Garkuwa 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Romance

Chapter   67 / 72

198K to 201K   out of 214K words

ke Win me banbancin ki da zararrun".
Shiru yayi ganin yadda Shatu keyin taku a hankali cikin isa ta nufi gaban Gimbiya Saudatu.
Ummi da Hibba kuwa mi?ewa tsaye sukayi.

Shi kuwa Sheykh gyara zamanshi yayi tare da Waura ?afarshi Waya bisa Waya.

Ita kuwa Shatu a hankali ta isa gabanta.
Ido ta zuba mata tare da yi mata kallon tara saura kwata.
Cikin dakkeyar Muryar rashin tsoro tace.
"Toh *Bushiya* mai mugun baya, Bushiya mai bayan ?ayoyi masu kama da allurai, ki buWe idonki da kyau ki kalleni Ni AYSHA ALIYU GARKUWA ba sa'ar yinki bace uwar mahassadan duniya, in kina cin ?asa to tabbas ki kiyayi ta curi, ki bar min mijina ya sarara ki far masa rayuwa, Wan shi ba sa'an yinki bane ki bar min mijina ya huta baya son ihun nan da kikeyi mishi, zan kuma iyan komai dan ganin na kauda dukkan abinda baya so."
Wani irin daWi ne ya rufe zuciyar Ummi da Hibba Sheykh kuwa ?afarshi kawai yake kaWawa yana mai binta da wani irin kallo mai tarin ma'anoni kalmarta ta *Mijina* yake ji tana sa duk wani hudan gashin jikinsa na amsa amon kalmar yana ratsa jikinshi da zuciyarsa haka yasa bai san sanda wani yalwataccen murmushi ya subce mishiba, tabbas Shatu akwai ?arfin hali.
Ita kuwa Gimbiya Saudatu tsuru tai da ido.
Itako Aysha cikin karsashi tace.
"Na lura ke dabbace, sam bakya gane yarukan mgna na bani Adam, kinfi son sai an miki irin yarukanku na dabbobi.
Kina tsaye da farin yawu a bakinki kina zubda jini.
Yayinda wasu ke bayanki da jini a bakinsu suna fidda farin yawu.
Sokuwar rama mai tsami.
Ni nan da kike ganina da idona tar a buWe na shigo Masarautar JoWa, kada ki ganni haka Ni Wan hakine da zaki iya renawa amman tabbas zan tsole idanun magauta ruwanshi ya tsiyaye.
In kin san fullanci to.
*MIN MI KURORI CITTA NFAM?A NHEYAH* NI ```DAKKEN YAJIN BORKONE INYI KA?AN IN KUMA ISHI MUTUN```
Ki tsumayeni tabbas zanyi daka inyi tankaWe inyi rairaya a masarautar JoWa!.
Ke ko kallo baki isheni ba domin bata ke akeyi ba da manyan Magauta nakeyi.
Ja mugun bakinki ki fice min a gidana!".
Rab-Rab.

Jalal da Jamil dake da Jafar shigowa ne, suka tafa mata da hannu bibbiyu.
Hakama Hibba. Ummi kuwa ?asa tayi da kanta.
Shi kuwa Sheykh ?an?ance idonsa yayi yana kallonsu yana kaWa ?afa ya watsa idanunshi cikin na Gimbiya Saudatu yana mata kallon itama ta isheki.
Aunty Juwairiyya kuma da tun Wazu tana bakin ?ofar shigowa da sauri ta juya ta koma Side Win ta.

Ya Jafar kuwa sai murmushi yake tare da dun?ulawa Shatu hannunshi kamar haka=?M?
Wani irin juyawa Gimbiya Saudatu tayi tare da jan al'kyabbar ta ta fita.
Har taje bakin ?ofa Shatu tace.
"Ki ri?e kalmar mahaukaciya tabbas zakiga mahaukata a masarautar JoWa zasu baiyana bila'adadin."

Daga nan ta juya ta nufi Dinning area Win babban falon.

Ita kuwa Gimbiya Saudatu ta juya ta fita.

Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali ya sau?e ?afafunshi kana ya mi?a ya nufi falonshi.
Haka nan yaji murmushi na tsubce mishi.
Tabbas ya gamsu da ?arfin halin Shatu da rashin tsoronta, sai dai yana jiye mata tuggun mutanen da bata san halinsu ba.
Yana shiga yaci abinci kana ya shiga yayi wonka.
Kana ya Wauki wayarsa.

