Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   33 / 72

96K to 99K   out of 214K words

da yayi abu ya gommace bayiba karo na forko a rayuwarsa da yayi mugunta yaji dana sani kan sace su Gaini. Da yatsarsa manuniya ya nunata, da mamaki tace.
"Nice na saka kuka?". Kanshi ya gyaWa mata, cikin al'ajab tace.
"Me nayi maka?". Motsowa yayi ta bakin bukkar sosai can cikin sassanyan murya yace.
"Kukanki ne yasani kuka Mata,
farinci bazai samu gurbi a rayuwataba, muddin ke kina cikin ?unci, dan Allah ki daina kuka,".
A hankali tasa tafin hannunta ta share hawayenta.
Shi kuwa Ba'ana, wani babban kura tanWu yajo, cikin sanyi ya ajiyeshi gabanta a tsakiyarsu. Cikin sanyi yace.
"Shatu". Da sauri ta Wago kanta ta kalleshi domin yauce karo na forko rana ta forko a tarihin rayuwarta da taji ya kirata da Shatu, cikin mamaki tace.
"Na'am ya Ba'ana".
Girgiza kanshi yayi kana ya fara fito da wasu sabbin aska cikin zabirar da yanzu ya jawota, a hankali ya Wago ya kalleta cikin ya?ini yace.
"Shatu, zan faWa miki abinda, babu wanda ya sani a kaina a duniya, Shatu zan nuna miki abinda duk duniya ban yarda da in nunawa kowaba, sabida ban yarda da kowaba sai ke Waya rak Shatu, nasan zuciyarki ciki da woje, ke mai imanice, bazaki taSa zalumtata ba, bazaki bari a kuma zalum ceniba. Na amince da soyayyarmu, zamu rayu a tare har gaban abadan."
Ido kawai ta iya zuba mishi.
Ganin Junainah ta iso wurin ne, yasashi jawo akoshin gasassun zabbin gabanshi.
Ita kuwa Junainah da sauri ta kuma sa hannu zata jawo akoshin.
Kanshi ya jujjuya mata alamun ta bari.
Cikin kwaSe fuska da Wan karen kwaWayi da yunwar da takeji yana azalzalar ?a?an hanjin cikinta tace.
"Yah Ba'ana ka bani mana yunwa nakeji".
Cikin sanyi yace.
"Bazan bayar ba".
Da sauri tasa hannu ta zari akoshin tayi gaba
Shatu ce ta fara kiranta tana.
"Junnu! Junnu!!! Junnuhhh!".
Ina bata kulata bama bare ta juyo.
Shi kuwa Ba'ana ajiyan zuciya yayi tare da mgnar zuci.
"Uhummm ?uda garin kwaWayi kya mutu, kwaWayinki ne zai karki". Kai ya gyaWa wa Shstu kana ya juyar da kanshi.
Ita kuwa Aysha shiru tayi tabi Junainah da ido.
Shi kuwa Ba'ana cikin sanyi ya wore ?afafuwan sa,
takalmin roba na sau ciki wato, tashi kabi shanun dake ?afarsa ya zare.
Sabbin askan ya Wauka, kana ya fito da wasu ?an kananun layu guda biyu.
cikin ya?ini yace.
"Shatu, kinga waWannan layun?".
Kai ta gyaWa mishi cikin yin kici-kici da fuska.
Jinjina mata kai yayi kana yaci gaba da cewa.
"Wadannan sune, ma?urar, mgnin kariya da zan saka a jikina, zan sasu a gaban idonki, wannan ?aramar ita zan saka a dundunyar ?afar dama, itace kuma layar, ?arfe, mudin wannan laya tana jikina, to wlh babu wani ?arfe dake kan doron duniya da zai shiga jikina".
Cikin mamaki tace.
"Koda bulet ne!?".
Kanshi ya gyaWa mata tare da cewa.
"Koda menene, kuwa su wannan sabbin layune, wanda babu makarinsu, sai dai ina na ciresu a jikina,
ita wannan da zan saka a ?afar hagu, layar zanace.
Duk sihirin mutun bazai karyashiba, zan iya Sacewa inje ko ina, makarinta abu Waya ne!".
A hankali tace.
"To menene makarinta?".
Cikin sau?e wani nannauyan numfashi yace.
"Idan wata rana dubuna zaicika za'iya kamani, to ammanfa tabbas, zan iya Sacewa sai dai in ba'a barni na sha ruwaba, amman muddin akabani ruwa nasha zan iya Sacewa."
Da sauri tace.
"Ya Ba'ana dubunka ya cika kuma, kamar wani mugu ko maiyin mugun abu".
Da sauri ya fizge mgnar da cewa.
"Eh to ai yanzu zan fara fataucin nemo. Suya Yaya GiWi ne, kinga kuwa, sai yadda hali yayi".
Ajiyan zuciya ta sau?e kana tace.
"To ita layar Satan da ta ?arfe menene makarinsu?".
Kanshi ya Wan jingina da bakin bukkar ido ya Wan zuba mata, kana cikin sanyi yace.
"Uhum makarinta sai in an samu maza tagwaye, da matar da bata al'ada sunyi tuwon sabon geron da za'a shuka a tsakiyar garken fulanin kana tuwon za'ayishi da garin dakan hannune, kuma maza tagwayen sune zasu tu?a tuwon kana matar da mijinta ya tara da ita batayi wonkan tsarkiba, ta kwashi tuwon , to su kam in naci, tuwon gaba Waya sihirin jikina zai karye, in kuma ba haka sai dai ina an tsaga dundunyar ?afar tawa an ciresune kafin makami ya iya min illa".
Cikin wani irin sanyi tace.
"In sha Allah zaka nemosu lfy ka dawo dasu lfy, zanyi ta addu'a Allah ya baiyanasu."
Kanshi ya tan?wasar kana a hankali yace.
"Uhum sai daifa Shatu akwai wasu bulalin da aka bani tabbacin zasu worwore duk wani asiri da kafi da nayiwa jikina,
Amman duk da haka bazasu worwore waWannan layunba, sai dai an bani tabbacin, muddinfa aka dakeni da wannan bulalin zan ji azabar dukan, da zai iya Wauke raina".
Cikin mutuwar jiki tace.
"Bazama su dakeka ba, Ya Ba'ana".
Kanshi ya mirgina kana, yasa hannu ya Wauki askarnan, kawai sai ya datsata kan dundunyar ?afar damanshi,
Da ?arfi Shatu tasa salati tare da rufe idonta, gaba Waya jikinta rawa yakeyi murya na rawa tace.
"Innalillahi ya Ba'ana zaka kashe kanka".
Cikin harshen fillanci yace.
"Ai bazanji zafinba Mata, bari yanzu in Winkesu, buWe idonki ki gani."
Cike da tsaro tace.
"Bazan iyaba, ina tsoro".
Jin hakane yasa bai kuma ce ta buWe idonba, har saida ya gama cusa layun kana yasa ?ayar aduwa ya rin?a hudawa yana Winkawa da zaren, gashin bindin shanu, saida ya gama yace ta buWe idonta.

