Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   52 / 72

153K to 156K   out of 214K words

kam in ba karatuba."
Cikin tsananin rauni da tausayawa,
idonta cike da ?walla tace.
"Allah sarki, Allah ya bashi lfy".
Karon forko kenan tunda suko fito dashi taji ya amsa addu'a duk da tarin addu'o'in da akayi ta musu sai yanzu taji yace.
"Amin ya Allah". Hakama Umaymah da Jakadiyarsu da Hibba sai dai duk ya riga su amsawa.
A hankali take Wan satan kallonshi a fakaice.

Hibba ce ta janye mata hankali da cewa.
"Aunty Shatu kin gaji kam. muje ki huta, gashi azahar ta kusa ma."
?an guntun murmushi tayi tare da cewa.
"Uhum".
Umaymah ce ta mi?e ita da Ummi kana sukace.
Taso mu tafi, yanzu Hibba zata cikaki dan zance."
Cikin murmushi Aunty Juwairiyya tace.
"Ayyah Umaymah ku bar mana ita mana".
Ummi ce tace.
"Lokacin sallafa ya ?ara to".
"Hakane kam". Juwairiyya tace tare da Waukar Foodflaks dake kan dinning table, tabi bayansu tana cewa.
"Hibba Wauko sauran!".
To tace kana ta suggumi sauran tabi bayansu.

Nan suka bar Jabeer da Ya Jafar Win.

A babban falon suka zauna.
Aunty Juwairiyya da Hibba suka ajiye Foodflaks Win bisa Dinning table,
kana suka dawo tsakiyar falon.
Umaymah ce ta mi?e tare da kallon Shatu, tace.
"Taso mushiga ciki, kiga tsarin wurin naku".
Mi?ewa tayi cikin alamun gajiya, domin zagaye masarautar JoWa babban aikine mai zaman kanshi. Donma su sun saba, ita kuma bafulatanar dajine tafiya baya bamu tsoro.
Bayan Umaymah tabi, ta gefen Dinning area ta Wan ratsa da ita,
Suka shiga cikin kitchen, juyowa tayi ta kallesu Ita da Hibba,
"Nan shine babban kitchen Win ki, dake babban falonki.
Shine wanda in kinada aiki mai yawa, kamar na salla ko azumi, ko zakiyi ki aikawa surakanki.
Hadimai zasu iya shigowa su tayaki."
cikin fahimta tace.
"Toh". Hibba ce ta Wan ?ara so shigowa ciki tare da cewa.
"Kai wanga kitchen badai girmaba, gashi komai a tsare gonin kyau. Kalarsa green and white komai na ciki gwanin kyau".
Murmushi suka Wan yi kana, Umaymah ta juya dasu.
Daga nan cikin kitchen Win ta gefen dama akwai wata ?ofar da sai ka hau stpes huWu.
A gefen ?ofarne wani datsetstsen Fridge mai girma yake kwance.
Haurawa sukayi kana Umaymah ta tura ?ofar ta shiga.
Store ne mai zaman kanshi.
akwai komai na bu?atar rayuwa, sai dai ba mai yawa bane.
Shatu ta Wan kalla tare da cewa.
"Ga kuma store Winki. Nan za'a ke aje miki duk wani abun bu?ata".
Kai ta gyaWa, kana suka fito.
Wata ?ofar daketa hannun hagu ta nuna mata suna buWe wa suka fito.
Sai gasu bisa wata baranWa mai girma, kana can ?asan barandar fulawine da kuma pompona ke jere iya ganinka,
Daga sama kuma igiyoyin shanya ne da a ?alla sun kai huWu.
sai saman barandar kuwa, injin wanki ne.
Nan dai ta nuna mata komai na wurin kana suka dawo cikin gida.

