Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   63 / 72

186K to 189K   out of 214K words

ki bar manya suyi mgna ba irinki ba".
Murmushi Umaymah da Aunty Hafsat sukayi dan sun san tsamarsu.
Kuma suna masifar shiri.
Ammi suke kiranta ita Aunty Rahman.

Jazrah kuwa hakanan take jin daWi in ta ganshi.
Shiyasa taketa murmushi.
Haroon kuwa girarshi ya Wagawa Jannart tare da cewa.
"Wai auren ya kusa ko?".
Cikin jin kunyar Umaymah tace.
"Ban saniba."
Haka dai sukaci gaba da tafiya.

Washe gari da safiya.
Duk kan al'amur musulmai na duniya suna farin ciki da ranar salla.
Manya da yara tsoffi maza da mata duk anata shirin zuwa idi. A dukkan ?asashen duniya a ko wani sa?on da suke da musulmai.

Hakace ta kasance a ?asashen Afrika ma.
Wanda ciki ?asar Nigeria yake.
Tun daga idar da sallan asuba.
Saratu da Larai sukazo.
Nan suka samu Ummi da Shatu suna kitchen.
Its Ummi fura take kirSawa mai Wan karen laushi da ?amshi yaji sugar.
Ita kuwa Shatu dakkeren Couscous tayi, dambu inji hausawa.
Bayan sun gamane suka killace shi gefe.

Kana ita Shatu. Ta haWa kajin nan tayi Pepper Checken mai Wan karen kyau yaji jajjagen taruhu da al'basa mai yawa ga kayan Wan-Wano dana ?amshi sunji komai yayi maWau.
Su Sara kuwa robobi ta mi?o musu, suka rin?a mulmula gumbar nan manya manyan mulmulellen masu kyau sai she?i da ?amshi gumbar keyi, dakkeren kuma a robobi Ummi ta rin?a zubasu.
Hibba ce data shigo tare da kuloli a hannunta tace.
"Wow Aunty Shatu lallai yau masarautar JoWa zata amsa sunanta masarautar FulSe zata kuma gane an auro mata cikekkiyar ba fulata, gsky tsarin yayi kyau".
Cikin jin daWi Ummi tace.
"Gsky nima naji daWin wannan abu.
Dama ace ko wanne yare ranar salla tayi abincin da yarenta keyi ta rabawa ma?ota.
Hakan zaisa asan cimar juna, kuma yasa aci abincin salla da marmari, amman kayan haushi duk sai a tafi kan shinkafa taliya masa, da dai ire-iresu.
Su kuma akeci kullum".
Murmushi Shatu tayi tare da cewa.
"Ha Ummi ai yanzuma sai nayiwa su Jalal koda dafadukan taliyace, nasan zasuce wannan ai sai mu".
Da sauri Hibba tace.
"Tab wlh Aunty Shatu karkiyi komai, kinga yanzuma an kawo abincin gidan Barrister Kamal.
Ga kuma na gidan Aunty Juwairiyya.
Sannan kuma Gimbiya Aminatu ma zata aiko".
Cikin sauri tac???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?e.
"Allah ko Ummi mu huta kawai kenan?".
Da sauri tace sosaima.
Dan duk yawanci sai an kawo abinci nan wai tunda ke ba?uwace, wannan karamawar masarautar JoWa akan bago.
Kuma koda kin dade ana aikawa juna abincin salla part 2 part".
Ajiyan zuciya ta sau?e tare da cewa.
"Shike nan mu haWa wannan a kai ko wanne sashin".
Ta ?arishe mgnar tana rufe ?atuwar Foodflaks Win da ta juye Pepper Checken Win.
Bayan ta Webawa sashin Ya Jafar da kuma LamiWo da Hajia Mama.

