Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   35 / 72

102K to 105K   out of 214K words

By
*GARKUWAR FULANI*
=???
=??=?J?????=?
?>?4?
*GARKUWA*

PAGE 16

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

=??????>?4?


*FREE PAGE SUN ?ARE DAGA WANNAN PAGE 16 DIN IN DAI KIKAGA LITTAFINA GARKUWA BA TARE DA KIM BIYA NA SAKI A GROUP BA TO NA SATANE, DAN ALLAH DA MANZONSA KADA KU FITARMIN DA LITTAFI DAN ALLAH KU BARI IN SAMU KU?I zuwa makka=??=??=??*


*Littafin GARKUWA na kuWine dan Allah da Manzonsa kada ki karanta na sata, kada ki watsamin littafi a sata, turo katin MTN na Wari uku kacal ta wannan number 09097853276 ki biya ki karanta cikin aminci ba tare da ha??i naba. Ko kuma ki biya 1k domin shiga Special Group wanda cikin sati biyu rak za'a gama Part 1, da izinin ubangiji kana a shiga 2, turo dubunki Waya ta wannan asusun 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidan biyanki ta wannan number 09097853276 in baki da halin biyan dubu Waya ko baki da ra'ayi kina iya turo Warinki uku kacal da ban tsauwalaba sabida halin rayuwa da muke ciki. Dan Allah da Manzonsa da darajar iyayenki kada ki sai littafina in dai kin san niyarki ki saya ki fitar da shine in kuma. Har kin sayane to dan Allah da Manzonsa gaya min in baki kuWinki in cireki a group na, dan Allah=?O?

"Na Amince!". Cikin tarin mamaki Jalal, Jamil, Imran, Haroon, Hashim, da duk sauran tawagar LamiWo suka, zazzaro ido cikin tarin mamaki da al'ajabi, sam basuyi zaton jin haka daga gareshi ba,
Ya Salmanu kuwa wani irin farin cikin mara misaltuwa ne, ya rufewa, domin yana ganin ikon Allah da yake nuna mishi zahirin abinda yake nuna mishi a mafarkansa tsawon kwanakin da yake a gadon asibiti.

Ba'ana kuwa da tun Wazu ya iso, wani irin ihu yayi mai cike da farin ciki, da jin daWin yana ganin zaiyi abinda gaba ko kashe mutanen Rugar Bani sukayi gaba Waya, masarautar JoWa bazata kulasuba,
Wani irin tsuma da karkarwa jikinshi keyi sabida azabar muguntarsa dake tasowa.

