Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   16 / 72

45K to 48K   out of 214K words

kiyi min TRANSFER Win 1k ta asusuna na Jaiz domin samun shiga Special Group, wanda cikin kwanaki ?alilan za'a gama littafin da izinin ubangiji. Ga asusun kamar haka 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, 1k ne SPG sai ki turo min shaidar biyan
ki ta wannan number 09097853276.


Gareku iyayen ?an mata da za'a aurar, akwai sittin amare mai kyau na gyaran jiki, bisa farashi mai sau?in, akwai na manyan robobi akwai na ?ananan robobi, akwai haWin masu jego, da na maida tsohuwa yarinya, sayan na gari meda kuWi gida, in kayan gyaran kikeso ki fara min text message ta inbox ta wannan number 09097853276 sai ki gaya min kaya kikeso, kana sai ki kirani to nan zan Waga kirankin sai muyi mgn zaki turo kuWi ta ACCOUNT number ni kuma zan tura miki kaya ta mota, duk garin da kike a Nigeria ina aikawa, in dai ba lungu yayi sosaiba. Kana mutanenmu mazauna ?asashen ?etare kamarsu Saudia, India, Gabon, Ghana, Niger, Cameroon, da dai sauransu in kinada dalili kayana na zuwa can cikin salama. Ina saida kaWan-kaWan ina kuma bada sari.



A dai-dai kan kofin madarar ya sa hannunsa, alamum zai mishi zaSi kenan, murmushi yayi dan ya samu damar, da zai tserewa tsarinsu. Cikin ihima da sanin makaman kariyar kai daga jin kunya ko yin abinda zai Sata ran wani, ?afarshi ta dama dake kusa da hannun Haroon yasa cikin hikima ya bugi hannun Haroon da ke gab da Waukar kofin.
ture hannun yayi da babbar yatsarsa, wanda, hakan yasa hannun Haroon ya bugi kofunan da Wan karfi, sai gashi duk sun tuntsure a tsakiyar tiren madarar da zumar kab suka malale cikin tray Win.
A tare suka zubawa tray idanu gaba Wayansu.
Sitti kuwa wani irin kallo tabi Madarar dashi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, cikin iya taku da kamalarsa murya a mutunce ya kalli Haroon daya kafeshi da idon tuhuma, cikin harshen larabci da kamala yace.
"Harooon meyasa baka da nitsuwa?".
Cikin tarin mamaki Haroon ya gwalo ido tare da cewa.
"Haaahh".
sai kuma ya kalli Sitti da ta kwaSe fuska tamkar zata kurma ihun takaici.
Shi kuwa Sheykh Jazrah ya zubawa ido, ganin yadda ta zuba mishi kekkyawan idanunta, wanda suke she?in hawayen dake nuni da zazzafan son da takeyi mishi.
Kauda kwayar idanunshi yayi, da sauri.
Jannart kuwa hannun Sitti ta kamo ganin zata jawo tray.
A hankali Sheykh Khalillullah wanda yake ?anin Sitti ya gyara zama cikin sakin fuska da murmushi ya kalli jikan nasu, nitse yace.
"Laaba'as". Dib-dib haka ?irjin Sheykh Jabeer Habeebullah ya fara bada sauti, fahimtar kakanun nashi zasu Waura zabin kan, fahimtar lafazin Haroon.
Shi kuwa Haroon, wani irin murmushi jin daWi yayi.
Shi kuwa dottijon nan, ido ya zubawa ?a?anshi da jikokin ?a?an nashi, da wasu jikokinshi. Kallonsu yake yana nazartansu.

A hankali wayar Sheykh Jabeer ta fara bada wani sauti mai masifar sanyi da daWin sauraro, sautin gwauraye yake da kukan sassanyan tsuntsaye.
da sauri ya zaro wayar a al'jihun tattausan al'kyabbar tasa.
Ganin sunan Maimartaba Nuruddeen ne, ya sashi sakin wata sassanyan ajiyan, cikin ladab ya kalli Sitti, kana a hankali ya kalli Sheykh Abdulkareem, cikin sanyi da nitsuwa yace.
"Mai martaba Nuruddee ke kirana, bisa alamu da babbar mgna domin baya kirana haka banza".
Murmushi dottijon yayi, domin ya fahimci hanyar fecewa, Sheykh yake nema, hakan yasa ya mishi izinin tafiya.
Cikin sauri Sitti ta yun?uro da niyar yin mgna, sai kuma tayi shiru, sabida nuni da tayi shirun da mahaifinta yayi mata.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, a hankali ya yun?ara, ya mi?e ya nufi hanyar fita bayan yayi musu, su huta gajiya.

