Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   46 / 72

135K to 138K   out of 214K words

a nan.
Kana a Wan Waga kafa har sai an gyara mata inda zata zauna, kamar ko wacce amarya.
Sannan kada kuyi mishi mgnar auren bare ita yarinyar,
in anyi haka fushinsa bazai tsanantaba, zaici gaba da al'amuran rayuwarshi, tunda shi mutum ne mai ibada da kuma aiyuka".
Murmushi Haroon yayi tare da cewa.
"In dai baza'ayi mishi mgnarta ba, to wallahi mancewa zaiyi da ita da babinta ma gaba Waya".
LamiWo ne ya gyara zama tare da cewa.
"Ya isa".
Murmushi Umaymah tayi sabida ta lura har yau su LamiWo basu gama sanin Jabeer da halaiyarsa ba.

Shi dai Jadda nan ya jadadda musu cewa, kada suyiwa Sheykh Jabeer mgnar sai an gama gyara komai na sashinta.
Ko gaisuwar su bari sai bayan kwana uku a zagaya da ita cikin Masarautar.

Nan dai sukayi sallama suka, tafi baki Wayansu.

Suna tafiya, Umaymah ta koma Wakin da Aysha take, nan ta samu Ummi na zaune da ita. Nan ta zauna ta suka Wan yi hira ganin alamun gajiya da bacci a tattare da itane yasa, sukayi mata saida safe suka fita suka tafi.

Ratsawa sukayi wurin Gimbiya Aminatu suka mata saida safe kana suka fita suka tafi.

Cikin tsananin jin daWi suke tafiya, har suka iso bakin.
Mashigar sashinsa, cikin nitsuwa sukaci gaba da tafiya.
Shiru ba motsin komai suna gab da isa bakin ?ofar, suka tsaya cikin zaro ido, suka kalli Laminu da Gimbiya Saudatu, cikin haWe fuska da zafi Umaymah tace.
"Aoozubikalimatillahi taaa'ammati minshirin makala?a!."
Cikin tsantsar tsanarta Gimbiya Saudatu tace.
"A kanki hegu masu jajayen kunnuwa".
Tana faWin haka taja hannun Laminu suka fita.
Su kuwa Umaymah da sauri sukayi ciki.

A falo suka tsaya. Ba kowa a falon haka yasa tayi sauri ta nufi arear'n Side Win Jabeer, a falo ta samu Haroon konce bisa kujera.
Yana ganinta ya tashi zaune.
Cikin gimtse dariyarshi murya a hankali yace.
"Yau duk kayan ahlin masarautar JoWa sai an yagesu baki Wayansu."
Ya ?arishe mgnar yana nuna mata ?ofar Wakinshi.

A hankali ta kutsa kai cikin Wakin tare da yin sallama.
Can ta hangoshi kan gadon yana konce rigingine, idonshi a lumshe,
a hankali takeyin taku tana nufo inda yake.
tare da mgnar zuci.
"Wato harda sharrin Haroon zayiwa Wan Umaymah".
A hankali ta zauna bisa bedside drower'n. Idonta ta sau?e bisa goshinsa, cikin mamaki ta juyo ta fuskanceshi da kyau ganin yadda Goshinsa ke....!





By
*GARKUWAR FULANI*Ido Laminu ya rumtse da ?arfi.
Ganin Sheykh Jabeer yayi wani irin tsayuwa na ingarman, jarumin namiji nitsuwa da kamala, sai lips Winshi dake motsawa a hankali yana ambaton Allah.
Shi kuwa Ba'ana cikin tsantsar mugunta, ?eda, da zalumci ya Wago bulalar nan da azaban karfi ya zabgawa mishi ita a inda ya zabga ta forko.
Wanda yasa gaba Waya mutanen wurin suka rumtse idanunsu.
Especially LamiWo da tawagarsa,
Shi kuwa Sheykh Jabeer, zuciyarshi ta rigada ta gama tafasa, idonshi baya ganin komai sai wani irin azabebben duhu, kunnuwanshi basa jin komai sai sautin muryar mahaifinshi da kuwa Umaymah. Da suke bashi umarnin cewa dole yayiwa LamiWo mubaya'a.
Wani irin azaba mai girgiza ran mutun a jikinsa yakeji yana sukarshi har cikin ?ahon zuciyarshi, sai dai duk wani sihiri na jikin bulalar duk baya tasiri a jikinsa illa dai dafin kuna min kam tabbas yana jinsu.
Barmuji wanda shine al'?alin gasar kuma mai irga bulalin.
Da sauri ya rumtse idanunshi lokacin da Ba'ana ya tsulawa Jabeer bulala ta biyar waccee, a take jini ya fara tsastsafo duk inda ta konta.

