Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   27 / 72

78K to 81K   out of 214K words

saima sanyi da ta Wanji daya bata tabbacin, suna lfy, sabida iya tsawon zamanta da Ba'ana bai taSa yi mata ?aryaba, koda zaiyiwa duk mutanen duniya ?arya to ita baya mata ?arya, kuma duk zafin gskyar mugun abunda yakeyi zai gaya mata. Abu biyu ya Soye mata a rayuwarshi sata da kisan da yakeyi, sai dai yana gaya mata in dai a kantane zai iya kashe kowa ma.
So cikin sanyi tace.
"To yasu Ya Gaini kuma".
Murmushin mugunta yayi tare da cewa.
"Shima na wuceshi wurin Binto sunata hirarsu har tanata raira masa wa?o?in soyayya".
Murmushi ta Wanyi tare da cewa.
"To ka gaida min su bari in Wanyi wonka".
Murmushi yayi tare da cewa.
"To Mata kiyi wonkanki anjima zan kiraki muyi hira".
To tace mishi kana ta katse kira, tare da cewa Rafi'a.
"Alhamdulillah duk lfyarsu lau ashe".
Itama Rafi'a murmushi tayi kana sukaci gaba da hirarsu sai dai still fa tsoro da fargaba da bugawar da zuciyar Aysha keyi bai bariba, ganin hakane yasa Rafi'a, kallonta kasancewar Rafi'a ?wararriyar mai koyar da girgirkene, a zahiri cikin makarantar tasu, da kuma social media. Cikin kula da son samawa aminiyar tata nitsuwa tace.
"Yauwa GARKUWA, zomu shiga kitchin, muyi Wan alalan kwai, naga kin kawo mana koyaye da yawa."
Murmushi Aysha tayi wace, akefi kiranta da ?arshen sunanta.
hannun ta mi?a Rafi'a, cikin sanyi tace.
"Help me my friend, jikina yayi sanyi da yawa, ji nake kamar bazan iya tashiba".
haka nan itama Rafi'a jikinta ya fara sanyi, sai dai sanin in ta baiyana kasalarta tashin hankali Aysha zaifi tsananta ne yasa ta dake, cikin sauri ta kamo hannunta ta jata-ta mi?a kana suka shiga kitchin Win.
Nan suka fara aikin sunayi tana Wan janta da hira.
a haka dai har suka gama, kana, ta shiga wonka.

Shi kuwa Ba'ana maida woyarshi yayi cikin al'jihunsa, kana ya kalli Sarkin maya?an ?abilar Sachama da yake ce mishi.
"Shege Ba'ana wato, yana bacci cikin kabarinsa babu ruwansa da damuwar duniya".
Dariyar mugunta sukayi dukansu,
wanda yake gefenshi ne ya kece da wata dariyar tare da cewa.
"Wai ita kuma Binto kukan natane wa?en SOYAYYA ko?".
Kanshi ya gyaWa musu cikin muguwar fuskarshi.
Wannan matashin Waya fara sokawa Ya Lado wu?ane lokacin da suka kasheshi. yace.
"Ita kuma da yake sokuwace har ta yarda k...".

Wani irin tashi sukayi gaba Wayansu sabida wani irin sha?a da naushi da Ba'ana ya kai mishi, wanda a take ya fara kakarin mutuwa.
cikin zafin rai ya hankaWa tarin mutanen dake son cotan yaron daya sha?e Win amman ina sun kasa, wata zabgegiyar wu?a ya lumtsumamishi a ciki wanda yasa sauran duk suka watse tura gawarshi yayi gaban su cikin Waga murya yace.
"Ina kashe wanda ya yabi Shatuma yace yana son Shatuma bare wanda ya zageta, duk wanda baya son ransa ya aibata min Shatu a gabana ya gani".
Cit kake jinsu sabida masifar tsoronshi sukeji.
Dan ya fisu ta?adiranci dan Ba'ana mugun babarbarene mai ba?ar zuciya.

