Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   34 / 72

99K to 102K   out of 214K words

?anin Abbanshi Baba Nasiru kenan na ce mishi.
"Kai! Jabeer tsaya".
Tsayawa yayi cak ba tare daya juyo ba,
Suma sauran duk tsayuwa sukayi,
Kusan a tare Baba Nasiru da Baba Bashiru. Suka isosu.
Cikin haWe fuska Baba Nasiri yace.
"Jabeer, in dai aure kake so ai gwara ka fito fili ka gaya mana, mu bazai gagara ba mu aurar maka koda yar baiwace, tunda shi ubanka zuciyarshi ta mace, baya iya tsinanawa kansa komai."
Da sauri ya rumtse idonshi,
Jalal kuwa wani irin kallo ya watsa bappanun nasu,
Shi kuwa Jabeer shiru yayi bai tanka musuba, Baba Basiru ne ya ne ya bugi kafaWarshi tare da cewa.
"Kodai kafi ganewa yawon zinace- zinacen daka saba Win ne? Kafin burin a barka ba mata, kana zaune ka tsufe a gida ka fake da rigar malumta kana iskanci a cikin tsarkakekkiyar masarauta ko".
Ido ya zuba mishi babu ko kebtawa, ganin haka Baba Basirun ya Wauke hannunshi dake kan kafaWarshi.
Dai-dai lokacin kuma Barrister Kamal da Dr Aliyu suka iso wurin.
Suna isa Ya Jafar yayi saurin kamo hannun ?anin shi Sheykh Jabeer, ya fara ja da sauri alamun su tafi su bar wurin gaba Waya, jikinshi rawa yakeyi.
Ganin hakane Haroon ya kalleshi cikin larabci yacewa Jabeer.
"?an uwana mu tafi".
Barrister Kamal ne ya kalli Jabeer cikin sanyi yace.
"Jabeer jeka, ku tafi kada ka biye musu, tunda sun girma basu san sun girma ba."
Jin hakane yasa Jabeer ya juya ya fara tafiya.
Jalal kuwa wani harara ya watsa musu kana ya juya yabi bayan yayunshi.

Jafar kuwa Jan hannun Jabeer yakeyi a kiWime gaba Waya jikinshi karkarwa yakeyi tamkar mazari.
Ganin haka yasa Jabeer ya jashi ya kaishi sashinsu, ya dam?a hannunshi wa Juwairiyya kana yace mata ta kula dashi, yanzu zai fita shida LamiWo.
Jiki a mace Juwairiyya ta mishi fatan a dawo 'lfy.

?arfe biyu da rabi dai-dai suna cikin motoci, wanda a ?alla sun kai su goma.
Motar forko Waziri ne wanda yake Wane ga Yayar LamiWo.
Sai Galadima, da Wambai,
?aya motar kuma ?an iyane da Sallama, da sarkin Dawaki, da sarkin fada,
Sai motar da LamiWo ke ciki, shida Garkuwa wato Jabeer sai Haroon sai kuma Hashim da Laminu, ?anin Hashim wanda duk yaran Gimbiya Saudatu ne matar babban yayansu Habibullah wato Abbansu Jabeer, wanda da shine Galadima. ?aya rasune aka bawa Ya Jafar sarautar wanda kwananshi goma da sarautar, komai na rayuwarsu ya sauya.

Sai motar dake binsu wanda Jalal, Jamil, Imran Sulaiman Wan Barrister Kamal, suke ciki.


Sai sauran motocin fadawa kamaru, ?an kazagi, mai yiwa sarki fadanci da kuna dogari mai ri?ewa sarki laima, da sarki mota da dai sauransu.
A jere a jere motocin ke tafiya.
Gudu sukeyi mai Wan yawa sabida ganin yamma ta ?arato, gashi basu je bama bare su fara shirin dawowa.

Gudu sukeyi, kana fadawansu, rirti?e da bulalin dogaye.

Kai tsaye Rugar Bani suka nufa.
Koda suka iso cikin garin Shikan, sunga alamun garin babu lfy, har yanzu dan sai matasan ?abilar Sachama da hausawa suketa yawo a garin ko wanne na bawa yankinsu kariya.

