Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   69 / 72

204K to 207K   out of 214K words

zuba mata mai Wan yawa.
Kana ta turo mata plate Win gabanta, kunu ta tsiyaya mata a cup mai Wan girma ta mi?a mata tare da cewa.
"Yauwa maza kici zakiji daWin jikinki".
A hankali ta gyaWa mata kai, dan bacci ya fara kashe mata jiki.
Cikin lumshe ido ta fara sawa a bakinta.
Jin wani irin WanWano mai daWi ya ziyarce harshenta ne yasata, lumshe ido tare da haWiye tsinkekken yawun bakinta ta cigaba da taunawa tana haWiyewa tare da korawa da kunun geron.

Ummi kuwa tana ganin ta faraci ne ta wuce ta fita.

Bayan ta gama ta shanye kunun don shi ma ya yi mata daWi sosai.

Cike da bacci ta Waura plate Win kan kofin ta turasu gefe kana a kasalance.
Ta wonke hannunta.
hamma mai sanyi tayi kana ta kwanta nan bacci ya yayi awon gaba da ita.

Shi kuwa Sheikh yana dawowa daga sallar isha Sangarensa ya wuce kai tsaye.
Yana shiga bedroom Win sa ya zare al,kyabbarsa tare ta ajiye hirami gefen gadonsa ya zauna, yana ajiyar zuciya tare da lumshe idonsa.
Wayarsa ce ta yi suwa,
Ido ya zubawa wayar yana kallon mai kiran, kamar ba zai Waga ba,
Sai kuma dai ya janyota hade da murza screen Win wayar.
Da sallama ya amsa. Cikin zolaya Haroon ya ce.
"Barka da dare angon Shatu."
Wani Wan guntun Murmushi Sheikh ya yi, haka nan yaji sunan yamishi raWau yayi masa a kunne a zahiri kuwa Wan gajeren tsaki yaja tare da cewa.
"Bana son surutu fa." Cikin Murmushi shi ma Haroon yace.
"Kasan dai ba ?arya na yi ba, balle ka fara yi min wa'azi."
Gyada kansa yayi tare da cewa.
"To ina jinka menene zaka kirani da daren nan?".
Murmushi nan Haroon ya cigaba da tsokanarshi har ya gaji ya katse kiran.

Dai-dai lokacin kuma ya ya fara jin yunwa haWe da zazzabi mai zafin gaske wanda ya jisa atake.
A hankali ya mi?e yana jin zazzaSin tamkar wanda ake ?arawa tun daga kan yatsansa har zuwa saman kansa, cikin tafiya a hankali ya fito daga bedroom Win zazzaSin na cigaba da fisgarsa da ?yar ya kai tsa?iyar falon ya zauna kan kujerun dake falon, a hankali ya kwantar da kansa jikin kujerar yana furzar da numfashi mai zafi, lumshe ido ya yi, saboda ?ugin yunwa da cikinsa ke yi, zaman da ya yi, so yake ya ji dama-dama ya ci abincin ya kwanta, tun yana iya jujjuya jikinsa har ya gagara yin hakan saboda ilahirin gaSoSinsa sun amsa da zazzafan zazzaSin ji yakeyi gaba Waya gabban jikinsa kamar allurai ake sokawa mushi, yana nan kwance har wajen ?arfe Waya na dare jikinsa na karkarwa.
Cikin rawan sanyi da?yar ya lallaSa ya samu ya shiga bedroom ya kwanta a kan gadon a gicciye, hannunsa na rawar Wari ya janyo blanket ya rufe dukkan jikinsa, shi kansa yana jiyo hucin numfashinsa da zafi, yana yi yana Wan nishin azaba ?adan,
a haka ya samu yayi baccin wahala mai cike da rikitaccen mafarki mara kan gado.

Kiran sallan farko ne ya tashe shi, cikin yanayi wanda bai saba tsintar kansa ciki ba ya mi?e, kasala-kasala gajiya-gajiya, ga mamakinsa zazzaSin ya sauka, don yana ga Wumin da jikinsa ya fitar da gumi alamun sau?an zazzaSi duk da akwai sanyi ac, addu'a ya yi ya mi?e a hankali ya shige toilet sai da yayi wonka da ruwa mai sanyi sannan yaji jikinsa ya yi masa daWi.
Da sauri ya fito ya fara shirin zuwa masallacin masarautar don har sun fara kiran assalatu.

Bayan sun idar da sallan acan ya yi zamansa don gabatar da azkar da sauran addu'o'in da yake gabatarwa a dai-dai lokacin, sai da gari ya yi washe sannan ya dawo ya wuce falonsa kai tsaye.