Haka dai aka tashi wannan taron da yake dama sun gama tattauna yadda zasuyi farmakin.


Washe gari ranar wata Tuesday 21 November 2017 itace ranar da har abada al'ummar Rugar Bani bazasu mance da itaba a tarihin rayuwarsu, itace ranar da duk motsin da numfarfashi Shatu zatayi sai ta tunashi ranace data girgiza, zukatan al'ummar musulmai, ranace da tasa duk wani bafulatani makiyayi jin ?una da tafasar zuciya.
Ranace da tada hankalin al'ummar ?asarmu nan dama ma?otanmu.

Tunda safiyar ranar, dattawan garin suka gama shirinsu cikin shigarsu ta al'farma, Malam Liman (Bappa) ArWo bani Jauronsu, Ahaji Horo da Ahaji Umaru, kana Malam Yero, da kuma Alhaji Sa'idu.
su rai takwas dai suka shirya cikin kamala da mutunci. Junaidu ne yake cikin Shikan ya samo musu mota kirar siyana wacce suka Wauki shatarta, domin zai kaisu har cikin fadar masarautar JoWa kuma zai jirasu. Su dawo tare.


Nan suka shiga Mota gaba Wayansu, suka tafi.

Kai tsaye har bakin masarautar suka tsaya dan an hanasu shiga,
sai da Waya daga cikin hadiman dake tsaron ?ofar, yaga duk manyan daddatawa ne yasa yaje ya samesu bayan sun gaisane sukayi mishi bayanin abinda ke tafe dasu.
Jin abin babbane yasa yaje yayiwa sarkin ?ofa bayanin.
Nan shima yaje suka gaisa suka ?ara jaddada mishi, zancen abinda ke tafe dasu, sannan
sukayi musu izini suka shigo cikin asalin farfajiyar mashigar masarautar.
Kan kujerun dake jere a wurin suka nuna musu su zauna.
Bayan sun zaunane sarkin kofa yaje, wurin sarkin fada ya sanar mishi, to nan sarkin fada ke cewa.
"To ai babu abinda zamu iya musu, tunda shi GARKUWAN FULANI, baya ?asar waye zai saurari kukansu, suje sai ya dawo su sake zuwa".
Cikin rauni sarkin ?ofa yace.
"Ranka ya daWe sarkin fada, da dai an nema musu izinin ganin mai martaba, domin bazaiji daWi ba in yaji sunzo kuma an medasu".
Cikin isa da izaya sarkin fada yace.
"A kul sarkin ?ofa ka tsaya iya matsayinka, kaje kace suyi maza su bar nan domin GARKUWANSU baya nan".
Cikin sanyi da mutuwar jiki sarkin ?ofa ya juya ya fita, koda yaje ya sanar musu, abinda sarkin fada ya faWa hankalinsu yayi masifar tashi.
Cikin tashin hankali ArWo Yabani yace.
"Shikenan danmu fulanine makiyaya mazauna daji, sai ya zama matsalarmu ba abar dubawa bace, wa al'ummar birane, duk inda muka kai kukanmu sai a koramu".
Cikin sanyi sarkin ?ofa yace.
"Kuyi ha?uri ba korarku akayiba, in sha Allah za'abi kadunku, wlh shi kanshi mai martaba in zaiji abinda sarkin fada yayi to zai barranta dashi, kuma haka nan shima GARKUWAN FULANI in da zaiji abinda sarkin fada yayi wallahi zai haWu da fushinsa mai tsauri, domin shi zuciyar Sheykh zuciyace mai cike da imani da tausayi".
Cikin rauni Alhaji Haron yace.
"Ana binmu ana kashemu, ana sace yaranmu ana kora dabbobinmu.
Munje Police station an koramu, da muka?i tafiya suka watsa mata tiyagas, muje masarautar Numan akaci mana zarafi, sannan yanzu mun gudo gareku da ya?inin zakubi kadunmu sannan kuma zaku koramu, so kuke mu Wauki makami domin ramuwa ne?".
Da sauri suka juyo gaba Wayansu jin muryar Jamil da yanzu ya iso wurin da hadimanshi, cikin sanyi yace.
"A a Baba kada ku Wauki makami domin ramuwa zuwanku nan shine babban abinda ya dace".
Cikin jin daWi suke kallonsa, murmushi sarkin ?ofa da sauran hadiman sukayi dan sun san yanzu dai sarkin fada bai isa ya hanasu ganin Maimartaba. Domin yanzu bai fito fada bama tukun so zasu ganshi a kebantaccen wuri na musamman.
Cikin kulawa da sakin fuska Jamil yace.
"Baba ku biyoni".
Cikin jin daWi sukace mishi to, kana suka bishi a baya.
Ta gaban shashin Sarkin fada suka shiga, kai tsaye har cikin fada ya shiga dasu,
shida kanshi yasa hadimai suka kawo musu ruwa.
Sannan a nitse yace.
"Baba ku zauna a nan zanje in sanarwa mai martaba, duk sanda ya fito daku zai fara, tattaunawa
In da masu bu?atan zagawa gacan wancan kusurwar in kumbi cikinta zata sadaku da bayi".
Cikin jin daWi sukace.
"Mun gode yaro Allah yayi maka al'barka".
Amin Amin yace kana ya sallamesu ya fita.
su kuma sukaci gaba da zaman jiran fitowan sarki.


