Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   38 / 72

111K to 114K   out of 214K words

sauya salon ba dai".
Cikin jin daWi yace.
"Ba zai sauya saloba, dole zai bar ?asar sai dai shiri zaije ya ?ara, kafin ya dawo kuma, an aura min ke, shi kuma jikan sarki.
Muyi musu mubaya'a, mun yarda su masarauta JoWo fulani ne".
Cikin tsananin jin daWi tace.
"Allah ya tabbatar da haka ya Salmanu yasa kuma a samo su Ya Gaini cikin Bonon don Ni dai nafi zaton can suka kaisu.
In anyi gasar an cishi, ya bar kasar, a Waura aurenmu a ranar".
Da sauri tasa tafin hannunta ta rufe idanunta alamun jin kunya,
Shi kuwa Salmanu murmushi yayi tare da cewa.
"Iye yan Matana an girma, me ma za'ayi mana?".
Cikin kunya tace.
"Ban saniba".
Murmushi yayi kana yace.
"Ni ai bazan manceba tunda yanzu burin mu na kusa da cika, ayi mana aure, nima haka ne tsarina ana watsewa gasar suna tafiya, za'a Waura mana aure.
Kinga gashi dama na samu aiki a babban birninmu.
Sai mu tafi can abinmu ko Wannan mugun saurayin naki ya dawo bazai samemu ba".
Murmushi tayi shi kuwa ido ya zuba mata yana jin tarin farin ciki.

*DAN ALLAH DA MANZONSA DA DARAJAR IYAYENKI DA SUKA HAIFEKI SUKA BAKI TARBIYYA, KADA KI FITARMIN DA LITTAFINA DAN AL'FARMA ANNABI DA AL'?UR'ANI, KU DENA FITAR MIN DA LITTAFI DAN ALLAH=?O?
Da sauri ta gimtse dariyarta, cikin sanyi da tsoro ganinshi tamkar gilmawar wal?iya sai gashi a gabansu.
Wani irin azabebben tsorone ya rufe Salmanu amman sai ya dake, cikin ?arfin hali da kalato jarumta ya kame jikinshi dake rawa.
Cikin Wan rawan murya yace.
"Me haka, zuwa babu sallama?".
Wani mugun kallo ya watsa mishi tare da cewa.
"Kiyaye bakinka idan maza suna wuri."
Cikin dakiya Salmanu yace.
"Ina mazan!? Ai ni banga wani na miji a nanba sai mata maza. Ai namiji shi zai iya sa namiji Wan uwanshi zubda hawaye ko tsuma da faWuwa, a dai yanzu ai babu wani namiji a Rugar Bani da kewaye sama da Jarumin da bulalar SHA?I bata sashi zubda hawaye ba Sheykh nake nufi".
Wani irin zabura Ba'ana yayi ya nufi kansa alamun zai sha?eshi.
Da sauri ya tsaya jin Shatu ta saki ihu tare da cewa.
"Bana so ya Ba'ana in dai kana son farin ciki na, to kada ka dakeshi ko ka cutar dashi da komai".
Wani irin kallo ya mata mai cike da tuhuma da razana da kuma karaya,
Ita kuwa Shatu cikin rawan murya tace.
"Ya Salmanu ka tafi, bana so kaje ka bar koya min komai".
Cikin sau?e ajiyan zuciya na tsoro.
Salmanu ya juya ya tafi.

Shi kuwa Ba'ana, zama yayi inda Salmanu ya tashi, cikin taraddadin ko dai Shatu bata sonshi ne, ya nuna mata gefenshi.

