'ana ne ya Wan kalleta tare da mi?o mata damin kuWi yace.
"Mata zanyi kewarki, amman ba matsala duk ?arshen mako zan ke zuwa."
Drivern ne ya katse su da cewa ta shigo su tafi, haka yasa ta juya da sauri ta shiga, yaja suka tafi tana Waga musu hannu, suma basu tafiba saida sukaga motar ta Sace musu.

Juyawa sukayi suka nufi cikin gari.
Shi kuwa Ba'ana da ido ya rakasu a a baiyane yace.
"Zanga ta yaya zaku zama GARKUWA'nnata, dan na fahimci duk bakwa son aurena da ita, toko zanyi mgninku."

Su kuwa basuma juyo sun kalleshi ba.


Ita kuwa Aysha tana komawa ta samu, Rafi'a ta dawo ta gyara musu komai na Wakinsu, to samun Rafi'a da tayine yasa ta Wan samu nitsuwa, ranar kam wuni sukayi suna hira, darema haka sukayi ta hirar yaushe gamo.


A Rugar Bani ( Rugar kikan) kenan nake nufi. kuwa, su Ya Gaini suna komawa suka tafi kiwo, kamar dai yadda suka saba, sukaje kiwo lfy suka dawo lfy.

Washe gari ranar Litinin!


25 / 72