?ananan robobin da a ?alla suma nonon dake cikinsu zai kai kwanon sha Waya da rabi ta fara firfitarwa.
Kana ta fito da madaidatan ?oren da zasuci kwanon sha biyu da kaWan sai manyan da sukaci kwanon sha uku da rabi-rabi.
A hankali ta jerasu kan table Win dake tsakiyar kitchen Win.
A hankali ta buWe ?waryar forko dake gabanta.
Wani irin murmushi tayi tare da cewa.
"Alhamdulillah kunWirmo ya konta yayi bacci yayi kyau".
Le?owa Ummi tayi tare da buWe na kusa da ita.
Nonon yana konce yayi lib ya daskare yayi fari ?al-?al sai alamun mai?on man nonon da yayi Wan yellow-yellow kaWan.
A hankali suka fara bubbuWe fefeyayen tsakan zaren taburma da aka rufe ?oren dashi.
Gaba Waya duk sun konta sunyi kyai
Yan madaidai robibin da akasa take Wauka na fura Waya na dakkere Waya sai na sugar Waya kana da ludayin duma. Sai ta jerasu kan fefeyayen da robobin.
Ganin haka yasa Saratu da Laraima suka matso suna taya.
Har saida ta jerasu kab. Gwanin sha'awa.
Manyan ?ore biyu ta maida cikin Fridge.
Kana ta irga sauran tsakanin manya da ?ananan
?oren da robobin su
Talatin da tara
Juyowa tayi ta kalli Ummi tare da cewa.
"To Ummi gashi mun gama ki gaya musu duk inda zasu kai.
Zasu isar ko".
Cikin jin daWi Ummi tace sosaima kuwa harma da sashin bayi zai isa sabida part-part talatin garemu a cikin masarautar JoWa.
Sai sashin bayi part takwas.
Cikin jin gamsuwa da tsarin Shatu tace.
"Yanzu a kai ?ore biyu sashin LamiWo kana duk manyan iyayen Sheykh akai musu kwarya WaWWaya, sai sashin Ya Jafar kinga manyan ?oren sun ?are sai abin na tsakiyan a kai sauran sashin ?a?ansu robobin kuma akai sashin bayi".

Haka kuwa akayi su Sara suka fara rabawa.
Ita kuwa Ummi ita da kanta da Hibba suka kai na sashin Gimbiya Aminatu.
Kana suka dawo da kuloli har uku na abincin sallan da Gimbiya Aminatu ta basu.
Kana Waya daga cikin tace na Sheykh ne a ajiye mishi.
Koda suka dawo samu sukayi su Saratu sun gama rabawa kab.
Kamar yadda Ummi ta tsara.
Har sun tattare ko ina sun gyara sun share sun goge sun tafi.
Zuwa lokacin kuwa gaba Waya kan dinning table Winsu cike yake da Foodflaks iri da kala abinci kala-kala.
Wani irin kallo Shatu tayiwa kulolin kana tayi murmushin da ita kaWai tasan ma'anarsa ta juya ta nufi tsakiyar falon.

A gaggauce sukayi wonka kowa yayi shirin idi.
?arfe tara saura kwata duk suka fito falo.
Tuni lokacin kuma liman har ya fara huWuba.
Su Jalal, Jamil Ya Jafar suna tsaye cikin shiga ta al'farma.
Karon forko dataga manyan kaya a jikin Jalal.
Sai kamanninshi da Hamma Jabeer Win nasu ya fito sak-sak kamar an tsaga kara hatta rashin yawan dariyarsu iri Waya ne.
Sai dai shi Sheykh ko yaushe zakaga lips Winshi na motsawa yana tasbihi saSanin Jalal da zaka ganshi baki a tsuke.

Hibba ce ta fito cikin tarin farin ciki da son Jalal yayi murmushi tare da cewa.
"Masha Allah ya Jalal kayi kyau kafisu duka".
Ya Jafar dake karatu kamar ko yaushene ya kalli Shatu da Hibba da sukayi shigar atampa iri Waya da manyan hijabai har ?asa ga sallaya da carbi a hannunsu sunyi matu?ar kyau, murmushi yayi musu kana ya juya yayi gaba.
Jamil ne yace.
"Aunty Shatu sai mun dawo, in munci abinci sai mu sharewa.
Oga, Dr, Garkuwa, Malam, akarmakallahu, Sheykh, mijin Sayyada, Win Wakinshi".
Dariya sukayi dukansu yadda ya jero masa sunayen nashi.
Ummi dake cikin shiga ta al'farma ta mi?a tare da cewa mu tafi.

Suna fita suka rufe ?ofar.

Suka tafi masallacin. Masarautar JoWa Wan yin sallan idi.
Suna fita su mata sukayi gefen mata su kuwa maza sukayi gefen maza.

Bayan an idar da sallane kuma sai suka zagaya suka shigo ta asalin ?ofar sukayi yadda sunna ta koyar.

