Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   42 / 72

123K to 126K   out of 214K words

fari kin amsowa Ummey mgninta, da har ina son cutar dake da tun wancan lokacin zan cutar dake.
To amman bani da niyar cutarki, ina sonki ne sabida Allah, da kuma gsky da zuciya Waya, Shatu koda zaki ?i yarda dani a kan komai dan Allah ki yarda dani cewa ina sonki, na kuma soki a baya zan soki har gaban abadan, wlh babu ?arya a cikin soyayyarki a zuciyata, Shatu sonki shine babban raunina a duniya.
Har yau babu wani abu dake firgitani da bani tsoro sai rasaki.
Babu wani abu na duniya daya taSa sani zubda hawaye sai soyayyarki, dan Allah ki dena zaton dan na matso kusa dake zan cutar dake, ki amince dani in baki abinda idonki zai buWu da gane sihiri duk ?an?antarshi".
A hankali take juya mishi kai cikin sanyi tace.
"Na sani Ya Ba'ana wlh na yarda da kai akan soyayyata, na sani bazaka cutar daniba, tunda baka cutar dani a bayaba, nasan kana sona, na kuma yarda da son gsky kakemin, to amman ni bana son wadannan abubuwa asirce-asircen sabida haramun ne.
A hankali ya zame jikinshi ya zauna kan jijiyan bishiyar.
Ganin haka itama tayi sauri ta zauna bisa guiwowinta ta dur?ushe a ?asa.
Cikin mamaki tace.
"Dan Allah ya Ba'ana meyasa kwanan nan duka sai kayi ta zubda hawaye a gabana, hankalina yana tashi."
Kanshi ya Wan Waga ya kalli sama, a hankali yace.
"Shatu ina sonki zan kuma soki har iya numfashin na, bazan bari wani abu ya rabani da keba, in kuma akasamu wani ya zama ?addarar rabani dake, to shi kuwa tabbas zan rabashi da rayuwarshi, kiyi ha?uri in dai a kanki ne zan iya yin komai, na kuwa san duk duniya babu wanda yasan hanyar da za'abi a kamani ko aci galaba a kaina, sai ke ranki ke Waya tak ce kikasan duk wani sirrina ban saniba ko zaki iya min halacci ki sirranta min rayuwata".
Da sauri tasa hannu ta share hawayenta tare da cewa.
"Ya Ba'ana ai rayuwa a hannun Allah take, wata ?ilma in rigaka mutuwa, kuma in dai nice in sha Allah bazan baiyana sirrinka dan a cutar da kaiba, ko ba komai kana soma kuma kace dan zaka nemo su ya Gaini ne kayi wannan tsarin gudun kada mugaye su cutar da kai, Ni na sani Ya Ba'ana waWannan layun bazasu kareka ba, sabida ba hanyar Allah ka biba amman ni zanyi ta maka addu'a".
Ido ya zuba mata a zahiri da baWininta gsky ta faWi dan yaga hakan cikin ?wayar idanunta.
A hankali ya jawo tandun duma dake rataye a kafaWunshi, cikin sanyi yace.
"Ga ruwa kisha".
Da sauri ta jujjuya kanta tare da cewa.
"Bana jin ?ishi".
Tura mata tandun yayi gabanta tare da cewa.
"Eh ba mgnin ?ishi bane, kishi dan kiji sanyi a zuciyarki naga kina kuka".
Cikin share hawayenta tace.
"Ba kai bane ka sani kukan kana ta barmin amanar sirrikanka bayan kuma shi amana rikeshi nada girma da nauyi da wuya".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Zaiyi wuya ki ri?e kenan?".
Da sauri tace.
"In sha Allah zan ri?e".
Kanshi ya gyaWa tare da cewa.
"Bazaki sha bako?".
Kanta ta gyaWa mishi alamar eh.
Kana ta mi?a tsaye, gaba ta Wan yi kusa da Rafi'a, tace.
"Rafi'a mu tafi".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Rafi'a ku tsaya".
Cikin tsoronshi Rafi'a tace.
"To Ya Ba'ana".
Da sauri ya ?ara so gabansu, tare da cewa.
"Mata Wago hannunki mu gani kinada zobene?".
Kai ta girgiza alamar a a babu.
kana ta Waga hannunta na dama,
Yatsarshi ya karkaWa mata tare da cewa.
"Lalala Wago hannun hagu mu gani".
Cikin gajiya ta Wago hannunta, fararen tausasan zara-zaran yatsunta suka zubawa ido gaba Wayansu.