Cikin tsoron ta zubawa wurin ido, ga jini ya Sata ko ina,
Sai kuma ta ?urawa ?afafuwan ido ganin yana shafa musu man shanu sai wani tafasa wurin yakeyi, cikin mintuna uku duk wurin yayi tib-tib kamar ba shiba.
Cikin tsoro tace.
"Ya Ba'ana, ka dena irin wadannan abubuwa, wallahi shirka ne, tsafine babu kyau! Haramunne."
Ganin yadda ya haWe fuska ne yasa tace.
"Kayi ha?uri, shiyasa tun forko ina son ince maka ba kyau bana son kana irin wadannan abubuwan".
Murmushi ya Wanyi kana yace.
"In kin sake min mgnar, bulala Waya zan Wauko cikin bulalin shaWi na, in zaneki da ita sau Waya kiji irin zafin da masu gangancin cewa suna sonki, sukeji a jikinsu."
Cikin tsoro tace.
"Bazan sake bama Ya Ba'ana wadannan, bulalin da kake tsumasu da dafin kunama ai Ni kam na sani bulala Waya zakamin zan mutu".
Da sauri yace.
"Azubillah, Mata kada ki sake cewa zaki mutu, domin duk randa kika mutu nima zan mutu, sai dai batun gsky ko Mata, duk mutumin da kikaga ya iya jure bulalin shaWi na, har ya kai matakin nasara, to wlh ki sani ki shaida, jarumine, irin jaruman da sunyi ?aranci a duniya."
Hannu tasa ta kange fuska daga wani irin kallo mai cike da so da yake mata,
Tabbas Ba'ana ba barbarene, amman yanada wani irin kyau mai ban mmki, a hankali tace.
"Ya Ba'ana wai da waye kake kamane?".
Cikin murmushin da ya bayyana kyawawan ha?oransa yace.
"Ni da kakata Maman babana nake kama, ita kuma ba kanuribace, fulatamare ce ita".
Cikin sanyi tace.