Suna dawowa kuwa a falo suka zube nan sukaci suka sha sukayi
hani?an.


A dai-dai lokacin kuma su Sheykh dama sauran al'ummar Annabi duk an sau?o sallan idi.
Suna Wawafin ban kwana.
Sosai Sheykh ke baza ido ko zai sake ganin wancan mutumin amman ina hakan bai samuba.

Koda suka fito daga Wawafin ban kwana.
Kai tsaye gidan Sheykh Abdulkareem suka wuce.
Nan yayi musu addu'o'in komawa lfy.
Kusan duk ba?in gidan a ranar suka bar gidan.
Da su Aunty Hafsat ma ranar suka juya Masco hakama Ibrahim.
Koda suka iso Airport kowa da inda ya nufa.
A nan Ibrahim ya ruggume Sheykh tare da Wan dukan bayanshi yace.
"In Sha Allah Auren Haroon dani za'ayi".
Shima Sheykh ruggumeshi yayi gam-gam tare da cewa.
"Allah yasa, ina kewar rashinka a ?asar mu".
Aunty Rahma ne tace.
"Kai jirgifa ba jiranku zaiba oga Sheykh".
Sakin juna sukayi kana kowa ya nufi inda jirgin ?asarsa yake.

Bayan duk matafiya sun shiga, jirgin ?asar Nigeria wanda zai sau?a jihar ?adamaya.

A hankali ya zauna.
Ya Hashim na gefenshi.
Kasan cewar yana kusa da window ne, ya Wan juya yana kallon mutanen daketa hada-hadar nufar inda jiragan ?asar su jihohinsu suke.
Can cikin wasu ayarin mutane maza da mata ya hango wannan fuskar da ya gani.
Sun nufi can ciki suna tafiya yankin da jiragen ?asar Cameroon suke.
Cikin tarin mamaki ya bishi da kallo tabbas badon jirginsu ya fara ?ugin tashiba da ya fita yaje ya tabbatar da fuskar dattijon da yake hangowa.

A haka dai suka Sacewa ganinshi.
Kana jirginsu ya Waga zuwa ?asarmu ta haihuwa.

Ana gida Nigeria kuwa cikin Jihar ?adamaya a Masarautar JoWa.
Zaune suke a falon.
Shatu na waya da Junaidu nan yake ce mata,
Sun samu sau?i dukansu.
Ance za'a sallamesu bayan salla.
Kuma harda Winkunan kayan salla akayi musu.

Bayan sun gama waya da shine ta kira Rafi'a.
Nan suka gaisa har ta bawa Ummi su gaisa.
Bayan ta bawa Ummi wayarne.
Jamil ya Wan kalli agogon hannunshi a hankali ya mi?e tare da kallon Shatu yace.
"Muje mu gyara Side din boss kar ya dawo ya samu da datti".
Kai ta gyaWa mishi kana ta amshi wayarta da Ummi ke mi?a mata.
tare da ce mata.
"Eh dan Allah Shatu tashi maza-maza kuje share wurin da kyau".
A hankali ta mi?e tare da cewa.
"To."
Hibba ce ta bisu a baya.
Jamil na gaba ita Shatu'n tana tsakiya.
Hibba na bayanta.
A haka suka shigo falon. Da komai na ciki yake fes-fes babu wani daddi ko ?ura ko hargitsewa, sabida an share falon safiyar yau, sai ?amshi da sanyi ke tashi.

A hankali Jamil ya Wan sa hannunshi tsakanin ziri-zirin igiyoyine masu sarkafe da jeren duwatsu masu she?in Daimond dake matsayin labulen Dinning area Win shi.
Ita dai Shatu ido ta zuba mushi,
ganin ya zaro key Win a cikinsu.
?ofar bedroom Win ya nufa tare da cewa.
"Muje."
To sukace kana suka biyo bayanshi.
Tana nazarin wurin da suke ajiye key Win.
Key Win ya saka cikin raminshi tare da murzawa.

Da sauri Shatu ta rumtse idanunta.
A hankali take jin zuciyarta na harbawa da sauri-sauri.
Shi kuwa Jamil tura ?ofar yayi bayan ya murWa key Win ya buWe.
Wani irin masifeffen harbawa da azaban ?arfi zuciyar Shatu tayi.

