Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   12 / 72

33K to 36K   out of 214K words

kuma mai hasken ras yana sama mai Wan dishi-dishin yana ?asa. Wanda a falsafar al'ummar Duniya ake cewa suma mata da mijine, muddin kaga mai hasken in ka zuba ido zakaga mai dishi-dishin wanda akecewa, mijin shine dishi-dishin kuma shike goyo matarsa shiyasa sai ake ganin mai hasken shine a sama.

Wasu irin numfarfashi take ja da azaban ?arfi da razana, kar-kar haka jikinta ke rawa.
Cikin tsoron halin da take ciki Hinde ta wurgar da goran dake hannunta, tare da cewa.
"Hande en boni, yau munga ta kanmu Shatu me haka meya sameki?". Ina babu mgna sai zamewa da ta farayi tanayin ?asa alamun zata faWi, ganin hakane yasa, Hinde juyowa da ?arfi ta fara rab?awa su Ya Gaini kira.
"Ya Gaini! Ya Seyo! Ya Lado, Wayyo Ya GiWi kuzo kuga abinda Shatu keyi".
Maganarta ta karshece ta sasu, tasowa a guje gaba Wayansu suka nufosu da gudu,
kafin su isoma Aysha ta faWi ?asa zaune, sai karkarwa da rawan sanyi takeyi.
Suna isa Ya Gaini yasa hannu ya tallabota ganin yadda taketa karkarwa, idanunta na rufewa,
Seyo ne ya kalli Hinde cikin kiWima yace.
"Subahanallahi Hinde me ya sameta?".
Cikin kuka Hinde tace.
"Ban saniba wallahi haka kawai naga tana karkarwa".
GiWi ne ya zauna kusa da yayan nashi kanshi ya sunkuyo kanta yana kiran sunanta a jere a jere.
"Aysha! Shatu. Ayshatu tashi buWe idonki ki gaya min meya sameki meke miki ciwo".
Ina babu magana saima kara rumtse idanunta da tayi tare ?ara ?a??ame jikin Ya Gainin nata.
Ya Lado ne da Seyo suka sunkuyo kanta addu'o'in suka rinka tofa mata, duk addu'ar da tazo bakinsu tofa mata sukeyi, GiWi kuwa ruwa yasa a tafin hannunshi yana shafa mata a fuskarta.

Cikin al'hini sauran makiyayan duk suka iso kansu, ganin yadda suke birkice ne Waya daga cikin ?a?an Alhaji Haro da kuma Alhaji Umaru sukace.
"Gaini mu tafi gida da ita, tunda dama lokacin tashinmu yayi, an kusa fara tafiya masallacin juma'a."
Cikin damuwa GiWi yace,
"To ai bazata iya tafiya ba".
Seyo ne ya mi?e cikin sauri yace.
"Bari inje in???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? kawo doki sai mu Waurata a kai".
Da sauri Manu Wan Alhaji Haro yace.
"Yauwa yi maza, kunga ku kuma Gidi kuje duk ku haWo mana kan dabbobi ku fuskantar dasu hanyan gida".
Ai kuwa haka akayi sauran yaran duk suka kaWa shanun.
Koda Seyo ya kawo dokin, shida kanshi ya hau baya sannan aka Waura mishi ita a gabanshi, a haka suka nufi gida.


Koda suka isa gida, da kanta ta taka har zuwa cikin gida, suna biye da ita a baya.
Kai tsaye Wakin Ummey ta shige, bisa gado ta konta ta du?un?une tana rawan sanyi.
Da sauri Ummey da Inna da Junainah suka biyota a baya.
Cikin tsoro Inna tace.
"Subahanallahi Shatu meya faru".
Ummey kuwa gefenta ta zauna, tare da jawo borgo tana rufe mata jikinta.
GiWi ne da yanzu ya shigo, shine ya basu lbrin iya abinda suka sani.
Seyo kuma cewa yayi a mata haya?i.
Haka kuwa akayi sukayi mata haya?in kana Ya Gaini ya zauna yayi mata rubutu nanma aka wonke aka bata.

Jin jikinta yayi zafi jau ne, alamun zazzaSi ne ya rufeta yasa, Ya Lado yaje ya Wauko mata mgnin a Wakin Bappa, nan Ummey ta bata tasha, a take bacci ya Wauketa.