Suna isa cikin Rugar Bani.
Gaba Waya mutanen Rugar duk inda suka gilma sai a bisu da ido,
Yara maza da mata sunata guduwa suna shiga cikin gidajensu.

Kai tsaye tsakiyar garin suka nufa wanda nanne fadar ArWo Bani taken kuma lokacin duk manya da yara maza tsoffi da dattawan garin duk suna harabar wurin sabida yau jumma'a duk suna dawowa kiwo da wuri.
Kuma duk a tsakiyar garin suke taruwa sabida bawa garinsu kariya, domin har yanzu suna cike da taraddadin abinda akayi musu.
Kuma ya rigada yanzu an ?ure ha?urinsu sunata shirin Wauk????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? an fansar rayukan da aka kashe musune. Fiw-fiw haka motocin keta gilma mutane suna wucewa tara da tada ?ura sabida babu kolta a garin sai yashi. Sai sauti da ?ugin mitocin ne ya cika kunnuwan mutanen garin baki Wayansu.

Motocin na isowa wurin. Gaba Waya mutanen Rugar dama ba?in mutanen ma?otansu sauran rugage duk suka mi?e tsaye.
Tare da gya tsayuwarsu, suka gyara ri?on da sukayiwa sanduna su.
Ba tsoro ba fargaba sukayiwa motoci goma nan zobe, suka sasu a tsakiya.
Cikin sauri Sarkin dogarai ya buWe marfin motar da yake ciki, ya fito tare da zungureriyar bulalarashi. A take kuma ?an zagi ma ya fito.
Da sauri duk sauran fadawanma suka firfito kowa da zungureriyar bulalarashi.
Cikin Waga murya Wanzagi yake cewa.
"Ta kawarka lfy Sarki Nuruddeen Bubayero JoWa, sarki Wan sarki jikin Sarki,uban sarki kakan sarki. Jama'ar gari sun gaisheka,
Da sauri duk sauran fadawan suka, firfito cikin motar.
Sar?in motane yazo ya buWe wa Sar?i ?ofar.
Dogari kuwa matsowa yayi da sauri ya buWe wata ?atuwar laima, gaba Waya sukayiwa ?ofar motar labule da mamyan jajayen rigunansu, yayin su duk sawunsu babu takalma, sannan kawu nansu naWe cikin wasu ?atti-?attin rawanunnuka masu girma babu kunne ko Waya a jiki.

Gaba Waya mutanen Rugar kuwa, sai ?ara tsuke fuskokinsu sukeyi, cikin jin haushin zuwa sun.