Kai tsaye Side Winsu ya wuce.
Yana shiga kai tsaye bedroom ya wuce, gyara al'kyabbar jikinshi yayi kana, ya zauna bisa wata tattausar doguwar kujera.


A nan ?asar kuma, cikin faWar masarautar maiartaba Sarki Nuruddeen.

Bayan Jamil ya fita, wurin da yayiwa su Bappa Masauki,
kai tsaye, sashin kakanin nashi ya nufa.
Bayan an mishi isone, ya shiga, ya gaisa da kakan nashi kana ya ?ara da cewa.
"Mai martaba, akwai ba?i ma bu?atar kulawarka, suna tsumayinka".
Murmushi mai cike da kamala farin dottijon bafulatanin yayi, cikin ratsin sarauta yace.
"Yau ka zama, sarkin fada kenan, kaine mai yiwa ba?i iso ko?, ko dai matane ba?in dan nasan ta nan kafi ?arfi". Ya ?arishe mgnar da yanayin tuhuma.

Kanshi ya Wan shafa, kana a hankali ya girgiza kansa tare da cewa.
"A,a mazane dattawan Fulanin dajine,".
Ido ya Wan zuba mishi kana yace.
"Kaje kace a kula dasu, gani nan zuwa yanzu".
Kanshi ya Wan rusunar tare da cewa.
"Nasa an basu dukkan kulawar da zasu, bu?ata, zuwa yanzu sunfi bu?atar ganinka fiye da komai".
Kai ya Wan jinjina alamar to.
Yun?urawa yayi tare da cewa.
"A fito lfy".

"Allah yasa".

"Amin Amin". Yace kana ya fita.

Shi kuwa Sarkin ya fara shirin, fitowa fada.


A can sashin Sheykh Jalal ne, zaune da Ya Jafar, Aunty Juwairiyya na gefenshi.
karatu yakeyi kamar koda yaushe, tun jiya ya?i barin sashin Sheykh, koda aka kira Sheykh Jabeer video call, ya ganshi sai yayi ta kuka.
Wannan abun shiya ?ara tada hankali Sheykh Jabeer.

Yana yawan, bin Jalal, wanda mutane ke zaton ko dan tsananin kamannin da Jalaluddin keyi da Sheykh Jabeer Winne yasa, yake ganin kamar shine, to sai dai sam Jalal baya iya mu'amalantar Babban yayan nasu, kamar yadda Sheykh keyi har yake sama mishi nitsuwa, sai dai shima yana iya yinshi.


Shigowan Hajia Mama da hadimanta ne, yasa Juwairiyya, jin rauni, a take hawaye ya cika mata idanu. A duniya bata da babbar matsala sama da larurar mijinta.
Ita kuwa Mama, gefenshi ta zauna, cikin sanyi ta kalli, Jalal da fuskarshi ke murtu?e kamar ko yaushe,
cikin baiyanar damuwa tace.
"Ya za'ayi ya samu gamsuwa da kulawarka, a yadda kake haWe fuskarnan tamkar wanda aka sanarwar labarin mutuwar uwarshi, ba haka Sheykh ke mushiba, yana kula dashi, da tausayawa da sakin fuska tunda yasan larurar haukace dashi, amman kai ko yaushe kana nan kamar boss".
Sai ta kuma kalli Jakadiyarsu Kana, ta kalli Jamil dake waya da alamun da budurwarshi yake mgna, hararanshi tayi tare da cewa.
"A haka kuke samawa kanku tabon nunawa a rayuwarku, shi wannan ya zama, mahaukaci, shi Jalal ya zama tantiri Wan shaye-shaye, kai baka da aiki sai bin matan banza. Kuna samin ciwo a raina, shima kanshi Sheykh duniya ta zata fara zargin cewa mazinacine shiyasa ya?i yin aure ya zauna, sin?itin fakitin. Shi kuwa Affan in banda shashanci da tarin ?uruciya babu abinda yasa a gaba.
Ya kukeso inyi, ya kuke son mahaifinku yayi? Yana da yaya maza har ku shida, amman ku biyar manyan duk kun zama, ababe masu taSo a idon duniya, ya za'ayi yayi mararin gadar mulki a hannun mahaifinshi, tunda yasan shi bashi da masu gadarsa, a kusa,ku duba, Imran da yake uwarsa ta tambaWaku, ta nesan taku da mahaifinku, sai ta kusanta Wanta da mahaifin naku.
Shiyasa mahaifinku keta ?in amsar sarautar har sai randa Imran ya mallaki hankalinshi, ku kuwa kun zama ababen kyarata. Yaya zanyi da raina.
Shiru sukayi gaba Wayansu,
Shi kuwa Ya Jafar sai ?ara sautin karatun yayi. Yanayi yana zubda hawaye.


