Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   44 / 72

129K to 132K   out of 214K words

su kamo hannun Jabeer suyi ta zabgar Ba'ana babu ?a??autawa.

Shi kuwa Jabeer wani bulalan ya kuma shimfiWa mishi a tsakiyar bayanshi tare da sunan Allah.
Still murmushi yayi sai dai wani irin masifeffen bugawa da zuciyarsa tayi ya tsinke ras.
A karo na uku ya tabka mishi bulalar a tsakiyan kafaWunshi wannan karon baiyi murmushi ba, ?ebta idonsa yayi, tare da gyara tsayuwa sai kace dutse ake tabkawa bulalin.
Fargabane ya fara dukan ?irazan dattawan Fulani, yayinda ?abilar Sachama kuwa, suketa ihu da tsalle da fito da kiran ba'ana suna ?ara mishi ?arsashi.
Bulala ta biyar Jabeer ya kuma tsula mishi, still babu sauyi.
Cikin sauri ArWo Bani ya juyo ya kalli LamiWo dake zaune.
Ko ajikinshi dashi da tawagarsa, Sarkin ShaWi kuwa murmushi ma yakeyi.

Cikin fargaba, ArWo Bani yace.
"Allah rene LamiWo wannan yaron bai iya duka da ?arfi bane? Ko dai ba bulalin masarautarku bace!?".
Wani irin kallo mai cike da mamaki da kuma tuhuma LamiWo yayi mishi.
Sai kuma dai ya kauda kanshi.
?anzagi ne yace.
"Hattara dai ArWo , Masarauta JoWa sun wuce aro, zuba ido kaga ikon Allah".
Bulala ta bakwai ne, Jabeer ya Wago ya tsulala mishi ita a gadon bayanshi.
Da sauri Ba'ana ya rufe ?wayar idanunshi sabida wani irin tashi da yaji tsikar jikinshi yayi.
Tsikar jikinshi bai gama konciya ba, yakuma jin Jabeer ya rausa mushi wata bulaliyar, da sauri ya buWe idonshi sabida.
Wani irin Yar-yar da yaji tsikar jikinshi tana zubawa duk gashin jikinshi ya mi?e tsaye.
Bai gama dawowa nazarin meyasa yakejin hakaba ya kuma jin wata bulaliyar.
A hankali yaji zufa ya fara keto mishi duk ta inda hudan gashin jiki yake a fatarsa.
Murmushi yakeyi har yanzu sabida bawai zafi yakeji ba, sai dai fargaba ta rufeshi, sabida jin alamun sihirurrukan jikinshine ke fecewa.
A haka Jabeer yayi ta tsula mishi bulala har zuwa bulala ta goma sha Waya.
Ata goma sha biyu ne, da ya tsula mishi yayi wani irin gantsarewa sabida wani irin azabebben ?ai?ayi da yaji wurin yanayi mishi.
Da sauri yasa hannunshin a bayanshi alamun zai sosa.
Ife-ife da sowan da matasa suka farayi ne da Muryar Barmuji na cewa.
"Dokar gasa banda susa".
Da sauri ya dawo da hannunshin tare da cewa.
"To ya dane karatun da yakeyi, bana so, ya dena kira min sunan Allah".
Wata bulalar Sheykh ya zabgawa shege tare da cewa.
"Sunan uwarka zan kira maka in ban kira sunan Allah ba?".
ArWo Bani kuwa wani irin ajiyan zuciya mai ?arfi yaja.
Shi kuwa Ba'ana wani irin masifeffen ?ai?ayi ne yakeji a duk inda Jabeer ya zuba mushi bulala, a bulala ta goma sha biyar ne, da aka zuba mushi.
Yayi wani irin gantsarewan da yafi na Wazu.
Wani irin azabebben zafi da raWadine yakeji yana tsarga mishi jiki da zuciya.
Zuface ta ketomishi tako wanne sashi na jikinshi.
Cikin sauri Jabeer ya juya bulalar ya amshi ta biyu ya haWa data forkon.
Ya dam?esu a hannun hagunshi.
Wanda dama shi badamene kuma bahagone duk abinda hannun damanshi kan iya yi to na hagun yana fi iyawa.
Sai dai kasamcewarshi mutun mai ilimi da sanin addini shiyasa yake amfani da hadinsin nan da Manzon Allah ke cewa.
A cikin dukkan abinda zamuyi mu wakilta dama a forko, har dai sai in shiga bayan gidane aka ware shiga da ?afar hagu.
To juya hannun yayi da hannun hagunshi, kana ya ri?e mahaWin al'kyabbar jikinshi da hannun damanshi.
Gyara tsayuwarshi yayi kana ya Waga bulalar da ?arfi ya zubawa Ba'ana a tsakiyar bayanshi.