A hankali ta zauna, shiru tayi tana sau?e shesshe?an kuka.
Cikin ?una da ba?in cikin rashin sa wancan Wan birni mai fata kamar ta jariri kukanne ya sakar mishi fargaba,
cikin sanyi yace.
"Mata!".
Bata kalleshi ba kuma bata dena shesshe?an ba.
Kiranta ya kuma yi a karo na uku.
"Mata!".
Cikin disashewar muryar tace.
"Na'am".
Juyowa yayi ya fuskanceta da kyau a hankali yace.
"Mata bakya so nane!?".
A bazata tambayarshi tazo mata,
ta ina kuma ta yaya zatace mishi bata sonshi, bayan tasan abin da yayi mata shekarun baya, dama fansar shi ta soshine kuma ta aureshi, da wanne bakin zatace mishi bata sonshi.
wasu zafafan hawaye masu Wumi ta zubda.
Ha?i?a ya Ba'ana mugune amman a iya saninta a kanta ya zama mugun, tunda sai wanda ya nuna baya sonta dashine yakewa mugunta,
Babbar matsalarshi mushirkine kuma baya salla.
Cikin rawan murya da kuka tace.
"A a Ya Ba'ana Ni bance bana sonka ba".
Da sauri yace.
"Uhhmmm to meyasa bakya ganin laifin Salmanu akan duk abinda yake min, ko dai shi kikeso ne Mata!?".
Da sauri ta jujjuya mishi kai sabida sanin ko jinkirin bashi amsa tayi zai iya yiwa Salmanu illa.
Cikin rawan murya tace.
"Bana son ka cutar da shine sabida, shi ya janye batun soyayyarsa gareni. Ka kuma sani karatu yake koya min amatsayinshi na wanda ya samu karantarwa a wata jami'a,
Yana sona da al'khairi kai kuma kana ?inshi, ko dai ka manta ka ce min zaka so duk wanda yake sona da al'khairi yake kuma taimaka min".
Jiki a mace ya gyaWa mata kai,
sai kuma ya rumtse idanunshi da yakejin suna cikowa da hawaye yace.
"Lokuta da dama sai inga kamar bakya farin cikin ganina, a madadin farin ciki sai inga tsorona cikin ?wayar idonki."
Juyowa tayi gareshi da kyau cikin kuka tace.
"Ba kai ke bani tsoroba, abinda kakeyi ne yake sani tsoronka, ya Ba'ana ka bar wannan asirce-asircen babu kyau shirka ne, wanda yake Waya daga cikin manyan zunuban da Ubangiji ya haramtawa mumini yin tsafi haramun ne".
Kanshi ya jingina da jikin gini yana kallonta tamkar yau ya fara ganinta,
A hankali ya fara mgna cikin muryar da bata taSa jin rauninta a muryarsa ba yace.
"Mata ina sonki, wallahi Allah kenan rantsuwar musulmai, ina sonki, son da ni kaina bansan adadinshi ba,
Duk abinda nakeyi a kanki nefa, Shatu ki min uzuri, na ro?eki kiyi min Wa'ar ri?e tukuicin abinda nai miki a baya,
Ki soni koda rabin yadda nake sonki ne.
Kiji tausayina Shatu ina jin tsoron kada ?addara ta rabamu,".
Kekkyawar fuskarshi ta zubawa ido, tana gani. Irin kyan da Allah yayi mishi sai dai sam babu kyan hali ya zama kyan Wan maciji.
Cikin sanyi tace.
"Ya Ba'ana tsoro kuma?".
Kai ya gyaWa mata cikin sanyi yace.
"Eh sabida muddin aka rabamu, zan zamewa fulani babban ?alubale a rayuwarsa, kuma duk wanda yayi sanadin rabuwata da ke, wallahi zaiga toskun rayuwar duniya, zaiyi dana sani, zan zama mugun zahiri. Na san ke Kum bakya son hakan.
Yau kuma fargaba na, yafi na baya yawaita da wannan jikan sarki ya iya daurewa azabar bulalina baiyi ?ollaba."
Wani irin ajiyan zuciya taja tare da cewa.
"Babu komai ya Ba'ana Ni dai ina tayi mana addu'an ALLAH yayi mana zaSi mafi al'khairi a rayuwata, ya kuma shige min gaba a dukkan motsina".
Ido ya zuba mata babu ko ?ebtawa, cikin sanyi yace.
"Nine mafa al'khairinki Mata".
Da sauri tace.
"Baka saniba".
A zafafe yace.
"Na sani mana".
Cikin tsoro tace.
"Kai masanin gaibu ne kenan?".
Mi?ewa tsaye yayi tare da cewa.
"Ehh kusan haka tunda nayi duba a kanki".
A hankali tace.
"Wa'iyazubillah. Duba ba gsky bane, zai iya maka ?arya".
Hannu ya Waga mata da sauri kana ya nuna mata hanyar shiga gida.
A hankali ta tashi tsaye cikin sanyi tace.
"Allah ya baka ha?uri ya shiryeka".
Ta ?arishe mgnar tana ?o?arin yin kuka.
Da sauri ya juyo cikin sanyi yace.
"Kada kiyi kukan mata, nayi ha?uri.
yanzu na fasa jiran Sai kin gama karatu ayi mana aure.
Duk randa wancan malamin ya dawo ya rama gasar ShaWinsa. Za'a Waura auren mu a ranar, domin
Koda duk bulalin duniyar nan zai zabgeni dasu wlh bazaici nasara a kainaba domin idona ba idon da zai zubda hawaye a kanki bane bilali Waya nake tsoro kuma babu wanda yasan inda suke.
In kuwa aka samu wani akasin dama bazai samuba, to zan bar ?asar nan zan koma ?asar Cameroon can babban birnin Yahunde, inbi cikin Rugar wasu fulanin.
Sai dai ko bana nan duk wanda ya aureki ya auri ajalinsa."
Bata iya tanka mishiba, a haka ya juya ya tafi.