Murmushi ya Wanyi kana yace.

Cikin sanyi tace.
"Haba shiyasa mana kake da kyau sosai".
Wani irin kallo ya mata tare da cewa.
"Eyeh ashe Ni kekyawan ne Mata, ke dama shine baki taSa gaya min ba inji daga bakin wacca nafiso fiye da komai a duniya dan inji daWi, kin bari sai wasu can keta cemin wai ni kekyawan ne".
Da sauri ta mi?e tare da cewa.
"Sai anjima, Mai kyau ka tashi kaje ka tafi masallacin kaga lokacin sallan jumma'a yazo anata tafiya".
Da murmushi ya rakata. Ita kuwa da haka ta tafi gida, sabida tuni wasu masallatan har sun fara huWuban sallan jumma'a.

Tana shiga gida ta samu.
Rafi'a, Junainah, Ummiy da Bappa, gaba dayansu a.


Cikin Babban birnin ?adamaya, a cikin masarautar JoWa, kuwa.
Tuni masallacin LamiWo Nuruddee, ya cika yayi ma?il da bani adam tako ina zuwa, akeyi.

Masallacin ya cika tab tamkar zai fashe, shiru kakeji babu wani amon sautin Wan adam dake tashi, sai sautin muryarsa.
Yana tsayene cas kan ?afafunshi,
Wata dan datsetsiyar, shaddar Super Nour ce a jikinshi wacce take Brown color a ?alla kuWinta zai kai dubu Wari da ashirin, shaddar irin mai mai Winnane,
Yayi kauri cikin kayan ko dan yanayin suturar da ya sakane, boxes ce fara ?al yasa a ciki, sai snglet itama fara ?al, kana sai Rigar half jomfar yaddan dake jikinshi sai wonWota, wanda sunyi cib-cib da madaidaicin jikinsa,
Kana sai watta tattausar doguwar al'kyabbar sa, Golding color, sai wani irin she?i takeyi, sai hirami fari daja irin mai Wigo-Wigo nan, yayi masa sakin manyan Dattawan bai lon?osashi, ya barshi a zube bisa kafaWunshi, sai ta gaban goshinsa da ya Wan matseshi ya bada Wan tsini dai-dai kan karan hancinsa,
Sai ba?in zagayen daya Waura bisa kam hiramin.
Kana sai wasu takalman shi dake can bakin ?ofar shuga masallacin ta ?ofar liman, takalman irin na sarauta ne half cover, wanda suma fari da Wigon jane.
Yayi wani irin kyau mai Waukar hankali haibarsa da kimarsa da dottakunsa sunyiwa fuskarshi ?awanya, sajen nan nashi yayi lib-lib tamkar anayi wa koren ciyawa bayi, sai wani irin sassanyan ?amshin turaren OudKareem Win sa, dake tashi a jikinsa.