Babu zobe ko Waya a yatsunta,
Murmushi yayi kana yace.
"To bari in baki zoben ziyara, koda bakya tare dani, duk lokacin da na nake kusa dake kawai zakiga zoben a yatsunki".
Da sauri ta buWe baki da nufin cewa a a.
Kawai sai tayi shiru ganin wani irin zoben azurfa mai masifar ?yalli da she?i sai Wauke ido yakeyi.
Ta juyo zata ce mishi a a Ya cire sai kuma tayi shiru ganin ya Sace daga gabansu.
Yatsunta tasa da nufin cire zoben da sauri ta barshi jin tamkar yatsunta zasu tsinke.
Rafi'a kam tuni tayi gaba, haka yasa itama tabi bayanta.


Suna zuwa bakin titin suka samu motar zuwa cikin ?adamaya.

A can cikin masarautar JoWa kuwa,
Bayan an idar da salla, kamar kullum LamiWo ya gaggaisa da mutane, talakawan garinshi.
Shi kuwa Jabeer dashi da tawagarsa duk sun nufi cikin gida.
Sabida Galadima nata ce mishi su tafi cikin gida su fara shirin tafiya.

Haka yasa duk suka nufi cikin gidan masarauta.
A nan babban farfajiyar suka Wan tsaya.
Ido Jabeer ya Wan zubawa jerin motocin da a ?alla sun kai ashirin da biyar zuwa talatin an bisa alamu anyi manyan ba?i ne ko kuma za'ayi fita mai mahimmanci.

Cikin suka wuce a falo suka samu Umaymah, Hajia Mama, Aunty Juwairiyya, da Ummi, duk suna zaune suna Wan hira.
Hibba kuwa tana kitchen.

Suna isowa ta fito da sauri jin muryarsu.
A hankali ta isa gefen Jalal cikin yin ?asa da murya tace.
"Ya Jalal kazo kaci abinci karku tafi bakaci komaiba".
Kanshi ya Wan gyaWa mata,
Jamil ne ya hararesu tare da cewa.
"Allah shi ?ara, ai in dai Jalal ne kaWan kika gani da gwatsalel, mutumin da ba'a iya masa bare a masa gwaninta".
Haroon ne ya Wanyi dariya tare da cewa.
"Haka suke shida Jabeer yadda suke kamanninsu iri Waya hakama halinsu".
Da sauri Jamil ya zare ido tare da Wan ja da baya yace.
"Tab a a Ni dai wlh bance hakaba".
Jabeer kanshi Jamil ya bashi dariyar da dole ya Wan murmusa, tuni sukuma sauran dariya sukeyi.
Ya Jafar kuwa shi ganin murmushin Jabeer shine ke sashi murmusawa.

Ita kuwa Hibba tura baki tayi ta koma gefe ta zauna alamun tayi fushi, baibi ta kantaba, sai Jamil Win ne ya Wan lallasheta, haka dai sukayi ta yar raha, saida LamiWo ya aiko su fito kafin.
Suka mi?a duk suka fita, shi kuwa Sheykh Jabeer gefensu Hajia Mama da Umaymah ya Wan rusuna kusa da Umaymah a hankali yace.
"To Umaymah bari inje bisa umarnku ba don raina yaso ba".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Allah ya bada Sa'a ya kaiku lfy ya kuma dawo daku lfy, Allah ya tabbatar mana da al'khairan dake cikin wannan tafiyar, al'farma Annabi da Alqur'ani".
Amin Amin suka amsa baki Wayansu, Hajia Mama dasu Ummi ma duk sukayi mishi addu'a, kafin ya fito.