Kana ita kuma ta koma cikin gida.


A cikin masarautar JoWa kuwa.

Sai da akayi sallan isha kafin.
Su Haroon suka dawo gida.
Suna tafe,
Abba da LamiWo da Galadima, da Dr Aliyu da kuma Sarkin ShaWi.
Suna biye dasu a baya.

Kai tsaye wucewa sukayi har bedroom Win Jabeer har yanzu bacci yakeyi.
Sai dai tunda lokacin salla yayi yaketa jin baccin ba daWi sai dai kuma Allah bai bashi ikon farkawa ba.
Dubashi sukayi tare da ?ara shafa mishi wasu magunguna kana suka fita suka tafi.

Hakama Gimbiya Aminatu tazo itama har Waki sai dai samunshi yana bacci yasa ta tafi.

Bayan fitanta ba daWe Barrister Kamal da Wan sa Sulaiman sukazo.
Suma har ciki suka shiga suka dubashi.
Kana suka tafi.


A ranan a daren gaba Waya mutanen masarautar kowa yaji lbrin abinda ya faru.

A falon su Jafar duk sukaci abinci.
Ganin dare ya tsalane yasa Juwairiyya jan hannun Jafar suka tafi.
Jalal, Jamil, Ya Hashim kuma sukayi musu saida safe kowa ya tafi side Win shi.

Jakadiyarsu kuwa itama ta nufi sashinta,
Ya zama dagashi sai Haroon.