Wani irin azabebben ihu mai ?arfin amo da karaji Ba'ana ya kurma tare da fara karkarwa kar-kar tamkar mai farfaWiya.
Ihun da ya kurmane yayi masifar tada hankalin dukkan kafurai magoya mayanshi.
ArWo Bani kuwa a gabansu LamiWo ya tashi tsaye ya juya ya fuskanci al'?ibila yayi sujjada.
Bappa ma da kanshi wani irin murmushin jin daWi yakeyi.

Hakama duk sauran dottawan.
Shi kuwa Ba'ana wani irin azabebben kuma masifeffen zafi yakeji a dukkan sashin jikinshi.
Wani irin tsalle ya buga da ?arfi lokacin da aka kumayi mishi bulala ta ashirin.
Wani irin tsuma da karkarwa jikinshi keyi hatta Ba'anansa mi?ewa tayi tana karkarwa, wata tafasashiyar zuface ta sin?o mishi, zafi yakeji har cikin ?o?on kanshi da zuciyarshi.
Bulala ta ashirin da biyu akayi mishine yasashi fashewa da wani irin kuka mai azaban ?arfi wani irin masifeffen fitinenne fitsarin azaba ya fara kwaranyo mishi, ihu mai cike da azaba yayi.
Wanda gaba Waya rugar saida kowa ya jiyoshi.
?abilar Sachama kuwa gaba Waya suma kuka suka saka.
Shi kuwa Ba'ana da ?arfi ya faWi ?asa yana burbuwa, tamkar wanda yayi al'janu.
faWuwanshi ?asane yasa Jabeer rusunowa ya rin?a tabka mishi bulalar, ihu da burbuwa da rarrafe alamun guduwa Ba'ana yakeyi cikin azaba da karaWi da kuka yake cewa.
"Wayyo! Wayyo!! Wayyo Bonon!!! Ka ceceni zan mutu zai kasheni.
Wayyo Bononnnnnn! Yau bakayi min ranaba, ga bulalin karin sihirina sun iso gareni wayyoooooooo Bonon meyasa baka gaya minba na hudu tun kan wannan malamin ya kasheni ya karya min komai na jikina da sunan Allah."
Ya ?arishe mgnar da ?arfi tare da mi?ewa tsaye ya fuskanci kudu. Ya Wiba a guje ya ari ta kare ya nausa a guje.
Wani irin taku Jabeer yayi tare da biyoshi baya da sassarfa abunka da dogon mutun sai gashi ya isoshi a gigice ya fara kai mishi bulalin hagu da dama,
Jin azabar ta zarce azabar da yake zatone, yasa Ba'ana kurma ihu da kururuwan da yasa kab mutane suka nufosu.
Gudu yakeyi Jabeer na binshi yana zaneshi har ya fiddashi cikin taron gaba Waya.
Barmuji ne ya ri?e hannun Jabeer tare da cewa.
"A dokar gasa ShaWi in dai ya gudu ka bishi ka korashi cikin farfajiyar shike nan ya faWi a gasa kaci.
Kuma bazai sake samun damar shiga gasarba bazai kuma sake zama a garinba."
Wani irin busar sarewa da al'gaita kana da kiWe-kiWen tsantsar farin ciki, al'ummar Rugar Bani suka farayi.
Sunayi suna zagaye Jabeer. Haroon kuwa da ArWo Bani da Galadima mi?ewa sukayi cikin farin ciki suka ruggumeshi.
Jamil, Jalal, Imran, Hashim, Sulaiman. Suma kab farin cikine ya cika musu zu?ata.
Laminu kuwa ji yakeyi tamkar ya sha?o Jabeer ya karshi sai dai tabbas dama ya zaci aha dan shi mari Waya nema Sheykh ya masa ya kusan suma, shiyasa ya tausayawa Ba'ana.
LamiWo kuwa jinjina kai yakeyi yana tattausan murmushi.