A can kasa mai tsarki kuma,
Sheykh ne zaune a gaban Sitti, kana Haroon da Jannart na gefenshi Sheykh Aliyu Abdulkareem, kuma da Sheykh Jabeer Aliyu da wasu manyan malamai na zuriyar tasu duk suna zaune a cikin falon.
Jazrah kuma na gabanshi da wani tray mai masifar kyau da tsada.
Madara da zuma take zuba mishi a cikin wasu ?an kananun kofuna masu masifar kyau da Waukan hankali.

Wannan ya kasance al'adarsuce ta baiyana nuna yarda da soyayya ko akasinshi, indan ana son a haWa yara aure, to za'a tattauna tsakanin manya, bayan sun gama dai-dai-ta magana tsakaninsu kamar yadda yanzu su Mai alfarma Jalaluddin da Sarki Nuruddeen, da kuma su Sheykh Jabeer Aliyu da babban babansu Sheykh Aliyu Abdulkareem da kuma Sitti suka gama haWa zancen auren Jazrah da Sheykh Jabeer, to yanzu ta zuba mishi madara da zuma a gaban kowa, ta ajiye mishi, idan ya Wauki kofin madara to yana nufin yana sonta ya kuma amince da ita da aurenta.
In kuma ya Wauki kofin zuma, to yana nufin ya tsaneta baya kuma sonta bazai kuma auretaba bare ya zauna da ita.
Za'ayi komai a gaban manya ne, don suga zahiri kuma a tsarin ko Wan uwanka zai iya yi maka zaSin da kuma in dai am zaSa maka sai ka aura.

Shiru sukayi baki Wayansu falon, kowa da tunanin da yakeyi.