ArWo Bani kuwa da Bappa da Alhaji Haro da Alhaji Umaru, da Sarkin aska, da sauran dattawan garin da kewayensa wani irin fargaba ne da taraddadi mai firgitarwa suke ciki.
Gaba Waya bakunamsu addu'o'in ne a ciki.

Laminu kuwa tuni yanata Waukar duk abinda ke faruwa a ?ar ?aramar na'ura sa. Yanayi yana dariyar farin ciki.

Jalal kuwa da sauri ya rumtse idanunshi kana ya koma baya.
Jamil kuwa cur-cur yake zubda hawaye ganin yadda jini ke tsastsafo wa, a tsakiyar bayan Hammansun.
Haroon da kanshi tsoro ya rufeshi, yaji ranshi ya fara zargin anya kuwa bada biyu aka haWa wannan gasarba.

Muryar Barmuji ce ta cika wurin gaba Waya da alamun tsananin tausayawa yace.
"Goma!".
Alamar anyi mishi bulala ta goma kenan.
Shi kuwa Sheykh Jabeer Idonshi a buWe suke, sai dai basa ganin komai sai duhu na tsantsar ba?in cikin abinda sashi yayi cikin bainal nasi a sashi tsayuwa da Wan kampai,
Idanun nashi suna buWe ras.
Launin su kuma ya sauya daga farin zaiba, zuwa jazir tamkar wanda maciji ya watsa dafi a cikinsu.
Gaba Waya fararen faratun yatsun hannunshi sun rine sunyi jazir tamkar wanda aka ?unsawa jan lalle.
Ji yakeyi tamkar tsikarinshi akeyi da bakin allurai.
Tabbas duk da bai san dafin kunama ko macijiba, ya gane cewa akwai gubar dafin wani abu a jikin bulalin da ake tsula mishi tamkar za'a zare ranshi dasu.
duk ta inda hudar gashi yake a jikin shi, ji yakeyi tamkar ana soka mishi ?arin kunamai.

Bukar kuwa, wani irin murmushin farin ciki yakeyi, ji yakeyi kamar ya fito ya taka rawa dan farin cikin ganin halin da jikan Sarki ke ciki.