Ummey kuwa da Inna woje suka fito sunata dariya dan su a zatonsu ko gajiyane yasata hakan tunda ita dai bata saba zuwa kiwoba tunda tanada yayu maza da yawa.

Koda akayi sallam Juma'a aka idar, su Bappa da yaranshi kab basu dawoba saida akayi sallan la'asar kafin suka dawo gida.


Ummey kuwa da Inna aikin abincin dare sukeyi wanda girkin ranar jumma'a na dabanne, zabbi biyar suke yankawa kullum jumma'a wata rana kuma tattabaru wani lokacin kuma jan nama Bappa ke saya to yauma hakanne.

Inna ce zaune tanayi musu wonke-wonke yayinda Junainah kuwa keyin shara, dama wonke-wonke aikintane to duk randa takeji tsiya sai tayi ta ?orafi, shiyasa yau tana farawa Inna ta fara aikin.
Ummey kuwa tana cikin kitchin Winsu, wanda dama da Shatu lfyarta lau muddin tana gida ita keyi musu, girki domin Ummey ta horeta da iya girke-girken na ban mamaki.

A hankali Shatu ta bude idanunta daga baccin da takeyi,
Cin karfin jikinta ya Wan dawo, a hankali ta tashi zaune, da sauri ta fito woje, sabida ganin ita Waya ne a Wakin.

Da sauri ta fito, Inna ce ta ganta cikin kula tace.
"Shatu kin taso?".
Kai ta gyaWa mata alamar eh.
Cikin kula tace.
"To ya jikin naki?".
A hankali tace.
"Da sau?i, Inna zanyi wonka".
Mikewa tayi dan dama ta gama wonke-wonken. Botiki ta Wauka kitchin ta shiga, ruwan zafi ta Webo nan take cewa Ummey.
"Shatu ta farka".
Murmushi Ummey tai tare da cewa.
"Na jita ai wai zatayi wonka, ke kuma harda biye mata kamar ta shekara ba lfy, Shatu ba dai rakiba".
Dariya suka Wanyi, ita kuwa a tsakiya gidan ta zauna kan dakalin da ke gindin bishiyar ceWiya dake wurin.

Bayan inna ta kai mata ruwan ne ta kalli Junainah cikin sanyi tace "Junnu zoki rakani inyi wonka Mana."
Ido Inna ta zaro tare da cewa.
"Hahhh Shatu yau kuma ta rakaki wonkafa kikace".
Kanta ta gyaWa cikin raunin fuska tace.
"Eh Inna tsoro nakeji shiyasa".
Ummey dake kitchin ne ta fito rike da aikoshn data zuba zabbin data soya a ciki, tace.
"Shatu ki rage tsorofa".
Kai ta gyaWa kana taja hannun Junainah tare da Waukan kondon kayan wonkanta,
A bakin ?ofar mashiga bayan gidan tace.
"Yauwa ?anwaliya jirani a nan".
To Junainah tace,
haka ta tsaya tana jiranta,
Ita kuwa wonkanta tayi, a nitse kana, tana fitowa.
Tayi al'wala, Wakin Ummey ta shiga, sallan azahar da la'asar Win tayi, sannan ta zira wata tattausar doguwar riga.


Turare ta Wan fesa kana, ta fito,
Gefen katangar kitchin Winsu ta samu Ummey tana haWa wuta a murhun dake wurin.

Inna kuwa zaune take a gefe, da turmi a gabanta, kana tana jajjaga tattasai da tumatur da kuma tarugu da al'basa.

Taburman data fito dashine ta shimfiWa gefensu.
Inna ce ta kalli Junainah da itama yanzu ta fito wonka tace.
"Yauwa Junainah zoki kawowa Addanki abinci."
To tace kana tazo ta shiga Wakin Inna.
Ta fito da tire a hannunta da wasu ?an kananun robobi guda huWu a kai masu marfi, sai kuma kula a tsakiyarsu.
A gaban Shatu ta ajiye kular.