ArWo Bani ma wani murmushi manufa yayi tare da cewa.
"To, ina gwanin naku?".
Cikin karaWi ?anzagi, ya kalli Jabeer tare da cewa.
"Malami ba faWen Allah, malamai magada annabawa, Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero JoWa, GARKUWAN sarki LamiWo, jikan sarki, mai martaba Nuruddee. Jarumin Masarautar JoWa."
Gimtse bakinshi yayi ganin wani irin kallo mai ma'anoni da yawa da Jabeer ke watsa mishi,
Cikin yin ?asa da murya tare da tsuke fuskarsa, ya Wan ron?ofo kanshi, kusa da LamiWo murya a kausashe yace.
"Wannan tatsuniyar da kukeyi, bafa koyarwan shariya bace".
Da sauri LamiWo ya katseshi da cewa.
"Eh amman koyarwar Masarautar JoWa ce".
Cikin kufula yace.
"Ya ina ce maka Allah kana cemin gadon masarautar JoWa ce".
Cikin haWe fuska da ?asaita LamiWo yace.
"Eh ba addini bane, kuma sai an yishi dan gadon masarautar muce".
Kanshi ya kuma motso dashi jikin kakan nashi cikin taSe fuska yace.
"Okay to ai sai ka tashi, ka tsaya su zaneka ciki da woje".
Cikin kausasa murya LamiWo yace.
"Kai ne dai zaka tashi".
Cikin watsawa kakan nashi wani kallo na lallai ma tsohon nan kanka ya kwance yace.
"Ai bani bane sarkin, kaine sarkin ko?".
Cikin faWa LamiWo yace.
"To ko Ubanka bai isa in sashi abu yace bazaiyi ba".
Jin muryar LamiWo ta Wan yi samane, yasa fadawanshi suka mi?e tsaye,
Ware rigunansu sukayi, suka kamgesu da jajayen rugunan nasu, ta yadda babu mai ganinsu,
Cikin haWe fuska Jabeer yace.
"Yesss shi bazai ?iba, tunda kai ubanshi ne, Ni kuwa babu wanda zai sani in zauna in bawa wani ?aton fatar jikina ya zane, kai jimin zancen son zuciya, kai ni kaWaine jikanka, a duniya, a nanma baga Ya Hashim ba ai shine babban jikanka, zancen gsky na gaji da wannan tirsashe-tirsashen naku, kanada ?a?an ai, ka kira Waya daga cikin ya'yan ka yazo ya wakil ceka mana, Amman ni dai kam Muhammad Jabeer babu wani tsohon da zanyiwa mubaya'a in tsaya wani gardin makiyayi ya Wimeni, tunda ba faWin Allah bane".
Ya ?arishe mgnar yana yun?irin tashi tsaye.
Da sauri Galadima yasa hannu ya kamo nashi, fuskar ya kwaSe tare da komawa zaune yana gyara hiramin kanshi da al'kyabbar jikinshi,
Cikin tausasa harshe Galadima yace.
"Jabeer kafa san ma'anar GARKUWA a masarauta."
Cikin sanyi da ganin kima da darajar dottijon Jabeer ya kwaSe fuska tare da cewa.
"Nifa shiyasa wannan mulkin bawai sonshi nakeyi ba, sabida wannan tsarabe-tsaraben daba na addiniba, a buwayi mutun dashi, yaya nasan abu ba Allah ne da manzonsa suka wajabta mana shiba, ace in zauna a cutar dani."
Cikin sanyi Waziri ke jujjuya mishi kai a hankali yace.
"Jabeer Garkuwa fa, kake dole ka kare martabar Masarautarmu kana ka nunawa su fulanin da kake Garkuwarsu kai Jarumine".
Rai a Sace ganin sufa da gske sukeyi, cikin dakiya yace.
"Bana so, ita wannan sarauta ta GARKUWAN FULANI ku bawa duk wanda kukeso, ni ban nemaba dama".
Shiru Haroon yayi dan gskya harga Allah shi wannan abun yazo masa a bazata.
Jalal kuwa cikin haWe fuska yace.
"Wannan ma ai zancen banza ne,
An bawa Ya Jafar Galadima, ko kwana ashirin baiba a kai, aka birkita masa rayuwa, kana yanzu kun likawa Hamma Jabeer wani GARKUWA kun kwasomu kun kawomu Rugar fulani, wai kuna cewa ayi gasar duka dashi."
Da sauri yayi shiru ganin Jabeer ya Waga mishi hannu.
Jamil kuwa tuntuni idonshi ke tsastsafo ruwan hawaye dan gani yake so ake a kashe Hammansu a ?arar da ?a?an Wakinsu,
Laminu kuwa Wan Gimbiya Saudatu matar bappansu Sheykh kuma Kani ga Yah Hisham wani irin dariyar jin daWi yakeyi.

Shi kuwa LamiWo, wayarshi ya zaro, Mai alfarma Sarki Jalaluddin ya kira wanda yake kane ga Jabeer. Wanda ya haifi Mamanshi.
Bayan sun gaisane yayi mishi bayanin abinda ke faruwa, jin haka yasa yace ya bawa Jabeer wayar.

A tsakar filin Rugar Bani kuwa, tuni.
ArWo Bani ya bada dama na suduka yana shekantawa gari cewa.
Ana gamgamin ShaWi yanzu-yanzu tsakanin Ba'ana da kuma jikan Sarki Nuruddeen.