Sheykh Jabeer dake zaune a tsakiyarsu cikin shiga ta al'farma sai she?i al'kyabbar sa keyi, ga tattausan hirami a kanshi, ido ya lumshe daya gane manufarsu.
"Domin shi basu gaya mishi cewa, zasuyi wannan abun bane daya sani wallahi da yasan duk yadda zaiyi ya gudu, ya tafi harami, har sai sun gaji sun watse.
A hankali ya kalli Sitti dake kallonshi cikin rauni da alamun.
"Dan Allah kada kace, a a yar Wan uwanane, kada ka bamu kunya nida kakanninka maza yar uwarkace kasan tarbiyarta".
Kauda idonshi yayi daga kallon Sitti, wani irin kallo yayiwa Haroon daketa yi mishi, murmushin muguntan yau dai an titseka baka da hanyar tsira.
Cikin ranshi yake mgnar zuciya.
"Ta yaya zan amince ince zan aureta? Dame zan zauna da ita?".
Sai kuma ya Wan fidda nannauyan numfashi.
"To idan ban amince da aurentaba me zamcewa, waWanannan bayin Allah'n da sukayi min dukkan gatan duniya, na zauna a gidansu tsawon shekaru masu yawa nayi karatuna har na gama, sukemin komai na rayuwa, suna nuna min soyayyar da mahaifinama baya nuna min, da wanne idon zan kallesu inna Wauki zuma alamar na tsani yarsu?".
A hankali ya buWe idonsa, jin muryar. Sheykh Aliyu Abdulkareem kakan Mamanshi kenan, baban kakarshi Sitti dottijon daya yake sonshi tamkar ranshi yana cewa.
"Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero JoWa, kayi zaSin da ranka keso, bamu da nufin yi maka dole, sai dai ina da burin aurar maka jikata Jazrah Wiyar mai sunanka. Ina so da fatan ganin nasabarka ta cika, cikar nasabarka kuwa, shene aure."
Wani irin sassanyan numfashi ya sha?a a hankali, wasu irin zafafan tunanuka ne ke zirya a zuciyarshi".
Cikin harshen hausar katsinawa, Haroon yayi mgna can ?asa yadda ko Sitti bazata jisuba.
"Sheykh kafa, shanyamu, nifa zan Waukar maka Madara".
Ido ya lumshe tare da Wan jingina da jikin kujerar da yake zaune, wanda yake kusa da Sheykh Abdulkareem.
Sitti ce ta Wan kalli Haroon tare da mishi alamun ya taSo Sheykh.
cikin harshen larabci Haroon ya kalli kakar tasu, tare da cewa.
"Sitti ai nasan zaSinsa, bari ki gani in nuna miki".
Ya ?arishe mgnar yana kai hannunshi kan kofunan.
da sauri Sheykh Jabeer ya buWe kekkyawar ?wayar idanunshi da wasu ke kiransu da zaiba, wato kamar idon mage, idon ya Wan zaro ganin Haroon yasa hannunshi kan kofin M...!




=??=??=??=??=??

Masu cewa na kulle musu kai kada ku damu zan kuce kawunanne, lokaci ne=??=?O???
By
*GARKUWAR FULANI*
=???
=??=?J?????=?
?>?4?
*GARKUWA*

PAGE 12

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

=??????>?4?


Littafin GARKUWA na kuWine turo katin mtn na Wari uku ta wannan number 09097853276. KO kiyi min TRANSFER Win 1k ta asusuna na Jaiz domin samun shiga Special Group, wanda cikin kwanaki ?alilan za'a gama littafin da izinin ubangiji. Ga asusun kamar haka 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, 1k ne SPG sai ki turo min shaidar biyan
ki ta wannan number 09097853276.


Gareku iyayen ?an mata da za'a aurar, akwai sittin amare mai kyau na gyaran jiki, bisa farashi mai sau?in, akwai na manyan robobi akwai na ?ananan robobi, akwai haWin masu jego, da na maida tsohuwa yarinya, sayan na gari meda kuWi gida, in kayan gyaran kikeso ki fara min text message ta inbox ta wannan number 09097853276 sai ki gaya min kaya kikeso, kana sai ki kirani to nan zan Waga kirankin sai muyi mgn zaki turo kuWi ta ACCOUNT number ni kuma zan tura miki kaya ta mota, duk garin da kike a Nigeria ina aikawa, in dai ba lungu yayi sosaiba. Kana mutanenmu mazauna ?asashen ?etare kamarsu Saudia, India, Gabon, Ghana, Niger, Cameroon, da dai sauransu in kinada dalili kayana na zuwa can cikin salama. Ina saida kaWan-kaWan ina kuma bada sari.