Can cikin motar kuwa Haroon ne sa?ale da wayarshi a kunne cikin sanyi yake mgn sabida kada LamiWo ya jiyoshi, haka kuwa babu mai jinshi sai Jabeer.
Cikin sanyi ya Wan kalli Jabeer kana yaci gaba da mgna a hankali yace.
"Umaymah ni dai hankali na ya tashi, da irin wasu mutane da wasu abubuwan da akeyiwa su Jabeer a masarautar su, Umaymah, meyasa bazasu bar musu sarautar da Masarautar tasu gaba Waya bane, sai kinga fa yadda Jazlaan dinki ke fuskanta ?alubale fa."
Cikin wata iriyar murya Umaymah tace.
"Yanzu kuna inane?".
Kanshi ya Wan jujjuya kana yace.
"Uhum ni ina zan san inda muke, na dai san munzo wata Rugar fulani ce, wai GARKUWAN FULANI nasu ya kawo musu ziyara dan ja-janta musu abinda ya faru, kuma gaba Waya mutanen rugar naga sai
Wani irin kallo suke mana kamar dai zasu huce a kanmu ne".
Cikin wani irin tattausan murmushi mai nuna jin daWi tace.
"Bawa Jazlaan wayar".
A hankali ya mi?a Jabeer wayar tare da cewa.
"Umaymah ce".
Cikin sanyi yace.
"Kace tayi ha?uri sai mun koma zan kirata".
Da sauri ya like mishi wayar a kunne jin tana cewa.
"A a amshi wayar".
?an haWe fuska yayi kana ya amshi sallamar da tayi mishi.
Kana ya meda kai jikin kujerar murya can ?asa yace.
"Umaymah, Na gaji tunda muka dawo ban hutaba, yau da sassafe wannan tsohon ya sani shara kamar wani bawanshi haka ya sani na share mishi wannan Wakin nasu na gado wanda in dan ta nine rusashi za'ayi gashi yanzu kuma ya kwasoni zuwa wata rugar FULANI da duk makamaine a hannunsu, ko wa zasu daka".
Cikin wani irin jin daWin daya bashi mamaki mai yawa tace.
"Ko kai zasu dakane Jazlaan, Sheykh Jabeer, yasha zana a hannun Fulani".
Cikin sanyi yace.
"Su kashe Ni dai Umaymah, ke kin sani tunda nake a duniya, ba'a taSa dukana ba, sabida koda iba yaroma ban taSa yiwa Mama da Ummi laifin da zai kaisu ga yimin dukaba, Abba na kuma baya dukanmu, Umaymah kema baki taSa koda marina ba, to kuma wa kika ga zai dakeni a faWin duniyar nan banda ruwan sama".
Murmushi tayi wanda har saida yaji sautin cikin sanyi tace.
"Allah ya tabbatar da al'khairi cikin tafiyar naku, ka dai lura kaine GARKUWAR dole da duk abinda zai cutar da LamiWo ko masarautarku ko sunanta dole kai ne zaka zame musu Garkuwa, so dan Allah bana son kayiwa LamiWo musu bare gardama a cikin duk abinda zai umarceka".
Cikin sanyi yace.
"To Umaymah, in na koma zamuyi mgna".
Daga nan sukayi sallama, cikin mamaki ya kalli yadda gaba Waya manyan hakimai sun firfito, ga LamiWo ya fita amman yana tsaye bakin ?ofar motar.
Cikin sauri ya kalli Hashim tare da cewa.
"Hashim Lfy kuwa naga duk suna tsaye, garin basu da abin zamane daza'a karrama ba?i?".
Cikin nitsuwa Hashim yace.
"Uhum cewa sukeyi, wai sun yafe ziyara da ja-jantawar LamiWo".

A wojen kuwa, cikin Waga sauti Danzagi yace.
"Hattara dai fulani mai ?asar ne gaba Waya, ke tsaye tsakiyar garinku, maza ku bada masau?i".
Ya ?arishe mgnar yana jujjuua bulalar hannunshi haka sauran fadawan.
Cikin fillanci Wan aiken ArWo Bani ya buWe murya da ?arfi cikin harshen fillanci tare da cewa.
"Maza ku bada hanya mai martaba ya iso fadar ArWo Bani".
Jin haka gaba Waya taron al'ummar fulanin suka fara buWa hanya,
Har gaban rumfar da ArWo Bani ke Wauke ba?i, inda aka shimfiWe wurin da manyan taburmaii kana aka malale manyan kilisai irin namu na fulanin dawa.
Bappa Malam Liman Alhaji Haro Alhaji Umaru, Musu, da kuma Ardo Duno da ArWo barwa ma?otansu, duk suka mimmi?e tsaye sai dai gaba dayansu fuskokinsu babu wal-wala, asalima wasun cikinsu jikinsu har Sari yakeyi, dan fushi da zafin zuciya.

A can cikin ?auyen Bonon kuwa, Ba'ana da sauran ?abilum Samawam duk suna gaban dodon tsafinsu Bonon Win,
Da gudu Maman Ba'ana ta iso wurin cikin Yaren Sacamancin ta sanar dasu zuwan, sarki LamiWo da tawagarsa, jin hakane yasa, Ba'ana ya mi?e jiki na rawa ya nufi rugartasu.
Su kuwa sauran yace in yaje yaga da matsala zai kirasu.
Nan ya tafi su kuma sukaci gaba da dariyar mugunta.