Kana ta wuce ta nufi Wakin Ummey.
Ita kuwa Aysha kular ta buWe, dambun zogalenen a cikin wanda yaji, ganyen zogalen da kuma al'basa, sai tururi yakeyi.
?ananan robobin kuwa, Waya dakekken yajin ?aragone wanda yaji magi da borkino da kuma tafarnuwa.
Kana Waya robar kuma, soyayyan man shanune a ciki.
?aya kuma yankekken al'basane da kuma tumatur, sai dafeffe kwai duk a yayyanka,
Kana Wayan kuma dambun namane mai laushi, a ciki,
Wan karamin aikoshin dake gaban Ummey taja, ta zuba dambun, kana ta zuba sauran kayan hadin.
A hankali ta fara ci.
Junainah da ta fito yanzune ta kalla tare da cewa.
"Junainah bani ruwa".
To tace kana ta juya ta nufi gindin randunarsu inda suke jere a ?alla sun kai shida ko dan ba manya bane dukansu na taSone masu Wan karen sanyi, ga kuma inuwar bishiyoyin ayaba da sukayiwa randunar ?awanya,
Shiyasa ko yaushe ruwan zakajishi kamar na firiji,
A kofin silver ta Webo mata kana tazo ta zauna gefenta, sunaci a tare.

Ummey kuwa tukunyar ?asa ta Waura a wuta tare da tsulala man shanu, a ciki.
Kayan miyan da inna ta kirSa ta amsa ta zuba a cikin manda yayi zafin ta fara soya miyar, zabbin da zatayi musu.
Kana Waya murhun kuma ruwan tuwo ta aza a tukunyan ?arfe.
Inna kuwa data gama kirSa kayan miyar, shinkafar tuwon ta Webo tazo tana wonkewa.

Suna cikin haka su Bappa da yayunta maza suka dawo.
Nan suka shimfiWa katuwar taburma a tsakar gidan.
kana GiWi ya ajiyewa inna ledodin tsarabar jumma'a da Bappa kanyi duk ranar sati.
Tirirruka Ummey ta miko mata ta baza, juye kayayyakin a cikin.
Reke,Lemu, kwakwa, da Giginya, da kuma dafaffiyar gyaWa, da ?osai mai zafi da biredi da soyayyen doya da fulawa mai jawa.
kayan cimarmu kenan fulani

Zubawa maza nasu akayi, aka basu a tsakiyarsu suka ajiye sunaci da mahaifin nasu.
Shatu kuwa da Junainah aka basu nasu. Ummi da Inna kuwa sun ajiye nasu dan aiki sukeyi.
Ya Gaini ne ya Wan danki ?osai da bredy yasa a bakinshi,
tauwana yayi kana idanunshi na kan Aysha saida ya haWiye kana yace.
"Shatu, ya jikin naki?".
Murmushi ta Wanyi sai kuma ta Wan harari Junainah dake cewa.
"Uhum ta worke ai dama kawai hegen tsorone da raki".
Dariya sukayi baki Wayansu. Seyo ne wanda yakeda tarin jin?ai da nitsuwa,
ya Wan afa geWan daya Sare a bakinshi tare da cewa.
"To Amman Shatu meya samekine lokaci Waya kika firgita?".
GiWi ne da shi kuma doya yakeci yace.
"Kamar mai cutar al'janufa ta zama".
Bappa ne ya Wan kalleta cikin kulawa yace.
"Shatu meya sameki ne?".
Murmushi ta Wanyi tare da kallon Ummey dake cewa.
"Uhum tsorone da gajiya fa".
Kai ta jujjuya a hankali tace.
"Allah ko Ummey ba tsoro bane".
Sai ta kuma meda hankalinta kan Bappa cikin sanyinta tace.
"Bappa naga abinda ya firgitanine.
Shin Bappa dama bakan Gizon cikin curi yake fitowa ne?."
Cikin mamaki suka zuba mata ido baki Wayansu.
Bappa ne da kanshi yace.
"Ban fahimceki ba Shatu".
Bredy dake gefenta ta gutsura kana ta dandola da zuman data sa Junainah ta kawo musu, a baki ta Wansa ta tauna kana a nitse ta basu labarin abinda ta gani da kuma yadda taji, ta ?ara da cewa.
"Bappa dama bakan Gizo a curi suke fitowa ne?".
Cikin mamaki da al'hini yace.
"Allahu al'alamu. Sai dai koma menene, lallai tabbas akwai abinda ke tunkarar rayuwarmu, fatana mu dage da addu'a koma menene Allah ya kawo mana shi kan al'khairi ya kuma sau?a?a manashi, zan kuma bincika in sha Allah.
Sannan kada ku gayawa kowa mgnar nan".
Ya karishe mgnar da kallon Junainah.
Wannan labari ya sasu cikin dogon nazari. haka dai sukaci gaba hira kamar yadda suka saba.