Sha biyu da rabi dai-dai na dare.
Haroon zaune kan wata doguwar kujera irin ta sarakuna dake cikin Wakin.
Waya yakeyi da Jannart,
yana konce ne dagashi sai boxes.
Waya sukeyi irin ta mosoyan da sha?uwarsu tayi yawa,
Wani irin mi?a yayi wanda gaba Waya gabban jikinshi suka amsa.
Cikin tarin kasala da masifeffen shau?i yace.
"Wash Allah na".
Cikin kashe murya da ta ingizo Bukatarsa tace.
"Ohhh sorry Ya Haroon meya faru gaya min me yasameka".
Cikin sakaliyar murya yace.
"Haroon yunwa yakeji".
Sam bata fahimci inda batunshi ya dosaba haka yasa cikin haWa fuska tace,
"Ya Haroon ka dawo gida, shi Hamma Jabeer ba matace dashi ba, bare ya kula da cikinku, na kuma san in kuna Side Winsa ba wani zuwa wurin Aunty Juwairiyya zakuyiba, kuma itama fama takeyi da mijinta.
Ni gsky ka dawo Tsinako nasan Umaymah zata kular min da kai da kyau, ko kuma kazo Masarautarmu Leddi julSe, nida Sitti mu kula da kai".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Masarauta JoWo fa masarautace mai daraja, da karrama ba?o baki san asalin tarihin inda masarautar tasamu suna JoWa bako.
Baby kada ki damu kular da muke samu ko sarki mai mata huWu da kwarkawara biyar baya samu.
Tako wani sashi na gidan abinci hadimai ke kawowa Side Win Sheykh a ?alla wani lokacin kusan abinci kala goma muke riska, kinsan fulani ba marowata bane.
Kawai matsalar wannan yunwar rashinki ne, a kusa yasa nake jina ina tashi sama kamar doki".
Cikin kunya da kauda zancen tace.
"Ya jikin Hamma Jabeer shugaban tuzuran ?asar mu?".
A hankali ya juyo kanshi ya kalli bisa makeken gadon da Jabeer ke kai.
Da sauri ya katse kiran bayan yace mata.
"Ina zuwa".
Kan gadon ya nufa, jabeer Win yana ?o?arin tashi zaune.
Hannunshi daya mi?a zai taimaka mishi, ya buge cikin haWe fuska yace.
"Yanzu ?arfe nawa?".
Wayarshi dake hannunshi ya duba cikin zuba mishi ido yace.
"?arfe Waya dai-dai".
Cikin tsuke fuskarsa tamkar zaiyi kuka yace.
"Shine ka barni ina bacci kamar kafurin da bashi da addini.
Anyi sallan bamgrib baka tasheniba, anyi Isha'i baka tasheniba, daga wannan masifeffen bacci mara daWi mai cike da mafarkai marasa daWin da nasan rashin yin salla a lokacin sane ya jazamin su.
Iya wunin yau duk so kuke kuyi min asarar lokuta masu muhimmanci da daraja, kun sani na makara la'asar da magriba hakama isha."
Ya ?arishe mgnar yana mi?ewa tsaye,
Tare daci gaba da cewa.
"Da fari ansa ni na tsaya gaban jama'a da baiyana surata,
Aka Wora min da duka kana, akasa na makara sallan la'asar,
Yanzu kuma mangriba da isha'inma kun barni ina baccin asara na makara, sabida baka san darajar yin salla a cikin jam'i da kuma yin ta cikin lokacin ta ba ko?".
Cikin taSe baki Haroon yace.
"Kasan ai ni ba musulmi bane, ban san komaiba".
Harara ya dannawa Haroon tare da cewa.
"Kai ka gayawa kanka, Ni bana kafurta mutum, abinda na sani dai kai tsarin yahudu da nasarane,
To bari kaji, Ni bani da laifin komai sabida bacci nakeyi, mai bacci kuma al'?alami ya sau?a kansa har sai ya farka.
Kai dake ganina ina bacci lokacin salla yayi idonka biyu baka tasheniba ha??in a kanka ya rataya."
Ya ?arishe mgnar yana shiga bathroom tare da cewa.
"Ka cire idonka a kaina banza mai kallo kamar mayun wancan garin mugayen".
Murmushi Haroon yayi tare da komawa ya zauna bisa kujerar.

Shi kuwa Sheykh Jabeer wonka ya kumayi da ruwan Wumi,
kana ya kimtsa cikin irin suturun da yake ta'ammali dasu, in yana gida.
kana ya Waura wata farar jallabiya kai.
Sannan ya fito bayan ya shafa mai ya fesa turare.

Yana fita ya fara ramuwar sallan daya wuceshi yana bacci.