Da hantsi ya fito daga falon. Cikin shigarsa ta yau da kullum.
A nan ya taradda su ita da Ummi suna zaune.
Da alamun Ummi nata lallashinta akan ta yi breakfast ne.

Tsayuwa ya Wan yi gefensu tare da cewa.
"Ummi yunwa".
murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Dama yanzu nakeso Aysha taci, sai ta kai maka nakan."

A hankali ya Wan yi taku biyu zuwa uku, ya kana ya zauna bisa kujerar dake fuskantar tasu.
Ido ya Wan zuba mata, tare da jingina kansa jikin kujera.
Cike da wani irin mayataccen shau?i.

Ita kuwa Aysha yatsun sawunshi ta zubawa ido, tare da sha?an ?amshin turaren jikinshi dan tun da ya shigo daddaWan ?amshin turarensa ya cika wajen har sai da Aysha ta lumshe ido, Allah ma ya sani tana masifar son ?amshin turarensa.

Idonshi ya Wan buWe tare da ?an?ancesu kana ya tsira mata su yana kallonta, a nutse sai kuma yayi wani gajeren.
Murmushi cikin nutsuwa da jera kalami yace.
"Me zai sa ace ba za a ci abincin safe ba? bayan kuma shi ya fi kowanne amfani a jikin Wan adam?".
Kallon shi ta yi tare da kwaSe fuska kana ta Wan tura bakinta tare da fara magana ?asa-?asa can cikin ma?oshinta.
"Dama ba dole kace haka ba, tunda kai ne sanadiyyar ciwon, kuma ba ajikinka yake ba." Ummi dake gefenta ta jita sarai duk da ba kalmomin duka ta ji ba amma tasan abinda take nufi.

Shi kuwa Sheykh Jabeer lumshe ido ya kumayi tare da sauke sassayan numfashi kana ya buWe idon ya zubasu kan bakinta.
Kallon bakinta yayi ba tare da ta gama haWe lips Wintaba yace.
"Kika ce kin yi yajin cin abinci?".
Ya faWa da zolaya duk da ba halinsa ba ne, ba kuma Wabi'arsa bane.
Shima kanshi bai san ya aka yi zuciyarsa ta raya masa faWin hakanba.
Lips Winsa ya Wan laso da harshensa lokacin da yaji tana cewa.
"Uhmm ni ba haka na ce ba."
Gyara zamansa ya yi yana mata wani irin kallo mai cike da fassara, kallon nasa ne ya sa mata mutuwar jiki da kasala, don sai da ta ji wani iri a jikinta sabida wani irin kallone mai tsada da masifar ratsa jiki da zuciya.
Shi kuwa cikin tsareta da idon yace.
"Uhumm to muna jinki Aaaaishhh!".
Kiran sunanta da yayi da wata siga haka ya sa ta Wago kai ta zuba mishi ido.
Sai kuma ta kauda kanta da sauri tare da sau?e numfashi,
kwarjininsa ne ya cika mata ido sai wani Murmushi mai tsada da yake mata.
Cikin narkekkiyar murya tace.
"Cewa na yi na ?oshi."
Ta ?arashe mgnar tana kauda kai aranta tana jinjina kwarjini da haiba irin ta shi.

"Yarinyar goye a ke yiwa dole ta ci abinci fa, ko kema sai Ummin ta goyaki zaki ci? Tunda naga nima mancewa sani takeyi sai ke".
Dariya Ummi tayi tace. "Idan zata ci sai na goyata".
Cikin jin kunya ta sunkuyar da kai ?asa tana nanata zancensa wai agoyata.
"Yi ha?uri ki ci abincin kin ji." ta kuma jin muryarsa a bazata.

Janyo flask Win yayi gabanta,
flask Win ta Wan kalla tana jujjuya kwayar idanunta, cikin ranta take jin kwarjininsa ke yi mata barazana da ta ji shakkarsa, ban da haka ba zata iya shan da ruwan zafi acikinta ba sabida Wazu da sassafe Ummi ta sata cin sauran naman ji data Wumama mata.
Sama-sama a haka ta ci abincin da Wan yawa duk da bata so cinsa ba.

Tana gamawa Ummi ta kwashe kayan kwanukan, shi kuma Sheikh ya wuce falonsa.