Suna shigowa falo. Sheykh na shigowa.
A nitse yake taku, kanshi na sunkuye yana kallon wayarshi da yake lallatsawa.
Umaymah ce ta Wan bi bayanshi tare da cewa.
"Zo nan Shatu".
Cikin zuba bayansu ido. Ta Wan gyaWa kai, tare da taka sawunta a hankali tabisu.
Hibba kuwa gefen Aunty Juwairiyya ta zauna.
Shi kuwa yana shiga falon nashi, ya juyo ya Wan kalli Umaymah cikin kwaSe fuska yace.
"Umaymah, Dan Allah ni bana son ana shigomin da wasu ababen cikin Side na, bare rayuwata, me wancan abun da kika kira zaizo yi anan?".
Ido ta kafeshi dasu hakane, yasa yayi ?asa da kanshi.
tare da shigewa bedroom yana cewa.
"Dan Allah iya kar abun can falo".
?eyanshi Umaymah ta zubawa ido.
"Wato ma wai wancan abun, lallai ma Jazlaan".
Juyawa tayi ta Wan le?o a corridor ta hangota, murmushi tayi tare da cewa.
"Taho mana".
Kai ta kuma gyaWawa tare da ?ara saurinta tafiyarta a hankali.

Suna shiga falon, tayi wani irin Soyeyyen ajiyan zuciya mai sanyi,
sabida wani irin masifeffen sanyi mai gauraye da ?amshi mai Wan karen daWi da taji ya bugu jiki da zuciyarta.
lumshe idonta tayi, ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?kana ta buWe su a hankali jin Umaymah na ce mata.
"Nan falonshi ne, namusamman ba kowa ke shigo mishi wurin kai tsaye ba.
dan ko Juwairiyya bata shigo mishi nan, kana akwai ?annenshi ?an uba maza da kuma Jalal basa shigo mishi nan.
Jamil kan shiga in baya nan in zai dawo shikeyi mishi shara da gyaran wurin.
Jalal kuwa yakan iya shekara ?afarshi bata tako nanba.
Sai kuma Ya Jafar Win sa, shi kam bashi da hijabi da Side Win Jabeer, yakan shiga har cikin Bedroom nashi wani zubin har bathroom.
Sai kuma Haroon da Ibrahim su dama, dan su yasa aka gina sama wai masau?insu in sunxo.
To ammanfa in sunzo a Wakinshi suke ko motsi zasuyi tare zasuyishi.

Sai kuma yayan Hibba, Hibbab shi na hannun damanshi ne.

Dan haka daga yanzu in dai yayi tafiya kece, zakiyi aikin da Jamil keyi".
A hankali tace "to".
Haura step Win Dinning area Win shi dake falon wanda akayiwa ?awanya da wani irin labule mai masifar kyau.
Labulen ziri-zirin igiyoyine masu sarkafe da jeren duwatsu masu kama dana Daimond. wasu farare wasu Sky blue wasu Royal blue. suna da wani irin haske mai wal-wal. Cikinsa kuma.
Wani badaidaicin Dinning table ne mai kujeru shida nan uku nanma uku sai wani fridge ma daidaici. Gefensa show glass ne mai kyau wanda yake Wauke da cups and plates and spoons and forks Mug. Da dai sauran ?ananan abeben bu?ata.
sai woshing hand Baby, dake li?e a can gefe.

sosai tsaruwan wurin yayi kyau, komai Sky blue and white. Abun sai ya zama kamar a duniyar taurarin yake yadda walwalin ke haska ko ina.
Falon kuma yanada Wan karen duhu, domin saida Umaymah ta kunna musu wuta.

Bedroom nashi ta nuna mata da yatsa.
"Ga makwancinsa, sai kuma wancan Wakin shi ba mai kwana a cikin Wakine na musamman babu mai shiga ciki sai shi ni LamiWo Galadima, domin Wakin aikinshi ne".
Ita dai da to take bin Umaymah, sabida sanyin falon yana gab da sata kuka.
Allah ya sani bata son sanyi ko kaWan. Ta kuma lura su kuma mayun sanyi ne.

Falon suka fito. Nan dai suka samu su Hibba nata hira da Ummi.
Side Win ta suka nufa.
Cikin kula tace.
"Ga Side Winki ga falonki ga kitchen Winki."
Ta ?arishe mgnar suna shiga kitchen Win. A hankali take kallon komai na Kitchen Win kalarsa Pink and white. Sosai tsarin wurin yayi kyau.
daga nan Dinning area Suka shiga ta nuna mata kana suka fito falon.
Suka shiga bedroom Winta komai ya tsaru.
Kuma komai sabone fil gwanin burgewa.
juyawa Umaymah tayi tare da cewa.
"Wancan Wakin kuma masau?i nane in nazo."
Cikin Wan murmushi tace.
"Ayyah". ?ofar Bathroom Umaymah ta nuna mata tare da cewa.
"Azahar tayi shiga kiyi al'wala kiyi salla sai kizo muyi Lunch".
to tace kana Umaymah ta juya ta fita.