Koda su Galadima suka ruggumeshi, ArWo Bani kuwa kama hannunshi yayi ya Waga sama alamun yaci gasar ShaWin.

A haka suka iso gaban LamiWo hannunshi yasa ya dafa kan Jabeer tare da sanya mushi al'barka.

Mutane kuwa duk an kacame da farin ciki.
Ya Salmanu kuwa kusan suma yayi tsabar masifar jin daWi.
Alhamdulillah yau dai burinshi ya cika ya samu konciyar hankalin duniya an Wauka musu fansa, shida masoyan Shatu na baya, harma da yayanshi.

Jan gefe makaWan suka sabi, da sauran zugar jamar gari.

Jabeer kuwa mamaki yakeyi yadda yaga.
Fulani nata shigowa garin tako ina wasu bisa dawakai wasuma ?an ra?uma.
LamiWo kuwa waya yakeyi da amalun a sirrance yake mgnar sabida ko Jabeer Win dake kusa dashi baya jinshi.

Bisa umarnin ArWo Bani ne aka rin?a fito da ?waran nono da fura da dambu da ?waran zuma,
Ana kawowa su LamiWo.

Wanda fadawa da dogarai ne sukasha.

A hankali Jabeer ya kalli LamiWo cikin gajiya yace.
"To ai sai ku tashi mu tafi ko!".
Shiru LamiWo yayi mishi, ganin hakane, ya gyara hiramin kanshi kana ya kuma cewa.
"Mu tafi ko".
Galadima ne yace.
"Ai bamu gamaba".
Cikin sauri Haroon yace.
"To meya rage kuma?".
Galadima ya buWe bakin zai bashi amsa kenan. Sai kuma duk suka juyo suna kallon wasu tsala-tsalan motocine masu masifar kyau da tsada, suna shigowa Rugar Bani a jere-a jere. Cikin fidda numfashi Haroon ya Wan kalli motocine da mamaki yace.
"Ha Jabeer kalli wannan kamar tawagar motocin Uncle Abdulkarim da Abudulfata kalli kamarfa harda Jadda". (Sarki Jalaluddin suke cewa Jadda)
Sai kuwa ya juyo ya kalli LamiWo cikin nitsuwa yace.
"LamiWo lfy kuwa?".
Kanshi ya gyaWa mishi alamar eh Lfy kau.
Shi kuwa Sheykh Jabeer cikin nitsuwa yake kallon ayarin motocin a fakaice tabbas.
Su Jalaluddin ne da yaranshi. Kana ga kuma Baban Haroon, ga kuma su Dr Aliyu da Barrister Kamal da su Baba Basiru Baba Nasiru dama duk sauran manyan masarautarsu.
Da sauri ya juyo ya kalli LamiWo da nufin yin tambaya sai kuma yayi shiru ganin LamiWo na mgna da Galadima da kuma wani amintaccen bafadanshi.
Tsaki ya Wan ja tare da cewa.
"To wannan ?us-?us du na menene, ku duk abinda babu kyau kuna jin daWin yinshi."
Shiru yayi ganin motoci sama da talatin ne suka shigo Rugar.
Kana duk manyan mutanene kuma sun fito cikin motocin sun nufo inda suke zazzaune.
Wanda tuni ArWo Bani yasa an kuma firfito da taburman cikin masallacin su.
Kana yasa an fito da sauran dardumai da kilisai anzo an shimfiWa.

Suna isowa sarki Jalaluddin da Abba suka dafa kafaWun Jabeer tare da sanya mushi al'barka kana suka zauna gefenshi ya zama sun sakashi a tsakiya.
Kusa dashi Abbanshi ya zauna,
Kana Jalaluddin ya zauna kusa da Abban.
LamiWo kuwa na kusa dashi shida Galadima.