Yauma kamar ranar mota Waya suka shiga da Haroon da LamiWo da Ya Hashim da Laminu.

Kana sauran tawagar sarki.
Daga nan suka nufi hanyar fita gari su nufi garin Shikan.
A cikin motocinsu kamar na ranan.

A tsakiyar garin ?adamaya ne suke tafiya sun zo dai-dai bakin Genaral Hospital ?adawaya.
LamiWo ya bada umarnin cewa su shiga cikin asibitin zai kai ziyarar dubiya wa marasa lfya.

Nan take kuwa suka jujjuya akalan motocin.
Suka fara kutsa kai cikin asibitin.
Da ?arfi Jabeer ya rumtse idanunshi tare da furta.
"Lahaulawalaqutailla billah".
A hankali sabida wani irin masifeffen bugu da zuciyarshi tayi da ?arfin masifa.
Wani irin taraddadi ya diro masa.
Ya ilahi shine abinda ya ambata a saman lips Win shi.
Dip dab dip dab dip dab dip dab haka zuciyarshi ke harbawa da bugawa a tare a tare,
addu'o'in ya fara karantowa a zuciyarshi da harshenshi, yadda suke ?ara kutsawa cikin asibitin haka bugun zuciyarshin ke ?aruwa.

Anan cikin asibitin kuwa, A maraba da ba?i Shatu take tun zuwanta sabida, anan aka juye duk fulanin da suka samu rauni sanadin wannan faWan,
an zubesu a wurin gwamnatin jiha kuma tayi burus da batunsu sam bata bawa likitoci damar dubasuba,
Sai ma cewa sukayi sai fulanin sun nemo polices kafin a karSesu.
Su kuma dama ?an agaji ne ma suka taimaka suka kawosu nan Win ma.

Zuwan Shatu ne da Rafi'a da ta samesu a yashe hankalinta ya tashi.
Ranta yayi matu?ar Saci nan ta haura gidan sama inda can jerin jadawalin officer's Win DOCTOR'S suke.
Rafi'a na biye da ita tana rabka mata kira.
"Garkuwa! Garkuwa!! Ke GARKUWA!!! Ina zakije ne wai?".
Sam bata kula Rafi'a ba sabida abin da akayiwa ?an uwanta yayi masifar ci mata rai.

Ganin yadda take gudu-gudu da sassarfa ne yasa itama Rafi'a ta fara Binta da gudu-gudu da sassarfa.

Yayinda kuma dai-dai lokacin LamiWo da tawagarsa ma ke tafe suna shiga cikin gidan saman.
LamiWo ne a gaba sai Jabeer da Galadima dake gefenshi da Sarkin ShaWi.
Kana su Waziri da Wambai Matawalle da Makawa ?urSi Turaki Tafida da dai sauransu, kana Dogari na rike da laima wa LamiWo,
?anzagi kuwa ya kware murya yanata.
"Gyara kimtsi sarki ya gaisheku".
Kana sauran fadawa masu red and blue Win Uniform kuwa da tabka-tabkan rawuna babu kunne ko Waya suna biye dasu a baya da gefe gefe, suna tafe babu takalma, ga dogin bulali masu masifar tsawo da kauri suna jansu a ?asa.

LamiWo, Galadima, duk shigar manyan kaya na sarakuna, masu al'farma sukayi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer shigarsa ta al'farma na limamai yayi, wannan yasa kwarjinshi ya fi nasu.
Daga nesa zakace yafi shekarunshi in ka hangoshi sabida kamala da haibarsa da suka baiyana a fili.

Laminu kuwa tuni yayi gaba yana Waukar shigowarsu.
Sabida aikinshi na jarida dama neman rohotone aikinshi.

Sanadin saurin da suke Wanyi ne yakesa al'kyabbar jikinshi Wan buWewa tana bazuwa hakan sai ya zama kamar ?asaitace tasa yake wannan abun a wurin mai kallonshi.