Yana shiga Jamil ya shigo, shi da Juwairiyya, zama suka yi suna hira Ummi ce ta Wan kalli gefen da Aysha ke zaune tare da cewa.
"Yauwa Aysha tashi ki kaiwa Sheykh abincinsa".
Cikin sanyi tace.
"Ayyah Ummi bawa Jamil ya kai mishi".
Sai kuma ta kalli Jamil tare da cewa.
"Jamil Wauki ka kai mishi".
Ta ?are mgnar tana Soye ainihin tsoron sake shiga inda yake da takejin.
Murmushi Ummi tayi dan ta ganota, tray'n ta mi?awa Jamil dake cewa.
"Ummi kawo dai in kai dan ke".
Murmushi sukayi, kana shi kuma ya kai mishi sannan ya fiti.
ba su daWe ba Yah Ja'afar ya shigo shi ma ya zauna kusa da Jamil nan suka Wan ci gaba da hirarsu

Haka dai sukayi wunin wannan.
Ranar cikin farin ciki suka yini don anan falon suka ci abinci dukansu.


Da daddare ba yanda Ummi ba ta yi da Shatu ba akan ta kaiwa Sheikh abinci ta ?i, sai da kanta ta kai masa.
Don Aysha tsoron zuwa Sangarensa take, saboda har yanzun tana jin jiki.

Washegari ma da safe Ummin ce ta bawa Jamil ya kai masa, don fir Aysha ta ?i zuwa.

Bayan yayi wanka ya fito, ya shafa mai ya kimtsa cikin wani tattausan yafi boyel mai taushi da kyau, Sky blue ne sai aikin da akayi mishi da farin zare sosai yayi kyau sai ?amshi yake zubawa.

A haka ya fito falonshi
breakfast Winsa Wanda yana kimtsawa ya jiyo muryar Jamil Win na ce masa ga breakfast Winka Hamma Jabeer.

Zama yayi bisa kujera, yana mai mgnar zuci. "Rabon Aiiish da side Winna tun shekaran da safe yau kwana biyu kenan ana na uku rabon data shigo nan". Murmushi mai yelwa yayi wanda bai san dalilinsa ba.
"Uwar raki da tsoro".
Ya faWi a fili lokacin da ya fito babban falon ba kowa a falon haka yasa ya wuce yana girgiza kai ya wuce dan sauri yake Asibitinshi zaije.


Bayan ya shiga asibitin Waki Waki ya bi duk marasa lafiyan ciki suna gaisawa tare da basu taimako na musamman yana duba lfyarsu wanda dama hakan al'adarsa ce kyautawa marasa lafiya, bayan ya gama da shiga Wakunan suna binsa da addu'o'in nasara da lfy a rayuwarsa.

Ya wuce office Winsa don duba outpatient, lumshe ido yayi bayan ya zauna kan kujerar,
Mi?a ya Wanyi a hankali tare da yin salati.
Gaba Waya yanayi shi ya sauya.
Tun jiya yake jinsa cikin wani irin matsi.
Yau kuma tunda gari ya waye yake jin wani abu na fusgarsa a hankali yake dannewa zamansa waje Waya ya ji abun na ?o?arin son bijire masa, patient ne ya shigo, ya duba sa cikin kulawa tare da Waukan dukkan bayanansa ya rubuta masa magani ya fice, kwantar da kansa yayi jikin kujerar haWe da lumshe idunsa da suka ?an?ance saboda wani irin feelings yake ji na bin sassan jikinsa a haka ya duba dukkan patient Win sai gab da magriba ya bar asibitin saboda hadari da ya fara haWuwa alamar za a yi ruwan sama.

Direct masarautar JoWa wuce.
Yana shiga cikin masarautar kai tsaye Masallaci ya wuce don yana shiga cikin farfajiyar gidan aka kira salla.

Bai fito daga masallacin ba, sai da aka yi sallan isha'i sannan ya fito ya nufi gida.

Sosai yake jin wani irin masifeffen feelings mai shegen fitina yana bibiyar sasan jikinsa gaba Waya, a haka ya shigo falon, su Jalal na biye dashi a baya.

Ba a falon Ummi na Walinta hakama Aysha.

Wuce Side Winsa yayi.

Su kuwa su Jalal abincindu suka Wauka suka tafi Side Winsu sabida jin yayyafi ya fara sauka tare da wata iriyar sassayar iska mai sanyi daWi mai ratsa jiki.