Haroon kuwa falo ya fita abincin da yasan zai iya ci ya kawo mishin

A ?alla awa Waya yayi kafin ya tashi kan sallayan
Gaban gadonshin ya dawo ya zauna bisa tattausan carpet Win da ke shimfiWe a wurin mai kalar Sky blue and white.
Sosai yaji daWin jikinshi, sai dai har yanzu yana jin raWaWin bulalin.
Tea kawai ya iya sha.
Kana a hankali yace wa Haroon.
"Canza min beshit Win nan da blanket Win."
Hararanshi Haroon yayi tare da cewa.
"Zan koma, yaseen na gaji da mulkinka da sarautar da kake ji dashi. Ji yadda ka medani tamkar wani bawanka ko hadimin gidanku, kuma duk abinda zanyi maka sai ka cini gyara, mutum ba'a iya mishi sai masifa kake min kamar dai nine nace a zaneka".
Ya ?arishe mgnar yana mi?ewa tsaye tare da gimtse dariyarshi, sabida ganin kallon da Jabeer ke mishi.
A haka dai ya sauya komai na gadon kafin suka, hau suka konta.
Tsaki Jabeer yaja tare da cewa.
"Ni dama ka tafi wancan Wakin sabida zancen gsky kasan ni bana son takura.
Sabida zaka hanani sakewa yadda nakeso".
Cikin gajiya Haroon yace.
"Allah babu inda zan fita inje".
Da haka dai Haroon yayi bacci.
Shi kuwa Sheykh Jabeer karatu yayi tayi har biyu da rabi tayi kana, ya buWe tafin hannunshi yayi addu'o'in bacci.
Fala?i 3 Nasi 3 ?ulhuwa 3 Ayatulkursi'u 1 kana amarrasulu 1 tofa a tafin hannunshi ya shafa a jikinshi.
Kana ya kuma yi. Haka ya tofa a tafin hannunshi ya shafa a jikin Haroon Wanda tuni ya Singire,
Shi kuwa Jabeer wannan al'adar rayuwarsa ce daya saba, kan Jalal da Jamil sabida suma haka suke bingirewa, shikeyi tofi ya shafa musu.

Washe gari LamiWo baiyi zaton Jabeer zai samu fitowa masallaci ba,
Shiyasa limamin dake jansu salla in baya nan ya fito ya jasu salla,
yayinda Jabeer ke cikin sahun forko.

Wannan yasa mutane sukayi zaton ciwon ne yayi tsamari bai samu ya fitoba.
Ana idar da salla kuma ya fito yayi cikin gida sabida.
Fushi yakeyi da wannan tsohon ya sani in ya tsaya kuma zai dameshi da wata falsafarshi da zaici karo da addini.


?arfe takwas dai-dai. Barrister Kamal da Ya Jafar, da kuma Baba Basiru ne zaune dashi a falon shi.

Suna zaune anan Jalal ya shigo cikin yanayin damuwa yace.
"Hamma Jabeer, Umma na falo tazo dubaka da jiki."
Cikin yamutsa fuska yace.
"Wacece hakan?".
Cikin fusata Baba Basiru yace.
"Ashe uwarka ma bazaka santa ba, ina dai baka san wacece Umma ba".
Wani irin kallon ido cikin ido Sheykh yayiwa Baba Basiru,
sai kuma ya Wora ?afarshi Waya kan Waya, cikin ?asaita ya kalli Jalal tare da cewa.
"Mene Umman!?". Ya sani sarari Gimbiya Saudatu ake cewa Ummu .
Gyara tsayuwa Jalal yayi tare da gyara zaman belt Win ?ugunshi yace.
"Matar tsohon Galadima marigayi, Baba Muhammad ce Ummar Gimbiya Saudatu."
Da sauri Baba Basiru yayiwa Jalal da?uwa tare da cewa.
"Kan uwarka hegen yaro Wan shila".
Shi kuwa Jabeer ?afarshi ya fara kaWawa.
Barrister Kamal kuwa ido ya zubawa Fuskarta Jabeer da Jalal. Cikin sanyi da tausasan laffuza yace.
"Jabeer tashi muje ka gaisa da ita tunda ta taso tazo har nan dubaka da jiki".
Kanshi ya gyaWawa Barrister Kamal Win wanda suke cewa Baba Kamal wanda yake mahaifin Sulaiman, sa'an Jabeer.
Da hannu yayiwa Jalal alamun yaje yace, yana zuwa.
Shi kam Baba Basiru bayan Jalal yabi.
A babban falon suka zauna shida Gimbiya Saudatu da Laminu da kuma Baba Nasiru.

Jalal, Jamil, Haroon, Jafar, kuwa duk suna can Dinning area kan dinning table sunayin breakfast.

A jere suka fito falon shida Barrister Kamal.