Muryarsace ta cika ko ina na yankin.
Shiru mutanen wurin sukayi kowa na jin, wa'azin yana ratsasu.
Yana Hudbane akan, wuraren da ya dace namiji ya gani a jikin matar da yake neman aurenta,
yana kan hankali, bisa wuce gona da iri da mafiya matasan yanzu keyi, a kan wannan dama da Allah ya basu.
Gyara tsayuwarshi yayi, tare da haWe hannayenshi wuri Waya, ya haWe bakin al'kyabbar jikinshin. Cikin tattausan lafazi mai ratsa kunne da zuciyar duk mai sauraro da imani yaci gaba da cewa.
"Aure wata muhimmiyar hanya ce, wanda idan aka ?ullashi zai bawa ma'auta daman saduwa, tsakaninsu, ba tare da wata ?yama ba, kuma ta hakane ma'autan zasu zama sutura ga junansu. Kamar yadda Allah maWaukakin sarki ya faWa, a Suratul Ba?ara aya ta , 187:-
(HUNNA LIBASUN-LAKUM WA, ANTUM LIBASUN-LAKUM). Ma'ana su mata suturane gareku maza, sannan ku maza suturane garesu (Su Matan)."
Gyara zaman al'kyabbar sa yayi tare da kallon tarin dubban al'ummar Annabi dake zaune gabansa, hankalin da nitsuwar kowa na kanshi.
Sai Wan haskem cameras da yake gilmawa ta kanshi da sauran na kusa dashi, shaidar ana naWar sautin muryarsa nayin huWuban. Cikin nitsuwa yaci gaba da cewa.
"Saboda haka, ya zama dole mutun, ya nitsu ya maida hankali ya zaSi abokiyar zama ta gari da zata zame mishi sutura ya zame mata sutura, wajibine kuma kayiwa kanka da jikinta iyaka har sai an biya sadaki, an kuma Waura aure, shaidu sun shaida sannan zaka samu nitsuwa da ita.
Domin shi aure, yana samar da nitsuwa tsakanin ma'auranta. ?an Adam bazai samu cikakkiyar nitsuwa a gidansa ba sai in har yanada mata, wacca ya aura. Domin zata Webe mishi kewa, ta sa shi ya samu nitsuwar hankalinshi. Saboda zamansu tare, a ?ar?ashin inuwar aure zatayi mishi maganin kaWaci. Kamar yadda Allah, (A.A.W) ya faWi a Suratul Rum aya ta 21:-
(WA MIN AYATIHI AN KHALAKA LAKUM MIN ANFUSAKUM AZWAJAN LITASKUNUW ILAIHA WA JA'ALA BAINAKUM, MA WADATAN WA RAHMA INNA FII ZALIKA LA AAYAATIN LIKAUMIN YATAFAKKARUN).
Yana daga cikin ayoyin da Allah mai girma ya halitta mana mataye daga kawunan mu. (Mataye da muke aure da su) domin su sami nitsuwa junanku, sannan kuma ya sa muku soyayya a tsakanin ku tare da Rahma da tausayawa juna. Lallai a cikin wannan al'amari akwai ayoyi abin lura ga jama'a'an da suke masu tunani".
Gaba Waya taron al'ummar babu, hayaniya ko motsi shiru kakeji,
Baba Nasiru kuwa, yana dai zaune ne cikin sahun da masallacin amman ji yake tamkar ya sha?o wuyan Jabeer sai ya kaishi ?iyama, Baba Bashiru ne dake gefenshi, ya Wan kalleshi tare da yin ?asa da murya yace.
"Ya Nasiru ka nitsu mana ka koyi danne abinda ke ranka".
Cikin tarin ba?in ciki yace.
"Haba Bashiru ya zanyi in iya danne abinda ke raina, bayan da kai sani dama duk sauran yan uwanmu, mahaifinmu ko sarautar sarkin ?ofa bai bamuba,
Tunda ya bawa Ya Muhammad, Galadima, yana rasuwa, madadin a maida sarautar Galadima kaina, ko kan Hashim tunda shi ubanshine Galadima, sai ya Wauki wannan sarautar ya bawa, Jafar shi Wan rashin adalci."
Murmushi Baba Bashiru yayi tare da cewa.
"To ai kuma dai gashi ya haukace ko? Ina dai yanzu sarautar tafi ?arfinsa, dole dai ya barta".
Cikin fusata Baba Nasiru yace.
"To Waya barta ya haukace Win ma, ya maidota ga ?an Wakinmu ne, inji, wancan tsohon ya bawa, waishi ya bawa ?aninshi, ai shima Wan tsohon sarkine
Sannan kana ganin yadda ya kuma Waukar sarautar GARKUWA ya bawa Jabeer, sannan babban tashin hankalin kanaga yau tare suka fito Wakin labbare dashi wannan munafikin yaro, waishi Sheykh Wan iska anyi asiri anyi tsafi duk baya kamashi yadda mukeso".
Barrister Kamal ne dake gefensu, yayi Wan wani guntun tsaki cikin tsuke fuskarsa, da jin haushin yan uwan nashi yace.
"Ya Nasiru kufa, ji tsoron Allah, ku tuna, cikin Masallaci kuke, kuma ba kyau liman na huWuba ana. Surutu."
Wani irin mugun kallo Baba Bashiru ya watsa mishi tare da cewa.
"To Wan masu matacciyar zuciya, wa'azin da yakeyi ai tun kan a haifi uwarshi mun sani".
A kufule Barrister Kamal yace.
"?aryane, da kun san abunda ya sani wala Allah da zuciyarku ta tsarkaka".
Shiru yayi tare da fuskantarta Inda limamin take jin yana cewa.
"Halaccin kallon matar da mutun yakeso ya aura.
Ha?i?a munsan matarka abokiyar rayuwarka ce. Kuma gonarka ce da zakayi shuka a cikinta, sannan kuma gareta zaka samu konciyar hankali. Kuma shi manufar yin aure ya hana kallon wata ko wasu matan wanda ba nakaba da dai makamantansu Irin hakan.
IN KUWA HAKANE TO LALLAI AKWAI BU?ATAR SAI MUTUN YA ?ARJE! YA ZA?A. Haka kuwa baya yiwuwa sai ka kalleta sosai da sosai. Saboda mahimmancin haka nema shariyar musulunci ta yardar maka da ka kalli wacce kakeso zaka aura da kyau. Don ka tabbatar da wancan abubuwan da aka ambata a sama.
Kuma wannan dama da Shari'a ta bada ta bada shine, a matsayin halasci na wurin mafi yawan malamai, kuma wannan Halascin da akace halasne ya haWa da cewa. Shin ta yarda ka kalleta, ko bata yardaba, halasne in dai ka kalleta. Kuma wannan hukuncin haka yake a wojen mafiya yawan malamai, sai dai Malikiya, sunce shi hukuncin Halascin ya dogara ne, in ta bashi izinin amma in bata bashi izinin ba to bai halasta ba.
Haka kuma shi wannan hukuncin halascin an samo shine daga, hadisin Abu Huraira (Allah ya ?ara masa yarda) yace, wani mutun ya nemi auren wata mata, ?ar Madina, sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa: "Shin ka kalleta kuwa?". Sai mutumin yace, wa Manzon Allah (S.A.W) "A'a ban kalleta ba". Sai Manzon Allah (S.A.W) yace.
"Tafi ka kalleta, domin mutanen Madina sunada wata illa a idanunsu."
A wata ruwayar kuma da Abu Dauda ya ruwaito.
Daga Jabir Bin Abdullahi cewa: Lallai Manzon Allah (S.A.W) yace.
"Idan Wayanku zai nemi aure to idan ya sami ikon kallonta wato kallon abin da zai burgeshi zuwa ga aurenta, to ya aikata hakan, (ma'ana ya kalleta) Jabir yace sai na nemi wata mata, daga cikin ?abilar Banu Salma na kasance ina bibiyanta har sai da naga abin da zai birgeni a aurenta.