Shi kuwa Jalal, shiru yayi yana ri?e da hannun Jafar Win.
Jamil kuwa katse kiran yayi.
Affan kuma wanda dama tare suka shigo, fuska ya Wan kele, cikin irin matsayin da ?an auta kedashi a wurin iyayensu yace.
"Mama, shifa zato zunubine koda ya kasance gsky. Ki dena jifar Mommy da batun wai ita ta tambaWamu, ya za'ayi keda kanki ki rin?a suffantamu da marasa nagarta mu dai gsky ba a tamSaWe mukeba,
Menene a cikin mulki da sarauta, Mama akwai wani mulkine matabbaci a duniya banda mulkin mahaliccin mu, in ma Imran ya gaji sarauta menene a ciki Wan uwanmu nefa".
Cikin sanyi ta girgiza kanta a hankali tace.
"?an uba dai ba Wan uwaba".
A tare suka zuba mata ido baki Wayansu.
Aunty Juwairiyya kuwa, ruggume yarta kawai tayi, tana jin ranta na suya.

A cikin fada kuwa, tun tuni Maimartaba ya fito, yana shigowa suka gaisa dasu Bappa ya amshesu a mutunce, cikin kulawa, da mutuntaka, bayan sun gaisa Winne suka koro mishi jawabin abinda ke tafe dasu.
Shiru mutanen fadar sukayi baki Wayansu, sai muryar Ardo Bani, da yake ?are zancensa da cewa.
"Babban tashin hankalinmu, kullum Wauki WaWWayan da akeyima yaranmu da tsoffinmu.
Kana a sace dabobbin mu, in mun kai kukanmu ga hukuma ko masarauta sai ayi burus damu, koma a ?ara mana da cin zarafi ko ?azafi. To gashi yanzu ankai matakin ana sace mana yara, ko gawarwakinsu ba'a bar mana, shiyasa mukayi tattakin isowa gareka adalin shugaba, ka duba lamarinmu."

Wani irin zafi da ?una ne ya cika zuciyar, Maimartaba Lamido, zalumci yayi yawa.
Gyara zaman babbar Al'kebbar sarautar dake jikinsa ya Wan yi, yana maijin ?una da tafasa a zuciyarshi, fargaba da tsoron, ha?in bayin Allah'n da aketa kashewa ya cika mishi zuciya, sabida sanin shine sarki kuma shugaba, ga duk wani mutun dake yankin.
Wani nannauyan numfashi yaja mai ?arfi.
Juyawa yayi ya fuskanci maga takardar fadar tashi, cikin bada umarni yace.
"A rubuta takarda a aikawa Haman-?achama cewar ina bukatar ganinshi, da gaggawa.
Kana ya tabbatar kafin ya isoni yankin da yake mulka babu sauran zalumci, ko ?abilanci!".
Cikin cika umarnin da maga takardar ya Wan rusuna, tare da cewa.
"An gama ya Mai alfarma Sarki Adalin Sarki."
Waziri, Galadima, Wambai, Sarkin fada, kana da sarkin dogarai, duk, shiru sukayi sabida a zahiri ake iya han?o tsantsar tashin hankali da Sacin rai a fuskar adalin shugaban nasu.