Jalal, Jamil, Hibba, Ya Jafar, Shatu kuwa zama sukayi a falon cikin mamaki Ummi tace.
"To wacece yar le?en asirin Gimbiya Saudatu a wannan sashin?
Ya akayi tasan abinda ya faru da Shatu?
Waya gaya mata?
Bayan in banda muyamu.
Ni Juwairiyya, Hibba, Jalal, Jamil, Jafar. Wanda shi baya mgna, ita kanta Shatu bata san meya faruba batasan ya akayi ba.
To waya fitar da wannan zancen a cikinmu?."

Cikin gsky da gsky duk suka ce wlh babu wanda suka taWawa mgnar Hibba harda ?ollarta tace.
"Wlh ita ko Umaymah ma bata gayawa ba".
To lallai kam akwai bu?atar bincike a tsakanin mu."
Ummi ta faWa tana mai cike da al'hinin abin.
Ita kuwa Shatu uhummm. Kawai ta iya cewa tayi shiru bata ce komaiba.


Haka dai suka tashi taron.

Sheykh kuwa, number Umaymah ya kira bayan sun gaisa ne yace.
"Uhumm Umaymah wai me kika sani ne ya faru da wannan yariyar shekaran jiya?".

Cikin tsoro da son kauda batun Umaymah tace.
"Wacce yarinyar kuma?".
Fuska ya Wan tsuke yace.
"Waccar yarinyar dai".

"To bata da sunane ita".
Ta kuma ce mishi.

Cikin gajiya da batun yace.
"To ni ba sanin sunanta nayiba, baku gaya min sunanta ba."
Wani irin murmushi Umaymah tayi tare da cewa.
"Ban gane bafa Jazlaan".
Hannunshi yasa ya Wan shafi sajenshi.
Yana mai son yasan meya sameta, meya faru da ita, shiyasa a hankali yace.
"Yarinyar dai da kike cewa Wiyarki!."
Kai Umaymah ta jinjina tare da cewa.
"Laah ni nama mance bamuyi mgnarba, ran sallane tayi aiki ta gaji tunda safe bataci komaiba to ashe tanada olsa shine fa, ta shiga Wakinka zatayi maka shara ta faWi ta suma, da kyar aka samu ta farfaWo suanta kuma Aysha".
?an gajeren tsaki yaja tare da cewa.
"Shirme in banda sakarci da raki mutun ya bar kansa da yunwa da gajiyan aiki mutun har ya suma". Ya ?arashe mgnar yana jinjina darajar sunanta a ranshi.
Cikin jin daWin bai tsananta bincike ba tace.
"Akwai wani abune?".
Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"Wannan mahaukaciyar Gimbiya Saudatunce tazo take cewa wai taji lbrin ta haukace".
Daga nan ya kauda zancen.
A hankali ya mi?e yana ri?e da wayar a kunne shi.
Dinning area ya nufa.
Murmushi yayi gano tabbas akwai abinda Umaymah ke Soye mishi.
Hannunshi yasa cikin zirin zirin igiyoyi masu duwatsu masu daraja she?in Daimond da sukayi Dinning area Winshi a madadin labule.
A hankali yasa hannunshin kan na'urar CCTV camera dake li?e a gefen inda yake ajiye key, wanda duk abinda za'ayi a falon zai gani.
Cikin sanyi yace.
"Uhummm Umaymah kiyi mata faWafa, ta dena hawan ?awara kan mutanen masarautar JoWa, ta kiyayi kanta da faWa da magautana zasu ilatata.
Bata san komaiba a kaina ta tsaya matsayin ba?uwa Umaymah zafa suyi mata illa".
Ya ?are mgnar a hankali.
System Winshi dake kan Dinning table Win ya jawo.
kana yaja kujera ya zauna ya fara haWa na'urar.
Ita kuwa Umaymah a hankali tace.
"To ya zatayi tunda ?addara ta kasantar da ita matsayin matarka, ko ita kurmace dole sai sun nemi yi mata illa sun sabautata.
Dole kasata cikin jerin mutanen da ka zame musu GARKUWA a masarautar JoWa, tunda ita dai matarka ce, amanarka kuma".
Shiru yayi yana jinta yana mai kallon fuskar System Winshi date Win shekaran jiya ya shiga.
ai kuwa Shatu ya fara cin karo da ita tana share falon da goge ko ina.
Sai kuma lokacin da suka shigo ita da Jamil da Hibba suka nufi bedroom Win sa.
A hankali yace.
"Uhmmm Umaymah sai anjima zan kiraki".
To tace kana ya katse kiran.
Ido ya zuwa System Winshi.
tsaki yaja karo na forko da yaji da ya haWa na'urar da cikin Wakinshi.
Gashi yanzu baya ganinsu sai dai ihun Hibba, da fitowa da tayi da gudu ta kira Ummi da yadda suka shigo da Aunty Juwairiyya.
Kanshi ya gyaWa lokacin da yaga sun fito a hankali ya rufe System Winshi.
Dafe kanshi yayi yana nazari.
Ya dade a nan sosai kana ya koma Wakin shi.