Da sauri Haroon dasu Jamil kan sukabi bayan fadawan da suka nufi motocin da sukazo yanzu da ido.

Shi kuwa Sheykh Jabeer ido kawai ya zubawa wayarshi.
Yana wasu aiyukanshi a ciki.

A hankali ya Wago kanshi ya kalli Haroon dake taSashi.
Da yatsa Haroon ya nuna mishi gabanshi.
A hankali ya juya kanshi ya kalli inda Haroon ke nuna mishi.
Fadawane da hadimansu keta jido katon-katon Win sweet ga kuma fufun goro shima sunata jidowa suna ajiyewa a gabansu ArWo Bani.

Cikin mamaki ya kalli LamiWo tare da cewa.
"Me za'ayi da wannan kuma? Kamar wanda suka zo Waurin aure!".
Da sauri Galadima yace.
"Eh ashe ka gane ai Waurkin auren ne".
Cikin mamaki Haroon yace.
"Aure kuma? To auren waye?".
LamiWo ne ya kalleshi cikin isa yace.
"Auren Muhammad Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero JoWa!".
Wani irin yun?ura Jabeer yayi zai mi?e, cikin tsananin haWe fuskarnan tamkar zatayi aman jini ya kalli LamiWo tare da yun?urin mi?ewa yace.
"Zancen banza kenan a wurin banza, ai wlh baka isaba, wlh LamiWo kafa kiyayeni kanafa shigemin rayuwa, ka fita hanyata ka fice min a ido kar in rintsa da kai fa kadafa ka bari in juyo kanka".
Ya ?arishe mgnar da mi?ewa tsaye. Sai kuma ya juyo jin an kamo hannunshi an medashi zaune, a fusace ya kalli inda yaji anja hannun nashi ganin Sarki Jalaluddin ne ya ri?o hannunshi ya sashi kuma tsuke fuskarsa cikin faWa yace.
"Jadda sakarmin hannu bana so! Bana son abinda kuke min da rayuwata, wlh gwarama kun tashi mun tafi, dan babu ruwana dan Ni bazanyi aure ba".
Da sauri ya juyo jin muryar Abbanshi yana cewa.
"...!

Littafin GARKUWA na kuWine turo katin mtn na Wari uku kacal ta wannan number 09097853276, sai in saki cikin Normal group wanda a kwana talatin za'a gama littafin. Ko kuma kiyi min TRANSFER Win dubu Waya ta asusuna na Jaiz 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853276. Sai in saki a Special Group inda cikin mako biyu kacal za'a gama Part 1 da izinin ubangiji.