Shi kuwa Sheykh Jabeer, yana shiga ya maida ?ofar Bedroom Win ya rufe shiyasa Umaymah bata gwada shiga da itaba.

Shi kuwa bathroom ya wuce wonka da al'wala yayi, ya sauya kaya. Kana ya fito cikin shigarsa ta musamman ya nufi. Masallaci.


Koda sukayi salla suka fito.
Falon ganin bata fito bane yasa, Umaymah cewa Hibba.
"Jeki kiramin Wiyata". Da sauri Hibba ta juya ta nufi Wakinta.
Kwance ta sameta bisa sallayar da tayi salla, ta kife kanta cikin hijabin jikin nata,
bisa dukkan alamu kuka takeyi.
jin shigowar Hibba ne yasa tayi saurin share hawayenta,
tare da juyowa,
cikin mamaki Hibba ta zuba mata ido.
A hankali tace.
"Aunty Shatu meya sameki kike kuka".
Murmushin ?arfin hali ta ?a?alo tare da cewa.
"Kuka kuma Hibba".
Cikin sauri tace.
"Eh mana gashi idonki yayi ja".
Mi?ewa zaune tayi da kyau cikin sanyi tace.
"No bacci na fara, shiyasa kikaga hakan".
Kai Hibba ta gyaWa kana tace.
"To taso mu tafi falo Umaymah tace kizo muyi Lunch".
Hannu tasa ta Wan shafa cikinta tare da cewa.
"Kamar na ?oshi fa".
Murmushi Hibba tayi tare da cewa.
"Tab ai Wlh taso kawai mu tafi, dan Umsymah bazata barki bakici abinci ba".
To tace kana ta mi?e ta ninke sallayan. Sabida gajiya ne da bege da kewar yan uwanta ne ya sata kuka da kuma jin yunwar ta mutu a cikinta.

Suna fitowa su Umaymah duk suka mi?a, Dinning area suka nufa.

Bayan duk sun zaunane, Ummi, ta mi?e da nufin saka musu abincin.
Da sauri Aunty Juwairiyya ta mi?e tare da cewa.
"A a Ummi ki huta bari in saka mana".
Foodflaks Win dake kusa da ita ta ture tare da jawo wanda suka shigo dasu.
Ummi ce ta Wan kalleta tare da cewa.
"Ya kika ture wancan?".
Baki ta Wan taSe tare da cewa.
"Uhummm wai fa Gimbiya Saudatu ce, ta turowa amarya abinci dan salon munafurci".
Wani irin kallon ?asa-?asa Shatu tayi mata tare da zuwa abincin data buWe ido, cikin mgnar zuciya take cewa.
"Uhumm wai zata cewa wata muna fuka, muguwa Itan ko meye sunanta!?".
Sai kuma ta kalli Umaymah jin tana cewa Juwairiyya.
"Ni zubo min na gidan Hajia Mama naga tu?e??en tuwone da biyar zogale".
To Aunty Juwairiyya tace kana ta zuba mata.
da sauri Shatu ta Wan kalli Umaymah lokacin da aka saka mata mal-malan tuwon farar Wanyar shinkafa,
tare da miyar a side sup.

Sai kuma ta juyo ta kalli Hibba da Ummi da tuni sun ja plate Win da Aunty Juwairiyya ta saka musu. Couscous and vegetables sup, mai Wan karen kyau da ?amshi.

Da sauri ta jujjuya kanta lokacin da Aunty Juwairiyya ta turo mata na plate Win gabanta, cikin sanyi tace.
"La da baki saminba". Da mamaki Umaymah tace.
"Sabida me?". Sunkuyar da kanta tayi tana tunanin.
suma ta yaya zata hanasu cin abincin. jin Ummi ta kuma mata tambayar da Umaymah tayi matane yasa ta Wan kallesu.
Ta buWe baki zatayi mgnar kenan.
Sheykh ya shigo da sallama, a bakisa.
kusan a tare, suka amsa masa.
A fakaice ya Wan kalli Aunty Juwairiyya kana yace.
"Kije ki bawa Ya Jafar mgninshi".
To tace tare da mi?ewa da sauri ta fita.
Ita kuwa Shatu, wata nannauyan ajiyar zuciya ta sau?e.
Kana tasa hannunta ta ture plate Win gaban Umaymah tare da jawo na gaban Ummi da Hibba,
Ido suka zuba mata cike da mamaki.
Ita kuwa cikin sanyi ta kallesu tare da cewa.
"Dan Allah kada kuci wannan abincin.
Kuci wancan ne".
Jabeer dake ?o?arin shigewa falonshi ne, a ranshi yace.
"Uhumm lallai kam wannan abun wato itace ma zata zaSa musu abinda zasuci".