A can cikin yola kuwa, yau tunda Ya Jafar yaje sallan juma'a ya dawo baiga ?aninshi Sheykh ba, gaba Waya ya tashi hankalin ?anenneshi da iyayenshi.
Domin kama hannun Jalal yayi yana kuka, yana jan Jalal zuwa sashin Sheykh koda suka shiga, Jamil kuwa sashin mahaifinsu ya nufa. Ba tare da ya saurari
Hadiman ba ya wuce.
A babban falon ya samu , Abba
Haurawa sama yayi yana shiga kuwa ya sameshi a falo shida jarabebboyar amaryar tasa cingom dinshi.
Sai dai tana konce bisa kujera,
Shi kuma yana zaune bisa sallayane ya fuskanci al'?ibla, da ?ur'ani a gabanshi yana karatu cikin suratul Khafi.
cikin rauni Jamil ya ?araso gabansa.
Bai kulashiba har saida ya kai ?arshen surar kana ya shafa addu'a.
Cikin haWe fuska da alamun faWa yace.
"Jamil lfy kuwa mehakan?".
ido na zubda hawaye yace.
"Abba Ya Jafa".
Rai a hade yace.
"To me zan mishi?".
Cikin zubda hawaye yace.
"Abba tunda aka dawo aka sau?o sallan jumma'a fa yaketa kuka yana bin Jalal yana kuka alamun a kaishi wurin Hamma Jabeer, yau ko abinci baiciba, Aunty Juwairiyya ma sai kuka takeyi hakama su, Jiddah."
Tsaki ya Wan ja tare da cewa.
"To ni zaka gayawa? Kaje ka gayawa Mamanku mana".
Wasu sabbin hawayene suka zubowa Jamil a hankali ya juya ya fita".

A can sashin Sheykh ya samesu, Juwairiyya da Jalal Win da Affan sun tasashi a gaba, Affan yanata kuma, shi kuwa Jalal sai tattaune laSSansa yakeyi, da sauri Jamil ya iso cikin sanyi yace.
"Affan je ka gayawa Mama".
Da sauri Affan ya juya har zai fita kuma ya dawo jin Juwairiyya na cewa.
"No Affan kada kaje, ka gaya mata, nasan yanzu tana bacci ne".
Shi kuwa Ya Jafar sai ya shiga Wakin nan ya fito ya shiga wancan ya fito yana kuka kuma.

Shigowar Abbane ya sasu su Jalal duka fita.

A hankali Abba ya kamo hannunshi suma suka fito, da mamaki a fuskar Jamil ya bisu da ido.

Shi kuwa Abba yana ri?e da hannun babban Wan nashi suka wuce har makoncinsa,
Gefen gado ya kontar da dashi, kana a hankali yake shafa kanshi cikin taushi da tausayawa yace.
"Jafar kayi ha?uri kayi baccinka kabar kuka, Sheykh yana lfy lau, ya tafi ?asar Saudia ne shida kakarku Sitti."
Shiru yayi yana kallon mahaifin nashi.
Shi kuwa Abba, kanshi yake shafawa yana kontar mishi hankali a take yayi baccinsa.


Bayan sallan ishane Jamil yaje wurin Kakansun ya sanar mishi halin da ake ciki ya ?afarsa cewa.
"Allah rene, magar gsky kace Hamma Jabeer ya dawo, sabida abin ya Jafar yana tsananta in bayanan".
Murmushi kakan nasu yayi tare da cewa.
"Uhum ai Allah ya sau?a?a abinda zai taso Sheykh ya dawo ba tare da an gama dai-dai-ta abinda ya kaishi ba Dole shi wannan mai saSulellen mondon Jalaluddin shi zai dena yawon iskanci ya zauna ya kula dashi tunda yafi kallonshi a madadin Sheykh".
Cikin takaici Jamil yace.
"To ni zan kai Ya Jafar saudia wurin Sheykh Win suci gaba da zama a can in sun so, tunda dai kun san Sheykh shine GARKUWAnmu".
Cikin kontar da murya kakan nashi ya Wan tausasashi kana yace in yaje ya turo mishi Jalal.