?an zagaitawa yayi kana yayi gyaran murya tare da cigaba da cewa.
"To matasanmu na yanzu suna, fakewa da waWannan hujjojin, suna fakewa da guzuma su harbi karsana, suna fakewa da hadisai suyi haramtaccen kallo, wata sun fake da rama suci Wanyen gari. Hattara gareku iyayen yara maza da mata, GargaWi gareku matasa, bari in tuna sar daku wuraren daya halasta ka kalla a jikin matar da kake son ka aura.
Dangane da inda ya kamata ka kalla, a jikin macen da zaka aura. Malamai sun kasu kan wannan hukuncin, saboda ba su, sami hadisin da ya yi bayani keSantaccen wuri wanda aka keSe ko aka ce nanne kawai za'a kalla ba, wannan shi ne musabbabin da suka karkasu kamar haka:
1 Mafiya yawan malamai sun tafi, cewa in mutun yana neman auren mace, yana iya duban fuskarta da tafukan hannunta.
A Duba Fi?hu wadi Juzu'i na 2. Shafi na 20 sannan kuma a cikin Fi?hu Sunnah Juzu'i na 2 shafi na 24 wasu malamai sun ?ara yin bayani da cewa idan mutum ya dubi fuska mace, zai gane kyawunta, in kuma yadubi Fuskarta zai iya fahimtar cewa, mai ni'imtaccen jiki ne wato mai tattausan fata jiki, ko kuma mata marar ni'iman jiki.
Sheikh imamul Al-Auza'i yana cewa.
"Mai neman aure yana iya kallon wuraren nama dake jikin mace da zai aura.
Duba cikin Fi?hu Sunnah Juzu'i na 2 shafi na 24.
Sheikh imamul Dauda kuwa yana cewa:
Mai neman aure yana iya kallon dukkan jikin matar da zai aura, shima an samu daga Fi?hu Sunnah Juzu'i na 2 shafi na 24.
?an tsagaitawa yayi tare da Wago kekyawan tsintsiyar hannunshi ya kalli agogon Daimond dake Waure samfarin Gucci,
Ganin lokacin salla ya ?ara tone yasashi yin gyaran murya tare da ci gaba da mgna gaggauce, yace.
" A wata ruwayar kuma da aka samo daga Abudurraza? Umar Sa'idu Wan Mansur yace,
(Amirul mu'minin) ya nemi auren ?ar Sayyidina Aliyu (R.A) wanda ake kira da Ummul-Kulsum, sai, Aliyu ya ambata masa ?an?antarta, sai yace.
Zan turo ita idan ka ganta tayi maka matarka kenan, sai ya aiketa wuri shi. Lokacin da taje sai ya yaye suturar da ya rufe ?waurinta.
Sai tace.
(Ba don kai Amirul mu'minin bane da na tsole ko buge idonka, (wato da na mareka) idan muku dubi, wannan in har maganar ya in?anta to ana iya yin hakan.