Su kuwa su Bappa sosai sukaji sanyi, a zu?atansu, sabida nuna kulawarshi garesu,
cikin iya sarrafa harshe da tausasan laffuza mai martaba sarkin Nuruddeen Bubayero JoWa yace.
"Kuyi ha?uri, ku gafarceni, bani da labarin dukkan abinda ke faruwa daku, sai yanzu, naji daWi da kuka nemeni, da matsalarku, In sha Allah ni kuwa zan Wauki mataki, da izinin ubangiji koda belbelun dake cikin shanunku baza'a sake kashesuba, bare dabobbin ku, bare a kai ga rayukanku. Zan kirayi GARKUWAN FULANI, yanzu, zan sashi maza ya taho ya dawo ?asar sa,
Domin shiga lamuranku nauyin a kanshi yake."
Sai kuma ya Wan numfasa kana ya kalli wani bafadensa dake tsaye bayanshi yanayi mishi fifita da maficin da akayishi da gashin kekkyawan Wawisu.
Cikin bada umarni ya umarceshi daya koma gefe,
Da sauri ya rusana ya koma gefen.
Shi kuwa Sarki Nuruddeen, wani Wan kekyawan matashi dake gefen damanshi ya kalla tare da cewa.
"Imrana, kiramin Sheykh Jabeer."
Kai ya Wan rusunar kana yasa hannu ya amshi wayar da Kakan nashi ke mi?a mishi.
Amsa yayi, kana ya kira Sheykh Jabeer, wanda shi kuma a dai-dai lokacin yana gaban Sheykh Aliyu, Abdulkareem, Jabeer, Sitti, Jazrah, Haroon. Da dai sauran ahlin nasu.

Wanda kiran ne yasa ya samu ya fece daga tarkon da ake naWa mishi.

Jin wayar tayi ringing har ta katse ba'a Waga bane, yasa Imran Wan rusunar da kanshi tare da cewa.
"Wata ?il baya kusa da wayar."
Kai ya jinjina mishi tare da cewa.
"A a zai kira, bayan amsa kirana yanzu zai kira".
Kai ya gyaWa alamar gamsuwa.
Suko su Bappa duk suna zaune cikin kamala.

Shi kuwa Sheykh kamar yadda ya saba, hakane baya amsa kiran kakan nashi, sai dai ya bari in tayi ta katse sai ya kira, shiyasa, yanzuma ya bari saida ta katsen sannan ya kira.


Gyara zamansa yayi tare da kara wayar a kunnensa na dama.

Imran kuwa yana ganin kiranshi yayi maza ya amsa,
cikin tarin girmamawa yace.
"Barka da hantsi, Hamma Jabeer".
A can gefen Sheykh Jabeer Win kuwa, ido ya lumshe cikin yanayinshi da sun rigaya sun saba yayi shiru.
Da sauri Imran ya kuma Wan rusunar da kanshi yace.
"Afwan Sheykh Assalamu alaikum ".
Murya can ?asa yace.
"Wa alaikassalam".
Cikin Wan tura baki Imran ya kuma maimaita mgnarsa ta forko.
"Barka da safiya, Hamma Jabeer ya, Sitti?".
A ta?aice yace.
"Alhamdulillah".
Da sauri Imrana yace.
"Masha Allah, ga LamiWo".
"Na'am". Yace a takaice.
Shi kuwa Imran mi?awa kakansu wayar yayi.
A hankali Sheykh ya Wan buWa laSSansa cikin zazza?an sautin muryarsa yace.
"Assalamu alaikum".
Murmushi mai cike da so da ?aunar jikan, nasa yayi tare da amsa sallamar tasa. Gaisawa sukayi, bayan sun gaisa ya tambayi labarin su Sitti da ?anennenta da kuma mahaifinta, sai kuma ya kora mishi jawabin abinda ke faruwa a jihar tasu.
Kana, ya Woro da cewa.
"Ka dawo, kayiwa lamarin tubkar hanci". Cikin sanyi yace.
"In sha Allah. Ina nan tafe, nanda kwanaki uku. Ina jajanta musu, abinda ya faru, kuma in sha Allah.
hakan bazai kuma faruwa ba.

Da haka sukayi sallama.

A can garin Numan kuwa cikin Rugar Kikan.