Da dare misalin karfe sha Waya na dare saura.
Shatu ta kalli Hibba dake konce tuni tayi bacci.
Yasa ta mi?a a hankali ta nufi Wakin Ummi.

A bakin ?ofar ta tsaya a hankali tayi sallama.
Cikin mamaki Ummi dake zaune bisa sallaya ta idar da shafa'i da wutri kenan taji sallamarta.
Juyowa tayi tare da amsawa tace.
"Shatu".
A hankali tace.
"Na'am Ummi".
Cikin mamaki tace.
"Lfy kuwa shigo mana".
A hankali ta shigo tare da cewa.
"Lfy lau Ummi, nazo wurinki ne."
"To".
tace tare da nuna mata wurin zama bakin gadonta.

A hankali ta ?araso kusa da ita,
Gabanta ta zauna kan sallayan cikin nitsuwa tace.
"Ummi kiyi ha?uri ko zakiyi bacci na hanaki".
Da sauri ta girgiza mata kai alamar a a.
Ajiyan zuciya ta sau?e tare da cewa.
"To Alhamdulillah".
Sai kuma tayi shiru.
A hankali Ummi tace.
"Kina bu?atar wani abune?".
Cikin nitsuwa tace.
"Uhum Ummi dama tambayarki nake son yi".
Gyara zama Ummi tayi kana tace.
"Ina jinki".
Itama zamanta ta gyara a hankali tace.
"Dan Allah Ummi in ba damuwa, dan Allah da Manzonsa ki sanar dani abinda Allah ya sanar dake a kan masarautar JoWa mana.
Ummi kaina na kullewa da mutanen masarautar JoWa, ban gane banbanci su da dankantakarsu da kuma. Ala?arsu ba".
Wani irin dogon ajiyan zuciya Ummi ta sau?e tare da cewa.
"To Shatu ai kin gama komai tunda kika haWani da Allah da Manzonsa.
Kuma dama nace miki ki tambayeni duk abinda baki gane ba, zan gaya miki. To amman akwai wani abun sirrine garesu masarautar in na faWa kamar cin amarsu ne, wani abun kuma nima kaina ban sanshi ba.
Hannun Ummi ta ri?e tare da zubda hawaye tace.
"Ummi gaya min yadda masarautar JoWa take ko zan san irin zama da takun da zanyi da mutane da Waukar mataki kan abinda ke faruwa".

A hankali Ummi ta gyara zamanta.
Ta jingina da jikin gado.
Kana itama Shatu ta gyara zamanta ya zama suna fuskantar juna da kyau.
Cikin sanyi Ummi ta fara bata lbrin.


*Masarautar JoWa*
tsohuwar masarautace.
wacce tun kafin zuwan Shehu Usmanu ?anfodiyo ?asashen Afrika tana kafe da ?afanta.
Kuma masarautar FulSe ce tun a wancan lokacin.

Lokacin da Shehu Usman ?anfodiyi ya iso nan ?asashen hausa ya basu musulunci ya kafa tutocinsa tako ina tako wacce masarauta.
A lokacin Masarautar JoWa sunanta masarautar FulSe.

Kuma lokacin Sarki Sule ne a kan karagar mulki. Baban JoWa kenan wanda yake shi JoWa shine kakan sarkinmu na yanzu wato LamiWo.