Tuni an firfito da ganguna anata kaWe-kaWe da bushe-bushen sarewa, kana ana buga babban gangan dake tsanar da makotan Rugar Bani sauran rugage alamun za'ayi ShaWi yanzu.

Kafin kace kobo, Rugar Bani ta cika tayi ma?il da mutane, Maza da mata, matasa da tsoffi, sabida an san duk sanda za'ayi ShaWi ana bada sanarwar, kwana uku kafin nan to jin wannan na gaggawa kuma da jikan Sarki za'ayi yasa, mutane taruwa, gashi ranar jumma'ace, duk matasan rugogin suna, gida tunda suka dawo sallan jamma'a.
Rugar Bani ta cika tayi ma?il da bani adam, tako wacce kusurwa tsastsafo akeyi kusufa-kusufa.
Jin karan tamSarin ganganr ShaWi ne ya ?ara gaiyato mutane harda na cikin garin Shikan, tuni ?abilun Bonon sun garzayo cikin Rugar Bani.

Bukar kuwa mahaifin Ba'ana shida kanshi yaje, cikin Garkensu ya Wauko tukunyar tsumin bulalim shaWin da Ba'ana ke tsumasu da dafin kunamai da sauran sihirurruka, na dodon tsafinsu Bonon.

Matasa majiya karfi ne keta Webo ruwa, cikin rijiyoyin garin.
Suna ji?a taron wurin dandamalin, da za'ayi gasar kaWe-kaWen duk sun taru sun cika kunnen kowa.
Jabeer kuwa bugun da zuciyarshi keyi shiyafi komai tada mishi hankali.

A can cikin gidajen Rugar kuwa, duk yan samari da yara sun firfito.
A gidansu Shatu kuwa,
Tunda taji Shelan da Nasuduka yakeyi cewa gasar ShaWi tsakanin Ba'ana da jikan sarki.
Kuka ta farayi, cikin tashin hankali da kiWima ta kamo hannun Ummiy da tayi shiru sai ido take binsu dashi, murya na rawa tace.
"Ummiy kijifa, zasuyi ya kashe, wani wanda baijiba bai ganiba, sunfa san illar dake cikin bulalinshi."
Ganin Ummiy dai ba mgna zatayi ba, yasa ta kamo hannun Junainah cikin tsananin tashin hankali tace.
"Junainah ki gudu, kije kicewa Bappa kada ayi gasar nan, Ni dai a bari na ha?ura zan auri ya Ba'ana a yadda yake, zan zauna dashi, zanyi ?o?arin gyara mishi, rayuwa na gaji, kada a sake cutar da wani a kaina".
Da sauri Rafi'a ta kalleta jin ta kamo hannunta cikin zubda hawaye tace,
"Rafi'a wlh ya Ba'ana zai iya kashe mutun a kaina, da dafin kunamai yake tsuma bulalinshi, da wani tsafin, me ribata ayi ta cutar da mutane a dalilina, babu fa wani mahalu?in da zai iya cin Ya Ba'ana gasar ShaWi, babu wanda zai iya jurar azabar bulalinshi fa."
Cikin sauri ta mi?e tare da mi?ar da Junainah, sai kuma duk suka koma suka zauna,
Jin muryar ma?ocibsu Sarkin aska, yana cewa.
"A a Shatu kada ki tura kowa, kada kuma kije kin tsumayi sakamakon gasar yau in sha Allah zata banbanta da na baya .
Yanzu ma ArWo Bani ne ya aikoni da in gargaWeki."
Yana faWin haka ya juya da sauri ya fita, kana ya nufi wurin gasar.