A cikin Rugar Bani kuwa, Bukar Baban Ba'ana ne yayi wata iriyar fitinenneyar murmushi mai cike da mugunta dan son haddasa fitina, ta yadda zai samu masarauta JoWo da kanta ta shiga matsala.
Kutsawa yayi tayi cikin mutane har ya samu ya shigo gaba-gaba.
LamiWo kuwa da tawagarsa taku sukeyi cikin al'farma da ?asaita.
Su Waziri, Galadima, Wambai, ?an iya, Wan buram, duk suna biye dashi a baya,
Dogari na rike mishi da laima, fadawa kuma na zazzaune a ?asa, gefe da gefe, ?anzagi kuwa muryarsa ce cika wurin baki Waya duk da hayaniyar da wurin kedashi.
A hankali Jabeer ya sako sawunshi woje, yana taka ?afarshi ta dama kan ?asar garin, yaji zuciyarshi ta buga da azaban ?arfi har saida ta kaishi da rumtse idonshi tare da ambaton.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun".
A saman red lips Winshi.
da ?arfi yasa hannunshi ya dafe ?ahon zuciyarshi, tare da kuma maimata.
"Hasbunallahiwani'imanwakil".
Sabida ji yayi tamkar zuciyarshi zata fasa ?irjinshi ta faWo ?asa. Jalal, Jamil, kuwa ido suka zuba mishi, sabida ganin yadda ya rumtse idonshi, sabida suna bakin ?ofar motar, sune ma suka buWe mishi marfin.
Haroon kuwa da Hashim da Laminu, jira suke ya fita kafin su fita.
Cikin mugun tsana Laminu ya kalli Jabeer Win da ya yun?ura ya fita,
zuwa yanzu, wani irin harbawa da tsalle zuciyarshi keyi, wani irin masifeffen fargaba, da kaWuwa ne suka dirar masa lokaci Waya.
A hankali duk suma su Haroon suka fito, a tsakiya sukasa Jabeer kana bayinshi na biye dasu a baya.
A hankali ya gyara tattausan al'kyabbar jikinshi, tare gyara hiramin kanshi ya kange kekyawar fuskarshi.

Takun da yakeyi ne ya ?arawa shigarsa ta al'farma daraja,
ya fito tamkar balarabe, gaba da baya, kamalarsa da kwarjini shi ya cika dukkan idanun bani adam dake kan doron ?asar wannan wurin.