Kutsa kai cikin Jamil yayi.
Tare dasa hannunshi jikin ginin a hankali ya kunna wutan Wakin hasken ya gauraye ko ina,
jikin window ya wuce ya yaye labulen tare da buWeglass Win.
Iskam cikin Garden Win dake bayan window wanda Wawisu yake ciki.
Ya buso Wakin.

Juyowa yayi ya kalli Shatu da ke tsaye bakin ?ofar.
"Ku shigo, in nuna miki yadda zakiyi mishi".
A hankali Hibba ta ratsa gefenta tare da cewa.
"Aunty Shatu mushiga".
Ido ta buWe a hankali tare da bin bayan Hibba da kallo.
Kana ta Waga ?afarta da kyar ta.
Taka cikin Wakin, wani irin azabebben sarawa kanta yayi tamkar ana buga mata guduma a tsakiyar kan.
Cikin rawan ?afa ta Waga ?afafuwan ta,
Tayi taku huWu zuwa biyar.
Ta kusa isa tsakiyar Wakin.
Kenan.
Wani irin jujjuyawa taga kanta nayi.
Wasu irin ababe masu ban tsoro ta fara gani suna gilmawa cikin ?wayar idanunta, shiyasa taketa jujjuya kanta.
Ta kalli gabas ta kalli yamma ta kalli kudu ta kalli arewa.
Hibba ce ta juyo tana kallonta jin Jamil nata mgna bata bashi amsaba.
Cikin sauri ta matso kusa da ita ganin yadda taketa jujjuya kai, ga idanunta da suka juye suka zama kamar harari garke, kana sai Rollin ball eyes Win ta take da sauri-sauri.
Cikin Mamaki Hibba tace.
"Aunty Shatu! Aunty Shatu!!".
Shiru ba amsa hakane yasa.
Jamil juyo kanshi ya kalli inda suke, da sauri ya juyo gaba Waya jikinshi ganin.
Wani irin karkarwa da jikin Shatu keyi.
Hibba kuwa da ?arfi cikin tsoro tace.
"Aunty Shatu lfy kuwa?".
Ita kuwa Shatu, zuwa yanzu bata jinsu bata kuma fahimtar me suke faWa hankalinta ya juye.

Cikin wani irin layi da rawan jiki tamkar mazari ta nufi tsakiyar Wakin.

A nan ta tsaya gis gaba Waya jikinta karkarwa yakeyi.
Cikin tsananin tsoro da firgita.
"Hibba ta juya a guje tana cewa.
"Wayyo Ummi! Ummi!! Ummi!!! Kizo zakiga yadda Aunty Shatu keyi."
Ummi dake falo ita da Aunty Juwairiyya,
Kamar daga sama suke jiyo muryar Hibba tana rabka musu kira cikin firgici da razani.
Haka yasa Ummi da Aunty Juwairiyya mi?ewa da sauri suka nufi corridor'n da suke jiyo muryar Hibba na fitowa.
KiciSis sukayi a bakin ?ofar falon.
Cikin sauri Ummi ta ture Hibba ta wuce da gudu ta nufi cikin Wakin.
Sabida jiyo muryar Jamil na cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahuwani'imal wakil. Ummi! Ummi!! Kizoooo".
Kusan a tare Ummi da Aunty Juwairiyya suka shigo.
"Dai-dai lokacin kuma rawan da jikin Shatu keyi ya tsananta.
Wani irin kuka tasa tare da tafiya ?asa luuu zata faWi

Kusan a tare Ummi da Aunty Juwairiyya suka tarota.
Bisa jikin Ummi ta faWi hakan yasa itama Ummi tayi ?asa ta zauna.

Babu abinda suke maimaitawa sai innalillahi wa innailaihi rajiun.
A kiWime cikin tsananin gigita Jamil yace.
"Subahanallahi Ummi ta sumafa".
Jiki na rawa Aunty Juwairiyya ta juya da gudu babban falon ta fito tare da Wauko goran ruwan sanyi.
Kana ta juyo a da sassarfa ta nufi can.

Hibba kuwa a gigice take gayawa Jalal da Ya Jafar abinda ke faru.
Da sauri ya Jafar ya tashi ya nufi can.

Jalal kuwa ya zauna dan ya lura Hibba tayi masifar tsorita.