Muryar na rawa Barmuji yaci ga da irge.
"Goma sha Waya! Sha biyu! sha uku! sha huWu! sha biyar!!!."
Cikin sauri Haroon ya iso inda suke, hankali a tashe ya kamo hannun Barmuji cikin sanyi yace.
"Kai kasheshi zakuyi ne? Bulalin har nawa ne za'ayi?".
Cikin rawan murya Barmuji yace.
"In sha Allah bazai mutuba, bulali Hamsin za'ayi a ?a'idar gasar, ba abinda zai sameshi tunda har gashi ya juri bulali 15 wanda a tarihin gasar Ba'ana babu wanda ya taSa jurar koda bulala biyar ne".
Da ?arfi Hashim ya zaro ido tare da cewa.
"50 wannan ai zalumci ne".
Da sauri Galadima ya mi?a ya nufi tsakiyar taron ganin Jalal ya nufi inda suke gadan-gadan bisa dukkan alamu kamo hannun Wan uwan nashi zaiyi yaja su tafi.
Da sauri Galadima ya kama hannunshi cikin Waga murya yace.
"Kai Jalaluddin ina zakaje?".
Cikin faWa yace.
"Zan ja Wan uwana mu tafi, in ku bakwa sonshi bakwa da bu?atar shi, mu muna sonshi munada bu?atar shi, a rayuwarmu domin mu dai shine farin cikinmu, shine silar zamanmu cikin masarautarku, da tuni kun koramu tamkar karnuka, shine kuka haWa Deel a kashe mana shi, to kuji ku sani zamu bar muku masarautarku in dai ganinmu ne bakwa tson yi."
Cikin faWa Galadima yaja hannunshi yaje ya ajiyeshi gaban LamiWo.
Yana mai jin tausayin yaran.
Da ?arfi Barmuji yace.
"Ashirin da biyar! Ashirin da shida!".
Zuwa wannan lokacin gaba Waya jikin Al'Sheykh Jabeer Habeebullah yayi ruWu-ruWu. Tuni farin boxes dake jikinshi ya cika da jinin dake gangarowa ta bayansa da cikinsa, inda bulalin suke taSawa duka.
Babbar yatsarshi ta ?afar damanshi da yatsun hannunshi kawai yake motsawa, wanda suke nuna alamun yana nan da rai daram da kuma haiyacinsa.
Bayan wannan babu abinda yake motsawa a jikinshi,
Cake ?asar garin yakeyi da yatsar kafar tashi.
yatsun hannunshi kuma, motsasu yake yana tasbihi dasu, wanda shima cikin zuciyarshi yake ambaton Allah dayi mishi kirari da kyawawan sunayenshi.
Zafin da yakeji a jikinshi tabbas ya wuce zaton mai zato.
Taune lips Winshi na ?asa yayi da fararen ha?oranshi tamkar zai hudasu, sai dai har cikin ?ashin ha?oran nashi yake jin azabar dafin dake cikin wadannan bulalin masu masifar siddabaru, sai dai babu wani siddabaru da yayi tasiri a kanshi ko a jikinsa domin shi Allah ya ri?e, Ba'ana kuwa tsafi ya ri?e.
Wannan gasace tsakanin gsky da ?arya, bawai gasar caWi bane kamar yadda mutanen wurin ke kallo.
Haka yasa duk da safin wannan bulalin sam basu kai zafin da yakeji a ranshi na sashi ya tsaya gaban dubban al'ummar garin da Wan guntun wonWo a jikinshi ba.
Allah ya sani shi mai kunya ne, kuma shi mai suturce kanshine, shida kanshi yana jin kunyar kanshi da kanshi.
Baya zama haka ko a Waki sabida yana tuna in mafa ya kaWaice yana tare da Ra?ib da Atib Mala'iku makusantan Wan adam, wanda in ka bar tsiraicinka ma su kauda ido sukeyi daga gareka.
Shiyasa shima yake kauda ido daga kan kanshima bare wani.
Allah ya sani babu wani abu da aka taSa yi mishi a duniya ya ?ona mishi rai sama da wannan abun.
Tabbas da an barshi hakama, yafi jin zafin hakan sama da waWanan bulalin.
A ranshi yake wani irin kuka mai cin rai yana mgnar zuciya.
"Anci min zarafi an wula?antani an tozarta ni a gaban waWan mutanen da wasun cikinsu zindigan kafuraine. An barni tamkar mara kima da galihu, wannan shine iya ma?urar zalumcin da akayiwa rayuwata a karo na biyu".
Sam baya jin zuciyarshi tanada raunin da zai iya zubda hawaye kan bulalin nan shiyasa ko zafinsu bai zame mishi abin zubda hawaye ko ihu da bakiba ko gudu ko wani motsi.

Zuwa yanzu hankalin kafuran ?abilar Sachama ya yi masifar tashi domin wannan shine karo na forko a rayuwar tarihin Ba'ana da ya zana mutun bulalin shaWi har talatin da takwas baiyi ihuba bai zubda hawayeba, bai sumaba, bai faWi ba, bai guduba.
Kai wannan abun yayi tsamari wannan wanne irin mutum ne, anya kuwa mutun ne ko al'jan.