Gaba daya duk ta inda suka zo wucewa, sai ya Waga hannunshi duka biyu, yayi musu sallama tare da cewa.
"Ya mai jiki?".
In sunce da sau?i. Sai yace.
"Laah Ba'as Wuhhuru in sha Allah".
Duk inda suka gilma sai an bisu da ido. Especially Jabeer da babu wanda zai kalleshi bai ?araba

Tuni labari ya kai ga kunnen Dim din asibitin.

Lokaci Waya ya kikkira DOCTOR'S Win ta wayar salulu ya sanar musu su kimtsa komai su kula da kowa yadda ya dace.
Mai martaba LamiWo na cikin asibitin.

Ita kuwa Shatu tana haurawa sama.
Ido take Wagawa ta duba sunan Office da mai Office Win Office na forko taga musulmine haka yasa ta kutsa kai ciki.
Zaune yake babu kowa sabida duk majinyatan sun tafi.
Wasu an duba su, wasu kuma korarsu akayi da cewa yau half day ne, sabida haka su tafi.
Da mamaki ya Wago kanshi jin an shigo mishi Office babu sallama. Da sauri yace.
"Waye?".
Sabida cikin shigar yan matan larabawa take.
Arabian gawd ne mai masifar kyau da taushi a jikinta wanda samanshi yake a dai-dai jikinta ?asa shi kuma yake a buWe, wasu irin duwatsune a jikin rigar tun daga sama har ?asa sai wal-wali sukeyi suna Waukar ido.
Tayi rolling kanta da Wan kwalin rigar fuskarta ta fito ras a ciki.
Wasu takalmi Golding color ne masu Wan tudu dai-dai misali sai ?ar ma dai-daiciyar hand bang mai masifar kyau shima Golding color ne, sai wayarta ?irar iPhone 11.
Fuskarta babu kolliya sai dai duk da haka bai hanata yin kyau ba gashin girarta ya konta lib-lib. Sai dai kuma ta rufe fuskar da tattausan Ni?ab sai dai bashi da duhu sosai.
To wannane ya hana Dr Salim ganin fuskanta, ita kuwa Shatu cikin tsananin Sacin rai da zafin tozarcin da akayi wa yan uwanta tace.
"Dr Salim".
Cikin Mamaki yace.
"Na'am". Yatsarta tasa tana nuna mishi maraba da ba?i ta wondon shi, cikin rauni tace.
"Dr Salim na tabbatar kai musulmine, kuma nasan kasan cew manzon Allah yace shi musulmi Wan uwan musulmine! Shin ko ka mance hakane, da ka kasa taimakawa yan uwanka musulmai da kafurai sukayi musu rauni akazo aka watsar dasu a nan kuma kuka ?i dubasu meyasa, ko dan kawai sun kasance fulanin dajine laifinsu?".
Cikin sanyi Dr Salim yace.
"Wallahi umarni ne ba'a bamuba daga sama".
Cikin tafasar zuciya tace.
"Umarni wanne irin umarni kuma zaku jira bayan Allah da Manzonsa sun baku dukkan dama da umarnin taimakawa Wan uwanku musulmi muddin kunada dama".
Mi?ewa tsaye yayi tare da cewa.
"Dim Winmu ne ya hanamu dubasu".
Cikin kufula tace.
"Kan kafurar uwarshi! wato a cikin asibitima sai an mana ?abilan ci, dan Allah Dr kuje ku taimakawa bayin Allancan".

Cikin jin ?arfin guiwa ya juya, ya fita, ya nufi can.
Ita kuma haka ta rin?a bin duk Office Win da taga na musulmi ne tana shiga.

Tawagar LamiWo kuwa suna isa ba?in wani tamfatsetsen Office Sheykh Jabeer, ya Wan kalli LamiWo tare da cewa.
"Ni bari in shiga office na, ko mutun biyar in duba kafin ku gama zagayawa".
Cikin gamsuwa da hakan LamiWo yace.
"To bisimilla".
Nan ya nufi babban barandar da Nurses suke tare a wurin maza da mata.
Jamil kuma na biye dashi da System Winshi a hannunshi. Hakama Haroon ya biyoshi.