Ya Hashimu ne da ya samu ya dawo gida jikinsa da sau?ine, yayi wani irin kabbara mai ratsa zuciya, cikin sanyi yace.
"Ziyararku tayi haske sabida kun zo mana da mai hasken addini a jiki da zuciyarshi".
Ga mamakinshi sai yaji ?anzagi na cewa.
"GARKUWA ya amsa Sheykh Jabeer Jikan sarki tsatson sarki gaba da baya".
Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali yake takunda yasa al'kyabbar sa buWuwa tana bajewa, sabida Waga hannunshi da yayi yanai musu sallama irin ta addinin Musulunci.
Mafi akasarin mutanen tafukan hannunshin suka zubawa ido, sabida kai da ganin tafin hannunshi kasan ya gauraye da ni'imar ambaton sunan Allah da rike littafi al'?ur'ani, da kuma jin daWin.
Shi kuwa Jabeer ?ara sar?afe carSin shi yayi cikin yatsun hannunshi, kana, ya fuskanci gefen hagunshi, ya Wanga musu hannu tare dayi musu sallamar kamar yadda yayiwa yan gefen damanshi.
A haka har suka isa tsakiyar ?aton filin.
Inda LamiWo da sauran tawagarsa ke zaune.
Bisa fararen kujerun robar da anka jera musu cikin rumfar suka zazzauna.
Bayan sun amsa musu sallamar da sukayi.
Cikin nitsuwa LamiWo ya kallesu tare gyara zamanshi.
Muryar ?anzagi ce ta karaWe wurin da cewa.
"Gyara kimtsi. A saurara dai LamiWo jikan Wan Lami Bubayero jikan LamiWo JoWa zaiyi mgna".
Wani irin harara suka watsawa Danzagin, shi kuwa LamiWo cikin nitsuwar datattaku tace.
"Da farko dai zan fara da baku ha?urin zalumcin da akayi, muku, Allah ya ji?an wanda suka rigamu gidan gsky."
Da ?arfi ?anzagi yace.
"Amin". Su kuwa dattawan ido kawai suka zuba mishi.
Shi kuwa LamiWo a hankali yaci gaba da cewa.
"Ina mai baku ha?uri da kuma umarnin kada kuce zaku Wauki mataki domin ramuwa."
Kamar daga sama sukaji Muryar Bakur yana cewa.
"Babu wani sarkin da ya isa ya hanamu Waukar fansa sai, Ubangijin daya busa mana, numfarfashi".
Da ?arfi Wani dogarin ya Wago zabgegiyar bulalarshi ya zabgawa Bukar.
Wanda saida yayi tsalle ya kurma ihu.
Cikin tsauri LamiWo ya Wagawa duka fadawanshi da hadimanshi da dogara shi hannu alamun kada su sake dukan kowa.
Saura su Waziri kuwa duk shiru sukayi,
Jabeer kuwa, a hankali yaci gaba da tasbihin da yakeyi, sabida danne abinda yakeji zuciyarshi nayi.
Shi kuwa LamiWo cikin sanyi ya fara mgna, dan yasan zafin rashin da sukayi ne yasa sukace sai sun rama, a hankali ya kalli fuskokin dattawan da yasan sunje mishi har fadanshi dan neman zaman lfy, cikin kula ya kalli ArWo Bani tare da cewa.
"ArWo Bani zaku ha?ura, hukuma da masarauta ta bi muku kadun cutar damu da akeyi, ko zaku Wauki makami dan ramawa?".
Cikin tarin kufula da harzu?a da kuma son cinma wata gagarumar manufar da ya daWe yana fatan ya samu da sai yau, fuska a haWe yace.
"Babu wani wanda zan kuma hana Waukan makami,
Dan kare kanshi da ramuwar kisar gillan da akeyi mana."
Cikin tarin Mamaki da al'ajabi Bappa da sauran dattawan suka buWe baki tare da kallon Ardo Bani, Jabeer ma idon ya buWe cikin sanyi yace.
"Baba Ardo kayi ha?uri, muyi aiki da al'?alami, domin al'?alami yafi tokobi, ina nan inata shirin samar da tsaro na musamman kan FULANIN ?asarmu da nake shugabanta."
Cikin nuna tsantsar fushi da son fusata LamiWo ArWo Bani ya dakawa Jabeer tsawa tare da cewa.
"Kada rufe min baki, meka sani akan Fulani? Me ruwanka damu? Damuwarmu ta shafeka ne? Ina kake sanda ake kashe mana mata, yara, jikoki, mu kanmu bamu tsiraba, in munje mun kai kukanmu a koremu tamkar karnuka, sabida duk baku san darajar fulani ba."
Cikin sauri ?anzagi yace.
"Hattara dai ?aramin Ardo, wannan sarkine na fulSe masarautar filSe ce gaba da bayanta".
Cikin Waga Muryar Ardo Bani yace.
"Tafi can ba?in bawa, bawan banza bawan wofi mai ka sani kan fulSe, meka sani banda bauta da fadanci, masarautar da kuke bautawa bata san menene fulSe ba".
Cikin sauri Waziri ya yun?ura zaiyi mgna, da sauri LamiWo ya dakatar dashi, sabida zuwa yanzu zuciyarshi ta fara tafasa, yaya daga kawowa mutane ziyara dan ja-jantawa suke neman tozarta mushi masarauta. Cikin Sacin rai ya kalli su Bappa daketa kama hannun ArWo bani daketa fizge-fizge yana kwaza musu ba?ar mgna, cikin fushi yace.
"Masarautar JoWa Wince bata fulani ba?".
A harzu?e ArWo Bani yace.
"Tabbas dan data fulanice, da an bamu kariya da tsaro, da an duba kukanmu, a kashemu a hanamu Waukar fansa, an kuma kasa bamu tsaro. Nan da mukaje ina shi jikan naka da yake matsayin Garkuwan Fulani, yana can ?asashen woje, da iya dukiyar da ake bashi tsaro da kariya shi rai Waya ta kai a kula da fulanin daji dubu a kuma basu tsaro.
Yau kwana uku da kashe mana mutane sai yau zaku Webo manyan riguna kuzo mana da batun wai kada mu rama, sara da suka da yanka mana mutane da akeyi,
Kaida kab zuriyar ka da masarauta ka, babu mutun Waya da zai iya jurar koda bulalar *(SHA?I)* ma bare sara da yanka da suka da wu?a a hakan kuke ganin kanku Fulani".
Cikin tarin zafin ?una da tafasar zuciya Waziri yace.
"To me kuke so muyi muku, tun randa akayi abun munzo bamu sameku ba".
A harzu?e Bukar yace.
"?arya ne babu wanda yazo".
A hankali Jabeer ya buWe baki da nufin zaiyi mgna sai yaji LamiWo na cewa.
"Uhum jinina kuke cewa ba fulaniba, to ko jaririn da aka haifa yau a jikin masarautar JoWa zai iya jurarar bulalar SHA?I bare manya ko Wan baiwa zai iya bare jinina ?a?ana ko jikokina, ko kun manta masarautar JoWa ce tushen ShaWi?".
Cikin son harzu?a LamiWo ArWo Bani yace.
"A da can baya ba, yanzu kuma da aka san lusarai ake haifa a masarautar inji an haramta shaWi a masarautar, yau in kun isa fulani ka bada Wan ka ko jikanka ayi gasar ShaWi dashi, in ya iya jurewa, to mun yarda mun gamsu ku fulanine ku masarautar Fulani, in kuwa kun kasa fidda goninku to, ku ba masarauta fulSe bace."
Wani irin karkarwa jikin LamiWo ya fara sabida fusata, wai suda masarautarsuce tushen fulSe a ?asar, su ake cewa ba fulani ba, har ake kiransu lusarai, Galadima, Waziri, Wambai, ?an iya, ?an buram, ?an Maliki, Sarkin Dawaki.
Gaba Waya hankalinsu yayi masifar tashi sabida ganin tsananin fushi da tashin hankalin Sarki LamiWo.
Jamil Jalal Haroon kuwa , hankalinsu na kan Jabeer bisa alamun yana cikin wani hali.
Shi kuwa Jabeer bugun da zuciyarshi keyi ne yasa,
Hankalinshi tashi, ?arfin addu'o'in da yakeyi ne, yashi iya fahimtar abinda suke cewa.
Kamar daga sama kamar cikin mafarki, sukaji murya LamiWo na cewa.
"Ga jikana, Jabeer GARKUWAN FULANI, na badashi a matsayin matashi mai yin gasar ShaWi ku fito da duk gwanin da kukega shine makurar gwayen yankinku. Ayi ShaWi dashi yadda zaku samu gamsuwar yakai matsayin ya kasance GARKUWAN FULANI".
Tunda ya amSaci sunan Jabeer, Sarkin Fada yayi wani irin murmushi mai cike da jin daWin alamun burinshi zai cika.
Hakama ArWo bani wani irin asirtaccen murmushi yayi.