A Dinning area ya nufa.
cikin kasala da gajiya da yunwa ya zauna.
Abinci ya Wan zuba kana ya fara ci yana mai matse cinyoyinsa yana mgnar zuci.
"To shi wannan me yake bu?ata ne da zai hanani zaman lfy, ina dalilin da zakayi ta tashi tsaye, uwar me kakeso kayi".
Sai kuma ya Wan sha ruwan sanyi tare daci gaba da mgnar zuci.
"To ita wannan uwar tsoron ma ni rabon da ita kwana biyu, na lura tsoron zuwa nan Win ma takeyi."
Mitssssss ya Wan ja dogon tsaki tare da tafin hannunshi ya dafe kanshi.
Yau gaba daya sha'awarta ta cika shi don har sai da ya ji Jabeer Winshi tana harbawa da cekiyar neman aminiyarta.

A hankali ya mi?e ya bar wurin.
A kasalance sabida ua fara jin zazzaSin nan na ?o?arin da yanzu kullum yake kwana dashi yana bin jikinsa, da sauri ya nemo paracetamol yasha.

Sai dai abin mamaki ba abinda yayi masa don ji yayi kamar ma ?ara ciwon aka yi jingina ya yi da kujerar yana sakin ajiyar zuciya tare da tambayar kansa meyasa ne? Meke damuna?".
Yau dare na huWu kenan Kullum da zazzaSi yake kwana a jikinsa, asuban fari yayi lfy, sai kuma wani daren. cikin sanyi yace.
"Ya zama dole inyiwa kaina medical checkup".
Don zazzaSin na da zafin gaske, saboda ya fara jin ya yi loosing appatite, da ?yar ya samu ya yi bacci don abubuwan sun haWun masa goma da ashirin ga zazzaSi ga azabebben Feelings mai fitinarwa.

Tun asuba ya tashi bayan zazzaSin ya sauka, cike da kuzari da kuma tarin Feelings ya shirya ya wuce masallaci yana danne kanshi.

Yau yini akayi zurr ana tsuga ruwa kamar da bakin kwarya sai gab magriba ya Wauke.
zuwa dare garin yayi luffff gwanin sha'awa sai iska mai sanyi da Wan karen daWi dake kaWawa tare da ?amshin ?asa, yanayin garin yayi daWi ko ina lib gwanin ban sha'awa da birgewa.

Bai shigo ba sai bayan sallar isha'i, kai tsaye side Winsa ya shige yana jinjina yau kwanansa uku rabon da ya sa Shatu cikin idonsa gaba Waya ta mai da shi dodo ta ?i yarda su haWu, ko abinci ne sai dai Ummi ko Jamil su kawo masa ga tsananin jarababbiyar sha'awarta da take fusgarsa yau kwana biyu, da ?yar ya iya cin abincin yana jin alamomin bayyanar nataccen zazzaSin da yake duk dare wanda baya jin magani ya kuma rasa meye sanadinsa ga kuma wannan mayataccen Feelings dake hanashi nitsuwa.

Zubawa sarautar Allah ido ya yi, yana jira yaga wai ko zata zo kuwa saboda yau kwana nawa rabon da su haWu.

Wuce su da ya yi a falo suna hira ya kuma ce Ummi ta bata zam-zam ta kawo mishi yasa ya yi tunanin ko zata zo.

Shiru-shiru har goma da rabi hakan yasa ya mi?e ya fito falon ya tarar da su suna hira ita da Ummin, jikinsa sanyaye alamun zazzaSin ya kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi zam-zam Winfa".
Juyowa Ummi tayi cikin kula tace.
"Aysha baki kai bane?".
Kanta a sunkuye tace.
"Na kai mana yana kan Dinning table Win ka na ajiye".
Juyowa yayi ya Wan zuba mata ido,
sai kuma ya jinjina kai ya juya ya koma cikin falonsa .
yana lallaSa kansa don sha'awarta na ta fusgarsa musamman sautin dariyarta da ya ji tana yi, sai da Jabeer Winsa ta harba da masifar ?arfi.


?arfe sha daya da minti goma ya kara komawa falon ya tarar da su har da Jamil da Jalal, da Ummin suna hira sosai, haushi ya kama shi, haka nan yaji sun nashi haushi, kamar ya rufesu da duka.
Don dariyar da suke yi cikin hirar ya sa ya Wan tunzira yana jin kamar ma da shi suke, hakan yasa ya fito da sauri cikin faWa yace.
"Jamil meye ya hanaka bacci ka zo ka tasa mutane a gaba da surutu kamar lalataccen Radio?".
Gyada kai Jamil ya yi tare da cewa.
"Eh yanzu zan tafi, Ummi ce ta faWa mana mana, in munci dai zamu tafi."
Sai kuma yayi magana ?asa-?asa.
"Yau kuma waya taSo Sheykh alaramma akarmakallu, Hamma Jabeer naga masifa da fushi yakeji."
Bai ji mai ya ce ba, amma yaga dukansu sun kuma yin dariya ?asa-?asa a hankali, mi?ewa Jamil ya mi?e tare cewa.
"Asha bacci lafiya Sheikh Hamma Jabeer".
Ya wuce ba tare da Sheikh Win ya sake magana ba, don shi ma daki ya koma, saboda yaga Ummin ita ko motsi bata yi ba daga inda take a zaune shima Jalal mo?ewa yayi yabi bayan Jamil dake fita yana dariya.