A can Saudia kuma, sosai aketa shirya yadda Waurin Auren Sheykh da Jazrah zai kasance, duk da basu sanar mishiba, sabida kashedin da Sarki Jalaluddin da Nuruddeen sukayi musu dan ko yaushe in dai ana shirya batun aurenshi muddin yaji sai ya?i fir yayi ta kaucewa dole a ?arshe aure ya fasu, to wannan abunne yasa ba'a sanar mishiba.
Sai dai yasan batun zuwan da Jazrah take sashinsu wai nune da ita suke zaSa mishi in tayi mishi.
To shi kuwa bayan gaisuwa ko sannu bai taSa haWasu da itaba.

Haroon kuwa da Jannart sunata shirye-shiryen dawowa gida Nigeria.


A garin Bani kuwa,

Yau tun bayan sallan isha'i yaro ya shigo yace, Ya Salmanu yana sallama da Aysha,
haka kuwa ta fita taje,
Suka zauna a dakalin ?ofar gidan nasu suna hango yadda,
Yara keta wasa a dandali domin ranar jumma'a tafi ko wacce rana a garesu wurin shanawa.

Ya Gaini ne ya fito ri?e da hannun Junainah, a bakin ?ofar suka wuce Su Shatu
Bayan sun gaisane ya wuce ri?e da hannun ?anwar tasa,
Murmushi Salmanu yayi tare da cewa.
"Shatu, inaga dai aurenmu dana babban yaya rana Waya za'ayi shi".
Murmushi itama tayi, tare da cewa.
"Tab shifa har an kai kayan aure".
Ido ya Wan lumshe tare da cewa.
"To ai in kin bani dama nima gobe-goben nan sai a kawo kayan aurenmu ko?".
Da sauri tasa tafin hannunta ta rufe fuskarta, alamun jin kunya.

Su Ya Gaini kuwa kai tsaye ?ofar gidan Ahaji Haro sukaje,
A bakin ?ofar suka tsaya, sunkuyowa ya Wanyi a hankali yace.
"Yauwa ?anwaliya maza shiga cikin gidan kicewa Addanki Bintu tazo".
Cikin happy tace. To kana ta shiga cikin gidan da sallama.

Kamar yadda gidansu yake hakama gidan Ahaji Haro duk suna zaune a tsakiyar gida da yaranshi da matanshi sunata hira, bayan ta gaidasune taje gefen Binto cikin raWa ta gaya mata sa?on ?a?ansu.

Wani Wan kekyawan matashi Wan kimanin shekaru sha takwas mai sunan Junaidu ne ya kalli Junainah cikin tsananin so da ?aunar yarinyar yayi murmushi tare da taSa mamanshi cikin raWa yace.
"Inno ga surkarki in Allah ya yarda".
dariya suka Wan yi dan kowa yasan Junaidu yasan son da yakewa Junainah tun tana ?aramar ta.

Ita kuwa Junainah hannun Binto ta ri?o suka fito tare,
Junaidu na biye dasu a baya,
Koda suka fita, Gaini ne ya kalle Junaidu tare da cewa.
"Yauwa Junaidu raka min Junainah gida ko".
To yace kana yabi bayanta suna tafe suna hira, sunzo dai-dai ?ofar gidansu Ahaji Umaru ne suka samu Ya Seyo da Hinde suna hirarsu.