Nurses Win kuwa suna hangoshi duk suka mimmi?e tare da cewa.
"Sir barka da zuwa".
Barka dai yake ce musu tare da ratsawa yana wucewa.
Su kuwa sun taru a wurin ne dan tawagar LamiWo na wucewa su sau?a ?asa su duba Fulanin nan kamar yadda Dim Winsu ya basu umarni sabida kada LamiWo ya gansu a yashe a ?asa yasan abun bazai mishi daWi ba.
Suna ganin ya shiga Office Win suka juya da nufin zasu tafin sai kuma suka tsaya jiyo muryar Shatu na cewa.
"Ku tsaya ina kuma zakuje? Baku da aikin yi ko? Amman da yake ba taimako ne a zu?atankuba kun bar bayin Allah a wula?ance ko?".
Cikin masifar Nurses da su ba komaiba sai iya ciwa mutane zarafi a hatsale tace.
"Ke kuma waye".
Kallonta Shatu tayi sama da ?asa tare da kallon rubutun dake saman aljihun rigarta ganin sunan arniyace ga kai da gashin doki ga uban faratu kamar na jaki yasa taja tsaki tare da cewa.
"Banyi da keba, da masu hijabi nake mgn".
Yadda tayi mgnar da ?arfi ne yasa, su Jabeer ma jiyo muryarta,
wanda shi kuwa zuwa yanzu yana jin zuciyarshi zata iya faWowa ?asa dan bugawar da takeyi.
Jin muryar wata nurse Win tana cewa.
"Wannan ma ai iskanci ne".
Cikin taSe fuska ya nunawa Jalal yatsa alamun ya buWe mushi ?ofar yaga meke faruwa da suka cika mishi kunne da hayaniya.
Da sauri Haroon yabiyo bayan Jalal suka fito.

Shi kuma Sheykh Jabeer komawa yayi ya jingina da jikin kujerar shi.
Tare da rage girman idonshi ya zubawa bayan Shatu ido.

Ita kuwa Shatu cikin zafi ta kalli arniyar nan da tace mata wannan ma ai iskanci ne tace.
"A kul kada ki kuskura ki sake kira min iskanci a gabana, ke kika sanshi ba niba, ke kika taso cikinsa".
Sai kuma ta juya harce cikin fillanci tace.
"Shegu masu wari".
Sai kuma ta juyo ta fuskancesu da kyau, Haroon kuwa da Jalal ido suka zuba mata cikin mamaki.
Shima Jabeer idon ya zuba mata so yake yaji meyasata ihun nan.
Ita kuwa Shatu cikin sanyi ta fuskanci musulman ciki murya a Wan tashe tace.
"Kada dai ku manta nace daku nakeyi masu hijabi sabida nasan kun san ma'anar Al'muslim akul muslim. Kun kuma san girma da daraja da kuma wanda ya faWi hakan".
Cikin gamsuwa duk suka Waga mata kai, rai a ?untace tace.
"To meyasa kuka bar waWanan can bayin Allah'n a tozarce a yashe a maraba da ba?i koda dreesing na raunuka su bakuyi musuba, menene laifinsu, kawai dan sun kasance fulanin daji, shiyasa DOCTOR'S da Nurse's kab bazaku ji?ansu ba".
Cikin sanyi Waya daga cikinsu tace.
"Ayyah yanzuma can zamu tafi. Sabida sai yanzu Dim ya bamu umarni".
Wani dogon tsaki taja tare da cewa.
"Daga baya kenan yau kwanansu goma cib babu wanda daya dubasu, sai da suka gama jigata".
Tsaki arnan ciki sukaja tare da juyawa suka tafi.