A dai-dai kan kofin madarar ya sa hannunsa, alamum zai mishi zaSi kenan, murmushi yayi dan ya samu damar, da zai tserewa tsarinsu. Cikin ihima da sanin makaman kariyar kai daga jin kunya ko yin abinda zai Sata ran wani, ?afarshi ta dama dake kusa da hannun Haroon yasa cikin hikima ya bugi hannun Haroon da ke gab da Waukar kofin.
ture hannun yayi da babbar yatsarsa, wanda, hakan yasa hannun Haroon ya bugi kofunan da Wan karfi, sai gashi duk sun tuntsure a tsakiyar tiren madarar da zumar kab suka malale cikin tray Win.
A tare suka zubawa tray idanu gaba Wayansu.
Sitti kuwa wani irin kallo tabi Madarar dashi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, cikin iya taku da kamalarsa murya a mutunce ya kalli Haroon daya kafeshi da idon tuhuma, cikin harshen larabci da kamala yace.
"Harooon meyasa baka da nitsuwa?".
Cikin tarin mamaki Haroon ya gwalo ido tare da cewa.
"Haaahh".
sai kuma ya kalli Sitti da ta kwaSe fuska tamkar zata kurma ihun takaici.
Shi kuwa Sheykh Jazrah ya zubawa ido, ganin yadda ta zuba mishi kekkyawan idanunta, wanda suke she?in hawayen dake nuni da zazzafan son da takeyi mishi.
Kauda kwayar idanunshi yayi, da sauri.
Jannart kuwa hannun Sitti ta kamo ganin zata jawo tray.
A hankali Sheykh Khalillullah wanda yake ?anin Sitti ya gyara zama cikin sakin fuska da murmushi ya kalli jikan nasu, nitse yace.
"Laaba'as". Dib-dib haka ?irjin Sheykh Jabeer Habeebullah ya fara bada sauti, fahimtar kakanun nashi zasu Waura zabin kan, fahimtar lafazin Haroon.
Shi kuwa Haroon, wani irin murmushi jin daWi yayi.
Shi kuwa dottijon nan, ido ya zubawa ?a?anshi da jikokin ?a?an nashi, da wasu jikokinshi. Kallonsu yake yana nazartansu.

A hankali wayar Sheykh Jabeer ta fara bada wani sauti mai masifar sanyi da daWin sauraro, sautin gwauraye yake da kukan sassanyan tsuntsaye.
da sauri ya zaro wayar a al'jihun tattausan al'kyabbar tasa.
Ganin sunan Maimartaba Nuruddeen ne, ya sashi sakin wata sassanyan ajiyan, cikin ladab ya kalli Sitti, kana a hankali ya kalli Sheykh Abdulkareem, cikin sanyi da nitsuwa yace.
"Mai martaba Nuruddee ke kirana, bisa alamu da babbar mgna domin baya kirana haka banza".
Murmushi dottijon yayi, domin ya fahimci hanyar fecewa, Sheykh yake nema, hakan yasa ya mishi izinin tafiya.
Cikin sauri Sitti ta yun?uro da niyar yin mgna, sai kuma tayi shiru, sabida nuni da tayi shirun da mahaifinta yayi mata.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, a hankali ya yun?ara, ya mi?e ya nufi hanyar fita bayan yayi musu, su huta gajiya.

Kai tsaye Side Winsu ya wuce.
Yana shiga kai tsaye bedroom ya wuce, gyara al'kyabbar jikinshi yayi kana, ya zauna bisa wata tattausar doguwar kujera.


A nan ?asar kuma, cikin faWar masarautar maiartaba Sarki Nuruddeen.