Jala, Jamil, Haroon, Hashim, Imran, Galadima, kuwa wani irin zazzaro ido sukayi.
Cikin tsananin kaWuwa da firgicin batun LamiWo suka zuba mishi ido.

Bukar kuwa cikin karaji yace.
"Ba'ana Bukar shi zai kara dashi."
Ya ?arishe mgnar da fatan Ba'ana ya kashe wanda aka kira da Jabeer tunda jikan LamiWo ne.

Jabeer kuwa wani irin kallo yayi kakan nashi, irin kallon nan.
Na lallai kam tsohon nan ka haukace, ka zauce, ai bani bakam ko inuwata bazaku kuma gani a garinkuba bare kuyi wannan gwajin dashi.
Ga mamakinsu kab sai sukaji ArWo Bani na cewa.
"A yau Winan kuma Yanzun nan, a kuma nan za'ayi gasar ShaWi in har kun isa fulani."
Sosai LamiWo yaji hakan bai mishi ba dan a zotonshi za'asa ranane ya koma ya shirya Jabeer kafin ayi gasar, to fahimtar ?uresu suke neman yi, yasashi gyara zamanshi cikin danne fargabanshi na anya Jabeer zai iya jura yace.
"Na Aminc....!



Yau bisa wani uzuri ban samu yin posting da wuriba, kana kuma ba editing a gurguje na watsoshi, bari in nemo PAGE 16 ko zuwa yan da yamma ne.


34 / 72