By
*GARKUWAR FULANI*"Muhammad!". Ya kira babban sunanshi tare da jawo hannunshi, ya zaunar dashi bisa kujerar da ya tashi a kai.
Cikin wani irin yanayi mai cike da tashin hankali da tsoron abinda suke shirin aikatawa, ya kalli Mahaifin nashi, kana ya juyo ya kalli LamiWo da Galadima gefen damanshi ya juyo ya kalli Jadda cikin rauni ya kuma kalli mahaifin nashi tare dayin ?asa da murya yace.
"Abba kada ka bari su Waura auren nan, dan Allah kace musu su bari, kada su Waura".
Ya ?arishe mgnar cikin tashin hankali da Sacin rai da tarin rauni a fuskarshi.
Cikin zuba mishi ido Abbanshi yace.
"Meyasa? Sabida me za'a bari!? Meyasa baka so!?."
Kanshi ya jujjuya tare da haWe hannayenshi wuri Waya ya fuskanci mahaifin nashi cikin sanyi yace.
"Ni dai bana so. Abba dan Allah kada ka bari suyi.
Bana son garin nan bare mutanen cikinsa, kuma bawai haka banza na?i auren nan ba, Abba inada matsala, Please Abba na tuba dan Allah kace su bari. In yaso a Waura da wani amman banda ni kam".
LamiWo ne ya kamo hannunshi cikin isa yace.
"Auren' nanfa, kamar ma an Waurashi an gama, domin babu wani abu ko wani mahalu?in da ya isa ya hana wannan Waurin auren, gwarama ka kontar da hankalinka. Tunda ka iya jure bulalin aiko tabbas dole ka aureta, babu shakka dole sai ka aureta, bazai yiwu a dakeka a kantaba sannan ka barmusu itaba."
Cikin jin haushin wannan fitinenne tsohon ya kwace hannunshi daya ri?e tare da cewa.
"Haka kenan kullum zanyi ta wahala a bisa wasu dalilanka da bana addiniba, me ruwanka da dukan da akayi min, ba dai kai-kasa dole aka dakeni ba".
A hankali Galadima yace.
"Eh da kuma bakayi kukaba, baka guduba, yau kuma kasa yayi kuka ya gudu ai dole ka aure matar da a kanta aka haWaku gasar, tunda mu dai ba sakarkaru bane, bare ace bamu san dokar gasar ShaWi ba."
Wayyo Jabeer ji yakeyi tamkar ya mammake tsoffin nan dan tarin ba?in ciki. Rai a Sace yace.
"Bakufa fini sanin kainaba, tunda nace muku bana son aure, bazan kuma yi aureba, to ku barni mana, rayuwata ce ko taku, ko dole ne duk wata matsalata da sirrin rayuwata sai kun sani! Nace muku bana son wannan garin na tsani garin bana son mutanen garin karankatab Winsu.
Bani babu su, in kuma kukayi gangancin cusa min wata muguwar yarsu, tabbas! lallai ilaihin! A kanta zan rama sauran bulali ashirin da wancan ?aton gardin ya min, hamsin, ni a talatin ya gudu".
Kai Jadda ya girgiza tare da cewa.
"Ka rama mana kaida matarka, ka rama ka kuma jinyace ta".
Shiru sukayi sabida jin muryar Dr Aliyu da kuma Galadima da ArWo Bani da Bappa suna tabbar wa juna lfyar yaransu, cikin Mamaki ya kalli Galadima dake cewa.
"Muma Wanmu lfyarshi lau, Namiji ne".
Cikin sanyi Jabeer yace.
"Ji ma?aryacin tsoho, wai lafiyata lau, ko yaushe ya zama likita ya gwadani. Harda wani karkacewa yana zuba ?arya ko farin gemunshi bai martaba-ba".
Jin Abbanshi ya daki gefen ?afarshi ne yasashi yin shiru.

A nan a gabanshi a gaban mahaifinshi. A gaban dubban al'ummar fulani makiyaya daketa tsastsafo tako wani sashi na duniya, a kuma gaban LamiWo da tawagarsa hakama Jalaluddin da tawagarsa.

Aka Waura auren Muhammad Jabeer da Aysha. Bisa koyarwan addinin Musulunci.

Sosai su Jalal, Jamil, Hashim, Haroon, Sulaiman. Sukayi mamakin wannan aure na ba zata. Ba zato ba tsammani.
Bayan an gama dai-dai-ta komai an Waura auren ne, kuma.
LamiWo ya kalli ArWo Bani, cikin girma da ?asaita yace.
"Yanzu zai tafi da matarshi."
Cikin sanyi da al'hini Bappa yace.
"Allah rene yanzu kuma!?".
Galadima ne ya amshi zancen da cewa.
"Ha??un yanzu zamu tafi da ita!".
ArWo Bani ne yayi murmushi mai cike da jin daWin yace.
"To ba laifi ai, muje a fito muku da ita".
Shi kuwa Bappa ido ya zuba musu.
Dan shi a zatonshi ba yau zasu tafin mishi da Shatunsa ba.

Nan duk suka Wunguzuma, suka shiga motocin. suka nufi ?ofar gidansu Shatu.

Ya Salmanu kuwa, tuni ya shiga cikin gidan su.
Ya shiga Wakinshi yana ta kuka kamar yaro. Bai tsamci haka abin kan iya juyewa ba, Ba'ana ya rasa Shatu shima ya rasata.

Suna isa ?ofar gidansu, duk motocin suka tsaya.
A hankali Bappa da ArWo Bani suka kutsa kansu cikin gidan.