A Wakin nashi kuwa,
Shiru ta lafe jikin Ummi kamar babu rai koda.
Ummi ta yayyafa mata ruwan sanyi a fuskarta, a banza saida ta kuma watsa mata a karo na uku ne.
Kafin taja wani dogon numfashi cikin sanyi da tsoro Ummi tace.
"Alhamdulillah".
Sai kuma ta sunkuyo kanta tana Wan kiranta.
"Shatu! Shatu!! Shatu!!!".
Ba amsawa kuma bata buWe ido ba,

A hankali ya Jafar ya zauna gefensu, karatun da yakeyi yaci gaba dayi.

Cikin sanyi ta buWe idanunta.

Sai kuma ta yun?ura a hankali ta tashi zaune.
Da sauri Ummi ta zaro ido ganin yadda idanunta suka juye a murWe.

Ita kuwa Shatu mi?ewa tsaye tayi, cikin rawan sanyi da karkarwa, ta fara zagaya Wakin a hankali taje baki Bathroom nanma buWe ?ofar tayi ta shiga.
Jim kaWan ta fito.
Idanun suna yadda suke sai dai.
Yanzu hawayene keta shatata babu ?a??autawa.
A hankali tazo bakin gadon.
Sai kuma kawai sukaga ta faWa kan gadon a sune!
Wannan shine tashin hankali da ba'a samishi rana.
Da gudu suka kumayi kanta, cikin firgici da tsananin tsoro Ummi ta ?ara yayyafa mata ruwan.
Amman shiru, haka suka tsaya cirko-cirko, shi kuwa Ya Jafar sai gashi yana karatu yana kuka kamar dai yadda yakeyi kafin a auro Shatu a masarautar JoWa in Sheykh baya nan.

Gaba Waya sun birkice sunma rasa me zasuyi.

Aunty Juwairiyya kuwa itama kuka ta farayi.
Jiyo kukanta da na Ya Jafar ne yasa, su Jalal da Hibba shigowa.
Ganin tana can yashe kan gado a sumene yasa Hibba ma kuka.
Cikin ?arfin hali Jamil yace.
"Aunty Juwairiyya Hibba kada kuyi kuka, kuja hankalin mutane nan.
Gashi yau salla ba mamaki akwai mutane a cikin Garden."
Cikin tashin hankali Ummi tace.
"Bari inje in sanarwa Gimbiya Aminatu abinda ke faruwa, ta sanarwa LamiWo, sai in biya in sanarwa Hajia Mama."
Da sauri Aunty Juwairiyya tace.
"Eh yafi kam".
Ta juya zata fita kenan sai sukaji tayi wani irin nakasheshen dogon numfashi mai sassanyan sauti.
Da sauri Ummi ta juyo ta dawo jikin sanyi tace.
"Shatu! Shatu!! Shatu!!!".
Shiru babu amsa sai binsu da ido tayi Waya bayan Waya.
Ganin hakane Jamil ya matso.
Tofi ya farayi mata.

Ummi kuwa ci gaba da kiran sunanta tayi.
Cikin tsoro Hibba tace.
"Ummi kinga idonta ya koma dai-dai."
A tare sukace Alhamdulillah.
Sai kuma Ummi ta kuma kiranta.
"Shatu!".
A hankali tace.
"Na'am Ummi".
Sai kuma ta kalli inda take, kana ta juya ta kallesu baki Wayansu, cikin mutuwar jiki ta yun?ura ta tashi.
Murya a sanyaye tace.
"Jamil sharan kenan ka tsaya kanata kallona.
Gaya min ya za'ayi sharar".
Cikin sau?e tagwayen numfarfashi suka kalli juna,
Cikin mamaki Jamil yace.
"No ki huta kawai my Aunty zan share".
Bata da ?arfi a jikinta ko ta dage tace sai tayi sharar.
Bazata iyaba jikinta duk a mace.
Hakane yasa tace to.
Hannu ta mi?a Ummi tare da cewa.
"Ummi Wan jamin hannuna mana".
To tace tare da kamo hannun.
Ta tsaida ita, cikin tafiyar sanWa ta juya ta nufi hanyar fita.
Binta sukayi a baya gaba Wayansu.

Jamil kuwa dube-dube yayi a cikin Wakin kana.
Ya fara tattarewa da kimtsawa da sherawa, ya canza mishi beshit and blanket, da rigunan pillows.
Kana ya goge ko ina fes
Sannan ya shiga bathroom ya wonke ya goge mishi.