A lokacin sarki Sule yanada ?arfin mulki yana da mata huWu ?war-?wara biyar.
Allah ya azurtashi da arzikin yara a ?alla sunfi hamsin a cikin matansa huWu na aure.
Akwai wata Waya da ake kira Gimbiya sumaye ?ar sarkin kal'anace.

Gimbiya Sumaye inrin matannane da Allah ke jarabta da haihuwar wabi.
Bima'ana tana haihuwa kuma yaran na rasuwa.
A haka har ta haifi yara kusa goma kuma bata da rayeyye ko Waya.
Cikin ?war-?waran sarki Sule ne Waya ta Wauki Wanta na miji ta bata halak malak kwanan yaron uku a hannunta ya rasu.
Wata cikinsu ta kuma bata still shima kwananshi uku ya rasu.
A haka duk ?war-?waran sarki Sule saida suka bata yara suna rasuwa.
Daga nan uwar gidan Sarki Sule wacce take babarbariya ce.
Tasa mata suna cikin wasa na tsakanin Fulani da bare-bari amman a zahiri da gaske takeyi.
Gsky mai tafiya da wasa kenan.
Sai ta sawa Gimbiya Sumaye suna da fillanci wai
*?adamaya* ma'ana wai duk wanda ya matso kusa da ita zai mutu, ko wanda ya bata ri?on Wa kowa kwana uku ne mutuwa zaiyi.
Kamar da wasa sunanta ya zama Gimbiya ?adamaya.
Mutanen masarautar akayi ta mata izgili da habaici.
Takan zauna tayi ta kuka.
babu mai rarrashi dan ita masarautarsu nada nisa a lokacin kuma babu ko Radio bare waya.

Anan Allah ya bata wani ciki ta haifi Wan ta namiji.
Akasa mishi suna Umar faruq.
Sai Gimbiya Sumaye take kiranshi da JoWa ma'anar JoWa shine zauna.
Da haka sai aka maida abun ba'a aka rin?a kiran yaro da JoWa.
Allah cikin ikonsa ta yaye yaro lfy lau.
Ta kuma haihuwa na goma sha biyu.
Yariyar watanta biyar ta rasu, sai aka rin?a mata dariya ana cewa saura *JoWa* shima ya *Dilli.*
Wato wai saura JoWa shima ya *tafi.*
Cikin ikon Allah kuwa ya raya JoWa ya girma.
Ya zama shine ?arami cikin ?a?an sarki Sule kenan.

Bayan wasu shekaru, sai Sarki Sule yace to shi zaiyi murabus, a cikin yayanshi yace zai naWa babban Wanshi Madu.
?an Gimbiya Falmata.
Sai ko sauran ?an uba duk suka tashi akece to sai ayi zaSen manyan.

To akwai Wan Madu wanda yake mai ilimin addini dana zamani sunanshi Bala, sai ya shiga cikin masu neman mulkin ya kafa hujja da cewa.
"Babanshi Madu jahiline dan haka a bashi shine ya dace da mulkar garin.
Haka kuwa akayi aka ba Bala mulkin masarautar FulSe.
Dole babanshi Madu wanda shine Magajin gari ya ?aura ya bar garin.
Tunda kinga bazai yiwuba ace yana mahaifinshi ya rin?a serving Wan shiba da ba?insa ba.

Haka dai Bala yayi mulki tsawon shekaru arba'in inda JoWa kuma yake matsayin Galadima tunda Wan tsohon sarki ne.
To shi kuma Sarki Bala sai Allah ya azirtashi da tarin ya'ya mata Wan shi na miji daya ne,
Sadik.
Ya bawa Sadik sarautan Sardaun.
Bayan wani lokacin sai tsoro ke rufe Sarki Bala kada fa abinda ya samu babanshi ya sameshi.
Wato kar Wanshi bai gaji mulkiba kamar yadda sarautar ta tsallake babanshi ta dawo kanshi.
To shinefa ya tura Wan shi Sadik wuraren sauran sarakunan ?asar, cewa zaiyi murabus zai bawa Sadik mulkin.
To dama bisa ?aida dole sai sarakunan sun yarda.
Cikin Sa'a kuwa duk sarakunan suka yarda sukasa hatimin amincewa a takardun.
To a kan hanyar dawowanshi ne kuma Allah yayi mishi rasuwa.
Wannan abu yayi masifar tada hankalin Sarki Bala.
Da mahaifiyarsa Gimbiya Salame, da kakarsa Gimbiya Falmata.
Saboda wannan pain Win mutuwar Wan nasa, shene ya tattara yaranshi mata kab ya Aurar dasu.
Harda ?ar shekara takwas duk ya kwashesu ya aurar.
Sabida wai baya son ya mutu baiga aurensu ba.
Ya musu aure ya kuma basu sarauta.
Suka zama hakimai."