Da ido suka bishi. Ita kuwa Junainah da sauri ta mi?a ta nufi kitchin Win su, tana cewa.
"Yauwa Adda Shatu, barin in kawo mana gasassun zabbin da Ya Ba'ana ya kawo mana muci.
?azu da nace muci Adda Rafi'a ce, tace mujiraki."
Cikin sanyi Rafi'a tace.
"Yauwa Junainah kawo mana, muci yau tunda gari ya waye bamuci komaiba."
Gyara zansu sukayi, kana ta kalli Shatu cikin kula tace.
"Dan Allah Shatu muci abinci, kinga Ummiy ma ta?i cin komai ganin, yadda kiketa kuka tunda kikaji Satansu ya GiWi da rasuwar Ya Lado da Inna."
Cikin zubda hawaye ta gyaWa mata kai, sabida ita kanta tasan tana jin wani irin masifeffen yunwa, tamkar zai kasheta.
Da sauri Junainah ta nufosu ri?e da akoshin gasassun zabbin da aka zuba dafin macijin a cikin.

A can cikin tsakiyar garin Rugar Bani kuwa.
Tuni su Ba'ana an gama shiryawa zalumci, domin dama ai a ?a'ida shi zai fara duka,
Yana tsaye sai zagaya filin yake yana zane iska, makaWa da mabusa nata yi mishi kirari.

A cikin wurin da Fadawa suka kange LamiWo da tawagarsa kuwa, anata kai ruwa rana da Sheykh Jabeer,
Cikin kufula, yake cewa Sarki Jalaluddin da suke waya dashi.
"Nifa babbar matsalarta wannan abun da za'ayi ba *Sunna* bace ba kuma *Farilla* bace, ba kuma *Mustahabbibace*, kai ko a babin *Makaruhi* ban taSa cin karo da wannan banzar al'adar da kukeso in yarda ayita dani ba,
Ina kuma da ya?ini in da zan bajeta a babin musulunci, kai tsaye za'a iya karhantashi, sabida ai cutar da kaine kuma, Musulunci bai yarda mutun ya cutar da kanshi ba, haka kurum kuce wai in tsaya a zaneni, inji shi kanshi kakan LamiWon JoWo da yaji haza a gasar ShaWin shine ya hana wannan al'adar a masarautarsa sannan yanzu ace za'a saketa a kaina bayan tsawon shekaru 145 ba'ayishi ba, tun zamanin jahiliyan ma an bar abu sai yanzu ku tara abu a kaina, to wallahi bafa zai yiwuba."
Cikin kufula Sarki Jalaluddin yace.
"To ya kakeso ayi Wan masu ilimi kowa jahiline sai kaine mai ilimi sabida tsabar tsoro da Wan karen son jiki kana gudun abinda zai taSa lfyarka shine zakayi ta jawo mana wasu dogin falsafofi, a hir Win kafa Jabeer ko uwarka bazan sata abu taimin musuba".
Gaba Waya sun hautsuna mishi zuciya,
Ji yadda suketa zageshi, dan kawai yace bazaiyi abinda al'adace ba addiniba sai wani ce mishi suke ko uwarka ko ubanka, bayan sun san baya kuran hakan, rai a Sace yace.
"Uwata kace ai tunda ita ai ka haifa ba niba ko?, zancen gsky bafa za'ayi wannan abunba, sun daWe basu ce mana lusaraiba, dolene, sai sun yarda mu fulanine, kai yau nifa ba bafulatani bane.
A kirani da ko wacce ?abilar ma in anga dama aikin kawai!".
Yana faWin haka ya katse kiran.
Laminu kuwa da yake cikekken Wan jarida, tuni yana naWe komai a faifai jawaban su.