Ya Salmanu kuwa, cikin tsanani kuka cur-cur da hawayenshi sabida yasan azabar da Sheykh Jabeer yakeji.
Juyawa yayi ya fuskanci gabas, sujjada yayi tare da fashewa da wani masifeffen kuka mai cike da rauni murya na rawa yake cewa.
"Ya Haiyu ya ?aiyum, ya ziljalali wal ikram. Ya Allah ka ?arawa wannan bawa naka dauriya da jarumta, ya Allah ka bashi ikon jure wannan azabar, ya ubangiji ka sanyaya mishi masifun dake jikin waWanan bulalin, ya ubangijin tali?ai ka hana wannan mugun mushirkin bawa naka samun nasara, ya Allah ka kare musulminka kan wannan kafurin matsafin da baya salla".
Kuka sosai ne yaci ?arfin Ya Salmanu.

Bappa ma wani irin raunine ya rufeshi tabbas kowa zaiyi tunanin Jabeer yana jin azabar duniya.
Sai dai kasan cewarsa Jarumin namiji haka yasa babu wata alama da ya nuna na yana jin zafi ko ciwo.
Sosai kuwa hakan ya tada hankalin kafuran.

Lamido da Galadima kuwa kallon juna sukayi tare da yin murmushi irin nasu na manyan fada, murmushi ne mai manufofi.

Jalal kam kife kansa yayi a cinyar LamiWo ya saki kuka mai sauti.

Haroon ma hawaye yakeyi zuwa yanzu.
Hankalin duk tawagar LamiWo yayi masifar tashi, ganin yadda wani irin azabebben zufa ya tsinkowa Jabeer tun daga tsakiyar kanshi, zufar nan take gangarowa har kan jikinshi gaba Waya, saida ya ji?e yayi jilak tamkar an kwaza mishi ruwa bokati Waya.
Wani irin karkarwa jikin shi, ya farayi yana tsuma yana Sari, gaba Waya jikinshi karkarwa yakeyi.
wanda duk fulanin wurin suka fahimci cewa tabbas.
Zai iya cinye gasar zai kuma iya faWuwa.

Shi kuwa Sheykh Jabeer daga can cikin naman jikinshi yake jin jikinshi na rawa tamkar mazari.
Zuciyarshi kuwa wani irin duka takeyi, wanda muddin kana kusa dashi zakaji yadda take bada sautin harbawa.