Gaba Waya garin shiru yayi, dan wannan abunda ya faru yayi masifar shiga jikinsu.
Da dama maza matasanmu sun tafi kiwo, kamar yadda suka saba, rayuwar yau da kullum.
Saura sai irin dattawan da aka bari, da mata da yara maza da mata.


Cikin garin Bonon kuwa, gaba Waya, matasan garin dama ?auyuka gefensu na ?abulun ?achamawa, duk sun hallara wuri Waya, suna cike gaban dodon tsafinsu, wato Bonon Win, giyar burkutu mai Wan karen tsami da wari, suketa sha, tamkar zasu fasa cikkunansu.
Yayinda gefe guda kuma, ma?erar dake gefe wasu matasa su ne ma?era keta wasa ababen faWansu, kamarsu wu?a?e, Adda, sitaka, barandami, mashi, kibau, da dai sauran mugayen makamai, sai she?i sukeyi.

Suna cike a wurin, Ba'ana ya iso, cikin wata shigar rigar sa?i.
Hanya suka rin?a buWa mishi, hardai ya isa ga sarkinsu, dake zaune gefen dodo sun. Zama yayi kusa da sarkin nasu ya sasu a gaba,
Cikin harshen Sacamancin yace.
"Ku hanzarta, ku shiga, duk matasansu majiya ?arfi, sun tafi kiwo. Dottijan su kuma sun tafi, kai gulmarku, ga Sarkin su wannan karon basu tsaya ga sarkinku na nanba, ina da ya?inin kuma za'a sauraresu a can.
Yanzu matansu da ?a?ansu, ?anana mata da mazane suka rage a garin.
Sai wasu dattawansu dake, dakon dawowar magulmatan can.
Kuyi maza, kushiha kafin su dawo, ku share garin kab.
Ku kashesu gaba Waya babba da yaro mace dana miji."
Da sauri wani daga cikin su yace.
"Harda gidansu Shatu?".
Cikin izaya yace.
"Harda su, domin Mata, bata nan, ku kashe kowa nata, ta hakane zata dogara dani kaWai tunda bata da kowa nata a duniya, dole Ni zan zama mijinta ubanta yayunta ?annenta uwarta, in zama Garkuwarta in zame mata duniyarta ta hakane zata yarda nine Waya gatanta kuma duniyarta, ba tare da ta zargeniba, a hankali wata rana in sata tayi ridda, musha giya, muyi tsafi tare da ita, bazatayi min musuba, mu haifi Wanmu na forko mu bawa dodonmu yasha jininshi yasa mana al'barka a aurenmu".
Wani irin ihu da sowa na tsantsar jin daWin bayaninshi sukayi baki Wayansu.
Hakama dodonsun, saida ihunshi ya firgitasu baki Wayansu.
Dariya mai amo mara daWin ji. Sarkin nasu yayi, kana ya busa ?ahon dodonsun, alamun ya basu izinin tafiya.

Nan fa duk suka rin?a shiga, cikin ma?erarnan suna Waukan makamai, suna nufar garin Rugar Kikan (Rugar Bani) kenan a guje...


Cikin garin Shikan kuwa, Bani rana ta fara tasawa, mata masu zuwa tallan nono cikin garin Numan, suka fara Waukar ?orarensu, suna fita garin.
Yara maza da mata kuwa, wasu na wasa wasu na Webo ruwa, wasu na Webo kayan lamSu.
Yayinda wasu kuma suka dawo break dan tara tayi.

Cikinsu kuwa harda Junainah.

Tafe take da saurinta da Wan tsalle-tsallenta tana rataye da yar jakarta,
da sauri ta tsaya ganin Junaidu a gabanta rike da kwanWon zabari wanda yake cike da ?a?an itatuwa.
Murmushi ta Wanyi tare da sunkuyar da kanta cikin surutunta tace.
"Har naji tsoro!".
ta ?arishe mgnar tana kallonshi,
Murmushi yayi mata shima cikin son ?arinyar yace.
"Haba dai, tsoron me kuma zakiji, tunda gani, babu abinda zai sameki muddin ina raye, zan zame miki Garkuwa".
Da sauri tasa hannu ta rufe bakinta tare da cewa.
"Kai! Kai! Ya Junaidu, sunan Babanmufa ka kira".
Murmushi mai kama da dariya yayi kana yace.
"Au na manta ashe sunan surki nane".
Kai ta gyaWa mishi kana tasa hannu ta amshi, nonon inabin da yake mi?a mata,
baki ta buWe da nufin sawa a baki,
sai kuma ta tsaya tare da tura baki jin yana ce mata.
"No kada kici ba'a wonke bafa."
Sai kuma ya ajiye kondon, ya amshi inabin ya Wan gangara, gefe kaWan ya wonkeshi a bakin ruwan wutsiyar Kogin da yayiwa Rugar tasu ?awanya.
Ya tahowa tana kallonshi.