Shi kuwa Sarki Jalaluddin, ido ya zubawa wayar jin jikan nashi ya katse kiran, murmushi yayi, irin nasu na manya, kana da sauri ya kira, Umaymah.
A can Babba birnin Katsina, kuwa Gimbiya Khadijah Umaymah kenan , wacce take matar Wan Sarkin Tsinako, Kekkyawar mata mai cikar haiba nitsuwa, tana kishinWe, bisa wata tattausar doguwar kujera, yayinda Hadimanta biyu ke mata tausa.
Jin wayarta na suwane, yasa ta buWe idanunta dake lumshe, tunda sukayi waya d, Wan ta Haroon ke gaya mata inda sukaje da ?a?an ?ar uwarta mafi soyuwa a rayuwarsu ne, taketa murmushi.
Ganin sunan mahaifinta ne yasa tayi saurin amsa kiran.
Bayan sun gaisane, Sarki Jalaluddin ya Wanyi murmushi cikin nitsuwa yace.
"Khadijah, kira Wan ki, ki bashi umarnin bin umarnin mu, domin yana nuna mana ai bamu muka haifeshi ba, bazamu tirsasashi ba".
Cikin tarin girmamawa tace.
"Ranka ya daWe, me kukeso in bashi umarni a kai nasan bazaiyi min musuba".
Cikin jin daWi yace.
"Kice dashi ya amince da gasar da za'ayi".
Cikin sauri tace.
"To An gama yanzu kuwa, in sha Allah zaku sameshi mai biyayya a gareku".
Daga nan sukayi sallama,
Kana ta kirashi, sau biyu tana kiranshi baya Wagawa, sabida kanshi ya Wau zafi yana ganin za'a tirsasashi ya cutar da kanshi.
Ga wani irin azabebben tsinkewa da zuciyarshi keyi,
Ji yake tamkar zata faso ?irjinsa ta fito, tayi ta tsalle a doron ?asa.
Gashi duk tsoffin Masarautarsun sun zagayeshi.
Kowa da abinda ke ce mishi.
Ga uban kiWen-kiWen dake hawa mishi kai.

Ita kuwa Umaymah ganin bai amsa kiran bane, yasa ta kira Haroon yana Wagawa tace.
"Ina Jazlaan bashi wayar".
Da sauri yace.
"To Umaymah uwar Garkuwa gashi nan ido ya raina fata".
Cikin barkwancinta da yaron nata tace.
"Kaci gidanku Haroon Ni Wana ba ragobane".
Murmushi yayi tare da cewa.
"To mu gani a ?asa mana Umaymah".
Yana faWin haka ya mi?a Jabeer wayar wanda yake cewa LamiWo.
"Bafa zan yiba, tsohon nan gwara ka mi?e kaje ayi da kai tunda kaine sarkin Masarautar JoWa, Ni nan babu abinda na sani bayan nonon uwata sai al'?ur'ani da hadisai, sai likitancin da kuka sani na karanta a dole badon raina yasoba, tun ina yaro kullum Ni a cikin sani dole kuke da tsabar rainin hankali, kaje a jibgeka, Ni kuwa nayi al'?awarin zan jinyaceka, LamiWo JoWa."
Ya ?arishe mgnar yana amsar wayar da Haroon ke mi?o mishi cikin faWa yace.
"Mitsss wai meye kaketa tura min wannan argar wayar taka ne?".
Cikin mamaki Haroon yace.
"Kan uba Jabeer wayar tawace ma arga, wayar da kuWi ta sun kai rabin million To inma argace Umaymah ce bisa layi".
Ba tare da ya kara wayar a kunneba yace.
"Hello Umaymah".
Cikin tausayi Jalal yace.
"Hamma Jabeer baka kai wayar kunneba".
Lips Winsa ya taune tare da cewa.
"Au, zama su sani yin abu da yawa".
Haroon kuwa mamaki yakeyi domin karo na forko kenan da yaji Jabeer yace Hello a madadin Assalamu alaikum, da shine abinda yakeyi.
Ita kuwa Umaymah tana jin ya kara wayar a kunne shi ya kira sunanta cikin rauni.
Murya a kausashe tace.
"Jabeer".
Da mamaki ya amsa dan sama da shekaru goma sha biyu kenan da Jazlaan take kiranshi, cikin sanyi yace.
"Na'am Umaymah". Cikin bada umarni tace.
"Jabeer ka tashi maza yanzu ka shiga fagen gasar nan ayishi da kai, bana son musu umarnine ba shawara ba".
Cikin sauri ya zaro siraran kyawawan idanunshi,
Dai-dai lokacin kuma LamiWo ya mi?e tsaye cikin tashin hankali da kiWima da firgici da ba?in cikin dakatar da gasar ShaWi da akayi a masarautarsu ya sani da anayi da Jabeer bazai ?alubanceshi ba, cikin sanyi yace.
"Zanje za'ayi dani, zan tabbatar da darajar masarautatarmu bata rusheba."
Da ido yabi Dottijon kakan nashi wanda a ?alla ya kai shekaru 91 a duniya.
Cikin kauda kai yace.
"To Umaymah yadda kikace haka za'ayi amman bari in kira Sheykh Abdulkareem in sanar mishi in ya amince dai zanyi".
Da sauri tace.
"A a ban yafe ka kirashi ba, wato don kasan in ka kirashi zai kira Sitti da Mai alfarma Jalaluddin da Sarki Nuruddeen ya dakatar da duk abinda za'ayin, tunda na san cemishi zakayi ba addini bane, al'adace, to ban yardaba maza tashi".
Ganin Ya Hashim na mi?a masa wayarshi ne yasashi cewa Umaymah.
To cikin sanyi.
Yana amsa wayar da Ya Hashim ya mi?a mishi yaki Muryar, mahaifinshi cikin sanyi da kuma alamun yana kukane yace.
"Jabeer ashe har kayi girman da LamiWo zai umarceka da yin abu ka?i yi mishi mubaya'a,
Ashe har na haifi Wan da zai ja da mahaifina."
Cikin sanyi da rauni yake jujjuya kai murya na rawa yake cewa.
"A'a Abba, kayi ha?uri kada kayi kuka a kaina."
Bai kulashiba yaci gaba da cewa.
"Jabeer Ashe zuciyarka har tayi tauri da kangarewar da kanaji kana gani za'a daki mahaifina a gaban idonka, bazaka zame mishi GARKUWA ba, Jabeer wannan shine tukuicin tsantsar son da mahaifina keyi muka, wanda har ya jazamin ?iyayya a wurin yan uwana sunaga ya fifitaku kan sauran jikokinsa Especially ma kai Jabeer komu daya haifa baya nuna mana son da yake nuna maka, shine zaka bari a dakeshi mutun mai shekaru 91 da Waya a duniya kai me shekaru 30 bazaka iya zame mishi GARKUWA ba?".
Cikin rauni da ?unar zuciya, ya mi?e tsaye hannunshi yasa ya kamo na LamiWo cikin tarin ?una da zafin rai da takaici yace.
"Na Amince, zanyi gasar na yarda, ka koma ka zauna".
Wani irin farin ciki ne ya ziyarci, zu?atansu gaba Waya, sai dai kowa da irin manufar farin cikinsa.