Hankalin Ba'ana yayi ?ololuwar tashi, ganin har yayi mishi bulala ta arba'in da biyar.
Baiyi Waya daga cikin ababen da zai hanashi cin gasar ba.
Ganin hakane ya juya a fusashe, bulalin hannunshin ya wurgar kana ya sunkuyo kam ranWar bulalin tsafinshi, bulali biyar ya zaro, ya haWa su ya dam?esu cikin hannunshi.
Cikin azaban ?arfi ya Wagosu ya yarfawa Jabeer su a tsakiyar kanshi.
Wani irin azabane ya ziyarci ?o?on ranshi, wanda hakan yasa yaji wani irin fitsarin azaba yana cika mishi mara.
Jinine ya tsinko ta kafaWunshi, yana bin cikinshi,
bai gama jin azabar waWannan ba ya kuma zarma mishi su a cinyoyinshi.
Da sauri ArWo Bani ya mi?a tsaye daga sujjadar da yayi jin ihun mutane, suna cewa.
"Ka karya dokar gasa ba'a haWa bulali biyuma bare biyar kasheshi zakayine.
Cikin wani irin isa ta jarumta da jinin sarauta Sheykh ya buWe kwayar jajayen idanunshi,
Barmuji da yayi kansu da nufin kama hannun Ba'ana ne,
Ya Wagawa hannunsa alamun daka dakatarwa alamun ya tsaya kada ya iso ya bar Ba'ana yayi komai ba komai.
Cikin tsananin mamaki duk al'ummar wurin suka zuba musu ido ganin jarumta ziraran miraran tana tsaye da sawunta.
Shi kuwa Barmuji cikin rauni yaci gaba da nufosu yana cewa.
"A a Sheykh bazan barshi ba, ai ya karya ?aida da dokan gasa".
Ya ?arashe mgnar yana isowa inda suke.
Cikin tsananin takaici da firgicin ganin faWuwa a karo na forko na rayuwarshi, Ba'ana
Ya zargawa Barmuji bulalin da ?arfi.
Wani azabebben ihu Barmuji ya narka tare da fara tsalle yana yarfa hannunshi yana zagaya wurin hawaye na shatata mishi sabida azabar da yakeji, cikin ihun azaban bulalin da aka yarfa mishi sau Waya, fitsari na tsiyaya a sawunshi yace.
"Arba'in da takwas!".
Ta gabanshi ya dawo ya shauWa mishi na arba'in da tara, wanda yasa Jamil yin tsalle yazo gabanshi cikin kuka yace.
"Kasheshi zakayi ne?". Cikin tsananin azabar da yakeji ne ya buWe jajayen idanunshi ya kalli ta inda yaji muryar Jamil.
Hannunshi yasa ya ture Jamil gefenshi.
Shi kuwa Ba'ana wani irin ihu yayi tare da buga tsalle yayi sama kana ya zabga mishi bulala ta hamsin kuma ta ?arshe.
Wani irin dogon numfashi Jabeer yaja tare da buWe idonshi kan fuskar LamiWo daya iso hango dishi-dishinsa yana nufo inda suke.
Wani irin ihu da karaji Ya Salmanu ya kurma da azaban ?arfi,
Wanda ya haWe ya gauraye da busar sarewa da al'gaita da dukan gamgar jami, aka saki a tare.
Wani irin sowa da ihu da hargowane ya cika illahirin gaba Waya Rugar Bani,
Wanda mutane fulani suketa rawan farin cikin jarumtar Jabeer,
ArWo Bani da sauran dattawan rugar kuwa gaba Waya sujjadar godiya sukayi wa Ubangijinmu sarki gagara misali.
Gaba Waya an zagaye Sheykh Jabeer.
Wanda shi kuma ya juyawa Haroon baya alamun yasa mishi suturarsa.
Da tsananin rawan jiki.
Haroon ya wore al'kyabbar, ya zura mishi ita kan jikinshi daketa zubda jini.
Yana jin Haroon ya saka mishi Al'kyabbar ya Wago kafaWunshi ya gyara zaman al'kyabbar.
Jiki na rawa yasa hannunshi ya kama gefe da gefen bakin al'kyabbar ya hadesu a jikinshi ya suturce kanshi ya kare kanshi.
Barmuji na shirin kamo hannunshi yayi maza.
Ya Waga mishi hannunshin kana ya juya ya nufi inda motoncinsu ke jere.
Jalal da na ganin haka yayi maza yayi gabanshi.
Marfin motar ya buWe mushi tun kafin ya iso.

Cikin taron kuwa, tuni Ba'ana da matasan ?abilar Sachama, sun Wauki ranWar bulalin tsafinshi sun nufi Bonon da tarin ba?in ci dan ganin Sheykh Jabeer bai faWi gasarba, kuma ga mutanen fulani daketa yi musu dariya da ihun rashin nasarar su.
Hakan yasa suka tafi dan sun sani a ?a'ida sai Jabeer yayi jinya ya worke da azabar da Ba'ana ya shayar dashi kafin ya dawo Waukar fansa.

Cikin taron kuwa cikin kukan rauni ArWo bani ya rusuna gaban LamiWo da tawagarsa murya na rawa yace.
"Sauran Waukar fansar da zaiyi a duk sanda ya worke a duk sanda yaga dama, fatana kuyi shirya bulalin tarihin masarautarku, domin ramuwa akan wancan ta?adirin da baya jin koda harbin bindiga baya shigarsa.
Ina yakun farin cikin nasarar da Jabeer yayi a yau, ina kuma fatan yayi nasara a ramuwar da zaiyi a wannan kuma in yayi nasarar mu zaku taya farin ciki, ko ba komai zamu rabu da wancan ta?aWirin."
Cikin wani irin tarin ?una LamiWo ya gyaWa kanshi.
Kana ya juya yayi gaba Dogari na rike masa da laima Wanzagi na cewa.
"Gyara kimtsi, a bada hanya, sarki ya barku lfy".
Waziri da Wambai ?an buram ?urSi Da iya duk suka mara mishi baya.