Hibba kuwa da sauri tace.
"Aunty Shatu abincin gidan Gimbiya Saudatu fa kike cewa muci."
Ganin kallon mamaki da tuhuma da Umaymah da Ummi keyi matane yasata yin ?asa da kanta cikin jin tausayinsu a ranta tace.
"To in bazaku cishiba, Umaymah bari ni in shiga kitchen nida Hibba yanzu zan girka muku duk abinda kukeso".
Ko inda suke Sheykh Jabeer da yanzu ya fito zai wuce baiba, yacewa Umaymah.
"Zan fita".
Juyowa tayi ta kalleshi tare da cewa.
"Allah kiyaye hanya, ya bada Sa'a".
Amin Amin yace, hakama Ummi tai mishi addu'a.

Ita kuwa Shatu kanta na sunkuye,
Umaymah ce ta Wan kalleta cikin nazartan yanayin ta, da yin tunani hakafa Wazuma ta?i shan madarar Barka da shigowa masarautar JoWa da Hajia Mama ta bata,
ta kuma amshi tuppar da Gimbiya Saudatu ta bata,
yanzu kuma tace kada suci abinci Juwairiyya.
Wannan abun shi yafi komai tsayawa Umaymah a rai.
Yaya daga shigowarta zata kasabto wasu hasashen a ?wa?walensu.

Kai ta jinjina tare da cewa.
"Hibba sa mana abincin Gimbiya Saudatu, muci".
Jin hajane yasa Shatu jawo Foodflaks Win ta fara saka musu.
Ita kuwa Hibba ta kwashe plate Win da Juwairiyya tasa musu ta kaisu kitchen.

Nan sukaci abincin kowa da abinda ke ransa.

Ita Shatu bataci na kirki bama.
Sabida ta lura da kallon da Umaymah keyi mata kamar da tuhuma.

Suna gamawa suka tattare wurin ita da Hibba.
tuni su Umaymah kuwa suna falon.


Suna gamawa suka fito falo.
da sauri ta kamo hannun Hibba suka wuce falonta har bedroom Winta.

Suna shiga Haroon, Jamil, suka shigo.
Shigarsu ba jimawa Jalal ma ya shigo.
Nan sukayi ta hira.
to ganin yanzu ta shigane yasa Umaymah bata kirata dan tazo taga ?annen mijin mataba.

Suko. Suna cin abinci suka fita sabida kiran sallan la'asar,
daga nan kuma basu kuma shigowa falonba sai kusa goma na dare kafin nan kuwa tuni Shatu da Hibba sunyi bacci ma.


Washe gari ranar Laraba, da safe.
Aunty Juwairiyya ta shirya musu breakfast kamar yadda ta saba, koda su Umaymah basa nan, abincin Sheykh a sashinta yake duk da ma, yakan iya wata biyar baisa abincin nata a bakinshi ba.
sai dai Ummi Jakadiyarsu ta Wan dafa mishi irin ababen da yafi so yaci lokuta da dama kuma na rayuwarshi da LamiWo yake cin abinci a Side Win kakarsa Gimbiya Aminatu shiyasa bai fiye cin wanda ake kawowa sashinsa ba.
Jalal Jamil Ummin suke cin wannan abincin.
To sashin Hajia Mama kullum za'a kawo Side Win shi.
Hakama gidan Barrister Kamal da Dr Aliyu yawanci suma sunasa ana kawo mishi.
kana gidan Baba Nasiru ma,
yawanci ana kawowa.
Especially kamar yanzu da su Umaymah ke nan.

To yauma haka abin yake tako ina an kawo musu breakfast, na maraba da zuwan amarya.