A hankali Jalal ya juyo ya kalli Hammanshi da yake cewa.
"Rufe min ?ofa wannan ta cika min kunne da ihu".
Da sauri yace to.
Haroon kuwa murmushi yayi tare da juyowa zai shiga ciki kafin Jalal ya rufe ?ofar.
Da sauri ta juyo jin takun mutun a bayanta,
Cikin muryar umarni tace wa Jalal.
"Kai mai kamar larabawa tsaya kada ka rufe ?ofar, Office Win na arne ne ko musulmi?".
Cikin dariya Haroon yace.
"Na musulmi ne".
Taku ta fara tare da nufo cikin Office Win.
Wani irin sunkuyawa Jabeer yayi ya kifa ?irjinshi kan babban Glass table dake gabanshi, sabida ji yakeyi tamkar kan zuciyarshi take taku. Ji yakeyi zuciyarshi zata fashe tsabar yadda take bugawa da azaban ?arfi yadda take ?ara matsoshi haka bugawa zuciyarshi ke ?ara tsananta.
Cikin mamaki ta zubawa Office Win ido. Office ne mai matukar girma da kyau da tsaruwa, kai bakace Dr Office bane in ba Wan wannan gadon da labulanshi da sauran kayan aiyukansu ka ganiba.
Duk da sai sati-sati yake zuwa nan Office Win tsab-tsab sai wani irin sanyi da ?amshi yakeyi, cikin taSe fuska tace.
"Me hakan shima DOCTOR baida lfy ne? Kodai tsabar wula?anci ne?".
Murmushi mai kama da dariya Haroon yayi sabida yasan babu abinda Jabeer ya tsana yake kuma tsoro kamar a tsaya a kanshi ana mgna da ?arfi, yo shi ko a hankali kake mgna sai yace kana mishi ihu a kai bare kuma wannan da take tsaye a kusa dashi kuma tana mgna da ?arfi cewa zaiyi haushi takeyi."
Shi kuwa Sheykh Jabeer hannunshi yasa yana dafe ?ahon zuciyarshi da yakejin yana tsalle.

Rafi'a kuwa tsaye tayi a bakin ?ofar tana kallon ikon Allah.

Sauran Nurses Win kuwa suma, tuni sun tafi, maraba da ba?in.

Ita ko Shatu a hankali ta ?ara motsowa gaban table Win hannunta tasa ta bug...



=??=??=??=??tsawon shekaru labarin littafin GARKUWA yana kimtse a kaina da zuciyata. Ni kaina in na tunoshi sai nayi murmushi nayi shau?i sar?a?iyarsa kan hanani baccin dare inyi ta nazartan lmrin lbrin GARKUWA, nakanji murmushi da daWi in na tuna lbrin nakan zubda hawaye wasu lokutan wasu lokutan nakanji jikina yayi sanyi da rayuwar duniya, labarin Garkuwa bazaka ganeshi ba, sai in ka karantashi duk iya lbrin mai labartawa bazai labarta maka yadda komai yakeba, Uhummm Allah ya nuna mana ?arshensa, salon soyayyar Sheykh ta musamman ce..

Masoyan Parvina kuna sani dariya.

Masoyan Shatu kuna burgeni.
Ina masoyan Boleru jinjinan girma gareku.

Masoyan Sheykh ina sonku,
Sheykh yana gaidaku.

Masoyan Jalal yace ku dena kallonshi.

Masoyan Umaymah tace ku tayata da addu'a Allah ya yaye musu matsalarsu.

Wai Ya Ba'ana baida masoya ne?
Allah sarki Ba'ana ina sonshi dan al'khairin da yayiwa Aysha a baya. To wai wane al'khairi yayi mata ne?

Littafin GARKUWA na kuWine in kina bu?atan Normal group turo katin mtn na Wari uku kacal ta wannan number 09097853276. In kuma special Group kikeso kiyi min TRANSFER Win dubu Waya rak ta asusun na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853276. Masu turo katin mtn numbers Win zaki turo ba hotonba.







By
*GARKUWAR FULANI*
Ta Wan buga table Win, tare da cewa.
"Malam ka

42 / 72