Koda ya iso mi?a mata yayi,
kana ya Wauki kondon, ganin still tanata kallonshi ne ya sashi cewa.
"Ya dai?".
Kai ta kauda tare da fara tsinkar ?a?an inabin tana afawa a baki tana taunawa,
Murmushi ya kumayi ganin yadda ta lumshe idonta.
A hankali tace.
"Ya Junaidu kayi kyau sosai yau, har kamar ka fini kyau".
Dariya ya Wanyi kana yace.
"Yo dama ai na fiki kyau".
Ma?e kafaWa tayi tare da cewa.
"Uhum a a kam".
A haka dai suna tafe suna hira.

Can cikin gida kuwa, Ummiy ce zaune bisa kujera ?ar tsuguno da buta a gabanta, alamun al'walan sallan walaha, zatayi.
Inna kuwa, da wasu ma?otansu uku Biba, Hari, da Innawuro. suna zaune bisa taburma a tsakar gidan. Suna amsar gaisuwa.

Can cikin garin kuwa su Alhamdulillah Manu dasu Siddine da dai sauran dattawan garin ne zaune a fada.
Sai yara daketa kai komo.

Da sauri su Siddi suka mi?e tsaye ganin, matasan maya?an ?abilar Sachama, sunata shigowa garin tako ina gabas da yamma kudu da Arewa, bisa dukkan alamu zobe sukayiwa garin
Kana ga zurma-zurman makamai masu tsawo tamkar ra?umai. Sai she?i sukeyi.

Cikin Waga murya, Alhaji Manu yace.
"Kai lfy? me haka?".
Ganin sun nufosu gadan-gadan ne yasa, suka mi?e gaba Wayansu, kowa ya fara, neman makari, to amman ina, basu da zato ko sanin za'a far musu, shiyasa basu da shirin komai na kare kai.
?aya daga cikin sune, yace.
"Mu gudu kashemu sukeda shirin yi ba tare da laifin komaiba".
Siddine ya kuma Waga murya tare da cewa.
"To in mun gudu matanmu da yaranmu fa".
Ihun da sukajiyo tako wani sashi na garinne ya tambatar musu, ana karkashe su.
Gudu suka farayi kowa ya nufi hanyar gidanshi dan Waukar matakan kare kai.
Sai dai ina basu da hanya duk inda suka Sullo sai sunci karo da, maya?an.

Lokaci Waya garin ya ruWe ya birkice kota ina sai ife-ife da gudun ceton rai da makiyayan Rugar Kikan keyi.

Wani irin sauti mai baiyana azabar fitan rai Alhaji Manu yayi, lokacin da wani kafurin ya caka mushi sitaka a ?ahon zuciyarshi.
Siddine ne ya juyo da azaban razani, amman sai shima ya saki wani sauti mai gigitarwa jin azaban sara da sukan da akeyi mishi.
Garifa ya kacame,
Hadi ne babban Wa ga Alhaji Haro mahaifinsu Junaidun Junainah, ya nufi cikin gidansu da azama,
Yana cike da fargaba, da tashin hankali domin wasu irin ihu da yake jiyowa a cikin gidan nasu.
Yana kusa kai ya samu, makasan suna cike a gidan.
Suna ta'addanci, sun kashe kowa na gidan.
Ganin haka ya juyo yana juyowa. Yayi kiciSis da abokinshi Sale, yana tafe jini na zuba an farka mishi ciki.
Cikin magagin mutuwa yake cewa.
"Hadi sun kashe kowa na garin nan sai wanda baya nan.
Hadi

16 / 72