Cikin sanyi Shatu tace.
"Tir?ashi duk wannan don son mulki ne?".

Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
"Uhum ai akan sarauta babu abinda ba'ayi sabida matsalar sai kowa yace shi Wan sarkine zai gada.
Sabida in basu gadaba sarautar tabar hannunsu, Shatu Sarauta masiface a zuciyar masoyansa da zasu iya komai a kanta."
Kai Shatu ta gyaWa tare da cewa.
"To Ummi ina jinki".
Gyara zama tayi tare daci gaba da cewa.
"To in takai ce miki a ?arshe dai JoWa shiya zama sarki wanda shine Wan ?aramin a ahlin Sule.

A lokacin ne kuma sunan jihar nan ya dawo ?adawaya sabida.
Nunawa duniya ba haka bane duniya Allah zai iya baka zai iya hanaka.
Masarautar FulSe kuma ta zama masarautar *JO?A.*
Sabida sunan sarkin kenan.
Kuna ya zama adalin sarki mai son ba?i duk inda ba?o yazo zai wuce.
Sai Sarki JoWa ya bashi wurin zama yace mushi JoWa wato zauna ga wurin zama kayi kasuwanci kayi kiwo ki ciya ka ciyar kasha ka shayar."
Shiyasa Jihar ?adamaya tayi zarra da tarin ?abilu sabida son ba?i da basu muhallin zama a wancan lokacin kawai fili za'a yanka a baka ka zauna in Kai ba?one

To babban Wan JoWa shine Bubayero wato kakan LamiWo.
Bayan JoWa ya rasune Bubayero ya hau kan karagar mulki masarautar JoWa.
Ahlin Gimbiya Falmata kuma suna yaWuwa suma buri da kwaWayin sarauta na ji?a a ransu duk burinsu suga yadda sarauta zata dawo Wakinsu.
To koda Bubayero zaiyi murabus ya bawa Wansa Nuruddeen mulki sai ya aurawa Wansa yar bappan shi jikar Madu Wanshi.
Sukayi aure aka naWa Sarki Nuruddeen da matarsa yakura.
Bayan anyi aurene da shekara biyu.
Ya auro wata ?ar masarautar su Gimbiya Sumaye.
To itace tazo ta haifi LamiWo.
Ita waccar bata taSa haihuwa ba.
To shima LamiWo sai ya auro yar masarautarsun Gimbiya Sumaye, wato Gimbiya Aminatu a matsayin matarsa ta biyu.
To Galadima da kike gani yanzu bappan LamiWo ne Wan autan su marigayi sarki Nuruddeen.

To shi kuma LamiWo da aka bashi mulki sai aka aura mishi yar zuriyar Gimbiya Falmata itace uwar gida.
Ta haifi Baba Basiru da Baba Nasiru da kuma Baba Kamal da kuma babban yayansu Marigayi Auwalu. Sai Dr Aliyu shi kuwa mamanshi daban itama ta rasu su biyu ta haifa da Gimbiya Surayyah.

To Mamansu Baba Nasiru.
Yanzu haka tana raye amman ta haukace babu mai shiga Side Winta, sai LamiWo da yaranta. Duk wanda yaje sai tace zatayi duka, ita da bakinta take bayanin Abbansu Sheykh da Gimbiya Aminatu da Gimbiya Aisha tayiwa asiri ya dawo kanta.

Galadima da yaga ya tsufane kuma baida Wa namiji da zai gajeshi shine.
Yacewa LamiWo ya naWan babban Wan shi Auwalu mijin Gimbiya Saudatu a matsayin Galadima.