Anan kenan in har ka kalleta batayi maka ba, to ka kama bakinka kayi shiru. Kada ka faWi wata magana wanda zata iya cutar da ita.
In kana ganin kai bata baka sha'awa ba, to tana iya bawa wani sha'awa ya aureta, domin ko wanne icce da ma tsincinsa, kuma abincin wani guban wani.
Allah yasa mu dace, lokacin salla yayi, bari muyi salla sai in Allah ya kaimu sati mai zuwa sai muyi bayani kan halaccin mace ta kalli mijin da zata aura.

Daga nan yayi addu'an kana, ya juya ya fuskanci gabas, tare da tada i?ama bayan yayi addu'an.

Bayan an idar da sallane, suka fito, a jere.
Ta ?ofarsun dai suka shiga, inda duk ahlin masarautar suke bin nan bayi da hadimai da sauran fadawa kusa, duk ta babbar ?ofar suke bi.

Kusan a jere a jere suke tafi.
Kasan cewar zasuyi tafiyar zuwa Rugar Bani ne yasa Mai martaba LamiWo ke sauri.
Hakama Sheykh Jabeer, wanda Jalal, Jamil, Jafar, Haroon, Imran, Hashim ke tare dashi,
A hankali ya tsaya jin muryar bappanshi

33 / 72