Su kuwa suna biye da ita har falonta.
Ganin ta wuce bedroom Winta ne yasa Hibba da Juwairiyya suka tsaya.

Ita kuma Ummi tabi bayanta.

Ganin tana shiga ta hau gado ta kwanta ne a take sai bacci yasa Ummi ta juyo ta fito.


Can babban falon suka koma suka zauna.
"Ikon Allah sai kallo wannan abu da ban tsoro da ban mamaki".

Ummi ta faWa cikin al'hini.

Jiki a mace Aunty Juwairiyya tace.
"Sosai kam wannan al'amari ya firgitani".
Hibba dai sai zuru-zuru tayi da ido.

Nan sukayi ta mamakin wannan abin.

Jamil na fito shida Jalal suka tafi.

Shi kuwa Ya Jafar bayan matarsa yabi suka tafi.


Hibba kuwa da Ummi nan suka zauna.
Ummi ce ta kalli Hibba tare da cewa.
"Sai anjima zan kira Umaymah na sanar mata abinda ya faru".

Kai kawai Hibba ta kaWan mata.

Ita kuwa Shatu baccin tayi mai nauyi sai kiran sallan azahar ne ya tasheta.

Su Sheykh Jabeer kuwa suna can sunata keta hazo.
Tafiya awa huWu ne zai kawosu ?asar mun.

A hankali ta buWe idonta, mi?a tayi tare da yin salati.
Kana ta tashi zaune.
Bathroom ta shiga, wonka tayi da ruwan Wumi.
Kana tayi al'wa tana fitowa.
Ta zura Hijabi tayi salla.
Bayan ta idarne, ta zauna gaban dreesing mirror.
Simple makeup tayiwa fuskarta.
Sannan ta sauya shiga, wani tattausan lace mai Wan karen kyau da tsada tasaka duguwar rigace tayi cib-cib da jikinta. Kasan cewarta kalar pink guava da Wigo-Wigin mint green ne yasa tayi masifar dacewa da kalar jikinta.
Gyara gashin kanta tayi ta tub?eshi tare da kitsen jelar.
Ta saketa bisa kafaWunta.
?aurin asseta tayi ya zauna Was a kanta, tattausan gyale minti green color ta yafa a kafaWunta.
Kana ta fesa turarukan ta masu daddaWan ?amshi.

Sosai jan lallen gargajiya dake kan ?an fararen yatsun hannunta yayi masifar kyau.
Ga kuma zanen da akayi a saman hannun hakama ?afafun ta, suma sun sha zanen jan lalle tayi kyau sosai,
Ta fito ras da ita.

Baki Wauke da sallama ta foto falon.
Cikin murmushi Ummi ta amsa sallamar tana mai kallonta,
Hakama Hibba da Ummi ta kokkontar mata da hankali taji tsoron ya ragu.
Gefen Ummi ta zauna, tana kallon Hibba na Waukarta hoto tana cewa.
"My Happiness Aunty kinyi kyau".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Na kaiki ne?".
Da sauri Hibba tace.
"Kin fini ma".
Murmushi ta kumayi tare da cewa.
"Ngd matu?a".
Sai kuma ta kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi me zamuyi abincin dare".
Cikin jin tausayinta Ummi tace.
"A a akwai abinci harda na gobe da safe ma, yanzu kam ki huta, sai dai in akwai abinda kikeso ki gaya min in yi miki".
Kai ta jujjuya alamar a a kana tace.
"To Ummi a kaiwa Hadimai wani abincin kada ya lalace a banza ko".
Cikin gamsuwa Ummi tace to.

A can Airport kuwa ?arfe uku dai-dai jirgin Ahlin masarautar JoWa ta sau?a.
Nan motoci suka kwatsosu.
Suna isa masarautar ana kiran sallan la'asar hakane yasa matan cikine kawai suka shiga cikin gida su mazan.
Masallaci suka wuce.
Ana idar da salla kuwa fada suka wuce baki Wayansu.


A sashin Gimbiya Saudatu kuwa wani irin dariya mai cike da masifar jin daWi tayi tare da cewa.
"Dai-dai kenan yaro zai dawo ya taradda da mummunan lbrin matarsa ta zama zautacciyar mata...!






By
*GARKUWAR FULANI*Cikin sassarfa bisa tsarin addinin

63 / 72