To bayan ya naWa shi da shekara biyu ne, ya rasu.
To sai ya naWa Ya Jafar Win nan da kike gani a matsayin Galadiman Masarautar JoWa.
Lokacin lafiyarsa lau yadda kikaga Sheykh haka yake da ibada addini ilimi nitsuwa tausayi.

Kwananshi goma a kan mulkin washe gari za'a naWa shi ne, ya dawo haka babu mgna sabida wani babban ibtila'i da tashin hankalin Waya samemu.
Kuma a lokacin an kusa amishi aure sabida sarautar da za'a bashi.
To wannan shine babban mafarin hargitsi da kitimurmurar dake masarautar JoWa a yanzu.
Dan ranar da Jafar ya zama haka akwai babbar masifar data fi wannan muni daya faru a masarautar JoWa.
Shine abunda yayi masifar girgiza mutane.

Lokacin Sheykh yana saudia yana karatu a jami'atul Madina.
Hankalin Hajia Mama yayi masifar tashi tayi ta suma tana sakewa Umaymah kuwa da Sitti mutuwace kawai da basuyi ba, dan ba?in ciki da tashin hankalin Waya samemu.

To kuma tun daga nan sai duk magautan suka dena kiyayyarsu kansu Jafar da ?annensa.
Koda Jabeer yayi karatunshi a can yayi digirinsa na biyu da PHD dinsa duk a can.
Wani sabon tashin hankalin da Jabeer ya dawo LamiWo yabashi mulkin GARKUWAn FULANI, nanfa Magauta sukace zasu mutu.
Dan ma mulkin na gefen yaya mata aka bashi shine abin ya Wanyi sanyi.
To kuma ingiza gabar sunga Wawisun masarautar JoWa tayiwa Jabeer abinda sai sarki takeyiwa.

To kinji lbrin a ta?aice sai a hankali zaki gane komai in kina bin komai a hankali."
Numfashi mai sanyi Shatu ta sau?e tare da cewa.
"Ummi wacece Gimbiya Aisha?".
Da sauri Ummi tace.
"Baki santaba".
Da sauri Shatu tace.
"Toh ina take?".
"Bata nan". Ummi ta bata amsa a gajarce.
Da sauri Shatu tace.
"Ta rasu ne?".
Cikin zubda hawaye Ummi tace.
"Bamu san halin da take cikiba shine babban burin Sheykh a duniya, sanin inda take".
Cikin sanyi Shatu ta kauda waccar tambayar dan ko Ummi bata amsa mataba ita ta gane matsayin Gimbiya Aisha. Haka yasa a hankali tace.
"Allah ya baiyana ta. Ya cika mishi burinsa."
Amin Amin Ummi tace tana sharce hawaye.
Cikin nitsuwa Shatu tace.
"To Ummi mene kuma banbancin mulkin gefen yaya mata dana maza".

Cikin jin bacci tace.
"Da safe ki tambayi Hibba ko Jamil zasu gaya miki, yanzu jeki shiga dare yayi bacci nakeji".
Da haka tatashi taje ta shiga ta fahimci a duddun?ule Ummi ta bata lbrin Sarkin yanzu da matsalar dake faruwa.

Washe gari da safe, bayan sunci abinci.
Ummi ta mi?e dan taje tayi walaha, Hibba kuma ta tafi sashin Juwairiyya da tun jiya da safe bata sake shigowa ba.
Jamil ne ya shigo neman Jalal da sauri tace.
"Uhum yauwa Jamil zo mana".
To yace kana ya dawo ya zauna.
Cikin nitsuwa tace.
"Dan Allah in Wan tambayeka mana".
Jingina yayi da jikin kujera tare da cewa.
"To ba matsala Allah yasa na sani".
Wayarta ta ajiye kana tace.
"In sha Allah ka sanima.
Wai menene banbanci sarautar gefen ?a?an ?a?a mata, dana gefen ?a?an ?a?a maza".

Dariya yayi mai sauti tare da cewa.
"Uhumm kema kin shiga Masarautar JoWa cikin kitimurmuran yanayi ko kin ratso cikin ahlin da ba'a sonmu, kin fara fuskantar ?alubale ko".

Tashi yayi yaje ya sha ruwa kana ya dawo ya zauna

67 / 72