Koda suka zauna cin abinci.
Kamar jiya da dare, haka yauma Shatu ta Wan kalli Aunty Juwairiyya cikin hikima tace.
"Aunty Juwairiyya asaka mana na gidan Gimbiya Aminatu".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Wato kema irin mijin nakine, kuna son girkin Gimbiya, kunsan nata yafi naku na zamani daWi da lfy".
Murmushi Shatu tayi cikin jin sanyi da daWin basu fahimci manufarta ba.

Sun fara ci kenan.
Jalal Jamil suka shigo.

Dama Haroon, Ya Jafar, oga Sheykh Jabeer suna falonshi.
can Ummi ta kai musu nasu karin.

Cikin murmushin Umaymah tace.
"Yauwa Jalal kuzo nan, kuga Aunty Amaryankun."
Matsowa gefenta Jalal yayi tare da kallon Shatu a fakaice kana yace.
"Uhumm aini na santa, taje ta tasa min Wan uwa gaba har cikin Office dinshi tana mishi ihu a kai".
Cikin sauri ta Wan kalleshi tabbas ta ganeshi ta kuma tunashi Umaymah ta Wan kalla tare da cewa.
"Sherri ne, Umaymah ni banyi ihuba".
Murmushi Jamil yayi tare da cewa.
"Eh ai ba ihun kukaba, shi da mijin naki duk bauWaWWun mutanene, da zaran kin Wan yi musu mgna da murya a sama to cewa sukeyi, wai kayi musu ihu".
Ya ?arishe mgnar yana kallon corridor fitowa falonshi.
Murmushi Hibba tayi tare da cewa.
"Ga baki ga tsoro".
Aunty Juwairiyya ce ta nuna musu wurin zama tare da fara zuba musu abincin.
Ita kuwa Shatu murmushi kawai ta Wan yi, sai taji hawaye na neman cika mata ido.
Zamansu hakan ya tuna mata yayunta, ko ina suke? Wani hali suke ciki? Ko ya jikin Ummeynta? Ya Junainah keyi da kewarsu.
Ba ya Lado, Babu Ya Gaini, Babu Ya Seyo, babu Ya GiWi, sannan nima an kawoni nan an cusani cikin wani irin bahagon gida mai wuyar ganewa".
A hankali tasa tafin hannunta tana share hawayenta cikin hikima.
?an juyowa tayi ta kalli. Umaymah dake cemata.
"Shatu, ga Jalal da Jamil tagwaye ne, sune ?annen Sheykh Jabeer da suke binshi
yanada wasu ?annen Affan baya ?asar.
Sai Imran Wan amaryar Hajia Mama mom.
sai kuma yayunsu mata, kin san su ai ko? Rumaisa da Rumana".
A hankali ta gyaWa kai alamar eh.
Ita kuwa Umaymah su Jalal ta kalla tare da cewa.
"Ga Auntyn ku, matar Hammanku".
Jamil ne ya Wan yi dariya tare da cewa.
"Allah ya Waiyiba".
Murmushi sukayi tare da cewa.
"Amin Amin."

Nan dai sukaci sukasha kana suka dawo falon.

Kamar jiya haka yauma suka wuni.

Umaymah da Ummi na yawan yi mata dukkan bayanin komai na Side Winta.


Washe gari ranar. Al'hamis, da yamma taja Hibba suka koma falonta.
Cikin yin ?asa da murya tace.
"Yauwa Hibba sammin wayarki.
Wallahi na nemi tawa har na gaji ban ganiba tun a Side Win Gimbiya Aminatu".
Da sauri Hibba tace.
"Dama kinada wayane? Kuma ya Sata baki faWawa Umaymah".
Da sauri ta jawo hannun Hibba tare da cewa.
"Ina zakije?."
"Zanje in gayawa Umaymah mana".
Ta bata amsa tana cire code Win wayarta-ta tare da mi?a matashi, da sauri tace.
"A a ki bari ke dai bani aron taki bari in kira Bappa na".
Ajiye mata wayar tayi bisa cinyarta kana ta wuce ta fita.
Ita kuwa Shatu, da ido ta rakata, jin tana ta rabkawa Umaymah Kira tun kafin ta fita.
Ajiyan zuciya ta sau?e tare dasa hannun ta Wauki wayar.