Bayan Jamil ya fita, wurin da yayiwa su Bappa Masauki,
kai tsaye, sashin kakanin nashi ya nufa.
Bayan an mishi isone, ya shiga, ya gaisa da kakan nashi kana ya ?ara da cewa.
"Mai martaba, akwai ba?i ma bu?atar kulawarka, suna tsumayinka".
Murmushi mai cike da kamala farin dottijon bafulatanin yayi, cikin ratsin sarauta yace.
"Yau ka zama, sarkin fada kenan, kaine mai yiwa ba?i iso ko?, ko dai matane ba?in dan nasan ta nan kafi ?arfi". Ya ?arishe mgnar da yanayin tuhuma.

Kanshi ya Wan shafa, kana a hankali ya girgiza kansa tare da cewa.
"A,a mazane dattawan Fulanin dajine,".
Ido ya Wan zuba mishi kana yace.
"Kaje kace a kula dasu, gani nan zuwa yanzu".
Kanshi ya Wan rusunar tare da cewa.
"Nasa an basu dukkan kulawar da zasu, bu?ata, zuwa yanzu sunfi bu?atar ganinka fiye da komai".
Kai ya Wan jinjina alamar to.
Yun?urawa yayi tare da cewa.
"A fito lfy".

"Allah yasa".

"Amin Amin". Yace kana ya fita.

Shi kuwa Sarkin ya fara shirin, fitowa fada.


A can sashin Sheykh Jalal ne, zaune da Ya Jafar, Aunty Juwairiyya na gefenshi.
karatu yakeyi kamar koda yaushe, tun jiya ya?i barin sashin Sheykh, koda aka kira Sheykh Jabeer video call, ya ganshi sai yayi ta kuka.
Wannan abun shiya ?ara tada hankali Sheykh Jabeer.

Yana yawan, bin Jalal, wanda mutane ke zaton ko dan tsananin kamannin da Jalaluddin keyi da Sheykh Jabeer Winne yasa, yake ganin kamar shine, to sai dai sam Jalal baya iya mu'amalantar Babban yayan nasu, kamar yadda Sheykh keyi har yake sama mishi nitsuwa, sai dai shima yana iya yinshi.


Shigowan Hajia Mama da hadimanta ne, yasa Juwairiyya, jin rauni, a take hawaye ya cika mata idanu. A duniya bata da babbar matsala sama da larurar mijinta.
Ita kuwa Mama, gefenshi ta zauna, cikin sanyi ta kalli, Jalal da fuskarshi ke murtu?e kamar ko yaushe,
cikin baiyanar damuwa tace.
"Ya za'ayi ya samu gamsuwa da kulawarka, a yadda kake haWe fuskarnan tamkar wanda aka sanarwar labarin mutuwar uwarshi, ba haka Sheykh ke mushiba, yana kula dashi, da tausayawa da sakin fuska tunda yasan larurar haukace dashi, amman kai ko yaushe kana nan kamar boss".
Sai ta kuma kalli Jakadiyarsu Kana, ta kalli Jamil dake waya da alamun da budurwarshi yake mgna, hararanshi tayi tare da cewa.
"A haka kuke samawa kanku tabon nunawa a rayuwarku, shi wannan ya zama, mahaukaci, shi Jalal ya zama tantiri Wan shaye-shaye, kai baka da aiki sai bin matan banza. Kuna samin ciwo a raina, shima kanshi Sheykh duniya ta zata fara zargin cewa mazinacine shiyasa ya?i yin aure ya zauna, sin?itin fakitin. Shi kuwa Affan in banda shashanci da tarin ?uruciya babu abinda yasa a gaba.
Ya kukeso inyi, ya kuke son mahaifinku yayi? Yana da yaya maza har ku shida, amman ku biyar manyan duk kun zama, ababe masu taSo a idon duniya, ya za'ayi yayi mararin gadar mulki a hannun mahaifinshi, tunda yasan shi bashi da masu gadarsa, a kusa,ku duba, Imran da yake uwarsa ta tambaWaku, ta nesan taku da mahaifinku, sai ta kusanta Wanta da mahaifin naku.

27 / 72