Suna isowa tsakiyar falon.
Cikin wani irin taku mai cike da ?asaita da rashin tsoro.
Ya kalli Gimbiya Saudatu dake zaune bisa kujerar zamanshi.
Yatsunshi biyu ya haWa ya kaWa mata tare da mata alamun tashi min kan kujera.
Cikin wani irin kallo mai nuna tsantsar fushi da tsana da zazzafan ?iyayya ta fara mgna cikin Waga sauti tace.
"Hegen yaro mai idanun mujiya, Ni kakeyiwa wannan iskancin dan kan uwar..!".
Kasa ?arisa zagin da tayi nufin yi tayi jin yana cewa.
"Kan uwarki ko? Ki ?ara sa mana kikaga ikon wanda ya hana mata gemu ya baiwa maza!
Maza tashi min kan kujerar zama tunda ba wancan jiSeSSen tsohon akun bane seyota".

Wani irin zabura Baba Nasiru yayi tare da Waga hannu zai kifeshi da mari, kamar a mafarki yaji an ri?e mishi hannunshi da sauri ya juyo.
Ido ya zaro cike da mamakin ganin wanda ya ri?e mishi hannunshi cikin tafasar zuciya da ?una yace.
"J....."






By
*GARKUWAR FULANI*
Cikin wani zare ido na masifa yace.
"Jalal ni ka ri?e wa hannu".
Shima idon ya zare tare da cewa.
"Ba iya rikeshi kaWai zanyi ba, in dai zai taSa lfyar Wan uwana a gaban idona, datseshi zanyi gaba Waya in wurgar". Ya ?arishe mgnar da ?arfi tare da yarfa hannunshi.
Wani irin asirtaccen murmushi Barrister Kamal, yayi tare da kallon Wan shi Sulaiman hannunshi ya dun?ule ya jinjina wa Sulaiman Win.
Kana suka koma suka zauna bisa kujera.
Shi kuwa Jabeer hannun ya nunawa Gimbiya Saudatu alamun ta tashi.
Mirtsitsi tayi tare da gyara zamanta.
Wani irin firgitacen tsawan da Jalal ya danna matane yasa, ta mi?e tsaye ba tare datasan ta mi?a Win ba.

Cikin ?asaita Jabeer ya baza tattausar al'kyabbar jikinshi,
Kana ya matso ya zauna bisa kujerar ?afarshi Waya ya Wora bisa Waya.
Gyara hiramin kanshi yayi tare dayin gyaran murya kana ya kalli ?annen mahaifin nashi kauda kanshi yayi ganin yadda suke wani irin cika da batse sun cika sunyi tamtsan da fushi.

Ita kuwa Gimbiya Saudatu zama tayi a kujerar dake kallon tashi
kujerar.
Itama Waura ?afa Waya tayi kan Waya.
Cikin iya tijara ta watso sabbin jaridu gabanshi.
Jaridar bankaWa da kuma kamfanin jaridar hantsi wato le?a gidan kuwa.
Murmushin muguntan tayi tare da cewa.
"Ga sakamakon sa insa da kayi dani jiya, na yau kuma shima yana nan tafe.
Nayi maka murna darajar labarin ya kai matsayin da shine a shafin forko na jaridun".
Da sauri Jalal ya sunkuyo yasa hannunshi ya Wauki jaridar ban?aWa.
Jiki na tsuma ya Wago ya kalli Gimbiya Saudatu cikin tashin hankali yace.
"Wannan ?arya ne, da babu jahilin da zai yarda dashi, wlh bazaku taSa cin nasara ba."
Hankali a tashe ya mi?awa Haroon jaridar tare da cewa.
"Ya Haroon gani zancen banzan da aka rubuta kan hotunan Hamma."
Da sauri Haroon dake sau?owa kan stpes Win sau?owa falon daga dinning area,
ya ?araso. Hannuyasa ya amshi jaridar.
Wani irin azabebben zufane ya fara keto mishin ganin abinda aka rubuta a jikin jaridar.

Jin jikinshi na rawane ya sashi zama kusa da Sulaiman.

Ummi kuwa dake tsaye a dinning area tana haWawa.
Jafar abin da zaici, gaba Waya ido ta zubo musu cikin taraddadin me aka rubuta.

Ita kuwa Gimbiya Saudatu wata iriyar sha?iyiyar dariya tayi tare da cewa.
"Ya haka dai ?an kanzagi, ku bawa shi uban gidan naku, jaridar yage me aka rubuta, daga nan sai inga bakinshi

38 / 72