Jujjuya wayar tayi tare da mi?ewa ta nufi bedroom Winta.
Number Bappa ta saka, kana kirashi.
tare da kara wayar a kunne mugu Waya ana biyu, aka amsa kiran.
Wani irin murmushi tayi jin muryar Junainah tana cewa.
"Bappa! Bappa ga wayarka ana kiranka".
Da sauri tace.
"?anwaliya".
Cikin wani irin mamaki da jin daWin Junainah tace.
"Laaaaah Adda Shatu, kece? Ina kike? Adda Rafi'a tazo jiya wai tana neman wayarki baya shiga, Bappa yace mata ai anyi miki aure, taita kuka tace to ya batun karatunki,
Bappa ma ya nemi number ki baya shiga.
Ina kika ajiye wayar ne to Adda Shatu".
Cikin sanyi tace.
"Wayar ta Sata ne Junainah".
Cikin tura baki tace.
"To mijinki ya saya miki mana".
Ido ta lumshe tare da cewa.
"Ina Ummey na? Ya jikinta?".
Cikin sauri tace.
"Ummey tana na Kitchen, yanzu jikinta da sau?i tana mgna kaWan-kaWan, ko Wazuma itace tace.
"Bappa ya kira mata ke!."
Cikin tsananin jin daWi tace.
"Alhamdulillah, kai mata wayar".
Da sauri ya juya ta nufi kitchen tana cewa.
"Ummey! Ummey ga Adda Shatuna".
Da sauri Ummey ta fito, ta amshi wayar.
Cikin murya mai cike da sanyi tace.
"Aysha na!".
"Wasu zafafan hawayene, suka zubo mata,
Cikin rawan murya tace.
"Na'am Ummey na! Ya jikinki?".
Ajiyan zuciya ta sau?e tare da cewa.
"Jiki da sau?i, Shatu yaushe zaki zo?".

Bappa da yanzu ya iso daga rakiyar da yayiwa Rafi'a ne, yayi murmushi tare da cewa.
"Bani wayar nan".
A hankali cikin girmamawa ta mi?a mishi wayar.
Shi kuwa amsa yayi tare da karawa a kunne.
jin muryar bappa yanayi mata sallama ne yasata jin sabbin hawaye masu masifar Wumi, sabida tausayinshi.
Duk da tsufanshi mugayen ?abilar Sachama basu barshiba, sun kashe mishi babban Wan shi.
Kana sun tafi da uku, sun barshi cikin zulumin suna raye ne ko sun mutu? A ina suke? Me akayi musu? Me sukeyi? Sannan itama data rage anyi mata wani irin bahagon auren da yafi kama da na mulkin mallaka.
Muryarsace ta katse mata mgnar zuci da takeyi da cewa.
"Shatu kina Lfy ko?".
Murya na rawa tace.
"Lfy lau Bappa, amman bana jin daWin gidan, ina kewarku, ya jikin Ummey na? Ya lbrinsu su Ya Gaini an samu wani lbrin ko har yanzu shiru? Ya Ba'ana bai muku komai bako? Ya tafi ne ko yana nan?".
Murmushi yayi tare da cewa.
"To Shatu wacce tamSaya Waya zan amsa miki'.
Tana kuka tace.
"Duka".
Cikin hikima da jin?ai irin na iyaye yace.
"To sai kinyi shiru kin dena kuka".
Da sauri tasa hannu ta share hawayenta tare da cewa.
"Na bari".
Taku biyu yayi zuwa uku kana yace mata.
"Ba'ana bai mana komaiba! Ya gudu ya bar ?asar ma baki Waya! Jikin Ummey ki da sau?i sosai! Su ya GiWi munata addu'a in Sha Allah, in Allah ya yarda zasu baiyana garemu da izinin ubangiji.
Kafuran nan kuma mun rigada mun karya ?arfi su yanzu bazasu sake samun damar cutar da muba, in Sha Allah munfi ?arfi su."
Sai kuma ya Wan tsagaita jin, tana murmushi mai Wan sauti alamun jin daWi,
a hankali yaci gaba da cewa.
"Rafi'a tazo, nayi mata bayanin komai, kuma in ta dawo zata zo, in an barta zata shigo".
Da sauri tace.
"Zan gayawa Ummi ta sanarwa sarkin ?ofa in tazo a barta ta shigo".
Cikin danne ainihin tarin ?unar watsewar gidanshi

52 / 72