Koda suka wuce, murmushi Junaidu yayi tare da cewa.
"Junainah sai yaushe zan fara zuwa muma muyi hira ne?".
Cikin yin ?asa da murya tace.
"Sai na ?ara girma kafin nan Addana tayi aure".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Ko dai bakya so nane".
Da sauri cikin yarinta tace.
"A a ina sonka mana".
Dariyar jin daWi sukayi baki Wayansu, sun zo kusa da ?ofar gidansu.
Ya Ba'ana ne sukayi kiciSis dashi, murmushi yayi tare da cewa.
"Yauwa ?anwaliya kuzo mu shiga in baki aike ki kaiwa Shatu".
To sukace kana sukabi bayanshi, a tsakar gida suka samu, Iya Bultu majaifiyar Ya Ba'ana kena ?atuwar mace ba?a ?arin da ita, ga jajayen idanu, fuskarnan a haWe ta kalli Junainah dake gaidata da fullanci cikin tsananin tsawa tace.
"Ke tafi daga nan ?an iskan fulani masu jajayen kunnuwa, dan uwarki Ni ba fillatace da zaki gaidani da fullanci, hegu kwarkwasa fidda mai gida a gidanshi yan iska masu kama da al'janu, in sha Allah ?arshen zamanku a wannan yanki yana nan tafe".
Da sauri Junainah ta koma bayan Junaidu, shi kuwa Junaidu wani irin tafasa zuciyarshi keyi akanme zata zagesu dan kawai sun gaidata da fullanci.
Bukar ne mijinta wanda yake babarbaree ya kalleta tare da cewa.
"Kuma dai al'barkacin fulanin kikeci".
Ba'ana ne ya Wan harari mahaifin nashi tare da waskewa yace.
"Fulani kecin al'barkacin ta dai, tunda kowa ya sani wannan yankidai na ?achamawa ne, ba fulaninba".
Cikin ?arfin hali Junaidu yace.
"Ato ai dai ba kyau aka bamuba da kuWin mu aka bamu, kai kamma ya Ba'ana kaifa bawanmu ne tunda kai babarbarene".
Wani irin suka kalawan yaron suka mishi a ?ahon zuciyarshi amman sai ya dake,
ledan su ayaba da inabin ya bawa Junainah tare da cewa.
"Uhu Junaidu kenan aini ba bakanuri bane ni ba Bachamene, Dan da in zama bawan fulani gwara in zama bawan karnuka".
Haka nan kalamansu ke tafasa zuciyar Junainah da Junaidu, haka yasa fuska a hade suka juya suka tafi, har sunje bakin ?ofar fita Ba'ana yace musu.
"Yauwa kuce mata ina zuwa yanzu bari inyi wonka".
To sukace kawai suka fita suka tafi.


A ?ofar gidansu suka tsaya gaban Ya Salmanu da Aysha, ledan Junainah ta ajiye a tsakiyarsu cikin jin haushi tace.
"Addana gashi inji ya Ba'ana wai in kawo miki, yace kuma yanzu zaizo wai wonka kawai zaiyi".
Tana kaiwa nan tayi cikin gida shi ma Junaidu Binta yayi a baya, har gabansu Ummey ya tsuguna suka gaisa kana yace.
"To Ummey ga ?anwaliya na rakota Ya Ganin ne yace in rokata har cikin gida".
Murmushi Ummey tayi tare da cewa.
"Mun kuwa gode, ka gaida min Innonka kace mata, in Allah ya kaimu gobe ta turo min Hari tazo tamin kitso".
Kanshi ya gyaWa tare da cewa.
"To saida Safe Bappa".
Allah ya bamu al'khairi sukace baki Wayansu.

Daga nan ya fito, har ya wuce Ya Salmanu yace.
"A a Junaidu zoka amshi tsarabar mana".
Cikin girmamawa yace.
"A a Ya Salmanu ya isheni".
Cikin kula Salmanu yace.
"Ni kam yaushenene zaku koma school?".
Da sauri yace.
"Saura kwana biyar hutunmu zai ?are".

"To Allah ya taimaka yanzu aji nawa kane".

Murmushi ya Wanyi tare da cewa.
"Ina SS 3 ne fa, Ya Salmanu na kusa gamawa ai".

"Masha Allah, Allah ya taimaka".

Amin Amin yace kana ya juya ya tafi.


Ita kuwa Shatu cikin tsoro ta kalli Ya Salmanu a hankali tace.
"Ya Salmanu tashi ka tafi kada yazo ya sameka".
Cikin harshen fillanci yace.
"To shi mala'ikan Waukan raine? Ko dai so kike in

12 / 72