A tsakar gidan suka samu.
Shatu na zaune dan dawowarta kenan, hannunta tasa ta tallabe haSarta ta zubawa su Junainah ido, shigowarta gida kenan daga dawowarta.
Cikin ?adamaya su Binto suka shigo gidan a guje suna ce mata wai an Waura aurenta da Wan sarkin da akayi gasar ShaWi dashi.
Jin hakane yasata yin murmushi tare sau?e dogon ajiyan zuciya na gajiyar tafiyar da tayi, ido ta lumshe tare da cewa.
"Auren kuma wasane, da zai zama an aura min wani wanda ba'a san halinshi ba, ko ?ar tsana ma ai ba'a aurar da ita a hakaba bare ni".
Ta faWi mgnar cikin fargaban ganin yadda suketa rantse mata. Duk da bawai ta yarda da zancensu bane. Junainah kuwa dariya takeyi tare da Wan tsalle-tsallenta tana cewa.
"Yeeh Auren Addana yazo, zanyi gayyan fati muyi gaWa".

Cikin zuba musu ido, ta zauna gefen, Ummey dake ta Binta da ido, cikin sanyi tace.
"Ummey na dawo! Ya jikin naki!?."
Da sauri ta gyara zamanta tare da zubawa Ummey ido, cikin mamaki take kallonta ganin idanunta nata zubda hawaye ne, yasata cikin ruWani da tashin hankali da fargabar abinda ke shirin faruwa da ita da rayuwarta.
A kiWime tace.
"Ummey meya sameki? meya saki kuka? Jikin ne yake miki ciwo?."
Sam Ummey bata iya mgna ba, sai kukan da takeyi,
hakanne yasa zuciyar Shatu karaya, cikin rauni wasu hawaye masu Wumi suka fara tsiyayo mata.
Hakan ya ?ara ingiza kukan Ummey hakama,
Junainah sai ta raSa gefensu tayi, zurui a zatonta aure abun daWi ne ba kukaba to gashi taga su kuma kuka sukeyi.
Sosai Shatu takeyin kuka mai tarin dalilai.
Suna isa Bappa yasa hannunshi ya kamo nata, cikin sanyi yace.
"Taso kizo".
Ido cike da hawaye ta mike tsaye bisa umarnin Bappa.
Shi kuwa Bappa cikin sanyi ya kalli Ummey da Junainah yace.
"Kada kuyi kuka, kuyi mata addu'o'in samun nasara a cikin wannan al'amari, muyi mata fatan aurenta ya zamo haske ne a rayuwarsa shi mijin da ahlinshin baki daya, fatanmu aurenta ya zamo ?ungiyar da zata jawo gskya cikin raminda aka binneta ya fito da ita kowa ya gani."
Shiru Ummey tayi sai hawayen da suke kwaranya.
Hakama Shatu hawayenta wani na korar wani.
Ita kuwa Junainah faWawa jikin Ummey tayi sukaci gaba da zubda hawaye.

Bappa kuwa hannunta yaja suka juya suna nufi hanyar fita.
Da kayanta na Wazu wanda taje Genaral Hospital ?adawaya dasu, hatta hand bag Winta na rataye a kafaWarta wayarta na ciki.

Cikin mamaki take bin bayan Bappa, tare da yin taku a hankali tana bin bayanshi yadda yake jan hannunta.
ArWo Bani kuma na biye dasu a baya.

Suna fitowa ?ofar gidan, Haroon da Jalal suka juyo suka kalli juna,
Cikin tarin mamakin ganin kamar yarinyar Wazuce.


Shi kuwa Sheykh Jabeer yana zaune cikin motar, shi Waya dan duk sun fita.
Da sauri ya dafe saitin ?ahon zuciyarshi jin ta tsananta bugawar da yakeyi.
A hankali ya maida bayanshi ya jingina da sit Win tare da rufe idonshi.
Yana mai jin sanyin A/C na ratsa mishi jiki da jini da zuciya.
Amman duk da haka zuface ke tsastsafo mishi a jikinshi sabida bugun da Zuciyarshi keyi ya wuce misalin.

A hankali ya juya kanshi ya kalli gefen hagunshi inda yaga motar Jadda da kuma Dr Aliyu ne da Barrister Kamal ke jere a wurin.

Bappa kuwa a hankali yake

44 / 72