Jin haka yasa fadawan janye labulen da sukayi musu.
Shi kuwa LamiWo hannunshi yasa ya kamo hannun Jabeer, cikin tsantsar farin ciki da al'fahari da ?asaita ya fara taku, suna ratsawa cikin taron.
Kana fadawansu na biye dasu a baya.
?anzagi yana.
"Takawarka lfy Sarki mai daraja LamiWo Wan LamiWo jikan JoWa. Gyara kimtsi".
A haka har suka isa cikin asalin dandamalin da aka ji?ashi jilak da ruwa, sabida hana ?ura wanzuwa.

Gaba Waya taron mutanen wurin maza da mata manya da yara, Jabeer suka zubawa ido, sabida duk wanda ya ganshi yaga sahihin Balarabe, mai kamala da nitsuwa, uwa uba kima da haiba, ?warjini shi ya cika dukkan idanun magautanshi dake wannan yanki,
yayinda masoyanshi ke taraddadin abinda zai faru.
A tsakiyar filin suka tsaya, hannunsu dake ra?e dana juna LamiWo ya Waga tare da fuskantarta gabas, kana ya juya yamma, ya kuma juyawa kudu da Arewa, sannan suka dawo tsakiyar filin,
Cikin ?asaita, yace.
"Ga GARKUWAN FULANI, kuma daga Wannan nasarar da zaiyi a gasar nan,
Zai tabbatar GARKUWAR Masarautar JoWa, GARKUWA kuma mai ikon zama inda yaso a

35 / 72