Hakama ArWo Bani da sauran dottawan wajen sukayo musu rakiya.
Sheykh Jabeer kuwa.
Yana tafe Galadima na biye dashi a baya. Haroon kuma na gefenshi.
Suna isa yasa kai ya shiga cikin motar,
kana Haroon da Hashim suka mara mishi baya, da sauri sarkin mota ya maida ?ofar ya rufe.
Kana ya buWewa LamiWo motar, gefen bayansu Jab????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
eer ya shiga, kana Galadima ya shiga kusa dashi, sannan aka rufe motar saura duk kowa ya shiga motar da yazo ciki.
Sannan duk suka rurrufe motocin.

Kana suma Fadawa da dogarai suka shiga nasu motoci biyun.
?aya tayi gaba, sauran motocin suka bisu a baya, ta LamiWo na tsakiyarsu, kana Waya ta fadawan ta biyo bayan uku da ke bin bayan ta LamiWo.

A haka suka ja motocin a jere a jere suka bar cikin Rugar Bani.

Cikin Rugar kuwa kowa ya tafi cikin al'ajabi da farin ciki.
Da yawa gani sukeyi kamar dai Jabeer ba mutun bane.

Sauran dottawan kuwa, zama sukayi cikin fadar bayan sunyi sallan la'asar ne, Bukar yazo ya tsaya tsakiyarsu cikin rashin mutunci yace.
"Kuyi kuka da kanku akan duk abinda zai faru gaba".
Kafin ma su bashi amsa tuni ya juya ya tafi.

Su kuwa nan sukaci gaba da al'ajabi da tuanjidin Jarumtar Jabeer.

A cikin motocin kuwa, mutanen ko wacce mota da abinda kowa ke tunawa.
Wani irin azabebben gudu sukeyi tamkar zasu tashi sama, sabida bin umarnin LamiWo wanda shi kuwa ya bada izinin gudun ne, dan ganin yadda Jabeer keta zubda jini, ga wani irin masifeffen karkarwa da jikinshi keyi.

Gudu sukeyi a 360 musamman ma da suka samu suka hau kan babban titin Shikan wanda zai sadasu da cikin babban birnin ?adamaya.

Shi kuwa Sheykh Jabeer, wani irin karkarwa jikin shi keyi, idanunshi jinsu yakeyi tamkar zasu zazzago su faWo ?asa, sabida wani irin masifeffen azaba da yakeji.
Ji yakeyi tamkar ya haWiyi zuciyarshi sabida masifar fushi da harzu?a da zafin rai,
babban abinda ya tsananta fushinsa shine yadda yaga lokacin sallan la'asar ya gota musu,
akan shirmen banza da wofi da zalunci an hanashi yin salla kan lokacin ta.
Hannunshi yasa ya fizge rigarshi da ke hannun Haroon dake ta sa hiraminshi yana tare jinin dake zubomishi ta ?eyanshi.
Taune lips Winshi yayi tare da sa hannun shi, ya kama wuyan rigar cikin ?arfi yaja ji kakeyi,
Fasss sautin yagewar sabon saddan.

Ido suka zuba mishi gaba Wayansu,
Ya Hashim kuwa jiki narawa ya kira Dr Aliyu wanda yake ?anine ga mahaifinshi da kuma Abbansu Jabeer Win.

A can baya kuwa inda Galadima dake zaune gefen LamiWo ne daya bashi umarnin ya kira sarkin gida ya sanar mishi ayi tanadin jinyar ShaWi cikin gaggawa.
Da sauri Galadima ya zaro wayarshi ya kira sarkin gida.
Cikin tashin hankali yake mgna a woya bisa alama duk da sarkin gida yake mgn.
"Ladodo, kayi maza yanzu ka sanarwa tsohon sarkin ShaWin masarautar JoWa yayi maza ya haWa tsumin igiyar bulalin shaWi, ya kaiwa Jakadiyarsu Jabeer,
A shirya duk wani abun bu?ata, domin Jabeer yana zubda jini sosai."

A can masarautar kuwa Sarkin gida yana jin haka ya mi?a ya nufi, sashin kananan sarakuna kai tsaye gefen Sarkin ShaWin ya nufa, ya sanar mishi umarnin da aka bada,
ai nan take Sarkin ShaWin da sarkin Gida, suka shiga bayan sashin mai

46 / 72