Suna fita Aysha ta Wan juyo, ta fuskanci Ummi da kyau kana da gyara zamanta.
Numfashin ta Wan fidda a hankali, sannan ta juya kanta ta Wan kalli corridor'n shiga falon Sheykh.
Ummi kuwa ido ta zuba mata ganin yadda take waige-waige da alamun mgna mai mahimmanci takeson suyi.
Cikin nitsuwa da yin ?asa da murya tace.
"Ayyah Ummi dan Allah zan tambayeki wani abun dake damuna, dan Allah Ummi ki gaya min gskyr meke faruwa a masarautar JoWa".
Woni dogon numfashi Ummi ta sau?e tare da cewa.
"In sha Allahu zan gaya miki gskyar da na sani a masarautar JoWa, sai dai ina sirrine shi bazan faWa miki sittin wasuba".
Cikin sanyi ta ?ara matsowa gaban Ummi kai ta ron?ofar bisa kafaWunta kana cikin sanyi tace.
"Ummi koda sirrin Yah Sheykh ne baza ki gaya minba?".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"To ai shi sirrinsa naki ne?".
Cikin jin kunya da daWi tace.
"To dan Allah Ummi wai me Yah Sheykh yayiwa Gimbiya Saudatu ne? Meyasa bata sonshi? Meyasa su Bappa Nasiru basa sonshi? Meyasa baya shiri da Mom Imaran? Waye Gimbiya Samira amaryar Abba".

Dogon numfashi Ummi ta fesar tare da gyara zamanta ta Wan jingina bayanta da jikin kujera, cikin sanyi tace.
"Tambayoyin ai duka amsarsu Waya ne!".
Da sauri tace.
"To Ummi gaya min sai muje tambaya ta biyu?".

Fuskantar Aysha tayi da kyau kana a hankali tace.
"Kwanakin baya can munyi makami ciyar wannan hirar.
Babu wani abu da Sheykh yayiwa kowa na masarautar JoWa, domin wannan ?iyayyar da suke nuna mishi ta samu asaline tun yana yaro".

Da sauri Aysha tace.
"To tun yana yaro kuma haka kawai kenan suka tsaneshi?".
Kai Ummi ta jujjuya mata tare da cewa.
"A a ?iyayyar da dalilin zaSin tambarine".
Cike da kaWuwa Aysha tace.
"Menene zaSin tambarin?".
Cikin yin ?asa da murya Ummi tace.
"Bisa al'adar masarautun gargajiya na Hausa Fulani, dole har kwanan gobe suna da al'adu ko wacce masarauta da al'adarta, sai dai mafiya yawan masarautun al'adar tambarin Waya ce.
In kinji ance tambari wani kayan kiWane da babu shi a ko ina sai gijen manyan masarautu. A bisa al'adar masarautar JoWa bawai sarkine ke ko mutanen gari kance wane ne zai gaji sarauta ko wanene zaiyi mikinba. Duk ranar bikin salla ana fito da kakaki da al'gaita mabusar masarauta da kuma tambari a ajiye a tsakiyar faWa, gaban sarki. Kana duk ?a?an sarki da jikokinsa da makusantasa maza, zasu hallara a fada, inda kowa zaije gaban sarki ya gaishesa, to muddin akwai nasibin gadar sarauta, a jikin mutun kana isa gaban sarki, kakaki da al'gaita nan zasu fara bisa kansu da kansu.
In kuma kaine zaka gaji mulki daga hannun shi wannan sarkin na wannan lokaci to tambarin masarautar zaiyi ta kaWa kanshi da kashi,. Duk sanda ka isa kusa dashi, in ka wuce zai bari in ka dawo zaici gaba da yi.
Wannan al'adace tun ta zamanin jahiliya, kuma har yanzu wasu masarautun sunayi, to Amman masarautar JoWa tun a kan Sheykh aka bar wannan

69 / 72